Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-13*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

_*Wannan Fejin Sadaukarwa ne gareki Anty Zee Uwar Marayu, Allah ya ƙara nisan kwana da arziƙi mai albarka, Allah ya shige miki aduk kan lamuranki, Allah biya miki dukkanin buƙatunki na alkairy duniya da lahira, Allah ƙara Haskaka Rayuwar ki da haske mafi inganci*_



_*Masoyan YEL Na ji matukar Dadi yadda na ga kun fara fahimtar Littafinnan wannan shi ne Burina kuma shi ne maƙadusin rubutawa, ba zan iya yi maku so kadan ba,son so fissabillah*_



Tamkar ba ƙauye ba,kuma ba anguwar talakawa ba, gabadaya wajen a tsaftace ga ruwa ga kuma wutar lantarki.


Daga Khaleel har Farouk ba wanda bai yi sha'awar kauyen ba da mamakin kasancewar sa haka, Mussamman fannin abubuwannan more rayuwa wuta da kuma ruwa.

Zuwan Halliru ne ya dakatar da su daga dogon tunanin da suka faɗa,"Barkan ku da zuwa dai yallaɓai." Ya ƙarasa maganar yana miƙa masu hannu.

Gaisawa su ka yi kafin ya musu iso su ka shiga ciki wanda suka kara jin mamakin da yafi na waje, duk da kasancewar gidan ƙarami ne kuma da galan galan ta gina, amman ba karamin kyau da tsari ya yi ba, hatta wajen zaman baƙi a tsare yake.

Zama su ka yi aka kawo masu drinks da ruwa,tana can ciki suna aiki, sai da Halliru ya kirata kafin ta fito.

Khaleel ta fara mikawa hannu suka gaisa kafin ta mikawa Farouk tana dariyar mugunta.



Murmurshi kawai ya yi suka gaisa.

Ya bi ta da kallo tana tafiya.

Komawa ta yi ta ci gaba da aikinta ta barsu da Halliru tamkar shi ne shugaban.

Khaleel ya lura da wani abu aran Farouk kawar da kai kawai ya yi ya ce, "Abokina ina ita ce shugabar ita ba za ta zo ayi da ita ba?"


Murmurshi Halliru ya yi ya kalli inda Zeeyter take tana ta fama wanke gorina ya ce, "Ta fi so tayi aikin bata taɓa daukan kanta a matsayin wacce ta fi mu akomai daukanmu take a duk ɗaya muke, bata so ana nunawa ita ce gaba."


Khalil ya ce, "Ok to ba wannan ba tukun za mu yi wannan maganar daga baya yanzu ina so ka mun bayanin tsare-tsare da shirye-shiryenku yadda suke gudana."


Har ila yau dai Khaleel ya kalli Farouk sam hankalinsa baya jikinsa idanunsa na kan Zeeyter.


Halliru ya ce, "Kamar yadda kuka sani ko inci muka sanar da ku.
Abu na farko shine:
Muna amfani da Leda,Roba(gorina).
Na biyu:Second:Solar Fenal and battery


Suka haɗu waje ɗaya solar fenal zai bada wutar da zai narkar da komai a heating jamber.

Saboda tsada mu maida shi a saukake yasa muke amfani da Solar

Da zaran an kammala komai za ayi amfani da Solar fanel domin fidda abubuwan

Kamar su
Kerosine
Petrol
Gas

Kudiri da manufofinmu kuma
Na farko: Taimakawa Kananun Yara Su nemi Halal dinsu ta hanyar basu aiki, su bar zaman banza da duk wani abu na gurɓacewar rayuwar.

Na biyu: Taimakon Magidantan da suka rasa aikin yi, da sauran yara samari.

Na uku kuma:Domin ingata rayuwar Karkararmu da ma al'ummar duniya gabaɗaya yadda za su iya siyan Petrol da sauran kayan a kudi kalilan , musamman marasa karfi.


Khaleel ya ce, "Ok komai ya yi daidai, hakan na da kyau, yanzu za mu Je ka nuna mun kowanne bangare da kyau don yanayin yadda kuka tsara ya yi sosai,ina tunani gini za ayi tare da faɗaɗawa kawai."

