Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne kuka san cewa shi naku ne? Kun manta lokacin da kuka watsar da shi da mahaifiyarsa?"

"Ke awa? Ke kuma awa ana maganar dangi zaki shiga, dakata daga nan." Antou ta fada.

cikin zafin rai Ammie ta ce, "Ni a yayar Mahaifiyar Haihu wacce bayan kinyi sanadiyar barinsu gidan mijinki suka dawo gareni,ko azamanin zahiliya ba ayiwa namiji auren dole bare kuma yanzu da kai ya waye matan ma ba musu ake ba,ba wanda ya isa ya sa Haiydar ƙara aure ba da son rashin shi ba,shi yaga matarsa yakeso koma ya take ba damuwar ku bane."


Antou ta ce, "Oh sannu gwana na ce sannu gwana to ubansa ya yanke hukunci sai ki hana."


Ammier tayi dariya tana, "Shin baki lura cewa kunya ta lulluɓeshi ya ma kasa magana bane da gani na?ai da kunya kam shi ya san bai kyauta ba ,ba tun yau ba. Mu zuba ni da ku wallahi ana ƙara tada batun auren nan zaku sha mamaki in shi Haiydar ba zai iya kai mahaifinsa hukumar kare hakkin Dan Adam ba,ni zan kai Ku da kaina."

Jiki a sanyaye Baba ya bar falon.
Zeeyter kuwa daki ta shiga tana kuka ganin ba abun da ke mata dadi aduniya.

Antou kuwa ta dage sai kokarin jan magana take da Ammier, Ammie ta mata tatas.

Har zasu fita Antou ta fadawa Unaisa abu a kunne nan take ta nufi dakin Zeeyter.

Zeeyter na kwance akan gado.
Unaisa na shiga tayi tsaki tana, "Banza ballagaza juya kawai wacce bata haihuwa inda zuciya ki haihu mana, wawiya kazamiya kawai."

Karaf a kunnen Haiydar wani irin gigitaccen mari ya makawa Unaisa wanda sai da ta firgice kafin ta bar dakin aguje tana kuka.

Ta rungumi Antou tana, "Antou marina yaya ya yi,kizo mu tafi kar ya biyo ni."

"Au akan waccer tsinanniyar yarinyar zai maran mun ke? Ah ba shakka zan dau mataki kuwa tabbas." Ta karasa maganar suna sakin tsaki tare da fita agidan.

Murmurshi kawai ammier tayi tana binsu da kallo.

★Wani Irin kuka mai ɗuma zuciya Zeeyter keyi tana shiɗewa tare da ajiyar zuciya.
Aranta bata taɓa jin raɗaɗi da zafin rashin haihuwa ba irin yadda yau Unaisa tai mata gori kai tsaye.

Da sauri Haiydar ya karasa ya rungumeta yana, "Mene ne haka? Ki bari bana so kinji."

Cikin shiɗewar kuka ta ce, "Don Allah ni na hana kaina haihuwa ko kuwa wa inda Allah bai basu haihuwa ba baya son su ne?"

Haiydar ya ce, "Aa sam sam wannan kuskure ne kar in kara ji kin fada, kowa da kaddararsa kuma in Allah ya ma kaddara ba wai yana nufin baya sonmu bane,aa watakila hakan shine mafi Alkairi ne rayuwarmu,da ki haihu da kar ki haihu ni ina sonki kuma zam rayu dake bare ke kina da 'Ya'yan da masu haihuwanma basu isa haifa ba zakiyi alfahari da su ako ina aduk sanda kika so kuma, ba a taɓa samun duk abun da ake so aduniya,amman duk wanda Allah ya baka sai kayi godiya kuma ka nuna farincikinka garesa,bana so ki kara damuwa da hakan kin ji Smile my bright Eye."

Ya karasa yana Murmurshi.
Murmushi ita ma tayi sai kuma ta taɓe baki tana dukansa a kirji.
"Da ba ka daina sona?"

Bude baki Haiydar ya yi yana zare ido, "Injiwa ni na isa? Indai zan daina son kaina to kisa aranki cewa zan daina sonki."


"Uhumm to ce kana so." Zeeyter ta fada.

"I love you,I Really Really Love Bright Eye." Ya fada yana yi mata kiss.

