Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an bude mishi get din gidan. Tare shi Nazzir yayi, tsaki yayi sannan ya tsaya tare da sauke glass din motar, kallon shi yayi tare da dauke kai.
"Lion! Jiya nazo baka nan kuma na kira wayarka, switchoff"
       Gyara zama yayi sannan yace mishi.
"Inda ka aike ni, Hamoud Boualem!"
Shiru yayi yana kallon Mahir, wato zunzurutun rashin mutunci ma da Abban shi ya haɗa shi.
"Toh kayi hakuri, zan raka ka!"
Wani irin kallon banza yayi mishi.
"Ko Ummi bata da ikon bina inda zani, balle kai karan kada miya, dilla bani hanya ko nabi kanka."
         "Wai Lion me kake takama dashi? Kana namiji ina namiji sai wani fisga kake min, uban me ka fini?"
       Jan motar shi yayi bai ma kuma tunanin ya bashi amsa ba, bude shi yayi da kura, sannan ya bar gidan baki daya. Cikin jin haushi ya shiga masifa, tare da rantsuwa sai ya cutar da Mahir sai ya lalata mishi kome.
         Kai tsaye Malam Mahir bai tsaya ko ina ba, sai Asibiti yana shiga ya tsayar da motar shi,  a hankali ya bude bayan motar ya dauko basket din abincin tare da wayar shi dake jikin chajin motar, sai key din motar ya saka a cikin aljuhun rigar shi, sannan ya shiga tafiya a hankali cikin nutsuwa. Zunzurutun yadda yake takun zaka dauka yanga ce ko kidifiri, a'a kawai tsabar miskilanci ne wanda a tafiyar ma sai anyi ta.
       Yadda yake shan kanshi zaka rantse Basarake ne, a'a Izzar kudi ne tare da jinin larabawa da yake gwaraye a cikin jikin shi, duk inda ya gifta nurse da drs mata bin shi suke da ido. Ba zaka tab'a cewa bai fahimci haka ba, sai dai yadda yake shan kamshi zai tabbatar maka da haka. Ganin haka ya kuma tsuke fuskar shi tam..har ya isa d'akin da take, wani karamin murmushi ya sauke tare da tura kofar da sallama, ana daru da ita tana musu larabci.
Tare da kai musu duka, kallon su yayi a hankali ya ajiye basket din. Ganin wani nurse namiji ya kai hannun shi kan k'ugun ta, cikin wani irin zafin nama,ya buge hannun!
         "Karka fara tab'a ta!" Ya daka mishi tsawa, tare da cewa su kyaleta, zai kira su idan ya gama bata abinci, suna fita yaga ta tsuguna a tsakiyar gadon, tana shashekar kuka. Abinci ya zuba mata, tare da saka cokali, ya taka a hankali har gabanta, kallon ta yayi tare da ajiye abincin ta kuma matsawa tare da dafe hannunta a saman gwiwarta.

      Gashin kanta ya watse a fuskarta da kirjinta, tattara sumar ya fara, tare da daure mata su baya, d'ago kai tayi tare da kuma takura kanta, a hankali ya cire mata belt din da aka daure mata kafa da hannun, ya rabata dasu. Sannan ya shiga ya zauna a bakin gadon yana kallon fuskarta wanda tafin hannu ya kwanta, a hankali yake bin jikinta da kallo, shiru yayi tare da kallon rigar jikinta da ya yage.
         Wanda ba yagewar haukata bane kamar yagewar karfi ne, a hankali ya Kum d'aga rigarta yaga shatin dukarta da akayi na cinyar da fuskarta ne ya saukar mishi da zargi ana yunkurin tab'a ta.
     Ita kuma tana gudun haka, shine yake zargin ana dukarta, jikin shi ne ya dauki mugun rawa, dan haka ya saka a ranshi zai spend yau gabaki daya a tare da ita. Dake asibitin kudi ne. Dan haka babu takura, sai ma zama da yayi ya tabbatar taci abinci, sannan ya fita shagon cikin asibitin da ita, tana ganin mutane zata shiga boye fuskarta a jikin shi. Hannunta rike da rigarshi ta baya.
              A haka suka shiga shagon kowa ya ganta sai ya koma gefe, ganin yadda mutane suke musu cin fuska yacewa masu shagon.
"Ka cewa kowa ya fita sai mun gama daukar abinda muka zo yi idan ba haka ba, toh zan saka Dr Harrison burg ya kore ka."

   Babu shiri aka kori mutane, ya zama daga shi sai ita, haka ya gama sayan kayan shi, wanda kusan nata ne, sai sani katon teddy bear da ta gani, yana dauko mata ta buga tsalle, tare da rungume shi, ajiyewa yayi tare da mika katin Atm din shi aka cire kudin sannan ya juya zai bar gurin, yaga wani  roba na chocolate, ya koma ya saya mata,ya manta ya saketa, aikuwa ta fice.
            Da sauri ya biya kudin yabi bayanta, hangota yayi tana boya a bayan Flower, tare da leken wannan nurse din da Mahir ya buge hannun shi, haka kawai zargin ya kuma dirsa a zuciyar shi, murmushi yayi tare da zuwa ya riko hannunta, kara ta saka ya zuba mata ido yayi.
"Muje!"
Bata fahimci abinda yake nufi ba, sai da yaja hannunta suka bar gurin, ya kaita d'akin sannan ya shiga ban dakin ya hada mata ruwan wanka, kafin ya dawo ya shiga ƙoƙarin cire mata kaya, anan ne ya fahimci ana niman tab'a ta, domin wani irin kuka take da zai cire mata kaya, tana kai mishi duka, da tirjiya tare da ture shi.

            Dakyar ya cire mata, rigar ya dauko wata shimi ya saka mata, sannan ya shiga cire wandon ta, anan ne ta yanka mishi cizo, rutsa idanun shi yayi tare da bude shi akanta, a hankali ya zare bakinta a kafad'ar shi, ya shammace ta tare da tab'a wuyarta take ta fara barci, da haka ya cire mata kayan ya kaita yayi mata wanka, sannan ya fito da ita, yana goge mata kayan jikinta da karamin towel,  a hankali yake kallon yadda kayan da yayi mata wanka dashi suka manne a jikinta, boons ɗinta ya fito sosai.

          Dauke kan shi yayi, ya goge mata kanta, sannan ya cire mata kayan.  Ya saka mata wata doguwar riga, sannan ya dauki kayan da kanshi ya wanke tass, bayan ya samu tana barci ya gama kome, sannan ya gyara mata kwanciyar ta, kafin ya bar dakin.
         Lokacin da ya fita, Office din Dr Harrson ya nufa, tunda ta shiga suka fara tattaunawa, har lokacin sallah azhar yayi, Mahir ya fita, tunda ya bar asibitin. Bai dawo ba sai karfe biyar sabida yasan ba zata farka da wuri ba, yana shigowa ya hango nurse din nan yana shiga d'akinta. Kiran Dr yayi shima kuma ya fito daga motar rike da kayan ciye ciye, yaje ya sami Dr suka nufi dakin.
                Ba zato ba tsammani, suka tura Kofar, sai samun mutumin suka yi yana yaye rigar Noorh sama, tare da kokarin sai ya zare boxes ɗin da Mahir ya saka mata.
          "Yayi kyau!" Da sauri ya sake kayan, tare da rufeta jikin shi na rawa, ya juya tare da rantsuwa babu abinda zai mata kawai duba ta ne,. Babu fada babu zagi, Oga Mahir ya kira sojoji. Suka tafi dashi.
       .Anan ya zauna a jikinta, Dr yayi ta bashi hakuri, yace mushi.
"Ai mun gama duba files din ta, har na tura can CANADA.
           Sannan zata iya samun sauki amma dole sai kunje, dai."
       Murmushi yayi, sannan yace.
"Ok! Amma zan shirya nan da kwanaki ƙalilan"
     Bayan sun gama tattaunawa ne, Dr ya fita. Zama yayi a bakin gadon yana kallonta, haka kawai yake son ta samu lafiya su Cigaba da fadar su, yana son ganin yadda take murguda baki tare da gatsina hancinta.
       Idan yace bayi kewar fadar su ba yayi karya, shi kanshi baya sanin lokacin da yake biye mata, amma tabbas sunyi shirme dayawa, wanda shi da girman shi ya biye mata, da ace bai biye mata da yau kusancin su bai kawo haka ba.
     Itace mutum na farko da ta tuna mishi da girman abinda yake aikatawa, itace mutum na farko da bai ga tsoron shi a kwayar idanun ta ba, kai tsaye take magana dashi babu tsoro tar a cikin idanunta. Murmushin gefen baki yayi sannan yace mata.
"Fitinaniya kawai!"
Yana zaune har aka kira sallah, sannan ya nufi masalacin asibitin, yana idarwa ya zauna na wani lokaci, kafin ya fito daga masalacin.
            Koda ya dawo, ya samu ta farka. Abincin ya bata bayan ya wanke mata baki, tana ci tana kallon shi, tare da kwaikwayon yadda yake kallonta, dake idan ya bata abincin sai ta kalle shi, sannan ta kalli abincin, sai yaci kafin take ci.
    Har yadda yake tauna abincin, sai ta karkace kai take kallon bakin shi, itama kuma ta fara haka, sannan bata san koshi ba, har ya koshi ita kan amsa take, ganin haka ya zuba mata ido yaga yadda take nishi.

