Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-38*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

*TALLAH*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

★★

Sai bayan sallar magriba ya maida su gida.

Deedarth kam ma bai tafi ba agidan ya zauna.

Washegari da sassafe Haiydar ya sa aje anemo masu sabon gida.

Deedarth da Zeeyter na kitchen suna haɗa kayan break.

Haiydar ya shigo yana, "Wato kazo kana son kwace mun mata karfi da yaji ko?"

Dariya Deedarth yi yi yana, "To ai daman tawa ce ba taka ba aro na baka ko ba haka ba Anty?"

Cikin dariya Zeeyter ta ce, "Eh mana ina ganin fine guy kamarka ai shi yanzu ya mun tsufa."


"Iyee ni ko? Dukanku zan rama, yanzu dai ba wannan ba,wani aikin zan yi abani nawa inyi." Cewar Haiydar.


Deedarth ya ce, "Anty kin san Yaya zaiyi kyau da dakan sakwara kawai mu ba shi dakan."

Dariya Zeeyter tayi tana kallon haiydar, "Yoo wannan ina zai iya? Kace dai ya fasa mana doya kawai."

Dukansu suka yi dariya

Haiydar na nannaɗe hannun riga ya ce, "Eheen aiko zan baku mamaki duka,ina doyar,dakun sakwarar Saudiya za ku ci agidannan, ba dai ni kuka raina ba."

Dariya suka yi Zeeyter na fadin, "We shall See Oh Oh."

Nan da nan Haiydar ya dage ya fara dakun sakwara yana zufa yana kara dagewa har sai da ya dakata lugwi ya kalli Zeeyter da Deedarth, "Kun ga bambamci ko? Na ce za ku iya daku irin wannan? Yara kuna wasa,baku san ni wane ne fa."


"Laaa Yaya daman ka iya? Anty ki ga yadda ya dakata sosai fa." Deedarth ya fada yana duba sakwarar.

Zeeyter ta ce, "Inhin Daz My Sunshine, mene ne ma ba zai iya ba da yardar Allah,Really Proud Of You." Ta fada tana rungume Haiydar.

Kissing dinta ya yi ya ce, "Thank you, Proud Of You More Bright Eye."

Zuwa tayi ta dauko Yam pounder tana nuna masa tana dariya, "Boyewa nayi daman in ga ko zaka iya."

Ta fice a kitchen din da gudu yana binta, "wato da yam pounder agidannan amman shi ne sai da kika bani wahala wannan yarinyar in kika shiga hannuna baza kiji da dadi."
Ya karasa maganar yana damkota.

Tsugunawa tayi tana riko ciki, "Wash cikina."

Da sauri ya durkusa shima "mene ne?"

Saki shi tayi ta tafi tana masa gwalo da dariya.

Shima dariyar ya yi.
Karasa hada kayan a break din suka yi kan suka shirya kan daining, tare suka ci,cikin wasa da dariya.

Shiryawa Haiydar ya yi tafi Office, Deedarth kuma gidan mai yaje kasancewar bai da lectures ranar.
Zeeyter agida ta wuni suna wasa da su Miemie.

Sai yamma ta koma bangarenta,har tayi girki ta gama,ta yi wanka, Sleeping dress tasa wanda ya yi matukar mata kyau Sosai.

Zama tayi afalo tana chatting da Farouk, wanda har yanzu bata san cewa shine ba.

"Hi Friend yakike? Ya kwana biyu? Ya Oga kuma?"

Zeeyter ta ce, "Alhamdu Lillah ya kake ya aiki? Oga na Lafiya oh oh ya tafi Office shi kadai nake jira."

Dariya ya yi, "Alhamdu Lillah nima,umm wato yanzu ba wasa har ana fada mun shi kadai ake jira, Amman in tambaye ki mana."

"Eheen ina jinka." Zeeyter ta fada.

"Wasu dabi'u ne na mijinki da yake birgeki kika ji cewa zaki iya rayuwa da shi har karshen numfashi?"

