Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dalilin da ban jin cewa zan iya aure ko da ya zame mun dole." Haiydar ya karasa maganar yana mayar mata da martanin kiss din da ta mai.


"Umm,umm Baby! Ni ina so in aure ka, ina so in aureka,ka aureni mana ka ji, za mu fi jin dadin soyayyarmu fiye da yanzu." Cewar Meenoh tana shagwabe fuska.

"Bana so,na ce ba zan iya ba, bana son Maganar." Cikin zafin rai ya fada yana turata gefe tare da janyo kwalbar giyarsa yana sha.


Da sauri ta karasa inda yake tana kokarin rugumesa ya bigeta ta faɗa ƙasa.


Cikin kuka take magana, "Na daina maganar Auren ka ji, abar maganar Okay ka sake ranka ,ina sonka a yadda ka ke za mu kasance."


Buguwar da yayi yasa shi mantawa da damuwar da Meenoh ke shirin tuna masa cikin sauri.

Ganin ya fara fita hayyacinsa ne nan da nan ta fara aika masa da wasu zafafan saƙonni wanda ya ƙara birkita shi.


Haka suka Kasance cikin daren nan


Meenoh ɗaya ce daga cikin 'Yan Matan da ke Rububin Bin Haiydar Don Dukiyarsa domin ko da bai kwanta da su ba indai zasu buƙaci kudi zai basu,ta kudiri niyar Auren sa ne gudun kar sauran su ruguta, kowacce a cikin su burinta kawai ta nuna soyayyar da zai ji sha'awar aurenta amman sam hakan yaƙi samuwa wanda a karshe ma Matsala suke samu ga duk wacce ta nacewa batun.


★★
Shirye-shirye ya kankama
Farouq
Khaleel
Deejerh
Zahra
Kowanne cikinsu ya nemi izinin ketare kasa domin zuw niger tattaunawa.
Amman Khaleel sai da yaje Indonesia daga Uk domin su tawo tare da Zahra.


Ban da farinciki ba abun da Haiydar ke yi ganin cewa za su ƙara haɗuwa da abokansa kowanni bangare na gidan sai da yasha gyara kasancewar babban gida ne akwai bangarori da dama.


A bangaren Zeeyter ma sunata shirye-shirye hakan ya sata Zuwa kasuwa wanda yayi daidai da isar Farouk Jumhoriyar nijar.


Tsaye yake daidai shagon da zata shiga ta zo har zata wuce taji an damko hannunta da mamaki ta waiwayo ga shi dai bata san shi ba amman yaki sakin mata hannu kokarin ɗaga dayan hannun tai domin kai masa mari karaf ya riƙe


08103080717
Urs Xayyeesherthou
[5/29, 9:22 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-9*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

Tafiya take tuna juyowa da kallon motar, shi ko baya ta ita ma daukan wani karanmin File ya koma.

Tafiya take tana yar wakarta, wanda team din sogha Niger suka yi , "Aujourd'hui on lutte pour l'editer l'éducation des filles le bonheur des femmes.
"A yau muna gwagwarmaya don gyara tarbiyyar 'yan mata, farin cikin mata."

Har ta isa bobiel
Tana isa kuwa bata wuce ko ina ba sai gidan abinci domin tasan lokacin zasu fara aikin girkin dare.

"Barka dai Madame,Barka da zuwa." Abun da yan wajen suke fadi ke nan.

Da fara'arta take fadin, "Barkanmu dai Allah sa baku fara girkin ba don yau Pancake na ke so mu ci, na jiga shinkafa tun safe."

Bude baki su kai dukkaninsu a tare.

Shugabarsu Meriyam ta ce, "Madame mene ne Pancakes?"


"A hausance kamar ana ce mai Sinasir da turanci kuma shi ne Pancakes yanzu za mu yi tare ku gani."


"To Madame ai ko za mu so koya ba a daura komai ba daman yanzu muke shiri."

