Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaya mata.
"Don Allah ki saurare ni, Wallahi."

"Kul ka rena min hankali, idan ita ka aure ta cikin renin hankali, Ni ba zaka rena min hankali ba, Mahir kar na kuskura na ga kafarka a cikin gidana, ni zan sanya ka kayi abinda ya dace.

      Idan naga kafarka a gidan, wallahi ko kana son auren ta,ko baka so sai na raba ku da karfin tsiya, hmm ba ka tozartani ba? Hankalin ka ya kwanta." Daga haka ta ja hannunta suka bar gidan, da motar ta dama tazo. Tunda ta shiga motar, bata ce ma Noorh kome ba, dan tana jin kukan yarinya yana tab'a mata zuciya, ga tausayin ta da ya kama ranta, zata iya cewa.itace yarinya na biyu da ta kwanta mata aranta, tun bayan wancan Aeesha da suka yi hatsari da ita, yau Noorh ta sami wannan damar shiga zuciyarta lokaci guda.

      "Ki min shiru, sakarya kawai. Ko wani irin wayo yayi miki da kika yarda dashi ya aure ki babu sanin danginki, wato da aka ce kin mutu shine kuka zauna kuna ta aikata shirme ko? Toh zan gaya miki gaskiya ko yau na barki dashi namiji ne bai da Tabbas zai iya juya miki baya, kuma ya miki gori yadda sai kinyi dana sanin abinda kika aikata, dan haka zan maida ke gurin danginki, domin shima ana niman matar shi ce, da aka daura musu aure tun da jimawa, dan haka idan zaki iya zama dashi toh idan kuma ba zaki iya ba, sau kuje can ku karata, dan ban san lokacin da kuka shirya haukar ku ba....
Reply by Noorh 🤣😂🙈😜 laf go feel kil me, domin team Mahir kuna ruwa kusa da kada 🙏🏼 sorry yau da gobe ina busy sosai zai yi wuya kuna samu da wuri. Amma Insha Allah duk yadda aka yi zaku ganshi sul ☺️
[1/23, 11:09 AM] Addah Ramlat MANGA: https://my.w.tt/nRXa3Y11Scb

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣2️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Budar bakin ta, cikin kuka tace.
"Wallahi dole yayi min domin ni bana son auren shi!" Cike da mamaki Ummi ta kalleta dai dai tana shiga cikin gidan.

"Kika ce baki son auren da kuka yi? Toh taya haka ya faru?" Kuka ta saka mata, har suka isa cikin gidan, ganin Shibha tayi da gudu, ta rungume ta.
"Aunty Noorh! Me yasa ki kuka? Yaya ne ya dake ki? Ummi dubu yadda?"

"Rufe min baƙi kiyi shiru, ki kaita dakin shi da yake sama," inji Ummi,
Kallonta Samiha tayi cikin fusata tace.
"Wannan ba yarinyar da ta lalata mana kamfanin mu bane?"
"Itace kuma matar shi!" Inji Ummi,
"What???"

"Toh wallahi ba zata zauna mana a gidan mu ba," inji Adeemah,
"Bata da masauki a gidan nan, zoki fita dan abukazan ki."

Inji Hidaya, ta fincikota zasu fita da ita.
"Ina ga kamar nice na zo da ita ko? Tunda Ni ce na shigo da ita babu ruwan ku da ita, kusake ta,kafin raina ya ɓaci da haukarku." Take suka shiga hankalin su, sakamakon yadda suka ji muryanta, sanin cewa idan ta barta a dakin Mahir ba zata sha ta dadi ba, yasa ta kira Shibha tare da cewa takaita dakinta. Domin tasan halin Yaranta. Suna da haɗin kai. Duk abinda ya sami daya toh kamar ya samu daya ne.

