Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ba zan baki mamaki, miji na ne mallakina,ban hana ki aure shi ba inda hali Bismillah ba zan yi fada dake ba domin ban ga abun yin fadan ba, ina kara jaddada miki dai ki fita sabgata har ma da tashi."

Meenoh ta yi wani Hamshakin tsaki tana dariya, "Yoo wai har business Marriage din ya samu wani mahimmin wajen zama da har xakiyi tutiyar shi naki ne?banxa wawiya mara galihu yar kan titi, balagaza mara asali, Ni na rasa ma in ba kaddara ba ai ko a hanya kika ga Dear ba ki kai ki kula shi ba bare har auratayya ta shiga tsakani,ki kwana da sanin cewa indai ina raye sai kin bar giddannan da kafafunki kuma bari na har abada."

Dariya Zeeyter ta yi sosai tana, "Faɗawa sakarai wanda bai san Allah ba,ba ki isa mun abun da Allah bai mun ba,domin kafinki dubunki sunyi ko ince suna kai, but bazan ce miki komai ba fatan Nasara muje zuwa."

Tana karasa maganar sai ga Haiydar ya fito cikin sauri ya fisge wayar yana ganin Meenoh ce ya daga murya tare da fadin, "wai ke wace irin wawiya jaka ce wacce bata san kanta ba? In kina son zaman lafiya ki fita cikin rayuwata kamar yadda na fita a taki,kaddara ce ta hada kuma ta raba." Tsaki ya yi yana katse kiran ba tare da ya jira amsarta ba.

Kallo ɗaya Zeeyter ta masa ta kau da kai tare da tashi zata shiga daki.

Rike mata hannu ya yi ta fisge tare da sakin tsaki ta tafi daki tare da kulle kofar.

Nocking kofar Haiydar ya fara yana, "Kiyi Hakuri Don Allah ki gafarceni, Dans tes yeux, tu as vu et tu sais que j'ai cessé de faire quoi que ce soit qui puisse t'offenser. Se pas moi qui l'a appelé tu vois. S'il te plaît, sois patient. Toutes les décisions que tu as prises, sauf d'être avec moi, s'il te plaît." ("A idon ki kin gani kuma kin sani na daina duk wani abu da zai bakanta miki,bani na kirata ba kin gani,kiyi Hakuri,duk hukuncin da zaki mun kiyi amman ban da na kasancewa da ke Don Allah."

Shiru tayi ba tare da ta ce komai ba,tana kokarin kwanciya har ta kwanta kuma sai wata zuciyar ta ce mata ta bude kofar.

Tana budewa ta gan shi zaune abakin kofar kawai yayi tagumi.

Tana budewa ta koma ta kwanta.
Ya bita yana, "na ce kiyi hakuri,shin ba zaki tausaya mun ba? Me kikeso inyi ne?"

Zeeyter bata ce komai ba ta kwanta ban da hawaye ba abun da ke ambaliya a fuskarta tana jin zafin maganganun da Meenoh ta fada mata.

Gabanta yaje ya durkusa ,yana ganin hawaye ya birkice.

Nan take ya hau kan gadon tare da janyo kanta jikinsa yana goge mata hawayen, "Ki yi hakuri koma me ta ce miki,na miki alƙawari daga yau ko kallon banza bazata kara miki ba,bare kuma fada miki magana,ina jin zafin kukanki har cikin raina,da kinsan kunar da nake ji da kin tausaya mun kin bar kukan nan."

Da sauri ta juyo ta kankamesa tana ƙara kukan.



Shima riƙeta ya yi yana ƙara share mata hawayen, "koma mene ne kiyi Hakuri,kar kanki ya yi ciwo ki samu kiyi barci,kinji."

Da kyar Haiydar ya lallaɓata har ta samu tayi barci.


Washegari
Asuba nayi ita ta fara tashi tayi sallah har ta idar bai tashi ba, zuwa tayi tana tashinsa a hankali amman ina ko alamar motswa baya yi

Cakul-kulu ta fara yi masa ya tashi yana dariya, "Bright Eye mene haka ki bar...bar...bari mana Please." Ya fada cikin dariya.

Ci gaba da masa tayi tana, "tun tuni ina tashin ka kayi sallah ka ki ai gwanda in m hakan gashi ka tashi dole."

Gabadaya dariya ta cinye Haiydar kokarin kamota yake ya rama hakan yasata ta tashi da gudu tayi falo,shi ma ya bita sai da ya kamata ita ma ya yi mata ,dukaninsu suka dinga dariya kafin ya je ya yi sallah.

Sannan suka fita training tare ana gasa kan za aga wanda ya riga wani gajiya.

Haiydar ya ce, "ke fa jikin nan naki ma ba zai barki ki taɓuƙa komai ba, big mama kawai ki hakur na ci garin."


Zeeyter ta ce, "iye? Allah ni ba big mama ce ba,kuma a gwada agani ai abun ba daga jiki bane,kuma mu ƙulla duk wanda ya fara gajiya shine zai na girki kullum a gida na 1month."

Dariya Haiydar ya yi harda riƙe ciki.
"Na yarda 💯 mu zuba mu gani, wannan kam anyi an gama."


Zeeyter ta ce, "Alright start."

Rimi rimi aka fara gudu tun Haiydar na daurewa har ya kasa.

Tsayawa ya yi ina nishi.
"Ni fa na gaji ai mun wuce yadda na saba wai ke ba kya gajiya ne,humm ba zan iya ba fa." Ya karasa maganar yana jan dogon numfashi.


Me Zeeyter za ta yi ban da dariya.

"Girki dai ya kamaka, break,da dinner,ranar da muke gida kuma harda Lunch na wata ɗaya, ba taimakon mai aiki babu nawa ehee, sai afara tashin wuri,da asuba kuma office ma adawo da wuri."


Haiydar ya harareta , "Wannan ma wasa ne, ni ba abun da zanyi ehe."

Shareshi tayi sai da suka koma gida taje ta dauko masa rigar girki tana, "Sunshine Oya Bismillah."

Ba yadda ya iya haka ya karba yasa rigar, wayarsa ya kunna yana duba page din Zahra da tasa abinci kala kala.

Zeeyter ta na daga falo tana, "Sunshine Nasi goreng Indonesian Fried Rice ina so fa."

Tsaki ya yi yana, "zan yi maganinki ne wallahi sai na rama."

Haka ya dub bayanan yadda ake nasi goreng ya daura alokacin ba yadda ya iya Gaɓadaya ya birkice ga shi yana duba Lokaci domin suna da meeting a office.

Yana gamawa ya wuce toilet domin sai ya kara wanka kafin yazo ya jera a daining Zeeyter tana kallonshi sai dariya shi ko hararta kawai yake.

Cikin sauri sauri ya ci abincin ya tashi ya daukar shi ya fita yana, "Byee byee Bright Eye, Take Care Of You Self ban da rigima da neman jaraba."


Dariya tayi tana, "Byee Allah tsare hanya nima xan zo nan din yau ina ga."

Haiydar na zuwa office ba dade sai ga baban Yusuf domin yaje gidan mai Zeeyter ta sanar masa cewa yana nemansa.

Bayani ya mai akan inda hali ya nemo masa mijin Ayshatou da Ameenatou su dan tattauna.

Ba musu kuwa ya kirasu awaya ya masu bayani ba adau lokaci ba dukansu suka hallara a office din Haiydar.

Bayan sun Haiydar ya gabatar da kanshi garesu suma suka gabatar da kansu.

Haiydar ya ce, "To ba komai yasa na nemi zama da ku ba illa mu ɗanyi yar shawara wacce nake tunanin mafita ce zamu nemo mai billewa, kamar yadda mata sukan iya zama domin dakile matsalolinsu muma muna da wannan 'Yancin kar ku ce naku katsalandan ko shishshigi a rayuwar auren ku ayi mun afuwa Don Allah da duk abun da zan ce, amman kafin nan shin kuna da matsala ne da matanku?"

