Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyara mata jikinta, suka mai da ita gadon.

           A hankali suke kula da ita, tare da bata magani da abincin da bazai kara mata karfin zubar jinin ba. Shi kuma Mahir baya zama sosai, yana can ana famar kasuwanci, amma idan ya dawo gare ta mantawa yake da kowa sai ita.

       Duk wanda ya ganshi yasan ya faɗa soyayyar Noorh amma ya kasa fahimtar kome akan haka, haka zai raba dare yana kallon ta, idan kuma idanunta biyu, haka zai sakata a gaba yana karatun Alqur'ani. Idan yana mata karatun nutsuwa take tana sauraron shi. Abinda ya Fahimta shine har yanzun bata rasa nutsuwar zuciya akan addininta ba. Dan ko sallah yake itama haka zata yi duk abinda yayi sai tayi. Kuma cikin nutsuwa da kamala. Wani abinda ya kuma kara mishi kwarin gwiwa akan ta, shine yadda take kame jikinta da kanta, bata cika dariya ko shiririta ba,.kawai dai idan larabci ya motsa ne zata cika mishi kunne da kiran Iyayen ta, da kanenta, sa zaran ta fara haka toh zuwa anjima zata suma. Kuma haka ya faru ne sakamakon shan maganin da ta fara.

       Dan haka ya mai da hankalin shi sosai akan kula da Ibadar su. After few one month, ta sami canji amma ba za ace wani abu ba, dan dai kawai tana nan sai haukar na raguwa, wanda ya haɗa da tasirin ibada da rokon ALLAH, duk da bokon da ya ratsa rayuwar shi, amma haka bai hana ya fahimtar dakai yana da ibada ba, dan mutum ne shima me yawan ibada, shi yasa Ubangiji yayi mishi iyaka da aikata masha'a, baya shan giya baya shan taba, shi mace bata gaban shi.

            Kuma baya damuwa da kallace kallacen batsa, Mahir bai damu da jin wakoki ba, abu daya zaka Fahimta a kanshi mutum ne me kishi da zafin niman na kanshi, duk inda zai zauna zaka samu yana da abun yi. Mutane suna ganin bai da mutunci, kuma ba haka bane kamewar shi, tare da bin tsarin da doka yasa ake ganin yana da zakewa.

          Kuma ko a gurin aiki ne yana yawan cewa, babu amfanin na baka hakkinka kaki sauke min nawa, ba zan maka hakuri akan hakkina ba, wannan yasa yake yawan koran ma'aikatan shi, amma kuma a haka yana musu ihsani. Toh basu gani yau da babu kamfanin zasu koka tunda yayi musu Alkhairi basu gani ba.

      •••
Yola.
Kwance take tana kallon dakin da take, yau kewar Noorh. Tashi tayi ta gangaro kasa, sanye take da wani doguwar riga me dogon hannu, amma kasar shi a tsage yake. Kana hango boxes ɗin ta fari kalar kayan, zuwa kirjinta kuwa, akwai botirin a rigar, sai dan igiyar da ta daure k'ugun ta fashi, yadda tayi kwalliyar kana ganin yan kananun boons ɗinta, a jikin rigar. Ta daura wani hular me kyau akanta.

Zama tayi Daddy ɗinta ya kalle ta, sannan yace mata.
"Ya dai baby Queen!"
"Babu dad mu yan wata ƙasa ce?"
Kallonta yayi sannan ya fara cin abincin shi.
"Dad tambayarka nake fa?" Ta faɗa tare da buga spoon din hannunta.
"Mahaifiyarki yar kasar nan ce, mu kuma annaba ne na kasar Algeria, Noorh kuma da iyayenta yan garin biskira ne, shi kenan!"

    Daga haka ya mike, kallon shi tayi cikin shagwaɓa tace.
"Dad yaushe zaka kai ni?"
"Idan kin gama Service."
   Daga haka ya fice daga gidan, ta zauna tana image yadda zata ga Zuri'ar su, dan haka cikin tsannanin farin ciki take shirya kome domin tasan idan ta tafi zata ga manyan masu kudin kasar kusan ba mamaki family ɗinta ne, haka ya saka take jin wani irin yanayi na shigar ta.

