Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duka." Wanda take cewa Baby ya fada yana kai mata kiss a fuska.

"Mun Gode Anty, Allah kara arziki mai albarka,Anty muna sonki da yawa kinji." Cewar Jumy tana shagwabe fuska.

Booboo ya ce, "Anty ni nafi sonki kin ji, Ki mana alƙawari ba za ki bar mu ba."

Murmurshi ta yi tasa hannunta a kasa tana" kowa yasa na Anan to."


Dukansu suka sa hannayensu.

"Yeeeeeeeee." Suka fada a tare

Ta ce, "Ina Tare da babies dina, Nima ina Sonku kunji Sosai."



★★kiran Khaleel Madame Ayshe tayi awaya cikin kankanin lokaci kuwa yazo dauke da takardun yarjejeniya.


Ko da yazo tsintar Zeeyter ya yi tana durkushe wujiga-wujiga da uban kayan wanki.
Ko lura da shi ba ta yi ba ya shige cikin gidan.

Kan su fito shi da Madame Ayshe ba Zeeyter ba labarinta sai kaya a jibge.

Massalaci suka yi kai tsaye nan Madame Ayshe ta ma liman bayanin komai, khaleel ne ya zama waliyin Haiydar, Liman ne na Zeeyter da sauran mutanen masallacin nan take aka daura aure abisa sadaki dubu Dari Biyar.



Amarya kuwa ta bazama can cikin gari kamar an tsikareta bata ma san meke faruwa ba.

Tana cikin tafiya

Hango bishiya tayi acikin wani gida, da sauri ta shige gidan, tana ganin
bishiyar mangoro ce ta karasa tana tsalle tsallen kokarin tsinka, Amman sam ta kasa tsalle tayi kamar biri ta haye kan bishiyar.

Wani tsoho ne ya fito daga cikin gidan yana masifa, "Waye ne? Wace mara kunyar ce kan bishiyar nan." Da wata ƙatuwar sanda a hannunsa.

Tsilif ya fara kokarin maka mata

Aguje ta sauko,aiko tana saukowa daidai da lokacin da ya maka mata sandar a duwawu.

Faduwa tayi sai da ta fasa baki da goshi.

Amman hakan bai hanata daukan mangoron ta zura aguje ba.


Kafin ta isa gida goshi da baki sunyi suntum kamar balon balo.


Harira da Hurera na hangota tun daga nesa mai za su yi ban da dariya.


Harira ta ce, "Kambala'iiiiiiiiiii yau kam Mutuniyar ta taro inda aka fi karfinta kin ga yadda Goshin ya yi kuwa kamar turela, bakin kuwa sai kace famfas din yara ya cika da kashi."

Ta karasa maganar tana shekewa da dariya.

Hurera ta ce, "Wallahi naji dadi Allah ya kara watarana ma Allah sa a cire mata kafa ko hannu ke ina ga ma fa abun malamin can ne ya fara aiki."


Harira ta ce, "Tabbas ba shakka da walakin goro a miya ga shi har kamaninta sun fara canjawa fa, ke tsaya ma ni fa naji wani kishin-kishin wai an daura mata aure?"


Zaro ido hurera ta yi tana, "Au me? Kar ki ce mun wannan matsiyaciyar har ta riga mu aure, yarinya da ita duka fa mun girmeta ah lallai wlh ba za ta sabu ba, sai an kashe aurennan na ga alama so take ta wuce mu a kullum."


Harira ta janyo hannun Hurera, "Hmm ke dai bari muje zuwa indai wannan labarin da naji ya tabbata daukan mataki ya zama wajibi a gare mu, kuma wai fa harda sadaki dubu dari biyar hmm asara wannan bai san wace irin yarinya zai aura ba,dama ni yazo ya bada dubu dari Wlh."

Hurera ta ce, "ke dalla can wake ta dubu dari biyar ni inba miliyan ba bani ba aure waya ce miki mu yan iska ne da za abada sadakarmu watakila ma karya ne sadakarta aka bada."


Gabadaya hankalin su ya tashi su kulla can su kunce can duk neman hanyar da zasu durkusar da Zeeyter ne kawai damuwarsu.


★★tana komawa gun Madame Ayshe ta nufa.

"Zeeyter bakyajin magana Meyasa kike son janyo abun da zai taɓa miki lafiya? Shin kin ganki kuwa? Ina ce wanki kike ina ka ka je kuma?"


Sosa kai ta fara tana, "Umm Madame Mangoro na je tsinka a bishiya."

Madame ta ce, "Oh oh Allah shirya mun ke, to gashi an daura auren dazu kisa hannu."

Daidai lokacin da Khaleel ma ya bawa Haiydar a office yasa hannu.

A tare gabansu ya yi wata irin hargitsattsiyar faduwa.

Dafa kai Haiydar ya yi yasa hannu ba tare da ya duba takardar ba.

Ita ma Zeeyter haka tayi.

Ba tare da ta ce komai ba kawai shigewa ciki tayi ta kwanta kasancewar wani irin zazzaɓi da ya lullebeta ga raɗaɗin da take ji ajiki ga kuma wani sabon al'amari da ya kunno cikin rayuwarta.



Khaleel kuwa yan fitowa a office din Haiydar ya tarar da su Deejerh a dakin hutu ya ce, "Albashirinku?"


A tare suka ce "goro."

Gyara zama ya yi yana daga takardar.

"An Daura auren Haiydar da Zeeyter."

Yana karasa maganar Farouk ya miƙye tsaye cike da mamaki tare da wani suka da zuciyarsa ke yi.


Dukansu komawa suka yi da duban Farouk.

Zahra ta ce, "Farouk Lafiya?"


Lokacin ya ankare cikin sauri ya goge zufar da ta keto masa yana, "Oh Oh Nothing wani tunani ne ya fadamun." Ya karasa maganar yana komawa ya zauna.

Deejerh ta karbi takardar tana dubawa.

"Alhamdu Lillah, Allah sa anyi Asa'a, Allah ba da abun da ake bukata."


Zahra da Khaleel suka amsa da , "Ameen."


Zahra ta ce, "Yanzu yaushe za adauko ta ne? Tafiyar mu fa jibi ya kamata ina ga tunda an kammala komai."


Khaleel ya ce, "Yap amman maganar daukota ku bar mun a hannuna komai zai tafi dai-dai in sha Allah."


Tattaunawa suka dunga yi ban da Farouk wanda gabadaya zuciyarsa ba dadi waya ya dauko kawai yana dannawa duk dan ya kauda damuwarsa ba tare da sun fahimta ba, wanda kuwa zufa bata fasa keto masa ba, tamkar wanda rana take kwalawa.


★★Madame Ayshe ce ta karasa inda Zeeyter ta kwanta sai da ta goge mata ko ina kananan ta bi wajen da mai

Shafa mata kai ta fara tana, "damuwar ki mu ko? Damuwarki kannenki da sauran mutanen gari ko? Ina so ki gyara kunnuwanki ki ji batun da zan yi domin kuwa ba ki rabu damu ba, sannan auren 'Yanci ne za ki yi, Aduk lokacin da kikeson ganinmu zaki zo, sannan gidan man da suke buƙata ma ai yana nan ko? Bana tunanin wannan auren zai sauya komai na tsarinki,illa kara fadada shi, aure ne na Kasuwanci kuma na ci gaba, kina tare da mu kamar kullum ,kiyi Murmurshi ki gode Allah zan ji fi jin dadin hakan."


Tashi Zeeyter ta yi tana hawaye tare da rugume Madame Ayshe, "Mammah na san auren nan ba zai hanani komai ba amman ji na nake wani iri tamkar bani ba, kamar an kara daura mun wani dutse mai bala'in nauyi arayuwata."


"Oh oh Rayuwarki tamkar Ta YEL ce, ke jaruma ce mai iya rayuwa a kowanni yanayi na duniya indai kin so da yardar Allah,ina Alfahari da ke kuma ba zan fasa ba har karshen numfashi na In sha Allah."


Da haka ta kwantar mata da hankali har ta samu ikon yi barci na yan mintuna, lokacin sallah nayi kuwa kamar an tsikareta ta tashi tayi sallah.

Bata damu da ciwon da ke jikinta ba har sai da ta wanke kayan da ta fito dasu dazu tas, Halliru da Yusuf har ma sauran yaran sunyi sunyi ta basu suyi taƙi,a kullum ta fi so tayi wahalar kanta da kanta, bata so ace wai tana zaune tana hutu wani na can na wahala dalilinta,shiyasa in dai za suyi mata wani abun sai dai in bata sani ba ko in ta fita.


Dare

"Hy Madame." Sakon da ya shigo wayar Zeeyter ke nan

"Hello aboki,fatan kana lafiya?" Ta fada.

"Lafiya lau ina fatan kema haka,ya labari ne?"

Zeeyter ta ce, "Umm na yi aure yau."

"To! Ikon Allah wane ne mijin nan da ya dauke mun kawa?"

"Ohon masa ni ban ma san sa,tunda ba shi ne damuwata ba." Ta fada hade da emijin cuna baki.

"Ba shine damuwarki ba kamar ya? Kar dai Ba kya sonsa ki ke nufi?"


Tsaki ta yi, "umm Oho watarana zan fada ma, ina so inyi barci da wuri yau byeebyee."

Haka Zeeyter ta kashe data ba tare da son ran Farouk ba,don shi burinsa ya sha cikinta sosai.


Kwantawa ya yi yana kallon sama a azuciyarsa yake fadin, "zaki dawo tawa in sha Allah."

Shirye-shiryen tafiya suke kowa zai koma Kasarsa domin ci gaba da aiki.

Zahra da Deejerh ne suka gyara gidan Sosai don basu bari mai aiki tayi ba,ko ina lungu da saƙu sai da suka gyara, musamman dakin Haiydar har wasu flowers suka jajjera a kan gadon da gefen dakin.

Misalin karfe shida na Yamma Khaleel ya tafi bobiel da niyar dauko Zeeyter.

Gabadaya hada yaran Madam Ayshe ta yi tana sanar da su cewa Antynsu za ta tafi gidan mijinta Amman zata dunga zuwa.

Kuka suka fara suna rungume Zeeyter.

"Anty jiya fa kikace ba za ki barmu ba, Anty muna sonki karki tafi kin ji." Jumy ta fada tana ƙanƙameta

Sauran Yaran ma suka fara kuka, "Aa aa Antynmu ba za ta bika ba,mu bama so ta bika ka tafi." Suka fada suna kallon Khaleel da jikinsa ya yi sanyi ganin tsantsar soyayya da kaunar da ke tsakanin Zeeyter da yaran.

A zuciyarsa yake fadin, "Na rasa wannan din wace irin yarinya ce, da da yadda zanyi dana sa Haiydar ya dauke yaran nan gabadaya sun ci gaba da rayuwa a tare, wannan ita ce Mace Mai Rayuwa Domin al"umma."


Madame Ayshe ce ka katse masa tunani da faɗin, "Oga mun gama."

Sai a lokacin da lura da Zeeyter kumburar riyar fuska ga uban kolin kaya agana most go da ta daura aka kai kace wacce aka kora a ƙauye.

Dariya ce take kokarin subuce masa ya damƙe yana fadin, "To Yaran Anty kuma kuzo muje ku raka Anty."

Da gudu yaran suka shige cikin mota suna dariya, Madame Ayshe ma ta shige, ganin wani saurayi ne yasa Zeeyter tsayawa da ke ƙarasowa gareta.

Mika mata hannu ya yi, "ban ji dadi ba ta wani fannin amman na ji dadi, ba kasancewa da ke kuma ba kudi, amman duk da haka ni masoyinkine ina miki fatan alkairy."



Zeeyter tayi Murmurshi ta ce, "Bana da bakin godiya gare ka domin kana biya mun buƙatuna aduk lokacin da na nema, ba zan barka haka kawai ba,kayi tunanin duk wani kasuwanci ko wani abu da kake bukata na rayuwa zan zo kuma na maka alkawarin cika ma burinka koma mene ne."

Ta karasa maganar tana shigewa motar.



Ko da suka isa gidan ba kowa duk sun fita.

Yaran sai zagaya gidan suke suna murna gidan Antynsu ne.

Sai da suka gama hutawa kafin Khaleel ya nunawa Zeeyter dakin Haiydar ta shiga tayi wanka sannan ya aje mata kayanta.

Ya dau yaran domin maidasu cen kauye da madame Ayshe.


Dakin ta fara bi da kallo yadda ya tsaru kamar ba a kasar nijar ba, mamaki take tana kara dubawa shin da gaske ne wannan gidan A Pleatau yake na nijar?

Khaleel na fita su Farouk suka dawo .

Gabadaya haiydar ya gaji hakan yasa shi nufa daki kai Tsaye.

Yana shiga..




08103080717
Urs Xayyeesherthou
[6/3, 4:14 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-18*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim


*AFWAN FEJIN YAU GUNTUNE BA MU DA WUTA SAI YANZU NA SAMU CHAJI*



Kwanciya ya yi akan gado, can ya ji alamun ruwa a toilet.

A Zuciyarsa yake saƙawa, "Mene ne a toilet dinnan ne?"

Jin karar buɗe kofar da aka yi ne ya katse masa tunani.

Zeeyter ce ta fito wanka daga ita sai ƙaramin towel.

Bai san lokacin da idanunsa suka ƙame a kallon yanayin sura da dirin jikin da Allah ya yi mata ba.

Ganin kallon yaƙi ci bare cinyewa ya sa ta ƙarasawa gabansa tare da yarfa mata ruwan hannunta ta ce, "Haiydar ko? Welcome Abokin Kasuwanci."

Ta karasa maganar dauke da Murmurshi mai dauke hankali.

Kautar da kai ya yi daga gareta yana sakin tsaki.

Ita kuwa tafiya tayi bangaren da aka tanada domin canja kaya.

Ba tare da ya ankare ba ya kara tsintar kansa da ci gaba da kallonta a ya yin da take tafiya, gabadaya kowanni bangare na jikinta sai
ya motsa aduk takun da take.


Tsaki ya ƙara yi a karo na biyu a zahiri ya furta, "shirme kawai."

Ya tashi yana ficewa daga ɗakin.

Ita kuwa kayanta tasa irin wanda ta saba jigari jigari kamar macen ƙaura.




Yana fita Falo ya zauna yana numfasawa.

Shigowar Khaleel ke nan yana, "Ah'ah Ango ka ga Amaryar kuwa tana dakin ka fa."


Tsaki kawai Haiydar ya yi yana ƙara kwanciya akan kujerar.

Farouk ya ce, "What ! You mean tana gidannan?" Ya fada cikin Mamaki.


"Eheen." Cewar Khaleel.

Zahra ta ce, "Ma sha Allah sannu da kokari Oga."

"Weldone Oga." Deejerh ma ta fada.


Murmurshi Khaleel ya yi yana, "Na so ace mun hada wani karamin Party kan mu bar Kasar nan,amman lokaci ya kure."


Zahra ce ta yi karaf ta ce, "Ah ah Why Not Yanzu? Ina ganin zamu iya shirya komai."

Deejerh ta ce, "Yess zan yi kokarin tsara karamin wajen taro yanzu a filin gidan nan And nasan Zahra za ta iya shirya mana drinks da Snacks."


"Alright, zan so hakan me kuke jira a fara shiri."
Cewar Khaleel.

Farouk da Haiydar kuwa ban da binsu da idanu ba abun da suke.


Nan da nan Zahra da Deejerh har da taimakon Khaleel suka shirya komai da komai yadda ya dace.

Misalin karfe 9 daidai Khaleel yaje ya kirawo Zeeyter.

"Madam za ki iya dan fitowa yanzu mun haɗa wani karamin Party ne."cewar Khaleel.


Zeeyter ta kalleshi kafin ta ce, "Ok ina zuwa."

Zama suka yi dukanninsu.

Farouk na ganin fitowar Zeeyter ya fara washe baki.

"Barka da fitowa Madame, haka kuma ina miki maraba da kasancewa cikin 5stars Expensive company."

Ya karasa maganar yana miƙa mata hannu .

Sigina ta masa da ido tana, "Barka dai,ina Godiya."


Zahra da Deejerh kuwa tsaya kallon yadda fuskarta ta kumbura suke ban da tabo ba abun da kake hangowa,ga kayan jikinta kamar na yan Caskale.

Zahra ce tayi karfin halin mika mata hannu ita ma tana, "Mrs Haiydar bar ka da kasancewa cikin Taurari biyar,ina tunanin ke zaki zama ta shidar."

Murmurshi Zeeyter ta yi tana, "Barkanmu dai,Godiya nake Yar uwa."

"Fatan alkairi sister na ji dadin kasancewar ki damu Allah ya sa zamanmu ya zama mafi alkairy." Cewar deejerh tana Murmurshi tare da mika hannu.

"Nima nayi farinciki godiya mara adadi."Zeeyter ta fada.

Khaleel ya ce, "Maddalla ni ma yanzu sai na kara magana kenan,to barka da zuwa Madame Zeeyter ko Mrs Haiydar din nima zan ce." Ya karasa maganar cikin salon tsokana

Dariya suka yi duka.

Khaleel ya riko hannun Haiydar.

Sai a lokacin ya kakalo wani Murmushin dole wanda kana gani kasan bai kai zuci ba.

Mikawa Zeeyter ya yi yana, "Barka da kasancewa da mu."

"Barkanmu dai Oga." Ta fada Cikin yanayin tsokana.

"Ya kamata mu fara shagalin mu yanzu, wane ne zai zo farko ne ciye-ciye da shanye-shanye ko kuwa rawa?."


A tare Haiydar da Zeeyter suka yi magana.

Ta ce, "Rawa."
Shi kuma ya ce, " Abinci."

Kallon juna suka yi duka suka tintsire da dariya

Zahra ta ce, "Dole ki dage da girki domin wannan mijin naki aci-ci ne."


Haiydar ya yi dariya, "Eh din an ji Food Is Life."

Khaleel ne ya katse su da fadin , "Yanzu ga takardu biyu duk wanda ya riga dauka aka bude abun da ya dauka shi za a fara Oya Madame Zeeyter da abokina."


Haiydar zai dauka kenan da sauri Zeeyter ta bige masa hannu ta riga dauka.

Ana budewa kuwa aka ga food.

"Food is Life." Suka fada duka suna dariya.

Nan suka fara ciye-ciye da shaye-shayensu.


Ban da tsokanar junansu ba abun da suke sautin dariya duk ya maye Falon.


Suna gamawa aka koma bangaren rawa.

Gabadaya Zeeyter ta dage tamkar wacce tai shekara da su.

Rawan da take ya bala'in daukan hankalin su hakan yasa gabadaya suka bata fili .

Ban da tafi ba abun da suke yi mata.

Farouk kuwa bidiyo ya shiga yi mata.

Sai da suka gama cashewa deejerh ta ce, "Zan zo koyan rawa gaskiya."


Zahra ma ta ce, "Nima dai kam ina son in iya rawa haka."


Farouk ya katse su da, "ni kadai Gimbiyata za ta koyawa ehee."


Ita dai Zeeyter dariya kawai take binsu da shi.




Ko da akazo barci suka je kwanciya, kowa juyawa juna baya suka yi.

Can kuma a tare suka juyo.
Tsaki suka kara yiwa juna a tare kafin suka kuma juyawa.

Har zuciyar sa ji yake yana bukatar kasancewa da ita amman ta yaya?


Tsaki ya dunga yi har barci ya yi awun gaba da shi.

Har gari ya waye.

Kafin Zeeyter ta tashi har haiydar ya tafi raka su Airport , rungumar junansu suka yi duka , nan take suka tsinci junansu da fara kewa.

Kowanne ya shiga jirgin kasarsa Farouk ne ya leko yana cewa Haiydar, "Sir a kula mana da gimbiya."


Murmurshi Farouk ya yi yana, "In sha Allah Sir,A sauka lafiya."



★★zeeyter kuwa tana tashi ta ga ba kuwa fara zagaye gidan tayi tana dube-dube ta ci karo da wani Tsohon AC Da ya lalace an aje agefe, adukkan alamu yarda shi ake shirin yi.

Zuwa tayi ta dauko karamar jakarta ta yi zaman dirshem awajen, ta fara kuncewa.

Tana cikin gyaran sai ga Haiydar ya dawo, ganinta zaune jaga-jaga ya sa shi yin wani kasargumin tsaki zai wuce ya bige mata wata robar Acn.

Tsakin tayi ita ma tana, "Iskanci kawai."

Ta ci gaba da aikinta shi ko ya shige cikin gidan.


Misalin karfe tara ya fito zai tafi Office da Mamaki har Zeeyter ta gyara wannan Acn kuma ta bar gidan.

Mai gadi ya tambaya ya tabbatar mai da cewa ai ta fita.

"Oho ." Ya ce azuciyarsa irin halin ko in kulan nan.


Yana fita wasu 'Yan mata biyu suka tare sa, ga dukkan alamu daman jiran fitowarsa suke.

Harira ne da hurera, wanda tun jiya suka biyo Khaleel domin tabbatar da inda aka kawo Zeeyter.


Harira ce ta fara magana, "Barka dai Yallaɓai, Ina kwana."

Tayi maganar cikin kissa.

Hurera ma ta ce, "ina kwana Oga."

A tsagaice ya ce, "Lafiya."

Hurera ta ce, "Daman daman gunka muka zo, kan yarinyar da ka aure Zeeyter,oga wallahii Yar iska ce, har biyan samari kudi take suna iskanci,kuma fa bata da iyaye,Yar duniya ce har dambe take da maza wallahi kuma mayyace ma."


Harira ta ce, "Ga shi har sata take yi, ka ga Oga amman mu wlh ba ruwanmu ba ma shiga harkar kowa da ma cikinmu ka zaɓa." Ta ƙarasa Maganar tana juya jiki.


Mamaki ne ya ishe Haiydar azuciyarsa yana saƙa, "To ni ina ruwana da rayuwarta,ko ance masu ni sonta nake da wani abu?".


Maganar su ce ta kara katse masa tunani.

"Oga Wallahi indai ka aure ni ba za ka yi danasani ba."

Cikin takaici ya ciro belt din jikinsa ya fara maka masu yana.


"Koma menene na ce maku ina bukata ne? Kar in bude ido ku bar mun wajen nan."

Da gudu suka tafi suna haki.

Hurera ta ce, "Wallah shi ma mahaukaci ne kamar Zeeyter."

Zeeyter kuwa Bobiel ta nufa

Tazo daidai wajen police station sai ga Dpo ya fito ya sha gabanta.

Kallonta ya yi cikin salon mugunta yana, "ba wai kinyi aure ba? Muje zuwa ni da ke , ko ma waye kuma ko shi waye dolen shi ya sako ki, ki zama mallakina,nine kadai na cancanci kasancewa da ke amatsayin mata, nayi alkawarin samun ki duk tsanani ko da kuwa komai nawa zai ƙare."


Kallon shi tayi ta tsintsire da dariya tare da sa hannun ta akan cikinsa.

"Allah ya sauke ka lafiya Oga." Ta ƙarasa maganar ta na dariya tare da gudu.


Takaici ne ya dakesa a kirji azuciya yana tunanin shin meyasa ma yake son yarinyar da kowa ya tsanane, tabbaas akwai wani abu.


Gidan marayu ta fara shigewa, suna jinta duka yaran suka fito suna murna har ma sauran yaran unguwar, mintin da ta siyo masu a hanya ta raba masu duka.

Madam Ayshe ta matukar jin dadin ganinta albarka ta sanya mata

Kafin ta nufi gidan mai kamar yadda ya dace kuwa su Halliru na ta faman aiki.

Can anjima Madame Naddja ta zo masu karatu bayan sun kammala Zeeyter take magana kan taron wayar da kan da za a kara fannin zamantakewa tsakanin mata da miji yadda ya kamata su kasance da fahimtar juna.

A lokacin Madame Naddja ta kira waya domin tabbatar da bakuwar da zasu gayyato tunda awannan karan ta ce mace ce za ta yi hawabin.


Sai wajen misalin karfe tara na dare Zeeyter ta koma gida, tana shiga tun daga nesa ta fara jiyo warin giya, can kuma sai ga Haiydar tunbur da...........



08103080717


Urs Xayyeesherthou

[6/4, 9:40 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-19/20*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

*Anty Tatuh,My Walida,Mhix Abdullahi,Mrs H.Y.G,Oum Al'ameen,Smasher, Rukayya Yakubu,Real Ayushat,Zummcy.com,Walisa Adam,Feena Yusuf,Nana, da ma duk YEL fans wa inda na sani da wanda ban sani ba,aduk inda kuke ,ina sonku, Indai nace ina sonku ina nufin har ƙaunarku nake fissabillah🥳🥰Sharhinku na bani nishadi ina so Sosai fiye da tunaninku ba zan iya maku so kadan ba🥰❤️*


★★★


Meenoh tana kwance a jikinsa.

Ga kwalbar giya a hannu ban da kwalaben da ke yawo a falon.

Cikin zafin rai ta karasa inda suke Giyar ta fisge, ta kwashe sauran ma tana fita ta zubda cikin shara, kara dawowa tayi ta duba fridge sune makil cike fam, wani irin tsaki ta kara yi,duka ta kwashe ta zubar.

Takaici take na ganinsa yana shan giya amman ba wai na kasancewar shi tare da mace ba,hasali ma ba ta jin kishi ko wani abu aranta ko kadan.


Meenoh ce ta yi kokarin tashi tana sa kaya don duk a tunaninta ma Zeeyter mataki zata dauka akanta amman da mamaki sai ta ƙare akan giya.

Janyota jikin sa Haiydar ya yi yana, "Baby kar ki damu da ita i wil tech her a lesson, na ga alamun yarinyar nan bata da kunya." Ya fada cikin yanayin maye.


A raunane Meenoh ta ce, "kar ta fito ta mun wani abun fa bana so ina tsoro."


Tsaki ya yi, "ba abun da za ta iya miki ba komai ba ce ita illa matar kasuwanci."


Wani irin dadi Meenoh ta ji nan ta ci gaba da biye masa suna ba juna saƙonni.


Zeeyter kuwa tana shiga ɗaki wanka tayi kasancewar tayi sallah tun a bobiel kwanciya ta yi akan gadon tana duba wayarta data ta kunna,kamar kullum saƙon Farouk ne ya fara shigo mata.

"Hey Friend, yau kinyi busy kin manta dani ko duk shaukin ango ne?"


Tsaki ta yi ta ce, "Wani Ango? Ba ya da kirki sam kuma bai son rayuwarsa giya yake sha, gabadaya na ji ba dadi ganinsa yana ta'ammali da miyagun kwayoyi, Indai ina giddanan na yi dau alwashin ba shi darasin da sai ya yi mamaki,sai nayi maganinsa wallahi, wannan ai iskanci ne."


Dariya Farouk ya yi, "Oh calm down Friend, mene ne na damuwa to tunda ba son shi kike ba,ya ma kashe kan shi mata."


"Don bana son mutum ba shi ke nufin in naga yana kokarin bata rayuwarsa in kyalle ba, duk da cewa komai ka ga mutum ya yi,ko yana yi to fa yana da dalilinsa, amman ni ban damu da miye dalilinsa ba,kuma ban damu da cewa ba son shi nake ba, ni dai ba zan taba bari Dan Adam ya yi wasa da rayuwarsa ba,ya rugusa kuma ina gani ba, mun sa kafar wando ɗaya ke nan ni da shi a gidannan."


Farouk ya ce, "To naji na ji muyi hirar mu ki bar wannan shirmen Mijin bogin na ki."


Dariya tayi ta ce, "What Ever,ni dai na fada ma,kada ka damu da batun cewa mutum na sonka ko aa ko kuma kace kai sai kowa ya soka, ban dauki hakan komai a rayuwata ba,ni dai kawai indai naga ana abun da zai cutar rayuwa to bana iya kawar da kaina, ko da zan ja magana ne fa sai nayi." Tayi maganar tana dariya.

"Ai kuwa kika ja magana ba ruwana zan yi kamar ban sanki ba a caskale ki." Cewar Farouk.

Dariya ta yi ta kalli jikinta azuciyarta ta ce, ",oh oh sai na kara wani wankan ma dole Akwai bukatar in gyara jikina,.

Kallon wayar ta yi ta ci gaba da rubutu, "Oho dai ka ga dare ya yi ina so in danyi gyaran jikina kwana biyu ban samu lokaci ba ga shi duk na kurje byeeebyeee."


"Amare kam sai da gyara,a gyara mana da kyau byee." Ya fada da alamar tsokana.


Murmurshi kawai tayi ta aje

Please Login or Register in order to submit comment