Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayar ko da ta fito falo har yanzu su haiydar suna sheƙe ayar su ko kallonsu ba tai ba, ta nufi kitchen.



Tana shiga kitchen gwangwanin madara ta dauko ta bude,sannan ta fita waje ta tsinko Aloe Vera duk da haka dai haiydar da Meenoh na ta fama, ko ajikinta ta wuce tana shiga ta yanka aloe veran kanana ta zuba cikin karamar roba sannan ta s ruwa kadan ta juya, ta zuba madara (Milk) da zuma(honey) duka ta haɗa ta kwaɓa da ruwan fulawa (Rose water) kadan fuskarta ta bi ko ina ta goga, sai da ya dan dauki lokaci kafin ta wanke ya dauko kankara ta bi duka fuskar da shi tana gogawa.



Sauran ruwan madarar da ta hada da su aloe veran ta koma toilet ta wanke duka jikinta da shi,nan take jikinta ya fara tsantsi tare da canja kala.


Wannan ne ɗaya daga cikin haɗin da Zeeyter take yi na gyaran jiki, Lokaci bayan Lokaci.

Tana yawan shan Nono (Youghourt) domin shima yana matukar taimakawa wajen gyaran jiki, sannan ta kan shafa shi a fuskar ta na yan mintuna kadan kafin ta wanke

Wannan shine silar da ko taje an Caskale ta tabo ko kuraje basa taba zama ajikinta ko fuskarta, sannan bata amfani da wani mai ko sabulu wai don gyaran jiki tafi ganewa ta hada abunta ta gyara kanta da kanta a komai ma
za aganta awaje ragaje-ragaje da shiga duk irin wacce taso amman bata taba barin jikinta ba gyara.

Ta tafi kaunar gyaran jiki fiye da kaya ko kwaliya.



Tana fitowa daga toilet din ko kaya bata sa ba daga ita sai towel ta duba karamin fridge din dake ɗakin gorar youghourt ta dauko tana sha, sai da ta shanye tsaf har tayi barci.


Shi ko Haiydar da Meenoh afalon suka kwana.

Sai asuba suka koma ɗayan ɗakin suka kwanta.



Lokacin Sallah nayi ta tashi tayi Sallah sannan ta kara shafa wannan hadin kafin tayi wanka.

Yarinya da take yi wa Haiydar girki ne ta shigo tana gaisheta.

"Madame me za a dafa na karyawan yau."


Zeeyter ta ce, "duk abun da ki ja ya dace kawai,bara ma inzo in tayaki."

Tare suka je suka yi girkin Zeeyter na nuna mata yadda ya kamata tana yi,binta take sau da kafa ganin cewa tana da saukin kai fiye da zaton ta.

Suna gamawa ta fice kafin Haiydar ya fito.

Ko da suka zo breakfast da Meenoh ya ji mamaki da babban sauyi yadda abincin ya yi dadi.

Meenoh ta ce, "Baby Amman gaskiyar yarinyar nan ta iya girki ."

Haiydar ya ce, "Eheen nima abun da nake tunani ke nan girkin yau ya bambanta da na kullum zan so ace ta ci gaba da irinsa."


Dariya Meenoh tayi tana, "Food Master."


Haka Haiydar ya ci abincin nan ban da santi ba abun da yake, bayan Meenoh ta tafi ya duba fridge zai dau giya sam babu ko daya, wani irin ɓacin rai ya ji zuciyarsa na zafi,a harzuƙe ya fita yana neman Zeeyter amman babu ita babu labarinta, a zahiri ya yi tsaki yana, "Wannan mahaukaciyar yarinyar sai na nu mata tawa haukar yau agidannan zata dawo ai."


Rai a ɓace ya koma ya zauna kasancewar bai da wani aiki a office ,abubuwane kawai zai dan tsara a computer sai zuwa yamma kuma yaje ya duba.


Ita kuwa tafiyarta take cikin kwanciyar hankali harda tsalle-tsallenta ganin wasu yara cikin wani yanayine ya sata yin turus ta tsaya tana kallonsu.

Ruwa suka dibo aka gabadaya sun jigata domin daga gani kasan cewa daga waje mai nisa suka samo ruwannan, wasu acikinsu har kuka suke.

Ƙarasawa tayi gabansu ta ce, "Meyasa kuke kuka? A ina kuka dibo ruwannan?"


Dakyar daya cikin yaran ta iya kulata , "Mun gaji ne,kuma acen Dajin Kura muka ɗibo, saboda bama da rijiya anan."

Tana karasa maganar ta wuce kamar yadda sauran suka wuce.

Duniyar tunani Zeeyter ta fada domin a saninta ba karamin nisa bane tsakanin dajin kura da nan ko da kuwa a mota ne akan jima ba a isa ba bare kuma a kafa ga ruwa a ka.


Kai tsaye dauko wayarta tayi ta kira masu mata aikin bowol da rijiya na bobiel,ba jimawa kuwa suka zo bayani ta masu kan cewa asan yadda za ayi ko da rijiya biyune da bowal ɗaya a yi masu cikin ƙauyen.

Nan take kuwa suka fara aikin, ganin kudin jakarta bai da yawa ne yasata komawa gida domin ƙara masu yadda zai wadace su wajen yin aikin Yadda ya kamata.

Tana shiga Haiydar na zaune a falo da system gabansa yana dubawa.

Cikin Fushi ya sha gabanta yana, "Ina kika samun kayana? Ko in ce waya baki izinin taɓa mun kaya?"

Tsaki tayi ta ce, "Ban Sani ba,in kuma zaka sani in fada dole to Bismillah." Kokarin bangaje shi ta fara za ta wuce.

Cikin zafin rai ya daga hannu zai marata da jarumta ta rike tana, "Marina shi ne mafi babban kuskure da za ka yi arayuwarka kar ka soma a shawarce ko da ba ni bama kada ka kuskura ka ƙara ƙoƙarin marin wata."

Ta karasa maganar tana sake masa hannu tare da bangajesa ta shige ɗaki.


Tana shiga ya dauko key ya kulleta, "zan ga ta yadda zaki fita, in dai rashin kunya ne aikinki to ni kuma sai na gyara miki zama agidannan muna tare ai."




System dinsa ya sa a jaka da keyn ya yi ficewarsa yana mita.

"Ni yarinyar nan zata kawowa raini? Shin ni Ɗan ta ne? Haka ake business Marriage din ko ni ce aka hadani da wacce zata rainani, ba zai saɓu ba wallahi ba i most tech her a lesson."

Motar shi ya shiga ya bar gidan.


Zeeyter kuwa ta dauko kudin kenan za ta fita taji kofa a sarƙame.

"Ok wato kulleni ya yi a ɗaki? Yanzu aka fara game din."

Komawa tayi ta dauko abun kunce kuncenta tas ta kunce keyn kofar ta fito tana, "zan rama wannan ai mai sauƙi ne,ka taro fadan da zai fi karfinka."


Fitanta tayi abunta ta koma suka ci gaba da aikin, kowa yazo yana tambayar waya sa ayi sai suce suma basu sani ba kawai aiki aka basu wanda kuwa harda ita acikin masu aikin atakaice ma ita ke basu direction din abun da ya kamata su yi.


Haiydar na zuwa office sai ga kiran Farouk bayan sun gaisa ya ce, "Ya Gimbiyata fatan tana lafiya."


Tsaki Haiydar ya yi yace, "Oho waya san mata ka kirata mana,ni ko ya labarin wannan yarinyar baka ci gaba da bani ba."


Farouk ya ce, "Hum ni kam fa ina jin irinta ɗayace a ka yi aduniya, kullum damuwarta ta gina al'umma masoyanta ko maƙiyanta,ga kwalwala komai ta iya,ni ban ga abun da za ace yau ya gagareta ba."

Aduk lokacin da Farouk ke ba Haiydar labarin nan tsintar kansa yake cikin wata nutsuwa da farinciki na musamman wanda bai san dalili ba.

Numfasa ya yi ya ce, "Just Call Her YEL."


Dariya Farouk ya yi ya ce, "Exactly Abokina, barin barka ka huta, byee ni dai a gaida mun Gimbiyata."


Katse wayar Haiydar ya yi yana tunanin yadda wannan tauraruwar zata kasance.


Da gangan Haiydar yaƙi komawa gida domin duk a tunaninsa Zeeyter na ɗaki yana mata hukunci i yanzu taji jiki, har sai karfe 12 na dare ya koma Amman abun mamaki kofar dakin ya tarar abude sannan bata gidan ma gabadaya.

Cizon harshen sa ya yi azuciyarsa yana fadin, "wai wannan wace irin aljanar yarinya ce."

Zama ya yi yana tunanin ta ina zata bullo.

Kwatsam sai gata ta shigo kallon shi ta yi sama da ƙasa ta ce, "anyi bonono rufe ɗaki da ɓarawo." Ta karasa maganar tana gwalo.

Da gudu ya bita ta kulle kofar karaf

Tsaki ya yi ya koma ya zauna yana , "wannan yarinyar so take sai ta maidani mahaukaci kamar ita."

Zeeyter kuwa....


*YAU MA DAI AYI HAKURI BA CAJI WALLAHI😰 KAN WAYAR TA MUTU GA WANNAN*

08103080717
Urs Xayyeesherthou
[6/5, 4:13 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-21/22*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

*Sadaukarwa gareku,Anty Safina,Maman Yusra,Ummu Nanas da ma duk Members din shahararru ku ji dadinku Lobiyu lodi Lodi*


Me zata yi ban da dariyar mugunta.


Tafiya ɗayan ɗakin zaiyi ya kwanta karaf yaga Silifas dinta data cire garin gudu .

Tsaki ya yi,har ya shige ya fito, tsabar ya rasa abun da zaiyi don ya wuce,wuƙa ya dauko,ya yyayyanka takalmin adaidai kofar ɗakinta kafin ya shige.


Da asuba tana fitowa da shi ta fara ƙaro, rike baki tayi tana, "Takalmi na? Tabbas kuwa yau da takalmin ka zan fita,indai nice har sai ka gaji da ramuwa .".
Ta ƙarasa maganar tana kokarin shiga kitchen.

Ganin System dinsa kan table a fallonne ya dawo da ita,ta kunna. Ganin ba Password yasata yin Hamdala a azahiri.

E-mail din computer ta shiga ta kofe awayarta sannan ta hada wanni shirmen sako ta tura zuwa computer.

Yana shiga ta bi link din ta cikin computer.

Tana bi ya nuno mata yadda zata datse na aurar ta daina aiki haka kuma tayi ta tafi tana dariya.

In dai ba ta gyara ba ko ya fahimci abun da ya same computer ba zai taɓa iya aiki da ita ba,ko kwasan bayanan ciki.



Kitchen ta nufa suka hada abun karyawa da Humy mai aikin gidan.

Kafin taje ta yi wanka tasa kaya, ta fito za ta tafi kenan sai ga Haiydar ya fito shi ma daga ɗaki.


Ƙarasawa gabanta ya yi, yana damƙo hannunta, cikin isa da izza ta dago ta kalle shi da wani mawuyacin Murmurshi, tsintar kansa ya yi da kasa yi mata magana,ga jikinsa duk ya yi sanyi Mussamman da ya taɓa lallausar fatar jikinta, kawai ya saketa.

Yana saketa ta masa gwalo ta wuce, ficewarta ta yi.

Tsaki ya yi azuciyarsa yana, "Yau kam kin tsira Amman za ki dawo ki tarar dani gidannan sai na baki mamaki."

Daining ya nufa ya karya yana karajin mamakin yadda girkin Humy ke dadi na ban mamaki cikin kwanakin nan.

Yana kammalawa system din kawai ya dauka ya nufi office.

Yana zuwa zai fara aiki,amman da mamaki sam ya kasa gane kan system din, ya yi iya yinsa amman ya kansa,wani irin ciwon kai ne ya fara sauko masa, cikin hanzari ya dauko kwalbar giyarsa ya fara sha.


Zeeyter kuwa tana fita wajen masu aiki ta nufa anci Sa'a har sun karasa komai ya yi daidai, hakan ya bata ikon biyansu kafin ta wuce bobiel dake yau ma suna da taro akwai bukatar kasancewar ta da wuri.


Zeeyter Oil And Gas ta fara nufa da mamakinta aiki ya kankama domin kuwa Khaleel ne ke jagorantar ma'aikatan, yana basu umarnin duk yadda za suyi komai ta internet sannan suna nuna masa duk inda suka yi kuskure yana yi masu gyara.


Daga nan ta nufi gidan Marayu suna gaisa da Madam Ayshe tare da sauran yaran, wajen taron taje suka fara shiryawa da su Yusuf, sannan bangaren gidan abinci ma sun daura girki.

Misalin karfe tara daidai Madam Naddja ta zo tare da Matar da zata jogaranci taron, Sunanta Madame Sajida wacce take koyarwa babbar jami'ar dake jahar Nijar.

Taro ya kankama gabadaya mutane sun cika wajen wasu ma don abincin kawai suke zuwa amman ko ba komai zasu karu Da.


Bayan Sallama ta fara jawabi.

Sunana Sajida Malama dake babbar jami'ar Jahar nan, sannan a kullum cikin bincike nake kan yadda zamu gyara zamantakewar mu a gidan mazajenmu.
Kamar yadda maudu'in yazo."

Ta nufa kafin ta ci gaba da magana, "ZAMANTAKEWA TSAKANIN MATA DA MIJI

Idan aka faɗa hakan ana nufin rayuwa ce cikin aminci cike da ƙaunar juna,sannan kuma da girmama ra'ayin juna ba wai ɓangare ɗaya ba, zan fi yin magana ne kan ku mazan da basa sake wa matan su, wanda sam babu walwala bare farinciki cikin rayuwar aurensu,miji ya zama tamkar dodo ga matar shi, wannan sam ba rayuwa ba ce,kuma ba ɗaɓi'a ba ce mai kyau, gaɓaɗayanku sai kun gyara indai kuna son in ganta rayuwar aurenku, Ya kai Miji ga wance,Uba ga wance, ka sani ba kwanciyar aure ko ciyarwa ba ne kadai hakkin Mata a gareka, akwai bukatar ka girmamata,ka mutunta, ka tayata daukaka darajarta, domin ba baiwa aka kawo ma ba, da zaka mai da tamkar tinkiya sai dai dare ya yi kazo ka ci abinci ka hayeta in ka gama abun da za ka yi ka juya mata baya, subhannallah wannan wani irin miji ne? Ina ka bar darajarta na 'Ya mace? Ina ka bar kimarta bare kuma azo kan ra ayinta, kasance mai girmama ra ayin matarka a kullum, kada ka tauye mata hakki aduk kan abun da tasa agaba indai babu aibu bata ƙwarin gwiwa karfafa mata ko da kuwa kowa zai juya mata baya to babu kai ciki,in ko ka kasance hakan to ina tabbatar maka da cewa ka zama asararre, duk namijin da zai hana matar shi fita ta nema domin dogaro da kanta to ba ƙaunarta yake ba, sai a fake da wani batun kishin banza da wofi daga karshe azo ana wulaƙanta juna ba tare da taimakon kai ba, kafin in ci gaba bara in dawo kanki 'Ya Mace, ke ba baiwa ba ce, E na ce ke ba baiwa ba ce, haka kuma ko da igiyar gidanki na hannun mijinki to ba za ta taɓa jahuwa ba sai kin ja, Eh ina nufin sai kin dage kin gyara tsarin rayuwarki, ba zai yu ace kin zauna ba abun da kike ba,kuma ba abun da kika sani ba bare ki taimakawa mijinki ku rufawa juna asiri,komai ace sai namiji ba dole ya wulakanta ki ba, shin ke ba za ki iya fita ki nema bane? In baki fita ba,baxa ki iya nema cikin gida bane? Akwai bukatar ki san kasuwancin mijinki , sana'ar sa, abun da yafi so da duk wani abu da zai iya ɓata masa rai, ya kasance aduk lokacin da wani abu ya kulle masa kai fannin business din sa ke ce makullin da ke buɗewa ta hanyar ba shi shawara, haka kuma aduk lokacin da kuke zaune kada ki taɓa rasa abun cewa ko da kuwa ba ki da shi, lalubo irin hirar da yake so kuyi, Mussamman maza masu son kallon ball, ko da bakya kallo yi kokari ki haddace duk wani abu da ya shafi hakan yadda ba za ku taba zama babu abun tattaunawa ba, kada ki taɓa yin abun da zai ƙosa da shi,in kin yi wannan gobe canja salo yadda zai fi jin dadin hira dake fiye da kowa a duniya, sannan kuma wai azo batun kishi, miji ya ce zai ƙara aure ki zama karamar mahaukaciya,ke ce gun boka ke ce gun malam, zauna ki fuskanci mijinki shi za ki ma haukar ba wai wacce zai auro miki ba ko yan waje,in kuwa yaƙi shafawa kan ki ruwan Sanyi Kai kukanki ga Allah , Ubangiji baya taɓa zalintar bawansa kuma shi ke bi masa kadi aduk inda aka zalincesa, Addu'ar ki kan miji tamkar yankar wuƙa ce wajen Ubangiji, in Aurensa ne mafi albarka, Ma sha Allah, cire komai arai gyara zama, ci gaba da gyaran kan ki da gidanki,ci gaba da neman kudinki , sannan kar ki fasa duk wani abu da kika saba yi masa ada, inda hali ma ƙaro wasu,ya kasance kin san lungu da saƙo na duk wani abu da ya shafe shi, zamto maganin matsalar shi ta kowanni bangare,ina tabbatar miki da cewa ko mata ɗari zai auro kece xaki kasance ta Mussamman aciki,da farko kin kawar da kanki kan dukiyarsa, sannan kin dasa masa soyayyarki arai haka kuma kin siyawa kanki mutunci, aduk san da ya miki ba daidai ba kuwa kada ki taɓa rikewa arai fuskance shi ku dirji juna sannan daga baya a sasanta, wannan ita ce rayuwar aure mafi inganci.
Ko da saƙago aka aura miki babu shakka sai ya dawo mutum indai zai samu irin wannan kulawar,eheen sannan ku ba wai ina nufin komai mata bane aa kuma mazan ya kamata ku tashi tsaye ku san komai da ya shafi rayuwar matanku, kasuwancin su da sauransu.kamar yadda zata baka shawara kan kasuwancin ka,haka ita ma tana bukatar ka kan kasuwancinta, ko da ka ga ta tsara abune da kuskure gyara mata aa ga yarda ya kamata abi, sannan komai zai faru ku bar shi cikin gida da an fita waje an xama ɗaya ko da kuwa dambe kuka yi agidan,ku kasance masu goyon bayan juna ko da kuwa ɗayan cikinku ne bai da gaskiya , duk wannan in an koma gida sai a gyara,amman awaje kam ka da ku taɓa raba kanku,wannan ita rayuwar aure mai daraja kada ka zama dodo ga matarka sannan kema kada ki zama ɓera don kin ga kuliya ki birkice, juriya da jajircewa duk mace na iya haɗawa domin gina rayuwarta,a karshe ina ƙara maimatawa gidanku ya kasance tamkar lambun farinciki sannan a kullum kuna da labarin bayarwa ga juna, mutunta juna tare da sanin darajar juna, ba sai mata ce zata nemi irin kayan da miji ke so ba,kai kanka inka lura da irin kayan da ta fiso kasance cikin sawa musamman lokacin da kayi laifi, anan zan dakata, Allah ya bamu ikon kiyayewa da gyarawa, Allah inganta rayuwar mu cikin aminci,masu aure Allah kara dankon kauna,Yan mata Allah bada mazaje na gari masu fahimtar ra ayinku da darajarku."



Gabadaya jikin mata da mazan wajen ya yi sanyi,sun fahimci illa da suke yiwa rayuwarsu ta zamantakewa.

Ban da godiya ba abun da suke yi wa Madam Sajida,tun daga lokacin da yawan cikin suka fara fahimtar kuskuren da suke tafkawa.



Ana gama taron wannan saurayin Zeeyter ta kira Nasur.

"Barka Madame na ji dadin ganinki." Nasur ya fada.


Cikin sakewar fuska ta ce, "Nima na ji dadin ganinka,yanzu me ka ke ganin za ka yi?"


Ya ce, "Madame ni ba karatu nayi ba,ban da bangaren karfuna kema kin san ba abun da nake ganewa sai yawo a cikin gari."


Murmurshi ta yi ta ce, "hakane fa, to za abude maka shagon mechanic sai ka dauki wasu yara kuna aikin tare musamman ma yanzu da abubuwa suka mun yawa bai zama lalle ina samun lokacin yin abubuwa kamar da ba."

Nasur ya ce, "Owk Madame na gode Allah saka da alkairi, Allah jikan iyaye, ina alfahari da kasancewa dake a kullum, Allah jiɓanci lamuranki."

Murmurshi tayi ta ciro kudi a jakarta ta miƙa masa kafin ta tafi.


Ji tayi kawai tana bukatar hutu hakan yasa ta komawa Plateau da Wuri, abun mamaki yau har haiydar ya dawo gida.

Zaune yake a falo yasa system a gaba sai fama yake.

Tana ganinsa ta kyalkyale da dariya.

Cikin ɓacin rai ya ce, "Me kike ma dariya?"

Tsaki tayi tana kokarin wucewa ta ce, "Ban sani ba."


Zai tashi kenan sai ga kira ya shigo masa ta Sykpe, video call ne Khaleel ya kira.

Komawa ya yi ya zauna da nufin amsawa.

"Barka dai Aboki." Cewar khaleel.

Haiydar ya ce, "Barka."

Khaleel ya gyara zama yana, "da Matsala ne ya na ganka somehow?."

Tsaki Haiydar ya yi yana, "System dinnan ce na kasa gane kanta wallahi jiya lafiya na yi aiki amman yanzu sam na kasa gane kanta."


Wucewar Zeeyter Khaleel ya hango

Ya ce, "Hi Madam."

"Hello." Ta karasa maganar tana zama kusa da Haiydar, nan take yaji wani irin sayayyen kamshin jikinta ya daki hancinsa,bai san lokacin da ya lumshe ido ba.

Murmurshi khaleel ya yi ganin yadda Haiydar ya yi.

Ya ce, "Madam ya ayyukan suna tafiya daidai kuwa?"


Zeeyter ta ce, "Eh sosai gaskiya, Don ko da naje yau sunyi nisa a aikin sosai kuma komai ya tsaru yadda ya dace kai dai sannu da kokari."


"Maddalla,daman ina so in nuna miki wasu Injina wanda zasu maku amfani sosai, sannan a fadada ma'aikatan nan sosai ta fannin kawo gorina,yadda har wasu matan gidan zasu rage zaman banza."

Ya karasa maganar yana nuna mata hoton wasu injinan tace mai.


"Eh Sunyi kyau Sosai Muna da bukata,maganar ma'aikatan kuma na sa asanar da wannan ma In sha Allah, tunda yanzu muna bukatar kayan aiki da yawa ba zaiyu ace a tsaya iya yaran ba, harda mata masu zaman gida, dama samarin duk mai ra ayi."Zeeyter ta fada.


Farouk ya ce, "Weldone Madam aikin na kyau kuma yana burgeni, abokina ya kayi shiru ne ko duk tunanin computer ne?"

Ya karasa maganar yana kallon haiydar.

Dariya ce zata subucewa Zeeyter ta danne, suna haɗa ido da haiydar ya hararata ita ma ta rama, Murmurshi Khaleel ya yi ya ce, "Wato tsabar Soyayya duka kun bar gun aiki kafin Lokacin tashi kun dawo gida kuna kallon juna, bama wannan ba ya kamata a fara shirin taron bude haɗakar kasuwancinmu Kafin a gama gyaran companyn tunda ina zaton sun kusa kammalawa, bangaren office din ka da nata ne kawai ya rage."