Gyaran Muryan Ammier ne ya sa su saurin juyawa tare da matsawa.

Murmurshi ta yi ta ce, "Ku zo falo muyi magana don ban jin cewa zan zauna agiddanan tafiya bobiel zan yi in sha Allah in huta acen."


Suna fitowa Zeeyter ta ce, "Haba Ammier Don Allah ki zauna anan zamu fi jin dadi."

"Aa fa ni awa gada adakin miji barni dai in koma can tsohon gidanku dake bobiel din in ina son ganinku nazo nan ko ku kuje, yawwa kuma gareka Haiydar kai kafi kowa sanin Cewa matar cen ba kaunarka taka ba amman har zaka tsaya kana wasa da lamuranta ya ci ace yanzu kasan kai waye ,ko da yake ma ba komai zan dau mataki,a kullum dai ina kara baku shawara ku rike kanku da amana kada ku bari rudin duniya ya biku,ku rayu tamkar sabin furanni da ke fitar da kamshi a kullum zan ji dadin hakan."

Nasiha Ammie ta masu sosai kafin suka kaita bobiel suka dawo.

Cikin kwana biyu Gaɓadaya Zeeyter ta shiga damuwa kan haihuwa zance Unaisa ya kasa wuce mata a zuciya aduk sanda ta zauna ita kadai sai kuka,sai dai tana jin motsi ta goge hawaye Haiydar da Deedarth sunyi sunyi amman taƙi fada masu menene matsalar.

Dakyar Haiydar ya fahimci cewa har yanzu zafin gorin haihuwar da Unaisa ta mata ne ta kasa mancewa.

Bai ce da ita komai ba, duk wani abu da zai ɗebe mata kewq kawai yake agidan har ta kai ga office tare suke zuwa,inma na shi ne ko nata duk suna tare duk gudun kada ta shiga damuwa.


★★Kasancewar babu aiki suna hutu kwance take adaki kamar kullum tana tunani.

Tun safe Haiydar ya fita bai dawo ba, tasan dai ba office yaje ba.

Shigowarsa ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data fada.

"Bright Eye ki tashi yanzu zamu fita."

Zare ido tayi tana, "Sunshine a daren nan ina zuwa kuma?"

"Muje dai kawai kada lokaci ya kure 11:40pm, kan 12 mu isa."

Ba tare da ta kara magana ba hannunta kawai ya rike suka fita.

Tana kokarin shiga bangaren su Madame Ayshe.
Haiydar ya ce , "ba ki ji shiru ba,sunyi barci ai mu tafi kawai." Ya karasa maganar yana bude mata mota.


Tafiya suke Zeeyter ta ga an dau hanyar bobiel a tsorace ta ce ,"Bright Eye ba dai Ammie ce ba lafiya ba ko?"

Shiru Haiydar ya mata, ban da faduwar gaba ba abun da take ji.

Har suka isa.

Suna shiga wutar gidan ta dauke dif.
A razane Zeeyter ta kankame Haiydar.



08103080717
[7/4, 7:30 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-42*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

*TALLAH*

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

★★
Agogo na bugawa sha biyu daidai.
Aka kunna wutar.

Suka fara wakar, "Beauty Personified, Love in Abundance,

Beauty personified, love in abundance,
You gave us everything, by your mere presence.
Fragile is your heart, yet you are strong,
Courageously you defend your children even when they are wrong.
You taught us how to take the right decisions,
And how to believe in ourselves and our ambitions.
We wish to thank you with all of hearts today,
Dearest Mother, may you have a brilliant day!
Happy Mother's day!"

Tafi suke dukansu kowa dauke da Murmurshi a fuska daga yaran har manyan.

Tsabar farinciki Zeeyter ta rasa abun cewa binsu kawai take da kallo Mussamman da ta ga dukkanin Yan Uwanta na gidan marayu manya da yara da ma wa inda aka aurar maza da mata, ga 5stars duka da su Noor, Da kuma Ammiern Haiydar,Halliru,Yusuf.
Kowa da kowa.

Binsu kawai take da hakwara tana washe baki.

Ba karamin tsaruwa falon taron ya yi ba, ko ina anyi masa ado da abubuwan Mother's day, kyalkyali da wuta kawai ke tashi.