Mijin Ameenatou ya ce, "ehto Don gaskiya duk soyayyar da nakewa matata ta fara fita mun akai dalili kuwa komai nine,ba abun biyar da na taɓa gani wai yau ita ce ta siya ko tayi, kullum sai dai ta zauna agida in fita in nemo,shin daman haka rayuwar auren take ba taimako? Komai sai dai namiji ya yi? Ina matukar sonta amman dalilin rashin dogaro da kanta yasa nake danne soyayyar inyi abun da ya dace."


Mijin Ayshatou ya ce, "Ni ban da wata matsala da ita sai dai ita da take da shi kan batun soyayya, soyayya,ni ban iya wannan ba kuma banjin cewa zan iya haka rayuwata take kuma wannan shi ne tsari na."


Haiydar ya numfasa kafin ya ce, "ke Indai na fahimta kana son matarka , rashin taimakonka da kuma ganin ta dogara da kanta ke ma ciwo har kake aikata wasu abubuwan,kana da gaskiya wani bangaren wani kuma babu,domin da ace tun farko ka daurata a hanyar hakan dolenta za ta bi,kuma ka karfafa mata gwiwa tare da binta cikin ruwan sanyi,watarana in kana da bukata ba sai kaje waje ba zata iya magance ma, in Allah ya yarda matarka zata tsaya da kafafunta amman da taimakonka domin sai ka bata goyon baya ɗari bisa dari sai komai ya tafi daidai,sannan kuma ba wai za muna tunanin cewa komai ya kamata mata su dauka ba aa ,ko da zai kasance sun dogara da kansu hakkinsu na kanka za ku iya tsari acire mata daidai yadda zata iya tallafawa sauran kuma ya rage naka kun hadu domin rufawa juna asiri,ai ko ba komai an rage wani abun, amman ina kara jadadda maku duka cewa karkuna expecting komai mata suyi,ko komai kuyi dole akwai taimakeke niya a tsakani,sannan kuma wani abun dole sai anyi hakuri tare da kawar da kai kafin azauna lafiya.
kai kuma a gaskiya akwai matsala,kada ka manta mata na da rauni kuma suna iya shiga halaka ga abun da suke so,ka ga Ayshatou abar tausayi ce domin ba bada abinci da kaya bane kadai aure sauke hakkinta na wuyanka na tabbatar da cewa ta gamsu ko akasin hakan,da yawan wasu matan auren na bin maza ne in basa samun abun da suke so wajen mazansu na aure,na ce mene ne matsalarku ka ce damuwarta soyayya, ba soyayya ba ce damuwarta gabadaya kaine damuwarta ka biya mata bukatarta kuma ka sake mata jikin da zata aminta da kai tamkar abokinta, kuyi dariya tare kuka ma tare wannan shine zamantakewar aure,amman yanzu ksm ina tabbatar maka da cewa rayuwarta na cikin hatsari in ba a ceto ba zata iya fadawa ga halaka."

Mijin Ameenatou ne ya fara magana, "tabbas nikam ina son matata kuma in har zata gyara rayuwarta ta dogara da kanta zan tsaya mata kuma zan dawo fiye da yadda take zato ma ko tsammani."

Mijin Aishatou kuwa tsaki ya yi, "hakane maganar ka amman nikam banjin zan iya zama wannan bata Lokacin xan saketa kawai taje ta auri daidai ita,nima Allah ya bani daidai yanayina wannan shi ne kawai."

Haiydar ya ce, "to Alhamdu Lillah indai hakan ya yi maku duka Allah ss hakanne mafi Alkairi, ya bamu ikon kyautatawa abokan zamanmu."

Da haka suka yi sallama.

Suna fita sai ga kiran Farouk ya shigo vedio.

Sun fara magana kenan ya ce, "Ya Gimbiyata?"

Daidai da shigowar Zeeyter..

Haiydar ya dago ya kalleta kan ya ce, "bata da waya ne da ba za ka kira acen kuyi ba sai ni zaka isa ya take?"

Karaf Zeeyter ta fisge wayar.

Farouk na ganinta ya daga hannu yana, "Ah welcome Gimbiyata, kin ga wannan mijin naki ina tambayar ki yana mun wulakanci ashe ma kina tafe."

Dariya Zeeyter ta yi tana, "Wannan gimbiya ba zai fita abakinka ba Should i call you gimbiyina?."

Farouk ya yi dariya, "Why Not? Ai kin fi hakan aguna kowani suna ma za ki iya fada kai tsaye."

"Alright yakake ya kwana biyu ya kuma aiki?" Zeeyter ta fada.

Farouk ya ce, "Alhamdu Lillah komai na tafiya a tsari."

Katse masu magana Haiydar ya yi da, "Eheen aban wayata ko? Zan yi amfani da ita ."ya fada yana katse wayar

Harar shi Zeeyter ta yi, "What Ever! Mai katon kai kawai."

Haiydar ya kare mata kallo yana, "ke kuma matar mai katon kai ba, Oyaaa ki tafi Office ɗinki kiyi aikin da ya kawo ki don nasan in kina nan ba barina za ki yi ba ban da neman tsokana da rigima ba abun da mutum ya iya."


Zeeyter ta ce, "Anan zan yi fa,in kanaso mu koma can din tare aikin yafi dadi ina ganinka ina tsokanarka."

Tsaki Haiydar ya yi, "Hauka kawai."

"Anji din,ba dai fita zan yi ba." Zeeyter ta fada tana dauko files din.


08103080717
[6/25, 2:51 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-37*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

*TALLAH*

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

★★

Haka ba yadda Haiydar ya iya anan suka yi aiki tare har lokacin tashi ya yi.

A tare suka fito kowa ya shige motarshi.
Zeeyter na gaba yana Binta abaya domin ko ya kauce ma,ƙara tare hanya take ba damar da zaiyi gaba.

A haka har suka isa gida a tare.

Suna shiga Falo ta ce, "Oga Yunwa nake ji fa?"

Haiydar ya kau da kai kamar bai ji ba.

Ta kara cewa, "Oga na ce yunwa nake ji."

Ya kara fiskewa.

Gabansa ta sha tana jan gemun sa.

"Sunshine Na ce Yunwa na ke ji fa."


Haiydar ya ce, "Na ji, Why Not yau ki karbi agidan abinci ki ci, gobe sai inyi na gaji wallahi a idonki na yi ta aiki fa na gaji wanka zanyi inyi barci."

Taɓe baki Zeeyter ta yi tana shagwabewa, "ni wallahi ba zan ci ba,anan nake so kuma girkinka in ba naka ba Shikenan." Ta karasa maganar tana sake shi tare da shigewa daki.

Dafa kai Haiydar ya yi yana, "Oh My God,This Girl ba za ta taɓa bari in huta ba, rigimar yau daban na gobe daban."

Ko wankan baiyi ba haka ya shiga kitchen ya ɗaura abincin.

Ya gama hada komai kafin aka kira sallah,hakan yasa yaje ya yi wanka ya yi sallan kan ya hada abincin duka kan daining.

Ya kirata suka ci tare.


Wata Safiyar Asabar Zeeyter ta tashi da mugun ciwon kai wanda ya kai ga har bata iya ɗaga kanta sama,ban da hawaye ba abun da take.

Cikin hanzari Haiydar ya dauko mota suka nufi asibiti.

Test aka mata sannan aka bata magani.

Haiydar ya ce, "Doctor Why Not A mata madical checkup domin wannan ciwon kai bai zo da wasa ba sam ya ban tsoro, in an mata nima za amun kawai ina ga."

"Ok As You wish Sir." Doctorn ya fada.

Nan take aka yi masu madical checkup Dukansu,kafin suka koma gida da fadin su dawo ranar Monday su karɓi result.

Haka aka yi kuwa kwana biyu suka koma karbo result din domin kullum cikin ciwon kai Zeeyter take kuma ko da tasha magani ba wani saketa yake ba.


Suna zuwa Dr ya basu sakamakon tare da fadin, "Sir daga kai har Madame kuna cikin ƙoshin lafiya ta kowanni bangare.
ga yadda sakamako ya bamu, ciwon kai ma gaskiya ba mu ga komai ba sai dai aci gaba da daurata kan magani kawai har Allah yasa a dace."


Da haka suka bar cikin asibitin bayan sun karbi samakon.

Suna komawa gida restaurant din suka shiga domin yin girki daga ita har haiydar
Don watarana haka suke da kansu suke shiga suyi girki sauran ma'aikatan sai dai su tayasu.
Haiydar na suya ita kuma tana yanka vegetable kamar an tsikareta ta ce

"Sunshine."

"Yes." Ya amsa yana juyawa miyar da yake soyawa.

"Ina so inyi magana ne fa,ka kalleni,kuma ka saurareni ni." Zeeyter ta fada tana taɓe baki.

Haiydar ya ce, "Eheen ki bari mu koma gida mana,don ke kam bakin ki ba sakata.kwana biyunnan tunda baki da lafiya sabuwar rigima kikeson bullowa da shi fiye dana da,kuma in kika yi wasa sai na zauneki."


Dariya Zeeyter tayi tana, "a wani jikin? Ai ysn sai dai in zauneka, Uhumm ni magana zan yi."

Haiydar ya ce, "Na ce ki bari mu gama ko,in ba haka ba zan bibbige ki yanzu acikin jama'a sai ki sani suman tsaye."

Zeeyter ta teɓe baki tana un uni.

Sai da suka gama girkin duka suka ci.
Suna komawa gida Zeeyter ta ce, "ni ban manta ba fa,na ce zanyi magana."

"Oh Allah karki cinye ni ɗanye yi maganar ki kawai nikam." Haiydar ya fada yana zaunar da ita.

Zeeyter ta gyara zaman tana, "ka san komai dangane da ni,da kuma rayuwata ni marainiya ce kuma ga uwata nan guda ɗaya jal wadda ta kasance mun uwa da uba,amman kai ban san komai akanka ba, na san dai muna waya da Anty Rahma amman bayan ita ban san kowa ba,ban san komai da ya shafi rayuwarka ba,ina bukatar sani."

Nan da nan yananyin Haiydar ya sauya ya ce, "Ki bar maganar nan,bana so, ka da ma ki kuskura ki kara mun irinta in dai kina so mu zauna lafiya,in Lokacin ki sani ya yi zaki sani,kada ki kara daga mun maganar nan,ke ma ahalina ce kuma gamu muna rayuwa cikin farinciki sannan wa incen yaran su Miemie duk namune ba mu cika dangi ba sai kin tuna mun da wani lamari da na ke son shafe shi cikin rayuwata?." Ya karasa yana ficewa a falon a fusace.

Waje yaje ya zauna kawai domin shi ma wani irin gigitaccen ciwon kai ya fara ji.

Zuwa tayi ta zauna kusa da shi tana kama kunne, "I'm sorry may be i put d question in wrong way, but i have d right to Ask, because i want to know you better,but if i hurt you i do apology to you I am Really Sorry Sunshine."

Ta karasa maganar kamar zata yi kuka.

Rungumeta Haiydar ya yi yana, "ke kam rigimarki ta yi yawa, shikenan komai ya wuce."

Zeeyter ta dago tana kallon shi, "Thank you amman ka manta abu ɗaya."

"What?" Haiydar ya fada.

"Murmurshin Fuskarka har yanzu bai dawo ba,ka dawo da shi Please ,Baka kyau in baka Murmushi."

Murmurshi Haiydar ya yi yana, "Shikenan?"

Zeeyter ta ce, "Yes Tashi mu koma ciki zan baka labari mai dadi." Ta fada tana tashi tare da rike masa hannu.

Binta ya yi suka shiga tare.


★GHANA
Accra

3:00am

Kamar an tsikaresa ya farka abarci yana dukan matar dake gefensa ban da gumi ba abun da ke kwarara daga jikinsa

"Rukayya ki tashi,ki tashi ,ki tashi,ni fa kwana biyu kullum sai nayi mafarkin Haiydar ina so in ga ɗana ina so in gan shi,kullum sai nayi Mafarki Allah na mun azaba kan cewa na zubar da shi,ba zan iya jurewa ba Rukayya dole mu je mu nemo shi Aduk duniyar da ya shiga,balle ina da tabbacin yana cen kasar mu Jumhoriyar Nijar."

Tsaki wacce yake kira da Rukayya ta yi tana, "Wai Kai Kullum sai ka tashe ni ne in kayi mafarkin nan? Na hanaka nemo Ɗanka ne? Na ce na Hanaka nemo shi ne ko ƙa-ƙa? Ɗan ai da ya damu da kai shi zai nemeka ko, shin ba zaka tsaya gun wa inda suke gareka ba sai shi? To Wallahi Ahir dinka ." Ta karasa maganar tana sakin tsaki tare da kara juyawa.


ya ce, "ki shirya ki fadawa Deedarth da Unaisa su shirya zamu koma gidanmu na Nijar daga nan mu fara binciken Nemo Haiydar in sha Allah."

Ya fada yana tashi daga kan gadon.



Tsaki tayi ta kuma juyawa.

Shi ko alwala ya yi ya fara saloli.

Aranar suka kama hanyar Nijar duk da cewa Rukayya bata so,haka ma Unaisa Illa Deedarth da ke ta Murna.


Suna isa Abdoullaye da Deedarth suka fara binciken neman Haiydar kusan kullum suka fita sai dai su dawo babu labari.

BAYAN SHEKARA UKU.

Zaune suke dukkanin su a falo kawo ya aiki a System.

Haiydar ya ce, "Bright Eye wai ina su Miemie ne yau ba su shigo ba fa kin dubasu kuwa?"

Zeeyter ta ce, "Yau Saturday ka manta ba hutu suna islamiya tun 8 sai 6."

"Oh oh na tuna shiyasa da yanzu baby na nan ya addabeni."

Dariya Zeeyter tayi tana, "Labaran da yake baka ne addaba ko? Bari yazo zan fada mai kuwa."

Haiydar ya ce, "ke kin san ba za ki iya shiga tsakaninmu ba."

★★kamar wasa Deedarth ya tambayi wani abokinsa kan Haiydar nan aka dace domin kuwa ma'aikaci ne a Compayninsa.

Komawa ya yi ya sanarwa da Babansu nan take suka nuƙo hanya ba tare da son ran Rukayya ba.

Suna zuwa mai gadi zai hana kallo ɗaya ya ma Deedarth ya basa amsar tambayarsa hakan ya sa shi bude masu kawai suka shiga.

Zeeyter da Haiydar nata hira suna aikinsu.

Sallamar da aka yi ne ya sa su saurin dagowa a tare.

Matashiyar budurwa ce da wani matashi da gudu suka karasa ga Haiydar tare da rungumesa.

Sai ga wani dattijo da wata mata.

Haiydar ne ya dago da mamaki yana kallon su ya ce, "Deedarth? Unaisa? Kune?"

Murmurshi Deedarth ya yi ya karasa gaban Zeeyter yana, "Ina Hini Anty?"

Cikin Murmushi Zeeyter ta ce, "Lafiya lau barkanku da zuwa."

Haiydar ya karasa gaban wannan dattijon ya gaida sa.

Matar kuwa sai bin gidan take da wani mugun kallo

Ko da ya gaidata ciki ciki ta amsa.

Unaisa ma kallon banza ta yiwa Zeeyter ita ko Zeeyter ta saki Murmurshi tare da durkuswa gaban Dattijon tana gaidasu da fara'a ya amsa saɓanin ita matar kamar yadda ta ma haiydar haka ita ma ta mata.

Haiydar ya ce, "Baba, Anty, wannan ita ce matata zainab."
Ya dubi Zeeyter kafin ya ci gaba da magana, "Madame Wannan shine Babana,ga Antouna kuma da kaninne na Deedarth da Unaisa."

Kara kallon Deedarth ta yi wanda ba musu kana yi masa kallo ɗaya ka kalli wannan dattijon da Haiydar ba su da maraba ko kadan tamkar an tsaga kara.

Sabanin Unaisa da tai kama da Mahaifiyarta sak.

Kitchen Zeeyter ta nufa ta dibo masu ruwa da abinci ta jera.

Tana Tsokanar Deedarth , "To Mijin azo aci abinci ka ci abincina daga yau ba za ka kara cin abincin wata awaje ba."

Dariya Deedarth ya yi yana, "Ah haba dai Anty? Za mu gani kuwa ,don ni dai na san babyna ta fiki iya girki."

Ko da suka gama cin abincin tare Deedarth da Zeeyter suka tattara Plate din ya tayata suka gyara komai kafin aka dawo ana hira.

Haiydar ya ce, "Mamaki nake Ji yadda ka girma Deedarth? Ji Unaisa? Wannan da an kara shekara biyar ina ga ban isa in gane ku ba."

Baba ya ce, "Ai kuwa kam tun ba Unaisa ba da har tana kokarin fin yayan nata ma."

Unaisa ta kalli Antou tana taɓe baki, "Antou kin ji Baba ko?"

Wani irin murmushin munafurci ta ƙaƙalo tana, "Ai daman 'Ya mace sai da girma,kai Haiydar wai ina yaran gidan ne?" Ta fada tana waige waige.

Haiydar ya ce, "Yara kuma? Suna bangaren gidansu ai."

Ta ce, "Yara naka fa,ko har yanzu ba a samu karuwa bane?"

"Eh." Haiydar ya fada yana kawar da kai.

Girgiza kai tayi kawai tayi shiru.

Baba ya ce, "Kuma Lafiya? Anje asibiti an duba ko da mai matsala cikin ku?"


Haiydar ya ce, "Eh munyi Babba kuma duka muna lafiya lokacine dai ina ga har yanzu baiyi ba."


Deedarth ne ya katse maganar da fadin, "Ai gwanda ma Amaryata karta tsufa da wuri."

Dukansu dariya suka yi ban da Antou da Unaisa da ke bin kowa da ido kawai.


Sai da suka fita sallah kafin baba Haiydar suka tsaya suna zantawa,baba ya bashi labarin wahalar da suka sha wajen shekara uku suna nemansa basu samu.

"Haiydar ka yafe mun,mahaifiyarka ta bar duniya bare in nemi yafiyarta, don Allah ku yafe mun ko ba komai nikeda alhakin lura da ku amman na banzantar da ku a kullum inna tuna hakan ina jin zafi araina." Baba ya karasa maganar yana kuka.

Haiydar ya ce, "Baba kar ka damu ba wanda ya zarce wa kaddara, yanzu zanzo in kaiku gida anjima sannan zan nema maku wani gidan nan da sati ku koma sai ka zaɓa mota in canja ma taka, dawainiyar su Deedarth da Unaisa kuma in sha Allah yanzu ta dawo kaina."

Godiya baba ya yi Sosai yana shi ma haiydar albarka.
[6/28, 11:53 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci,

Please Login or Register in order to submit comment