   And she promise idan ta fito one of large family house na kasar toh tabbas  sai taci Uwar Nazzir, dan haka take kallon yadda abubuwa zai tafi cikin jin dadi da farin ciki..And wat about Noorh? Idan kuma tana raye fa? Tabbas akwai matsala, domin idan taje Annaba sai taje taga yadda family ta suke.. tirkashi ga Mahir da Noorh! Mahir ya faɗa fa, Tasleem tana nata shirin cin Uban Nazzir, hmmmm
Yacin yawan Vote yawan page 🤨🤣 🙏🏼 Kuyi hakuri jiya anyi min rasuwa ne.....
[1/23, 11:09 AM] Addah Ramlat MANGA: https://www.wattpad.com/1004232557?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published

MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣5️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

Idanun ta ne ya kuma komawa kan bindin shi, tana kallon shi kamar taga dodo, ta leka sai kuma ta rufe fuskar ta, tana kuma lek'awa zata rufe fuskar ta.
Wandon ya dauka ya saka tare da xora jallabiyar shi ya bar mata d'akin, dan ya fahimci haukata shi take son yi.

     Ga yadda yake ganinta naked babu abinda zai hana shi bai farmata ba, kitchen ya nufa, har zai fara bada oda abinda za a girka mishi dan yasan Haroon zai iya zuwa da wuri, sai ya koma dan yasan ba karamin aikinta bane fitowa tsirara. Allah sarki tana can ta gaji har ta fara barci, rufeta yayi tare da gyara mata kwanciya. Sannan ya wuce daya dakin ya kwanta.
            Washi gari da safe, ya rigata tashi, har ya gama zai fita sai ya tuna babu kaya a jikinta, dan haka ya dawo ya saka mata kaya, tana barci sannan ya tashe ta tayi wanka da karyawa kafin ta sata tayi sallah. Tana idarwa ta fara barci. Sannan ya fita ya barta.
           Karfe sha biyu zata sha na rana, tun sha biyu saura ya dawo, ya bata sannan ya koma gurin aikin shi, haka ya bashi damar kulawa da ita, kuma sosai yake hakuri da kiriniyarta, domin wallahi bata jin magana.

    Ga barna kamar bera, sau uku tana fasa mishi Center table,  na farko wai ta hau zata zauna, tana cikin zama kawai taga ya canza channel din tv dake tana kallon Dora in Magic Land ne, kawai ta fasa ihu tare da tashi tsaye ta daka tsalle badan yana gurin ba da sai ta raunane, ya dauke ta, aikuwa ta shiga ya kushinsa tare da kai mishi duka, abin ya masifar b'ata mishi rai, dan haka yana sauke ta, ya dalla mata mari. Sai da ta dauke wuta a tsorace ta kalle shi.
"Uncle duka na! Ammyn Abbina."
Yadda tayi maganar shi kan shi sai da idanun shi ya cika da kwalla, wato abinda ya Fahimta duk da manta kome iyayenta suna makale a ranta rungumo ta yayi ta fashe da kuka.

    Rungume ta yayi, ta k'amk'ame shi tana goge fuskarta a jikin shi, daukarta yayi ya kai ta d'akin dan haka kawai yaji kamar zai yi baki, yana sakata a daki ya bata maganin barcin ta, ko minti biyar bayi da ita ba, yaji muryan Nazzir.

     Rufe kofar d'akin yayi, sannan ya fito kallon juna suka yi sannan ya koma ya shiga tattara Broking glass din falon, ya kai waje. Sannan ya dawo yana jin shirmen Nazzir, da ya gaji ya kwanta tare da daura daya akan daya, yace "mishi idan ka gama shirmen ka ina zaka iya rufe min kofar gidan."

         Haka na biyu, ma ta fasa wai zata yi wasan sauka da hawa, shima faɗowa tayi daga Center table din, na uku ne tayi a gaban Haroon, bai san tana gidan ba, lokacin da yaji karar fashewar abu a falon,.sama ne ya zo da dubawa yaga wata cutie face.

    .kamar ya zura da gudu, amma ya tsaya, tare da kallonta itama kallon tsoro ta mishi sannan ta gudu dakin ta, shiru yayi tare da cewa a ranshi yaushe tazo.
Dan haka da Mahir ya dawo bai san abinda ya faru ba, sai da tace mishi.
"Uncle! Wani yazo?"
Shiru yayi tare da kallonta kamar yana son tuna wani abu, kafin ya shiga dakin shi na aiki ya ga, ai Haroon ne bai kuma bin ta kanta ba, domin shiri yayi akanta a cikin gidan.

              ---
Yau asabar, wanda yayi dai dai da cikar su wata daya da dawowa ta tashi da ciwon mara, haka tayi ta birgima gashi harun ya tafi kwara, tun daga d'akinta take fama har ta fito falo, shi kuma yana can Gym room, haka ta yar yada mishi jiki tun daga falon farko na sama har falon kasa, kuma taki zama guri guda.