Da sauri Deejerh ta zo ta jata suka shiga daki.

Wata irin hadaddiyar riga ta bata ta sa sannan ta gyara mata kanta tare da yi mata light make-up.

Suna fitowa da gudu Baby da Noor suka karaso tare da rike mata hannu suna.

"Appy Mother's day Mom, U are The Best Mom All Over The world, We Loves You."

Da gudu su Miemie da Anitha, Anushka ma suka karaso.

"All your life you sacrificed your own happiness for ours. As a mother, you did everything to make things perfect for us. My eyes fill with tears when I remember all that you have done for us. Words are not enough to express how thankful I am. I love you Mom! Happy Mother's day!."Miemie ta fada
Kafin duka suka hada baki da su Anushka suka ce, "We Love You Mom,We Really,Really Love You,
You are the most beautiful miracle of God,
You are a gift from heavenly abode, we can't Love You Less."


Hawaye ne ya fara zubowa a idanun Zeeyter ta rugumesu tana kissing dinsu .

Cikin kuka take fadin, "I Love you Too,You Me Alot To Me Can't Do Without You ."

Noor ne ya dauko kyautar da suka tsara mata ya mika mata.

Gaɓadaya falon taron ya yi shiru dukkaninsu jikinsu ya yi sanyi kowa ban da share hawaye ba abun da suke yi.

Adam ne ya katse shirun da suka yi ya karasa gabanta tare da rike mata hannu ya ce, "Ni ne babba acikin 'Ya'yanki ko kin manta cewa har jikoki gare ki?"
Ya karasa yana nuna yaransa mata biyo suka tawo da gudu suna rungumeta kan ya ci gaba da magana.
"Da ance ba za a kira ni ba ko in ce anma ki kirana amman tunda labari yazo mun naji cewa tabbas ya kamata inzo domin nine babban ɗa a gare ki,ko kin manta lokacin da kike sani aiki ne in Mami Ayshe bata nan? Duk girma na mantawa kike da shi fa ki sa ni agaba sai mun gyara gida tsaf hatta zubar da shara."

Dariya suka yi dukansu hatta ita Zeeytern dake share hawaye tana dariya.

Ya ce, "Eheen Ki zam tamkar uwa a gare mu duka ba wai iya yaran kadai ba,kin lura da mu aduk lokacin da Mami ta fita neman mana abincin da za mu ci, wani zubinma kinka fita da kanki ki nemo mana, A lokacin da aka kawoki gidannan ji nake nafi kowa tsanarki,bana son ganinki sam acikinmu in kin lura ko wasa ake na gan kinzo gun tashi nake,ban san cewa da ke da taimakonki rayuwarmu zata inganta ba,ba zan taba mantawa da wannan ranar ba, Mami bata nan,na tashi da wani irin azababben zazzaɓi ji nake kamar zan mutu, acikin ruwa haka kika fita kina bin gidan mutane kina zubar masu da shara har kika samo kudin da kika kira likita ya dubani, wannan ranar da bakya nan ina da tabbacin cewa sai dai wani bayan ni,taya za ayi ba zan kiraki da sunan uwa ba? Ke uwata ce da a ko ina kuma a koyaushe zan iya nunaki cikin alfahari da gadarar cewa ke ta mu, duk da cewa mun girmeki amman hakan bai sa kin karaya ba, atakaice ke ka tarbiyantar da mu."

Yana karasa maganar sauran suka karaso wajen mata da mazan duka suna Murmurshi.

A hade suke fadin.

"To the most beautiful soul on earth,
You are the reason why we smile,
You are the reason why wy are happy all the while,
You are the reason why we give our best,
You are the inspiration for every test,
You are our world, you mean a lot,
You are in our prayer and thought,
You are the most beautiful soul,
In our life, you have the most important role,
We love you mom,
Happy Mother's Day!"

Adam ya kara cewa , "Mu 'Ya'yanki ne,Ke Uwa ce a gare mu har karshen numfashi."

Ban da sautin tafi da share hawaye ba abun da ke tashi a falon.
Kyautar da aka yi rapping suka mika mata

5stars a tare suka zo suna fadin, "Happy Mother's Day Maman Yara da Manya Allah kara daukaka mai inganci da hakuri tare da juriyar rayuwa."

