Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kan likitan, cikin yanayi na damuwa na nuna zak'uwa cikin hanzari suka k'araso a tare wajen likitan ,binafa ce tayi saurin cewa

"Doctor any good news?"...

Ajiyan zuciya Dr yayi ,a lokaci d'aya kuma fuskar shi ta sauya kamar Wanda ze sanar da mummunan albishir. Dikkan su jire ye suke suji daga bakin likitan ,ganin yayi shiru yasa suka fara yanke tsammani da zaton ko ba ayi nasara bane wajen aikin.
Murmushin Nasara likitan ya musu tare da cewa cikin harshen turanci

" ina taya Ku murna ,da yi muku albishir na cewa anyi Nasara a aikin, bugu da k'ari ma ciwon k'odan Allah yayi ikon shi ,Dan kuma bayan an gama tiyatan na sake masa gwaji se naga babu wannan matsalar ,sedai yanzu zamu d'ora shi akan magunguna ,se aci gaba da bashi kyaky-kyawan kulawa ,sannan ya dinga cin abinci me Gina jiki ,Wanda ze dawo masa da kuzarin sa cikin d'an k'ank'anin lokaci..."

Cikin murna da farin
ciki binafa ta bashi amsa da "mun gode Dr".

" Allah abun godia", likitan ya bata amsa cikin fara'a, kafin ya nufi office din shi.

Murna gun Hajiya da umma ba'a magana ,umma hannu ta d'aga sama tana me godia ga Allah. Binafa ce ta rumgume Hajiya ,tana cewa

"Hajiya ta kinji ko? "

Gyad'a kai Hajiya tayi cikin nuna jin dad'i ,tace
" shakka babu naji Fatima. Allah ya muku albarka baki d'aya ,Allah kuma ya raya mana zuri'a"...

Binafa da umma suka amsa da "ameen"

Nan suka shiga yiwa juna barka da azziki. Nan umma ta bassu ,taje gida Dan had'o musu abinci.
Misalin k'arfe 6 na umma ta dawo, lokacin ana gab da kiran sallan magriba. Seda sukayi sallah ,sannan umma ta zuzzuba musu abincin ,ba lefi kuwa sunci sun sha masha Allah. Wata kula binafa ta gani da ba'a bude ba ,tace

"Umma ! Miye wannan a kula" ?

Hararar wasa umma ta watsa mata tare da cewa
"Naki ya b'ata ne?. Naga dai cewa kinci kin k'oshi ko? To se Yaya kuma?"

Binafa tace
"Lah kaji umma ,to gaskiya ban k'oshi ba ,wannan da bakya son aci shi zan ci"
Bata jira me umma zata ce ba ,ta janyo kulan ta bud'e. Wani k'amshin dad'i ne ya daki hancin ta ,zaro ido tashi ta tana fad'in

"Woww !farfesun arish me kayan lambu ,kayan ciki da kifi taitos. Lallai zamu sha dad'i"... Janyo plate tayi tana k'ok'arin zuba wa ,umma ta fizge marfin kulan ta datse. Shagwab'e fuska binafa tayi tana cewa

" kai ummah! Kad'an fa zanci ba da yawa ba. Hajiya kice ta bari inci!"

Murmushin manya Hajiya karime tayi ,tace

"Yanzu rowar abinci za'a wa 'ya ta?"

Umma tace "to ai naga ba hajiyar ta ta dafo ta kawo ba. Ni kuwa d'ana na dafowa, taya ko zan biyewa wannan k'walmammiyar ta lashe komai"...

Dariya dikkan su suka sa ,binafa tace " lallai umma ,Wanda ko farkawa beyi ba! To aci lpia"

"Lpia ma za'a ci ja'ira".

Hajiya tace " kyale umma 'ya ta ,tunda abun na 'yan ubanci ne ,mu zuba ".

" yauwa Hajiya ta ta kaina. Muma zamu rama ai" binafa tace cikin sigar shagwab'a kamar wata k'aramar yarinya.

"Oho dai" umma ta amsa su a tak'aice. Hira suka d'an fara tab'awa sama-sama. Kafin wata nurse ta shigo bakin ta d'auke da sallama, gaida su umma tayi cikin ladabi ,sannan ta sheda musu Salim ya farka. Aida binafa da umma har rige-rigen tashi tsaye suke yi ,Hajiya ita dai jikinta yayi sanyi ta kasa ko motsi.
Sallamar nurse din umma tayi ,sannan tace "Hajiya tashi muje mu duba shi ko"

"Toh" shine kawai abunda Hajiya ta furta sannan ta mik'e jiki ba k'wari ,hannun ta umma ta rik'o ,a tare suka jero binafa na bin su a baya ,har suka kai d'akin hutun da aka kai salim.