Ya fada yana kokarin tashi.

Sai a lokacin Farouk ya dawo daga duniyar kallon Zeeyter da ya shiga.

Halliru ya bi da su ko ina ciki da waje ya nuna masu komai da cikakken bayani har wajen da Zeeyter take, Khaleel ya ce, "Barka da aiki Madam."


"Barkanmu dai." Zeeyter ta fada tana Murmushi.

Daga nan suka yi sallama, har wajen mota ta rakasu kafin ta dawo Halliru ya tsaya da ke Khalil ya ce yana so suyi magana.

Mota suka shiga dukan su Khaleel ya ce , "Bayani nake so ka bani sosai dangane da shugabbarku da kuma ƙauyen nan shin gomnati ce ke gyara maku?."


Halliru ya gyara zama kafin ya ce, "Batun Ƙauyen nan da kuma Madame Zeeyter duk kusan abu ɗayane, domin duk wani abu da ka ke gani na gyara anan ita ce sila."

Ƙara kallewa kauyen kallo Khalil ya yi, ya yin da shi kuma Farouk ya kara gyara zama don jin bayani.


Halliru ya ce, "Eheen kusan komai ita ce Sila, Zeeyter Marainiya ce gaba da baya cikin marayu ta taso,bata da kowa sai Uwar marayu Madam Ayshe wacce ta kasance tamkar uwa a gareta, Zeeyter bata yarda da zama ba,burinta da kuma tunanin ta akullum shine wace hanya za ta bi ta samu abun da zata taimakawa Al'umma? Ta saudaukar da lokacin ta, Rayuwarta, Fatincikina da komai nata domin al'umma, bata damu cewa kana sonta bane ko kai makiyinta bane kawai intayi ra ayi zata taimaka ma,mace ce mai kamar maza, ko ince ta ma fi wasu mazan dan da yawanmu ba za mu iya kwatankwacin abubuwan da take yi ba, kun ga rijiyar nan da wancen bowal din?" Halliru ya fada yana nuna masu da hannu

Kafin ya ci gaba da magana

"Kowa ya gani zaiyi tunanin gomnati ce tayi mana Mussamman bowal din amman sam, babu aikinsu ko ɗaya anan duk na Zeeyter ne ,da kanta take shiga cikin gari ta dauko masu aiki tazo ayi aikin da ita ,duk wata rijiya da bowal da kudinta, da hannunta aka yi su a ƙauyennan wanda yanzu har ya kai ga yan cikin gari in suka rasa ruwa nan suke zuwa su ɗiba, batun wutar lantarki ma haka, hatta massalacin can."

Ya nuna masu wani karamin masallaci da hannu

"Da ita aka gina shi kuma da kudinta, akwai gidaje da yawa da take tallafawa da abinci kayan sawa da dai sauransu, tana kuskure kuma tana yin daidai kamar kowanni dan Adam,in taso tayi abun yabo in kuma taso tayi abun kushewa ba ruwanta da kowa, inna ce zan fada wasu abubuwan game da Madame za ku kwana anan ban gama ba wannan a takaice kenan."


Khaleel ya ce, "ina so ka kai mu gun Madame Ayshe in ba matsala."


"Ba komai mu je."Halliru ya fada yana kokarin fita a motar.

Tun daga kofar gidan marayun suka fara kalle-kalle musamman da suka shiga ciki yadda aka ƙayata gidan da kayan wasan yara gwanin sha'awa.

Madame Ayshe na ganin shigar su ta tashi da sauri tare da basu wajen zama cikin fara'a.

Halliru ya ce, "baƙin Madame Zeeyter ne suke son ganin ki."

Ya fada yana kokarin fita.

Gaisawa suka yi dukkaninsu kafin Farouq ya gabatar da su.

Shi kuma Khaleel ya ce,"To ban sani ba ko za kiyi mamakin maganar da zan yi amman Allah yasa ki fahimta,kamar yadda abokina ya miki bayani mun haɗa halakar kasuwanci tsakanin mu da companin Zeeyter to muna so ayi auren kasuwanci wanda dukkanimu kowanne bangare zai samu ci gaba,domin bunƙasa kasuwancinmu kawai indai hakan ba matsala, ba ma da niyar cutarta kuma ba za muyi ba in sha Allah,in hakan ya kasance ba mu ba har ita za ta yi farinciki domin ba inda aikinta ba xai xaga ba a faddin duniyar nan da ikon Allah."

