Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»ΏπŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
KISHI KO JAHILCI

Story & written
By

Ummu AmeerπŸ’ƒ


Short story


Page1⃣


Mata ne cike d falon ana daga kayan lefen d aka kawo, sai faman shewa d guda ake tare d yabon kayan d aka kawo, domin kuwa kaya ne n gani a fada, naira tayi kuka anan, duk wani abinda ke ciki ba na banza tun daga kan sutura zuwa sarkoki mayukane abindai sai wanda y gani, yan uwa d abokan arziki n fadin Amarya tayi goshi, Ana t sanya Alkhairi d fatan Allah y nuna mana ranar biki, can bangaren kuwa amarya ce cikin daki tare d kawayenta sai xolayarta suke daya daga cikinsu mai suna hafsa tace matar mutum kabarinsa, Aysha ba irin wulakancin d bakima Abbas ba y jure kamar karamin yaro lallai y cika jarumin maza gashi nan ynx y kamaki a hannu ta kare maganar ta sigar zolaya t dan bugi Amaryar acinya, ita dai kawai murmushi tai, a zuciyarta kuwa Allah Allah take bakin d suka zo karbar lefen su tafi take domin t ganewa idonta kayan d kawayenta suke t zuguguta wa ankawo mata.
Ita kam uwar amarya sai wani cika take tana batsewa tare d wurgawa kayan muguwar harara ita a dole kayan basuyi mata adalilin rashin sanya sisinan gwal, kasancewarsu yan bidiri wayo 'yan maiduguri, Anty salma ce ta matso kusa d ita tai mata rada a kunne tace mata don Allah Anty kiyi hakuri ki saki fuskarki a gaban jama'a ne fah, kar ki ba da mu plx.. Kuma m ai bawan Allah nan yai kokari daga baya ai sai ai mishi magana. Sai alokacin t dan sakin murmushin d bai zuci ba, inda aka shiga tattare kayan ana maida su cikin akwatinan, har mutane suka fara watsewa cike d yabon kayan, y rage daga anty salma sai d kakar Amaryar wato uwar Amaryar d kannen amaryar a wurin, kawayen Amarya kam uwa jira suke su watse suka fito aka sakw baje kayan suma suna t santin lefen tare s Amaryar itama sai washe baki take tana duba kayan, inda kakar tace "OH ni hauwa yaran zamani ynx d ke ake duba kayan naki Rukayyah"
Goggo nikam kin sa min ido da yawa zamaninku da bamu ai ba daya bane, ko kishiru kike ne da kaya ta kare maganar d yi mata gwalo tare da mikewa ta ruga Daki a guje tana dariya, goggo tace ja'ira da kin tsaya sai na koya miki hankali.


Nan dai aka tattara kaya aka maida su cikin akwatunansu, mommy kuwa tashi tayi tabi Rukayyah Daki, ta sameta suna waya da Abbas, Rukayyah kuwa ganin yanayinsa mom din nata yasa ta saurin katse wayar tace masa 'sorry I will call you back''
Ta cire wayar daga kunenta, ta tattara nutsuwarta Ga mom wacce ke ta jifanta d harara, tace momy Lfy kuwa,? Bansani ba ta bata amsa a gajarce, ina so ki gaggauta kiran Abbas kice ina son ganinshi!
Mommy me y faru ne don Allah?
in yazo kyaji a wajensa, Tunda na fuskanci kina neman xubar d darajarki a wajensa Tun kan ki shiga ciki gidansa, komai yayi a wjenki daidai ne kin Dora wa kanki son mai mata, sai Kace kin rasa masoya ne, ta juya ta fuce daga dakin.


Rukayya kam doguwar ajiyar xuciya ta sauke tare da fadin, mommy ban san ran da zata canja ba, bawan Allah nan kullum cikin mata biyayya yake kamar ita ta haifeshi amma bata gani?

Daukan wayar tayi tai dialing no shi, "hello"
Baby mommy tace tana son ganinka plx...
Ok insha Allah zanxo bayan magriba, ok sai kazo bye! Ta katse wayar.



Ku biyoni don jin yadda zata kasance.....

