Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[9/3, 5:56 PM] My Number: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-1/2.

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

*ALLAH KA BANI IKON RUBUTA ALKAIRI FIYE DA SHARRI CIKIN RUBUTUN NAN,YA RABBIE KASA DUK WANDA ZAI KARANTA YA KARU KUMA YA FAHIMCI INDA NA DOSA🙏🏼*

*11/08/2022*
★★★

Ni 'yar talakawa ce.
Kuma Yarinya Mai Rauni.
Rayuwa ta mun tsanani Sosai.
Nayi kuka.
A lokacin da na cika shekara shida a duniya an fara amfani da ni ta hanyar saduwa.
Haka kuma sun sanar da ni cewa wasa ne kawai tsakanin yarinya da babban Namiji.
A lokacin da ya kamata inyi wasa da Yar bebi kamar sauran yara, da abubuwan ban dariya, kaina dauke da adon ribons.
Amman Ni ina kulle a ɗaki mai duhu ana kasancewa da al'aurata na 'Ya mace da wanda ban sani ba.
Ana zaluntata.
A lokacin da yara yan uwana suke kallon Tom And Jerry.
Ni ana nuna mun abubuwan da basu kama ce ni ba a lokacin.
Batsa.
Kuma suna kara sanar da ni cewa kawai bidiyo ne na kallo.
Ina tunanin cewa yara na samun minti da chocolate ne lokacin da suka kammala nursery class za su shiga primary,ni kuwa ina samun su ne kawai a lokacin da wani mutumi yake son kwanciya dani a gado tare da sharadin kar in fadawa kowa.
Ban da muryar fada, kuma bana da muryar furtawa.
Har yanzu ni yarinya ce,duk da cewa yarintata ta jima da ɓacewa aguna.
Mai makon kasancewa 'Yarinyar da ake tarairaya na zamto yarinya da ke kallon kowa tamkar dodo.
Kawu na ya zamto mun zaki wanda inna ganshi zan iya rasa tunani tsabar dimaucewa.
Maimakon ya kasance karfina shi ne ya kasance babban rauni a gareni.
Ina jin labarin sunan makaranta amman ban ma san ya take ba.
Wani kala ne da ita?
Sannan me ake yi acen?
Ina ganin Yara sa annina suna wasa fuskarsu fal walwala.
Ina mamakin yadda a ka yi suke samun wannan damar da kuma 'Yanci.
Ko da yake
Ni da nake rayuwa cikin keji.
Ban da madubin kallon kaina bare insan ya nake kuma ni wace ce.
Raɗadi ne fal a zuciyata.
Gangar jikina kuwa ciwuka ne zalla.
Mahaifiyata ta rasu.
Ban sani ba,ko wanda nake tare da shi mahaifina bane ko Aa.
Kowa ta rayuwarsa yake sam ba a damu dani ba.
Ba mai kallona bare batun a share mun hawayen da ke kwance a fuskata a kullum.
Ban san dadin rayuwa ba, sai dai in hango wasu na yi.
Na kan ji cewa ni ba kamar kowa ba ce.
Kakata kuwa tayi tsufan da take buƙatar taimako, ba za ta iya yi mun komai ba.
Ina rayuwa da shugaba wanda bai da zuciyar ɗan Adam sam.
Wani lokacin ina ji a azuciyata tamkar ina da hannu a mutuwar Mahaifiyata.
Na tambayi kaina
Yaushe ta bar ni.
Kuma
Me yasa ta bar ni?
A lokacin da nafi bukatar kasancewa da ita.
A duk lokacin da na yi kokarin guduwa ana mun dukan kawu wuƙa.
Dole in rayu cikin ƙunci.
A lokacin da Yara yan uwana suke kara samun kulawa daga wajen iyayensu domin ingata masu rayuwa,
A lokacin ni kuma kawuna ya bada ni kacokan ga wannan mutumin ya manta da karancin shekaru na shekara shida aduniya ko in ce shi da matarsa idonsu ya disashe,ta zuga shi kan cewa lallai dole ya aurar da ni ko in ce saidani domin ba shi da karfin da zai iya daukan nawainiyata da kuma na kakata.
duk da cewa bai so ba amman ita ta dunga kara tunzura shi.
shi kan cewa ya aurar dani a hakan tunda mutumin ya nuna yana sona, an rage masu nauyi.
Ina da shekara goma sha hudu ɗauke nake da yara biyu, ina rayuwa cikin azaba da galabaita, da sunan da an aurar dani ne amman kowanni irin namiji ya zo zai biya shi kudi ya kwanta dani.
ni da ya kamata na kasance 'Ya na zama Uwa.
Wa zai lura dani bare kuma 'Ya'Yana?
Na zam tamkar kwanon zuba abinci, in wannan ya yi amfani da ni yau gobe wani ne.
Kuka nake ba yadda na iya.
haka aka maidani tamkar jaka.
Duk da hakan ban rasa rayuwata ba.
Har yau ina raye.
A taimaki rayuwata.
Don Allah ina so in rayuwa kuma in girma.
Ban da karfin gwiwa.
Ban da wanda zai taimake ni.
Ina bukatar taimako a rayuwa ta da ta kasance mara amfani.
Amman na tabbata kuma na yarda akwai wani wanda zai tallafa mun har ya bani gwarin gwiwar yin sabuwar rayuwa.
WA ZAI TAIMAKE NI YA BA WA RAYUWATA DA YARANA MA'ANA?
WA ZAI TALLAFA MANA MU RAYU KAMAR KOWA?


FATEEMA ZAHRA
(Indonesia)


★★
A kullum Mahaifiyata na fada mun cewa 'Ya mace Sarauniyace, Gimbiyace kuma abar tarairaya ce, na Yarda da hakan kuma na aminci,amman kash anawa bangaren 'Ya mace ke kokarin tarwatsa mun rayuwata.
'Ya mace ke kokarin Ruguza mun ginin da na gina don inganta rayuwata.
Munyi aure na SOYAYYA wanda a tunanina hakan shi zai ba mu damar yin ingantacciyar rayuwar aure,ashe bahaggon tunani na ne ya bani hakan.
Matata ce Amman ta maidani tamkar Ɗanta Kodayake Ɗan da ta haifa ma ba za ta mai hakan ba.
Bana da iko da gida na bare matar da na aure.
Hatta kai ta kawo ban isa ince zan kasance da ita ba,bana ma da bakin furtawa har sai ranar da ta ji tana bukata ta, haka zata zo tayi abun da ranta ke so ni kuwa bana da bakin magana.
Na zama gunki.
Na zama shara.
A lokacin da za ka ga mata da miji na walwala cikin nishadi suna cin abinci ni ina kitchen ina girki da aikin gida wanda ita ya dace ta yi.
A lokacin da uwa take ba da lokacin ta ga yaron ta haifa
Tawa matar ta watsar da shi ta ci gaba da sabgoginta.
A cewarta ai Ɗana ne.
Ta mun mai wuyar tunda ya zo duniya.
Ban da Muryar kai ƙara ko faɗa.
Ko da na furta maganar dai ɗaya ce Mahaifiyata na kara maimaita mun mace abar tarairaya ce.
Ɗana ya taso ba tare da shakuwa da mahaifiyarsa ba, a takaice ma nuna tsanarsa yake gareta ƙarara.
Ya zam shi ne mai iya buɗe baki ya furta mata cewa ba ta yi daidai ba.
Duk da karancin shekarunsa.
Na zama kurma.
Tsoro ya hanani iya aikata komai.
Bana da katabus bana da walwala.
Har ta kai ta kawo matata na iya daga hannu ta mareni.
Sai dai in zubda hawayen takaici amman babu halin ramawa.
A karshe ma watarana da ta mareni na rike mata hannu kirawo mun jami'an tsaro tayi don hannunta ya yi ja.
Adole naci zarafinta.
Na daketa a matsayinta na 'Ya mace.
Ranar a ofishinsu na kwana,cikin duhu da sauro,ga sanyi.
Agun Ɗana kawai na ke jin sanyi tare da dadi arai.
Bana da muryar da zan fito duniya in fada halin da nake ciki za amun kallon cewa na zubda mazantakata na zam mara amfani kuma asararren Ɗa namiji,wani ɓangaren kuwa za amun kallon mara hakuri ne wanda ya kasa tarairayar Matarsa,na tabbaatar akwai yan uwana maza da yawa da suke fuskantar wannan kalubalen amman basa da Muryar dagawa aji, ina so zan yi amfani da muryata tare da aran Muryan sauran yan uwana in fito da boyayyen kuncin da aka dasa mana cikin ranmu.

ZAN DAGA MURYATA KUMA NA TABBATA DOLE A JI SANNAN DOLE A GIRGIZA.

IBRAHIM KHALEEL
(Uk)

★★★Zaune Zahra take gaban murhu tana girki, ga tsohon ciki, duk wanda ya yi mata kallo ɗaya sai yaji tausayinta gami da yanayin da take ciki.
Tafiya take da kyar domin jan kafafunma kawai take.
Sai da ta kammala girkin nan tsaf ta zuba a foodflask.
Ji tayi tana jin wata irin azabbiyar yunwa hakan ya sa ta janyo tukunyar gabanta domin cin sauran da ya rage.

Ta ɗiɓo tana kokarin kawai baki kenan kamar daga sama aka bige mata hannu ya zube a ƙasa tare da fisge tukunyar.

Dagowan da za ta yi Adams ne tsaye gabanta yana sakin tsaki, "ni sa ankine da zan saki girki ki gama kuma ki fara ci ba tare da na baki ba? Wai ke wacce irin mayyace ce ?"

Hawayene kawai ya fara Ambaliya a idanunta.

Sukunyar da kai tayi domin tasan ko da ta dago ba ta da abun da za ta yi , a karshe ma zata iya janyowa kanta dukan da sai tayi dana sanin zuwa duniya.

A fusace ya kara kallonta yana nuna mata ɗaki.
"Maza ki shiga kiyi wanka domin akwai bakon da muka yi da shi zai zo,ki tabbatar kin tsabtace wannan kazamin jikin naki kada ya zo ya kasa abun da ya kawosa,kuma Wallahi in baki masa tarɓa mai kyau ba kin fi kowa sanin sauran."

Haka ta ja jiki ta shige tare da janye Anitha da ke kwance a ƙasan kitchen din.

Ba yadda ta iya haka ta shiga ta kwantar da ita.
Sannan ta shiga tayi wanka.
Hawaye ya kasa tsayawa daga idanunta.

Kamar yadda ya furta kuwa haka wannan bakon ya zo.
A kunnenta suka yi ciniki ya biyasa sannan ya ba shi umarnin kwanciya da ita.
Ba ta da karfin bijirewa.
Haka ta mika kanta ya yi duk abun da ya ke da muradi sannan ya tashi ya tafi yana washe baki.

Shi kuwa Adams budurwarsa Nusy ya kira.
Ganin idon Zahra suke duk abun da suka ga dama a bayyane.
Kawar da kanta tayi ta fice waje ta zauna domin azabar yunwar da take ji ya sa ta gagara bambamce abun da ke damunta.

Kamar an tsikareta ta fara jin mararta na ciwo.
Kokarin tashi ta yi amman sam ta kasa.
Jin abu na kokarin fito mata ne yasata sakin wata ƙara.
A firgice Adams da Nusy suka fito
Nusy na zuwa ta ce, "kamar fa haihuwa ne,ina tunanin ya ci mu kaita asibiti."

Kawar da kansa ya yi yana, "Akanta zan biya kudin asibiti?
Lallai ma,in zaki iya kawai ki tallafa mata."

Ban da kuka da cizon harshe ba abun da Zahra ke yi, Anitha ma da ke gefenta kukan kawai take.

Dakyar Nusy ta tallafa mata ta haihu ta yanke mata cibiya sannan suka tafi suka ci gaba harkarsu.

Haka zahra ta rarrafa ta nemo ruwa ta wanke jinjirar sannan ita ma ta wanke jikinta duk da ciwon cikin da take fama da shi.

Nusy ce ta tausaya mata ta kawo mata sauran abincin da suka rage tare da ruwan Lipton.

Tamkar mahaukaciya Zahra ke ci tsabar yunwar da ta riga ta daki hanjin cikinta.



*A CI GABA KO A TSAYA? SHARHIN KU NA DA MATUKAR MAHIMMANCI DOMIN CI GABAN LITTAFIN NAN*

08103080717

Urs Xayyeesherthou
[9/3, 5:56 PM] My Number: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-3

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_A Shawarce Duk Wa inda suka fara bibiyar *FREEYA* in dai basu karanta *YEL* ba su nema su karanta domin dukkaninsu bangaren juna ne_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Mtn Data At Affordable Prince_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Sai da ta ci ta koshi tukun ta hau gyaran gidan,inda ta bata.

Sallah tayi kafin ta zauna tana tunanin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki, ga yara biyu wanda take kallon duk amakwafinta za su dauwama indai bata samu wanda zai kawo mata dauki ba.


★★Kwance yake yana barci, kamar daga sama Khaleel ya ji ruwan sanyi a fuskarsa, a razane ya farka yana fadin, "Innallillahi wa inna illar raji'un." In da sabo ya saba amman ba a taɓa sabo da wahala bare Wulaƙanci.

Kallon kaskanci take masa tana fadin, "Ka kwanta kana barci,nufinka don yau baka da aiki shine ya kasance ni ce baiwa da zanta aikin gida? Ka san wannan ba mai sabuwa bane domin ni ba baiwarka ba ce, ban zo na zauna don a mulkeni ba, zai fi kyau ka tashi ga danka can yana kukan yunwa ka ji da shi sannan ka daura mana break tunda dai ni ba baiwarku ba ce."

Ta karasa maganar tana masa wani irin wulakantaccen kallo.

Har aran Khaleel ya ji zafin abun da Sarah tai masa, Amman ya tsinci kansa da kawar da kai tare da jin cewa ba zai iya ja da ita ba.
Goge fuskarsa ya yi sannan ya sauko daga gadon.

Ita kuwa hotuna ta shiga dauka da wayar hannunta tana tafiya tana waƙa.

Ba tare da ya ce mata uffan ba ya nufi kitchen, ruwan zafi ya daura yana yi ya damawa Noor formula sannan ya zo ya dauke sa ya bashi ya masa wanka sai da ya samu ya yi barci tukun ya kara komawa kitchen din domin hada masu kayan break.

Gaɓadaya aikin ya masa yawa kuma babu damar kinyi ko bijirewa cibi ya zama ƙari.
Haka ya gama hada kayan break din ya gyara kitchen din sannan ya koma falon ma gyara da bedroom din Sarah da na shi.

Sarah Na break hankalinta kwance shi ko yana aiki yana tunani tare da mamaki cike da zillimin cewa shin haka maza suke fuskantar kalubale a rayuwar aure? Shin basa da muryar furtawa ne , mene ne zai sa kullum ana fifita ɗiya mace kan namiji fadin cewa mace sarauniya ce shin namiji ba sarki bane shi ma?"

Da wannan sake-saken ya gama aiki tas kafin ya zauna ya yi nasa break din.

Noor ma na tashi ya kara dama masa Formula din ya basa kafin ya ci gaba da yi masa wasa.

Aransa kullum tausayin Noor yake domin sam bai san dimin jikin uwa ba,bare kuma kasancewa da ita.
Sarah bata damu da shi ba,bare kula da shi a kullum aikinta da kyale-kyalen rayuwa ne kawai gabanta.

★★Washegari.
Da Asuba Adams ya tashi Zahra kan cewa yana da baki da zasu zo ta tashi ta daura masu girki.

Ga jego ga yara biyu haka ta tashi ta shiga fara cuku-cukun abinci ba yadda ta iya.

Tana kammalawa ta hada masa duka awaje guda kamar yadda ta saba.
Ta yi wanka,ta ma Anitha da Anushka wanka ta sa masu kaya kafin ta fita gefen gidan ta zauna.

Daga ita har yaran yunwa suke ji amman ba yadda ta iya, Anushka na kuka ba ruwan nono,Anitha na kukan abinci, ga shi ita karan kanta yunwar take ji,tana kallon abinci amman ba damar ci.

Dabara ce tazo mata ta je ta ɗiɓo zallan farin ruwan zafi ta raba biyu ta sirkawa Anitha ta bata sannan ita ma ta sha mai dumin.
Dukkanin su ya dumama masu ciki,hakan ya ba ruwan nono damar zuwa kadan.
Ta samu ta bawa Anushka ita ma tayi shiru.
Dukanninsu suka yi barci rakabe agefe.
Tana kallonsu ban da hawaye ba abun da ke zuba daga Idanunta.
Aranta take fadin.
"Wani laifi na aikata? Shin wani laifi na aikata aduniyar nan da nake fuskantar cin zarafi ta kowanni ɓangare? Anya zan yi dariya kuwa? Akwai ranar da hawaye zai bar zuba daga idanuna kuwa? "
Nan take kuma ta share hawayen ta furta , "Tabbas in sha Allah watarana zan yi dariya kamar kowa da ikon Allah." Ji tayi furuncin na fita a bakinta ba tare da tasan dalilin hakan ba.


Shigowa ya yi da bakinsa yana sakin Murmurshi wanda baya taba wannan Murmurshin sai in har wasu sun kasance a gidan a kullum gareta fuskar zaki yake, ganin shi cikin fuska mai kyan gani sai dai hangi daga nesa ya yin da wasu suka kasance cikin gidan.

Suna hada ido da ita ya galla mata harara cikin sauri ta kau da kanta kasa, abokinsa ne ya ce, "Ah ka ce mutuniyar ta haihu, me aka samu."

Tsaki ya yi ya ce, "ba gashi ka gani ba, ni mu je ciki muyi abun da ya dace wannan shirmen yarinyar ba."

Su uku suka wuce suna kallonta tare da shi hudu.

Ɗayan sai satan kallonta yake yana suɗe baki tamkar ya ga gashashshen nama.

Suna shiga ciki bayan sun fara tattaunawa suna cin abinci,ban da koɗa girkin ba abun da suke, Adams nata kokarin basarwa Zahra na jin su ta yi shiru.

Kallon wanda ya zubawa Zahra ido Adams ya yi,ya ce, "Kai lafiya ya dai ko kana bukata ne?"

Suɗe baki ya kara yi yana kallon Zahra wacce idonta ke kasa ta kasa dagowa ya ce, "Gaskiya in zan samu ba zan ƙi ba, yanayin surarta kadai abun burgewa ne yarinya amman mai zubin manya, ba musu ko daga waje kasan raken kwai zaki."


Dariya Adams ya yi, yana "shege mutumina baka da Matsala indai ta wannan fannine, a wani farashi ka siya, kai kanka dai kasan wannan harkar ba karama ba ce."

Wata irin dariya ya yi,yana ciro masa wani bandir din kudi.
"Dauka kawai kasan ni bana wasa a wannan fannin mussamman inda nasan zan samu biyan bukata."

Shewa suka yi dukanninsu da sauran abokan.

Adams ya kwalawa Zahra kira tare da fadin, "ki kawo yaran nan ki kwantar da su,sannan ki shige daki ana bidarki maza maza."


Ba yadda ta iya haka ta kwantar da su Anitha afalon ta shige cikin dakin, tunda ta shiga ta cire kaya bata kara wani motsi ba har sai da ya yi abun da ya yi niya ya kamala,ya shige toilet.

Tamkar gawa gangar jikinta yake,illa fuskarta da ke zubda hawaye wanda ya xame matar tamkar jiki.

Fita ya yi yana washe baki tare da fadin, "kai Abokina amman kai kwarone,kana da irin wannan agida kake neman wasu? Anya baza mu yi ciniki mai girma ba ta danje ta mun ko kwana biyune, gaskiya ta mun,fiye da zato ko tsammani."


Dariya Adams ya yi,yana, "kar ka ji komai,indai wannan ce har sai ka gaji da ita indai baxa ka yi kasa a gwiwa ba wajen bani abun Duniya."

Da kyar ta sauka a gadon ta nufi toilet,tunawa ta yi da wani jawabin da ta gani a tv kan cewa mata in sun haihu suna shiga cikin ruwan zafi da gishiri.

Hakan yasa tai saurin dibo gishiri ta zuba cikin ruwan ita ma ta shiga.
Sai da ta tabbatar ya gasata duk da raɗaɗin da take ji kafin ta fita, nan ko taji jikinta ya dan yi mata karfi.


Su kuwa ko ajikinsu suna ta shagalin su da sheƙa ayarsu hankali kwance.

Sai da suka gama cacarsu suka fice, Zahra na ji da sauri ta zo ta,tattara sauran abincin da kowannensu ya rage a flet ta hada waje ɗaya.

Ci ta fara yi cikin sauri, ba dan ta koshi ba ta tuna cewa Anitha bata ci abinci ba, ta dauko leda ta zuba ta boye mata.

Kayayyakin da suka bata ta kai kitchen ta shiga wankewa.

Anitha ta tashi tana ta kuka bata ji ba,Adams na shigowa ya fara masifa yana kwalla mata kira.

"Wai ke wacce irin matsiyaciya ce? Kin bar mun yarinya na kuka ga shi ta mun fitsari akan kujera?"

A fusace ya shige kitchen din ya fara dukanta yana mari.

"Wallahii ke da kazaman 'Ya'yanki ba zaku bata mun gida ba,ban san tsautsayin da yasa na baki izinin sanya su akan kujera ba,gwanda kuta zaman a kasan shi yafi dacewa da kazantar ku."


Sai da ya jibgeta son ransa kafin ya bari.

Zuwa tayi ta dauke Anitha ta wanke kujerar tas, sannan ta goya Anushka.

Wajen da suka saba rakaɓa taje ta zauna,ta ba Anitha sauran abincin ta ci.


*Uk*
★★Zaune yake yana kallon Tv wani Malami na wa'azi.

Ya ce, "Aduk Lokacin da kake da wata bukata kowacce iri ce karanta wannan adduar _*Rabbie-Innee Lima Anzalta Ilayya Min Khairin Faqeer.*_
("My Lord Indeed I Am For Whatever Good You Would Send Down To Me,In Need.")

Maimaita Addu'ar Khaleel ya yi,yana dauko littafi tare da rubutawa.

Aransa kadai ya ji dadin karanta addu'ar a lokacin kadan bare kuma ya kasance jiɓanci yinta a lukuta da dama.

Tabbas saukin Ubangiji na tare da mu,aduk

Please Login or Register in order to submit comment