★Shinkafar ta dauko ta wanke ta dauko blanda da coconut oil, yis, custard da youghourt , Albasa,ta zuba duk a tare tayi blending din su, sannan ta juyo a wani babban bowl tayi rapping dinsa da leda.
Awa ɗaya har ya tashi, nuna masu yadda za suyi tayi suka fara suyan sannan ta fara hada vegetables soup dinta, Kabej ne da Karas,sai green pepper da hanta aka yanka kanana-kanana, da attaruhu ,albasa sai su magi da kori suyawa tayi duka ba ko ruwa ajikin miyar sai simas wanda shi ne madadin mangyada ba karamin kyau ta yi ba.


Suna cikin yi tana masu bayanin komai, "wannan ya fi cin kudi da yawa shiyasa ba kowacce kasa suke irinsa ba, musamman Nigeria basa sa coconut oil da youghourt da dai sauransu,amman turawa sun fi yin irin wannan."

Ana kammala abinci karfe 7:30 kowa ya hallara ciki kuwa harda su Harira da hurera musamman da suka ji labarin cewa Zeeyter ce ta yi girki, sun san cewa na musamman ne kuma ba karamin dadi zai yi ba, domin tana son girki Sosai a rayuwata wani Lokacin ma kirkirar abu take kawai ta dafa, duk da cewa bata damu da ta ba cikinta ba don ko da ma zata ci kadanne.


Suna cikin cin abincin Hurera ta kalli Zeeyter tana, "ni na rasa wannan wace irin mayyace wai wannan fa girkin yan gayu yan kasar waje ne ko ina ta je ta iya kuma har yake dadi haka oho."


Harira tai ƙasa-ƙasa da murya, "ni na fara zargin ma cewa Aljana ce, na tabbaatar ta sha wannan juice din da na kai mata Amman ki ga fa bai mata komai ba."

"Koma Sheɗance ba Aljana ba wallahi sai mun yi maganinta." Cewar Harera tana zuba sauran sinasir dinta aleda,haka ita ma harira ta kwashe nata suka fita suna ƙus-kus.

Ita ko Zeeyter bata ma san me suke ba,tukunya ce agabanta yar sauran miyar da aka rage ta jefar sinasir guda ɗaya tana ci,kai kace almajira ce tazo cin saura.



Sai dare su ka kama hanyar komawa gida anan ne Zahra ta ce da Khaleel su tsaya a kasuwa za ta yi siyayya.

"Um Madam ba za ki bari gobe muyi ba? Dare fa ya yi ina son yin barci." Cewar Khaleel yana shagwabe fuska.

Kallon shi Zahra tai tana kokarin fita a motar cikin dariya take fadin, "Just Few minutes Oga mai ciwon barci, Mutum baya gajiya da barci."

Dariya shi ma ya yi ya fito yana binta, "E na yarda I love Sleeping So Very Very Much Oh oh, kowa da abun da ya dame sa."

Siyayyanta tai tsaf Khaleel na tambaya me zata yi da su ta ce, "Ina Ruwanka Just wait na."


Tuni su Haiydar sun rigasu isa gida har ma sunyi wanka kowa ya kwanta,hakan yasa suma suna zuwa Khaleel ya nufi dakinsa zahra tana mai dariyar ciwon barci.


Washegari
Karfe biyar na safiya tun da Zahra ta tashi sallah bata koma ba kitchen ta shiga domin yi masu break.

TUWON MASARA DA MIYAR FAKOU ta shirya yi wanda yake ɗaya daga cikin abincin gargajiya na jahar Niger.



Nama ta fara wankewa sai da ta dan tafasa shi a wuta kafin ta sauke ta sa shi agefe

Sannan ta hada kayan miyanta waje guda, tumatur,Albasa da attaruhu da tattasa suma ta wanke su tas, karamin turmun da ke kitchen din ta dauka sai da ta jajjaga su tas kafin ta kwashe tasa su agefe suma.

Kafin ta kara yanka wata albasar.

Gas ta kunna ta daura tukunyar kai kafin ta zuba mangyada wannan naman tasa aciki.
Sai da naman ya dan soyu kafin ta zuba wannan yankakkiyar albasar aciki, ta dauko kayan miyan da ta jajjaga ta zuba da wani tumaturin na gwangwani kadan, sai da ta basu wajen minti uku kafin ta zuba garin daddawa ma ta zuba da citta,da tafarnuwa kadan saboda ba kowa ke so ba, sannan tasa kabou dan kadan domin in ya yi yawa miyar za ta iya ɗaci,sai da suka soyu sosai kafin ta zuba ruwa kaɗan ta rufe tukunyar.

Bushasshiyar Fakou ta tankade ta ta kara gyarawa kafin ta Murje har sai da ya yi laushi, komawa ta kan wannan miyar ta zuba dadai yadda take so kaurin ya kasance ta kara ruwa kafin ta sanya sinadarin dandano kadan da gishi, domin yan jahar niger basa shan magi Sosai.
Miyar ta ta kammalu hakan yasa ta zubawa a food flask.
Ruwan zafin da ya tafasa ne ta zuba masa ruwan garin masaran da tai talge da shi da yar kanwa kadan ta rufe sai da ya dan sulala kafin ta dauko muciya tana zuba garin tana tukawa har y yi mata kaurin yadda take so, rufewa tayi ya dan kara sulala na mintuna kadan kafin ta daura shi aleda yan daidai.
Shi ma a flas din tasa kamar miyar.

Ruwan zafi ta kara daurawa a akan gas din

Ta sa lipton,citta,kaninfarux, citta,mante,cittronnelle (gimba),goruba duka tasa acikin tukunyar sai da ya tasa sosai kafin ta juyo acikin waterflask.

Shi ma Tean irin wanda yan Niger suke yi ne.


Sai da ta jera kayan tsaf akan daining kamar an fada masu Haiydar ne ya fara fitowa yana, "Morning Mrs Cooker My Noise is telling me something special,tun ina barci kamshi yake ta jana,da kyar na iya yin wanka."

"Ya naji gidan ya dau wani salone yau ne na matso in ga wani irin kamshi ne Wannan." Cewar Deejerh dake fitowa.


"Dis ur Surutu ba zai bar mutun ya yi barci ba ma, na fito kafin atashine." Khaleel ya fada yana gyara glass din idonsa.

Dukansu a tare suka karasa daining area din.


Haiydar ne ya fara bude abincin, "Wooo Delicious,Amman wannan abincin kasar nan ne fa taya kika iya." Ya karasa maganar cikin mamaki.


Dariya tai ta ce,"Girki dai ako ina yake in sha Allah za mu iya."


"Iyee kana wasa da Madam Zahra Mrs Cooker ko? Ko da yake wannan din ma nine ya koya mata jiya." Cewar Khaleel

Dariya su ka yi, Farouk da Deejerh suna, "Koma miye za mu ji abaki dai."


Da Sauri Haiydar ya ja kujera ya zauna, "Hanjin cikina sun fara sukuwa daga jin kamshi Mussamman ma sun jima basu hadu ba,kuma in fada miki wani abu wannan miyar ita ce fevorite dina." Flat ya dauka yana kokarin zuba ma kan shi.


"Oh Food Master ba wasa." Deejerh ta fada tana dariya.


Duk da cewar Farouq, Khaleel da Deejerh basu taba cin irin girkin ba Amman ba karamin dadi da burgesu ya yi ba, tunda suka fara ci suke yabawa har suka kammala Mussamman Haiydar shi baya iya Magana ma sai loma da dariya.



Suna kammalawa Company suka nufa Domin zaman su da Zeeyter Oil And Gas da zai kasance A yau .