Dukansu suka rugume juna Zeeyter na fadin, "Thank you So much My People."

Farouk ya ce, "Eheen Nawa daban ne fa So Abani fili in gaida Gimbiyata."

Dariya duka suka yi.
Kafin ya ce, "She is so strong

A woman is strong enough to face life
She has that smile on her face through strive
She sacrifices for her loved ones without a hint
There is sadness in her eyes but she does not tint
She feels happy to see everyone smile
For her love is what matters all the while
She is complete in every sense
She will remain lovely in every tense
A woman is a beautiful creation of god
So a big salute to her from heart , that's you."

Ya fada yana mika mata wata kyauta.

Sannan Zahra ma ta mika mata tana fadin, "From 5stars Just For you Dear."

Karba tayi tana rungumeta.

Sai da kowa ya gama aka bada kyautuka tukun halliru ya ƙarasa gabanta da sauran yan company su Yusuf da sauransu .

Halliru ya ce, "Inna fara magana kowa zaiyi shiru ko ince baku da ma abun fadi zan takaita amman duk da hakan zaku sha mamaki,bana da bakin godiya ko abun cewa gareki Madame don ko ni aguna kin zarce shugaba sai dai ince uwa,kin tabbatar mun cewa da alaka ba ruwanta da cewa dole sai jininka in dai da yarda da amana to kowa ma naka ne, kin maida ni shugaba a kasuwancin ki,mallakinki, kin karfafa mun gwiwa aduk lokacin da nace ba zan iya ba,ki kan ce zan iya, kin maidani abokinki,abokin shawararki kuma jinin jikinki, kin tallafo rayuwata daga fadawa halaka,in ban manta ba a baya fashi nake yi kan hanya cikin dare na miki fashi kika daukoni kika bani shawara ,kika gyara mun rayuwata sannan kika bani aikin yi,to me zan ce? Shin me zan ce? Kin gama yi mun komai ba ma ni ba harda dangina da sauran ma'aikatanmu, kina da kyakkyawaar zuciya da kyakkyawaar alaka da kuma ingantacciyar rayuwa, ace mutane da yawa zasu yi koyi da ke da anji dadin rayuwa cikin duniyar nan,ke ce madubina kuma abun dubawana har karshen numfashi in sha Allah."

Haduwa duka suka yi suma suka mika mata kyauta suna, "Muna kaunar ki Madame."

Sai a lokacin Haiydar Ya ƙaraso tare dafa mata kafada ya juyo da ita suna kallon juya.

"Kin gani? Kin ga Soyayya? Yau kin yarda cewa ke Uwa ce kamar kowacce uwa? Kin gane cewa ba sai Ɗan da ka haifa acikinka bane naka? Kin gane cewa wasu yaran sune Alkairi a garemu? Allah ya fi mu sanin daidai ya turo miki da 'Ya'Ya ta hanyoyi daban daban ba tare da kin haifa ba,wannan ma kadai abun alfahari ne da jin dadi, sannan nima ina alfahari da hakan ba haihuwa ko wani abunki nake so ba,ke din dai,ke din kawai nake so kuma Alhamdu Lillah na samu me zai sa inyi wata damuwa? Yanzu ya ci ace ki cire damuwar kowa aranki ko sanya wani abu da za a fada miki arai,bai zama lallai kowa ya soki ba,amman kiyi farinciki da wa inda suka so ki, ki manta da komai ki cire komai arai yanzu Lokaci yayi da kema zaki nunawa kanki soyayya ki kula da kanki sannan ki aminta da kanki zan yi Farinciki da hakan,ina sonki har bayan raina,They say when love is real, it never fades away. It just keeps getting more and more stronger with time. That is the way I feel with you. Married life would never have been half the fun it is, without you as my wife. I could never give you away for anything in this world. You are so special to me, Bright Eye."


Rungume shi tayi tana kuka tsabar farinciki.

Ya ce, "kowa ya baki kyauta amman ni ji nake komai zan baki ya yi kadan sai dai in mallaka miki kaina I thank God for the root I Took Even if i die in thousand times i will take thesame root because it going to lead back to you. ."

Murmurshi Zeeyter ta yi ta ce, "I thank God for the sorrow,The sadness, the hardship i had being through,the Mistake i had made that brought me to you,I don't mind follow it for the thousands times if is going to lead back to you.I Love You So Much Sunshine."


Tafa masu suka yi.
Zahra da Deejerh suka janyo tankareren cake din da aka yi gabansu.


Zeeyter ta yanka har haiydar ya washe baki zata ba shi ta fashe da dariya tana nufi gaban Madame Ayshe da Ammie.
Basu tayi suka ci kafin ta ce, "Nima wa innan sune iyayena, iyayen da babu kamar su, farincikin su da walwalarsu duk tana gareni,ina Alfahari da ku iyayen kware." Ta karasa maganar tana rungumarsu duka.

Madame Ayshe ta ce, "Diyar kirki diyar kwarai Diyar da babu kamarta, ke haske ce aduk inda kika kasance , Allah ya miki albarka ya kara haskaka rayuwarki da hasken sa ina alfahari da ke."

Ammie ma tayi Murmurshi kan ta ce, "Tabbas Yarinyar kirki baki ya yi kadan wajen iya misaltaki,kyawun zuciya ciki da waje alhamdu Lillah, Allah kara hada kanku ke d mijin ki ya zaunar da ku lafiya har karshen numfashi."

Sai da suka gama sanya mata albarka kafin ta tafi ta bawa dukan yaran cake,hatta su Adam da Farouk sai da suka ci.


Haiydar ne karshe ya yi fushi cikin zolaya yana fadin, "Wato saboda ni ke ba mamata ba ce shine za anuna mun wariyar launin fata,ba komai zan rama."

Dariya suka yi duka yana bude baki ta bashi ita ma tana dariya.


Daga lokacin aka sa waka suka fara tikar rawa masu cin abinci na yi masu rawa nayi, haka ma masu barci na yi.


Kusan kwanan zaune suka yi aranar.

Kasancewar sun gama shirya komai har na wunin gobe a gidan duka zasu kasance ayi wassani don nishadi da faranta ran juna.

Zeeyter na shiga daki Haiydar ya shiga wanka kamar wasa ta bude gifts din da Farouk ya bata.
Abun mamaki Sako ne yake fadi mata, "happy Mother's day Kawar Dole kuma Gimbiyata, Allah ya kara daukaka da basira mai inganci da albarka,za ki ga kudi na turo miki wannan karan kiji dadinki kai tsaye naki ne ba na kowa ba."

Suman zaune tayi tana tunanin cewa ashe Farouk ne take chat da shi suka yi wannan mugun sabon.
Duba wayarta tayi ta ga alert kuwa irin wanda aka saba turo mata kudi ace tayi aikin Alkairin da ta saba.

Bude baki tayi azahiri tana fadin, "Duk shi ne."


*A YI SHARHI KO IN BADA MAMAKI😎*

08103080717
[7/6, 2:57 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *YEL*🦅

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ba ko wata, sannan labarina yana dauke da yaruka uku ne zuwa huɗu:*Hausa, French, Turanci, Malay*, Haka Kuma ka/ki faɗi alkairi ko ka/ki yi shiru! Yadda ki/ka ga labarin haka tsarinsa yake kuma babu canji,Salon na Mussamman ne sannu a hankali komai zai bayyana🦅_

_R.I.J.F. Little Baba *(Suhaan)*😭_

*PAGE-43*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

*TALLAH*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

★★

Gift din su Noor da miemie kuwa hotonta ne da Haiydar anyi katon frame sannan da rubutu agefe.

Na 5stars kuma Kayane,Gida da kuma keyn wata tanƙareriyar mota.

Su Adam kuwa Abubuwan wasanta ne na yarinta suka yi gyara tare da bata su a matsayin kyauta.
Gaɓadaya bakin Zeeyter yaki rufuwa da ko ina kayayyakine.
Har ma ta kasa bude wasu.

Haiydar ne ya fito a wanka yana, "Madame me za abani ne nima?"

Ya ƙarasa maganar yana daga wata guntuwar riga tare da mannawa a jikinsa.

"Ina ga wannan rigar fa za ta mun."