Knocking umma tayi sannan ta tura k'ofar ta shiga tare da sallama. Salim dake kwance yana jin sallamar su seda gaban shi ya daki tara-tara .

'Kok'orin mik'ewa ya fara yi da Sauri umma ta k'araso ta taimaka masa ,nuni tawa binafa data k'araso ta d'ago kan gadon. Binafa tayi kamar yadda umma tace ,sannan ta samu kujera ta zauna.

Umma ce ta fara masa ya jiki ,sannan Hajiya, kafin binafa ta biyo baya. Sosai salim yaji dadin yadda suka yo ayari suka kuma nuna damuwa akan shi, dukda yasan ba aikin kowa bane aikin umma ne.

Hawaye ne ya fara sauko mishi, magana yake k'ok'arin yi ,umma ta dakatar dashi

"Ash-sha Ahmad ! Da girman ka, mu da muke mata muka daure se Kaine zaka yi ragwanta? To bana son jin komai ,kuma kayi gaggawan goge hawayen nan kaji d'ana !"

Jaka umma ta bud'e ta d'auko anki ta bashi


Murmushin jin dad'i salim yayi ,sannan yasa hannu ya karb'a ya goge fuskar shi. Tea umma ta had'o masa me k'auri ta bashi ,aikuwa kamar Wanda akawa yasa ,ya shanye tas ya mik'a mata k'ofin ,sannan ta zuba masa farfesun data had'o masa ,ba lefi ,yaci sosai Dan kad'an ya rage.

Lukman ne ya shigo dasu ba'ish ,ai tun kafin ya k'araso suka rugo da gudu suna k'ok'arin hayewa kan gadon ,dariya abun ya bama kowa. Umma tace

"Lah! Kai Dan iyayen Ku ina zaku hau?"

Cikin muryar marasa lpia da nuna mutum yaji jiki salim yace

"Umma zasu zo yiwa Baban su ya jiki ne fa!"

"Kodai kakan su ba", binafa ta bashi amsa

Salim yace " ke kuma waya gayyato ki ?yara da uban su amma ana Neman sa musu ido"

Dariya binafa tayi tare da cewa "sannu Baba me 'ya'ya, sauki kaji Dan nema"

Dariya dikkan su suka sa.



Kwanan salim 7 a asibiti aka sallame shi. Bayan sun koma gida ba karamin kulawa salim ke samu a wajen hajiya da binafa ba ,'ya'yan shi koda yaushe suna tare dashi suna mai gwalam-gwalam. Zuwa yanzu salim ya fara murmurewa ,ya fara maida jikin shi.

Bayan kwana biyu umma tazo duba salim ,daga nan ta buk'aci son zama dasu. Nasihohi ta fara musu ,sannan ta buk'aci su nemi gafarar juna ta kuma nemi alfarman komai ya wuce daga yau har abada... Bata tashi a wajen sa seda aka sa ranar auren binafa da salim nan da wata biyu me zuwa. murna gun salim da hajiya ba'a magana .
Addu'o'i ta musu sosai na samun zaman lpia, kafin ta musu sallama ta koma gidan ta.

Ana auren salim da binafa saura wata 1 ,Hajiya ta shiga gyaran binafa ba kama hannun yayace yara ba nida gyara ba ciki da waje, har wani kiba ta k'ara tayi haske abun ta.

Ga kad'an daga cikin gyaran da binafa ta samu kuma Ku k'aru insha Allah


SIRRIN MALLAKAR MIJI

Uwar Gida ga hadin da zaki gigita Mai gida da Dadi...

_Ki sami hulba ki dakata sai tayi laushi tamkar garin fulawa ko foda ma'ana dai tayi laushi sosai. Sannan sai ki nemo zuma mai kyau ki samu madara ta ruwa ko gari amma ki tabbatar kin sami cikakkaiyar madara ba wacce take da hadi ba, Sannan ki nemo Nono Kindiirmo mai kyau wanda ba'a kade shiba._
_Sai ki sami ruwan dumi ki zuba garin hulbar nan dai dai yadda zai ishe ki kawo madarar nan a kai kina zubawa kina juyawa har sai ya hadu sosai sannan ki zuba nono"ma'ana kindirmo" a kan wannan hulba da madarar taki bayan sun hadu sai ki kawo zuman nan kina zubawa har sai kinji yayi dai-dai da yanda zakinshi yayi miki dai-dai._