Bayani Sosai Khaleel ya yiwa Madam Ayshe yadda zata fahimta.

Madam Ayshe ta ce, "Na fahimci komai duk da cewa a dunkule ka ba da,zan sanar da ita kuma zan mata bayani sannan zan kiraku kuma ku shirya takardar yarjejeniyar kasuwancin ya kasance ready na san bana da matsala da ita, Indai zan fada to an gama."


Da haka suka yi sallama da Madame Ayshe, suna komawa mota kowa ya lula duniyar tunani.

"Tabbas muna da bukatar irinta,muna da matukar bukatar irin ta, ta kowanni fanni za ta iya mana amfani, ba zan bari Haiydar ya san komai yanzu ba, amman ba makawa ya zama dole in tabbatar da anyi auren irinta muke bukata a tafiyar mu."

Khaleel ya karasa Maganar a Zuciya yana jinjina kai.


"Lallai wannan ba abar zubarwa ba ce, zan so ace nina sameta fiye da Haiydar,amman duk yadda ya kasance zan zama makusanci gareta in sha Allah." Farouk ya fada azuciya yana sakin Murmurshi a zahiri.

Tare suka kalli juna Khaleel ya ce, "Farouk bayan ni da kai bana so bayanin yarinyar nan ya fita ko ina, hatta su zahra, deejerh da kuma Haiydar sai dai su fahimta da kan su."


A zuciya Farouk ya ke saƙawa, "Yoo ni daman yaushe xan so Haiydar ya sani, ni da nake so abar mun ita."

A zahiri kuma ya ce, "ba ka da matsala da hakan Aboki an gama."


Da haka suka koma gida kasancewar dare ya yi.

A falo suka same shi, Deejerh na aiki , Zahra kuma na karatu a laptop na wani girki, shi kuma Haiydar yana ta faman duba bayanan wata mota.

Da sallama suka shiga duka dauke da Murmushi.

Su ka amsA masu tare da fadin, "Barkan ku da dawowa."


Haiydar ya ce, "Na zata acen za ku kwana ai har na fara tunanin yadda zan cinye abincin yau." Ya fada cikin sigar tsokana.

"Acici komai cinka dai dole ka ci ka bari." Farouk ya fada yana dariya.


Khaleel ya ce, "What Ever a jira mu muyi sallah tunda na san ku kunyi sai azo aci abincin Food Master."


Ya karasa maganar yana kallon haiydar.

Sai da suka yi sallah kafin suka dawo suka fara cin abincin.

Khalil ne ya kashe shirun nasu na ya ce, "Guys mun gama komai fa And nayi magana Da mai rikon nata kasancewar marainiya ce ayadda ta nuna ba ma da matsala in sha Allah."

Haiydar ya ce, "wai har yanzu kana nan kan batun auren nan ne?shin babu wata manufa sai hakan?"


Deejerh ta ce, "Hakuri za ka yi fa Haiydar tun da ka ga Khaleel ya dage na san akwai abun da yake hangowa And in ba ci gabanmu bane ba zai taba kawowa ba."


Karaf Farouk ya ce, "wai miye hakan ne? Ana dole ne? Kasuwanci ba zai taba haduwa bane sai da Business MARRIAGE? Ku bar shi mana haba."

Zahra ta kalle shi
"Farouk to ko kai za ka aureta ne,in shi yaƙi??"


"Eheen nima fa ban gane ba, ina ga shi zai dawo Nijar mu haɗa su." Khaleel ya fada cikin tsokana.

Murmurshi Haiydar ya yi azahiri kan ya ce, "komai ya wuce domin kasuwancin mu kadai na aminta Sannan da sharadi daga baya kar azo mun da wani batu kuma?"


Nan Gaban Farouk ya yi wani irin mummunar faɗuwa.

Khalil kuwa da sauran Hamadala su ka yi.