By ummu AmeerπŸ’ƒ

πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€KISHI KO HAUKA

Story & written

By
Ummu Ameer

Short story:


Afuwan 'KISHI ko HAUKA' ne nai mistake a page 1





Page 2⃣




Rukayyah zaune gabab dressing mirtow tana make-up, ta gama kwalliyar tana Yana mayafin abayar da ta saka ta dauki turare ta feshe jikinta da shi,tayi kyau ba laifi simple make-up tayi dake ita Bata cika son kwalliyar fuska ba in ta shafa powder ta dan saka lip glow a lebenta shikenan ta saka flat shoe, wayar ta ce Tai ringing sunan da ta gani a fuskar wayar ne yasa saka ta sakin murmushi, 'babynta' ta daga wayar tare da fadin gani Nan fitowa" baby"!



Dakin momy ta wuce direct domin sanar Mata da cewa Abbas ya iso, sallama tayi tare d tura kofar, Nan ta sameta tare da wata kawarta Anty batula, rukayyah ta gaishe ta sannan tace Mata "momy Abbas din ya zo!
Ok! Kije ki shigo da shi falo ganinan zuwa..
Ok, ta Bata amsa tarr da fita zuwa wajen bakon nata,



A hanyarta ta fita ne ta hadu da kaninta wato junior tace junior "zo ka raka ni, a guje ya karaso yace Anty uncle Abbas ne yaxo tace "ae"
Nan ya hau murna domin yasan duk sanda zaizo sai ya kawo Masa tsarabar kayan kwalama su chocolate, ice cream, f dai sauransu.


Tun dosowarsu wurin kamshin turarnsa y mamaye farfajiyar da kamshi.
Sallama Tai masa tare da sannu da zuwa, ya amsa cikin farin ciki tare da riko hannu junior,
Uncle Ina wuni!
Lfy lau junior ya su momy?
Lfy!
Ya bashi amsa yace to ga tsarabar ka Nan,
Ya amsa tare da fadin
Thank you!

To maxa ka shiga cikin gida, ganinan shigowa,
Ya ruga a guje.

Allah yasa Masa son yara, Abbas don ko a gidansa in ya dawo haka yara zasu xo suna ta amsa tsarabar sweet ko capri-sonne.


Ya tatttara nutsuwarsa ga gimbiyar tasa, my luv! Ina fatan dai lfy ko when momy, ta bashi amsa da cewa lfy lau, tace dai tana son ganinka ne,
Ok!
Tace Kaya fa sunyi Allah y Sanya Alkhairi ya Kara budi,
Ameen-Ameen,
In Akwai abinda Bai yi ba sai ki fada acanxo Miki,
A'a wlh komai yayi Allah y saka d Alkhairi,

Yaji dadin yabon kayan da tayi domin yasanta da yaba kyauta gata d kawaici
Kazo mu shiga momy tana jira, Tai masa jagora izuwa falon, yana biya d ita.

Can dakin kuwa momy da Anty batulu, sai xuga momy take akan irin rashin mutumci d zataiwa Abbas,akan rashin cika Alkawarin saka sisin gwal a cikin lefen, har tana ce mata wlh indai bazai saka ba kice sai dai yaxo y kwashe lefensa domin ko bashi ne kadai namiji a duniya ba ehe,
Momy tace hmmm! Bar ni da shi zai gane kurensa tare d daukar mayafinta tana Shirin fita zuwa wajensa,



A zaune ta sameshi a kasan carpet, ta Sami daya daga cikin kujerun ta zauna Tai kicin-kicin da ita,
Momy Ina wuni!
Lfy !
Ta amsa Masa a gajarce!
Dama na Kira ka ne akan lefen da aka kawo, Raina yayi matukar baci da rashin ganin sisin din gwal da na fada was rukayyah ta Gaya maka tsarin mune duk sanda za'a kawo lefe y Zama dole a saka shi ciki, Amma ka tashi k kawo lefe ba tare d ka cika Al'adar muba, ba lallai ba dole in kaga Abin yai ma tsauri to ka iya kwasar kayanka domin ko ba Kai kadai namiji ba,

Subhanallahi!
Momy kiyi hakuri ya furta hakan cikin ladabi, wlh Bata gaya min ba,ai da an saka aka saka sarka ma balle sisi, kiyi hakauri insha Allahu xa'a kawo gone insha Allah!

A zuciyar ta ko ta cika taf da mamakin wanna diyar Tata kwata-kwata ta yi nisa a son wanna mutumin da ke da Mata, ko me ta gani oho!

