Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saba amman in mutane suka ci namana sai sunyi amansa."
Haiydar ya fada suna fita shi da zoe.

Suna fita Zeeyter ta kyalkyale da dariya tana kallon Farouk.
Shi ma dariyar ya yi yana, "Yana ? Ina fatan ba wata matsala komai na tafiya daidai ko?"

Murmurshi ta yi ta ce, "Ehen Alhamdu Lillah kamar yadda na fada ma haiydar na kirki Sosai inda ba shi ya kasance mijina ba,bansan ya zanyi in cika burika na na rayuwa ba, shi din na Mussamman ne bazan gaji da fada."

Farouk ya ce, "alright haka na ke son ji Gimbiyata a ci gaba da hakuri domin kowacce irin zamantakewa sai an hada da hakuri,sannan ki cire damuwa ki dunga hango farinciki a kullum, yanzu mene ne kike shirin yi ko da taimakon da zan iya yi miki?.

Zeeyter ta ce, "Babbar makaranta wacce za ta iya kasancewa kamar jam'i ta wayar da kan mata da maza, ka san muna seminar kuma kullum ci gaba ake samu Alhamdu Lillah da wannan nasarar nake tunanin bude makaranta mai zaman kanta Mussamman da na haɗu da wa innan matasan duk cikinsu babu wanda ya fada wannan sana'ar ason ransa sai da dalili,ina ganin bude makaranta babban jahadi za mu yi."


"Weldone Gimbiyata, Shiyasa kike kara birgeni a kullum, zan yi binciken yadda abun ya kamata ya kasance har ma kudaden da za a bukata in bada nawa gudunmawar daga nan sai a ba Khaleel aikin tsara makarantar ayita yadda kowa da ya gani ta manya ce da kuma abun da ta kunsa."

Zeeyter ta ce , "Thank you Abokin dole kuma abokin fada,sannan abokin shawara kai kam abun naka da yawa fa."

Dariya suka yi dukanninsu sannan suka bige da hira.

Har su Haiydar da Khaleel suka dawo suma aka ci gaba da hiran.

Sai da suka yi sallan isha kafin suka fito da niyar tafiya airport.

Haiydar ne ya dauki motarsa ya kaisu duka.

Suna zuwa bayan zoe ta yi signing sannan ta biya kudi ta dauki jirgin daga hanger.

Haiydar ya rugume Khaleel da Farouk yana, "Misali na abokan kwarai hoton ku kadai ya isa ya nuna ainihin abotar da babu Algus,baki ya yi kadan wajen nuna godiyata gareku, hannu ya yi kadan wajen daukan nauyin ku,ku din na daban ne kuma na musamman ne sannan bangare na rayuwata,ina alfahari da ku har karshen numfashi."

Zeeyter ma ta rungume zoe tana , "Thank you sister, Thank you so much."

Gaɓadaya godiya Haiydar da Zeeyter suka dunga masu har suka shiga jirgin sai da ya tashi kafin suka koma gida.

Suna komawa Haiydar ya yi parking motar cikin xaƙuwa cancak ya dauki Zeeyter.

Wutsilwutsil ta fara tana, "Sunshine mene ne,miye ne wai ka bar ni in taka da kafafuna." Ta fada tana dariya.

Shi ko bai direta ko ina ba sai bedroom .
Yana ajiyeta ya rugumesata yana sheƙan kamshin jikinta.
"Bright Eye ban jin cewa rayuwata zata yi dadi in babu kai, na yi kewar ki Sosai fiye da zatonki."

Dariya Zeeyter tayi tana dukan cikinsa , "Amman ai ba ka yi kewar food ba, tunda nasan ba musu kana ci."


Daga mata rigarsa yyi yana, "ki ga, ki ga yadda cikina ya rame za ki ce ina cin abinci, ni kaina bansan ya nake ba,bare kuma batun abinci, komai ma in zanyi ki sani in kina kusa ne kuma na san lafiyarki,amman indai zan kasance babu ki ina tabbatar miki cewa ba za ataba gane meke damuna ba."

Rugumesa tayi ta ce, "Sorry Sunshine yanzu za a dawo cin food sau biyar arana ko?"

Dariya yyi yana kara kankameta.

"Ina sonka abun sona." Zeeyter ta fada.

Haiydar ya ce, "Da Gaske?"

Dariya tayi tana dukan kirjinsa , "Aa wasa."

Shi ma dariyan ya yi yana kokarin kwantar da ita kan gado.


★★washegari

Suna tashi da safe bayan sunyi wanka sunyi breakfast kai Tsaye police station suka nufa domin an tabbatar masu da cewa an kama ogansu Habun.

