Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yola, yana mara mata baya cikin tsannanin b'acin rai ya shiga hango wasu daga cikin mutanen da suke gaisawa sama sama, kira wayar shi akayi cikin mugun zuciya ya dauka.
       
"Lion! Gobara ta tashi a cikin kamfanin amma anyi nasarar kashewa."

     Sake wayar yayi tare da dafe kirjin shi da yake barazanar fashewa. Jingina yayi karfen da ya d'aga, ta sauke a kansa ba dan ya tare ba, da wallahi tayi mishi lahani. Ji yayi zuciyarshi tana ci da wuta. Dan haka ya mike tare da tangadi ya bude yar medium din frig din da yake gurin ya bude tare da daukar goran ruwan sanyi ya bude bakin shi sai da ya shanye tass. Yayi wurgi da goran yana sauke wani irin gurnani.
       Da zai sami wani a kusa dashi tabbas sai yayi mishi mugun duka, tashi yayi zuwa dakin shi ya budewa kan shi ruwa, haka ya jike jagwab. Sannan ya nufi inda towel ɗin shi yake ya dauka tare da daurawa yana goge kanshi da da daya.
         Wani irin huci yake, tabbas da zai ga marubucin wancan abun sai na lahira yafi shi jin dadi, wani irin bakin ciki yake ji kamar zai kone, haka yayi ta ambaton Allah.

    Har ya gama shiryawa sannan ya fito, yana fitowa yaga Nazzir ya wani firgice, bai ce kome ba, ya shiga mota aka tafi da su kamfanin, kafin su iso an kwashe kome. Sai an kananun kayan da aka barshi suna cikin wuta, lumshe idanun shi yayi domin ji yayi kamar zai sake kuka, Kamfanin nan amanar shi ce.

         Mahaifin shi ya bar mishi, duk da yana da wasu masana'antu amma wannan ji yaƙe kamar mahaifinsa ne a raye.

"Kuyi hacking din Acct ɗin Tweeter din marubucin, duk wanda yayi rubutun nan makusancin kamfanina ne, ku tafi ki nimo min wanda yayi wannan ta'addanci..."
"Lion! Jornalist!"
Juyawa yayi da fuskar shi da tayi jajjur.
"I don't care! Koma waye yazo babu abinda ya dame ni, kuje ku nimo min wanda ya lalata min suna. Idan ba haka ba, toh wallahi zaku ji a jikin ku."

            Yaki magana da yan jaridu, asalima abin sai ya koma siyasa, domin wasu na cewa sharri aka mishi wasu na kuma cewa zai aikata idan aka yi dubi da yadda yake da Arziki gashi matashi wanda yake ganiyyar samartaka shi. Dole yayi abinda ya gadama.
  Yana zaune a kamfanin anan yayi Sallah magarib da isha, suna zaune ana cigaba da aikin, aka turo Super visions from ministry of health, da Kuma wasu daga Shari'a committee, tare da Da'awa. Mahir ya kasa magana, a hankali aka shiga bincike sosai, binciken da ya kai har sai da aka zakulo wasu abubuwan na daban, ba abinda ake zargin ba.

              Dake duk abinda yake faruwa ana dauka a live, karfe goma na dare Ummi da wasu manyan lauyoyyin daga lagos suka iso. Anan aka shiga tashin hankali tare da musayan kalamai.

    Har zuwa karfe ɗaya na dare, suna cikin wannan yanayin Noorh ta kuma sake videon da ta dauka, tare da asalin yadda giyar take, da yadda ake tacce rubabben kayan marmari ana sarrafa su a gida, tare da tambarin Hamoud Boualem Drinks. Kamar zai fadi. Ummi ta riko shi.
"Kar wannan ya dame ka, ka nutsu a ranka babu wanda ya isa wuce kaddarar shi jarabtace."
       Muryan shi a raunane yace.
"nagode sosai Ummina"
duk yadda aka so yayi magana ya kasa cewa kome, dan haka Manyan Jami'an gwamnati, suka saka hannu a rufe Kamfanin, komawa gefe Nazzir yayi sun jima ana magana can aka kira wani daga cikin masu binciken.  hakuri yayi ta badawa sannan ya kalli Ummi da lauyoyyin yace musu.
"karku damu ministan harkokin lafiya yayi maganar,"
Haka suka dauki kayan su, suka fita amma ta fannin addinin Musulunci, sun ce a karkare a kotu. Lumshe idanun shi yayi sannan ya mike, suka nufi gida.