_Uwar gida koma ki fesa wankanki da ruwa mai dan zafi-zafi ki sheka kwalliya sanya turarenki mai sanyin kamshi, kiyi shiga mai nuna siffar jikinki yanda zaki dauki hankalisa da zarar yaπ kalleki...._
_sami kujera mai taushi dauko wancan hadin naki ki sanya karamin cokali kina sha kafin mai gida ya dawo................._
_Sauran jawabi kwa karasamin._

GYARAN JIKI


Gyaran fata da kankana
Gyaran fata da kankana
Kankana na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan dake dauke da sinadaren gyaran jiki da gautsin fata da kuma rage tsufar jiki domin tana dauke da sinadaren dake wanke maikon dake taruwa a magudanar gumi a fata wanda yawanshi ke haifar da fesowar kuraje da dama. Don haka, amfani da kankana a jiki na da matukar mahimmanci sosai ga rayuwarmu ta yau da kullum. A yau na kawo muku hanyoyi da dama da za’a bi domin yin amfani da kankana domin samin fata mai laushi da kuma sheki a kodayaushe
·Kodewar fuska; markada kankana tare da gurji sannan a rika shafawa kamar sau biyu a rana na matukar magance wannan matsalar. Sannan za’a iya markada kankanar zalla sai a dauko auduga ana tsomawa ana shafwa a fuska sannan a barshi ya bushe na tsawon mintuna goma sha biyar. Za’a iya markada kankana da ganyen na’ana’a sannan a rika shafawa a wannan wajen da fatar ta kode. Amma abu daya nake so a yi amfani dashi a cikin ababen da na lissafo.
Domin yankwanewar fata; a markada kankana sannan a zuba mata zuma kadan sai a rika shafawa a inda fatar ke yankwanewa sau biyu a rana. A samu kankana da ruwan lemun tsami da sukari sai a hadasu guri daya. Kafin sukarin ta narke sai a rika dirzawa a inda fatar ta yankwane domin mikar da fatar.
· Rage shekaru; a samu kankana da man zaitun da kindirmo da kuma kwanduwar kwai sannan a kwaba a rika shafawa a fata a kullum domin samun sakamako mai kyau mai inganci. Za’a iya markada kankana sannan a samu ayaba a kwaba sannan a hadasu guri daya sai a rika shafawa a fata. A samu markadaddiyar kankana da madara da kuma fiya sannan a kwaba a rika shafawa a fata domin samun sakamako mai kyau.
·kurajen fuska; a sami kwallon kankana a busar a rana sannan a daka yayi laushi sannan a tafasa ruwa a zuba sai a tace sannan a rika wanke fuska dashi .
·Gautsin fata; a markada kankana sannan a zuba mata man ridi da na kwakwa sai a shafa a fata a barshi ya kai tsawon mintuna ashirin sannan a motsa

*TSAKIN KUKA*

Kisamu tsakin kuka kidinga zubashi a garwashi kina tsugunawa yana hana gaban mqce wari kuma yana matse gaban mace

*LALLE*


Kisamu lalle kidinga tafasashi kina shiga ruwan yana maganin sanyi yana matse gaban mace

*FARIN MISKI*

Kisamu farin miski kidinga dankwalowa da abin Sosa kunne kina matsi dashi zakisha mamaki

*MAN ZAITUN*

kisamu man zaitun kihadashi da man hulba da man karin fani kidinga matsi dashi yar uwa baa magana

*KANUM FARI*

Kisamu kanin fari kizuba akan garwashi kidinga tsuguno yana matse gaban mace sosai....

Wannan kenan a tak'aice👌.



**************


Bikin binafa saura sati biyu ,su Abdallah k'annen ta suka dawo. Wata safiyar asabar ,imran ,abdallada uncle idris k'anin umma suka shirya fita tunda sassafe, basu sanar da kowa inda zasu je ba ,se yamma lik'is suka dawo kowannen su fuska d'auke da damuwa. Suna dawowa ,wanka kawai sukayi suka ci abinci sama-sama ,shiryawa sukayi sannan suka sanar da umma cewa ta shirya ita dasu musaddiq zata raka su unguwa. Umma batayi k'asa a guiwa ba, ta shirya ta kuma shirya 'ya'yanta kamar yadda suka buk'ata. Inda kanta yayi marfi shine rashin tambayar su ina zasu je ba, wannan Abu kuwa ba k'aramin dad'i yawa su imran ba.

Misalin 7:30 na daren wannan ranar ,suka isa babban asibitin abuja dake gwagwalada. Mamaki ne fal a ran umma ganin sun shigo asibiti, kan ta be k'ara k'ullewa ba seda taga Hajiya da binafa cirko-cirko, ganin bata ga salim a tare dasu ba yasa ta tsinke, hankalin ta ya tashi ,a tunanin ta ko ciwon salim dinne ya tashi.

Ta bud'e baki zata yi magana se ga likitan su ya fito, yace



Zaku iya shiga ya farka. Ai kafin kowa yayi azama ina! Umma har tayi gaba ,ko sallama bata tsaya yi ba ta shige ,salim take tunanin gani ,amma a mamakin ta se taga ba haka ba. Zaro ido ta shiga yi tana waige-waige ,kunsan wata gani? Baban su binafa ta gani ,Alh Ibrahim Arielle. Idan akwai abunda umma ta tsani gani bai wuce wannan halittar ba, amma yanayin yadda ta ganshi kuma seta tausaya masa ,jini ake kara masa tare da ruwa duk a lokaci d'aya, ya wani tsotse ya rame ,babu komai a jikin shi daga k'ashi se fata, ga wani abun bak'i dayayi kamar an mai fenti, da alama ma ya Dade yana fama da rashin lpia ,kai bama rashin lpia kadai ba ,yunwa kanta ta samu gindin zama a jikin shi ,umma ke rayawa a zuciyar taa. Kasa motsawa tayi daga inda take ,shigowar su Hajiya dasu Abdallah shiya dawo da ita cikin hayyacin ta. Juya wa tayi zata fita ,amma abunda ta gani ya tokare mata magudanar yawun ta.

Daga Hajiya ,har su binafa zube wa sukayi akan guiwowin su lokaci d'aya ,suna rok'arwa Alh Ibrahim gafarar ta. A razane umma ta mik'ar da Hajiya tare da cewa cikin muryar kuka

"Hajiya kinfi k'arfin komai a waje na ,wllh na yafe mishi saboda Allah kuma saboda ke"..

Wani dad'i ne ya rufe Hajiya a lokaci d'aya kuma umma ta fashe da kuka. Hajiya ta maida duban ta kan su binafa ,tace " to Ku kuma me kuke jira ,inace wacca akawa lefin ta yafe ,to maza Ku durk'usa Ku nemi yafiyar shi ,saboda mahifin kune duk yadda ya lalace yana nan a matsayin mahaifi a gare Ku, sannan tsakanin 'ya'ya da iyayen sa Allah yace biyayya ne da kyautatawa ,matuqar be sab'awa shari'a ba ,saboda haka kamar yadda kuke ganin ya muku lefi kazalika kuma kun masa lefi. To gara tun yana da sauran kwanan shi Ku samu daidaituwa dashi ko kwa samu rahmar ubangiji."

Basu musa ba sukayi kamar yadda Hajiya ta umurce su. Kuka Alh Ibrahim keyi kamar wani k'aramin yaro ,yana fadin

"Nina zalunce Ku ,saboda haka ni ya kamata in roke yafiyar Ku. Ku yafe min Dan Allah" ya kasara maganan yana me fashewa da kukan takaici .

Imran ne ya matso kusa dashi yana lallashin shi ,tare da nuna masa aibun abunda dikkan su suka aikata. Nan Abdallah y shiga basu labarin ,tun sanda Hajiya ta kira su ta musu fada tare da musu nasihohi masu shiga jiki ,sannan ta basu shawaran akan suje su d'auko mahaifin su, ta nuna musu lallai duk halin da mahaifin su ke ciki shakka babu yana buk'atar su.
To a ranar da suka je d'auko shi a ranar suka samu mummunan labarin cewa , bela ta tattara komai nashi ta gudu ,hatta gidan da suke ciki ta saida ta karb'e kudin ta sannan tasa kai. A hanyar ta na barin k'asar ne zuwa nijar se ga masu kamun bayi sun tsare su ,cikin wa'yanda aka kad'a keyar su na zama bayin sarkin Agadaz har da bela ,sannan aka karbe duk wani guzuri data zo dashi, data so tayi musu gaddama ne ma ,suka narka mata dukan tsiya ,sannan suka k'ulle ta a jikin rak'umi yaja ta a sahara daga biu har cikin kasar agadaz...

Kun gani ko ,shi Allah ba azzalumin Sarki bane,shiyasa ake cewa idan zaka Gina ramin mugun ta ka Gina gajere. Kun dai ga yadda karshen bela ya kasance. Allah yasa mufi karfin zuciyar mu ameen.