Tunda Shibha ta kai ta, dakin kallon duniya tayi sosai, cikin mamaki tare da al'ajabi take bin ko ina da ido, yadda d'an adam yake rayuwa cikin yancin da salama, Kamshin turaren dakin ne ya cika mata, hancin ta rike bakinta da take lubiyar amai,.da gudu ta nufi hanyar fita, suka yi kicibis da Ummi.
"Ga ban daki can, juya ki shiga"
Da sauri ta shige ban ɗakin,, tai yita kokarin juye shi,. amma bai fito ba, karshe zama tayi a ban dakin tare da kishimgida barci, tare da kamshin sabulun wankan da na wanke ban dakin yana ratsa ta, sai kuma baza hanci take, cikin kwanciyar hankali.
Idan ran Ummi yayi dubu sai da ya b'aci sosai, kallon Noorh tayi da take barci a ban dakin.
"Yarinya na! Tashi nasan ai kin san babu kyau kwanciya a cikin ban ɗakin, fito ki kwanta."

          Idanun ta ne suka cika da kwalla, tace.
"Ummi bana son kamshin turaren dakin ne."
   "Toh shi kenan, zo na kai ki daya dakin."
Haka ta mike jikinta babu kwari, amai take ji amma cikinta babu kome, ta wuce da ita daya bedroom ɗinta, ta kwantar da ita a saman gadon, sannan ta kira likita.

       ..... "Shibha gashi ki bata wayarta, don Allah ki tambaye ta meke damun ta, ki tabbatar ta i abinci."
"Insha Allah."
"Amma Yaya yarinyar nan fa tayi maka abubuwa da yawa, me yasa ka taimake ta?"inji Hidaya da Samiha, Adeemah kan ta cika tam kamar zata fashe.
Furza da iskar bakin shi yayi sannan ya juya yana faɗin.
"Kwatsam Allah ya juye min kaunarta, bayan nan bana jin akwai abinda zaku bukata daga gare Ni,.sai dai kar ka yarda naji wani kallon banza ya shiga tsakanin ku da ita. Naji haka toh zan sab'a muku."

      Daga haka ya bar gidan, dan wallahi ya rantse ba za a raba shi da matar shi kuma ace kar ya zo ba.
           --- tunda likita ya gama ainu ne ainun shi, ya amshi fitsarinta yayi mata duk wani test, ya fita, bai kuma dawowa ba sai dare dake ya saka mata drip, lokacin da yazo ya samu, ya kare tana sallah isha, nan ya mikawa Ummi sakamakon,.bata yi mamaki ba. Dan tun daga daukota ta fahimci danyen ciki ne da ita.

             Bata kuma bin ta kanta ba, ta sallami likitan, fada dai na Uwa da d'a Ummi tayi wa Noorh ita da Hajiya, dan sosai suka nuna mata illar abinda suka aikata, tare da mata barazanar sai sun kashe auren, dake yar banza ce bata da hankali, ai kuwa ta sake bakinta ta gayawa Ummi cewa bata son auren dole yayi mata, tare da gaya mata na kwangila ce.

    Ita bata tab'a kaunar shi ba, sam bata son shi, kawai bata da yadda ta iya ne, ita don Allah su rabata da cikin jikin ta, amaida mishi cikin shi. Yadda take fadawa Ummi magana tare da niman amata adalci, Yasaka jikin Ummi yayi sanyi, domin ita kanta tasan tunda Mahir ya kasa bin dokar ta ya shigo gidan, tana ganin shi tayi imani ba karamin son Noorh yake ba, ya kuma iya jure duk wani abinda tayi mishi ya zab'e ta, a matsayin abokiyar rayuwar shi, akwai tsananin kauna a ranshi.

         Duk wannan Maganar da suke a kunnen Hidaya, dan haka jikin Hajiya da Ummi a sake, suka bar mata d'akin, suna fita hadiya da Samiha suka shiga dakin suka mata wulakancin da tunda take babu wanda ya tab'a mata.

   Karewa suka ce mata cikin da take ihun a cire toh ai sun san labarin yadda take rabawa maza,dan haka dan uwansu ba zai zauna da taxi ba fasinja ba.