Bayan sunje ne ya fara bayani kan cewa shi ma wata 'Yar uwarsa ce ta sa shi ba shi yasa kansa.

Nan take aka ce yaje ya nuna yar uwar tasa,sannan ya kirata awaya ya fada mata cewa yana son ganinta zasu hadu.

Haka kuwa a ka yi.

A motar station din aka sa shi, Haiydar da Zeeyter tare da kuma suna binsu a baya.

Wani kango ya tsayar da su, da mamaki suna shiga wa za su gani ban da Antou.

Jikinta rawa ya fara harshen ta na hardewa, "Baaa....baaa...niiiiiniii ce ba."

Gaɓadaya ta rasa abun fada ma.

Murmurshi kawai Haiydar ya yi ya ce, "Banyi mamaki ba."


A wajen suka kamata kai tsaye aka wuce da ita police station.

Ko da suka je can da bincike ya tsananta ta tabbatar da cewa ita ta ba dan uwanta kwangilar bibiyar rayuwar Zeeyter tun lokacin da ta ji Haiydar ya aureta.
Kuma ba dan komai take hakan ba illa don ta hargitsa masa rayuwa,tayi tayi ta bangarensa ta kasa samun galaba shiyasa ta koma kan zeeyter.

Kulleta a kayi a cell kafin Haiydar da Zeeyter suka yi gaba abun su.

Haiydar gun babansa ya nufa ya masa bayanin komai.

Ya ce ayi duk yadda hukuma suka ce, ayanke mata hukunci daidai da laifinta shi baya da ta cewa.

Deedarth kuwa yana kuka shi ma ya , "ban san cewa tsanar da Antou ke ma da Anty har ya kai ga,ban ji dadi ba don Allah ku yafe mana Yaya,kuma a yanke mata hukumcin duk yadda ya dace.'

Rarrashinsa Haiydar ya yi har ya samu nutsuwa.
Tare da fadin, "Yanzu dai za abarta acen amman batun yanke hukunci ba yanzu ba,nasan ba za ta taba sona ba,amman nima uwata ce duk kashinta."

★★da dare Haiydar da Zeeyter tare da Deedarth suka nufi police station din domin kai mata abinci.

Tana ganinsu tayi tsaki tare da fadin ba ta so.

Ko alamun nadama babu cikin kwayar idanunta.
Haka suka ajiye abinci suka dawo abunsu.

Haka rayuwa ta ci gaba.
Sai da Antou tayi sati guda a cell Haiydar ya je belinta bayan sunyi shawara da 5stars amman sam station din suka ki aminta da hakan domin acewar su kotu ya kamata ma akaita a yanke mata hukunci zaman gidan kasu na shekara ko fin hakan ma.

Da kyar suka amince zata kara sati uku ya zama wata guda hakan ma sai da yarjejeniyar ba ruwanta da rayuwar Haiydar ko Zeeyter inko wani abu ya samesu to za a kamata.

A kwana a tashi har watan ya cika cif

Fitowarta maimakon ta risa sai ƙara tsanar su da tayi abu ɗayane kawai babu halin ta ce zata dau mataki ko kara shiga cikin rayuwarsu.
Kasancewar an kafa mata dokoki masu tsauri tare da masu bibiyarta

★★★rayuwa ta ci gaba da kasancewa cikin aminci da kaunar juna tsakanin Haiydar da Zeeyter.

Da sassafe Haiydar ya tashi ya haɗa masu breakfast.
Zeeyter ta fito tana, "Sunshine ehen yau akwai meeting da sassafe kenan shine baka tada ni munyi kayan break din tare ba?"

Zama ya yi yana, "Na ga agajiye kike yanzu tunda kin tashi kizo muyi break din sai mu fita tare."

Zama tayi tana, "Owk Baby sunshine acici, yanzu haka ma yunwar ka ce ta tadaka."

Ko kulata Haiydar baiyi ba shi dai ya ci gaba da cin abincinsa.

Sai da ya ci ya koshi yana, "Bama zan jiraki ba,byeebyeee na tafi don ke zaki ce sai kin shiga gidan mai." Kiss ya mata kafin ya fita da sauri.

Dariya ta yi kawai tana, "Byeebyee adawo lafiya, daman ba zuwa nake son yi ba yau kam ko naje sai dai in tayaka aiki don ni kam ban da aikin komai."



Haiydar na zuwa suka shiga meeting bayan an gama ya lura ɗaya daga cikin ma'aikatansa babu walwala a tare da shi.