A tare dukkansu suka kalli juna...



08103080717
Urs Xayyeesherthou
[6/7, 6:58 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-23*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim


Khaleel ya ce, "Oh Oh Dis Luv na ga alama yau kuna jin shaukin Juna, To Ni dai kar a manta da batun taron, Byeebyee."

Yana fada ya katse kiran.

Haiydar Da Zeeyter kuwa basu ma san yana yi ba,gabadaya sun tafi wata duniyar, ganin abun ba yi yasa haiydar fara rabata da kayan jikinta, ya yinda ita ma nan da nan ta fada cikin shauƙi, Lulawa suka yi cikin wata duniya ta ban, Mussamman Haiydar da ban da sambatu ba abun da yake yi.

Sai da suka tabbatar sun biyawa juna bukata kafin suka tsagaita,kowa na saukar da Numfashi.

Zeeyter ce ta fara tashi ta shige Ɗaki.

Bin ta kallo Haiydar ya yi kawai a azuciyarsa yana sakawa, "Ban taba jin irin ta ba, Daman Akwai mata kamar haka A duniya? Lallai Meenoh bata da komai kuma bata shayar dani komai,kuma bata iya komai ba,tamkar a mafarki, na kasa yarda." Wani irin kayataccen Murmurshi ya Sake a zahiri ka fin ya ci gaba da saƙawa, "Ina son yadda take, Amman yarinyar mahaukaciya ce." Ya karasa yana tashi tare da sakin tsaki kuma yana tuna wacce Farouk ke ba shi labari da yayiwa lakabi da YEL, a zahiri yake fadin , "Nasan sai ta fi mahaukaciyar cen komai."

Dakin da ta shiga ya bita, daidai Lokacin da ta fito daga wanka shi ma wankan zaiyi yana zuwa daf da ita suka bangaje juna tare da yin tsaki a tare.


Kafin ya fito har ta shirya ta fita waje tana jagaya unguwar duk da kasancewar dare ne amman ko ajikinta, ita kan ta azuciyarta jin hakan take ana Mussamman tamkar karonta na farko a kasancewa wannan duniyar.

Ji tayi wani na binta a baya tana juyawa kuma sai ta ga ba kowa, hakan ya sa ta tsaya cak tana tunanin ta ina za a bullo, ganin cewa taƙi motsawa yasa a turo mata wani baƙin basamuden kare, da gudu ya nufo gareta yana kokarin cizonta,dakyar ta samu ta kauce tana gudu yana bin bayanta, ta fadi,ta kurje, ta tashi ta ci gaba da gudu,da kyar ta koma gida tana shiga mai gadi ya rufo kofar da gudu.

Shi ko Haiydar in ya hango kasancewar ta su ba abun da yake sakewa ban da Murmurshi,Amman in ya tuna zeeyter kuma sai ya sake tsaki.

Yana fitowa ya ganta zaune duk ta kurkuje riga duk ta yage mai haiydar zai yi ban da dariya,har yana riƙe ciki,ƙula tayi kamar zata fashe cikin zafin rai ta ce, "Imbécile (Iskanci) Banza mai kan gwanda kawai Ido Kamar Gujjiya."



Tsaki tayi ta wuce daƙi tana tafiya da kyar.

Shi ko Haiydar ya kasa daina dariya sam Mussamman in ya kara kallonta tana tafiya da kyar ga jiki ko ina na girgiza.


Shigewa tayi ta shige ɗaki domin gasa jikinta ko zata samu ta yi barci.


Shi kuma zama ya yi yana dauko System dinnan ransa ya jagule ya ɓaci har ya manta da cewa ya yi wata dariya, gabadaya damuwa ya shiga ganin cewa gobe yana da meeting,kuma komai na baya nan meeting din na ciki.
Number Farouk ya kira don

Please Login or Register in order to submit comment