Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi magana ba.

Sai a lokacin Haiydar ya yi magana, "Za mu tallafa maku ta dukkanin bangarorin da kuke bukata sannan muna bukatar yin haɗin gwiwa tsakanin companin mu da naku, amman da sharadi in in mun tallafa maku zai kasance kowacce shekara muna share namu da za ku dinga fitar wa,ba mu za ku bawa wasu wa inda suke ƙasa da ku zaku tallafawa,Ko gidan marayu ko ma dai ya,yadda kuka so kawai ya kasance kun tallafa wa masu karamin karfi dai kamar dai yadda muka maku, ba ƙasa ɗaya ba kowacce ƙasa a fadin duniya ba a zaɓe guda ba, in dai kun aminci za ku sanya a hannu komai ya kammala da ikon Allah."



"In sha Allah hakan zai kasance ba ma da matsala awannan bangaren da ikon Allah mun yi maku alƙawari."
Zeeyter ta fada.

Halliru ma ya ce, "In sha Allah Godiya mu ke."


Ana ta jawabi ban da Farouk da ya ƙurawa jikin Zeeyter idanu ko kiftawa ba ya yi.

Suna haɗa ido zata galla masa harara sai ya saki murmurshi yana wani tanɗe baki.

Takaici ne ya isheta ta matsar da kafarta inda yake ta take shi,ga shi daman takalminta irin mai karfinnan nan.

Saukar ihu kawai aka ji Farouk nayi.

Dariya Zeeyter tayi tana, "mene ne ya faru?"

Dukansu suka ce meya faru.

Shafa kai ya fara yana, "Nothing Oh Oh Bege kafa na yi."


Kallon shi ya kara yi kafin ta kyalkyale da dariya.


Drinks din suka sha kafin aka kawo fefofin Zeeyter ta yi signing , Halliru ma ya yi sannan Su Farouk, Haiydar, Zahra, Deejerh da Khaleel su ka yi .


Rabuwa suka yi cikin aminci da karamci tare da batun za su kara nemansu ko awayane inda wani abu sannan za aje aduba companin.


Fita suka yi ,har sun hau nafef suka ga mai nafef ya tsaya cikin mamaki Zeeyter ta ce,"ya zaka tsaya kuma, lafiya?"

"SORRY,Kun manta da file din ku ne." Cewar Haiydar yana mikawa Zeeyter.


Karba ta yi ta ce, "Ayyah Mun gode."

"Welcome." Ya furta kawai sai ya tafi.


A hanyar su na tafiya su ka dunga karo da yan shaye-shaye duk sunyi mankas, duniyar tunani Zeeyter ta fada, "Shin meke janyo shaye-shayen nan? Me yasa matasa suke ruguza ganin Rayuwar su ta wannan hanyar."

Ta tafi duniyar tunani har sun iso bata sani ba.

Halliru ne ya ce, "Madame mun iso."

Juyowan da zata yi taga wani karamin yaro da ba zai wuce shekara goma sha hudu ba, dauke da sigari yana sha, cikin sauri ta fita a nafef din ta, ta dalla masa mari...


Urs Xayyeesherthou
08103080717
[5/29, 9:23 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-11*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

_*Allah ya ba mu ikon aiki da abun da muka rubuta kuma muka karanta🙏🏼 Allah ka cire mana son duniya hassada da kyashi, Allah ka bamu ikon jurewa duk wani ƙalubale da xa mu fuskanta na rayuwa🙏🏼 Allah kasa mu kasance masu kyakkyawaar fahimta da fata na gari ga kowa🙏🏼*_



"Mene ne kake haka? Ba ka san rayuwarka ne? Ba ka san illarsa bane ? Meyasa kake son ɓata rayuwarka da duk wani makusancinka?,wannan ba rayuwa ba ce mai kyau,kuma ba rayuwar nunawa ba ce, kai baka jin kunya? A cikin mutane ma ka ke sha? Subhannallah." Ta karasa maganar tana dafa kanta.

Rike kumatunsa ya yi kawai ,kunya ta kama shi ya ma kasa magana kwata-kwata kallon kasa kawai yake.