   Sun gaya mata maganar da sai da ta kusan haukacewa, sannan suka barta haka.
    Kiran shi Ummi tayi, ta mishi fada sosai tare da mishi iyaka da Noorh, ta kuma mishi magana akan lallai yazo su nemi matar shi, yace wallahi sai ya sake wancan dan shi wannan yake so.

Ita kuma tace mishi idan ta haife shi ya sake wancan, sai ta haramta mishi Noorh, sai dai idan bata raye ya auri Noorh, jin haka sake mutum ne me ilimin addini, tuni ya hakura ya kuma nuna mata tayi mishi duk abinda ya dace amma shi bazai je niman wancan ba.

    Jin haka bai wani dame ta ba, domin Noorh ta b'ata mata rai, amma bata son ta gaya mishi gaskiyar abinda tayi mishi balle ya kai su ga samun sab'ani, karshe su dawo su shirya ita su barta da kunyar abinda ya faru.

    Dan haka ta mike sosai, gurin Niman A'isha, sanan ta je har jos aka turata Yola, bata gaya mishi ba. Ta dawo gida, a hankalinta kwance bayan kwana biyu, suka tashi har da yaran ta suka nufi yolan inda aka kai su har gidan su Tasleem.

            Anan suka fadi abinda ya kawo su, babu tsoron Allah. Baban Tasleem yake kuka tare da gaya musu ai Tasleem ce, su yar su ta jima da rasuwa, itace a lokacin da abin ya faru, yanzun shekaru goma sha biyu kenan, kuma dan uwan shi ne mahaifinta, sun tattauna sosai. Ganin irin kaunar da suka nuna mata, kamar ba mareniya ba, yasa Ummi karban ta, amma ranta bawai ya kwanta bane, haka suka gama abinda zasu yi, sanan suka bukaci Tasleem tazo Lagos a gabatar da bikin auren tunda an tabbatar da auren su yana nan Babu abinda ya faru,

Nan Baban Tasleem ya dire akan lallai a kuma daurin auren, wanda zai kai karshen shekarar da za a shiga, dan haka Ummi take cewa, sabida mareniya an zama daya akwai gida a cikin Estate din su, yazo su zauna acan.
             Kunga ne, irin tuwon girma miyar nama, Ummi tayi musu, amma dake mutanen banza ne, basu ki tayin su ba, suka ce zasu zo nan da sati biyu masu zuwa.
                   --- A ranar suka dawo, anan suke Baje irin abubuwan da ya faru, kallon su Hajiya tayi sanan tace.
"Ni kuwa bana jin wanan abu akan wancan me kama da katakon, nafi jin wani al'amari akan wannan yarinyar na cikin gidan."

   Haurawa sama Ummi tayi takai hannu zata bude ɗakin, ta Abinda Noorh din take faɗa.
"Yaushe nace ina sonka? Me yasa ba zaka sake ni ba, wallahi kaji na rantse duk lokacin da na fita sai na zubda cikin nan. Bana sonka ka gane ma,   idan kun gadama ka auro wacce ta fini MAHIR Hamoud Boualem, Allah sai ya saka min mugu tantirin mara mutunci."
"Ke wacce irin Sha-sha-sha ce? Mijin ki, kike gayawa magana kamar kina yi da sa'ar ki?"
Sam Ummi ta rasa me zata gayawa Noorh ta fahimci halin da Mahir yake ciki tana azabtar dashi.

   Kyaleta tayi tare da barin d'akin, wallahi tana masifar jin ciwon abinda Noorh take mishi, kuma bata son ta tsani Noorh sabida Mahir, sam a matsayin ta na Uwa bata son ta fara tsanar matar danta, duk da Matar shi ta fari tana nan toh amma a matsayin ta na second Wife bai dace tana wannan haukar ba, haka ta zuba mata ido.