Sai da kowa ya fita kafin ya tsaida shi

Haiydar ya ce, "Sadiq me yake faruwa ne kwana biyu ba ma yau kadai ba don na jima ina ganinka ba walwala."

Dafa kai ya yi yana, "Yallaɓai wlh akwai matsala ne,mata na da matsala Sosai."

Haiydar ya gyara zama, "matsala kamar ya?".

"Matata sam ni da ita ba jituwa ana cewa ana yin aure hankali ya kwanta to ban da ni,tunda nayi aure nake fuskantar kalubale gun matata,na farko bata da tsafta, sannan ban san mene ne tsakaninta da dangina ba sam basa sonta,uwa uba bata iya tarban baki ba, sannan ko ni za ta yi ma magana bata iya magana mai dadi ba, ji nake dama banyi aurennan ba wallahi ayau na kudiri niyar sakinta kowa ma ya huta."

Numfasawa Haiydar ya yi kafin ya ce, "kana da Matsala tana da matsala dan karfe ɗaya baya taɓa amo, amman kafin nan zan haɗata da matata su tattauna kasan yadda suke cewa Matsalar 'Ya mace sai 'Ya mace, sannan kuma kai ma zan baka shawara da ba zama zaka yi kace komai sai mace ta iya ko ankoya mata agidansu ba, a yadda tazo take kazantar nan,nuna mata baka so cikin shigar laluma in taki ganewa nuna mata yadda za ta yi da kanta,kumq cikin magana ta ce kaza da baiyi maka ba, cikin dariya ka ce aa ba haka yakamata kice ba ga yadda zaki ce,kuma in anyi baki da Fara'a ake tabarsu ibo masu ruwa yi masu kaza ka dai gane,gobe ai babu office ko,zai fi kyau ka kawota gidana inda hali."

Har ƙasa Sadiq ya rusuna yana yi ma haiydar godiya.
"Tabbas Yallaɓai ko a haka ka barni ka haskaka mun duhun da nake ciki,a tunanina tasan komai da zanso kuma tasan yadda zata yi komai,na manta da cewa lallai koda ta sani akwai bukatar tunin yadda nake so kuma nake buri."

Murmurshi Haiydar ya yi.
"Kar ka yi mamaki innace ma Ni kaina wasu Abubuwan agun matata na koya, na tabbata in matarka ta kasance da Zeeyter za ka ga chanji in sha Allah."

Godiya ya kara yi masa sosai kafin ya tafi Office dinsa.



Haiydar kuwa yana komawa gida ya sanar da Zeeyter komai
.ta ji dadi Sosai a lokacin take sanar da shi kan batun makarantar da suka yi ita da Farouk.

"ma sha Allah gaskiya da kun taimaka domin irin wa innan kanananun matsalolin ba karamin kashe aure suke ba,nawa ne albashhin nima adauke ni aiki Hajiyata?"

Dariya Zeeyter ta yi ta ce, "yoo kai kam indai zaka masu lectures ai ba mu da kudin biyanka,dazu muka yi waya da karamin miji Deedarth ya ce in gaidaka."

"Oh ni ba zai kirani ba yana skul sai dai ke wato ni agaishe ni to ban amsa ba."ya fada yana tashi.

Dariya Zeeyter ta yi, "in ya kirani ai kamar kai ya kirako."

"Dadin baki dai kawai." Haiydar ya fada yana shigewa daki.

★★washegari Zeeyter da wuri ta fara shirye-shiryen zuwan sadiq da matarsa ita da Haiydar suka fara yi masu girke-girke.

Misalin karfe biyu kuwa sai gasu sunzo.

Tun daga kallon haiydar da Zeeyter cikin shigar da suka yi ya tsurar da sadiq tare da matar shi surayya.

Riga ne da wando wanda deejerh ta yi masu duka iri ɗaya ba karamin kyau ya masu ba.

Tare suka fito Zeeyter ta rugume surayya tana welcome, Haiydar kuma ya mikawa sadiq hannu suka gaisa.


Suna shiga sai faran faran Haiydar da Zeeyter suke yi da su gwanin sha'awa.
Suka ci abinci duka tare kafin Haiydar ya je sadiq dayan falon suka bar Zeeyter da surayya a tare.

Zeeyter ta ce, "Kawata,kar ki boye mun komai kinji zan miki wasu tambayoyi ne."

Surayya ta ce, "To In sha Allah Anty."

Zeeyter ta ce, "in Yan uwan mijinki suka zo kina basu abinci? Kina sake masu fuska kuma kina masu kyauta?"

Girgiza kai tayi tana , "Aa basa sona kuma nima bana sonsu ko sunzo sai dai in fita in bar masu ɗakin yanzu ma sun daina zuwa ."

