Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke nan Yayar Mahaifiyar Haiydar.wacce suka koma gunta alokacin da Antou tai sanadiyar barin mahaifiyar sa daga gidan babansa wanda bayan rasuwar maman ta sa ita ta ci gaba da kula da shi har ya girma ya tsaya da kafafunsa kafin daga bisani ta koma Saudiya da zama.


★★★ci gaban labari
Sun gama waya da Ammie kenan Zeeyter ta ji wayarta ta yi ƙara kamar yadda aka saba alert ne na kudi wanda tamkar albashi yake duk karshen wata sai an turo kuma har yanzu ta rasa gane wane ne.

Ta ce, "Sunshine koma wane ne mai turo kudinnan nikam kullum ina mai addu'a da fatan alkairi na wancen watan ma cikawa nayi na bada ayi masallaci a ƙauyen ƙaura wannan kuwa ina ga makaranta za mu gina masu domin yan ƙauyen na fama da zahilci ba arabi na boko wannan ai babbar masiba ce."

Murmurshi ya yi, "duk mai badawan ma yafi bukatar aikata alkairi ne fiye da asan shi, Allah ya mai albarka,kuma ya biyasa da Alkairansa,ke kuma Allah baki nasara adukkan aiyukanki na alkairi da kika sa agaba, sai ki samu Khaleel ku tattauna yadda ya kamata Makarantar ta kasance tun da kin ga kauye ne."


"Ameen Ameen ya Allah, can't love you less my Dan Lukuti acici, karfafa mun gwiwa da kake ya fi komai faranta mun ayanzu kam cikin rayuwata, bari dai in zama Hajiya zan yi maka rumbun abinci acikinka yadda ba sai ka ci ba za ka ji ka koshi."

Dariya ya yi yana, "Allah ya shirya mun ke Bright Eye."

Shigowar Deedarth ne ya dakatar da su kasancewar dare ya yi.

Alwala suka yi shi da Haiydar suka fita zuwa masallacin da ke gidan.

Suna fita Zeeyter ta shiga daki kenan aka kashe wutar gidan ga shi ta bar wayarta afalo.

Dibirbircewa tayi tana neman hanyar fita sai aka kunna.

A kunna a kashe a kunna a kashe ga wani irin taku da take ji tamkar ba mutum ba.

Daura hannu tayi aka da tayi wata kara daidai lokacin da suka idar da salla karaf Haiydar yaji a kunnesa.

Ko takalmi bai sa ba ganin yadda ya hango gidan ba wuta ya nufa.

Deedarth ma ya bi bayansa tare da tsayawa wajen inda wutar gidan take ya kunna.

A gigice Haiydar ya shiga gidan Zeeyter ta make agefen daki ban da rawa ba abun da jikinta ke yi ga hawaye da kwararowa daga fuskarta,tana ganinsa ta rungemsa tana, "ba za abar ni ba, wallahii kashe ni za suyi Shikenan."

Share mata hawayen ya yi ya zaunar da ita kan gado sannan ya dibo ruwa ya bata ta sha.

"Ba komai in sha Allah ki kwantar da hankalinki, ina tare d ke kinji."

A lokacin ta tashi tayi sallah tukun ta dawo ta kwanta a jikinsa ba tare da ta ce komai ba.

Deedarth kuwa dudduba gidan ya yi bai ga komai ba, ya dawo ya zauna yana jin takaicin wani azzalumine ke son ganin bayan zeeyter.


Washegari

Da sassafe sun dawo daga training.
Suna hutawa kenan Deedarth ya ce, "Anty me za ayi na break ne?"

Kafin Zeeyter ta bada amsa an fara nocking kofa.

Zuwa ya yi ya bude da Mamaki,Baba ne da Antou da kuma Unaisa.

Cike da mamaki Deedarth ya ce, "Baba Lafiya?"

"Lafiya lau Deedarth batu ne kawai muka zo da shi."

Ya ƙarasa Maganar suna shigewa falon.

Suna shiga shiga kowa ya zauna da sauri Zeeyter ta tashi tana gaida Antou kai ya kauce ta amsa Unaisa ko ban da kallon banza ba abun da ba abun da take yi ma Zeeyter, ko da ta gaida Baba ba yabo ba fallasa ya amsa.