Jan hannunsa ta yi bata dire ako ina ba sai cikin gidanta.

Ruwa mai sanyi ta ba shi sai da ya sha kafin ta zauna gefe kusa da shi.

"Me Sunanka?"

"Yusuf." Ya fada jikinsa a sanyaye.

Murmurshi ta yi kan ta ce, "Kana jin yunwa?"

Shiru ya yi bai ce komai ba.

Ta kara magana
"Kana jin yunwa? Ka fada mun ka sake jikinka ni fa kawarka ce ko nama girma ne?Maintenant si tu veux on peut jouer au football (Yanzu sai in tashi mu buga kwallo in kana so)."

Maganar da ta bashi dariya ke nan ya sake.

Abincin ta zubo masa nan take ya cinye tas tamkar mayunwaci.

"Yawwa Yusuf ko kai fa to fada mun Me yasa ka ke shaye-shaye?"

Idanunsa ne ya cicciko ya ce, "Anty ba abinci muna da yawa a gidanmu ba abinci ba makaranta, ba komai kullum da yunwa muke kwana,ba komai ba ma da komai."

"Ina babanku? sannan ku nawa ne a gidan."

Yusuf ya ce, "Babanmu ya tafi kasar waje aiki,kuma baya dawowa sai bayan wata Biyar ko shida in ma yazo baya sati ɗaya yake komawa,kuma mu takwas ne Nine babba sai kannena."
Maganar ya karasa yana hawaye.

Tausayin sa Zeeyter ta ji har cikin ranta zuciyarta na sosawa tare da yin Allah wadai da Wasu Iyaye mazan masu haihuwar gaba gaɗi ba tare da damuwa da abincin su ba,tufafinsu ko makarantar su ba,bare kuma tarbiyarsu, haka kuma su bar 'Iyaye mata da wahala.

Share masa hawayen ta yi kafin ta ce, "Kana son ka yi karatu?"

Da "eh." Ya amsa cikin zakuwa.

Murmurshi ta kara sakewa tana, "Za ka yi karatu In sha Allah Yusuf har sai ka sanya wasu ma sunyi, tom yanzu fada mun da su waye kuke irin shaye-shayen nan?."

"Abokai na ne, mu goma ne."cewar Yusuf.

"Za ka kaini inda suke, sannan daga nan muje gidanku?" Zeeyter ta fada tana kallonsa.

Girgiza kai Yusuf ya yi alamar "Eh."

A jiye jakarta kawai ta yi suka fita, wajen da abokansa suke rabewa wani kango ya fara kaita, kallon mamaki ta tsaya yi masu domin duk acikinsu ba wani babba,ba za su zarce shekara goma,sha biyu zuwa sha hudu ba.

"Irin wannan ne in sun girma suke zama babban matsala ga ƙasa , kashe-kashe,sace-sace,fyade wa yara mata, Allah ka kare mu ka tsare mu ka bamu ikon kubutar da yan uwanmu." Abun da Zeeyter take sakawa aranta ke nan.

Shiga cikinsu ta yi suka zauna cikin wasa da dariya kowanne ta ji damuwarsa daga wanda ke zaune agun kishiyar uwa, sai wanda Mahaifinsu ya tafi ya barsu, wasu kuwa suna tare da duka iyayen amman ba a damu da tarbiyarsu ba, wasu almajiranci aka turosu ba tare da sanin inda suke ba.

"To amman a ina kuke samun kudin da kuke siyan wa innan abubuwan?." Cewar Zeeyter tana daga wata gora agun.

"Zuwa muke mu dibo kudi in mun ga an ajiye."karaf Yusuf ya fada.

Bude baki ta yi tana, "Iyee? To ba kyau daga shan abun da kuke har daukan kudin da ba a baku ba in kuna yin hakan tabbas babu makawa za ku shiga Wuta."

Ba karamin tsoratar da su tayi ba akan shaye-shaye da satan kudi.

