Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

YEL .

Ba karamin kyau da sheƙe zanen nata ya yi ba, tamkar a kirata ta fito.


Suma yaran duk sun dage kuma kowanne zanen gidansa ya yi kyau,suna gamawa ta ba kowannensu chocolate tare da fadin, "Kowa ya je ya ajiye littafi da kalolin agida, ranar da ba makaranta sai mu kara."

Dukansu suka fita suna dariya.

Harira da hurera ne suka shigo suna leƙe.

Zeeyter na ganin su ta ce, "Ku shigo mana,da matsala ne? Ko xan iya taimakon ku?"

Shigowa suka yi suna Murmushin munafurci.

Hurera ta ce, "Umm umm wallahi za mu fita anguwa ne kuma bama da kudin mota."

Murmurshi Zeeyter tayi ta ciro dubu biyu ta mika masu.
Godiya suka mata suna kallon juna da ido.


Suna fita Harira ta ce, "Banza bata san cewa inda za a illatata zamu ba, har tana bamu kudi."


Dariya Hurera tayi, "Bar jaka ai za muyi maganinta."

Suna fita kuwa ta nufi gidam marayu hira tayi sosai da yaran suna murnar ganinta sannan tayi masu sadakar da ta saba masu a kullum.

Washegari

Da Sassafe Zeeyter ta tafi gidan abinci domin dafa abincin da xa aci wajen taron wayar da kai.

Madam Ayshe da Madam Naddja kuma suka tsaya tsara gun.

Misalin karfe 10:00pm aka fara.

Wanda haiydar ne ya kasance bakonsu na ranar.

Tun daga zuwan shi yanayin ƙauyen ya birge shi,duk da cewa bai taba zuwa ba sai dalilin Madam Naddja da ta gayyace shi.

Ba ɓata Lokaci ya fara jawabi kamar yadda aka umarta kan Ilolin shaye-shaye da ma shi kan shi shaye-shaye menene kuma taya ake farawa.

Bayan ya yi sallama da gaisuwa ya fara da, "Kwaya ko magani shine duk abinda idan ya shiga jikin dan adam yake kawo chanjin yanayi cikin kwakkwalwa ko jikin sa ta kowani fanni, misali ko ta hanyar sha ne, shaƙawa ne ko kuma ta yin allura.

Miyagun shaye-shaye
Shan maganin da doka ta hana ayi anfani da shi.
Shan magani barkatai ba tare da ixinin likita ba.
Wuce umarnin likita gurin shan kwayoyi.
Shan abubuwan da addini ya haramta.

Dalilan da ke sanya matasa afkawa cikin shaye-shaye.
Jahilci, matsalolin rayuwa kamar ace damuwa tayi wa mutum yawa ko kuma ya tuna wani abu da bai son tunawa da ya shafi rayuwarshi, nan take mutum kan iya shan komai ma, hada-hadar siyasa, hulɗa da abokan banza, sakacin iyaye wajen tsawatawa yara, a fannin sakaci yana nufin kowanni fanni ke nan Mussamman masu kudi da suke sakarta yaransu ,ba tsawatarwa kullum sai dai anuna masu cew suyi abun da suke so,su ji dadin rayuwa,talakawa kuwa hakan na nufin halin ko in kula da wasu iyayen keyi kan 'Ya'yansu,sannan kuma da yanayin wurin zama, da dai sauransu.

Wasu daga cikin miyagun kwayoyin da aka fi amfani da shi gurin shaye shaye.

Hodar aljanu (cocane), tramol, kashin kadangare, afarci kasa (pemoline tablet), hodar iblis (heroine), maganin mura da ake sha ba bisa ƙa'ida ba (emzolynn, tutolyn, codine, benelyn) Alkaho,da dai sauransu.

Matakai na soma shaye-shaye

Gwaji mutum ya soma kusanta ko mu'amula da masu shaye shaye daga nan kuma sai mutum ya ce bari ya gwada yaji mai ake ji.

Masu shaye shaye akai akai.
Shine matakin kama shaye shaye a kai a kai, wanda ya kai wannan matakin ba zai iya komai ba sai ya sha idan bai sha kwaya ba ba zai zauna lpy, wanda ya kai wannan mataki zaka sameshi kullum cikin maye, a wannan matakin yana iya yin sata domin ya siya kwaya.

Alamomin gane mai shaye shaye kuwa,
Rashin natsuwa,talauci, kora daga gurin aiki ko makaranta, yana kawo haɗari ga wanda suke yin tuƙin motar ko babur, yana kawo ciwon huhu, yana kawo ciwon hauka, yana kawo lalacewar mazakuta, yana kawo cutan kanjamau saboda idan hankali ya gushe yana kawo jima'i barkatai ba bisa ka'ida ba, yana kawo lalaci yadda mai shaye shaye bai iya yin komai sai ya sha kwaya.


KAƊAN DAGA CIKIN HANYOYIN DA ZA ABI DOMIN MAGANCE SHAYE-SHAYE

Ya zama wajibi Iyaye su tashi tsaye domin lura da 'Ya'yansu, abokan su,wajen da suke zuwa da duk wani abu da ya shafesu, sannan Al'umma suba jami'an tsaron goyon baya wajen hukunta duk wanda aka kama da wannan badakala , haka kuma iyaye su kasance suna yawan nusar da 'Ya'yansu kan iloli kamar wa inda na gabatar.

Ba yara kadai ba,duk wani babba ya kamata ace ya lura sannan ya kiyaye da tsarin rayuwarsa domin bai san me zai zama nan gaba ba,kuma bai san ya iyalansa zasu kasance ba."

Tsayawa ya yi a daidai nan wajen, jikinsa ya yi sanyi, ya tafi wani guntun tunanin dake cewa wannan jawabin tamkar da kan shi yake.

A zuciyarsa ya furta, "Allah ka bani ikon gyara rayuwata nima."

Ya numfasa kafin ya ci gaba da cewa, "mu daure, mu cije, duk da cewa sabo na da wuyar dainawa amman haka zamu danne zuciyoyinmu mu gyara,fatana anan kowa ya fahimta masu yi su daina wa inda basu fara ba su kiyaye, Allah ya bamu ikon gyara rayuwarmu da ta al'ummarmu,sannan ka da ku manta ba 'Ya'Ya maza kadai ke shaye-shaye ba har da wasu 'Ya'ya matan, jawabin mu na dauke da kowanni bangare nr."


Da haka Haiydar ya kammala jawabansa.

Gaɓadayansu jikin mutanen wajen ya yi sanyi daga iyayen har yaran,batun ya shiga jikinsu matuka.

Yana kammala ya nemi ixinin tafiya Amman Madame Ayshe da Naddja sun hana kan dole ya tsaya ya ci abinci.
Ko kudin da Zeeyter ma ta tanada kan abashi sam yaki karba ya ce arabawa mabukatan wajen sadaka.

Ganin cewa su Farouk nata kiranshi ne ya basu hakuri ya fita da niyar tafiya daidai lokacin da Zeeyter ta tawo da abincin d za a raba agun.

Ya juya kenan sai ga kira ya shigo wayarta ta koma gefe.

Shi kuma yaja motar shi ya tafi.

Tana sa wayar a kunne ta ji, ".........



08103080717
Urs Xayyeesherthou

[5/31, 3:34 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-16*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

Muryar Dpo ta ji yana, "Madame barkanmu Dai."


"Barka." Ta furta.

"Uhumm Madame ke nan, daga tafiya sai mantawa dani kuma? To ya ki ke."


"Lafiya." Ta amsa a gajarce.

Ya ci gaba da magana , "Madame kamar bakyason yin magana."

Katse wayar tayi tana tsaki kawai.

Shiga cikin wajen taron tayi aka fara raba abinci, hatta Maman Yusuf da Babanshi kuwa sun zo, sai da kowa ya ci ya koshi kafin aka watse.

Madame Ayshe da Madam Naddja suka sanar da ita Haiydar yaki karban kudi, da kuma abun da ya ce.

"Allah sarki bawan Allah, Allah ya saka masa da gidan Aljanna, Madame ku bawa duk wanda ya dace kamar yadda ya bukata."Zeeyter ta fada tana nuna farincikinta ƙarara saboda hukuncin da Haiydar ya bada,duk da cewa bata san waye ba amman ta ji cewa ya birge ta cikin zuciyarta.


Zaune take tan hutawa kamar an ce mata ta dauko wayarta tare da leƙawa facebook.

Sakon Farouk ne ya fara shigowa, "Hy Kawata, barkanmu da rana."


Gyara zama tayi kafin ta ce, "Barka dai Aboki, fatan kana Lafiya?"

"Alhamdu Lillah kamar yadda kike."

Da, "Ma sha Allah ." Ta maida masa.

Ya ce, "Ni Ko inyi tambaya mana Kawa."

Zeeyter ta ce, "Bismillah za ka iya, Allah sa ina da amsar."


"Kina ma da shi,Don Allah me kika fi so aduniya?" Farouk ya tura mata dauke da emijin tunani.


"Farincikin Al'umma a ko ina na fadin duniya, wannan shi ne abun da na fi so."

Har ya fara typing ya tsaya yana kallon haiydar kan ya ce, "Abokina Kasan cewa aduniyar nan tamu akwai wata 'Ya mace ɗaya tilo tamkar da maza? Rayuwar tamkar Don al'umma take, za a iya cewa ita tazo duniya ne kawai domin taimako,da kudinta,da karfinta da basirarta tana kokarin maida ƙauye birni,tunaninta a kullum shi ne ya za ta taimaki Mutane ba bambamci tsakanin makiyanta da masoyanta, na tabbata za ka ji mamaki in kaga abubuwan da take kirkirowa a duniya, wannan duk abun mutum dole ya sara mata, dama ace zan iya mallakar ta da nafi kowa jin dadi arayuwa, Wallahi duk wanda ya samu yarinyar nan ba karamun dace ya yi ba, yarinya ce fa karama,abun nata bani mamaki."


Haiydar na kwance sai da ya tashi, "Daman da gaske akwai mata irinsu aduniya? Ban santa ba amman har kasa mun cewa nima na ji tana birgeni, ace za asamu irinsu d yawa aduniyar nan ai da munji dadi mun huta,ba wai komai ace namiji ba,komai na miji,ko ba komai ka ga yarinyar da kake faɗa ta nuna cewa mace za ta iya gyaran al'umma da ɗaukan dawainiyarsu har ta gina su, Amman ina yarinyar nan take da zama ne? Yar wace kasa ce?"

Haiydar ya fada cikin zakuwar yana son sanin wace ce.

Dariya Farouk ya yi, "Yoo to wannan ai shine babbar Matsalar kowa ya kasa ganota." Ya karasa maganar a zuciya yana, "In sha Allah tawa ce."


Haiydar ya yi Murmurshi, "aiko nayi alkawari da ikon Allah sai na nemo yarinyar nan aduk inda take ko da kuwa a karshen duniya take rayuwa."


Cikin dariya Farouk ya ce, "Mamaki yau kai ne wata ta burgeka kuma kake alwashin nemanta? Don ma ba ka ji Tarihin Rayuwarta Gabadaya ba,abun al'ajabi, tausayi da mamaki, Lallai to mu zuba mu gani za aga wanda zai riga nemota, amman da kashedi, duk Wanda ya riga shi zai dauketa."


Dariya suka yi dukkan su.

Farouk ya ci gaba da danna wayarsa domin ba wa Zeeyter amsa.


"Ummm Lallai kin ji dadi dama nine, ni fa ban damu da kowa ba,kuma bana damuwa da damuwar kowa."ya tura mata.

Zeeyter ta turo emijin bata rai, "ni kam bana son mutum haka, ka kasance mai son mutane ko da basa sonka,taimakonsu ko da basa godewa, a gun Allah muke nema kuma dominsa mu ke yi domin ya biya mu da AlherinSa,za ka ga kullum zuciyarka ta kasance fayau ba tare da daukan nauyin komai ba, sannan duk wani ƙalubale da zaizo ma a rayuwa zaizo cikin sauki, komai za ka yi, kasa Allah a gaba domin kuwa shine Mahaliccin mu duka duk duniya."

Farouk ya ce, "Haka ne dukkanin jawabinki gaskiya ne, zan kokarta ko da kadan ne daga ciki in fara kwatantawa."


"Yafi dai kam Abokin Dole." Ta karasa maganar da emijin Murmurshi.


Dariya ya yi, "Wato ma abokin dole, Okay byee ina da wani aiki yau."


"Byee A yi aiki Lafiya." Ta fada.


Chating dinta ta ci gaba da yi tana dube dube.

Wani messege ne ya shigo mata.

Tana dubawa ta ga Namijine ya Turo mata hoton gabanshi yana, "Yane?."

Tsaki tayi kawai ta shiga duba profile dinsa da komai na kan facebook din sai da ta bincika


Tana ganin numbersa

Fita tayi a facebook din ta shiga facebook Tracker ta rubuta

Sannan ta dawo facebook ta kwafe URL dake profile dinsa.

Ta koma Facebook Tracker tayi paste din URL din, daga nan ta shiga Hack Account.

Processing ya fara sai da ya kai 100% sannan ya nuno mata Password dinsa.

Copyn password din tayi kafin ta kara komawa facebook tayi logging din account din na shi.

Duk abun da ta gani ban da sexy chat ba abun da yake yi da yan mata , Murmushin takaici tayi a zahiri ta ce, "Yanzu na ga Account din da zai kara shiga har ya nemi rainawa mutane hankali karamin Dan Iska kawai,indai za ka bude Account da number nan niko sai nayi hacking."


Fita tayi tana kokarin shiga gidan marayu shan gabanta da aka yi yasa ta dagowa.

Dpo ne yana sakin Murmurshi.
"Haba Madame Meyasa ki ke son bani wahala ne? Baki san yadda nake sonki bane wai? Zan iya mutuwa fa a kan ki."


Kallon shi tayi ta kyalkyale da dariya kafin ta ce, "Mutuwa ko? Ah lallai za ka iya mutuwa akai na, to bama nan ba indai kana so in kara tabbatar da hakan ka ga rijiyar cen?"

Ta fada tana nuna masa da hannu.

"Eheen." Ya fada


"Ok to ina so ka yashe mun cikinta daman ina neman masu yasa." Zeeyter ta fada.

Cikin Mamaki ya kalleta, "Yasa kuma? Ni? Madame ki bar irin wannan wasan zan dai sa yara suyi."

"Aa ni kai nake so kayi,in ba haka ba kuma kar in kara ganinka anan."

"To to naji zan yi Amman zan kira yara su tayani." Ya fada cikin wani yanayi.

Murmurshi ta yi, "Yawwa to Bismillah a kira su."

Kira ya yi aka turo masa da Yara Biyu daga Office.

Zigidir ya tube daga shi sai singileti da gajeran wando

Kayan aiki ta dauko masu ta ja gefe tana rufe baki da hannu don dariya.

Domin Dpon irin Samudawan lutayennan ne, Mussamman da ba kaya in ka kalli cikinsa kadai ya isa ba da dariya.

Suɓutur-suɓutur shi da yara duk sun ɓaci da laka mai Zeeyter za ta yi kuwa ban da dariya.

Gabadaya yara da manya duk anzo ganin Dpo yana Yasa gaɓadayan su Mamaki suke sun zubawa sarautar Allah ido kawai

Suna gamawa Zeeyter ta fara tafi ganin haka sauran yan ƙauyenma suka biye mata tana, "Maddalla da shugaban kwarai, ace wai har da kanka za ka zo kana bincika matsalolin al'umma kuma kuma ka gyara? Anya akwai sauran irinka aduniya kuwa? Muna alfahari da Dpo Khalid." Ta fada cikin zaƙewa.

Suma sauran yaran suka fara ihu, "sai DPO Khalid."

Shi kuwa Dpo mutuwar tsaye ya yi,yana kallon Zeeyter kawai.


Dariya tayi ta karaso inda yake ta dauko kayansa a inda ya ajiye ta mika masa tana, "Oga Khalid Wannan tunbin naka na da ban dariya."
Ta kunshe baki
Kan ta ci gaba da fadin, "Wannan ita ce soyayyar da tafi ta komai aduniya ka nunawa al'ummarka kana tare da su duk tsiya duk rintsi hakan zai sa su alfahari da kai, ace cikin mune wani ya yi wannan aikin ba mai damuwa da nuna jin dadi,amman su dubi fuskokinsu?"

Ta karasa maganar tana nuna masa mutanen wajen

Kallonsu ya yi kowa ban da Murmurshi ba abun da ke fuskarsa.

Ta ci gaba, "A yau Yan bobiel sun yi farinciki saboda da kai,kuma na tabbata wannan abun ba zai taba gushewa aransu ba har karshen numfashinka aduniya,darajarka zasu na gani fiye da baya."

Jingina masa kayan tayi kan hannunsa

Da dariya take fadin, "In kaje gida kacewa Madame tana kula da wannan tunbin naka,in ya cika wata tara zamu zo suna."

Tafiya tayi tana yi masa gwalo, wanda shi ko ya tafi duniyar tunani mai fadi.


★★Aiki take tayi cikin gidan abinci domin taya su girka abincin dare.

Da kuka ya shigo yana, "Madame Don Allah ki taimake ni, za mu mutu,yunwace za ta kashe mu."


Da sauri Harira ta karaso wajen tana, "Tabdijan Wallahi karki taimaki wannan kafirin Zeeyter arne ne fa baya sallah."

Zeeyter ta kalleta cikin yanayin nuna rashin jin dadi.
Shiru tayi ba don taso ba.

Zeeyter ta ce, "Nneka mene ne ya faru?"

Ya ce, "Jari zaki taimaka mun da shi Madame Don Allah kamar yadda Allah ya taimake ki nima ki taimaka mun,ko me kikeso zanna miki ko so kike akashe miki wani zan kashe."

"Subhannallah." ta furta

"Addinmu bai ce mu kashe kowa ba,kuma ba a koya mana ba, kawai ina so ka faɗamun me ka karanta kuma mai kafi kwarewa akai tunda na san kayi karatu."

"Madame Na yi shiru ba za mu yi kisa ba,mun daina, na karanci fanin kimiya ne wato camputer ."

Zeeyter ta ce, "Shikenan za abude ma shago za azuba ma komai na bukata Amman da sharadi ɗaya, zan turoma yaran da zakana koyawa ,daman kauyen nan ana fama da matsolar rashin injin din buga takardu sai an shiga cikin gari,haka ma bincike in za ayi mai zurfi ba a iya sai an fita,zamu kirkira Anan kuma kaine shugaba ni dai damuwata biyune kawai zaka dau yara kana koyar da su sannan duk dalibin da yazo bincike ko duba jarabawa da dai wani abu za abar shi ya yi kyauta ba sai sun fita birni sun biya ba."


Tsabar dadi Nneka bai san lokacin da ya rungume Zeeyter ba yana rawa da waka.

"Ina Sonki Madame,Ina Sonki, Allah ya bar mun ke ni kadai."

Harira ta yi tsaki, "kin gani ko arne ne fa bai da hankali wallahi ko in bude mai shago giya zaina sha."

Nneka ya tsaya kallonta.

Zeeyter ta ce, "Ina ruwanki? Ina ruwanki? Mene ne damuwarki da ko ma miye zai yi?."


Tafiya tayi tana un-uni , "An daiyi asara ace wai har kafirai za ana taimakawa,tur wallahi, daman da irin su kike iskancin da kika saba ai."


Zeeyter ta ce, "Nneka karka damu da maganar ta ka ji, komai zai yi dai-dai."

Murmushi kawai ya yi.

Yana, "Na gode Madame."


★zaune suke a falo anata musu ai mata sun fi maza iya ball, cewar Deejerh da Zahra, Shi kuma Su Farouk sam sunki yarda.

Haiydar ne ya katse maganar da, "abu mai sauki, bara in sa a gyara mana fili kowa yaje yasa kayan ball din sa, sai a tabbatar, indai kun ci mu na yi alkawarin Sabuwar motar da zata fito a shekarar nan ga kowacce cikinku, Deejerh da Zahra."

Khaleel ya ce, "Ni ma kamar kai gidan da zan fara yi sabo a shekarar nan na mallaka masu."

Farouk ya ce, "Eheen ni kuma kudi zan bada wanda ni kaina ban san adadinsa ba."


Zahra ta ce, "Alright ni ma kudin zan bada."

Deejerh ta ce, "nima kayan da zan fara tsarawa a shekarar nan naku ne duk yadda kukai da shi,komai na ribar na mallaka maku, Indai kuka ci mu."

Tashi suka yi duka kowa ya tafi shiri.


Cikin minti talatin dukkanin su cikin kayan sport suka fito bayan sun gama cin abinci wanda deejerh tai Designing ba karamin kyau ya yi masu, babban filin gidan suka fita domin buga ball.

Khaleel ne ya fara kurin baki, "Yau za mu nuna maku bambamci ai, yaushe mata zasu fadawa maza ball muje zuwa."


"Sai mun ci su goma a minta ɗaya." Cewar Farouk yana dariya.


Haiydar ya ce, "ni ba zan yi magana ba sai a fili."

Suka sa dariya dukansu.


Ball aka fara abun mamaki duk da cewa Zahra da deejerh su biyune kacal amman suke ci har aka gama ball din.

Gaɓadayan su ban da farinciki ba abun da kake gani afuskar su.

Hotuna da bidiyo kawai suke suna dariya.

Deejerh ta ce, "bambamci ya fito, waye ya ce maku bamu iya ba ai kun ganewa idanunku."


"Ni fa daman team din Madam zahra nake,so mu muka ci."

Dariya suka kara yi dukkaninsu.

Kokarin shiga gidan da za su yi kawai deejerh ta fadi....

Gaɓadayan su rikicewa suka yi suka je suna riketa.

"Deejerh tashi,ki tashi don Allah kar ki mana haks." Zahra ta fada tana girgiza ta.

Farouk ma kiran sunanta kawai yake

Shi ko Khaleel ganin numfashinta na kokarin daukewa ya fara janyo mata ta baki yana sheka mata.

Mota haiydar ya dauko domin atafi asibiti.

Cikin minti daya zuwa biyu duk sun gama rikicewa.

Dariya deejerh ta fara ta tashi tana gudu suna binta.

★washegari

Yusuf ne ya fara shigowa sai ga babanshi.

"Barka da safiya Madame."

"Barkanmu dai baban Yusuf, fatan kana lafiya?".

Fuska fal walawala ya ce, "Alhamdu Lillah daman ina so ne kixo ki ga shagon dana bude a kasuwa in ba matsala."

Da fara'arta ta amsa, "Ma sha Allah, bara inzo muje."

Suna zuwa kuwa suka ga shago ne na kayan ɗinki, da keke biyu tare da yara Guda Uku,sai babba daya dake koyar da su dinkin.

A bangare guda kuma kayan dinkin ne aka tara na saidawa.

Ba karamin farinciki Zeeyter tayi tana fadin, "Allah sa silar arzikn ke nan, Allah sanya Alkairi na ma murna baban Yusuf."


"Amin Amin ya Allah Madame ban san da bakin da zan miki godiya ba domin kin kawo canji mai girma a rayuwar gidana, Allah shige miki gabanki da bayanki ya kara arziki da daukaka mai albarka."


Tafiya take zata koma gida gabadaya farinciki ya mamaye mata zuciya, wani waje ta hango da taron mutane ana partyn biki.

Kamar ance taje aiko ta karasa, rawa suke ba ji ba gani ita ma ta shige fili.

Tsayawa suka yi suna kallonta cikin Mamaki.

Ita kuwa bata ma san suna yi ba tikar rawaarta take ban da ihu da tafi ba abun da ke tashi ana mata bidiyo, tamkar ba da jikinta take rawar ba, gwanin sha'awa.sai da tayi mai isarta kafin ta fita ta ci gaba da tafiya
★★
Sun fito zasu tafi Office kenan Zahra ta ce, "Ya batun Zeeytern ne?, Abokina ya kusa zama ango." Ta karasa maganar tana kallon haiydar.

Farouk ya ce, ".......

08103080717
Urs Xayyeesherthou
[6/2, 8:56 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-17*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

"Angon Dole ba." Ya fada shi ma yana kallon haiydar.

Khalil ne ya ce, "Bana so fa, eheen Mutum Ya yi Sadaukarwa ana damunsa wasu ma suyi mana."

"Ni dai damuwata daya in ga yadda zasu kasance kar mu bar kasar nan nasan Anytime muna iya tafiya,so abarni in ga ko Episode one ne." Ta fada tana dariya

Da haka suka tafi company suna Tsokanar juna shi dai haiydar an kashe masa baki ya kasa magana sai binsu da Murmurshi kawai .


★★★Anata aikin gyaran gidan Mai ita ma ta shige cikin sahun masu aiki, kai kace wata Yar aiki ce, a takaice ma duk ta fi su yin aikin.

Madame Ayshe ce ta turo Jamy , "Anty wai kizo inji Mammah."

Ta fada.

Kallonta Zeeyter ta yi tana fadin, "Ok Ki ce ina zuwa."

Wanke hannunta tayi da ruwa tana karkade wando ta fice.

"Barka da Safiya Mammah."

"Barka dai, Fatan kin tashi Lafiya?"

"Alhamdu Lillah Mammah." Zeeyter ta fada.

Madame Ayshe ta ce, "Ma sha Allah,ya maganar mu? Ina ta jiran amsarki shiru Yayane?"


Sunkuyar da kai Zeeyter tayi tana, "Mammah duk hukuncin da kika yanke ya yi daidai ba zan butulce miki ba Indai ina Numfashi In sha Allah."

Madame Ayshe ta kalleta cikin sigar tausayi ta ce, "Kowacce Uwa na yi wa 'Ya'yanta zabi na alkairy ne wanda zai taimakesu duk da cewa bani na haifeki ba, Amman na kan ji cewa tamkar jinin jikina kike, kamar yadda tun kina karama ban taba tilasta miki a kan komai ba yanzu ma ba zan ba, ina bayan duk wani zaɓinki ne, indai baki amince ba kar ki ji shakka ko tsoron fada mun."


"Mammah ki daina cewa baki haife ni ba,tayuhu ke ce uwa mafi Alkairi gare ni fiye da nawa iyayen Shiyasa Allah ya daukesu ba tare da na sansu ba ya bani ke, ke kadai ke goyon bayan komai da zanyi na rayuwa,kin sanni fiye da kowa,kuma kin fi kowa sanin abin da ya dace da rayuwata, bana da ra ayin aure, Amman zan iya komai domin farincikin ki da. Kuma Al'umma, ki sa aranki cewa na aminci da Auren nan ne domin ra ayina ba takura ba,ina sonki,zan yi alfahari da ke a duk inda zan Kasance har karshen numfashi na."


Ban da ambaliyar hawaye ba abun da ke saukowa daga fuskar Madame Ayshe.

Share mata hawayen Zeeyter ta yi tana, "ko ba komai za ki zama sirikar wani ko? Mammahnmu kin tsufa fa." Ta ƙarasa maganar tana dariya.

Ita ma Madame Ayshe dariya tayi sosai.

Jumy ce ta dawo tana, "Anty ki zo muyi wasa,mun dade ba mu yi wasa ba." Ta ƙarasa maganar tana taɓe baki.



Zeeyter ta janyo ta jiki tana, "Oyaa yau ba wasa daman anguwar nan tayi datti maza ki kira mun su booboo da Baby da kowa a fito ayi aiki, yau hutu ba karatu ina?"


Jumy ta girgiza kai alamar , "Eh."

Zeeyter ta ce, "Oyaa My Jumy je ki kira su to muyi aiki."


Da gudu Jumy ta tafi tana, "Anty na Kira Azo ayi aiki inji Anty kowa ya sa kayan aiki."


Nan da nan Yaran suka hadu waje ɗaya suka cire kayan jikinsu tare da sa wanda aka tanada domin yin aiki.


Tare da ita suka fara aikin masu shara na yi, masu kwashe kwata da cire yana na yi,sai da suka tsabtace anguwar nan tas kafin Zeeyter ta ce, "Yawwa Yaran Kirki aje a wanki jiki ayi Sallah ,in kun idar zan zo in maku kyauta."


Da gudu sukaje suka nemi buta suka yi alwala suka yi sallah.

Sai da suka idar ta ce kowa ya rufe ido.

Leda ta fara mikawa kowannensu suna budewa sai Qur'ani Izu Biyu da Chocolate.

Murna suke suka tashi suna tsalle da rungumeta...

"Anty Ina Son wannan Qur'anin Sosai Zan haddace shi

Please Login or Register in order to submit comment