Doguwar ajiyar zuciya ta ta tare da ce Masa ka iya tafiya,
To godiya nake momy a tashi lfy.
Ya tashi,ya fita
Ita ko bin bayansa Tai cike da tsana, ita dai Bata kaunar Abbas tun da yazo neman auren diyarta don kawai Yana da mata, acewarta ita Bata da kishiya sai diyarta zata je ta tarar da kishiya, don aurenma ba'a son ranta ta yarda ba fin karfinta ne kawai akai.

Ta tashi ta Mike don komawa daki wajen kawarta.

Tana shiga ta sameta a kishingide ya kukai sis?
Dake haka suke Kiran juna.
Ke dai Bari wlh yarinyar Nan fa in banyi da gaske ba wlh sai ta tixartani a idon jama'a,
Ashe wai Bata gaya masa.
Ah lallai sai kin you da gaske Alan rukayyah domin na fahimci tana da shegen taurin Kai,

Amma yace gobe za'a kawo.
Yafi Masa ai indai Yana son aurar diyarmu!
Cewar Anty batulu,

Anty batula Aminyar momyn su rukayyah ce, bazawara ce, tayi aure ya Kai sau hudu ta kasa Zama gdn Miji, kasancewarta mace Mai son Abin duniya gata da munafurci ga hassada Bata son ta ga wani ya fita ki kadan, ga yawo Bata iya Zama waje daya, kusan kullum tana gidan momyn, Tai ta kitsa Mata mugayen halayya.


Rukayyah ki tun da ta fito wajen Abbas taga yanayinsa ya canza, axiciyar ta tace, na bani, ni rukayyah ki me tace Masa oho!
Ta karasa wajensa a sanyaye tace har ka fiyo?
Na fito!
Amma Ina fushi dake
Me nayi Kuma ta tambayeshi cikin sanyin jiki.
Momy ta Baki sako ki gayan kafin akawo Kaya Amma Baki fada min ba.
Why?
Shiru Tai na Dan secondAm bashi amsa da Kai hakuri na manta ne shiyasa.

Kinga ran momy y baci, Amma nace za'akawo gobe.

Zan wuce ni ynx in kin shiga ciki ki Kara Bata hakuri, kinji my luv!
Gyada Masa Kai tayi ,
Ya bude motar zai shiga ya tsaya Yana dan kallonta yaga kamar fushi take, me y faru ne luv! Naga kin canxa, bashi amsa Tai cikin shagwaba ba Kaine xaka tafi daga zuwa ba,
Sorry my luv! Wlh akwai uxurin danake da shi ne shiyasa ai goben zan dawo tunda yau Kinga zuwan momy ne ko ta gyada Masa Kai
Tace bye!
Sai da safe baby, Allah y tsare
Ameen!
Ki kularmin da kanki
Insha Allah suka rabu cikin kewar juna tana daga Masa hannu.har ya fuce daga gidan.

Ta juya domin komawa cikin gida Amma a xuciyarta ranta ya baci akan abinfa momy tayi, kuma tasan wanna munfukar matar ke zugata, ta shige dakin su, tana shiga ta Sami kanenta biyu Aisha da zainab, suna hira,
Anty rukayyah lfy Naga ki haka kuwa cewar Aisha dake sunfi kusanci da ita Kuma ko wane matsala tare suke sharing sun shaku da juna sosai,
Tace momy ce fa tasa na Kira Baby, akan zancen sisin gwal da ta fada na Gaya Masa Ana sawa alefe, shine da Bata gani ba tasa aka kirawo shi, Kuma Ina sane naki Gaya Masa ai tunda shi ba Al'adar mu daya da shi ba.
Aisha tace da kin sani kema kin fada tunda kin San hakin momy, Kuma don dai Bata son auren kune,Amma kiyi hakuri kiyi ya addu'a Kuma kiyifatan rabuwa d ita lfy,
Nan dai sukai ta hirarsu ta yan uwa.





Ki biyo ni domin sanin wacece Rukayyah
Da Kuma Abbas?


By
Ummu AmeerπŸ’ƒ

πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
KISHI KO HAUKA


story & written

By


Ummu AmeerπŸ’ƒ




Page 3⃣



Wacece Rukayyah?