Zeeyter ta numfasa kafin ta ce, "Mijina, shine asalin misali kan miji na gari kuma mijin kwarai,yana da duk wani abu da 'Ya mace zata so kasancewa da shi,sai dai azanci na dan adam wanda ba arasa ba,in zan ce zan fada ma wanene Sunshine sai mu kwana mu hini ban gama ba ai,amman ga kadan daga ciki,Yana da tausayi, Fara'a, Rashin girman kai, girmama da gaba da shi, kyauta da kuma son kyautatawa duk wani mukusancinshi har ma da sauran al'umma, Mijine mai goyon bayan matarshi a kullum kuma ako ina, har sai ga ta kai ga cin Nasara,mijine mai son matarshi don zuciyarta ba don siffa ko yanayi ba,mijine na rufin asiri,rayuwarmu ba boye-boye muna gudun bacin ran juna fiye da tunaninka, yanzu zan yi mai abu ya ce zai rama, kuma sai ya raman Amman ba hakan ke nufin zamu kullaci juna ba, na kanyi fushi mara dalili ko da nice da laifi amman zai aje girmansa ya ban hakuri, kasan meyasa duk yake hakan? Ba wai na fi kowacce mace ba ne aa, ya san darajar mace ne,yana mutunta mace,yana girmamata da kimarta, bai son ganin mace tayi ƙasa arayuwarta sam, burin sa a kullum mu dagu mu gyara komai ya tafi daidai, ban ya zan misalta maka ba amman a yanzu yadda muke Companyna ya fi na shi daguwa da daukaka ,harma da samun kudi wanda kuma duk asanadinsa ne amman bai damu ba ko kadan duk da hakan a kullum ci gaba na yake burin gani ,baya jin assara, hassada ko kyashi kuma baya tsoron matar shi ta fi shi,yasan zan iya bijere ma shi amman bai damu da hakan ba,saboda so kuma saboda Allah kawai yake komai,akomai nawa sai yadda karfinsa ya kare he is one in the Million ba ba kowanni namiji yake da wannan jarumtar ba na sha wuya arayuwa amman haduwata da shi alhamdu Lillah,duk da cewa yana da tashi Matsalar kamar yadda nima nake da tawa tun da bazaka taba samun mutum 💯 Amman Allah na tare da bayaninsa,duk zabin da Allah ya ma kamata ya yi ka gode masa ba kokarin nuna damuwa ko bijirewa ba Sunshine na daban ne aduniya ma gabadaya ba zan yi shakka ko jin tsoron nuna shi ako ina ba, ina alfahari da shi."


Farouk ya ce, "Umm gaskiya ne kun birgeni sosai da Sosai ina ma ace zan Kasance da tawa matar haka da nayi farinciki sosai, kasancewar ki cikin farinciki na sani Farinciki fiye da zatonki, ina miki fatan alkairy a kullum akuma kodayaushe sannan ina kara baki shawarar da ki rike mijinki tsakani da Allah kada ki bi rudin duniya."


"Hakane In sha Allah na gode sosai my abokin Dole watarana dai zamu hadu har ma in nuna ma Sunshine ko?"

Farouk ya yi dariya yana, "Eheen very Soon In sha Allah,byee Bara inyi wani aiki."

Zeeyter ta ce, "Owk Byee."


Kallon agogon wayarta tayi ta ga har 11 na dare babu Haiydar ba Deedarth.

Ga shi harta fara jin barci.

Kiran wayoyinsu tayi duka yaƙi shiga.

Hakan yasa ta tashi ta nufi gidan mai,ba kowa aciki sai mai gadi ko da ta tambayesa ya sanar mata cewa tun rana Deedarth ya bar compaynin.

Hakan yasa ta koma gida cikin damuwa.

Tana shiga falon wuta ta dauke.

Ji tayi an makure mata wuya ta kasa Numfashi bare magana .

Kokawa suke sosai amman sam anƙi saketa.

Jin alamun shigowar mutum yasa aka yi saurin saketa.

Haiydar da Deedarth suka shigo .

"Ya haka gidan ba wuta? Lafiya? Ina kike?"Cewar Haiydar.

Haska wayarsa da zaiyi sai ga Zeeyter agigice ta fita hayyacinta ban da kuka ba abun da take.

Da sauri ya ce Deedarth ya je ya duba wutar shi kuma ya karasa inda take.

Kankamesa tayi tana kuka.

"Mene ne ya faru? Ki fada mun Mene ne ya faru? Meyasa kike kuka?"

Cikin shashsheƙar ta ce , "wuyana,wuyana aka rike mun ina zaune kawai aka kashe wuta aka rike mun wuyana." Ta karasa maganar tana nuna wuyanta.

Dai-dai lokacin Deedarth ya kunna wutar yana, "cirewa aka yi kuwa."