★★★Shirye-Shiryen tafiya suke ita da Halliru wanda ya kasance shine mataimakin ta a campanyn, ganin shigar da tayi na ko in kula ne ya sa shi yi mata, "Madame ba ki sa kaya ba ai."


Kallon shi tai kafin ta kalli kayan da ke jikinta wani gajeran bakin wando ne ya fara koɗewa har ya yi jurwaye da wata riga Blue duk ta cicciinye.

"Ba yan kayan da ke jikina akwai wani abun buƙata ne da zan sa? Ko kuwa tallan Ado za mu je masu?." Ta karasa maganar tana Murmushi tare da karkade wandon.


Murmurshi ya yi yana kokarin daukar jakarta ,da sauri ta karɓa tana, "Laisse je vais faire (bar shi zan dauka) sai ka sa ana mun kallon wata boss." Ta karasa maganar tana dariya.

Ƙa'idarta ne sam bata so ace za amata wani abu da tasan cewa za ta iya koma bai fi karfinta ba,ba abun birgewa bane ace za a rike mata jaka ko wani abun.


Fita suka yi Halliru ya duba address din Da 5stars suka turo masa, Nafef suka shiga, suna cikin tafiya nafef ta carke a tsakiyar titi ga shi ba kowa a hanyar domin ya yi nisa da gari sosai.

Fitowa su ka yi mai nafef din ya fara dubawa amman fir taƙi tashi kuma ga mai aciki komai ya duba ƙalau.

Gajiya tayi ta fito tana fadin, "wai mene ne?"


Halliru ya ce, "Madame C'est la moto voiture(NAPEP) qui refuse de se demaré (Madam Nafef din ce taki tashi)."


Karasawa wajen tayi ta jiyo salansar na wani irin kauri.

Gyalenta ta dammare a ƙugu ta ce, "bani kwandon kayan gyaran can."

Tana karfa ta kunce salansar , ashe dattine ya shiga ciki ya toshe kofar da iska ke fita sai da ta goge tas kafin ta maida, yana kunnawa kuwa ta tashi.


Saura minti biyu cif Lokaci ya cika suka isa bakin get din .

Su Haiydar kuwa duk sun halla a ɗakin taro.

Zuwa tai tayi wa mai gadin magana tare da mai bayanin zuwansu.

Da mamaki ya tsaya kallonta sai a lokacin ta lura da da Petrol din da ya ɓata mata jiki.

Nuna masa ID card din ta tayi na Zeeyter oil and gas
Bude masu ya yi kawai yana ci gaba da binta da kallo.

Suna shiga......




08103080717
Urs Xayyeesherthou
[5/29, 9:22 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-8*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

Kasuwa ta shige abun ta domin siyan basket ball din da za su yi amfani da shi gobe a wajen karantunsu da yara, ta manta shaf dazu bata siya ba yanzu ko duk da dare ya yi tana tunawa ta fito,duk da kasancewar bobiel na nesa da cikin gari Sosai amman tsoron dare ko duhu baya sa Zeeyter ta kasa fita siyayyanta komin dare indai za ta samu shaguna abude, dalilin fitowar ta kenan da yasa ta kara karo da Farouk a karo na biyu.


Shi ko yana shiga bangaren falon da suke hutawa na campanyn zama ya yi yana wata irin a rarrauniyar ajiyar Zuciya.

Deejerh ce ta fara dagowa tana dariya, "Oh My Friend Me ya faru ne kuma naga face din ka looking some how."


Tsaki ya yi kawai ya fice ba tare da ya ce komai ba.

Zahra Da Khaleel kuwa Hira suke bangare guda su biyu ba mai jiyo abun da suke fadi.

Haiydar ya kallesu yana, "Deejerh Help Me observe Something ba ki lura da mutanen cen bane wai?

Da sauri Deejerh ta juyo tana fadin, "Oh oh tun tuni na fahimce there's something secret i just keep my mouth Shut,in ga ko wani cikun zai ga abun da na gani."