Rukayyah diya ce ga Alh usman, Alh Usman mutum ne Mai karamci da sanin mutumcin mutane yana da hakuri gashi da tausayi.

Matarsa daya wato Haj. Binta wadda suke Kira da momy, wacce Tai karatun degree dinga a ABU Zaria inda ta karanci mass "communication" mace Kuma duk anan gdn Alhaji Usman Tai karatun, kasncewarsa mutum ne Mai son karatun ya Bata damar yin kartunta agdnsa har ta kammala a lokacin suna d yara uku, ta farko Rukayyah, sai Aisha, sai zainab sai junior shine karaminsu, mai sunan Baban momyn ne wato mallam Abubakar.

Momy mace ce mai fadin rai gata da hangen rayuwar wasu ita kullum gdn wane sunyi kaxa grn wance sun you kaxa, a kullum Raina rauuwat da take ciki takeyi, Alhalin ba abinda ta rasa, a gidanta.

Wannan yasa ta burin tana gama karatu aiki zata Fara yi.

Alh. Usman ko Yana aikin banki ne, Kuma Yana da rufin asiri, ba abinda suka nema suka rasa, mutum ne Mai kyautatawa iyalansa ko da ace shi zai takura ne,

Yana hakuri sosai da halin momyn, ko kadan Bata raga Masa a matsayinsa na mijinta.
Sai dai shi Kuma ya Sha alwashin bazai barta tayi aiki ba.

Ya saka yaransa a makarantu masu kyau da teada domin shi indai akan karatun yayansa sai dai inda karfinsa ya Kare.

Rukayyah ta gama kartunta na sakandire,ynx haka tana level 200 a buk.
Sai Aisha inda take s.s 3
Sai zainab tana j.s 3
Sai junior dake primary 1


Momy Yar Asalin garin maiduguri ce haifaffiyar maiduguri, lokacin da Alh.Usman yaje service din shi ne suka hadu har Allah yasa ya aure ta , Shima lokacin auren nata ba karamin wulakanci ya Sha ba gurin danginta don wai su Basu cika son aurawa bahaushe ya'yansu ba haka dai sukai ta bujiro Masa d Al'afinsu, ya jure duk wani bidi'oinsu har akai bikin nasu, ba don sun so ba, kasancewar ita da ta dage akan lallai shi takeso. Kuma baburawa ne daman.

Gashi in ta Fara bala'i kamar da rashin mutunci Abin ba dadi. Ki ya'yan nata tsoronta suke kamar me, rukayyah ce ma da Bata cika shakkar ta ba irin cin fuskar da take wa mahaifinta in ta tashi yi ko gaban wa aye Bata shakkah.
Hakan tasa rukayyah ranta ke matukar baci da halayar mahaifiyarta.

Kuma Bata fiye shakkarta ba kamar sauran yaran, ita sai dai suna da way halayyah guda:
In ransu y baci dikkansu kamar ba su ba misali ko fada y hada su da wani ko makamancin haka, Amma a zahiri suna d fuskar Kamala da hakuri a fuska Kuma ba laifi suna da tarbiyyah dai dai gwargwado.


Rukayyah sun kwashe akallah kusa da shekaru uku suna soyayyah da Abbas, tun tana ajin karshe a secondary, suka hadu, ta dalilin wata kawarta 'sadiya'

Watarana taje gdn su sadiya da yamma shine, shi Kuma ya raka friend din shi wajen yayar sadiyar, tun daga lokacin y kyallah ido akanta yace wa yayar Yana kamu.

Tun daga ranar sadiya ke ta kokarin kafa gwmnatin Abbas Amma kememe yarda da soyayyarsa, ba irin wulakancin da Bai Sha ba Amma fir Taki shi saboda Bata son zuwa gdn kishiya.
Sbd tana da wani saurayi dake karatu a B.u.k, Shi Kuma a wajen yayansa yake d Zama kasancewar su iyayensu sun rasu, sunan jamilu, Yana level 300 a lokacin haka dai Kuma yaro ne karami, Bai yI 25 ba a lokacin, haka dai soyayyah ta shiga tsakaninsu Mai karfi don ko duk ranar da basuyi waya ba sai ka ganta kamar wata mara lfy, har tayi candy Kuma ta Sami kyakkyawan result inda ta Sami admissions itama anan b.u.k.