Haiydar ya ce, "Kira mun mai gadi da sauran yaran gidannan dole akwai wanda ya shigo."

Dukansu suka ce su basu ga kowa ba,kuma basu san lokacin da aka shigo ba.

Cikin fushi Haiydar yake magana, "Kenan baku da amfani in har za a iya shigowa ba tare da kun sani ba,har a kashe wuta azo ana sheƙe mata wuya,da bamu zo yanzu ba da Shikenan ko? To Wallahi ba zan lamunci hakan ba,koma waye nasan yanzu yana cikin gidannan ku duba ko ina, lungu da sako a tabbatar an binciko mun shi in ba so kuke ranku ya ɓaci ba."

Ya karasa maganar yana sharewa Zeeyter hawaye tare da rike mata hannu su shiga daki.


Nan Gaɓadaya suka bazama bincika gidan amman abun mamaki an rasa gane ko waye babu kowa har suka gama bincikawa.

Kwantar da ita ya yi yana shafa mata baya , "ki yi hakuri kin ji.koma mene ne kuma koma wane ne zan nemo shi, ba zan taba bari wani abu ya sameki ba in dai ina numfashi kin ji."

Zeeyter ta ce, "nikam wana tarewa gani? Wa na hana rayuwa ake son kashe ni? Na san da kyar za abar ni, kullum da abun da ake bullowa da shi fa, Shikenan rayuwata cikin hatsari zata kare? Ba zan iya ba,na gaji wallahi."


Haiydar ya ce, "ba ina tare da ke ba? Koma me zai faru sai dai ya faru dani dake mu biyu bare ma in sha Allah indai ina raye ba wanda ya isa ya taɓaki, zan kira akaro mana securities cikin gidannan da ma company kuma za a kara zurfafa wannan binciken mu gano ko wane ne, kiyi hakuri harda dadewarmu ne silan faruwan hakan wanda an samu gida ne,muka je nida Deedarth muka kai su Baba kawai a wuce gun, kiyi hakuri kin ji,ina tare da ke har karshen numfashi na."


Gaba-daya Zeeyter a tsorace take da kyar Haiydar ya lallaɓata tayi barci.



Washegari
Da sassafe Haiydar yaje har office ya samu Dpo.

A fusace ya shiga ya ce, "Wato dai ba za ka fita harkarmu ba ko? Na ce ba za ka fita harkarmu ba ko? To Wallahi daga yanzu duk abun da ya sameta kaine na fada ma kuma za ka yi danasanin hakan,don haka tun farko ina kara tunatar da kai cewa ka fita a sabgarta domin in dai nina shigo rayuwarka za ka sha mamaki fiye da zatonka." Ya ƙarasa maganar yana ficewa.

Kallon fitar sa Dpo ya tsaya yi kawai yana dariya tare da fadin, "ga dukkan alamu matarshi ta manna masa haukar shi ma."

Haiydar na komawa gida Zeeyter ta ce, "Ina kaje ne da sassafen nan?."

Murmurshi ya yi kawai yana, "kinyi break?"

Zeeyter ta ce, "Aa amman ga Deedarth can a kitchen din ban san koyi yake ba."

Haiydar ya ce, "Ok zauna bara inje in taya shi, yau agida zamuyi aiki duka,in da abun da kike bukata a dauko ki aika tun yanzu."

"Ok."Zeeyter ta amsa.

Suna gama breakfast kowa ya fara aikinsa.

Zeeyter ta dafa kai tana tsaki.

Da sauri Haiydar ya juyo yana, "mene ne ya faru kuma?"

Zeeyter ta nuna masa system din tana, "na rasa yadda zanyi in fidda lissafin komai ya tafi a tsari tun shekaran jiya nake a company amman na kasa."


Haiydar ya karbi system din yana, "muga."

Sai da ya duba Sosai kafin ya ce, "tun farko ke kika yi mistake a lissafin ga yadda ya kamata ya kasance."

Sai da ya gyara mata komai kafin ya bata.

Murmurshi ta yi ta ce, "Sunshine."

Ya ce, "Yessss."

"Thank you,You are indeed a husband who has helped me in need. I Love you,I really really Love You."

Rumeta yana, "U are welcome My Baby."

Dagowa tayi tana cino baki, "am not ur baby oh oh am ur anty eheen."

Dariya Deedarth da Haiydar suka yi.

"Umm my Anty son girma." Deedarth ya fada.

Zeeyter ta kalli agogon hannunta , "Eheen rana ta kusa yi tunda Oga yace zaman gida za ayi kuxo mu je free food muyi girki,kowa ya sako kayansa yau mu barsu su huta."


"Owk Madame." Duka suka fada a tare.

Dariya tayi ta shige daki tare da dauko rigunan da hulunan ta ba kowa yasa suka fita.
Suna zuwa ma'aikatan suka fara yi masu barka da

Zeeyter ta ce, "CHICKEN BIRYANI za mu yi, yau ku huta duka kitchen din namune."

Deedarth ya ce, "Yesss Ant ina son cin abincinki da dadi Sosaii,

Attaruhu,gree pepper,Albasa ta ba Deedarth ya yanka.

Haiydar kuma ta bashi nama ya wanke sannan kuma ya tafasa.


Tukunya ta daura akan gas din ta zuba mangyada da albasa mai yawa wanda Deedarth ya yanka sai da yan fara soyuwa kafin.

Ta zuba Tafarnuwa da attaruhu suma ta juya su sosai.


Tukun ta dauko naman kazan da Haiydar ya tafasa ta zuba, kayan kamshinta ,kori,kurkur da sauran abubuwan duk ta zuba sannan magi tana juyawa sai da komai ya kama jikin kazar sosai ta fara soyuwa kafin ta zuba tumatur nikakke.

Shima da ya kama jikin kazar sannan ta zuba ruwa.

Kafin ya tafasa ta wanke shinkafar ta.

Yana tafasa ta juye shinkafar cikin ruwan.

Note:ruwan daidai yadda shinkafar ba za ta caɓe ba tasa.

Yana dawuwa ta kwashe tare da jera naman kazar ta sama sama sannan ta daura green pepper dinma asaman shinkafar.

Juyowa ta yi tana, "Ma sha Allah this is our chicken biryani."

Deedarth ya ce, "Anty na matsu in ci wallahi."

"Kun san dai bazam iya jira ba ko? A kira mun baby mu ci abincin mu."

Dariya Zeeyter tayi tana, "Food Master karfi da yaji ka koyawa Baby son abinci irin naka."

Kan wani ya kara magana sai ga su booboo da gudu baby ya karasa jikin Haiydar.

"Uncle where is our food I'm hungry." Ya karasa maganar yana taba ciki.

Zeeyter ta ce, "acici Mala'ikun tauna,ku je kowa ya zauna akan table za a kawo."

Nan ta kira sauran ma'aikatan suka fara raba abincin sai da aka tabbatar kowa dake cikin gidan ya samu kafin Zeeyter ta zauna suna ci da Deedarth Haiydar kuma da baby.

Sai dariya ke tashi kowa na santi abinci ya yi dadi, MUSSAMMAN Haiydar da baby sai da suka fi kowa ci.


★★zaune Antou suke da baba afalo suna cin abinci da Unaisa.

Antou ta ce, "Alhaji ni fa ina da magana ba zai yu ace mun zubawa yaron nan ido yana abun da ya ga dama ba atakaice ma ni sam ban yarda da matar shin nan ba,domin bincike ya tabbatar da cewa bata da ........



08103080717
[6/29, 1:48 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-39*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

*TALLAH*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

★★★★

Asali, ba mu san ita wace ce ba, inko har muka yi shiru karshe mune da nadama mai cike da dana sani,sam ban aminta da ita ba,kuma bata kwanta mun arai ba,ka ga fa ranar farkon haduwarmu har ta fara shigewa Deedarth, dazunnan Unaisa take nuna mun wasu hotuna da Deedarth yasa astatus shi da ita suna aiki dayan kuma suna cin abinci,ga dukkan alamu sonshi take,kar azo ayi biyu babu abata mun sannan shi kuma Haiydar acuce shi." Ta ƙarasa maganar araunane cikin kissa.

Baba ya ce, "To ni dai ban ga aibun wannan yarinyar ba,ayyadda ya nuna ma a bar tausayi ce amman kuma maganar ki ma abun aduba ne kam."


Antou ta kara raunana fuska ta ce, "atakaice fa sun kusa shekara biyar da haihuwa amman bana jin cewa ko ɓari ta taɓa , gaskiya akwai sake ni in baza ka dau mataki ba wallahi zan dauka Mussamman da take kokarin yin noma a filin da ba nata ba,dole Deedarth ya bar wannan gidan ya dawo gabana,ba zai yuhu ba."


"To me kike so ayi? Mene ne mafita? Ni kaina ai ina son ganin jikokin da zasu fito daga tsatson rayuwata ko ba komai in na gan su zan ji dadi kafin Allah yasa in bar duniya."cewar Baba.

Antou ta dan dara kafin ta ce, "Wannan ai me sauki ne,ina da mafita a hanuna me zai hana a aura masa saudatou yarinyar Aminiyata ,yarinya mai ilimi,ga kyau fara sol son kowa kin wanda ya rasa samari har fada suke akanta amman saboda kamun kai irin nata ko shiga harkar su ba ta yi, inada tabbacin indai Haiydar ya aureta to ba abun da wannan makirar yarinyar Zeeyter ta aikata,lamarin ita da Deedarth kuwa zan ji da nan zan tsatstsayar mata ta fita mun asabgar ɗa domin shi ba gantalle bane irinta."

Numfasawa Baba ya yi sai da ya yi dogon tunani kafin ya ce, "Tabbas kinyi tunani mai kyau kuma hanyar nan mai bullewa ce,amman tukun shin ita saudatoun za ta so shi? Sannan shi ma haiydar din zai so ta? Ina ganin mu ba shi dama kawai ya samu zabinsa."

Antou ta fara kame-kame, "umm yhum uhum saudatou ai yarinyar kirki ce ko da ni na tsara abu ba Mahaifiyar ta ba zata amince bare kuma Mahaifiyarta ,sannan shi ma haiydar kai ba ubansa bane da zaka fada ya ki amincewa ko da baya so? Ko kuwa ka taba sa Deedarth abu yaƙi yi sai shi Haiydar don yana da kudi? Bare kuma saudatou ba ta da mukusa arayuwa cikakkiyar mace ce ba irin matar shi ba ina da tabbacin zai sota don wannan matar ta shi ma in an bincika asirce shi tayi ta aure shi."

Ta karasa maganar tana kwalawa Unaisa kira.
"Ke Unaisa zo ki nunawa babanku hotunan da Deedarth yasa astatus."

Unaisa na zuwa ta fara nuna mai tana, "Baba kalli Yaya Haiydar fa ta mai da shi mai dakan sakwara shi kuma Yaya Deedarth harda yanka kayan miya,baba wallahii ta raina su,nikam na tsaneta wallahi gata munanniya ga jiki,kuma gata baƙa fa Allah sa ma Yaya Haiydar ya sake ta karta cinye masa kudi."

Antou ta teɓe baki, "umm to ka ga yarinya ma kenan bare kuma mu masu hankali."

Girgiza kai Baba ya yi yana, "ku shirya gobe za mu je can bobiel din."

Ya karasa maganar yana fita.

Tafi da shewa Unaisa da Antou suka yi.

Unaisa na fadin, "Antou kin fada masa ko? Ai gwanda nikam ma Allah sa in ya auri Sadatoun ya saki wacce zeeyten ni ko ganinta bana son yi."


Antou tayi wata irin dariyar mugunta, "kar ki ji komai ɗiyata indai ina nan komai ma mai sauki ne ai,na iya kora Mahaifiyar sa bare kuma matar sa? A dai juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe, zamu dawo mune da komai shi kuma sai yadda muka yi da shi,na ji dadin yadda Deedarth ke shige mata jiki ko ba komai zan bi hanyar sako zargi a tsakanin su."

"Shi yasa ina sonki Antounmu ai gwanda wallahi muyi maganinta sai ta rasa wannan Murmurshin da ke fuskarta a kullum."


★★★
Su Zeeyter na kammala cin abinci masu aiki suka fara wanke wanke bangarensu suka koma ita da Haiydar Deedarth kuma ya shige bangaren su Madame Ayshe yana yiwa su Baby Lesson.

Sallah suka yi duka tana ganin Haiydar ya zauna a kujera yana danna waya tayi saurin kwanciya acinyar shi tare da fisge wayar ta ce, "Sunshine."

"Uhumm bani wayata mana sako zan duba fa ko an turo mun." Cewar Haiydar.

Zeeyter ta ce, "Yanzu ai ba lokacin duba sako bane ka ce yau free muke ba wanda zaiyi aiki, Don haka ka ta shi muyi rawa ka ji."

Haiydar ya bude baki, "Rawa ana zaune kalau? Ke dai je ki yi zanna miki video."

Dukan cinyarsa tayi cikin Shagwaba ta ce, "ni ba zan yi ni kadai ba, tare za mu yi."

"To ki daga ni sai muyi ko? Amman koya mun za ki yi." Haiydar ya fada.

Dariya Zeeyter ta yi tana, "eh mana daman kai mai ka iya ban da juya kai." Ta karasa maganar tana tashi tare da kunna kidan.

Yi take tana nuna masa suna yi tare Haiydar ya kyalkyale da dariya, "ke wallahi na gaji,wai ke bakyajin nauyin jikinki ne ma har kike iya abunnan? Bar ni in huta wallahi." Ya karasa yana dariya.

Ita ma dariyar tayi tana, "Yoo kai ba acici Mala'ikun tauna ba ai dole jiki ya ma nauyi ga shi ba wata kibar azo agani ba,zan fara tsara ma abubuwan da za ka ci yasin in kuma kayi wasa ka tsufa nikam ina yar cafes dina."

Haiydar ya rike mata kwankwaso yana, "ina yar cafes din anan?"

"Gani nan ko kana musu ne in nuna ma? ." Ta karasa maganar tana kokarin cire kaya.

Dariya ya yi yana rike mata hannu tare da fadin, "ba zai dai ki girma ba, kin fiso kullum kina birkitani,kin san yanzu indai na shiga wannan yanayin ba mai gane kaina So ki taimaka mun ki bari sai dare don gidan naki baya rabo da jama'a." Ya karasa maganar yana kissing dinta.

Ita ma din kiss din ta maida masa tana dariya, "Matsoraci kawai."

Ta karasa tana tafiya cikin kitchen.

Youghourt ta dauko tana sha, shi kuma yana duba wayarsa suna hira sama sama .

Zeeyter ta ce, "Sunshine wai ina Ammie ne? Kwana biyu ta manta damu tana can Saudia abinta."


Haiydar ya dafa kai, "Oh kin tuna mun fa,bara in kira ta ta Sykpee jiya mun gaisa a office ta ce tayi missing ɗinki ba ku yi hira ba."


Matsowa daf da shi Zeeyter ta yi ,yana kira kuwa Ammie ta dauko.

Tare suka mata sallama da gaisuwa.

Da Murmurshi ta amsa tana, "Allah ya maku Albarka 'Ya'yan kirki."

Dukansu suka amsa da "Ameen."

Ammie ta ce, "Yarinyar Kirki yakike ya kwana biyu? Ince yaron kirki baya bata miki rai ko? In yana yi ki fada mun inzo in zane shi ai bai wuce duka ba ko?" Ta fada tana dan dariya

Murmurshi Zeeyter ta yi ta ce, "Ammie ai in yamun tuni zan kiraki,tunda Ammie na ce ke ba tashi ba tashi ba,ina lafiya lau."

Haiydar ya ce, "nikam ina ganin kwace kiri-kiri."

Dariya Ammie ta yi tana, "kai na yayeka ai."

Zeeyter ta ce, "Ammie kinki zuwa Don Allah yaushe za ki zo?"

"Na kusa kadan in sha Allah kawai ku kasance cikin shirya mun abubuwan tarba , jiya munyi magana da Haiydar ya fada mun zuwan babansa da komai ,abun da nake so da ku shine ku rike junanku da amana sannan ku kawar da kai kan komai dole nasan akwai wasu sabun lamura da zasu bullo Mussamman gareki Zeeyter zai zo miki cikin bazata gwanda shi zsn iya cewa akusan cikin hakan ya taso, Amman duk wuya duk rintsi ina rokonku da ku rike junanku ka da kuyi abun da zai iya sanya ku dana sani daga baya,ku rungumi duk wata kaddara kamar yadda kuka rungumi na baya to na gaban ma masu zuwa ko wa inda suke zuwa ku rungumesu hannu bibbiyu Allah yana tare da ku aduk inda zaku kasance adduata da fatan nasara na na gareku har karshen numfashi na, ku rayu tamkar hanta d jini shine burina kuna ji ko? Allah ya yi maku albarka agaida su Madame Ayshe da Baby."

"In sha Allah Ammie don ma bata ji yarinyar taki." Haiydar ya fada.

Murmurshi Zeeyter kawai ta yi tana, "Mun gode sosai Ammie Allah saka da alkairi za su ji in sha Allah."

Da haka suka katse kiran.


WAIWAYE
Wannan Ammie

Please Login or Register in order to submit comment