Kallon shi Zeeyter tayi tukun ta tintsire da dariya tare da fadin, "tab wayaga namiji da suna Hajara Sunshine da Anji jiki kuwa."

Zama ya yi a bakin gadon tare da riko mata kwankwaso yana, "Jin jiki akan me? Kayan ki ba nawa bane? Sai ma inzo in fiki kyau ai in kinyi wasa."

Hannunta tasa kan bakinsa tana, "Umm Naka ne mana kamar yadda kake nawa ni kadai ko?"

Haiydar ya yi Murmurshi kan ya ce, "Ke daya? Kina nufin ko aro ba zaki ba kowa ba?"

Girgiza kai tayi alamar Aa cikin Shagwaba.

Kissing dinta ya fara yana dariya, "Bayan kin hana Saudatou ni kinji dadi ko?"

Filo ta dauko ta fara buga masa tana, "Bana so,bana so Sunshine ni bana son Maganar yarinyar nan."

Rike mata hannu ya yi ya ce, "Daman Rayuwar Aure ba komai bane illa sadaukarwa ,kuma sadaukarma na nufin godiya ga Allah a kowanni irin yanayi,watakila za mu so 'Ya'ya amman Allah ba zai bamu ba,saboda ya riga ya rubuta mana abun da yafi cancanta ga rayuwarmu,kuma dole mu gode ma Allah,sannan mu yarda da junanmu, na yi Sadaukarwan kasancewa da ke ko ba kowa, Rayuwa bata da tabbas kuma ba komai bane yake zama daidai,za mu iya cewa aure tamkar kawance ne wanda Allah ke haɗawa , na dau wannan auren a matsayin sadaukarwan da zan zo inyi dana sani,amman ban san cewa khaleel ya gama yi mun komai bane,ba zan gaji da gode masa ba,kuma ba zan gaza ba wajen girmama shi,ba zan taba bari ki subuce mun ba, duk rintsi kowacce irin matsala za muyi maganinta tare ba boye-boye illa goyon bayan juna a kullum a kodayaushe sannan mu godewa Allah da duk abun da ya bamu ba tare da nuna gazawarsa gare mu ba.
Kaddara ce ta hadamu ,ke kaddara ta ce kuma ina marhabun da wannan kaddara da ta zam mafi Alkairi a gare ni,kuma zamu kasance tare har karshen rayuwarmu in sha Allah da dadi ko ba dadi."

Murmurshi Zeeyter ta yi ta rugumesa tana, "In za a ce in bada misalin farincikin raina kai kawai zan nuna ba tare da fadin komai ba,kai din na musamman ne acikin maza ,mazan ma wa inda suka kasance taurari,taurarinma ɗaya kwal dake iya haskaka duniya."


Kallon Haiydar ya na wasa da kumatunta ya ce, "Ya isa,Ya isa Oya Ataimaka mun da kaya ina so insa inje in nemi abinci cikina ya fara kuka."

Dariya tayi ta ce, "Food Master ba za dai a fasa halin ba." Ta karasa ta ciro masa kaya, taimaka masa tayi yasa ta feshesa da turare tare da rugumesa tana, "Thank You Sunshine."

Da mamaki ya ce, "Thanks For what?"

"For Everything, Worlds can't explain how Happy Am I ,Ba zan taba gajiya da yi ma godiya ba har karshen numfashi na,Ina Sonka."

Zaro ido ya yi cikin zola yake maganar , "Da Gaske kina Sona daman ai ban sani ba."

Ya ƙarasa maganar yana ficewa.
Binsa tayi da gudu tana, "Zan rama Ai."

Yana fita gun abinci ya nufa yana, "Madame, Anty Zahra Food Please." A sanyaye ya fada irin yanayin abun tausayi.

Dariya suka yi duka.
Zeeyter ta karaso tana, "Yau ba zai ci abinci ba,kar ku ba shi, Sunshine yau sai na disfila ka Allah."

Toshe kunnesa ya yi yana kallon Zahra ya ce, "Ki rabu da Ita ban abinci kin ji,kin san ana sanyi ,shi ya tabata ina ga."

Zahra na ba Haiydar abinci Zeeyter ta addabesa ga nata amman taki ci sai da suka cinye

Please Login or Register in order to submit comment