A karshe ta tambayi kowa abun da yake so

Wasu cikinsu suka ce makaranta wasu suka ce aiki, wasu kuwa burinsu kawai su girma su zama Jami'an tsaro.

"In dai Ina Raye kuma ina numfashi sannan ina karfin da zan taimaka maku wajen gina rayuwarku za ku zama abun kwatance nan gaba."

Zeeyter ta fada tana Murmushi.

Ba karamin Dadi yaran nan suka ji ba, sai da tasa suka zubar da duk wasu miyagun kwayoyi tare da yi mata alkawarin ba za su kara kusantar sha ba.

daga nan gidansu yusuf suka je.

yadda zeeyter ta fara cin karo da kanun yara wanda a kalla ba zaifi ratan shekara guda guda ba suka bawa juna, da ganin mahaifiyar karamar yarinya ce amman wahala ya sa ta tsufan dole.

Arazane ta ce, "Yau kuma wa ce maganar ka kwaso mun Yusuf? Don Allah ya ka ke so in ji da rayuwata da rikicin kannenka ko kuma naka?"


Zeeyter ta ce, "Oh oh kwantar da hankalinki bai yi komai ba."

Wajen zama ta bata tare da ruwan sha, nan Zeeyter ta fara mata bayanin komai yadda aka yi ta ga Yusuf da kuma dalilin zuwanta.

Kuka mahaifiyar ta fara tana,"Ban san ya zan yi da su ba." Ta karasa maganar tana hawaye da nuna yaran.

"Da kuruciyata an durkushe ni anmun auren dole an aura mun wanda bai san darajar 'Ya mace ba sai biyan buƙatar shi kawai,a kullum burinsa bai wuce yazo ya mun ciki ba ya tafi, inya dawo ya ga yara ya tambaya sannan ya kara gaba, na kan ji cewa tamkar in kashe kaina,amman inna tuna da Yaran nan sai jikina ya mutu,ina rayema rayuwar su na kokarin tarwatsewa ina ga na bar duniya?"


Zeeyter ta nemi bayani sosai dangane da rayuwar matar da 'Ya'yanta kuma ta samu bayanai masu gamsarwa.

Washegari
Gabadaya Zeeyter ta tattaro yaran nan ta kai su makaranta kowanne ta biya masa, almajiran ciki sai da ta nemi izinin malamansu kamar yadda ta nemi izinin masu iyayen.


Sannan kowannen su ta ce ana tashi daga skul suna zuwa Zeeyter Oil And Gas ta dauke su aiki.

Daga nan kuma ta koma gidansu Yusuf ta kai masu kayan abinci da kayyayyakin sawa, a karshe ta sanar da mahaifiyar cewa zatana basu kayan abinci duk karshen wata in sha Allah, sannan ta bata jari kan cewa ta kama karamar sana'ar da zata iya.


"Kar ki manta duk sanda yazo gari a sanar dani." Cewar Zeeyter tana fadawa Maman Yusuf kan cewa duk sanda mahaifin Yusuf ya zo gari a fada mata .

Ta ce"In sha Allah Madame in yazo zan tuntuɓeki mun gode, Allah ya saka da Alkairansa."

Komawarta gida har Madam Naddja taxo sun fara lesson da yara.

"Madame Sannu da kokari yau anyi nisa bana nan Afwan ban sanar ba." Cewar Zeeyter.

Madame Naddja ta ce, "Oh kar ki damu ai nasan uzuri ne ya kamaki."

,"eh Madame in kin gama ma ina so muyi wata magana." Zeeyter ta fada tana zama a kasa.


Madam Naddja ta ce, "Ok yanzu zan sallame su daman."

Tana Sallamarsa Zeeyter ta fara magana, "Madame ina bukatar wa'inda za su na wayar da kan al'umma kan ilolin shaye-shaye, matsalolin ma'aurata,zaman banza har ma da zamantakewa,in da zai yuhu ina so in dunga haɗa taron wayar da kan Al'umma duk bayan wata guda zuwa biyu haka ko uku."


"Ma sha Allah zainab kin yi tunani mai kyau kuma a halin mu da muke ci ki al'umma na bukatar taimako ta kowanni bangare, ciki kuwa harda tunatarwa da wayar da kai, indai hakan zai kasance In sha Allah nayi alkawarin tayaki tsara komai ko da ina office ne zaki iya zuwa,sannan zan samo wa inda ya kamata muna gayata ,wa inda suke da labarin ba dawa cikin al'umma mai cike da tunatarwa tare da fadakarwa uwa uban kuma wayarwa."


Da haka suka yi sallama da Madame Naddja ta tafi Office.

Gidan zama tayi agida ba tare da ta je gidan man ba, kasancewar tana da aiki sosai na ɓatattun kayan wuta, TV, generator,Har da wasu kwayayen Wutar lantarki , da in suka ɓaci ake zubarwa sai ta tsinto ta zo ta bude shi ta ciro wayoyin wa inda ya kone ta yanke,ta haɗa har sai ya gyaru, ta saida masu a kudi kalilan sabanin sabo da wasu basa da halin siya.

Aiki ta sha sosai Mussamman generatorn wani mai chajin waya sai da tayi falla falla da shi ta ta ciro ma zubin Petrol din (Tank) da ya kuje,ta masa walda da wuta ,ta goge shi tas kafin ta maida komai.


Tana gama gyaran da kanta take bin kowanne wajen aikinsa ko gida ta basu sannan su biyata.


Tana gama kai masu kenan zata gida ta ci karo da wani makwabcin sun.

"Zeeyter nemanki nake daman ina shirin zuwa gida, na ce wutar lantarki nake so amman ta hanyar sata yadda baza agane ba." Cewar shi.


Zeeyter ta ce, "Ok ba matsala amman sai zuwa dare, ka san ba dama yin wannan aikin da rana."

Dariya ya yi, "Madame Zeeyter da girman kujerarki,ba matsala sai kinzo."


Direct gidan abinci ta wuce domin aiki.


★★★zaune suke dukkaninsu a makaken falon Haiydar.

Khaleel ne ya yi gyaran murya, kasancewar kowa ya sa waya agaba ana dannawa.

"Hey Friends Ina da magana fa,ko in ce ina da shawara, I need Ur Attention Please."


Ya karasa maganar yana gyara zama.

Dukkaninsu juyowa suka yi tare da bada hankulansu gare shi kamar yadda ya bukata.

"Muna da matukar bukatar Zeeyter Oil And Gas, ba iya wannan kasar zai taimaka ba har karsa shen mu so akwai bukatar samun kyakkyawaar alaka tsakani ba wai zallan hadin gwiwa ba, yanzu batun nan ba nijar kadai zai tsaya ba kafatanin faɗin duniya da bukatar mu nuna masu, ba zan boye maku ba tsarin su da yadda abun ke tafiya ya matukar kayatar da ni duk da cewa ba mu je mun gani ba,amman wannan mai sauƙi ne,nayi wani tunani da watakila xaku yi mamaki watakil kuma ba xa ku yi ba, yanayin yadda kuka fahimci maganar shine amsarku."

"Akwai bukatar kasancewar wannan yarinyar cikinmu ne gaba-daya ba wai companin ta ba kadai, Haiydar." Sai kuma Khaleel ya dakata da magana.

Numfasawa ya yi kafin ya ci gaba da magana, "Haiydar akwai bukatar ku kulla alaƙa da yarinyar nan, ba alaƙa kawai ba, alaƙa ta rayuwa a tare, Aure."

Khaleel na kai wa daidai nan da batunsa gaɓan Farouk ya yi wani mummunan faduwa.

Haiyar kuma suman zaune ya yi, "What? Ni? Kuma Aure? Like? Wannan yarinyar." Nan take wata irin zufa ta keto masa.

Cike da Mamaki Zahra ta ce, "Oga Ka san me ka ke cewa kuwa?"

Khaleel ya ce, "Eheen ni nasan me nake fada kuwa."


Haiydar ya tashi yana, "Never ba zai yiwu ba."

Farouk kuwa ya kasa magana zuciyar sa ce kawai ke bugawa tare da Haiydar suka fita a falon kowanne ya shige dakinsa cikin wani yanayi.


Deejerh kawai kallonsu take ta ma rasa abun fada.

★★
Dare misalin karfe 9:00pm Zeeyter ta dauki jakar kayan aikinta domin zuwa yi ma makwabcin su aikin da ya sata.

Tana zuwa a kasa ɗani,tamkar tsuntsuwa ta haye ko dauyin jikinta bata ji sam.

Gyaran ta fara cikin sauri har ta kusa kammalawa kamar daga sama sai ga folisawa cikin gidan sun zagayeta



_*Ina kuke masu so a tallata masu hajarsu ? Ku marmatso kusa ku zo domin a tallata muku cikin farashi mai sauki ku tuntuɓeni ta number da ke ƙasa*_

08103080717

Urs Xayyeesherthou
[5/29, 9:23 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-12*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim




Tsayawa tayi tana kallonsu da mamaki kawai sai ta fara dariya..

"Ah Mun yi miki kama da abun dariya ne ko? Téléchargez ou nous le téléchargerons (ki sauko ko mu sauko da ke)."


Cike da Isa Zeeyter ta ce, "Laisse-moi finir Ah. (Ku bari in gama mana Ah.)



Cikin zafin rai wani acikin su ya ƙara magana, "
Voulez-vous descendre ou allons-nous vous déposer ? (Za ki sauko ne ko sai mun jefar da ke?)"



Wani irin kallo ta masu ta ci gaba da aikinta.

Ganin sun fara girgiza tsanin da take kaine yasata yin wani masifaffen tsalle kamar birin da ya ga ayaba.

Dira ta yi ta wajen katangar kan ka ce miye ta fara gudu, bazuwa su ka yi, suka fara binta.

Sai da tasa suka dunga karade bobiel cikin dare lungu da lungu saƙo da saƙo.

A jigace wani police ya ke fadin, "Don Allah ku barta wannan 'Ya sai ka ce mayya ko Aljana har ta fimu gudu, ba zan iya ba wallahii."


Sauran kuwa ban da nishi ba abun da suke sun ma kasa magana.

Cikin tsawa ɗayan ogan su ya ke bada umarnin su ci gaba da binta sai an kamata.

Ai kuwa haka ta ci gaba da wahalar da su kusan awa guda sai da ta gaji ta tsaya tana nishi , "Je suis Fatigue,Je suis Fatigue,Je suis Fatigue, (na gaji, na gaji na gaji), ku tsaya mu huta sai a ci gaba ta faɗa tana dariya.

Dukkaninsu ban da nishi ba abun da suke da wayo suka zagayeta duka yadda ba halin gudu.

Tana hutuwa ta ƙara numfasawa da kokarin gudu da sauri wani ya cafketa nan take ta gantsara masa cizo a baki, wata irin hargitsattsiyar ƙara ya yi, ganin hakan yasa su haduwa duka suka sanya mata ankwa da kyar aka tafi station din, kusan dukkanin su sai da ta ji masu rauni.

Suna isa station din suka wurga cikin sel sai da ta fasa kai.

★★★Farouq na shiga ɗaki wani irin zazzaɓi ne ya damƙesa da ya rufe ido surar Zeeyter kawai yake hangowa.
Tsaki ya yi azahiri yana faɗin, "Why Khaleel? Why? I said Why na fi shi buƙatar ta,ina da bukatar Sosai fiye da kowa, tana da yanayin da nake so,ina da burin Kasancewa da ita,zan so ace ka da Haiydar ya aminta kamar yadda ya nuna yanzu, ina da bukatar ta sosai." Wannan sambatun Farouk ya ta yi shi kadai aɗaki ya na dafa kai.


Haiydar kuwa dan takaici ya ma kasa tunano yadda yanayin Zeeyter yake,ji yake tamkar an daura masa wani dutse a kirji, nan da nan wani zazzafan zaxxabi ya lulluɓe shi, maimakon shan magana fridge ya nufa ya dauko giya ya fara sha.

Meenoh ce ta shigo da sauri ta rungume shi tana fadin, "Baby i miss You uhum umm."

Cikin zafin rai ya ja ta gefe yana fadin, "bana bukatar kowa, bana son ganin kowa anan ki fita, i said you should getout,get out." Ya karasa maganar da karfi yana nuna mata kofa.

Jikinta ne ya yi sanyi ganin yadda bai saba yi mata ba, a hankali ta fice tana kallon shi.

Dake ta kofar baya wanda zai sada ta da dakin Haiydar driect ta shiga har ta fita su Khaleel basu sani ba.


★Deejerh ta ce, "Me zai sa ka ce haka ne wai? Na rasa gane Dalili, ka fi kowa sanin cewa Haiydar baya son Aure,kuma ko da zai yi auren ma bai ka mata ka ce wannan ba."


Murmurshi Khaleel ya yi ka fin ya ce, "Ka da ki duba siffar mutum a komai na duniya in za kiyi kina cire suffa a ciki, abu mafi mahimmanci ya kamata muna lura da su, kwakwalwa, basira, kaifin tunani ,hali, kyakkyawaar zuciya da kuma ilimi, So wannan bana so muyi magana kan siffarta,yanayinta,ko yanayin shigarta ,tunda duk ba mu san su ba, Amman magana ce za mu yi kan basirar ta da take afili fiye da komai, am telling watarana za ku fahimci in da na dosa, amman maganar cewa Haiydar ba ya son aure ta kau, ba wai kan shi zaiwa auren ba,kasuwancinmu ne, kin ga kuwa ko su dauki juna Matsayin maaurata ko akasin hakan wannan ba damuwarmu bane as fer as suna tare kawai ya wadatar shi ne abun da na ke bukata."



Zahra ta ce, "Amman to shi Farouk me ya sa shi tashi anan bayan ba shi aka ce ba, ko hakan da wata matsala ne a bangaren sa shima."

"Nop kar ki damu da Farouk ta yuhu shi ma tunanin sa irin na ku ne." Cewar Khaleel.


Deejerh ta ce,"Business MARRIAGE."


"Yap." Cewar Farouk.


Zahra ta yi murmurshi, "Ko ma yane Allah zaɓa mafi alkairy shi ne burinmu."

Dukansu suka amsa da Amin

Deejerh ta tashi tana, "Gudnyt,ina so ƙarasa designing wani wando kafin in kwanta."

"Owk byee." Cewar Khaleel da Zahra.

★★A station din Zeeyter ta kwana karfe biyar dai-dai lokacin sallar asuba na yi ta tashi tana jijjiga masu karfen da ke kofar.

"Ke wai yane? Miye za ki dame mu ki hana mu barci,ki mana shiru a wajen." Cewar wani kofir dake shingiɗe akan kanta .

Zeeyter ta ce, "Na ce ko ba ku ga Lokacin sallah ya yi bane ko kuma ba kwa yi?"


Tsaki ya yi yana, "na ce ki mana shiru ko?".

Ƙara buga karfen tayi da karfi tun yana shareta har sai da ya gaji yazo ya bude mata tayi alwala ta yi sallah.


Gari na wayewa aka dauko file dinta.

"Ke wai anya mace ce ma kuwa? A manta ma mutane?" Cewar Dpon da take zaune gabansa.

"Eheen ni Mutum ce mace kuma kamar kowa amman Mai daraja,kuma cikakkiyar ma ce." Zeeyter ta fada.

Ya gyara zama yana mamakin yadda take magana ya ce, "Me ya sa kike aikin wutar lantarki? Kuma kina 'Ya mace?"

"Ya mace ba mutum ba ce? Kuma bata isa ta yi kowacce sana'a ba domin dogaro da kanta? Ko kuwa an ware wa mace iya sana'ar da zata iya ne aduniya?" Zeeyter ta fada tana kallonshi cikin sigar tambaya.


Ya ce"Amman meyasa kike wannan aikin da kika san bai kamata ba,ta hanyar sata?"