Inda ita Kuma alokacin ta dage kan lallai sai ta Fara aiki domin har a wake biyu ta Sami offer, shiko Daddy yace Sam Bai San zance ba, sai dai ta zaba aiki ko aurenta Nan ko ta zabi aiki, take ya Bata takardar ta saki daya, dama kawai hakuri yake da ita hattah Yan uwansa Basu d damar zuwa gdn sbd babu fuska ko kallon arziki basu samu a gidan Dan uwansu, suna ji suna gani gidan Dan uwansu y gagaresu, Dama suna zaune a k.d a unguwar tudun wada, Amma Asalin iyayensa Yan garin Kano ne a unguwa g/Kaya, mahaifinsa y rasu sai mahaifiyarsa mace Mai mutumci da karrama mutane, domin ita ce ma Mai tausasa zuciyar Dan nata akan halayen matar sa itama Bai fi sau uku ta taba zuwa gaishe da mahaifiyarsa ba, sai dai yaran da suke zuwa in sun samu hutu domin suna Jin dadin Zama da kakarta tasu. Ko da taji labarin sakin da yai Mata Bata ji dadi ba ko kadan ranta ya baci.



Bayan rabuwarsu ne tace ita Kam bazata bar yaranta ba anan domin kuwa ita baxata bar yayanta ba, ai ko Nan akai ta tafka muhawara har da su zuwa kotu daga karshe dai ya hakura ya bar Mata da sharadin Yana aure zai karbi yayansa.



Haka ta tarkata yaranta taje ta Sami gida Mai kyau ta Kama haya da sharadin ubansu ne zai dinga biya, domin Bata dauke Masa komai ba, Alan yaran duk Abinda ya tashi shi ne yake yi shiko Yana yi ne kawai don yaransa, mutum ne Mai matukar kaunar yayansa.


Bayan shekara biyu da rabuwarsu ne mahaifinsa y auri wata diyar mutumci da karamci gidan dattijai masu dattako, sunan Nasiba, Amma itama bazawara ce, tana da yaro daya Ahmed, Bai wuce 4yrs ba, mahaifinsa ne y rasu, Kuma y amince zai rike shi kamar shine mahaifinshi.




Itako momy tuni ta Fara aikinta a gidan t.v, dake nan k.d. Anan ta hadu da wani Alh. Yace zai aureta ganin kudin da ya ke da shi ne yasa ta amincewa Nan da Nan akai bikin, suka tare a wani gidan tare da yaran Shima gdn haya ne Amma Yana da kyau sama da kasa ne, part dinsu daban na yaran daban, Amma yaran duk Basu so ba, sunfi son gdn mahaifinsu , duk da suna zuwa hutu, Kuma matar tana kaunar su don duk Abinda suka ga dama suke Yi ba kwana ba hantara, suna Jin dadin Zama da ita sosai.




By
Ummu AmeerπŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
KISHI KO HAUKA



Story & written

By



Ummu Ameer







Page 4⃣






A lokacin ne Kuma daddy ya cewa Rukayyah in da gaske jamilu yake y fito, don baison doguwar soyayya.


Ta shaidawa jamilu sakon mahaifinta, shi Kuma y shaidawa yayansa Nan yace Bai San zance ba, nawa yake da zai dauko aure ynz ko karatunsa Bai karasa ba, Nan hankalinshi y tashi saboda Yana kaunar Rukayyah, suna so juna, tun daga lokacin ya Fara janyewa daga gareta, itako duk hankalinta y tashi ta Fara tunanin dama soyayyar yaudara yake Mata, itama duk ta fita hayyacinta ta shiga matsananciyar damuwa.


A lokacin dama tana gidan dady, mahaifin nata y kirata yake tambayarta damuwarta, Tai shiru Bata bashi amsa ba, nasan baxai wuce akan jamilu bane, yace kiyi hakuri ki kyaleshi haka Allah yaso, ki maida hankalinki kan karatun ki kinji, Allah y musanya Miki da mafi Alkhairi a gareki,
Tace to daddy ngd!
Yace yawwa doughter
Allah ya yi Miki Albarka,
Ameen


Tashi tayi ta shiga dakinsu, da suke sauka in sun xo hutu.