"Subhannallahi wannan ba ɗabi'un matar kwarai bane, ko da ace da gasken basa sonki bai kamata ace ki nuna bakya sonsu ba, inda hali ma ki nuna masu cewa tamkar yan uwanki na jini suke,ki jasu a jiki, ki nuna komai naki zaki iya basu baki damu da su soki ko aa ba,ke kina kaunarsu saboda Allah kuma saboda soyayyar da kikewa mijinki,bai zama lallai su soki ba,amman hakan kadai zai iya cetonki,nuna masu cewa kema baki da mutunci ba naki bane ."

Surayya ta numfasa tana kokarin yin magana.
Zeeyter ta ce, " tsaya tukuna in gama,akwai wani abu muhimmi da mata muke mantawa da shi wanda shi ke kara mana daraja a idon duniya da mazajenmu,wato tsafta ki kasance cikin tsafta tare da tsaftace muhallinki babu wanda ya isa ya rainaki ko da kuwa ya fiki a komai,jikinki kamshi,gidanki kamshi,dakinki da gidanki a gyara wannan ba karamar daraja ba ce, sannan ki kasance mai tauna kowacce irin magana abakinki kafin ki fito da ita zahiri,ki kasance mai sanyi da sanyaya rai ga duk wanda zaki Kasance da shi."

Surayya ta ce, "Na gode sosai Anty kuma In sha Allah zanyi amfani da duk wani abu da kika ce,tun daga shigowata gidan nan kuka birge ni Wallahi."

Zeeyter tayi Murmurshi, "kina so ku zama kamar mu?"

Surayya ta ce eh

"To kiyi duk abubuwan dana fada miki sannan har cikin jikinki ya kasance a tsaftace da gyara in sha Allah sai kun fi mu ma."Zeeyter ta fada.

Tsabar dadi rugume Zeeyter tayi tana kara yi mata godiya.

Hira suka sha sosai.
Har yammata tayi zasu tafi.
Zeeyter ta bata kyautan turaruka na jiki da na kaya masu kamshi.

Daga ita har sadiq din ban da godiya ba abun da suke yi

Tun agidan suma suka rugumi juna tare da ba juna hakuri.


Sun juya kenan zasu shiga gida Zeeyter ta hango ƙadangare.

Ihu tayi tare da kankame Haiydar tana, "Sunshine shine zai hau mun jiki."

Dariya Haiydar ya yi yana, "Ysn ki bini a sannu ko a tuna baya."

Bayansa ta ɗane tana, "Sorry mu tafi."

Dariyar Mugunta yake yana kokarin kaita gun.

Da tayi wata ƙara Dariyar ya kara kafin ya shige da ita ciki.

Suna shiga ta dau filo tana binsa da gudu yana gudu suna zagaye falon.

Sai da ya gaji ya tsaya yana numfashi, "YEL kina sona?."

Da gudu ta karaso ta rugumesa tana, "Da yawa ma,amman da fa bana sonka."

Dariya ya yi ya ce, "nima da ai haushi kike bani, Amman yanzu duk wanda yake jin haushinki nima haushinsa nake ji, za mu rayu har karshen numfashi in sha Allah ke ce hasken Rayuwata."

Karshe
Alhamdu Lillah
Alhamdu Lillah
Alhamdu Lillah
Anan na kawo karshen wannan littafin Allah ya bamu ikon amfana da abun alkairan ciki.
Allah hanemu ga aikata sabonsa.
Allah mun tuba ka yafe mu🙏🏼🙏🏼


Kamar yadda nayi alƙawarin fadin maanar YEL a karshe zan fada in sha Allah yanzu.

*Phoenix* shine asalin sunan da indiyanci kuma *YEL* Sannan Yel na nufin tsuntsu ne mai ban sha'awa da ke rayuwa a cikin tsuntsuyen garke,yana mutuwa duk bayan Shekara dari biyar sannan ya kuma tashi daga toka, rayuwar tsuntsun tamkar irin rayuwar Zeeyter ne, sannan wannan tsuntsun na taimakon ta saboda ɗabi'un su da suka Kasance ɗaya,in ba a manta ba ata farkon labarin Lokacin da aka kafar mata da ƙafa tana cikin addu'a wannan tsuntsun ta gani har kafar ta sake,haka kuma ta zana shi a takarda ba tare da tasan abun da take zanawa ba zuciyarta kawai take bi Kawai saboda ya zama bangare na jikinta🥰🥰


*DOMIN SHARHI KO TSOKACI,KU TUNTUƁENI:*

08103080717

Urs Xayyeesherthou

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment