Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan kokarta 🙏🏼😘😍
~#PI~
"Deem baki tunanin ya biyo ki, kin san ba hakuri ne dashi ba, karshe yazo ya haɗa dani, dan na fahimci ya tsane ni." Inji Zoolfa,

      "Ina ruwana, shi ya sani, ayi rayuwa babu wanda zai maka gwaninta, na tsani rashin mutunci. Wallahi na tausayawa matar da zata zauna dashi dan nasan a duniya babu wacce take mishi gwanin ta, sai Ummi da Jaddih, sai ko Alishbah. Dasu Hadiya da Suhaila. Amma ni kullum sai yace ban iya ba.

Ke kwalliya idan nayi sai ya harare ni, wai na cika hauka. Ubangiji ya sa ya hadu da wacce ta fini hauka ta mishi rashin mutunci yadda sai ya san cewa kowa hakuri yake da rashin adalcin shi."
         "Aikuwa nayi imani da Allah, yan matan da yayi breaking heart dinsu sai sunyi farin ciki, mutum sam bai san ana mishi adalci ba, wai da Jaddih ta mishi magana yazo ya nemi aurena cewa yayi wai bani da kunya.
        Kiji fa, sai kace a kaina aka fara rashin kunya kuma ban tab'a mishi kome ba."

     "Ba dai Uban yan tsari ba, muna nan dake sai ya dama bilayin shi sannan ya hadu da wata kucaka..yayi fell in love da ita."
   Haka suka gama kare mishi tanadi, sannan suka shiga hiran samaruka su.
     •••
Cikin nutsuwa yake saukowa daga jirgin, iska na kad'a rigar jikin shi, sanye yake da riga da wando na Puma, rigar me hula ce.
    Kayan jikinshi baki daya Black ne, hatta takalmin shi puma ce, daga can nisa ya hango autar su, tana d'aga Mishi hannu. a cikin wani irin taku me tattare da jarumta, yake tafiya yana isa gurinta, ya bude mata hannun. Da gudu ta isa tare da fadawa jikin shi tana faɗin.
"Barka da hanya Ya Mahir!"
Peck ya mata a goshi sannan yace mata.
"Queen Shbah, ya school!"
"Lafiya lau!"
Ya fada tare da gyada mishi kai, a hankali suka isa motar su, bayan driven ya tawo da kayan shi.  Sai zuba mishi surutu take, yana lumshe idanunshi, tare da shafa kanta.
  Har suka isa gida, tunda ya fito masu aikin gidan suka ganshi, kowa ya nutsu, sun san cewa kana mishi karamin kuskure kora ne.
    Da sallama ya shiga falon gidan.
"Barka da zuwa, miskili kafi mahaukaciya ban haushi."
Murmushi yayi sannan ya isa gurin Jaddih ya zauna tare da daura kanshi a kafad'arta.
"Ina kewarki." Ya faɗa ƙasar makoshi, yadda ita daya ce ta jiyo muryan shi,
    "Magulmaci karya kake, ka fadi gaskiya dai, ya dace kayi aure dai wallahi daga kai har wancan d'an uwan naka, ku nimo mata. Ga yan mata a gari idan ma nan basu muku ba,.ku tafi can algeria akwai yaran mata a cikin dangin mu gaba da baya,.zaku sa.."
      "Hmm!"
"Hmm, din gidan ku. Kai gaya min Aljana ce ta aure ka."
Lumshe idanun shi yayi tare da taryo abubuwan da suka gabata a rayuwar shi, a hankali ya saka hannu a cikin aljuhun wandon shi ya ciro wata sarkan azurfa. Irinta kafa.
    Sake shafa sarkan yayi yana kuma sake motsawa, ba zai iya cewa akwai dalilin mallakar wanan sarkan ba, amma kuma yana da Tabbacin mallaki ne. Na wata, a kala sarkan tafi sama da shekaru goma sha biyu a hannun shi.

           "Allah Alhaji ka fita idanu na, matukar baka yi wani abu ba, nan da karshen shekara zan muku auren dole." Mikewa yayi tare da haurawa sama, ya barta a gurin, bayan shi tabi da harara, tare da musu addu'a Allah ya kawo musu mata na gari.
      Tunda daga bakin kofar dakin shi, yake hango alamun datti. Idanun shi suka nuna mishi, har ya bude dakin cikin takaici yake kallon kura a saman Center table din shi, cike da mugun kyam-kyame ya juya zai bar d'akin. Yaga Ummi tana tawowa.
      "Baba ka dawo lafiya." Yake yayi sannan yace mata.
"Alhamdulillahi Ummi. Na same ku lafiya ya aiki."
Kallon shi tayi na wasu lokuta kafin ta share, duk da tasan shi ba ma'abocin tsawaita magana bane, but.
"Ina zaka kuma, ka shiga ka huta mana."
Cikin gajiya da damuwa, yace.
"Waye aka bawa gyaran dakin?"
Lek'awa tayi ta dai iya hango Center table da dan kura amma shima daga nesa zaka fahimci haka.
           "Haba Babana, kuran nan ba mannewa zai yi a jikinka ba,ka shiga kayi."
"Hmm! Bari naje Apartment dina kawai."
Ya gwammace da ya shiga, cikin wannan ƙurar gwara ya koma gidan shi wanda kullum na duniya, sai an gyara gidan har bedrooms din gidan. Wani yaron shi haroon.
        Yaron bayarabe ne, kusan Mahir shi ya kub'utar dashi daga shaye shaye, ya kawo shi gidan, yana bq. Duk wani nauyin shi Mahir ya dauka. Shi kuma sai ya zabi ya kula da gidan Mahir din.
             A gaggauce ya bar inda Ummi take, tana jin saukar shi, bata dakatar da shi ba, domin ko tayi haka ba zai saka ya kulata ba.

        Tun yana yaro karami ya tashi da mugun mugun tsafta, zai yi wuya ka ganshi da kaya yau gobe ya maimaita, sannan baya cika zama da kaya daya har dare,  mutum ne da yake da kulawa akan lafiyar shi.

        Shi ya hanata daukar masu aiki mata, hatta me girkin su namiji ne, wankin su ma duk maza ne, sannan ya tara kannen shi yace musu.
"Ban damu da duniyata ba kamar yadda na damu da goben ku, dan haka. Kar na yarda naji labarin wata tasaka inner wear ɗinta a cikin kayan wankin da za a kai loundry, idan kuwa na fahimci haka, toh zan karya yarinya."
Yana maganar rike da goshin sa, sabida bai cika magana mai tsayi ba, idan kuwa yayi toh sai yayi ta fama da ciwon kai.

       Shi yasa a Office bai magana sai kora.
     ... Lokacin da ya isa gidan shi, bude kofar falon da yayi kamshin turaren zamani tare da wasu turaren na musamman, irin su Oud da sandal, Whiter flora, miski, Maryama, tare da bakhoor. Ya sanya shi lumshe idanunshi tare da sake murmushin jin dadi.
             A hankali ya shiga cikin gidan, yana kallon ko ina kamar ya jefa abinci ya dauka yaci.

        A duk lokacin da yayi tafiya sannan ya dawo ya sami gidan shi haka, ji wani irin dad'i yaƙe domin kuwa duk inda zai shiga, cikin nutsuwa yake yin shi, a da bai ji gajiya ba, sai da ta isa master bedroom din shi ya zube a bakin gadon.
     A halin yanzun, yake hango alamun kamshin gaskiyar su Ummi da Jaddih, yayi girman da yake bukatar abokiyar rayuwa. Amma wacece ita? Daga ina zata zo mishi.

           Sake damke sarkan hannun shi yayi sannan ya bude idanun shi da suke lumshe, ya manta wasu abubuwan amma abu biyu nan sun kasa goge mishi a ranshi,  kwayar idanun ta, tare da wannan sarkan da ba zai iya tuna kome akan shi ba.
                 A hankali ya mike zaune ya shiga cire kayan shi, tare da shiga ban dakin ya dauki wani karamin light blue towel ya daura a k'ugun shi, sannan ya kuma dauki  kayan wankan shi ya da suke ajiye a wani dan karamin locker ya fidda su,.sannan ya tari ruwan zafi sosai ya jefa sosan wankan da sabulun a ciki wani roba.
                A sanyayye ya gama wanke sosan shi tare da dauko brush din shi ya kuma jefa wa a cikin ruwan zafi, shaving cream ya dauko tare da wasu tarkacen gyaran fuska. Ya shafa cream din a fuskar shi tare da gogawa a duk wani ajiye suma a jikin shi.
    Sannan ya bude wata karamar drower ya dauko wasu park na gyaran farce, ya shiga gyara farcen shi, yana aiki yana kallon yadda ruwan wankan shi yake taruwa.
Bayan minti sha biyar, ya shiga goge fuskar shi a hankali yana yi yana bude idanun shi, har ya gama, sannan ya zuba wasu Mayun turaren wanka, sabida shi mutum ne da yake masifar son kamshi. Shi yasa koda ya isa cikin ruwan wankan ya shiga hada shower gel da sabulun. Kafin kace me har ruwan ya tara kumfa. Lumshe idanun shi yayi tare da kwanciya cikin ruwan sosai.

                ***
Yola.
Wani irin kallo yayi mata, lokaci guda ta shiga nutsuwar ta, sanan yace mata.
"Takardu Noorh ta kawo min, kuma duk rashin hankali na, bana kusantar matar aure, kin tsaya zaki mare mata baki san ina kallon ki ba."
 
   "Kayi hakuri! Na tsani naga tana kusantar inda kake ne, Kuma"
"Dalla ki min shiru, kina wani zakewa, idan kika Kuskura Lion Man ya shigo wannan kamfanin ya fuskanci kina Iskanci a cikin a wannan kamfanin koran zayi kuma karki yi tsammanin dan muna da wata alaƙa a kasa bai dame shi ba. Gaba zai yi dake."

     Shiru tayi ba wani abu yaja mata wannan  fadar ba, sai dan kin bashi hadin kai da taki shine yake ta niman hanyar da zai mata rashin mutunci. Ya dai na kulata, tare da disgata a gaban jama'a, bayan ya kuma saka hannu Noorh zata yi aiki da Mr Mahir.  Daga baya ake gaya mishi ai Noorh auren ta ya mutu, abin ya bashi haushi shine yake son ya ci Ubanta. Kamar yadda ta saka ya rasa Noorh haka itama sai ya fanshe akanta."

Rud'ewa tayi tare da bashi hakuri, dake ta gama gayawa kowa aure zasu yi, kuma sauran matan ganin yadda yaki nunawa akan zai yi mugun nufinsa akanta yasa suka yarda akan aure zasu yi shi yasa suka masifar tsanar ta.
      Ita kuma idanunta yana kan Noorh, ko yanzun abinda ya faru Noorh ta kawo mishi wasu takardu ne, akan yau zata fara aiki a Office din shine take ta cike wasu takardun. Sabida tsarin Mr Mahir.

      Yau kwana uku kenan da aka kuma fente Office din shi, tare da na kamfanin baki daya, ta kai mishi takardun kenan ya tsare ta da ido. Sai da ta kuma gyaran murya yake cewa.
"Wato da aurenki ya mutu ko na samu labarin sai a bakin mutane?"
" Kawai dai na gan kamar abinda ya shafi rayuwata ce, babu amfanin raba shi da kowa"
"Haka ne! Gaskiya kinyi gaskiya. Amma idan babu kome ko..."

"Ina da abubuwa da yawa a gaba na,ba aure da mutuwar shi bane zaɓi na, ko SOYAYYA da kauna." Tana fadar hakan ta amshi takardun ta juya zata fita, yace mata.
"Ni kuma da aure nake bukatar ki, wallahi ba batun wasa ba."

Girgiza kai tayi sannan ta tabar mishi Office din, tana fita suna haduwa da Tasleem, wacce dama tana tsaye a bakin kofar, kuma shima Ya ganta, ta Cctv.

Noorh tana fita ta wanke mata fuska da mari, cike da mamaki Noorh ke kallonta ranta ya b'aci sosai, dan haka ta watsar da takardun, ta shake wuyar ta, ta rama marinta har uku ma, sannan ta barta a gurin yana ganin shi sai murmushi yake dan ya gaji da rena Noorh da tayi.

     ina isa Office din mu, na sami Badar kallona yayi sannan yace min.
"Rufe kofar nan, za nuna miki wani abu. Ban sani ba ko zaki iya taimaka min dashi Kinga daga Office din Mr Mahir key din yake ciki..idan kika dauko mana zamu iya yin kome tare."

     A hankali ya kunna laptop din shi wani daukar video ne na minti ɗaya da sakon hamsin da takwas, yadda ake sarrafa giya tare da wasu abubuwan sha amma na mayye, kuma da tambarin Hamoud Boualem Company.
"Yanzun wannan abun da yake faruwa, da sanin mr Mahir kenan, haba shi yasa arzikin shi yayi yawa ashe ana haɗawa da kazamta."

     "Noorh abinda bamu sani ba, shin da hannun Mahir ne ko kuma wasu ne suka bude gurin tunda shi bai da lokacin sanin abinda yake faruwa. Matslar da ake fuskata, ana samun mutuwar matasa tare da tsofin. Abin da na fahimta kuma akwai hannun manyan mutanen da suke tare da kamfanin. Yanzun ni ba zai yiwu na fara bincike ba, sabida wifi din kamfani ne, dole zasu san shiga da ficce na, amma ke da kike wajen kamfanin zaki iya wannan ya zama personal information tsakanin mu."

     🙄🤔 Malam bahaushe yace kaza me tone tone... Wata rana zata tono wukar yanka kanta..
https://my.w.tt/i6E1Vi9ETbb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 0️⃣8️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

   _Allah ya baki lafiya ubangiji ya da zakkar jiki ne Aisha Bagudu! Allah ya baki lafiya_

My Honey Fans ina alfahari da ku, musamman comments dinku.😍😘 Da masu daukar dumin mr kyam-kyam😜

~Sisterhood~
.......
"Noorh! Amma dole zaki sake jiki da Mr Nazzir, ba dan kome ba dan kawai ya samu ya shigar sake cikin mutanen da yake da kusanci da su, haka zai taimaka wajen shiga gurin ba tare da wani ya fahimta ba.
      Sannan wancan yar uwar naki, kiyi kokarin dakatar da ita domin tana gab da rasa darajar ta, idan haka ta faru. Ba lallai bane kome yazo da sauki amma idan kika shige jikin Nazzir ita zata kuɓuta domin Nazzir manemin mata ne na bugawa a jarida kafin ya ci nasara akanta kinyi nisa da ita, kema nasan zaki kub'uta, sabida Mr Mahir ba zai iya bari wani abu ya same ki ba."
    "Toh idan wani abu ya fito daga baya fa? Kai da kanka ka gaya min Mr Mahir bai da kirki idan wani abu ya hada mu da, ya kore ni."
"Ba zai tab'a faruwa ba, na gama shirya mana kome Insha Allah koda zan yi Survive na, am sure dat zaki kai labari, nasan zaki tsira Insha Allah." Kallon shi nayi sannan na lashe bakina, dai dai an buga kofar Shigowa.
   Mikewa nayi na isa bakin kofar, shi kuma ya mai da kome, sannan na bude kofar, wani irin kallo take bina dashi, tare da jan tsaki me ƙarfi. Bata hanya nayi. Sannan ta bangaje ni ta wuce,
Dariya nayi mata, me cike da tausayin ta, sannan na koma na hada takardun na saka a jakata, daurewa take kawai amma dan abu kadan kuka zai sakata.
              A hankali muka tashi tare da nufar gida, Ni Badar ne ya mai dani tare da bani wasu kayan aikin. Muna isowa Mr Nazzir yana isowa da Tasleem. Kanta na rawa, ta fito murmushi nayi ta sake min, sannan na nufi cikin gidan.
"A'isha Omar Jimeta!"
A hankali na juya ina kallon shi, cak ta tsaya itama, na isa har gurin shi. Murmushi muka sakewa juna, tare da cewa.
"Sir!"
"Noorh! Ina son magana dake, idan da hali."
"Gaskiya na dawo gida kenan, kuma ba zan iya dogon magana ba, kuma bani da lokacin da zan yi magana da kai."
   Murmushi yayi sannan yace.
"Toh ba damuwa, ranki shi dad'e. Idan da hali a bani lokacin da zan zo mu gana."
"Amma kamar akwai wani abu a tsakanin ku da Baby Queen?"
Na tambaye shi, murmushi yayi min sannan yace min.
"Am deeply sorry, babu soyayya."
"Aikuwa babu abinda zai hada ni da kai, kawai ka rabu da ni, karka ja min magana, don Allah ka rabu dani, idan kace abota zan yi da kai but babu batun soyayya, sai dai abota na yarda da haka. Shima sai na duba yanayin mu'amala da kai. Da kuma Baby Queen."
Daga haka na barshi tsaye, fuskar shi zaka kalla ka fahimci yaji yana cike da mamaki, sabida tunda yake babu macen da tab'ata nuna bata yin shi, asalima bai tab'a jin akwai ranar da mace zata ce bata yin soyayyar shi.
   Dan ya fahimci shi yakewa mata alfarma basu ke mishi ba, sai gashi once, A'isha Omar ta mishi kwarjini.
             Murmusawa yayi yana bin bayanta da Mayun idanun shi nan, ji yaƙe kamar ya dauke ta ya boye ta a gidan shi. Yarinyar ta yi mishi bazata, ta cika mishi ido.
     Kamata yayi ace ta kware akan harkan rayuwa, amma wani sirrin da yake hangowa cikin idanun ta, ya sanya shi jin shakkar ambaton soyayya a tsakanin su. Ina ba zai iya zama da ita ba, a matsayin abota ba, abinda zuciyar shi ke son dai itace tazo a matsayin matar auren shi haka zai bashi damar tafiya da ita yadda ya dace.
           Dakyar yaja kafar shi ya shiga motar shi, yana sake kallon yadda tasleem take tsaye, tare da kallon shi, bai damu da ita ba.
        Bayan fitar shi ta shiga cikin gidan, a haukace tana shiga ta hango Noorh tana haurawa step. Kafin ta iso step din ta zame, sakamakon zubewar ruwa, lokacin da me aikin su ta dauko daga sama dauke da kayan wankin da Mommy ta jika, aikuwa sai da ta bugu. Wani irin kuka tasaka, me mugun karfi ta kuma tashi da sauri ta haura sama.
... Tana shiga ta samu Noorh tana banɗaki shiga tayi tare da, niman rufeta da duka. Allah ya taimaka Bata cire kayanta ba, aikuwa suka kacame da dambe, Tasleem ta fadi ita kuma ta haura cikinta tayi ta dukarta, ihunta ya janyon hankalin Mommy.
               Tana zuwa ta sami Noorh bisa Tasleem, aikuwa ta rufe Noorh da duka, ita kuma ta Cigaba da dukar Tasleem sosai take dukarta, ganin zata kashe mata Ƴa kawai ta tureta da karfin tsiya, sai da ta fadi cikin zafin nama ta mike tana zubda yawun bakinta, sabida bakinta ya fashe.
    "Wayyo Allah na, Mommy ta kwace min shi, Mommy zata kashe ni, sai na kashe ki wallahi wayyo Allah na, na shiga uku na lalace."  Inji Tasleem,
Murmusa musu Noorh tayi sannan tace.
"Wallahi matukar baki daina haukar tab'a ni ba, toh ba zan daina dukarki ba."
"Yar iska, yar cin arziki ita da gidan Ubanta ki saka hannu ki daketa"
Kallon Mommy tayi sannan tace.
"Gidan ubana ne nima,.babu wanda ya isa ya kore ni."
"Ni zaki yiwa rashin kunya?" Cikin taurin kai tace.
"Koyarwarki ce ni, tunda na taso kika koya min kuma na haddace."
    Sake baki tayi, tana kallon Noorh.
"Idanunki sun bude ko? Kin saba da maza?"
"Bani ya dace ki gayawa haka ba,sai wacce take damuwa akan wanda bai san tana yi ba. Ni da ayi namiji kar  ayi shi, itace mayyar maza, wacce zuciyarta ta rayu saboda maza."
Daga haka na fito, daga bayin na zauna ina huci, tare da jiran me zata ce. Haka suka fita can sai ga Daddy, ya shigo da masifa, kallon shi nayi cikin kuka nace mishi.
"Tunda Na rasa kowa, kuka mai dani bare, baku da wani abu sai Yarki baku san kome ba sai Yarku a duniya babu abinda kuke boye akanta.
  .kunsan yadda nake ji? Kun rabani da  dangin Mahaifiyata, kun rike min dukiyata, ku bani hakkina da iyayena suka bar min, sai na fita a rayuwar Yarku."..
Daga haka ta shiga hada kayanta tana kuka, tare da cewa zata bar gidan ma ta huta,
   Shiru yayi sannan, ya fita ya rasa abinda zai ce, tabbas dole ya hakura da abinda yake shirin faruwa, domin tunda ta fara fad'ar haka, wata rana zata iya yunkurin sai ta karbi kayan ta. Shi kam ya gama barnata da kome.
           **
Ranar kwana akayi a gidan, babu wanda ya iya, cin abinci sabida wutar da Noorh ta kunna musu, washi gari, ko karyawa bata yi ba tabar musu abincin su.
Kafin Tasleem ta isa gurin aiki, sai da suka mata fada, tare da cewa karta kuskura tayi wani shirme da Noorh zata daketa, ko tayi wani abu da zai sanya tayi magana. Don Allah tayi shiru ta zuba mata ido. Zasu san abinda zasu yi da Noorh.

        ---
A gurin aiki kuwa, tsoron Allah da tsoron Noorh ya hana Tasleem yin wani abun Arzikin, asalima tsoron kar Noorh ta fusata ya saka ta ki sake jikin ta.
   Koda aka tashi tare da Mr Nazzir suka  dawo, domin shi ya kawo  Noorh har gida.

    Ba sannu ba madalla ta ficce daga motar, ta barshi rike da kayan shirmen shi, da ya kawo mata, ta shiga gidan. Fitowa Tasleem tayi tare da harde hannu a kirjinta, tana kallon Nazzir.
Har inda yake ya isa, sannan ta zauna a cikin motar,
"Me kake nufi? Meye nayi maka da nayi deserve abinda kake min? Ka rasa wacce zaka yi mu'amala da ita sai Yar uwata.
    Don Allah ka rufa min asiri, zan baka duk abinda kake bukata don Allah kayi hakuri kaji kaina."
Ta faɗa cikin kuka, tare da hade hannun ta, gwanin tausayi. Kallon ta yayi sannan yace mata.
"Toh me zan miki? Na biki na biki, baki fahimci ma'anar soyayyar mu ba, Ni ina miki so tsakani da Allah, da kika ki sake jikinki dani shi yasa nayi tunanin na tuntubi A'isha Omar."

   "Yanzun idan na baka kaina zaka soni?" Ta tambaye shi cikin kuka.
Wani irin murmushi yake me cike da nutsuwa, tabbas tarkon shi ya kama kurciya. Yarinyar da yake bukata, ta kawo kanta jan iska yayi tare da kai hannun shi wuyar shi.
"Ok! Ki gayawa Parent din ki, akwai gala a gurin aikin mu, kin shirya"

Cike da farin ciki ta bar gurin, ta iso cikin gidan. Tana kallon Noorh da take ta fama da aiki tare, cikin budar murya tace.
"Mommy daddy, kuzo kuji akwai event din da aka gayyace ni,Ni da Mr Nazzir Abu Aswad, yan bakin ciki Tabbas zaku mutu, Mommy an jima karfe takwas."

      Murmushi nayi tare da zuba musu. Idanu  domin na fahimci kwadayi ya dame su, ban tab'a jin tausayinta ba sai yanzun da na fahimci, sun gama lalata tarbiyyar yarinyar su. Ga baki daya sun zama sakarkaru.

        Haka ta shirya cikin wasu fitinanne gown, kan nan kuwa aka gyara shi, haka ta shigo da wani abu a cup tana sha, haka ta gama. Sannan ta dauki kayanta pursed din ta, bata kalle ni ba.

      Har zata fita nace mata.
"Tasleem! Karki yarda da Mr Nazzir, Samarin shaho ne. Karki yarda ya kai ki ya baro ki, Tasleem karki yarda kije inda Allah bai kai ki ba, Tasleem idan kika yi hakuri Allah zai baki abinda ya fi Nazzir.

    Don Allah don Allah karki yarda ki kai kanki daga hallaka."

"Ke wacece da zaki hanani, abinda nayi niyya ko Mommy da Daddy basu hanani ba, sai ke ke din banza ke din wofi.

   Mr Nazzir kuwa yanzun zamu fara soyayya dashi, banza mara zuciya. Idan ke yar halak ce karki kuma shiga harkata."

.daga haka ta fice abinta, tana fita na lallubi wata ta, na kira Badar ya turo min, Number Nazzir.

Ina sakawa, na kira shi..
"Kasan nace zamu yi abota da kai?
And karka yarda wani abu ya shiga tsakanin ku da Tasleem..idan kuwa ka bari har wani abu mara dadi ya shiga tsakanin ku, toh karka yi tsammanin zan tab'a kyale ka, ka bar min yar uwata."

   "Ok na barta, babu abinda zan mata," ya fadi haka cikin lalluma, lokacin tana gaban shi, kura mishi ido tayi cikin b'acin rai. Tace mishi.
"Me nene?"
"A'isha Omar wai kar na fita dake"
Rufe bakinta tayi sannan ta fashe da kuka, tana girgiza kai tare da juyawa zata fita ya fincikota ta zube a jikin shi ta sake wani irin kuka. Nan ya shiga rarrashin ta, tare da gaya mata magana masu laushi da dad'i.

     Yadda ita kanta bata san yaudarar ta yake ba, kafin wani lokaci har ya kashe mata jikinta, tana jan motar yayi ya nufi Hamoud Boualem Estate. Da ita.

   Gabaki daya hankalin Noorh ya tashi wani irin Fargaba tare da tashin hankali ya saka ta kasa magana, sai zirga-zirga take..kamar wacce tayi karya, zunzurutun tana gudun abinda zai faru da Tasleem, har kusan karfe goma, ta leko step taga babu kowa duk sun shige dakinsu. Wato basu damu da rayuwar yarinyar ba, takan su kawai suke "innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ya Allah protect Tasleem!"

Kiran wayar Mr nazzir tayi cikin tashin hankali tace.
"Please! Ka barta ta dawo gida, don Allah karka mata kome, bata san waye kai bane, don Allah."
Kashe wayar yayi tare da sake murmushin mugunta..
Yana cizon lips din shi yace.
"A'isha Omar, ke matar aurena ce. Ba zaki hanani abinda

Please Login or Register in order to submit comment