Sosai umma ta tausaya masa ,kowa seda ya zubar masa da k'wallah. Nasihohi sosai Hajiya ta musu na tsakanin hakkin iyaye da 'ya'ya yen su, a karshe aka rufe taro da addu'a.


Imran ne ke sheda musu ,ciwon Alh ya tsanan ta kamar yadda likitan ya sanar dasu ,Dan haka sun gama shirye shiryen su sun kuma kai karshen zasu fitar dashi waje Dan a duba shi. Addu'a da fatar nasara kowa yayi musu.

Bayan sati d'aya visa nsu ya fito ,imran da Abdallah ne zasu tafi dashi can kasar da suke aiki wato Turnkey a babban birnin Istanbul. Lokacin ya rage saura sati ukku bikin binafa.

BAYAN SATI UKU

Aka d'aura auren binafa da salim ,ba ayi wani shagali ba bayan d'aurin aure, se walima ,ganin yadda al-amurra suka cakude musu , na rashe-rashe da kuma rashin lpia da aka yita yi daga b'angarorin biyu.

Amarya ta tare a a wani narkeken gidan da salim ya siya ,a unguwar maitawa. A inda Hajiya ta buk'aci a bar mata su ba'ish, ko banza sunfi sabawa da ita.

Alhmdulillah zaman nasu ba lefi ,dukda cewar binafa ta kasa jure rayuwa da wani daban daba Umar faruk ba ,amma haka tayi ta rak'ar zuciyar ta.

Bikin binafa da wata d'aya ,Allah yawa mahaifin su Alh Ibrahim Arielle rasuwa acan k'asar Turkey, mutuwar ta girgiza kowa ,musamman da basu samu daman dawowa da gawar shi gida ba ,acan aka masa sutura aka rufe shi. Hakan be hana an yi ansan gaisuwa anan gida najeriya ba.




BAYAN SHEKARA D'AYA


Binafa ta santalo kyawawan 'yan matan ta su biyu masu masifar kama da ita. Ranar suna Hassana taci sunan umma wato Fatima binta ,inda ake mata lak'ani da SHUKRA ,sannan hussaina taci sunan Hajiya wato karima, inda ake mata laqani da HAMEEDA...


Farin ciki da yalwar azziki se d'ad'a bud'uwa yake daga b'angarorin guda biyu, had'ida kwanciyan hankali. Soyayya da tarairayan duniyar nan ba kalan Wanda binafa bata sha a wajen salim ,baya k'aunar duk abunda ze b'ata Mata rai. Kowannen su naba d'an uwan shi girma. Wannan ne ya k'ara shakuwa a tsakanin su...

Duk sati kuma suna gida, wannan satin idan akaje gidan Hajiya ,wani sati to gidan umma za'a wuni...











ALHAMDULILLAHI!!! GODIA TA TABBATA GA ALLAH MAI KOWA MAI KOMAI, WANDA CIKIN IYAWAR SHI DA GANIN DAMAN SHI YA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN ME SUNA (BINAFA). INA ROKON ALLAH INDA NA FAD'I DAIDAI ALLAH YA BANI LADA, KUSKUREN DAKE CIKI KUMA ALLAH YA YAFE MIN.


INA GODIA GA D'UMBIN MASOYA NA ,MASU BIBIYAR WANNAN LITTAFI TUN DAGA RANAR FARKO ZUWA YAU. ALLAH YABAR ZUMUNCI .


SAK'ON GAISUWA ZUWA GA K'UNGIYAR INTELLIGENT WRITERS ASS. ALLAH YA K'ARA D'AUKAKA WANNAN K'UNGIYA DAMA SAURAN K'UNGIYOYI MASU MANUFAR YAD'A ALKHAIRI IRIN NAMU.


JINJINA GA DUK WANI MARUBUCI KO MARUBUCIYA, FATAR ALLAH YA K'ARA D'AUKAKA MU BAKI D'AYA.


WANNAN LITTAFI NA SADAUKAR DASHI GA DUK WANI SHARIFI DAKE FAD'IN DUNIYAR NAN (AHLUL BAITI RASULULLAH S.A.W) ,JIKOKIN SAYIDIS SADATI, WA'YANDA BASU DA DATTI. ALLAH YA LAMUNCE MANA AHBARIR RASULULLAH S.A.W. 👏👏👏




Se kun sake jina a sabon LITTAFI na me suna COMING SOON...😛




SIDIYA TAKU CE ,KUMA NAWA NE


ONE LUV❣


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment