Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi.

          Lumshe idanun shi yayi lokacin da ake diban jinin, ana gamawa ya mike tare da jingina da bangon dakin, yana sauke ajiyar zuciya, sai da yakai minti ashirin da biyar, kafin ya sauka ya kira Abokin shi Brrst Usman Kamfut, ya kai shi gida. Kota kan Noorh bai bi ba.

         --- kwana biyu kacal yayi bai leko ko falon shi ba, Haroon yake mishi kome, tare da kai mishi abincin shi, da duk wani abinda yake bukata, yana kuma bibiyar lafiyar Noorh, daga gidan shi, shiryawa yayi yau cikin kananun kaya sannan ya nufi gidan su. Da kafa yake takawa, hango motar Nazzir yayi. Ya dauke kanshi kamar bai ga gidan su ba.

      Har yazo zai wuce, Nazzir yace mishi.
"Lion!"
Kallo daya yayi mishi tare da murmushin ina jinka.
"Baka ji labarin an rufe Kamfanin bane?"
"Ni na tura musu da a rufe Kamfanin bayan na saka an biya mutanen da suke aiki da kamfanin Hakkokin su."

     "Amma kaji labarin mutuwar yarinyar nan? Da fatan babu hannunka a cikin?"
Wani irin jan iska yayi tare da fesarwa, sannan ya wuce abinshi yana faɗin.
"Haka nima naji!"
"Wai meye nayi maka ne?"
"Me yasa kake zargin kanka?"
"Ni kuma? Akan me zan zargi kaina bayan kai ne kake nuna min halin ko in kula!"
"Toh shikenan daga yau zan na kulaka."
Daga haka ya wuce abun shi, cikin bakin ciki da damuwa yabi bayan Mahir da harara, kome nashi sai ya nuna iko akai,nan gaba ma sai ya nunawa duniya shine yake juya mutane.

     Da wannan ya kad'a kai yayi tare da shigewa gidan shi yayi dan ya dauko wata kodaddiyar yarinya ce, zai rage dare da Ita.
  •••Sosai ya tsakuri abincin da aka dafa mishi, yana ci abincin Zoolfa da Kanwar shi suka shigo gidan, hango shi a saman table yasa suka nutsu, yana gamawa ya mike tare da ɗaukar wayar shi da Key din Motar Ummi, ya juya zai fita, ya juyo muryan Zoolfa tana faɗin.
"Allah kasa Ya Mahir ya aure ni!"
Wani karamin murmushi yayi, sannan ya juya tare da kallonta, a tsorace ta sunkuyar da kanta.

     Sanan ya saka kai ya fita, a ranshi yace. "Faduwa tazo dai dai da zama"
Sannan ya fice daga gidan baki daya, yana kara nazarin yadda zai duba masu bin bayan shi.

    .. lokacin da ya isa asibitin ya same ta, ta farka, kanta sunkuye sumar kanta ya basu a fuskarta da kafad'arta, yadda yake ɗaukar idanu ya sashi nazarin yanayin jinsin mutanen da tafito, kallon kafad'ar ta yayi wanda yake waje, sai rigar da wandon da aka saka mata, a kai kaice yake hango tudun kirjinta, da yadda dukiyar fulaninta ya taso cur, har wani kara tsini suka yi, ga bakin yayi wani daukar ido a cikin rigar, dukar goshinsa yayi cikin nutsuwa, sannan ya isa gabanta yaja kujeran dakin ya zauna tare da Crossing leg din shi.
"Zombia!"
D'ago kai tayi kamar tasan sunan nata ne,
Tashi yayi tare da tattara mata gashin kanta, ya kai bayanta ya kalli yadda idanunta suka yi jajjur.
Rike hannun ta yayi ya kwace tare da yin baya, kallonta yayi yadda take murza yatsun hannunta, rike hannun yayi ta nemi kwacewa, ya kuma rikewa, ihu ta fasa mishi tare da niman faduwa, nurse suka shigo da Dr.
"Ku bani Alluran!"
Ihun take tana kokarin kwacewa, tare da kai musu duka. Idan yakai alluran zai mata sai ta kai musu dukkan tare da fasa ihu, a hankali ya taso, sannan ya isa gurin su, ture hannunsu yayi sannan ya rungume ta, tana ihu, tana kome, haka ya daura kanta a kirjinshi, kuka tasaka tare da shasheka.
"Ayna Ammyn! Waina Abbi! Muhabub! Nimrah!"

"Tab'jam! Dr mike faruwa kuma?"
"Kamar ta manta wasu abinda ya faru ne ko nace kamar akwai wani boyayyen matsalar da ta sami brain ɗinta, domin tinda ta farka bata magana kuma bata cewa kowa kome, sai dai Kamar larabci ne kawai take."

          Komawa tayi ta kwanta,.tuni barci ya dauketa,.kallon kafar da aka daure yayi, tare da bin zararran yatsun kafarta da ido, ajiyar zuciya ya sauke, sannan yace.
"Ko zaku bincika brain ɗinta, bana son wani abu ya same ta?"

     Yadda yayi maganar zaka Fahimci daga kasar zuciyar shi yayi, gyada kai Dr yayi take ya bada umarnin a kaita dakin bincike, tare da mahir ɗin hada hannun shi yayi yana zirga zirga, ya kasa tsayuwa guri guda, zunzurutun tashin hankali, tsoron shi karta sami matsalar da zai iya shafar rayuwarta da tayi abaya, yana bukatar wani abu daga gareta, matukar haka ya faru, Tabbas ya kwala kai kuma yayi biyu babu, domin bai da yadda zai dawo da kamfanin shi.
             A hankali ake dauko hoton ƙwaƙwalwar ta, suna exam dinshi. Sun kai awa daya da rabi ana abu daya, haka zasu duba dubawa, can Allah ya taimaka suka fara samun abinda suke bukata, kallon juna Dr suka yi da wasu abokan aikin shi, sannan suka kalli Mahir, dayan su yace.
"Sake duba mana ciwon ya kai tsawon wani lokaci ne?"
Sake zooming suka yi suka ci-gaba da aikin su. Jikin mahir yayi mugun sanyi, yana kallon yadda suke tattaunawa akan matsalar ta.
"Amma abin da tashin hankali, tsawon wannan lokacin babu wani treatment? Baka ganin zai iya zama cancer?"
"Wannan wani irin shirme ne?!"
"Sir Mahir! Ka nutsu akwai matsala"
Sake dubawa suka dayan yace.
"Gaskiya ya jima! Kuma bai wani samun kulawar Asibiti ba, da ace an sami haka ba mamaki ba zai zauna haka ba, kuma yanzun babban tashin hankalin matukar ta farka tana bukatar wani na jikinta. Domin haka ne kawai zai rage mata tasirin ciwon, domin ya tab'a wancan gefen ƙwaƙwalwar ta, cizon karen nan ne ya dawo da shi sabo."

   "Wai me kuke nufi dani ne? Meye ya same ta? Ba zaku gaya min ba?" Ya faɗa a tsawace.
Dafa shi Dr yayi tare da bude baki zai mishi magana, ya ture hannun shi.
"Meye ya sami Noorhhhhh!"
"Sir, yarinyar ta sami Matsala ne muke hasashen tun da jimawa, abin bayi tasiri ba, sai cizon da kare yayi mata tare da buga kanta, shine karfin tasirin abun.

    Amma ka bincika mana wani abu ko zamu sami masalaha ga yadda zamu sha kan matsalarta, but am sorry, sabida any more zata iya samun da sai..."
"But me yasa kuke magana akan Cancer?"....🤨 A hankali dai makiya na kuma samun Approched. Indai dan Noorh ne kake tsawar ba zai hana idan ta tashi ta falla maka Iskancin ba..
[1/23, 11:09 AM] Addah Ramlat MANGA: https://my.w.tt/zaUNQPJWzcb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣1️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

    Alhamdulillahi Ubangiji nagode maka da Ni'imar da kai min ☺️
*
"Wato ciwon ne ya koma yadda bazamu iya shawo kanshi lokaci guda ba, sai munyi takatsantsan kafin mu tab'a kanta, domin zaman kwayoyin halittar jininta ya haifar da yiwuwar cutar Cancer a gurin" inji Dr,

     Dafe keyar  shi yayi tare da fidda manyan idanun shi waje.
A lokaci guda zuciyar shi ta shiga wani irin lugude! "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun" yana ji kamar zuciyar shi zata fado, kallon tausayi yayi mata zuciyar shi tayi rauni, kallon yadda ta koma lallai Allah abin tsoron ne duk.wanda bai ji tsoron Allah ba yayi asarar dimun da'iman.

    Cikin abinda bai fi kwana goma ba, ji yadda yarinyar ta koma. Fesar da iskar bakin shi yayi tare da kallon shi yace.
"Ya zamu yi?"
"Za iya fita da ita waje!"
"Toh kana ganin babu matsala?"
"Bana tunanin haka, amma Insha Allah akwai nasara!"

A hankali ya taka har inda suka fito da ita, sannan yana kallon su, suka fitar da ita zuwa dakin da aka kwantar da ita. Karo na farko da yaji a ranshi yana son bibiyar alamarinta, taya ta tsinci kanta cikin wannan yanayin, dan haka abinda ya fara, fita yayi bai tsaya ba, yayi amfani da abinda tambayar da yayi mata suna cikin dajin nan.
*Ina zan kai ki?*
*Gidan Marayu na Jos*

     Wani irin huceccen numfashi ya fesar, kafin ya saka kai ya fita daga Asibitin abu daya yake son sani. Me yasa Baban Tasleem yayi watsi da ita, dan haka ya tashi jirgi zuwa Jos ba tare da b'ata lokaci ba, ya kira wani abokin kasuwancin shi, maitamakin Governor Bitrus Yam ne, yana gaya mishi gashi nan zuwa, tuni aka baza jami'an tsaron sojoji da yan sanda.

      Tafiyar awa daya ta isar dashi garin jos, cikin farin ciki suka gaisa da juna, yace mishi.
"Da fatan zuwan ka zai zame mana Alkhairi."
"Insha Allah ba zai zama sharri ba, Mr Yam.

    Gaya mishi abinda ya kawo shi yayi, cikin azama ya kuwa dauke shi tare da jagorancin P.A d'inshi suka tafi har gidan Marayun.

             Tunda ya shiga gidan yake zubda kwalla, musamman yadda yaga yaran,  Mahir mutum ne mai raunin zuciya, da zaran yaga abu me tausayi sai ya zubda kwalla, kallon yaran yake cikin sanyin jiki, a hankali ya isa Office din shugaban gidan. Bayan sun gaisa sannan yace mishi.
"Suna na!"
"MAHIR Hamoud Boualem CEO na MHB Foods ko?"
Lashe bakin shi yayi tare da sake wata irin murmushi, kafin ya gyara zama, yana lashe bakin shi.
"Ranka ya dad'e! Muna baka hakuri da abinda A'isha Omar Jimeta tayi! Ba laifinta bane,  halin da ta shiga ne na rayuwa, amma kuma sai gashi an sami labarin mutuwarta."

Lumshe idanun shi yayi kafin ya bude shi fess akan mutumin, yace.
"Babu kome na yafe mata, amma taya tazo gidan nan?"

        "Sir Mahir Hamoud Boualem, na yarda da kai shi yasa zan gaya maka abinda ya faru da A'isha, gashi kuma akwai wasu takardunta yana gurina.

2006

Bayan hatsarin da ya faru, daga hanyar jirgin kasa na jos zuwa garin Bununu na bauchi, mutane sun kone Wasu sun fada a ruwan bununu, dan haka lokacin da aka yi Report jirgin yayi hatsari garin cire mutanen muka sami wani mutum, wanda ya jikata.

     Mika min hannu yayi domin ina cikin yan agajin gaggawa na Red Cross. Mika min wata jaka yayi cikin wahalar azabar da yake ji.
"Nasan ko ya aka yi zata rayu, mune dai ba zamu rayu ba, ga hotonta nan, don Allah ka tayani mikata ga Hussain dina, don Allah karka sake ka bar mishi dukiyar dukka kai ma kayi kokarin daukar wani abu, don Allah rayuwarta nake son ta mike, burinta na zama likita ya tabbata, don Allah akwai wani diary,.akwai bayanin inda Dangin Uwarta suke tare da dangin mu.

     Duk da tarihin nada tsayi, amma ka bata Insha Allah zata fahimci kome. Nagode sosai"

      "Yallabai ka tsaya bari a kawo maka dauki, zak..." Maganar da nake ne ya tsaya, sakamakon sauke numfashinsa,.alamar ya rasu, haka nakira al dauke shi, sannan muka bazama bin inda sauran mutanen suke, a lokacin da muke duba ta ne, muka same ta hannunta dana mahaifiyarta tare da na wani wanda bamu samu damar tab'a shi ba, hukumar Nema suka hana mu sakamakon cewa da suka yi da ne ga wani attajiri shima yana cikin tafiyar. Toh wallahi sun fadi sunan shi amma na manta gaskiya, dan haka dakyar muka raba hannun su, da A'isha wani abinda zai baka mamaki hannun Mamanta yana saman nasu, ita da mutumin, amma kuma basu ga juna ba, haka muka dauke su A'isha Omar wacce muke tunanin ma ta mutu, sai da aka dai ta Jos aka tabbatar tana raye. Tunda aka kaita take barci.

      Kwana da kwanaki, tun muna kirga kwanakin har muka shiga bashi watanin, karshe dai a cikin kayanta muka ga wani katon abin hannun Daham, mun so sayar da shi, Allah sarki Madam Mary, ita ta hananu.

A cikin Baitul Malin gidan marayu muka kaita, asibiti ana aka shiga bincike, suka kuma tura mu Asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria,aka dubata nan ma suka kuma tura mu Kano, anan ka tabbatar mana da ta bugu ne a kanta, sai dai kuma barcin ne na lalura.

     Haka muka yi ta hidima da ita, har dai aka samu aka bata magani domin sun so mata aiki ne akwashe jinin dake gurin a mata wankin ƙwaƙwalwa. Haka bai samu ba, sai aka bata magani.
        Tunda muka dawo da ita, take samun kulawa dan har lokacin bata farka ba, sannan muka tura sakon har zuwa gurin Hussain Jimeta, abin haushi nan ya taro mana korafin shi da shi bai da shi, yana fama da babu fatara ce ke damun shi.

         Haka dai muka gama jin shi, sannan muka tura mishi da bayanin baban Noorh, nan ya sako kai yazo yana bamu hakuri da farko ban so a bishi ita ba, amma ganin ya kafe har da kaita asibitin dake garin lagos, aka dubata anan suka mata wani karamin aiki ta tashi, yana zuwa kawai naji a raina ban yarda dashi ba, dan haka yana zuwa aka bashi wani abu na cikin dukiyar sauran kuma Ni da kaina na kai banki na ajiye mata.

Tunda suka tafi na kasa samun nutsuwa ina yawan kai musu ziyara, a hankali ba fahimtaci yarinyar har yanzun bata samu sauki ba, dan zata jima tana kallon ka bata maka magana ba, idan zata yi magana Abinda zata ce Abbih Ammyn Mahbub da Nimrah, ko zama tayi zata yi ta dariya tana kiran su, wato tana ganin su suna mata gizo.

          Sau biyu ina zuwa ina samunta haka zaune a rana tana imagination din su, dan haka wani aikin kwalkwala da aka zo yi da kaina nazo gombe na dauketa aka kaita cikin ikon Allah aka dace, sai dai kuma ta manta kome nata, kuma su kanshi likitocin sun tabbatar da ciwon yana bukatar kulawa na duk bayan wata shida.

    Toh bayan na kawo ta gombe ne domin lokacin yana zaune a garin gombe, bayan wata shida da nazo daukarta muje naji sun koma Yola, nayi bakin ciki da takaici, daga nan na fara zargin akwai abinda ya saka shi guduwa da ita zuwa Yola.

          Toh abinda na samu bai wuce yadda wasu suke gaya min, ai mahaifin Noorh da Baban Tasleem yan uwane da iyayen su maza, suka zo daga wata ƙasa, dan suna  kama da larabawa, Amma iyayen su mata, yan nan Gombe ne.
Domin a wancan lokacin Ana samun auratayya tsakanin Fararen fata da bakaken fata, musamman lokacin da aka yi ta kwaso fararen fata suna zuwa aiki kasar nan,  domin suma likitoci ne, suka haɗu da kakar Noorh Shatu, tare da kakar Tasleem Denaijo, domin kakan Tasleem da Kakan A'isha abokan juna ne,ganin yadda suke kama da juna yasa ake zargin jini daya ne.
Dr Muhid Almukutuom tare da Dr Muhammad Aatiq.  Toh an sami matsala da yasa Suka bar Gombe suka koma Yola, inda suka sauka a garin Jimeta.

             Dogon tarihi, kafin dai suka haihu, kusan lokaci guda, i da aka sanyawa Yaran Hassan da Hussaini, toh daga nan kuma suka kuma dawowa gombe baki daya, lokacin yaran su sun kai fara karatu. Abubuwan sun faru, amma kuma wasu ba zance nasan su ba. Sai dai wannan diary din ya warware maka matsalar, bayan wani lokaci naje Yola domin duba A'isha, amma ban sami labarin ta ba.

     Amma kuma ina jin  jikina ciwon A'isha bai sami kulawa ba, sakamakon yadda ake wofantar da ita.

                 Ga takardun nan, ka duba zaka sami matsalarta tare da wasu abubuwan, amma ko lokacin da nake zuwa duba su, ina  yawan ganinta cikin kadaice da maraici wannan ya taka rawar gani a rayuwarta, ya kuma kara lalata kome, domin irin ciwonta yana bukatar kulawa tare da janta a jiki, a lokacin naso na basu sauran sakon mahaifinta amma ganin yadda take cikin damuwa kuma bata san kome ba, ya sani barin sai ta samu sauki kuma yata san wacece ita.

    Bayan shekara takwas na koma tare da bin makarantun sakandare da Jami'a anan na ganta a jami'ar Yola nan nake gabatar mata da kaina, toh da sauki amma karatun da na samu tana yi ba zab'in iyayenta bane da ita kanta, zab'in iyayen rikonta ne, a fakaice yarinyar tana shan wuya, kuma wani sa'in idan ciwon ya juya suma suna shan azaba, domin abin ya sata mugun rashin ji da taurin kai.

     Kuma koda can da take nan, bata cika shiga hayaniya ba, kasancewar muna jansu a jiki yasa ta sake da kowa, amma zaman ta a can ya kuma koyar da ita fanɗarewa, dan zai yi wuya bata saka kanta abu ba. Ko lokacin da na gaya mata wacece ita, tayi kuka sosai, na kuma sake mata magana muka je asibiti,anan na kuma fahimtar ciwonta ya kuma samun zama a jikinta. Da zaran zata shiga damuwa toh ciwon zai iya daukar wasu abubuwan ya aika mata jikinta, daga nan rashin hankali da kafiya zai wanzu a jikinta.

          Tunda likitan ya gaya min haka, naki gaya mata. Domin zata iya tsangwamar kanta. Da farkon rikicin ku naso na dakatar da ita, amma na Fahimci tana taya wani aiki ne, domin shima yazo har nan, lokacin da ya fara haduwa da ita, da hira ta gaya mishi ai ta zauna a Jos, nan gidan marayu. Da ban da shi ba, sai da ya haɗa Ni da ita, anan nake gaya mishi laluranta.

   Naga tashin hankali a idanun shi, domin kuwa ya gaya min taki ta saurare shi, nace ba laifin ta bane, sanya ta abinda kayi ne. Da ace baka bata wani abun da zai bata wahala ba da zata iya dauke kanta akan ka, sai gashi ka saka ta a gaba, ita kuma ta koma duk abinda yazo mata aikatawa take, daga baya mutuwarsa ya kuma dagula al'amurran ta,. Toh duk wannan aikin da kuma abun da nake gaya maka ya zama tarihi amma A'isha Omar Jimeta marainiya ce. Toh bayan ta tawo da ka fada ka sakata a Motar Jos, tun kafin ta iso aka fara zuwa niman labarinta,  Mr Mahir na yarda da kai ne yasa na baka tarihinta, bayan haka babu wani abu da ya rage zan iya maka."

             Ga baki daya ya dauke wuta, so yake ya tuno abinda ya faru shekaru sha biyu da suka wuce, amma ya kasa karshe kanshi daukar ciwo yayi, a hankali ya mike zufa na karyo mishi, yana kuma kallon lokacin da ya sakata aiki take kin yi, yasha kallon yadda take mishi kallon k'iyayyar shi, amma bai tab'a kawowa dan tana da tabo a rayuwar ta bane, ya dauka sabida rashin jituwar sune, ashe ita kam tana da nata damuwar ce.
"Bani takardun lafiyarta, sauran kuma ka ajiye zata zo da hannun ta, ta karb'a Insha Allah."
"Yarona tana raye ne?"
"Haka nake fata!"
Tashi yayi ya fita, bai dawo ba sai da ya kwashi kusan minti talatin ya dawo, yana karkad'e files din ya mika mishi tare da cewa.
"Kayi hakuri,ka kai mata kayanta domin akwai abinda nake ganin zata bukata a cikin littafin nan, don Allah karka ce min a'a indai kana fatan ta rayu."

Amsa yayi tare da mishi godiya, sannan yace mishi.
"Me kuke bukata a cikin koda yake bani Acct Number gidan."

   Babu musu ya ya bashi domin kowa yasan gidan marayu suna bukatar kulawa sosai. Dan haka ya tura Mishi kudin da sai da ya kasa magana, sannan suka fito shida Mataimakin gwamnan Jos, yake gaya mishi ai yarinyar tana raye, sannan baya son ya gaya mishi tana raye ne, domin babu makawa za a iya zuwa a tambaye shi. Idan bai gaya musu ba zasu iya kashe shi.

        Shi yasa yace mishi yana fatan haka, sannan ya bawa Mr Yam, damar ya nima musu babban fili su gina kamfanin lamon Kwalba.

  Da haka ya bar garin, cikin damuwa da alhini, koda ya iso lagos dare yayi gida ya wuce, sannan ya kira asibitin ya jikin Noorh, tunda ya isa gidan shi, ya sami abincin rana, kallon Haroon yayi tare da cewa.
"Ka nima min maganin ciwon kai, sannan da black coffee."

    "Sir Abincin da?"
"Barshi kawai" yace mishi a gajiye ya shige dakin shi, ya cire kayan shi, sannan ya nufi ban daki, ya dauki dogon lokaci a cikin bayin, sannan ya fito. Coffee ya samu, kafin ya gabatar da sallah da ake binshi,

Dakyar ya sha coffee din sannan ya kwanta, ya jima sosai yana juyi a gadon shi, tun ranar da yaga kirjin Noorh ya nemi nutsuwar shi ya rasa, gabaki daya ji yaƙe kome nashi ya tsaya cak, amma idan ya tuna halin da ta wurga shi sai yaji ya tsanarta, sai dai yau jin kome akanta ya sanya shi rage takaicin abinda tayi mishi.

  .     Kwanciya yayi yana juyi, a hankali ya kuma mik'ewa ya bude drower gadon shi,ya ciro wani roba me dauke da magani, ya haɗiye, sannan ya kora da ruwa,  komawa yayi ya jingina da gado, yana me nad'e hannun shi a kirji shi, lumshe idanun shi yayi. Yana kara nazarin yadda zai ɓullowa Al'amarin rayuwar shi, dole yaje Yola, domin yana son ya diba wasu abubuwan da A'isha Omar ta yi amfani dashi.

         Amma zai so sai tana cikin hankalin ta, dan haka koma ya kwanta sakamakon jin yadda jikin shi yayi sanyi, tare da kwantar mishi da kwalamar shi.

      ***
Tun karfe hudu ya farka tare da shiga ban daki yayi wanka, ba dan kome ba, sai dan yadda yayi wani mafarkin da ya dame shi, wai yana tarayya da Noorh, koda ya farka ya tashi ne ya samu ya jika jikin shi jagwab.

          Sannan ya koma ya sake ajiyar zuciya, kafin yayi wanka ya shimfid'a abin sallah..tare da tadda kabbara, raka'atun fijr ya gabatar,.yana zaune yaji masalacin da yake bakin Estate din su, ya fara kiran sallah shi... Dama na gaya muku muna biki🙏🏼
[1/23, 11:09 AM] Addah Ramlat MANGA: https://my.w.tt/CWCIoWRQBcb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣2️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

    Tunda aka yi sallah dashi, ya nufi gidan Ummi. Ya zauna kallon hanyar Kitchen din yake, a hankali ya nufa, ba tare da ya san cewa zai iya haka ba, kawai ya shiga aikin hada girki, tare da nutsuwa yana yi idan baka nutsu ba, zai yi wuya ka fahimci girki yake domin kome da yake cikin nutsuwa da sanin ya kamata yaƙe.
      Yana kome bakin shi bai fasa ambaton Allah ba, har ya gama ya goge kitchen ɗin tare da wanke kome da ya b'ata, mutum ne me yalwan tsafta, ko me zai yi zaka samu a tsaftace yake, hatta girkin sai da ya saka afro, yana gamawa ya nufi inda Ummi take ajiye warmes ɗinta masu shegen kyau, ya dauke ya juye abincin a cikin su. Sannan ya jera a cikin wani basket. Ya dauko tare da gyara ko ina ya bar kitchen ɗin.
     Idan baka ji kamshin girki ba, ko wuka aka saka maka zaka rantse kace bai yi kome a kitchen ɗin ba, sannan ya nufi gidan shi. Tunda ya shiga ya samu haroon yana gyara gidan, a sanyayye ya nufi Master bedroom din shi. Yana shiga ya ajiye abincin akan wani table, sannan ya nufi kitchen dan yaji yana kaurin girki.
Wanka yayi sosai, sannan ya saka kai ya fito daga ban dakin babu abinda ya dame shi domin babu kome a jikin shi kamar doya haka ya fito.
          Tsayawa yayi gaban mirror ya goge jikin shi da karamin towel, sannan ya shafe jikin shi da mai me dadin kamshi tare da turare me sanyin dadi, ya wuce closet d'inshi ya dauko riga da wando masu kyau da laushi na wani material na kasar Senegal. Ya saka dinki yayi mugun amsar shi.
        Gyara gashin sa yayi sannan ya dauki jar dara, ya saka a kanshi, take hular ta tsaya akan shi, kamar yadda Nasiru Sarkin waka, yake saka hular shi akan sumar shi.
            Simple shoe ya zura a kafar shi, sannan ya dauki basket ya fita dashi, key din black phantom ya dauka, tare da fita a nutse yana kallon yadda gidan ya dauki kamshin turaren wuta.
           A hankali yana motar tare da barin gidan bayan

Please Login or Register in order to submit comment