Haiydar na gaida Antou kuwa cikin fara'ar kissa ta amsa, Unaisa taje ta rungume shi tana Murmurshi.

Gyaran Murya Baba ya yi yana, "To kun ganmu da sanyin safiyar nan, to batu ne ya tada mu batu wanda bana sanya bane, game da kai Haiydar mun yanke hukuncin da muke ganin yafi dacewa da kai da mu ma gaba-daya,domin zama da mata ɗaya ba naka ba ne,akwai yarinya ta wajen kawar Antounku Sadatou Mun zaɓa maka a matsayin wacce za ka ƙara a mata ta aure."

Wani irin mugun faduwar gaba Zeeyter ta ji, zuciyarta na bugawa cikin sauri a zaune take amman sai da jiri ya ɗibeta.



*Kwana biyu fa comments ya yi karanci zan yi maku tawaye😒😒*

08103080717
[6/30, 1:08 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-40*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

★★

Ganin ba za ta iya jure sauraren batun ba yasa ta saurin tashi ta nufi daki.

Tsaki Antou tayi.

Haiydar da Deedarth kuwa bin da ido suka yi.

Cikin zaƙuwa Deedarth ya ce, "Baba meyasa haka? Meyasa za ku ce haka? Me Anty ta rage Yaya da shi." Ya karasa maganar yana kokarin bin bayanta.

Cikin tsawa Antou ta dakatar da shi da fadin, "Kul na ce ma kul, Alhaji ka ga abun da nake fada ko? Ko baka gani ba? Rawar kafa yake zai bi biyanta me aka mata? Ince kishiya aka ce ba komai ba wanda Allah ya hallita ayi uku ma bayan ita? To dawo ka zauna ba za ta saɓu ba,baza amaidani uwar gantallu ba." Ta karasa maganar tana wuci kamar bijimin sa.


Deedarth ya koma ya zauna , "Antou Amman hakan bai dace ba sam ko da za a nemi ya kara auren bai kamata a fada gabanta ba,wannan ai kamar cin fuska ne, Gaskiya bai dace ba."


Baba ya ce, "ka ci gidanku na ce ungo nan ka ci gidan ku,kana nufin ka fi mu sannanin abun da ya dace kenan?mune muke ba daidai ba amman kai kana daidai ko? Hakan ya yi kyau,ko shi dan uwan naka bai musa zancen mu ba sai kai uban yan kaudi ka shiga tuggun mata zan yi maganin ka ne."



"Ahto ai ruwa ba ya tsami banza an gama da dan uwansa ne aka dawo kansa kuma wallahi ba za ta sabu ba zan dau tsattsauran mataki."


Haiydar kuwa kan shi a ƙasa ya ce, "Baba na san duk batunnan ba zai wuce kan haihuwa ba, kuma kamar yadda na sanar ma munje asibiti an duba mu lafiyarmu kalau sannan na yarda da wannan gwajin dari bisa dari,lokaci ne kawai baiyi ba ko ince Allah bai bada ba, bare ni bana daukan kaina a matsayin wanda bai da 'Ya'Ya yara birjik ne cikin giddanan wanda Zainab take raino komai ita take daukar dawainiyarsu tun suna jarirai har yanzu da suka fara girma, na dauke su tamkar 'Ya'Yan cikina domin kuwa Allah kadai yasan dalilinsa na yin hakan, watakila suna mafi Alkairi gare mu a yanzu ko da ace nan gaba za mu iya samun haihuwar. Ita kanta Marainiya ce amman hakan bai hanata walwala da inganta rayuwar yan uwanta marayu ba, ba abun da na nema na rasa gareta farinciki daidai gwargwado Alhamdu Lillah muna samu ina ga ko da 'Ya'yan cikin da zamu haifa ne baza su kasance mana yadda muke so ba kamar marayun cen,ta kasance dani lokacin da nake cikin kadaici, ta haskaka mun rayuwata babu amfani ace za a wulakanta mace wai don bata haihu ba, Gwanda in ya kasance ra ayine ga mijin ya kara ba laifi, Amman muna tunawa duk zafi da raɗaɗi bamu san irin wanda take ji azuciyarta ba take dannewa ba tare da ta nuna ba, amun wannan alfarmar a bar maganar kara aure ina son matata aduk yadda take kuma Aduk yadda za ta kasance."

Baba na kallon Antou ta kyafta masa ido tare da girgiza kai.

Gyaran Murya Baba ya yi kafin ya ce, "Na ji kuma na yarda da batunka amman maganar kara aure ba fashi, domin rashin haihuwarta bai dameni ba, a yadda kake ya kamata ace qn samu mata biyune a giddanan ba ɗaya ba, abun kunya ne a gareka ma ace mata ɗaya kake da sam hakan baiyi ba kuma ba tsari bane, na riga na yanke hukunci sannan yarinya za su zo da Unaisa har gida ku fahimci juna ba sai kaje can ba mun yanke wannan hukuncin da Antounku,bana son jayayya ko wani batu magana ta kare."

Deedarth ya bude baki zaiyi magana Antou tai saurin dakatar da shi, "To shugaban marasa kunya za ka kara ja da maganar ko? To Ahir dinka maganar aure anyi an gama kai kanka aurar da kai zan yi kwanan nan don ba zan bari a lalatamun kai abar ni da salati ba."


A lokacin Baba ya tashi yana fadin, "ni dai na gama magana,ku tashi mu nufi gida in samu inje gun aiki."

Haiydar ne ya rakasu har inda suka yi parking mota sai da ya ga fitar su agidan kafin ya dawo

Deedarth kuwa na falo ya yi tagumi ya rasa meke yi masa dadi domin yasan wannan tuggun duk na mahaifiyar sa ne.

Cikin daki Haiydar ya nufa ya samu Zeeyter kwance tana kuka.

"Bright Eye,mene ne na kuka? Ki daina kuka kada kan ki ya yi ciwo mana." Ya fada yana zama akusa da ita.

Matsawa tayi tana share hawayen dake fuskarta.

Ya kara matsowa inda take yana rike hannunta.

Ta fisge .
A karshe ma tashi tayi ta fita adakin ta koma ɗayan tare da kulle kanta.

Buga kofar duniyar nan Zeeyter taki budewa ranar ko office ba ta je ba adaki ta wuni ba ci ba sha.

Tun daga ranar Haiydar ya kasa gane kan zeeyter domin in dai yana guri to bata zuwa inko zuwa inda take ya yi nan take zata bar gun.

Ta kai ga kullum baya sanin tafiyarta da dawowarta daga Office.

Tana dawowa zata shiga daki ta kulle kofa

In dai ka ganta tana magana da dariya sai dai in Deedarth ne ko su Miemie sunzo suna hira, suma din tana ganin Haiydar duk dariyar da take zata bari ta bar wajen.

Ko ya mata magana bata kulawa in ma abun da ya shafi companyne sai dai ta tura Deedarth ko Halliru koma miye.


Dukkaninsu kowa ya shiga damuwa da ka gansu zaka tabbatar da cewa akwai matsala ko da Madame Ayshe ta ma Zeeyter magana ba ta ce komai ba.


Hatta daki sun raba kowa a na shi yake kwana.

★★★Wata Safiyar Lahadi.

Zeeyter na zaune a falo tana break Sallamar Unaisa da Saudatou ne ya dago da ita.

Daidai da fitowar Haiydar daga dakinsa.

Unaisa suna haɗa ido da Zeeyter ta galla mata harara, Sadatou kuwa karasa wa tayi gaban Zeeyter ta na gaidata, "Ina kwana ANTY?"

Wani gigitaccen kallo ta mata ba tare da ta amsa ba ta kawar da kai tana sakin tsaki.

Murmurshi kawai Sadatou tayi taje ta zauna afalon tana wasa da ya tsunta.

Unaisa kuwa zuwa tayi ta rungumi Haiydar tana, "Yaya Ga Anty Saudatoun Baba ne ya ce in rakota.
Ka ganta a falo kyakkyawaa Wallahi Yaya,Ina sonta."

Dago kai Zeeyter ta yi suka hada ido da haiydar
Murmurshi kawai ya sake tare da fadin, "Nima kuwa ta mun kyau tun kafin in karasa gare ta."

Rike masa hannu Unaisa ta yi tana, "Yawwa Yayana na san za ka sota ai, kyakkyawaa ce sosai fa muje."

Ta karasa da shi har falon ya zauna kusa da Sadatou.

Kallon Zeeyter tayi ta sake wani irin tsaki afusace ta bar falon.

Haiydar na lure da ita ya kare sake wani Murmushin.


Ya ce, "Unaisa ki je dayan falon muyi magana da Antyn taki ko."

Unaisa ta washe baki tana, "Tom Yaya." Ta fice.

Murmurshi Sadatou ta yi ta dago tana, "Barkanmu da warhaka barka da safiya Yaya Haiydar."

"Barka dai ina fatan kina lafiya." Haiydar ya fada yana kau da kai.

Sadatou ta ce, "Alhamdu Lillah kamar yadda ka ke in sha Allah."

Gyara zama ya yi yana, "To na san dai kin san dalilin da yasa aka turo ki gidannan ba buƙatar in maimaita,amman kuma gaskiya ni ina son matata fiye da kowa a Duniya, farinciki da walwalata duk sun tattara ne a gareta ,ba zan iya mata so kadan ba,bare kuma inyi karyar hada soyayyarta da wata, ko da zan aure ki.....

Ba ta bari ya karasa ba ta katse shi da fadin, "Ayyah kar ma akai ga nan,Duk na san hakan kafin zuwana, na san kana son matarka son da kai kanka ba ka san adadi ko yanayin son ba,kuma ko shigowata giddanan a yanzu na ga tsananin kishi da kaunarka acikin idon matarka ban ga laifinta akomai ba kuma a ko ina, sam sam ba zan shiga rayuwarku ba na maka wannan alƙawarin ba ma zan iya ba,kasan iyaye ba a kin ta tasu azahiri Amman a badini muna amfani ne da abun da ke cikin zuciyoyinmu, ka sa aranka cewa ba za ka aure ni ba,ni ma kuma nasa hakan ina da wanda nake so. zasu fahimta a hankali abu ɗayane za mu yi da zai iya daidaita komai can we be friends?"

Ta fada tana mika masa hannunta.


Murmurshi ya yi shi ma ya mika mata yana mamakin yadda yarinyar ta kasance mai hankali da tunani haka.

"Why Not? Daga yau ma nine babban abokinki." Ya fada yana dariya.

Ita dariyan ta yi tana, "Eheen ba matsala ai daman ina rashin aboki yanzu kam na samu."

Hira suka sha sosai cikin aminci da farinciki har suka yi exchanging number waya.

Zeeyter na kallonsu ta window sai ƙula take kamar zata fashe, zuciyarta na buguwa cikin sauri.

Wani irin haushin Haiydar take ji kamar ta bige shi ya fada.

Da kan shi ya dau mota ya maida su gida.

Yana fita Deedarth ya dawo yana tambayar Zeeyter meya faru.

Cikin kuka take ba shi labarin.

Ya ce, "Anty share yaya fa ba naki bane ke da kike ba mata shawara ka da ya kasance kinyi na banza ki kara dagula gidanki da kanki."


Zeeyter ta ce, "Na sani da laifi na Amman shi ma fa nunawa ya yi yana sonta ba ka ga yadda suke bane kafin su bita har yana karban numberta me zan yi? Ya ake so inyi? Amman shikenan koma mene ne bara ya dawo zan mai magana in ba shi hakuri."


Da haka suka ta tattaunawa har ta danji sanyi aranta.

Ya tafi masallacin kenan sai ga Haiydar ya shigo.

Da sauri Zeeyter ta je zata mai magana ya yi saurin kawar da kai yana sa waya a kunne.

"Hello Baby Kin shiga gida Lafiya? Ka da ki manta fa ki kula mun da kanki sosai ina sonki." Ya karasa Maganar yana kissing din wayar.

Wani irin zafi Zeeyter ta ji aranta, tsaki ta yi ta wuce daki.

Shi ko ya kalleta ya kyalkyale da dariya.


Wayarta ta dauka ta fara chatting da Farouk.

Da yanayin maganar ta ya fahimci cewa akwai matsala.

Farouk ya ce, "Madame! Lafiya kuwa na ji ki yau ba walwala."

Numfasawa Zeeyter ta yi kafin ta ce, "umm wai aure zai kara."

"Aure? Ikon Allah aure kuma to meya faru laifi kika masa?"


"To wa ma ya sani, iyayensa ne suka fara bukata amman shi ma ya nuna yana so."


Farouk ya ce, "Eheen to sai me? Wannan ai ba abun damuwa bane akwai kishi dole Amman kin fini sanin hanyar da ta dace ki bi domin yi cikin inganci, in ma matar dari ne ya karo Amman ki tsere kanki ki zarce kowacce ba wadda ta isa ta kara da ke."


Hira suka sha sosai da Farouk

Daga ranar Haiydar na ganin Zeeyter shi ma ya ke kau da kai tare da kaucewa duk wani abu da zai iya hada su.

Yana ganinta zai fara waya da Saudatou.

Hakan yasa kowa ya kara fita sabgar kowa.
Sai dai suje office su dawo ana zaman doya da manja.


Fannin su Antou da Hajiya maman Sadatou kuwa shirye-shiryen biki ya kan kama ana ta yi.


Suna zaune ita da Deedarth suna break Haiydar ya fito.

Deedarth ya ce, "Yaya Barka da safiya."

"Yawwa Deedarth daman ina so in baka details din katin bikin nan ka je abugo don aiki ya mun yawa kwana biyu."


Da sauri Zeeyter ta......


08103080717

[7/2, 7:20 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-41*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

*TALLAH*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

★★


Dago tana kallon haiydar.

Kau da kansa ya yi yana danna waya tare da saurin ficewa.

A fusace ta sha gabanshi ya bangaje ta ya fice.

Agun ta durkusa tana zubar da hawaye.
Da sauri Deedarth ya ƙaraso yana, "Haba Anty kar ki mun haka, ki daina Don Allah,Don Allah na ce kar ki mun haka, kuka bai cancanci rayuwarki ba, ke kika koya mun kayi Murmurshi aduk sanda kake cikin matsala sannan ka kira Allah da ya kawo maka dauki domin shi kadai ne ma ji roko da kukan bawansa,Anty ki yi Murmurshi ki mikawa Allah lamuran ki kamar yadda aka saba komai zai wuce."

Rike mata hannu ya yi ta tashi tana sakin Murmushin da ya kasance na dole da bai kai har izuwa ga zuci ba.

"Thank you." Ta furta tare da shigewa daki.


Haiydar na office zaune suna call ta Sykpee 5Stars.

Bayan sun gama Farouk ya ce, "Kai Abokina wai yane ya Gimbiyata ta ce mun akwai damuwa fa."


Dariya Haiydar ya yi yana, "Barta da shirmen ta ba komai fa Dadyne ya zo wai sai na kara aure, har an hadani da yarinyar amman mun gama tsara komai yarinyar bata da Matsala ba wani babban issue bane har na magance shi amman in ya kasance da matsala i wil let you know in sha Allah, yanzu kam komai daidai."


Deejerh ta ce, "Ah dole fa ta damu wannan ne ba babban issue ba? Kuna da son kanku maza."

Karaf Farouk ya ce, "Yi mana shiru ni yanzu abokina ko za a hadani da yarinyar ne mu sasanta kawai?"

Dariya suka yi duka.
Khaleel yana, "wato dai ba zaka canja ba son matan nan yana nan zan ma aure in huta."


"Da dai yafi kam Haiydar ka bincika mun yanayin aure a niger za mu zo ayi a gama kawai."

Da haka suka ta Tsokanar Farouk har suka rabu.

★★★Antou zaune da momyn saudatou ana ta shirye-shiryen biki.

Tura Unaisa Antou tayi ta kira saudatou tana zuwa ta ce, "Haba haba saudatou kamar ba amarya ba? Ko irin gyaran jikin nan ma fa ban ga kin fara ba ga baki saura kwana uku kacal sannan banji kina batun yin wasu abubuwa ba,ko kawaye bana gani suna yawo cikin gidannan tunda nazo."

Mamin Saudatou ta ce, "umm Aminiya kin dai gani,ni tun ina magana har na hakura na bar batun tunda ba za ta yi komai ba ai Shikenan kishiya dai gareta in ba ta koreta ba,mu a karo mana ita."

Da sauri Antou ta ce, "Subhannallahi Aminiya kin manta ni ne? Ai wuyarta ayi Auren sauran komai na gareni ,sai dai mu mu fitar ai ba a isa a fidda mu ba wallahi ko samun mutum muka yi aciki zamu fitar muyi kane-kane kin sanni sarai ba wasa."
Ta karasa maganar tana mikawa Ammin saudatou hannu.

Mika mata ita ma tayi suna shewa a tare.


"maddalla da Aminiyata Shiyasa kullum nake kara alfahari da ke, samun ki babbar nasara ce a gareni, amman ni fa damuwata sam saudatou bata fahimtar komai."

Antou ta kalli saudatou tana, "Ke wai lafiya kuwa,meke damunki ne ?"


Murya a sanyaye Sadatou ta ce, "Anty wallahi ni bana son Haiydar kuma shi ma baya sona, we are just a friends ba komai ba,daga nan ba kari,inda zaku bar batun auren nan zaifi wallahi,ku bar shi da matarshi suna son juna."


Salati Antou da Ammin saudatou suka fara a tare da sallallami.

Antou ta ce, "Saudatou wai so kike ki tozarta mu ki ba mu kunya? Ko ince ki zuba mun kasa a idanuna? Me kike nufi? Wai duk fadi tashin da muke ni da mahaifiyarki ya tashi a banza? Ba zai saɓu ba,kuma ba zai yuhuba ya zama dole ayi auren nan ko kinki ko kinso."

"Hum ga shi nan dai kina gani kuma kina ji ga dukkan alamu bokan wannan munafukar matar tashi ya yi aiki akanta ba musu ba shakka." Ammin saudatou ta fada tana nunata.

Tashi tsaye Antou tayi tana, "ban ga ta zama ba, wallahii ban ga ta zama ba,tabbas zan je in kara tunzura Alhaji ayi auren nan cikin gaggawa in ba haka ba waccer tsinanniyar yarinyar ba za ta taɓa bari mu cika burinmu ba."

A fusace ta fita Unaisa ta fita da jakarta suka tafi.

Ammin saudatou kuwa dukanta ta fara yi ba ji ba gani tana fadin, "Shegiya matsiyaciya hassada kike mana da samun arziƙi to wallahii kinyi kadan yo ban da ma ni nayi tsufa ai wlh da sa ubanki zanyi agefe in aure shi,Allah wadaran naka ya lalace kamar bani na haifeki ba wallahi arxiki na binmu kina korarsa."

Antou na zuwa gida ta samu Baba ta kara kitsa masa gaskiya da karya duk abun da ke faruwa tare da umartashi kan cewa adaura aure ko yanzu ne in ba haka ba Zeeyter zata raba Haiydar da komai,da kowa.

Hakan yasa baba ya kira meeting din gaggawa na duka kafin yanke hukunci a daura aure.
Dukansu gidan Haiydar suka nufa harda saudatou da Amminta.

Suna zuwa ya fara jawabi, "To na ji wani lamari da ya kunno kai kuma wanda karara an nuna cewa laifin ki ne ko in ce da sa hannunki aciki." Ya fada yana nuna Zeeyter dake gefe tayi jigum.

Gabanta ne yyi mummunan faduwa tana kallon baba.

Karaf Antou ta ce, "Bakar munafuka ba, ko ma menene daga ke har bokan naki munfi karfinku wallahi kuma aure babu gudu babu ja da baya, saidai ki kashe kanki in kinso."

Haiydar ya ce, "Aa fa, kome xa ayi ban da cin zarafi Antou koma miye ya tsaya iya kaina."

Kallon baba Antou tayi tana hawayen munafurci.

"Alhaji ka gani ko? Na fada ma ta mallake shi wallahi in har ba mu dau mataki ba shikenan kuma."

Dogon numfashi baba yaja yana , "Tabbas na ga zahiri to wannan auren babu fashi atakaice ba yanzu za a daura shi da mun fita Masallacin gidannan."

Zeeyter ta tashi tana kuka kenan zata tafi daki daidai da shigowar Ammie tana, "Ba fa za ayi wani aure ba,na ce ba fa za ayi wani aure ba, yanzu kuka san cewa shi mutum ne da har za ayi gadara akan shi iye? Na ce yanzu

Please Login or Register in order to submit comment