           Sai da ranar Hajiya ta sameta cikin hikima da dabara take gaya mata kuskuren da take aikatawa, tare da nuna mata illar abinda take yi, take jikinta yayi mugun sanyi, sannan ta mata misali da kanta zata ji dadi wani yazo ya gayawa dan da yake cikinta zata ji dad'i, indai ba zata ji dadi ba haka Ummi take ji idan tana aibatan Mahir. Kuka tasaka tare da zuwa study room, ta shiga ta sami Ummi, ta zube a gabanta, tana kuka. Duk sai taji babu dad'i domin kuwa duk uwa ta gari ba zata tab'a barin wannan al'amarin ya tab'a zuciyarta ba, matukar tasan akwai alaƙar jini a danta.

     Dan haka tayi mata nasiha, tare da gaya mata nan da sati biyu matar Mahir ta fari zata zo, ita bata yi haka dan ta muzanta mata ba, asalima ƙaddara ce ta hada kome, dan haka ko dan albarkaci Babyn cikinta ta ajiye kome a gefe ta rungume mijinta, idan tana nuna mishi hanyar da wata zata kwace mata shi zata wahala,

        Jikinta yayi sanyi amma ta kasa daina kuka, tunda ya gaya mata maganar auren shi take kuka, da matar shi na farko take yawan kuka, ta kalli Ummi cikin kuka tace mata.
"Ban san yadda zan yi ba, don Allah kice ya kaini gurin dangi na, bana son wata rana ayi min gorin rashin dangina."

              "Zan mishi, amma kije dakin shi, ina jin yana can tun safe. Ki gaya mishi cikin nutsuwa da hankali, karki yarda ki gaya mishi magana mara dadi, matukar haka ya faru, Am deeply sorry, ba zan sanya shi dole ya rabu dake ba, kuma zan sanya shi dole ya Aika dake ba. Amma duk wani matakin da ya dauka ba zan hana shi ba."

     Gyada kai tai, zata fita Ummi tace mata.
"Daga nan ina zaki?"
"Dakin shi."
"Kuma kinyi zaman jami'a? Dalla wuce kiyi wanka, ki gyara jikinki kizo nan na ganki."

    Cikin matsanancin kunya, ta wuce ba tare da tayi magana ba, ita dai Ummi son Noorh take wallahi, haka tayi wanka ta shirya tsaf, sannan tazo dakin karatun, murmushi tayi sannan tace mata.
"Ko ke fa? Maza kije ki dafa mishi Black coffee." Sannan ta yi mata fada sosai, tare da nuna mata illar da take wa kanta da cikin jikin ta, haka Noorh ta je kitchen tana aiki taga Adeemah. Bangaje ta Yarinyar tayi, bata kula ba, ta gama abinda zata yi.
"Matsiya ce bai iya samun dama ba, an sake ana ta cin Arziki."

        Bata kulata ba, haka ta gama abinda zata yi, ta haura tare da nufar dakin shi, yana zaune a gaban laptop, ya tara Uban kasumba,  sai uwar hancin da suka fito da kasumbar shi, dauke kai yayi sannan ya cigaba da abinda yake.