Haiydar ne ya tafa hannu tare suka juyo suna kallon shi
Dariya suka fara daga shi har Deejerh suna fadin, "Romiyo And Juliyat."

Deejerh ta kara da , "Sai ku tashi mu koma gida, dare ya yi ko anan zaku kwana kuna soyayyar ne?"



Haiydar ne ya tashi yana daukan key din mota , "leave them Ou, ko za su kwana anan ba za su ankare ba zo mu fara gaba,i think Farouk ma ya jima da komawa gida."

Dariya Khaleel ya yi ya suna tashi a tare da Zahra, "ba za dai ku canja ba a gulma Haiydar And Deejerh kun gama da Farouk an dawo kan mu to Oya Madam mu je kinji."


Dariya ita ma Zahra tai tana, "Kyalesu ka ji, zan yi maganinsu a abinci i will only cook for you tomorrow su kam sai dai suyi takeaway."

Haiydar da Deejerh suka shiga mota ɗaya, Khaleel da zahra, shi ko Farouk tuni ma ya tafi shi ɗaya.


Washegari

Da Sassafe Zeeyter ta fito saboda yara na kawo mata gorina da robobin aikinsu ne duk karshen mako.

Misalin karfe 7:00am suka fara tururuwan zuwa tana karba tana basu kudadensu kowanni yaro sai farinciki, ba karamin dadi Zeeyter ke ji ba ta ga Murmurshi a fuskar al'umma Mussamman talakawa bare kuma ace ita ce sanadi, Shiyasa ko da gorinan su da ledoji basu kai kudi ba take basu ishasshe don farincikinsu kawai.


Sai da ta gama karɓa kaf kafin ta tattara su, kamar ance ta shiga daƙi, juice din da Harira ta kawo mata ne ta ci karo da shi abun mamaki ya zama tsuntsu domin tunda ta karba ta ajiye ta manta da shi shaf.

Tsayawa tai tana kallon ikon Allah
Can kuma sai tayi dariya ta dauka tare da zubarwa a toilet.


Karfe 10:00am daidai Madame Naddja mai koya masu karatu ta zo , domin yau suna da abubuwa da yawa harda basket ball bayan sun kammala karatun.

Duk sun taru har Zeeyter English ta fara masu wanda har turanci take koya masu aciki kafin ta koma bangaren computer da lissafi wato maths, duk a subject din da ake ba wanda yafi birge Zeeyter ta ke so fiye da computer hakan yasa ta siyo masu system ana koya masu abubuwa da dama aciki Sosai,suna gamawa aka koma karatun Qur'ani tare da sauran littafan Islamiya, sai da suka gama karatunsu kafin aka fita buga basket ball din kowanni yaro ta siya ma shi kayan Sports irin nata dake ita ta kware sai take jagorantarsu awannan ɓangaren.


Madame Naddja Fashiya ce afannin karatun bako da na addini kasancewar a kasar waje tai karatun ta tana da gogewa akan fannoni da dama agunta Zeeyter ke fahimtar wasu abubuwa da suka shafi na'aura
Duk ranar d suke da karatu sai Madame Naddja ta zo tayi masu kafin ta wuce Offishin ta,sun saba Sosai ko da basa da karatu wani zubin Zeeyter ta kan je har ofishin Madame Naddja tana lura da abubuwan da take yi Sosai.

Sunyi wasa Sosai cikin nishaɗi har lokaci ya yi suka tashi,ta zaɓi shirya masu wasan ne don karfafa masu ta hanyar nishaɗi ka da su nuna gajiyawar su ga karatun

Sai anan Zeeyter ke tunawa ashe ba tai break ba hakan yasa direct ta nufi gidan abinci.


★★★zaune suke dukannin suna jiran saukowar deejerh domin fara break.


Tun daga sama suke jin karar sautin takalminta.

Ƙarasowarta sai da dukkaninsu suka yi suman tsaye ganin shigar da ke jikinta.