Ita ma Antyn su wato matar babnsu Nasiba, lallashinta Tai tayi, har take ce mata ki dauki dangana Allah yayi bashi bane mijinki,
Kuma ba kina da wani dake sonki ba, wai Abbas kwananki Zainab take bani lbrinshi, har da wulakancin da kike Masa Kuma Kinga shi daga jin lbrinshi na fahimci auren ne ya kawo shi gurinki da xaki daure ki bashi dama ki gwada irin soyayyarsa ki gani ko kuwa?


Tace Anty fa Yana da aure da yara, gaskiya ni shiyasa ma tun farko naki Amincewa da shi Kuma har ynx ma Yana min waya, kawai dai naki bashi dama ne.

To ki daure ki bashi, tunda har ynx Yana tare da ke,Kuma da be damu dake ba da tuni ya kyale ki, Yana sonki,kinji Yar gidan daddy, Kuma insha Allahu Alkhairi ne a gareki.

Gyda Mata Kai tayi, tare d nuna Jin dadin nasihar ta, tana matukar Jin dadin Zama da Matar babanta, sbd mace ce Mai saukin Kai kuma ta daukesu kamar it's ta haifesu, Rukayyah tana matukar Alfari da ita, domin tana samun kulawar da ko momy Bata Mata.
Ko shawara ne da ita take wani lokacin ko basa tare ta waya zata buga don neman shawara.


Ita momy barta da son ya'yan a Baki Amma Bata cika jansu ajiki ba, harkokin ta sun fi shige Mata gaba, dake tana business, bayan aikin da take har tattaki tana zuwa lagos, Abuja domin gudanar da kasuwancin, ita dai neman kudi ta ko inaπŸ˜„


Shiko mijin da wani ba babba bane ta maishe shi mijin tace abinda taso shi take yi, sai yadda tayi da shi, wannan yasa duk lokacin da taso tafiya zata tafi tayi sati daya ki biyu, kasancewar akwai wata dattijuwa a gidan dake kula d yaran ita ke musu girki da sauran ayyuka.

Mijin kuwa aurensa biyu suna rabuwa da matan akan rashin haihuwar da bayayi, ita dama momy tun akan junior tace ta gama haihuwa hudu sun isheta.




A hankali rukayyah ta Fara saurarar Abbas, har ya zamo soyayyah da shakuwa ta shiga tsakaninsu Mai karfi, har tana ji sai ynx ne ma take soyayya saboda Abbas irin mazan Nan ne da suka iya soyayya, in suna waya har Bata so dena, ita kanta tana mamakin irin soyayyar da take Masa.





Itako momy tunda ta fuskanci wa take so, hankalinta ya tashi, tace Sam Bata Isa ba ta rasa Wanda zata so sai Mai mata, mazan sun Kare ne .

Tun wuri ki gaggauta fita a rayuwarsa don muddin Ina Raye bazaki auri Mai Mata ba, kina yarinyarki Zaki je ki Fara was kanki bakin ciki.


Itako yarinya ta kafe akan lallai ta ga miji, shi take so Tai aura duk da itama da ta dauko tsarin uwarta, Amma daga baya ta gane shi yafi dacewa da ita Kuma matarsa Bata dameta kowa zaman mijin sa zaiyi.

Tunda ya Mata Alkawarin cewa kowa da gidansa bazai hada su ba.


Rigima sosai akai akan batun auren inda Daddy yace shi Wanda diyarsa ta kawo tana so shi zai bata, indai ya Yaba da shi.

Momy ko tace Abinda bazai yiwu bane muddin Ina Raye
Aiko yace mu zuba Dani da ke tunda 'yar Taki ce ke kadai.


Daga karshe ma sai gidan mahaifinta ta koma.

Anan ne ma yasa ta Kira Abbas Yana son ganinshi , ta sanar Masa da sakon daddy.

Bayan magriba suka zo shi da Abokinsa Mai suna Nasir.

Daddy yai musu tarbar mutunci suka gaisa, yace Yana son Jin takaitaccen tarihinsa,
Nan ya fada Masa shi maraya ne iyayensa duk sun mutu a hannun yayansa ya taso inda ya Gaya Masa yayi a ynx haka shi Dr. Ne Amma doctor ne na bangaran yara wato" peadiatric"
Kuma Yana da Mata da yara guda

Please Login or Register in order to submit comment