                 Sai kuka take tana niman Uncle, yana cikin daki yana faman d'aga karfe, jin sautin muryan ta yasa shi, fitowa, yana zuwa ya ganta zaune ji yayi zuciyar shi kamar zata fado kasa, domin daga ita sai pant da wata shimi, kamar ya fashe da kuka, yadda ta b'ata ko ina, da jini. Haka ya rikota suka nufi ban dakin falon kasa, ya cika da ruwa ya turata ciki, sannan ya koma kitchen ya nufi loundry ya dauko bokitin mopping ya ciko da ruwa, zunzurutun tashin zuciya, haka ya zuba hypo, Klin, izal da dettol, sannan ya zo ya fara goge falon yana yi yana yatsina fuska, yana jin da yau Noorh da hankalin ta zai tasha faɗa, dan ya tsani kazamta.

      Haka ya gama goge gidan tass, sanan ya dauko turarukan wuta duk ya saka, ya dauko rum frsh ya fesa, sannan yaje yayi wanka dan ji yaƙe kamar yayi yawo cikin jinin, sannan ya nufi ban dakin yayi mata wanka tare da nuna mata yadda zata yi tsarki, yana gamawa ya dauke ta suka nufi dakin ta, ya ajiyeta sannan ya fito ya rasa me zai mata, kawai ya koma dakin shi domin bata da pad.

            Wata riga ya saka mata tare da cewa yana zuwa, da sauri ya fita. Ganin ya fita ai kuwa ta fito daga inda ya ajiyeta ta fara barna,  tana zuwa kitchen ta kunna gas, tare da cika ruwa a tunkuyar non stick ta fara kokarin daurawa a kan gas sai ga Shibha tana sallama. Sake tukunyar tayi akan kafarta, dan tunda yazo gidan bata tab'a ganin mace ta shigo ba, da gudu ta bangaje shibha, ta haura sama, tana lekota. Ita kanta Shibha tsoro ya kamata balle Noorh.
         Akan lokaci ya dawo san bai jima ba, ya shigo gidan yayi turus.
"Waye yace kizo baki sanar min ba?"
Ya fada fuskar shi a tamke, da gudu Noorh ta sauko tare da buya a bayan shi yana sauke ajiyar zuciya, sai lokacin ya fara jin kamshin gas, a saba'in ya shige kitchen, yaga b'arnan da tayi tare ya rufe gas din ya fito ya rike kunnenta ihu take tare da yarfe hannunta, mikawa Shibha pad din yayi sannan yace mata.
"Wuce ki saka mata!"
Babu musu ta wuce, suna shiga dakin taga Noorh na mata wani irin kallo da gudu ta sauko abinta, ta gaya mishi da kanshi ya rakata ta, yana shiga dakin yaga zanin gadon duk sun b'aci da jini.
Kamar yayi ta zunduma ihu, haka yake ji, dakyat ya samu Kanwar shi ta gyara dakin, tana gamawa Noorh na b'atawa, cikin jin haushi tace.
"Wallahi ba zan zauna ba,guduwa gida zanyi ku Cigaba da kazamtar ku."

     Haushi ya kama shi sosai, domin yana ji yana gani ta b'ata ko ina, dan Allah yaso ya saya pad din me panta ne da bai san ya zai yi da Noorh ba.

            Kafin Shibha ta bar gidan, sai da tasha kashedi, sosai tare da jan kunne, aikuwa tana komawa gida,taja bakinta shiru, ta same su, suna jiran zuwan Azumi nan da wata biyar masu kyau.
         •••
Nazzir yana yawan zuwa gidan Mahir, tare da saka idanun shi, akan Mahir abinda da ta kai har Mahir ya hada shi da mahaifin shi, ya ja mishi kunne baya son hayaniya, amma yaki. kamar ya san Mahir yana boye mishi wani abu, shi kuma ya nace sai ya nima.
     ... Baby Queen kuwa suna gama Service ta uzurawa Dad, ya shirya har da Mommy suka nufi Annaba, garin su dake ƙasar Algeria. Duk da Sun isa da dare, bai hanata ganin yadda garin ya hadu ba, a wani hotel suna kwana, washi gari. Suka nufi garin su yana cikin garuruwan masu dinbun tarihi, dan haka ta dauki haka a matsayin Destination place, haka tayi ta daukar shi a hotona.

              Ba laifi Familyn baban ta suna da ƙarfin iko a garin, kuma suna rike, da madadin iko. Domin sune suke roling garin baki daya, haka ya saka mata wani irin izza, domin matsayin Mahaifinta ne, Kawun shi ya rike mishi, dake yana zuwa suka ce ba zai koma ba, dan haka suka bashi damar ya rike garin.

   Karku ga yadda kan Tasleem yayi wani irin kato, tare da jin ita wata ce, Mom duniya sabuwa, amma dake Dad me wayo ne yaki amsar mulkin, yace sai ya dawo zai amsa,  haka suka yi ta yawo a garin har na tsawon wata uku, sannan suka fara tattara nasu zasu dawo Naija, anan ne ta ji aranta taje taga Family Noorh.

     Lokacin da aka kaita biskira, har cikin gidan Kakannin Noorh sai da taji kamar zuciyarta zata buga, me yasa kome na Noorh sai an nuna mata fifiko akanta, Kanin Baban Noorh Me suna Dr Dr  hisham abdullah keluarga  shine Ministan lafiya na kasar Algeria, D'aya kanin shi Dr Nahid Abdullahi' keluarga shine matsayin Governor Biskira, ga wasu manyan manyan mukamai da suke rike dashi, bata kuma rudewa ba, sai da aka gaya mata ai Maman Noorh Familyn ne, sau uku ta shiga ban daki Zunzurutun cikinta ya tsirga, kamar ranta zai fita lokacin da ta gama fahimtar itace tazo duniya a zero  zata koma a empty. Bata yi kasa a gwiwa ba, ta gaya musu ay Noorh ta rasu. Sunyi kuka sosai domin a ranar aka fara zaman makokin Noorh. Kakar Noorh wacce suke kiranta Ummul Banun, tace ita bata yarda Noorh ta rasu ba, tana ji dai bata lafiya. Haka dai suka bar garin kwanan su daya, amma ba karamin shatara na arziki aka musu ba, domin sun san gaba da gabanta, duk sai ran Tasleem.ya fara b'aci, abinda bai kai faɗa bai sai fada da kuka. Ita me ya sa aka haifeta a karamin family, domin karamin me degree daya shine mata shi dan shekara ashirin da daya, daga masu degree biyu sai masu uku, kuka take tare da jin tsanar familyn ta.

           A cikin wannan yanayin suka dawo Annaba, suka hada kayan su, suka dawo Naija. Tare da burin dole ta nimo mijin da zata burge kowa, domin a yanzun babu wanda yasha gaban ta, shine target din ta na gaba.

       •••
Yau ma Shibha tazo gurin Noorh da katon teddy bear, sai kwalin chocolat, ai kuwa suka zauna a falo suka fara sha, suna gamawa,suka shiga kitchen. Akw shiga barna wai ana girki.
Flour da kayan miya sai da yaci uwar shi domin pancake suka watsa a kitchen ɗin, haka suka gama aka fito falo, aka kuma baje suna kallo ana cin pancake kafin kace kwabo an lalata falon an sauya mishi halitta launuka.

     Jin ana alamar ruwan sama, yasa Noorh, fita da mugun gudu. Ta faɗa wasa da ruwa, nan tana wanka tare da wasa da ruwa. Ita kan Shibha gyara ko ina tayi domin tasan idan yayan su ya dawo zata sha fada, kuma sake yarinyar na da nutsuwa haka ta gyara ko ina tsaf, sannan ta fito bata ganta ba, ashe ta zaga can bakin swimming pool, tana wankar a can, har Mahir ya dawo, kallon ko ina yayi alamar anci Uban gidan sosai, yadda ya balbale Shibha da fada dai dai shigowar Noorh gidan, zata jata suje suyi wanka. Taga Yasaka Shekara Shibha da a gaba da fada.
Kuka tasaka mishi tare da ture hannun shi.
"Uncle daina fada!" Ta ture shi tana kuka, mutuwar tsaye yayi sakamakon Jikewar da tayi daga samar har kasa, kayan jikin ta ya lafe a jikin ta, gashi wani irin yanayi kome na Jikinta sai da ya fito, kallon kasa yayi yadda take zubda jini, idan ya Fahimta pad din Jikinta ne ya jike jagwab.
Dauko lema yayi ya mikawa Shibha.
"Kar na kuma ganinki cikin gidan nan!"
"Yaya ka barni muyi hira da Aunty Noorh don Allah ba zan kuma ba zan zo da abincin mu ma"
"Ni zaki janyowa fitina Ummi tasan ina ajiye da Yar mutane, maza ki tattara kar na kuma gani ki!"
"Ni wallahi zan kuma dawowa!". Ta faɗa kasa kasa, tana fita yayi ciki da Noorh yarinyar nan tana son Haukata shi, dubi yadda kome nata yafito, maketa yayi tare da kaita daki yasata dole ta cire kayanta ya haɗa mata ruwan zafi, tayi wanka tare da hada mata ruwan zafin da zata sha.

                  Sabida kar mura ya kamata, tana fitowa ya bata pant ta saka, wanan ya mika mata kayanta, ita nan fushi take dashi har da wani b'ata rai, tare da juya mishi baya.

       Tana gama shiryawa ta fito tare da ɗaukar chocolat dinta ta fara ci, wasa wasa sai da ta cinye kusan rabi, yana fitowa ya samu ta cinye, buge mata baki yayi tare da cewa.
"Chocolat girl kawai!"
"Uncle bindinka kawai!"
Zaro idanu yayi waje, tare da rike bakin shi, wato tasan ta zage ka, itama. Make mata baki yayi ta bata magani tasha bayan ya bata abincin da yazo da shi, fir taki ci. Sabida sunci pancake.

          •••
"Aysar! Ina jin kamar Noorh tana raye, domin ban ji ta mutu ba, wancan bad guy din yaƙi bani damar muyi magana, ban san meye project din shi na gaba ba,"

    Gyara zama Aysar Haladu yayi tare da ɗaukar kwalbar ruwa yayi tare da sha, yana kallon Manager.
"Kuma kasan Mahaifiyarshi tana daga cikin manyan alkalan ƙasar nan, don haka bazamu tab'a lokaci guda ba. Dole sai mun san meye yake nufi da shirun da yayi"

    "Why him kept quiet? Shirun shi yayi yawa, me yasa ba zai yi magana ba, toh mu zamu yi Analysis wani abu da zai saka dole yayi magana!" Inji Manager,

    "Karku fara takalo shi! Nasan waye MAHIR! Idan aka takalo shi matukar ya fashe mune a ruwa, dan haka ku bari akwai lokuta da zamu tab'o shi kuma zai yi magana,"

     "Ya kake abu kamar kana jin tsoron shi ne?" Inji Aysar Haladu,
"Ba tsoron shi nake ba, nima umarni ake bani, idan na sab'a zan iya samun matsala."

   Shiru duk suka yi tare da mikewa, sannan suka bar gidan.
  Ya jima yana kallon yadda zai karya Mahir amma har yanzun bai Samu damar ba, amma Insha Allah next target din shi, sai ya kure shi. Sai yaji tsoron fitowa media ya kare akan shi. Sai ya mishi abinda ba zai tab'a mantawa ba.

         Dan haka ya ajiye abun a ranshi, tare da Cigaba da abinda yake gaban shi.
    •••
Tsaye yake yana gabatar da project din da yake bukata,  tana shigowa,ta kurawa abun ido, tayi kamar tana son tuna wani abu, kawai me zai faru, kawai ta juye mishi ruwan hannunta a samar project din, dama kan shi ya gama kuncewa tana zuwa ta kuma watsa mishi ruwa akai.

  Cikin wani irin yanayi ya kalle ta, ya rasa yadda zai yi da ita, dan haka yana juyawa, ya fincikota yayi waje da ita. Tare da rufeta a daki, yazo ya d'aga takardar yana kad'ewa, kamar ya tsalla ihu, yana shan iska, ya duba abin mamaki, sai ga abinda yake bukata da project, din ya fito yadda yake bukata, kallon kofar da take bugawa yayi cikin nutsuwa, murmushi yayi tare da bude kofar yaga tayi tsuru tsuru, cikin tsoron kar ya buge ta...
[1/23, 11:09 AM] Addah Ramlat MANGA: https://my.w.tt/xijcyGD1Gcb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣4️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

_Wadanan mutanen ba zan gama labarin nan ban gaida ku ba! Musamman Mum Sayeed da Maman sadeeq tare da Mom Ases! Maman Khadijah da Sadeeq! Zahrah Adda Ramlat! Tare da Naja'atu! Mamana Nanah, Maman Sultan, Fa'izah, Maman Areef  na grp din tare da Maman Meenat Untichlobanty⁩ Wassh Matan Quarts Iya Wuya muna tare 🤨🤩😍🔥_

A ɓangaren Nazzir kuwa yaso bin didigin Mahir, amma abu ya ci tura. Haka ya je har Yola ya bincika ko da gaske Noorh ta rasu, mutanen da yabawa aikin suka ce, Tabbas sun kona motar da zata Jos a ranar amma bai yarda da batun su ba. Dan haka ya nufi Jos, anan ya sami labarin mutuwar Noorh, tare da tabbatar mishi mareniya ce.

                Duk yadda yaso yaji wani abu a bakin shugaban gidan Marayun yaki cewa kome, dan haka ya bar gidan.
   •••
Hannun shi ya kai marar ta, yaga ta lumshe idanunta, kasancewar ta gama kwanakint hailarta,har ta shiga kwanakin kyankyasar kwan halittar mahaifa, sai abin ya sakata jin wani irin feelings sosai, tare da narke mishi, kallonta yayi sannan ya hura mata iskar bakin shi, tare da jan hancinta. Lumshe idanun tayi tare da sakar mishi jiki, ta lafe a jikin shi luf.

                Hannun shi ya saka a cikin rigarta yana wasa da kirjinta, sake narkewa tayi tana rike rigar shi, kamar zata sake mishi kuka, a hankali yake shafa jikinta, shi kanshi ya gama sauka akan hanyar da ya dace, lallubar fuskarta yayi tare da hada bakin su, ware idanunta tayi akan shi suna kallon juna, lumshe idanun tayi tare da cusa hannunta cikin gashin kanshi, tana yatsunawa. Ji yayi baki daya ya dauke wuta, ya dauki dogon lokaci yana dauke wannan yanayin tare da janyewa ya kyaleta sakamakon tuna mishi da zuciyar shi yayi cewa babu abinda yake tsakanin su sai gaba, kuma babu wani alaƙa na aure, shi da yake gudun kar a b'ata Kanwar shi zai b'ata yar wani.

      A hankali take sauke numfashi, ya kalli yadda idanun, sake mannewa tayi a jikin shi, tana sauke ajiyar zuciya tare da kwalla, shiru yayi yana kallon yadda take mutsu mutsu, sannan ya kalli agogon lokacin shan maganin ta ya kusa, tunda fita yawo suka yi, dan suna masaukin shi ne. Yana ganin ma idan ya koma da ita za a sallamo tane kawai kafin zuwan likitan, domin kashe kudin yayi yawa.

            Buɗe kyakyawan idanunta tayi, sannan yace mata..
"Zamu tafi asibiti."
Makale mishi kafada tayi, tare da tura baƙi gaba. Kai bakin shi yayi kan nata, a karon farko da ta fashe da dariya tana me fadawa kirjin shi, wani irin murmushi ya sauke, haka kawai yake jin kamar ita din mallakar shi ce.

    Gani yake kamar dama can, tashi ce, a yanzun da ya shaku da ita, yana matukar shakkar ranar da zata dawo hankalinta, bai san yadda zata amshi alaƙar su ba. Yana jinta har cikin ranshi,  gani yake kamar itace abinda ya rasa na tsawon shekaru da yake niman, yana ji kamar dama can da ita aka yi zuciyar shi, shi yasa yake kuma nanne mata, yana kuma manne mata, zai iya zama kome idan ta kama a kira shi kaska ya amince, dan ba zai iya daukar kasadar rabuwa da ita ba.

             Duk inda Danginta suke a duniya sai ya nimo mata su, ya kuma damka musu ita, kafin ya.
Sumbatar haɓɓar shi tayi wanda ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, tallafe fiskarta yayi ya haɗa nashi da nata, yana dariya, tare da jan hancinta da bakin shi.
"Mmmm!" Ta furta iya wuyarta, sake cizon bakin ta yayi ta kuma cewa.
"Hmm!"
Murmushi yayi cikin jin dadi,ya sumbaci goshinta, sannan ya mike tare da gyara mata kayan sanyin jikinta, ya gyara na shi suka fito, da gudu ta danne bayan shi, sosai fa. Saura kiris su zube a kasa, ya tsaya da kafarshi, juyota yayi tare da haɗe ta da jikin kofar. Kallon ta yayi yadda ta kafe shi da ido, sai da yaji tsigar jikin shi ya motsa sakamakon hango wasu irin sakonnin cikin idanunta, bakin shi ya kai bai san lokacin da ya fara squeezing kirjin ta ba, cikin wannan lamari na daban wanda shi kanshi sai da yaji mamakin yadda ya sauya lokaci guda, sosai ya haukace mata kamar yadda take

Please Login or Register in order to submit comment