    Tunda suka shiga gidan shi Ummi ta zauna a kujera, daura kanshi yayi a kafad'ar ta, yana me lumshe idanun shi, sai ajiyae zuciya yake, zunzurutun b'acin rai.
Wayar shi tayi kara Ummi ta duba, taga Nazzir. Kashe wayar tayi tare da wurgawa a cikin jakarta. Yana kwance a jikin ta, har yayi barci, zamar da kanshi tayi tare da sakawa akan pillow.

   Tausayi ya bata, tare da jin ta ina zata taimaka mishi, toh babu Mahir yaki aure, tana fara maganar aure zai tashi kamar me aljanun.

              Dakin shi ta nufa tayi alola tare da gabatar da sallah nafilla. Tana idarwa tayi kwanciyar ta, a d'akin.
   •••
Wato Noorh da ta samu ana giya mata baya, kawai ta shiga bankad'e Abubawan da babu ruwanta, kiranta Badar yayi yace mata.
"Ki dakatar da abinda kike! Domin mutumin da kike yaka bai san kome ba, kiyi maza ki goge abinda kike daurawa, kafin zuwa lokacin da zaki yi danasanin abinda kike aikatawa "

    "Kaga Don Allah ka barni nayi aikina, idan na gama shi kenan.". Dakyar ya dakatar da ita, sannan ya sakata ta goge kome, sannan suka yi sallama.

     ••• Washi gari.
Da wuri ta shirya zuwa kamfanin, tun a bakin kofar shiga ta fahimci yau abu mutunci ,.kowa zai ci Ubanshi. Tana shigowa Yana shigowa ko kallon shi bata yi.

     Duk yadda Ummi taso lakwasa Mahir abin yaci tura, domin kuwa sai da tai mishi nasiha, da kuma kar taji ya kori kowa, sanan tabar Yola bayan taje gurin Yan uwan ta, suka jajjanta.

    Bata ce kome ba, har suka isa airport. Nasiha take mishi gyada kai kawai yaƙe. Bayan tafiyar ta, suka juyo zuwa kamfanin, tun daga bakin kofar ya fara ruwan bala'i, har ya shiga office din shi, bai yi kora ba, amma an dakatar da mutane da yawa, dama a yau Tasleem ta shirya tsaf domin tun karar Mr Mahir da marurun zuciyata, bata san abinda yake faruwa ba.

     Sai dai yadda taga Noorh tana kaf kaf da kanta, tare da saka nikkab ɗinta ta cikin fiskarta sannan ta daura hijab a saman shi.
     Sannan ta dauki hand bag dinta, suka fito Tasleem ta shige dakin Mommy, ta sami guri ta zauna, tana daukar turaren mallaka da kuma idona idonka.

     Tana gamawa ta fito, a hankali tana yatsina fuska, a gurguje suka karya, tare da mik'ewa suka fita.

         •• kowa ya gama shan jinin jikin shi, domin an dakatar da mutane arba'in, yana tsaye ya kasa magana idanun shi jajjur, suka shigo kamfanin, bai juya ba dan yasan sune zasu iso.
"Ba zaku fitar min da wanda yayi min zagon kasa ba?"

      Kunshe dariya Noorh tayi, take tare da kallon shi, ganin yadda ga baki daya ya rud'e, tana hango tsoro injita, da tashin hankali. A fuskar shi a tunanin ta kenan. Amma a yanayin shi babu tsoro, tsabar bala'in da yake cin zuciyar shi ce, ya tsare su da masifa. Yadda yake musu tsawa.

Cikin niman tsokana tace.
"Mufa ba yara bane, da wani zai tasamu a gaba da ihu, ai idan mutum bai aikata abin da ake zargin shi ba, ba zai damu kan shi ba, sai ma kare kan shi da zai yi salon mugun nufinsa ne ya janyo mishi rikicin duniya."

   Cikin fusata ya juya tare da janyo hijab ɗinta yayi hanyar waje da ita, rashin sani yafi dare duhu. Watsar da ita yayi akan idanun Yan jarida. Da suka zo wurin domin niman abinda zai ce da kalubalantar shi da ake.

       "Kar na kuma ganinki a cikin kamfanin nan." Ya faɗa.
"Wannan kuma matsalar kace sai dai ka sani ka kuma dagula kome, ashe cin zarafin mata da kake gaskiya ne."

   Cikin makirci ta mike tana kuka, tare da tunkarar shi, ana kuma dauka a hoto, haka ya kuma tureta, kamar da gaske.

     Security ne suka zo suka fita da ita, ai kuwa yan jaridu, suka shiga tambayar ta, ta shiga basu amsa.
"Wallahi ban san me nayi mishi ba, kawai ya shiga wulakantani, sannan yau ma ya nime ni ne, naki shine yake tozartani a cikin jama'arsa tare da koro ni."

      Wannan muryan nata da tayi sanadiyar janyo mishi mugun asarar me girma a wannan kamfanin, a cikin kasa da awa biyu, masu hannun jari sama da mutane 70, suka zo janye hannun jarinsu. Juya musu baya yayi tare da kallon waje, kunna mishi tv aka yi, yana jin muryan ta ya juya da sauri, yana kallonta, tare da bawa babbar yar jaridan nan amsa cikin nutsuwa wato Mimiqueens. Tace mata.
"Toh Malama A'isha Omar Jimeta, shin akwai abinda ya tab'a had'a ku da shi?"
"Eh toh gaskiya zan iya cewa,ya sha bani azaba a cikin office din shi sannan kuma Dan uwan shi Sir Nazzir ya sani, domin ya mishi magana yaki!"

"Toh wai da gaske ya tab'a niman yayi miki fyade." Kasa tayi da kanta, tasan karya haramun ne, amma ta nan take ji zata cutar da Mahir yaji yadda take ji.
"Ya tab'a, domin Office din shi da akwai dakin da yake aikata hakan da yan mata irina."

    "Shin ya samu nasara akanki."
"A'ah!"
"Toh anan muke kira da Malaman musulinci da kuma hukumar kare hakkin dan Adam da kuma na kare mata da kananun yara, su shiga domin karewa A'isha Omar Jimeta, dalibar jarida, sannan ina tayaki murna sakamakon daukar ki da gidan tv Gaskiya tafi kobo, ta dauke ki. Zamu kuma kare mutuncin ki."

   Cikin rawan jiki ya cincibo tv daga wall ya buga da kasa, cikin bala'in b'acin rai.

"Meye mata? Meye nayiwa mutane suke son ganin bayana?" Duk wani abu sai da ya farfasa, ya shiga tashin hankali, tare da  jin wani irin bakin ciki, duk yadda kake da taurin zuciya, idan kaga Mahir Hamoud Boualem CEO ya zama wani irin mutum lokaci guda depression yana niman kai shi kasa.

    Dole aka nimo Dr din shi,da taimakon alluran da aka mishi ya sami barci.

                 •••
"Noorh! Ki boye wannan hujjojin, suna bina zasu kashe ni,na tura abinda kika bani kafin ki fitar da naki, sannan yanzun zan shiga gidana,yadda muke zaton abun ba haka bane, na kiraki da privet Number ne domin kar su kamaki, ni kuma na kawo su gidana ne domin kafa hujja, Noorh Sir Mahir..."