Zahra ta ce, "za ka iya, na sani za ka iya,muna matukar alfahari da kai Haiydar, Allah ya tsaya ma kamar yadda ka yi sadaukarwa domin mu, Allah sadaukarma da hasken da ba ka zato arayuwa."


Da haka suka rabu Yanayin Farouk sam ba walwala suko da ka ga fuskarsu cikin farinciki
Mussamman Khaleel.



Washegari
Da Sassafe Zeeyter na tashi police station ta nufa domin biyan kudin da aka ci tararta a jiya.


Tana zuwa D.P.On na hango zuwanta ya bada izinin ta shiga cikin office din sa.


Murmurshi ya fara yi mata mai dauke da maanoni daban, hannu ya mika mata.
Cike da mamaki ta bashi suka gaisa ita ma tana sakin Murmushi.

"Zaune mana." Ya furta yana kallonta.

Zeeyter ta ce, "Aa ba zama na zo yi ba, ga kudinku nan magana ta kare." Ta fada tana kokarin fita.

Hannunta ya riko da sauri ta juyo tana, "ƙalau?"

"Ƙalau Don Allah ki zauna muyi magana wannan kudin ma na biya miki ba sai kin biya ba." Ya fada yana wani munafukin Murmurshi.

Ta ce"Aa bana so, na biya da kaina ai ni aka ci tara ba kai ba." Ta kara kokarin fita
Ji tayi ya ƙara riko hannunta.

Cikin fushi ta juyo.......


08103080717
Urs Xayyeesherthou
[5/30, 12:42 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-14/15*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

*SADAUKARWA Gare ku Antie Mie Group,ZAUREN SWEERY,I Lobiyu lodi Lodi🥰🥰Team Haiydar da Team Farouk har ma da Team Zeeyter ina yinku Over Son so fisbillah*

*10READMORE💔🙌😹🏃‍♀️*

Ta ce, "Lafiyanka kuwa , za ka sake ni ko sai na fallama gigitaccen mari?"

"Haba Madame Don Allah, ki zauna ina so mu yi magana ne ta fahimta." Dpo ya fada yana ƙasa da murya.


Zeeyter ta ce, "Na ji to sake ni."

Yana saketa ta zauna.

Gyara zama ya yi yana, "Yawwa Ko kefa Madame tsarinki na burge ni Mussamman karfin gwiwarki, da farko dai na ce ki dau kudinnnan na biya miki, sannan kuma ni dai Sunana Abdullahy ina da mata ɗaya,amman....."
Sai ya tsaya shafa kyeya.

Cike da mamaki Zeeyter take kallonsa ganin cewa ya na bata jawabin da basu shafeta ba,kuma ba damuwarta ba, "To miye haɗina da hakan?" Ta furta.

Murmurshi ya yi, ya ce, "Au Afwan Madame na ce ko za ki iya bani Number ki in ba matsala?."

Ba tare da ta masa magana ba ta dauki wayarsa dake kan table ta rubuta number ta ajiye.

Tana tashi ta ajiye masa kudin nan tayi gaba ko a jikinta.

Kiranta yake amman tamkar ba da ita yake ba,har ta bar harabar station din.

Tunani ya shiga yi ba abun da zuciyar sa bata saƙa masa, duk neman mafita yake shin ta ina zai bullowa Zeeyter.


★★★tana komawa gida Madame Ayshe ta kirata.

Tana shiga cikin gidan marayun

Gaɓadayan yaran su 20 suka fito suna rungumeta suna murna"Oyoyo Anty ina kika je? Yau ba ki zo mun je gudu tare ba,Anty ina kika tafi kika barmu?"

Tambayoyin da suka fara yi mata kenan.

"ya isa ya isa ai kun je da mammah ko? Kuma gani na dawo, cikinku akwai mai bukatar wani abu?."

Da sauri karamin cikin su ya ce, "Anty Takalmin kwallona ya ɓaci ina so a siyo mun wani,kin san ina so ne in zama babban mai buga kwallo."

Jan kumatunsa tayi, "Ehen In sha Allah Messi na biyu In sha Allah,za a siyo ma."

Da gudu ɗayan yaje ya dauko wata torchlight
"Anty Kwan Wutar dakin Mammah ya ɓaci na gyara."ya karasa maganar yana mika mata.

Karba tayi tana
"Woo Ma sha Allah Sannu da kokari Booboo na,My little Engineer."

Wata Yarinya cikinsu ma ta ce, "Aunty Madame ta ce asiyo mun kayan zane nawa sun ƙara."

"Tom In sha Allah Babyna, yanzu ku je ku ci abinci zan dawo muyi hira in baku labari kunji, bara inje gun Mammah."

Gun Madame Ayshe ta nufa bayan sun gaisa ta ce

"Magana za mu yi Zeeyter amman ina fatan ki mun kyakkyawar fahimtar da kika saba a baya.
Na sani cewa ba aure a gabanki ko ince ba shi ne damuwarki ba,kin fifita farinciki masoya da makiyanki a kan karan na ki, ban sani ba a matsayina na wacce nake tamkar uwa a gare ki inna yanke hukunci na yi daidai ko akasin hakan, Ina so kiyi aure."

Da sauri Zeeyter ta dago tana kallon Madame Ayshe ya yin da zuciyarta ke bugawa cikin sauri.


Murmurshi ta yi ta dafa kafaɗarta, "na san wannan furucin zai iya baki mamaki kam, amman ka fin komai kin tuna da cewa ba zan taba abun da zai cutar da ke ba, Aure za ki yi, ya amsa sunan Aure ne kawai Amman ba cikakke ba, domin auren kasuwanci za ki yi, wanda ni na sani ba ki da wani buri fiye da ki ga kin Habbaka kasuwancinki, wannan dama ce tazo guda biyu a gare mu, na ɗaya domin kasuwancinki na biyu kuma za mu rage abun faɗi da gulmace gulmacen tare da tsanar da mutane ke nunawa kanki, ina so ki sa aranki cewa za kiyi aure ne don kasuwanci ki da kuma farinciki na."

Numfasawa Madame Ayshe ta yi kafin ta ce, "jiya da yamma companin da kika sanar da ni cewa sun baku tallafi sannan za ku yi haɗin gwiwa,biyu daga cikinsu sunzo cikin gidannan bayan fitowa daga gidan mai, sun mun bayani Kasancewar ki a kusa da su na da mahimmanci hakan yasa suka yanke wannan shawarar, sannan na aminta da dukkanin bayanan da suka yi mini kamar yadda ki ka ji, aure ne na Kasuwanci, Amman aguna ba na Kasuwanci bane kadai harda na kima da darajarki na 'Ya mace."


Gabadaya jikin Zeeyter ya yi sanyi, aranta tana jin cewa zata iya komai domin al'umma amman wannan batun auren fa? Ya za ta yi da shi, shin zata iya rayuwa awani waje bayan nan? Shin wace rayuwa za ta koma yi acen?

Madame Ayshe ce ta kara dakatar mata da tunaninta , "Ka da ki damu,ban tilasta miki ba,kamar yadda ban taba tilasta miki akan komai ba, amman ina so kije kiyi tunanin kafin yanke hukunci."


Murmurshin karfin Hali Zeeyter ta yi tana, "Tom Madame In Sha Allah."


Tana komawa gida sai ga Yusuf ya zo tare da fadin cewa baban sa ya dawo inji mamansa.

Nan take Zeeyter ta dauko gyalenta ko hutawa ba ta yi ba, ta nufi gidansu Yusuf.

Da fara'a Maman Yusuf ta karbeta har ma Baban dake ta bashi labarin komai tun kafin Zeeyter ta zo.

Bayan sun gaisa ta ce, "Ka yi hakuri Ba rayuwar cikin gidan ka nake son shiga ba, amman ina so nayi dan gyara ne in ba matsala, ina so ka fada mun meyasa ba ka damuwa da rayuwar iyalanka? Me yasa ba ka son zama da su? Sannan me yasa ka fifita Saduwa da haifan 'Ya'Ya fiye da komai cikin hakkin Aure?"

Jikinsa ne ya fara sanyi kafin ya ce, "ban da karfin da zan iya ciyar da su, Shiyasa na zaɓi tafiya."


"Zamanka tare da su yafi komai mahimmanci a rayuwarsu sannan bakin da Allah ya tsaga baya hana shi abinci, kai baka basu abinci ba, kuma baka basu tarbiya ba,amman kullum cikin kunsa mata ciki tana haifewa, wannan wace irin rayuwa ce? Sam hakan bai dace ba,ko da ace kana da arziki ba shi ke nufin zaka iya tarbiyantar da 'Ya'ya barkatr ba,bare kuma akasin hakan, ba ace kar a haihu ba, Amman a haifi abun da akasan za a iya tarbiyantar da su da kuma dawaniyarsu,ba wannan ba tukunna wace irin sana'a ka ke da sha'awar yi?"

Zeeyter ta fada tana kallonshi.

"Kasuwanci na ke so wanda zanna sai da kayyaki na sawa." Ya fada.

Zeeyter ta ce, "Zan baka jari da ikon Allah amman ina so ka mun alƙawarin cewa ba zaka kara barin matarka da 'Ya'yanka cikin wani hali ba, sannan zaka bata darajarta na 'Ya mace, ita ma mutum ce ba bola ba, sannan ka bata izinin ita ma ta fara kasuwancin da zata dogara da kanta ba sai abun da ka samo ka bata ba."



J'aimerais que vous compter sur vous-même, en plus d'avoir de bonne relation en sachant que ce pas seulement le rapport sexuel qui est un mariage. (Zan fi so ace dukanku kowa ya dogara da kan shi,sannan ku samu kyakkyawar alaka da sanin cewa ba saduwa bane kadai aure,)"

Murmurshi baban Yusuf ya yi ya ce, "In sha Allah Madame na miki alƙawari,nima daman nasan abun da nake ba daidai bane kawai dai ina biyewa son zuciyata ne, wanda a yanzu kuma na gyara ke nan Da ikon Allah."


"Alhamdu Lillah na ji dadin hakan,sannan ina gayyatar ku kai da Maman Yusuf har ma YUSUF din wajen taron wayar da kai da za a ana gabatarwa a cikin ƙauyen nan, ga kuma wata shawara wacce bata zama dole ba,amman inda hali ku Kasance masu taimakon na ƙasa da ku a kullum, sannan kada ku sa hassada ko kyashi a zuciyoyinku,ku koyawa kanku farinciki ta hanyar faranta ran kowa hatta makiyanku ku kyautata masu watarana za su iya zama masoyan ku."


"In sha Allah Madame mun gode sosai Allah saka da alkairi kuma za mu zo in ansa Lokacin."

Suka fada a tare.

Nan Take Zeeyter ta bawa Baban Yusuf jarin dubu ɗari Uku,Maman YUSUF Kuma dubu ɗari Biyu.

Suka yi mata godiya sosai.

Bayan tafiyarta ne mamaki ya kama baban Yusuf, "Oh Allah ƙaramar Yarinya da halin manya,zuciyar manya tunanin manya, Allah na gode ma da ka turo wannan baiwar Allahn cikin rayuwarmu tun yanzu."

Durƙusawa gaban Maman Yusuf ya yi yana, "Na san na zalinceki , kuma na cutar da rayuwarki,amman Don Allah ki yafe mun, daga yau na miki alƙawari zan baki farinciki wanda bakya tsammani,zan baki ikon daga darajarki na 'Ya mace dana durkufe shekarun baya, cikin kankanin lokaci tare da dunkulallen jawabin yarinyar nan ya sauya mun komai na rayuwa, tabbas 'Ya mace ba abar wulaƙantawa bace."

Ya karasa maganar yana hawaye.


Murmurshi ta yi ta ce, "Babban burina bai wuce ashe ka fahimci darajar 'Ya mace da Ahalinka ba,kuma ka fahimta Alhamdu Lillah,na yafe ma duniya da lahira."


Daga wannan lokacin salon ya fara canjawa.

Zeeyter na komawa gida Madame Naddja ta sanar da ita za a fara taronnan nan da kwana ɗaya domin ta yi wa wani magana wanda shi ne farkon target dinsu.

Hakan yasa suna gama karatu Madame Naddja ta tsaya sai da suka gama shirya yadda komai da komai zai kasance tun ranar kafin ta tafi.


★★ Kwance Farouk yake amakeken gadon dake dakin wayarsa yake dannawa can kuma ya tsaya tamkar an bashi umarni kamar wasa ya yi creating sabon account a facebook, ba hoton shi sai zallan suna kuma ba details din komai da za a iya gane wane ne searching sunan Zeeyter ya fara yi ,ai kuwa sai ga shi ta fito,ko da ya duba dpn ta ita ce kuwa sanya da kayanta digijari-digijari, Friends request ya Tura mata, da mamaki har ta amsa.

"Hi." Ya Tura mata

"Hi ya tafi koyo Sallama da kan ka agun kamar gwanda." Ta fada da emojin harara.


Dariya ya yi kan ya ce, "Oh Oh Sorry Madame Assalam alaikum."

Emojin Murmushi ta dauko tare da fadin, "Wa alaika Salam."

"Ya ki ke? Ya jin dadi? Ya zafi,ya kuma sanyi." Ya fada.

Emojin bata rai ta tura, "Wanne zan amsa ciki?."

"Duka mana." Farouk ya fada.

Daga nan suka ta dariyamarsu abun mamaki har tayi saurin sakewa da shi sunata hira yana bata dariya.
Dariya.

Daga karshe Farouk ya ce, "zamu iya zama kawaye? ."


"Sosai ma mai zai hana?"

Ya ce, "To Shikenan daga yau Zanna ce miki kawata ni kuma me za ki na kirana?"

"Aboki mai kan gwanda." Ta fada cikin zolaya.

Dariya suka yi dukkaninsu.

Har suka yi sallama Ba karamun dadin hirar nan Farouk ya ji ba, ban da ita ba abun da yake hangowa a idanunsa har barci ya dauke shi.


Ita kanta mamakin kanta take ya akayi tayi saurin sabawa da mutum da bata sani ba a lokaci kadan?

Tsaki tare kawai ta tashi cikin darennan ta shige toilet, tayi wanka sannan ta kara Sadiq (saurayin da ta saba kira in tana da bukata) tare suka kwana har sai asuba da ta tashi sallah ta tada shi ya tafi.

★★Zaune suke dukkaninsu kowa na aiki Deejerh ta fito, "Hi Guys ku duba mun wandon nan ya yi fasali kuwa?"

"Woooo My Deejerh ke ta Mussamman ce, ban jin cewa a yanzu zan iya sa wani kaya da ba designing ɗinki ba, wandon nan ya bala'in yin kyau ba kadan ba,wannan nasan yana fita kasuwa sai an nema an rasa." Zahra ta fada tana kara duba wandon.


Farouk ya ce, "Eheen na fada maku muna da sarauniya komai nata na musamman ne "

"Kullum cikin fito da salo mai ban mamaki kike Deejerh." Khalil ya fada yana karewa wandon kallo.

Cikin zolaya Haiydar ya ce, "tunda abun wariya ne maimakon ayi na maza sai na mata to bai mun kyau ba."

Dariya suka yi dukansu Deejerh na, "Mai kake ci na baka na zuba, na mazanma na loading kasan ko wani irin kaya sai dai afara gani a jikinmu."

Wani irin wando ne golden colour, gabadaya botira ne jiki anyi kamar ado dasu har wajen shafe din,kasan kuma anyi wani irin tattara kanana mai step-step.

Ba karamin kyau ya yi ba,yanayin yadda kowacce mace xa ta iya sawa kuma zai mata kyau, lutiye ko sirara.


★★Zeeyter ganin cewa bata da abun yi ga shi Madam Naddja bata zuwa ran Sunday,gidan mai kuma an fara gyara masu aiki ne da su Halliru ke lura da gun kawai.

Tattara kananun yaran unguwar tayi ta ba kowa littafi da pencil,da kaloli.

Tare da fadin, "Kowa ya gina gida mai kyau duk wanda na shi yafi kyau zan ba shi sweet,."

Ita ma ta fara zanen ba tare da tasan abun da take zanawa ba, zuciyarta kawai take ba sai da ta gama ta ga

Please Login or Register in order to submit comment