Murmurshi ne ya bayyana afuskarta ka fin ta ce, "Domin talakawan da basu da karfin biyan kudin Wutar lantarki, da ace za a saukaka kowa ya biya daidai karfinsa da ba zan yi ba,ba zan fasa zuwa ba indai za a kirani in janyo su biyani daidai karfinsu, in dai ina numfashi kuma ina guri in sha Allah ko da makiyi na ne ba zai yi kuka ba."



Shi ma Murmurshi ya yi ganin irin karfin gwiwarta da yadda take magana cikin izza, "Na ji,amman kin san cewa za aci ki tara bisa kamaki da mu ka yi kan bin mummunar hanya, sannan kuma dole za ki daina."


Gyara zama tayi kafin ta ce, "na dau na farkon amman ban dau na biyun ma,domin indai ba a sauya ba,nima ba zan taɓa sauyawa ba."



Miƙa mata takardun ya yi kawai tayi signing tare da kashedin za ta kawo masu kudin da suka ci tarar ta da kanta.


Sai lokacin da tazo fita ta tuna da buguwar da kanta ya yi, wani irin ciwo ta fara ji, dafe wajen ta yi da hannu.

Bata wuce gida ba sai da ta shiga wajen wannan maƙocin nasu.

Ta ci sa'a kuwa yana gida zaune suke da iyalinsa suna karyawa, bata ko kula kowa ba, ƙara sawa gare sa tai ta falla masa wani danƙareren mari ta fice ta barsu da mamaki musamman shi da ya yi summan zaune da hannu a kumatu .


Gidan marayu ta fara shigewa kananun yaran suka fara yi mata oyoyo, Madame Ayshe na ganinta da ciwo a goshi cikin damuwa ta karaso gareta
"Mene ne ya same ki."

Kallonta tayi ta ce, "Barka da Safiya Mammah bigewa nayi a station."

Ba ta ce komai ba ta tafi ta dauko ruwan zafi sai da ta gasa mata wajen sosai ta wanke duk jinin da ya bushe.

★Zahra na gama yi masu break kamar kullum amman ba wanda ya fito hakan yasa ta yi masu Noking kofa.

Khaleel ne ya fara fitowa yana mita, "Oh Oh Madam ba za ki bar mu ,muyi barci sosai ba dai."

Farouk kuwa kokarin yadda zai boye kuncinsa ya yi ya fito yana Murmushin da za ace da babu gwara babu dadi.

"Weldone Madam an gama Food din kenan." Cewar Haiydar yana dariya wanda sam ya manta ma da wani batu na jiya.

Zama suka yi suka fara break din bayan sun kammala Deejerh ta ce, "Eheen ina tunanin yaune ya kamata kuje ku duba gidan man a fara aikin gyara shi komai ya kammala tunda saura mana kwanaki kadan mu bar kasar."

A lokacin Haiydar ya tuna da batun zuciyarsa ta canja gabansa ya yi wani irin mummunan faduwa.


Khaleel ya ce, "Oh Yess hakane ,ni da Farouk za mu je an jima, Madame zahra a sanar da su zuwan mu."

"Ok." Zahra ta amsa.

Tashi awajen Haiydar ya yi, kasancewar ya ji cewa ba zai ma iya cin abincin ba ya koma kan kujera ya zauna.

Khaleel ne ya bishi ya zauna kusa da shi kafin ya ce, "Abokina, na sani, na san damuwarka amman ina so ka ajiye su agefe ba don komai za ka yi auren nan ba sai dan kasuwancinmu, ka cire komai arai ka zauna ka yi tunani and ita ma yau nake so mu tattauna batun da ita in munje, Don Allah ka yi tunani kar ka ce Aa ka mun wannan alfarmar."


Da haka suka tafi company kan cewa zaiyi tunani tukunna.


Misalin karfe 4:pm ta nufi gidan man dai-dai da lokacin zuwan su Farouk, kallon yanayin kauyen suka tsaya yi

*Ana hakuri da typing errors ba editing🤭*


08103080717
Urs Xayyeesherthou
[5/29, 9:23 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*,

Please Login or Register in order to submit comment