  Karar harbi taji ta sake wayar da sauri jikinta na rawa, cikin tashin hankali, take kallon wayar, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, tana kallon wayar jin yana magana ta kuma saka wayar a kunnen ta.
"Noorh! Kanina yana Asibiti yana shan magani, mata na kuma tana Ghana na turata da yarinyata, ga kuma karamin ciki, don Allah ki taimaka min akwai sako, zata bawa gidan jaridar ku domin Sir Mahir Hamoud Boualem.."

Sake bude mishi wuta aka yi, tare da bankawa gidan wuta. Kashe wayar tayi, cikin minti talatin tana zaune a Office din su aka kunna tv.
"A yau ne muka samu labarin wanda ya fasa irin badakalar da ake a masana'antar Hamoud Boualem Company, ya mutu. Sakamakon gobara mutuwar dai ta girgiza zukatar jama'a, Mr Badar Dan jarida ne da yake aikin sirri da kamfanin tacce labarai na ƙasar nan NAN, kafin mutuwar shi yayi aiki da CNN, sannan yayi aiki da DW, kafin ta dawo yake aiki da kamfanin tacce labarai na NAN,  matashin dan shekaru talatin da tara, ya rasa rayuwar shi ta dalilin da ba a sani ba."

    Kayan aikinta ta dauka, a yau ta shirya fuskarta MAHIR Hamoud Boualem, tare da cire Hijab ɗinta da kuma Nikkab....
🙄 Na wetin go hapun?
https://my.w.tt/ylGexVK5jcb
MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 1️⃣6️⃣
     MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
#the name
Kar da wayarta yayi ne ya dakatar da ita d'aga nikkab din, ta dauka.
"Assalamu alaikum!"
"Kizo manager na son ganinki!"
"Ok!"
Ajiyar zuciya tayi sannan ta juya zuwa cikin Station din, tana shiga ta tsaya.
"Sir gani!"
Kallo daya yayi mata sannan ya had'iye yawu.
"Wato zunzurutun kokarin da kika yi ta kuma sawa za a d'aga darajar gidan tv nan, amma ga wani bincike da na samu, akan mutanen da Mr Mahir Yasaka aka kashe su! Sannan sun sha bada hujjar cewa ba kisan kai bane kashe kai ne! Har zuwa mutuwar Badar,  am sorry!"

Ya faɗa sakamakon ganin yadda fuskarta ya kuma cikin jimami, tura mata yayi, sannan ya kuma kawo wani list yace.
"Wannan kuma mutane ne, da idan wani abu ya faru dasu ake koran su, babu kyakyawan sallama."
            Wannan kuma mutanen da yake tozartawa ne, ba tare da sanin su ba, zai kore su babu sallama.
                 Noorh nasan zaki iya, amma maganar gaskiya, sai kin cire wannan nikkab ɗin da yake fuskar ki, da haka zaki iya ladabtar da Mr Mahir, a bisa tozarta ki da yayi."

          Cikin farin ciki, ta zauna tare da cewa.
"Nagode yallabai, sannan kuma zanyi aikin da zai d'aga darajar Station dinka, sannan batun nikkab Insha Allah gobe zan fara zuwa babu shi."

"Yawwa akwai taron manema labarai da za ayi a kamfanin Hamoud Boualem, CEO zai gabatar da abinda ya kashe Badar, kuma ina ga wannan sune Hujjojin da zaki rike, Noorh sakamakon abinda kika yi, ta janyo miki nasara, sannan ki bani Acct Number ki, domin Mr Aysar Haladu yana bukatar ki fara mishi tallar kayan ruwan shi."
       Dake bahaushe yace duk wanda ya rigaka kwana toh fa shi asubanci zai yi, sam Noorh bata san dalilin da Badar yace karta kuskura tayi magana ba! Saboda, sai da ya gama bincike ya fahimci akwai manyan mutane da suke buƙatar durkusar da Mahir da kamfanonin shi na kasar.

           Abubuwa da ya bankado ya tura mata ta email din ta, dan ya yarda da ita sosai, sama da yadda ya yarda da kowa, shi yasa ya zaɓi ya bata aikin, sakamakon yadda take bata da hayaniya, kuma bata da rawan kai irin na Tasleem.

       Murmushi Manager yayi sannan ya ce mata.
"Insha Allah zuwa yamma zaki fara ganin kuɗin aikinki." Godiya tayi sannan ta fita, fitowa wani matashi wanda ba zai wuce sa'ar Mahir ba ya fito yana murmushi.

"Yarinyar tayi aikin da ake bukata, kuma kamar yadda akan gaya min, akwai wasu abubuwan da ake bukata ne ta fito dashi, domin kafin mutuwar shi yayi waya da ita. Kuma itace tasan halin Mahir ita kadai zata iya tunzura shi ya aikata abinda nake buƙata, sauran kuma zamu ji dashi. Idan nace zan saka a mishi wani abu, Ni zan fadi domin ana tab'a shi hukumar tsaro zasu yi magana, amma idan na barshi aka sami fitinannen da ya shiga gaban shiga cikin al'amarin shi zai zama na duniya ta zuba mishi ido. Abu na farko da ta faɗa wallahi nasan ba haka bane! Mahir ba mazinaci bane domin na zauna dashi a Militry College 2003, sannan mun kuma haduwa a team na a Kashmir 2007. Kuma dukkan mu course yake hadamu.

          Kawai nasarar shi nake son ta zama namu ni da Abokina, sauran da suke ƙoƙarin ganin bayan shi, sai su kara himma, Ni dai kamfanin shi nake son ya rufe."
           Murmushi Manager yayi sannan yace masa.
"Ba kai kadai kake son ganin shi ya fadi ba, amma ka sani duk abinda zaku yi, ku tabbatar kun gama shi cikin kwanakin nan. Idan ya wuce haka wani abu ya biyo baya toh wallahi zaku iya fadawa matsala."

        Sun jima suna tattaunawa, sannan suka yi sallama.
---
Duba takardun tayi lokacin da take cikin napep, kamar daga sama taji an daki napep din su, haka tayi ta tangal tangal, kafin Allah ya taimaka suka tsaya, Motar Mahir ta gani amma bashi bane.
      Fitowa tayi tare da kallon mutanen da suka tsaya suka jajjanta musu.
"Wannan al'amarin ba su kyauta ba, Allah ya tsare ku."
    "Wato dan yaga bai samu damar min kome ba, shine ya turo a kashe ni?"
"Kin san shi ne?"
"Mahir Hamoud Boualem CEO!"

Shiru gurin ya dauka kafin kowa ya shiga darewa, sakamakon jin wanda ta kira, tare da sanin me zai aikata, tunda ya rigada ta bata mishi suna. Dan haka suka watse dakyar me napep din ya kaita gida, tana isa babu wanda ya ce mata me kika aikata me muka ji, asalima kamar ma tsoronta suke ji, cikin dare kuwa bayan ta idar da sallah dare, kawai ya shiga sake wasu bayanai tare da cewa yau ma Mahir ya kaiwa Noorh hari zai kashe ta, bayan abinda ya faru. Abubuwa da yawa ya kuma sakewa har da Voice din shi na karshe.

      --- washi gari abubuwan suka watsu a duniya, Nazzir shi kan shi sai da ya girgiza balle kuma Aysar Haladu, wanda suke tsammanin daga bakin Noorh na zahiri dan babu wnda ya san itace take wallafa shafin, sannan Badar ya bata kariya ta hanyar hacking din Acct ɗin, ba tare da sanin ta ba.

                Mahir kan zan iya cewa jinin shi ya haura sosai, domin kuwa baya iya magana sai kallo da ido.
    Da ta isa gurin aiki kuwa kowa sai da ya rufe tare da mamakin dama itace Noorh, Manager kasa zama yayi ya kasa tsaye, sabida bai taɓa dauka ta haɗu har haka ba, gashi dai riga da zani ne sai After dress da ta daura akai, tayi kyau sosai, domin tayi rolling kanta da dan karamin gyale, babu wanda bai yi farin cikin sake bayanin da Light yayi ba, musamman yunkurin kasheta da aka yi jiya da yamma. Haka da ya faru ya matukar girgiza duniya.

       Ranar ta tsara abubuwan da zata tuhumi shi tayi, dan ya gayyaci tashar ne. Su kuma suka tura mishi Noorh.

         A cikin kwanakin da aka shirya tattaunawa da yan jaridu, ta sami damar shiga Hamoud Boualem Estate, tana cikin napep tazo wuccewa shi kuma ya fito zai tafi gidan kakar shi, kallon juna suka yi ta sake mishi murmushi, dauke kan shi yayi tare da gyara zaman shi Wali na jan shi, wani irin bugu zuciyar shi yayi haka kawai ya rasa sukuni, dan har sunyi nisa, gani yake kamar yasan kwayar idanun da ta wuce, kamar ya santa. Amma ba zai ce ga ita ba. Ita kuwa ana sauke ta a kofar gidan Badar ta zaga ta bayan gidan ya shiga ta window, tayi ta yawo, bata sami abinda yazo nima ba, har ta gaji ta bar gidan dan tana tsora ce kar ya kuma sakawa a biyota, tana fita ta bayya, shi kuma yana shigowa ta gaban gidan.

        Ya shiga kallon ko ina, tare da bin yadda gidan ya kone, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kai kan shi zai fita yaga wani dan karamin frame bai kone ba, kawai ya ciro tare da fita dashi a gidan. Yana kallon gaban abin.

         Tsaki yayi tabbas, ya me irin idanunta sai dai ba ita bace, da yau itace ya kamata, abinda tace zai mata sai yayi ya barta a wulakance, wannan shine alkawarin da yayiwa kan shi, duk ranar da ta shiga hannun shi.

      •• cikin kwana biyu, ta gama shiryawa tsaf,ranar Talata ya kira taron manema labarai, lokacin da suka isa gurin, ana cikin tattaunawa, har Mataimakin Kwamishina yan sanda, ya tabbatar da cewa Mutuwar Badar kashe kan shi yayi sakamakon yana fama da ciwon hauka. Maganganun mara sa dad'i aka yi akan shi, wanda ya sanya aka dauko hoton kanen shi aka gwada domin ya zama shaida ga zargin da aka ga kamfanin.
"Mutuwar Badar ba Suicide bane Murder ne." Juyawa kamarorin Suka yi lokacin da Noorh ta mike tare da cewa.
"Idan mun fahimci Sakon da shafin Light take gabatarwa yana fada mana cewa, CEO yana sane da mutuwar yan jaridu guda takwas yan bautar ƙasa shida, sannan shaidar da ya fitar na muryan Badar yana cewa, Noorh ta fahimci abinda yake faruwa Mr Mahir... Anan aka ji karar harbi shine kashe kai?"
Shiru kowa yayi cikin tashin tsoro take kallon shi, yana kallon ta.
"Wacece ke?"
Inji Mataimakin Kwamishina,
"A'isha Omar Jimeta! Noorh!"
Wani masifaffe b'acin rai ne ya kuma cika mishi zuciya, tare da kura mata ido, wannan itace abar da take mishi Iskanci.

    Tunda aka tambaye ta, sunanta, Noorh ta shiga jefa mishi tambaya cikin, renin hankali tare da disga shi a gaban jama'a, wani irin yanayi yake ji na duhun bakin ciki, ya mike cikin zafin rai tace.
"Kunga abinda nake gaya muku ko, baya da alkibla sannan baya kaunar gaskiya! Mr Mahir, nifa akan aikina nake, dan haka zaka iya shafawa kanka ruwan sanyi, kasha ruwan sanyi."
Takowa tayi har gaban shi tana kallon shi cikin wani irin murmushin nasara, tace mishi.
"Nace maka zan dauki fansa? Kace idan na dauki fansa zaka baki kyauta na musamman, mr Mahir Hamoud Boualem, na gama ina jiran kyautar da zaka bani."

      Wani irin bugu zuciyar shi take, dan kamar zuciyarshi zata fado daga cikin shi, yana kallon ta murmushi yayi mata sannan yace mata.
"Zan baki kyauta! Zan kuma kara miki kyau, amma ina jiran ki gama wasanki da kike yine, domin Ni sunana Zaki ne, Ni zan farauto kuma na ci na barwa sauran, Ni sarki ne idan zan shimfid'a mulki dole ina bukatar irinki, tun anan zan gwadawa duniya ina shirye na fara aiki aikan iyayen gidanki."
Wani irin fisga yayi mata, tare da jiyar da ita, ta fada kirjin shi ta baya, ya Kuma kai hannun shi duka biyu ya rungume ta ya daura kanshi a kafad'arta yana kallon mutane. Wani murmushi yayi cikin kwarin gwiwa, sabida yadda yaga kowa ya razana, gashi sai kokarin kwace kanta take tana masifa tare da cewa yan uwanta yan jaridu.
"Kingani  ko? Kunga abinda ya tab'a min a gaban ku ma yayi min!"
"Mahnoor! Shine ya dace da sunanku!" Inji wani daga cikin tsirarun mutanen da suke gurin, bayan yan jarida, tureta yayi sannan yace.
"Ku fita ku fice min daga cikin kamfanina, kafin b'acin raina ya kwace ba baku mamaki, kuma tambayoyin da kika yi min, zaki kuma maimaitawa a kotu,.sannan wannan haukar da kike zaki gane baki da hankali, ba dai Aysar Haladu ba? Mutumin da yaci amanar kasar shi wani shege ne ba zai ci amanar shi ba, b'ace ki bar min nan kafin raina ya kuma b'aci na karasa kunyar dake a gaban mutane."

     Cikin zunzurutun rashin kunya ta shiga gaya mishi magana tare da tabbatar mishi, sai ta gallabi rayuwar shi, rikicin da takai ana rike su zasu daku, abun ya bawa kowa mamaki, yadda Noorh take kokarin sai ta zabga mishi rashin mutunci. Shima kuma ya rantse matukar ta iso gare shi sai ya nuna mata tsagwaron rashin mutunci, ganin abin ya kazamta yasa aka janye su aka tafi da ita.

     Wannan rikicin ya zama wani irin rikici, dan ta kai ta kawo ana fara hada sunan su, ana fashin baki kai, dayawan mutane suna alakanta abin da sunan hadin Ubangiji ne yake shirin faruwa kan su. Gidan jaridar ta kuwa sun kara mata kudi da uban matsayi, yayinda suka fara niman bude mata ido da kashe ta kudi na bala'in, abinda ya kwace ta a wannan lokacin shine mace ce mai ibada, bata wasa da sallah. Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, ya tabbatar matukar karike sallah zai yi wuya ka tsinci kanka da aikata masha'a da wasu abubuwan da aka haramta su a musulinci.

   Daga Tasleem har iyayenta babu wanda yayiwa Noorh magana sai ma jin dadin da suke ta kwaso ruwan dafa kanta..

   A cikin sati guda, Mahir ya tasota a gaba, idan zata aiki sai ya tare hanyar, idan ta fito zata yi ta fita da kafa, yana cikin tafiya zai saka a tsare hanya babu gaira Babu dalili, haka zata rasa yadda zata yi ko ta kira Office, aka zo hanawa yake, idan kuma ta tsare abin hawa, Yasaka akwace ita kuma ya saka a hanata tsayuwa a bakin shagon kowa sai a tsakiyar titi, domin kashe hanya daya yake.
Gefe guda jama'ar gari sun kuma kamala musu sunan su a tare har

Please Login or Register in order to submit comment