   Ajiye mishi tayi a table din shi, tare da juyawa zata fita, yace mata.
"Wannan rashin darajar da?"
Juyawa tayi kamar zata tsigale shi, sai kuma ta fasa, ya nufi inda yake tana shashekar kuka, bude mata hannun yayi. Da sauri ta isa gare shi, ajiyar zuciya ta sauke cikin kuka tare da kara shigewa jikin shi, tana shaƙar kamshin turaren shi. A hankali yake goga kanshi a bisa kafadar ta, tare da shafa lap ɗinta, kusan sati biyu, bai sakata a ido ba. Kallon manyan Boons ɗinta yayi,  a hankali ya zare mata hijab ɗinta, tare da kallon rigar jikinta, irin net din nane, kana kallon kome ta cikin shi, a hankali ya zare rigar, Allah ya gani yana azabar kewarta, dan haka bai wani ja lamarin yayi nisa ba, ya daura kanshi saman Boons ɗinta wanda suke shirin zautar da imanin shi, ya shiga aikata musu da sanarwar yana tare dasu. Aikuwa jin murza tare da tab'ayya, sai gasu nan sun mike tarr..
Daga nan kuwa, (Mugu ya sami yar mutane da bindin shi, kar dai garin zungura a zungunro Babyn 😏😒) haka ya dauke abar shi zuwa dakin shi, anan yayi ta gurgureta, dama gashi tayi wani irin dumi irin na masu, ta wani irin bala'in haɗewa, kome na Jikinta ya koma wani iri dumi me shegen dad'i da wani irin armashi, shi kan shi a zaucce yayi ta Binta, kamar ba zai barta ba musamman da yaji tana ambaliya, nan ya kunce mata. Yana tab'ata kadan ya juya zsu huta, kuka tayi shi kamar ranta zai fita,ga ciwon ciki da mara. Wajen karfe biyu tana rike hannun shi cikin kuka tace mishi.
"Ya Mahir, karka cutar da babyn mana, wallahi ina jin abu zai zubo min"
Mai da hannun yayi baya, cikin gurnanin dad'i yace mata.
"Karki damu babu abinda zai zuba, ina tare daku."
(😏🙏🏼 Mayye kawai sai ka cinye muruyar ka huta)
     Dakyar mayyen karfen ya rabu da karfin ya huta, wani irin ajiyar zuciya ta sauke, tare da lumshe idanun ta, ita kan bata san dadin wannan abin ba, domin bata tab'a fahimtar yadda abin yaƙe kallon shi da sunan wahala take, da Mahir zai sassauta mata Tabbas da ta gudu inda tafi wayo, shafa boons ɗinta yayi cikin nutsuwa, yana kuma kara shigewa jikinta yace.
"Noorh baki samun nutsuwa dani, kawai Ni ke jin dadina Amma ke baki jin kome akan rayuwar mu, lokacin."
"Nifa ba shine matsalata ba, don Allah ka kai ni gurin dangina idan ma ba zaka kai ni ba, ka barni naje gurin su da kaina don Allah."

   "Tab! Ki bari idan Allah ya kai mu bayan sallah layya na kai ki, Amma yanzun da kike fama da ciwon laulayin nasan rike min ke zasu yi, ina dalili ina son duk lokacin da na zaga, na kawo miki bindina ku gaida juna."

     Kura mishi ido tayi, bakinta ne yake motsin rashin kunya, mik'ewa tayi zaune ta fashe da kuka, tare da jan zanin gadon ta rufe jikinta tana kuka, tare da juya mishi baya, murmushi yayi sannan ya kai hannun shi k'ugunta, yana goga mata gemun shi, cikin rarrashin da yake tafiya da zuciyar mace, ya shiga bata baki, dakyar tayi shiru, sannan suka bar dakin zuwa bayi. Tare suka yi Wanka.

   Koda suka fito, taso dawowa d'akinta, amma ya hanata. Yayi ta mata hanya hanya har barci ya dauke ta, yana shafa bayanta....

     ..... Cikin dabara da hikima, Ummi tayi ta nuna mata yadda zata rike mijinta, tare da kulawa dashi. Amma haka bai hanata rikice musu ba, idan ta tuna da auren shi zai yi da first Wife din shi, bata son shi amma haka take wuni tana kuka, yan uwan shi kuwa dama haushinta suke ji, gashi yazo ta wani shige musu jikin mahaifiyar su da Hajiya, tare da Zoolfah suke mata wulakancin sosai.
[1/23, 11:09 AM] Addah Ramlat MANGA: https://my.w.tt/YXHFir6fUcb

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣3️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Sun dauka zata biye musu ne, sai suka ga bata da lokacin su ma, matsalarta daya Mahir ya taimaka ya dauketa daga cikin su, dan ma cikin yayiwa Ummi cikas domin tsakanin ta da Allah take bawa Noorh kulawa, kuma ta fahimci irin rabon nan ne da matukar ba a Barni na zo ta hanyar da ya dace ba, Tabbas zan iya zuwa ta karfin tsiya kusan akwai irin wannan cikin.

Idan bai zo ta hanyar halal ba, toh ko yayi kisa ko kuma yazo ta hanyar banza, dan haka Hajiya take girmama al'amarin cikin jikin Noorh, koda Baban Nazzir yazo da maganar Zoolfah, dakatar dashi Hajiya tayi tace.
"Yanzun muna son mu lallaba shi ne, akan wancan auren da aka yi a cikin jirgin kasa, yaki nutsuwa domin yace ba zai rike mace sama da daya ba, shi mijin mace daya ce."

"Amma Hajiya haka zai cigaba da juya ku, kamar shine sama da kowa? Haba ai ya kamata a tsawarta mishi." Jin sautin takalma ya sashi d'ago kanshi Mahir da Noorh ne hannun su sarke da juna, fuskarta fayau. Dan yanzun take jin laulayin sosai.

            Sai da suka sauko kasa, ta gaida Baban Nazzir, sannan ta koma kusa da Hajiya ta kwanta, tare da jin kewar Mahaifiyarta, dan ji take kamar tana tare da wani na jikinta, shafa kanta tayi tare da saka mata albarka. Jin dumin kwalla yasa ta zubawa Mahir ido, mara kirki ya kame a kujeran yana wasa da puzzle box mission.

      Kallon Baban Nazzir yayi tare da cewa.
"Kawu! Nikam kwana biyu bana ganin Nazzir, ko ya bar kasar nan ne?"
"Yana nan akwai wani gasar da ya shiga ne na chased"
"Ikon Allah yaushe aka fara wasan ban sani ba?"

    "Tun ranar da aka tare mu na sashi shiga gasar."
"Toh kuwa za a buga wani domin ina son farar sarauniyar!"

"Kasan kuwa ba zai dauki bakar sarauniya ba!"
"Zai dauka mata tunda na tsare bayan shi a ina ke buga wasar!"
"A Nicol hotel ne!"
"Har abuja?"
"Ko baka shirya zuwa bane?"
"Tsaf na shirya cikin fahimtar haka!"
"Toh ita wannan wasar ta sake haja ce!"
"Tuni na fahimci haka!"

A wasa a wasa, sukai ta gayawa juna magana, tare da tilasta juna saka abubuwan da suke bukata a game din chased, shi kuwa Mahir yana sane da hakan, domin ta fahimci kawun shi burin su, ya saka Noorh a gasar, shi kuma Mahir Burin shi, a saka Zoolfa a cikin wasar.

    Cikin tsananin zafin rai Baban Nazzir ya tusa Zoolfa, inda yake cewa.
"Na saka kadara Mafi daraja a cikin ahalin gidan mu, kai kuma yarona me ka saka a cikin naka kadara?"
"Kadarar da zan saka biyu ce, akwai abinda nafi so. Akwai kafatan dukiyar Hamoud Boualem,.da  kuma jiragen ruwa tare da masu Safara. Sai numfashin Mahir Hamoud Boualem na saka."

"Maka sane zaka kai labari."inji Baban Nazzir.
"Me zai hana na kai labari an haife ni domin nasara ce!"
."Yarona inda ba kasa?"
"Kawuna nan ake gardaman kokuwa. Mu hadu a garin Abuja."
Daga haka kowa ya mike, dan Mahir zama da Noorh ya koya mishi iya tinzira mutum.

       Domin yaga fusata a kwayar idanun Kawun shi, kuma burin shine ya fusata dan banza, dan haka suka fita. Asibiti ya kaita aka duba lafiyar cikin jikinta, duk da tana nan da halinta bai hana shi kaita gidan shi da yake Ekoyi ba, ya gurgureta son ranshi . Itama yar banza bata hana shi domin tana son haka, musamman cikin ya saka mata son kamshin turaren shi.

     Daga nan yana tab'ata toh zata mika wuya sai ta nutsu ne zata shiga mishi rashin mutunci da borin karya.

   Haka ba karamin dad'i yake mishi ba, kuma ya lallabata da dadin bakin zai kaita Algeria. Dake sokuwa ce, lokaci guda take manta kome.

    Wani lokaci Ummi har dariyar Noorh take yadda ta tsani Mahir amma kuma bai hanata idan ya dauketa suka fita ba, ba zai dawo da ita gidan ba sai bayan kwana biyu, bata tab'a hana shi ba, dan ta fahimci danta mutum ne me bukatar kulawar Mace ta wannan bangaren. Shi yasa take yawan bawa Noorh din fruit akai akai, tana sha. Kuma tana jin dadin hakan domin da farko kullum sai ta taimakawa Noorh din sabida ciwon mara da magani, amma tana fara bata fruit ta daina sabida tana samun wadataccen ni'ima, wanda shi kanshi Mahir din ta Fahimta, dan haka yake ninkayar shi a gonar shi son ranshi.

        ..... Bayan kwana goma, suka nufi Abuja a can suka fara  samun an fara game din, inda suka tarar da Nazzir ya gayyaci wasu gogaggun yan wasa, da suka iya game din, murmushin jin dadi Mahir yayi dan yasan abinda yake yi, kuma ya yarda da kanshi, game din da ya koya a las vegas.

Game din da suka yi kamar Hauka, lokaci zuwa lokaci yana bugawa da shida abokan shi. Dan haka yana zuwa bai nemi taimakon kowa ba, ya saka game din aka fara bugawa, anayi ana hira kamar ba zai damu ba ko wani abu ba.

      Abinda ya sani matar shi da ya saka dai sai ya cire ta, cikin sauki..dan haka aka fara wasan cikin nasara da faduwa kuma hukumar wasan sun san cewa duk wanda da aka saka mace a cikin shin. Toh matukar aka ɗauki farar sarauniya hmm. Ba a cewa kome.

    Awa biyu suka shiɗe, kafin Allah yabawa Mahir Sa'a ya fitar da Ben daga kasar Dermark,karfe sha biyu suka fita zuwa dakin su da suka kama, kwanciya yayi sannan ya kalli Noorh da ta saka Idanunta akan laptop din shi.

Tana faman aikin, kamar babu wani abu dake damunta, tana idarwa ta kalle shi tace mishi.
"Next game dinka, da Nazzir ne nayi musu kutse."
Kallon ta yayi na wani lokaci.
"Me yasa kika yi haka!"
"Lokacin ana game din, ina lura da shi yana turawa abokin game dinka sako ta wayar tare da bluetooth."

     "Toh meye fa'idar hadin da kika yi?" Ya tambaye ta.
"Zaka gani, domin nima sani aka yi." Cike da mamaki yake kallonta,
"Waye ya saki?"
Mik'ewa tayi zuwa ban daki, ya biyo ta,juyawa tayi ta zuba mishi ido.
"Ina magana kin share ni?"
"Baka bukatar amsata!"

"Noorh!"
"MAHIR!"
Mai da ita jikin bango yayi, cikin wani irin kallo.
"Bana son haka!" Tace mishi,
"Toh meye nufinki?"
"Kai baka iya tinzira abokin adawa bane? Ko baka iya sanya shi yayi abinda bai yi niyya bane? Kasaka a ranka wannan game din domin Badar da ahalin shi zaka yi, tare da sauran al'ummar da suka rasa rayukansu a sanadin son zuciyar shi." Daga haka ta kwace jikinta tayi fitsarinta da Me girma ciyaman (😜😂🤣🤨)  fita yayi ganin da gaske pu take, tunda ba abin Arziki bane da zasu raba tare,(😂🤣)
Tana gamawa ta yi wanka tare da gyara ko ina, na jikinta ta fita, saka kaya tayi tare da gabatar da sallar azhar.

      Karfe hudu na yamma aka koma game din, tare da Nazzir kallon Juna suka yi sakamakon shigar da Noorh tayi wanda ya tafi da kafatan rayuwar shi, zama tayi

Please Login or Register in order to submit comment