            Ajiye plat din yayi, sannan ya dauki ruwa ya bata tasha, maganinta ya bata, tana gama sha wanda naka yi kokuwa kafin tasha ga shegen karfin tsiya. Dama shi namijin duniya ne murɗe ta yake ya bata tasha.

      Dake akwai na barci a cikin maganin, kafin ya tafi sallar isha, har tayi barci, haka ya shirya tare da sumbatar goshinta, sannan ya fito bayan ya nimo sojoji biyu, aka zuba su a kofar shiga dakinta.
       Tunda ya baro asibitin, yake nazarin abinda zai gayawa Ummi, domin ya samu barin kasar. Dan haka tun a hanya yake ta sakawa da kuncewa, yana isa gidanta ya yadda zango, dan ya sami hidaya da Saminah duk sun zo gidan, ga Namamajo a tsakiyar shi wato Nazzir, yana zaune anata hira da shi. Wanda kusan akan Noorh suke hiran.

       Zama yayi suna ta zaginta Nazzir na kara gaya musu su karuwa ce, kuma yarinyar bata da kamun kai, waye ya mutu waye ya dawo, maganganun marasa dad'i, sai da yaja tsaki kowa ya nutsu.
"Koma meye munin Halin Noorh ai ba ita ta fara neman hanyar wargazani ba! Ban san suwaye suka shigar da sayar da giya da sunan kamfani na ba, ita nata ai taimaka min tayi ko Ummi
         Taimakona tayi ta hanyar amfani da bankad'e Abubawan da ake aikatawa, da ace na fahimceta tun farko da zan kuma kara mata matsayi a rayuwa, domin ita abokiyar tafiya ce.

          Sannan wasu daga cikin makusantar kamfanin sunyi amfani da wasu abubuwan domin lalata min suna, ban tab'a kawowa a raina zan b'ata yar wani ba, Hakazalika ban tab'a zagin d'an wani ba, abinda yayi karanci a cikin al'umma kenan, ka zagi dan wani ba tare da ka damu ba. Bayan kana da y'aya da kanen, sannan duk abinda zaka fada akan Yaran ka, shi yasa Manzon Allah yayi hani da zagin wani a bayan shi gudun karka fadi abinda zai koma kanka.

          Amma a wannan era din mutane sun mai da cin naman yan uwan su kamar lantarki, basu damu ba, zasu dauko aibun shi, su zage shi idan ka nuna musu illar haka suce kana goyan bayan shi. Bayan kuma iya gaskiyar kenan. Gulma da munafunci tare da kyashi da Hassada itace ke damun mutanen mu, tare da rashin aikin yi. Sannan idan kuna ganin ta hanyar zagin shi zai saka ya daina karya ne, domin haka da kuka yi ba zai saka ya fahimci abinda kuke cewa ba. Kuma fa wasu zunzurutun ba ayi da sune!

     Idan suka ga kayi kuskure shikenan ka shiga uku, wallahi muji tsoron Allah, domin abinda muke bazai kai mu ko ina ba, kowa ya b'aci da bakin ciki, ko gulmar wani. Na kuma jin an dauko maganar Noorh sai na karya kafar mutane Allah ya shirya mu baki daya."
    Ya haura sama abinshi,bin shi da kallo suka yi tare da shiga hankalin su, kafin Ummi ta sake dariya tana faɗin.
" Wallahi yayi min dai-dai, kuma banga laifin shi ba, ai kun wuce makadi da rawa, yau idan kaga dayan ku yana aikata abu kuyi kokarin ganin ya daina ta hanyar kiransa kuyi mishi wa'azi, ko ta samun shi privet ku gaya mishi gaskiya, idan yaki toh ku yake shi. Idan ya fiki ku barshi tare da nima mishi fatan shirya.

     Amma mutane basu yin haka, sai dai a koma gefe a zagi mutum, wai da sunan Nasiha, bayan abinda sukayi shima haramun ce domin ba nasiha bane, kawai zunzurutun gulma da munafunci ne.

        Wasu akan idanun ka zasu gaya maka, wasu kuma zasu koma gefe duk wanda zai iya gaya aka magana a gabanka, toh ka dauki hakan matsayin kome domin ya nuna maka soyayya ne, amma wasu wallahi ko dabbobi sun fisu sanin ya kamata, sai anyi abu sai suce suna kafa hujja da ayoyi da hadisai. Abinda na sani mutanen Da suka cewa.
    Me hannu da hannaye bai da hurimin zagin hannun wani, domin baka san me ciki zai haifa ba gobe,  a'a mu wannan lokacin mune zagin mutane, muna kiran su yan wuta, tare da musu hisabi a duniya, ai wane dan wuta ne, idan aka tashi mishi azaba a hada da su waye mabiyan shi ko masu kare shi ayi dasu. Alhamdulillahi a koma cikin arba'una hadisi. Tsakanin hadisi na sha shida zuwa sha bakwai. Manzon Allah yace.
Dayan ku zai ta aiki irin na yan wuta, sai ya rage tsakanin shi da wutar zira'i kalilan sai yayi aiki irita yan Aljanna sai Littafin shi ya yasauya. Dayan ku zai ta aiki irin ta yan Aljanna sai ya rage tsakanin shi da aljanna zira'i kalilan sai yayi aiki irinta yan wuta, Littafin shi ya sauya.  Dan haka babu hurimin zagin wani ko wata dan ya aikata aiki da zamu mishi Addu'a.

        Domin wani lokaci fa, wallahi muna cikin zagin wasu, kawai sai kaga wanda bamu zargin sune zasu cuce mu. Allah ya sa mu dace, ya kuma kara mana imani, ya bamu damar aikata alkhairi, Allah ya kare mu da mugun ji da mugun gani, ku iyaye mata ne, ku daina zagin wasu, gudun kar mu haifi abinda muka zaga, kai kuma Nazzir kana da kane don Allah ka daina zagin wasu, gudun kar haka ya fadi kan kanen ka. Allah ya shirya mu baki daya."

Daga haka ta dauki wayar ta, tare da kiran Mahir, fitowa yayi tare da laptop din shi zaka dauka abin Arziki yake, tare da zama.
Sanye yake da three qrts sai farin armless wanda aka rubuta Any soja have a love story.

          "Officer sir! Yau kuma an tuna da filin daga ne?" Inji Nazzir, murmushi yayi sannan yace.
"Me ka gani?"
"Ni dai abinda na gani Broh you fell in love!" Inji Hidaya,

Dariya Samina tayi, dai dai shigowar Adeemah, taja kujeran da yake kusa da Nazzir ta zauna, kallon su Mahir yayi da gefen ido, kawai yaji a ranshi haka bai mishi ba, ganin kowa ya nutsu ana cin abinci ya sake wayar shi ta fadi,  a hankali ya sunkuya da niyyar dauko wayar shi, ganin Hannun Adeemah yayi akan cinyar Nazzir. Yana daukar wayar shi ya tashi tare da Cigaba da abinda yake kafin ya kalle ta yana faɗin.
"Tashi ki koma falo kici abincin a can, kuma daga yau kar na kuma ganinki a waje."

               Dake munafukai ne sun tsorata da yadda yayi maganar, da sauri ta mike, maran kunyar kuwa cewa yayi.
"Lion!"
"Please!" Ya faɗa da karfi, tare da dukar table din, take kowa yasha jinin jikin shi.
"Tashi kafin na karya miki kafa."
Da sauri ta bar gurin, ya cigaba da abin da yake, Nazzir duk ya diririce, suna gama cin abinci Nazzir yayi musu sallama zai fita Mahir yace mishi.
"Tsaya mu fita tare."
Aikuwa haka suka fita tare, har bakin kofar gidan.
"Kar na kuskura na kama ka da lalata min kanwa, domin wallahi azim zan yanke maka Dick dinka, idan na kuma ganin hannun Adeemah a jikinka wallahi zan maka yankar kauna, zan yanke maka Dick, yadda mace haka zaka ganta ka barta, stay away daga kanwata, ka rabu da ita.

     Bana son na kuma ganinku tare, Nazzir ina gaya maka haka ne between me and you, idan na kamaka da wani abinda yafi haka toh wallahi kayi kuka da kanka, domin zan maka abinda ko gani na kayi zaka wahala, Adeemah Kanwar ka ce, idan duniya da gaskiya, yadda bazaka b'ata Zoolfa ba haka ba zaka b'ata Adeemah ba, idan na kuma ganin haka." Bubuga kafadar shi yayi sannan yace.
"Zan baka maka ki!"

   Dake bai da gaskiya sai ya shiga kame kame, tare da rantse rantse shi bai mata kome ba, wallahi kawai ta ajiye hannun ta ne akan cinyar shi, amma ya tambaye ta...
[1/23, 11:09 AM] Addah Ramlat MANGA: https://my.w.tt/VtYbk6o8Ecb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣3️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

"Wannan kuma matsalarka ce, itama Adeemah zanci zarafin ta, idan na shiga cikin gidan, wallahi idan baka fita hanyar kanwata ba, zan baka mamaki banza kawai wanda kazamtar shi bai tsaya a iya shi ba."

    Nan Mahir ya sille shi sannan ya bar gurin, duk da ya razana amma dan kar ya nuna cewa ya razana sai ya bi Mahir da harara.  Shi kuwa Mahir da ya shiga cikin gidan sai ya rasa me zai mata ya huce bakin cikin da ya gani dan haka ba tare da cewa kome ba, ya riko hannun da ya gani akan cinyar Nazzir.

     Murdewa yayi baya, sai da ta sake fitsari a jikinta.
"Na kuma ganin ki a cikin gidan su Nazzir ki kuma na ganki da shi sai na ɓalle hannunki mara mutunci kawai."

Cillata yayi ta fadi, kallon Ummi yayi cikin baƙin ciki ya juya zai fita cikin tsawa yace mata.
"Kar na dawo baki gyara gidan ba! Daga yau ita zata cigaba da aikin gidan ta tunda tasan daura hannunta akan cinyar namiji."

               Kallon shi Ummi da Hajiya suka yi, sannan suka ce.
"Da haka ba gwara idan tana da wanda yake sonta ya fito ai mata aure ba,"
        "Ita tasani gata nan dai." Ya fadi haka, bayan ya bar falon. Tsabar tashin hankali, a ranar kasa barci yayi, yana hango Abinda aka soyiwa Noorh da wanda Nazzir yayiwa Deemah, gani yake da zaran ya bar kasar Nazzir zai samu damar lalata mishi tarbiyyar kanwar shi.

      Dan haka, washi gari hana Haroon aiki yayi, ya nufi gidan Ummi ya karya sannan ya turawa haroon sakon yayi mishi abinci sai fita da shi.
Kallon juna suka Mahir da Ummi,
"Hmm! Sai kumbiya kumbiya kake min meye nufinka?"
      "Hmm! Ke bani wayar ki, da laptop din ki."

    Babu musu ta dauko kome ta bashi, sannan ya kalli Ummi yace mata.
"Hmm ina son zanyi tafiya!"
"Ina zaka?"
"Canada!"
"Allah ya tsare kuma a kiyayye tab'a yar wasu domin kar haka ya faru akan na ka"

     "Insha Allah" ya faɗa a takaice,
   Mikewa yayi ya bar gidan ya nufi gidan shi ya dauki abincin ta, tunda ya isa cikin asibitin yaga yadda mutane suke bin shi da ido, ya fahimci akwai matsala. Yana nufar hanyar da zai kai shi ya samu anata kiciniyar kaita d'akin ta, taki sai dambe suke da nurses, yana isa gurin ya mikawa wata nurse basket din abincin yazo ya rikota, d'ago kai tayi sannan ta fashe da kuka tare da fadawa kirjin shi, lumshe idanun shi yayi tare da rufa hannun shi a bayanta.
"Don Allah Sir idan mun daureta karka kunceta."
Dakin ya nufa da ita, yana shiga ya rufe kofar ya ajiye ta a bakin gadon. Juyawa yayi ya bude kofar ya karbi abincin sannan yazo ya ajiye shi daukar brush da maclean yayi ya saka mata, sannan ya riko hannunta suka shiga ban daki, karshe dai ta shanye maclean din.

        Brush kuwa karya shi tayi zata taune ya matse bakinta sai da ya fitar, sannan ya koma ya dauko wani ya kuma, lakata mata dakyar ya wanke mata baki da idanunta suka fito, zama yayi da ita ya zuba mata.
      A hankali yake ci yana hura mata iska, tare da bata a bakinta tana ci hankalinta yana kan kofar dakin da take ganin wucewar mutane ta kasa, can sai ta rufe idanunta, sai da ya lura da haka ya mai da ita tana kallon kofar shi yana zaune a inda take.

        Yasan bata cewa bata san koshi ba, dan haka ya shiga bata dai dai tare da kai hannun shi cikin ta, jin ya d'an taso ya ajiye abincin ai kuwa ta fara ihu, haka ya bata tayi mugun koshi, sannan ya dauke abincin.

         Kwanciya tayi a kafar shi, yana shafa kanta, a hankali yana wasa da gashin kanta,  sannun sannu yaji ya kama barci, gyara mata kwanciya yayi sannan ya kuma gyara mata gashin kanta, yana kallon yadda take b'ata fuska, tana numfashi dai-dai kamar wacce ta dauki kaya.

             ••• idan akwai abinda yake ɗaukar hankalin shi, toh surar Jikinta ne, tana da zubin halittar da yake son matar shi da ita, tana da cikar kamala a fiskarta, kallon shedar sallar goshinta yayi, yayi tare da sake murmushin jin dadi, duk yadda aka yi ma'abociyar ibada ce.

      Lokaci daya yaji tana samun nasarar yaki da duk wani matakin jin haushinta da yake ran shi.

      •••
Bayan kwana uku, ya gama shirin shi tsaf, yana lura da yadda Nazzir yake mishi shishigi da son sanin, me yake fitar da shi.
Kwana na uku ya suka bar kasar bayan an mata alluran barci, haka kawai yake jin. Wani yanayin da bai tab'a kawowa a ranshi ba, ji yaƙe kamar ya daukota zasu tafi yawon cin amarci ne, domin yanayin yana masa kama da ita din mallakar shi ce, baya jin ita din ta wani ce. Yanayin yana kara mishi kwarin gwiwar jin shi kamar ango ne. Lumshe idanun shi yayi ya bude akan kyakyawan fuskar ta, tana barci cikin nutsuwa.

       •••
Lokacin da suka isa, an karb'e su hannu bibbiyu, asalima suna ganinta suka daurata akan magani.

     Kwana goma, tana amsar magani kafin kuma aka fara kula da matsalar ta, su kansu. Jikin su yayi sanyi, sakamakon idan aka ce Za'ayi aikin za a iya rasata dab haka suka mai da hankali gurin bata magani tare da nimo Dr Zeng chang, na babban asibitin Beijing da ke China. Wanda a tarihin likitanci ya sami lambar yabo, sakamakon yadda yake aikin shi idanun mutum biyu.

      Shi aka turawa sakon, Amma ya basu hakuri tare da cewa, ba zan sami zuwa ba, sai nan da wata uku, su fara bata wasu magunguna. Duk yadda suka so yazo ya gaya musu yana da abubuwa ne,kuma dan babban asibiti ne ma suka nime shi da ba zai saurare su ba, sai bayan shekara daya, sakamakon baya zama yana yawan zuwa ƙasashen waje aiki yanzun haka ma ya amshi aiyukan wasu ne na kusan wata bakwai.

   Insha Allah idan ya gama nasu, zai zo amma a Cigaba da bata magani kafin yazo, abin ya dami Mahir dan har tayin kudi masu mahaukatar yawa ya bashi, yace mishi a'a ya bari zai zo dan kanshi.

             A haka Mahir ya hakura tare da zubawa Sarautar Allah ido, ya kuma cigaba da kula da ita. tare da shawarwarin da suka bashi yake daukarta suna fita, yawo, idan lokacin sallah yayi yana tare da ita idan taga yana yi itama yi take, sosai wani irin jituwa da shakuwa ya shiga tsakanin su, gabaki daya Mahir ya tattara zuciyar ya mikawa Noorh, ba tare da sanin ya mutu a kanta ba.

    Sai da ta fara ciwon cikin period, zarewa tayi tana ta ihu. Tare da dukar shi, dakyar aka mata alluran da zai rage mata ciwon tare da barci, shine aka sami saukin abun. Tana barci, duk ta jika jikinta da jini, koda ta farka ganinta cikin jini ihu ta saka tare da niman kwace jikinta daga saka mata belt, sai da Nurses har biyu suka mata allura da zai hanata kome, tana kallon shi suka mata har wanka, tare da

Please Login or Register in order to submit comment