Zahra ce tai saurin bude baki tana, "Woooo Deejerh! Wannan rigar fa ke kika yi designing? Au can't believe this Oh oh ban taba ganin riga irin haka ba."


"Dis is our fashion designer i so much like dis kind of ur dress's." Cewar Farouq

Haiydar ya tashi yana, "wannan wace irin fitanniyar riga ce."

"Oh na ce ko zaku bani damar magana nima, seriously wannan rigar kam ta tafi dani Friend Ama Madame Zahra irinsa mana." Cewar Khaleel

Dukansu suka kwashe da dariya.

Sai a lokacin Deejerh tayi magana, "A tunani na rigar ba za ta birge kowa ba,i just design it for myself amman na ji dadi da mamakin yadda kuke koɗata."

Riga ce doguwa amman ba har ƙasa ba, da wani irin stones mai kyalkyali, hannu ɗaya dogo ɗaya karami kamar yadda tsagun gaban rigar yake.


Fara ce sol sai stones din da aka bi tsagon adon da su golden colour.

Ku rufe idanun ku tare da tunani yadda irin wannan tsaleliyar rigar zata kasance.

"Yunwa na ke ji fa, kun ga lemme take dis food." Cewar Haiydar yana kokarin janyo kujera ya zauna.


Dukansu zama suka yi kamshin abincin ne ya fara dakin hancinsu da sauri Khaleel ya kalli Zahra tare da fadin, "Our Best Cooker, ni anya inna koma zan iya cin wani food da ba girkin ki ba? Pride rice haddadiya da sassafen nan gashi ta ji hanta, kina Shagwaba mu fa"


Ya karasa maganar yana yi mata wani iri kallo.


Haiydar ya ce, "ni ji nake kamar in koma Indonesia ko dan abincin nan zan shige jakarki mu koma."


Haka suka ci gaba da tsokanar Zahra ana wasa da dariya har suka gama cin abincin.

Cikin gari zasu shiga kamar yadda suka tsara Haiydar zai fita dasu domin ya nuna masu fadin garin Niemey.

Gaɓadayansu sunyi kyau Sosai matuka, duk kayan jikinsu designing din Deejerh ne basa siyan kaya awaje,kamar yadda mota ma duk na Haiydar ne, computers na Farouk, gidaje kuwa ko kuma masana anta in za a tsara Khalil ne ke yi kowanne na aikin bangarensa tare da logon su na 5stars.


Zahra da Khaleel mota ɗaya
Deejerh, Haiydar da kuma Farouk mota ɗaya amman duk matan ne suke driving, suna tafiya a jere.


Sai da suka gama za gayawa kafin daga karshe Radisson babban wajen shakatawa ne da ke Birnin Niemey, akwai abubuwan nishaɗi,ban al'ajabi da mamaki, cike da kayan abinci kala kala.


Tunda suka fito Farouk ke zuba ido ko zai ga Zeeyter amman sam ba ita ba labarinta, har bakin titi yake zuwa ya tsaya.

Mantuwa Haiydar ya yi amota da sauri ya fice, kasancewar da nisa Sosai tsakanin inda suka yi parking motocinsu
Zuwan da zaiyi ɗare-ɗare ya ga Zeeyter a saman mota kallon mamaki yake mata kamar ya taba ganinta amman ya kasa tunawa ita ko bata ma san yana gun ba tafiya take ta gaji ta hau ta zauna tana hutawa sai da ya buga motar yana, "


Bien? (Kalau)"

Kallon shi tai sama da kasa kafin ta ce, "Je ne sais pas (ban sani ba) mutane sai sa idon jaraba."

Murmurshi ya bita da shi kawai ya wuce ya kunna motar da mamakinta sai taga ya shiga, zum ta tashi kafin ya fito har ta arce

08103080717
Urs Xayyeesherthou
[5/29, 9:22 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-10*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

*FEJIN YAU KADAN NE AYI HAKURI🙏🏼🙏🏼*


Suna shiga da Farouk suka fara karo tsayuwar Mamaki ya yi yana kallonsu ita ma Zeeyter kallon shi take cike da mamaki, Halliru ne ya katse masu tunani tare da mikawa Farouk hannu, "Daga Kamfanin Zeeyter Oil And Gas." Ya karasa maganar yana nuna masa shedar ID card dinsa.

Nan ya masu iso zuwa dakin taron,tun daga shigowar su kallon mamaki Zahra, Khaleel da Deejerh ke yi wa Zeeyter ban da Haiydar da ko a jikinsa kallon sani kawai yake mata amman sam ya kasa tunawa.

Gaisuwa suka fara yi cikin karamci dukkaninsu suka gaisa da juna kafin kowa ya zauna.

Khaleel ne ya fara magana, "Welcome To 5stars Expensive company, Burinmu a kullum shine kowa ya tsaya da kafafunsa ya gina rayuwarsa yadda zai tallafawa na ƙasa da shi, ba don muna da shi ko mun fi kowa yasa muke fidda tallafi ba, aa dukkaninmu anan kowa sai da ya sha gwagwarmaya arayuwa, muna son ganin murmurshi a fuskar al'umma,muna so kowa ya rayu cikin aminci da karamci,ka da mu ce za mu zauna ,mu tashi mu nema,sannan mun nema mu bada ,mu fadawa wa inda muka bawa suma su bayar Allah zai saka mana da Alkairansa duniya da lahira,
duk da cewa dukanmu mun san dalilin kasancewar mu anan amman akwai bukatar kara takaitaccen bayani."

Ruwan goran da ke gefensa ya sha kafin ya ci gaba da magana.

"A duk karshen shekara muna neman kananun company domin tallafa masu su tashi domin tsayawa da kafafunsu And in yazo daidai da wani ɓari da muke bukata mu kan iya haɗin gwiwa da shi,ko da ace munyi wannan tallafin,mun fitar da sanaarwa Sannan a jerin duk companyn da suka turo naku ya fi daukan hankalinmu zamu tallafa maku haka kuma muna da bukatar yin haɗin gwiwa da ku, Companynmu na reshen jahar ƙasa wannan shine babban abun da ya fi birgemu da janyo ra ayinmu gareku."

A nan Khaleel ya dakata kafin Deejerh ta ce, "muna da bukatar karin wasu bayanai da ya shafi companinku."


"Kamar yadda muka sana'ar daku campaninmu karami ne da ke cikin karamin kauye muna yin Petrol gas,da kuma kerosine, da robobi gorina,wanda muke sa yara na tsintowa mu biya su,sannan in munyi muna saidawa mutanen cikin kauyenmu mu da wasu yan cikin gari da suka zuwa,a ƙalla ko wace rana indai munyi aiki muna samun riba daidai gwargwado."Cewar Zeeyter

"Wooo dakyau amman ma'aikatanku sun kai nawa?"Zahra ta fada.


Halliru ya ce"Mu uku ne daga ita shugaba sai ni sannan sauran maza biyun."

Zahra ta gyara zama tana, "Zan iya zuwa nima adauke ni?" Ta faɗa cikin sigar zolaya.

Dukansu suka yi dariya Zeeyter na , "Me zai hana."


Haiydar ne ya ce, "Yanzu muna son sannin me kuka fi buƙata domin habbas Companinku."

"Muna da karancin ma'aikata, kasancewar ba ma da waddataccen kudin da zamu dauka da yawa, sannan muna bukatar ƙara gyara companin mu ta hanyar gini na zamani da sifafon da ake yiwa kowanni Company sannan babban abun kudin da zamu siya waddataccen kayyakin aiki."

"Weldone Gimbiyata." Farouk ya furta ba tare da ya Ankare ba.

Dukansu juyowa suka yi suna kallonshi, ganin hakan ya sa shi basarwa kamar ba shi ya

Please Login or Register in order to submit comment