Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nazzir, wannan y sake wani irin murmushi.

       Takowa yayi gabanta, sannan ya zuba hannun shi a cikin aljuhun wandon shi, tare da juyawa cikin isa da girman kai, yana kallon ta, tare da sake murmushin mugunta. Fakonta yake ya cire nikkab din, itama da ke ta ankara da nufin shi, kaf kaf take da nikkab ɗinta, tana kuma kallon motsin shi.

              Cikin wani irin zafin nama, ya kai wa nikkab din cakfa tare da riko hijab din ta, ya sab'a riko nikkab din, ture shi tayi zata fita, ya fisgota tare da wurgata tsakiyar Office din, ya zuba mata ido, tare da balle botirin hannun shi, ya kalli Nazzir tare da daka mishi tsawa.
"Dauko min A4 din!"
Ya kuma takowa gabanta, tare da  zuba mata ido, dukawa yayi tare da jan dogon hancin shi.
"Zaki kwafe!"
Cikin tsiwa da rashin tsoro tace mishi.
"Idan naki fa? Zaka saka a b'atar dani kamar  yadda kuke sawa ana yiwa mutane."

   Cikin fusata, ya kai hannun shi wuyar shi tare da jan iskar bakin ciki, tare da bude idanun shi, ya sauke akanta.
Hannun shi ya kai keyartar da, daidai shigowar Nazzir, ya ajiye A4, ya janyo ta ya wurgata gaban takardun sannnan ya koma table din shi ya dauko takardun ya zuba a fuskarta, sannan ya juya bayan shi tare da yin wani motsa hannun shi, yace.
"Zaka iya bamu guri!"
Ya faɗa haka, fita Nazzir yayi tare da cewa.
"Please Lion!"
"Ka karo wani A4 din!"
Haka ya kuma karawa fahimtar da yayi matukar ya roke shi, kamar yaja mata rashin mutunci ne ya sashi fita, tana zaune a gurin bata d'ago domin tayi magana ba,asalima ma itama wani karsashin rashin mutunci take ji, dan ta rantse a ranta ko gawarta za'a fitar ba zatayi rubutu ba. Ai ita ba baiwar shi bace.

              Juyawa yayi ya cigaba da aikin shi bai kuma d'ago kai ya dube ta ba, asalima Mantawa yayi da ita a cikin office din, wani silent Office din ya bada, baka jin kome sai karar Ac. Babu wani alamar motsin rai a cikin gurin.

        ---
"Me yasa Aeesha Omar take da taurin kai, gashi can mahaukacin can ya sakata aikin da ba zata iya ba.". Tsaki yaja,

   Haka yayi ta yawo a Office din shi, shi kuwa ya damu da ita ne, kamar zai zubda kwalla, domin yasan halin mutumin tunda bai kore ta ba, tabbas haka zai sanya ta.
        ... Awa daya ta wuce, biyu yazo ya kuma wuccewa, d'ago kai yayi daidai lokacin da agogon Office din ya buga, ganin yadda ta manta da abinda ya saka ta, tana zaune ta daura  daya akan daya, irin ga gidan Ubanta. Ranshi ne ya b'aci. Bai tab'a gamo da mutum irinta ba, tasowa yayi gabanta, tare da kurawa hannunta ido, fisge wayar yayi tare da buga shi da ƙasa. Ya nuna mata aikin da ya sakata, d'ago kai tayi tare da kallon wayarta a kasar ofishin sa.

  Da sauri ta nufi gurin laptop din shi, saka mata doguwar ƙafarsa yayi tare da  take kafarta. Ya durkusa a gaban ta.
"Zaki yi ko sai na baki mamaki! Allah ya bani damar gyarawa irinki sittings."
Ya fadi haka tare da zare tie din shi, ya wurga saman table din shi, da wani mugun sauri ta kalle shi tare da rufe fuskar ta da hannunta biyu. Yana ɓalle rigar shi ya fara.
"Zanyi!"

     "Kinyi kyan kai!"
Mikewa yayi tare da gyara zaman kayan shi, sannan ya juya tare da tab'a wani abu, kofa ya buɗe hango  daki tayi kamar yadda cikin office din ya kasance, fari sosai kome na ciki fari ke, hatta Furniture din ciki, shiga yayi kofar ya rufe kanshi.. kamar zata yi kuka tace.
"Yanzun don Allah ya zanyi da wannan haukar da ya tara min?."

   A hankali ta fara, tattara takardun ta fara rubutawa, kamar wasa ta cika shafi biyu. Murmushi tayi tana yi har kusan karfe biyu na rana, mik'ewa tayi tare da fita sallah, tana zuwa ta samu yana zaune, kallon agogon hannun shi yayi, bai ce mata kome ba. Har la'asar sannan ya kuma shigewa dakin, karfe biyar ana tashi ya fito, zai bar Office din yana fita itama ta mike tare da tattara kayan ta barsu a gurin, bai ce mata uffan ba. Kawai abinda ya sani zata ji a jikinta ne, ba dai shi zatawa taurin kai ba.

        Haka ya fita, da sauri Escort din shi suka amshi kayan hannun shi, tare da isa gurin motar shi, suka zuba mishi kayan a cikin motar bayan sun bude mishi. Zama yayi tare da kallon inda take tsaya yaga yadda take yarfe hannun ta, alamar hannun yayi tsami.
 
   A ranshi yake cewa, baki yi kome ba, yanzun kika fara, domin sabo zaki fara.
Koda Tasleem ta iso, bata iya magana ba, motar Badar suka shiga, tunda ta zauna take ajiyar zuciya,a saninta tayi ya kai page goma idan bai fi ba, da suka iso gida.  Tana shiga wanka ta shiga gasar wuyarta, saboda zaman rubutun da tayi, haka hannunta, sallah al'adar tayi kawai, ta kwanta akan abin sallar. Ciwo kawai hannun yake mata, kamar zata yi kuka, haka take juyawa, Tasleem ana can ana shirya karya.
         •• Da dare suna zaune, amma hankalinta bakan hirar Tasleem da Nazzir, wanda sakusan fada ne da rashin kirki, juya baya tayi tare da mik'ewa tayi sallah isha, ko hirar da suke yau basu yi ba, kawai ta Cigaba da kwanciyarta, abinta sai da tayi barci kai ɗaya, sannan ta tashi tayi alola tare da gabatar da nafilla, addu'o'in. Sannan  kusan rabin addu'o'in da tayi duk na niman tsari ne daga sharrin Mahir, Allah yayi mata katangar karfe dashi, kar ya bashi sa'ar cutar da ita. Allah ya kare ta daga sharrin sa.

       Haka ta jima har ta idar da Addu'ar ta koma gado ta kwanta, washi gari suka tashi da wuri, sannan suka shirya, duk da taga yadda Tasleem take wani cin magani, kamar wacce aka mata wani abu. Har suka fito,sai lokacin suka ga motar Tasleem a can gefe an gyara, amsar key din motar aka yi tare da shiga suka bar gidan.

     Lokacin da suka, isa sun same shi zaune da masu tsaron ma'aikatar, kamar ba wani ba. Dauke kai Noorh tayi bata kaunar ta kalli inda yake ma, yana zaune ya harde kafa daya kan daya, da alamun akwai tsiyar da ya shuka.
Domin taga Nazzir yadda yake bashi hakuri, tare da magana kasa kasa, da alamun yana bashi baki ne, dan taga wasu mutane biyar a tsaye hankalin su a tashe, sai hakuri suke bashi. Cikin masifa ya daka musu tsawa.
"Kuyi min shiru! Kai Nazzir kasan yadda kome yake taya zan zuba jari ana salwantar min da dukiyata, kona min kayan aiki. Masu kyau idan ina bukatar su sai nayi odar su daga China, suje na sallame su, kudin su zai shigo musu cikin satin nan."

     "Mtsew! Aikin banza aikin wofi." Ta faɗa kasa kasa.
"Ke!" Duk suka tsaya dama Tasleem ta gama tsorata, dan tayi Allah ya isa yakai kwando dubu a zuciyarta, yanzun  ta gama tsorata juyawa tayi kamar wacce aka shaketa, tace mishi.
"Sir Noorh ce tayi magana wallahi bani bace,"

Bakin ciki ne ya turnuke shi, bai san lokacin da yayi wata irin, kwallo da kayan ruwan zafi da yake gaban shi ba, dan mutum ne me son coffee, ya tako gabanta.
"Dube ni! Ni sa'an kine? Ki biyo Ni kamfani na, kina min rashin mutunci."
Lek'awa tayi tana duba gefenta kafin ya kalli inda Nazzir yake tace mishi.
"Don Allah da waye wannan yake? Ko dai yana da shafar junnu ne? A Toh idan bai da lafiya gwara a fara duba shi dan mutum shi daya yana magana abin hankalin ba zai dauka ba."
  Dariya suka kwashe mishi har Nazzir, haka yake so yaga an sami wanda zai tanka mishi, a wulakanta kimar shi a gaban mutanen da suke ganin shi da kima.

  .yaji kunya da shakkar mutane, sabida an sami me tanka mishi, isa da ji da kai ya zube ya zama shine me wannan abun.

    Saka takalmin shi yayi ya take mata kafarta, sai da ta saka kara, ya kuma take mata, yana huci yace.
"Yau zaki ga hauka iya ganin idanunki."
Ya faɗa tare da wuccewa Office din shi. Yana shiga ya shiga dukar table din shi, tare da lacce shi da kafar shi, yana huci.
....
"Noorh kinyi abu me kyau, ki Cigaba da abinda kike mishi yadda kowa sai ya tsane shi. Ki gayawa duniya abinda yake miki,"
Cikin azabar zafi tace.
"Jiya yayi kokarin raping dina, yau kuma ban san abinda zai iya min ba"
"What??"
Ya tambaye ta, tare da zaro idanu.
     "Wallahi kuwa, domin sai da na amince zanyi Rubutun ya fasa,"
Cikin jimamin karya yace mata.
"Kinga abinda baki sani ba ko? Ana tace miki ni mutumin banza ne, toh bari kiji yan mata irin ki, haka yayi ta raping din su a Office din shi, sannan yana koran su, wasu ma bazan iya gaya miki ba"
"Amma me yasa baku dauki mata ki akan shi ba?" Ta tambaya a dame,
"Sabida babu hujja ke kuma kina da hujjar yakar shi, tare da ganin bayan shi."
Shiru tayi kafin ta mike ba tare da tace mishi kome ba, ya bar gurin shi, murmushin gefen baki yayi sannan yace.
"Duk inda shiga sai na shiga, sai na rusa maka farin cikin ka, sai na maida maka rayuwa majiginar bakin ciki. Sai na hanaka walwala da sukuni."

   Sannan ya mike tare da rantsuwa, akan abinda zai aikata.
     --- a dararre na shiga ofishin sa, bai d'ago ba bai kuma fasa abinda yake ba, asalima sai ganin A4  da nayi har guda biyar, wai nayi rubutu. Ya watsar da na juya wani ya kuma cirowa.
"Kai wani irin Azzalumin mutum ne? Anya da zuciya a kirjinka? Taya zan yi wannan aikin?"
"Wallahi ko kwana zaki yi sai kinyi,.kuma a tsaye idan ba haka ba zaki sha mamaki."
  Juyawa nayi zan naje na bude kofar ya rufe rub.
"Ai kofar da remote control take amfani!"
A hankali na dauki takardan Ni game zuciya, na fara rubuce-rubucen,.kamar ba da gaske na fara, ban san ya akayi ba ko awa biyu banyi ba, bayana ya fara rikewa, hannuna da kafana suka fara rawa, karku manta Mr Mahir Major ne na sojojin ƙasa.

Duk wani muguntar duniya, babu na biyun sojojin ƙasa, tun ina yi zufa kadan kadan, har na shiga diga sosai, kwalla ya jika min nikkab, jikina sai rawa yake, karshe haka ya fita tare da nufar meeting, yana fita ina sake kuka. Har da shasheka,  minti arba'in da biyar ya dawo, yana shigowa ina hadi kukar, dake yaji ajiyar zuciyar da nake. Tsayawa yayi a gaba na tare da cewa.
"Ba dai kuka kika yi ba? Toh ance miki rashin kunya abin dad'i ne, mara kunya karamar mara mutunci, mu zuba Ni dake shege ka fasa,"
"Yanzun muka fara" na gaya mishi.
"I like your confidence!"
"Mugu!"
"Cigaba da tsayuwa!"
"Azzalumin kawai"
"Anan zaki tabbata!"
"Allah ya isar min!"
"Dama Ai shi din ishashe sarkin sarakuna ne! Dan haka tun ba a haife ki ba yake da isar shi."

"Allah kaga abinda yayi min, Ubangiji ka bani damar daukar Fansa"
"Duk ranar da kika dauki fansar ki, nayi miki alkawarin kyautar da babu wanda aka tab'a bawa shi a duniya!"
Kukan da take had'iyawa ne ya kwace mata.
"Simple kice min Boss am sorry,"
"Da na kiraka Boss gwara nayi hatsari hakoran da harshe na, narasu har abada."
"Cigaba da rubutu."
Bakin ciki ya sata had'iye Kukan, gashi zaka ji yana muryan kuka, amma zunzurutun taurin kai irin na jinsi biyu da suka yi gamayyar halitta a jininta ya sanya taki accepting din laifinta, Cigaba tayi da aikin
   ....🤣 Wadannan mutane 🙄🤔 🤦🏽‍♀️ sai kace  kaji.....
https://my.w.tt/Ewo0CLV9ccb
MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 1️⃣4️⃣
     MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

  ~#Courage~

"Sai na lalata maka duk wani ji kanka!" Ta faɗa cikin karfin hali.
"Duk ranar da kika yi nasarar haka, na miki alƙawarin, sai na baki mamaki a rayuwarki balle poor girl like you, me zata iya min. Me zaki iya? Cigaba da Rubutu."
"Mahir! Sai nayi destroye nasarar ka da ka gina."
"Ni kuma na zame miki karfen kafa, duk inda kika shiga sai na hana ki sukuni, ke me gadin kamfanina baki isa tab'a kimar shi ba, balle kuma Dolna dan karen da ake kiwo."

       Har biyar suna muhawara, tare da kudirin abinda zasu aikatawa junar su, ana tashi ta zubda takardun, sannan ta sauke ajiyar zuciya, me tafe da kuka. Dan bata jin zata iya motsa legs din ta..
       ......
    , ya kirga takardun yaga bata yi wani dayawa ba, amma sun jike da kwalla tare da gumi, table baki yayi sannan ya d'aga kafad'arshi.
"Gobe daga farko zaki fara!"
"Idan ka ganni anan kenan, sai kayi abinda yayi maka dan ni ba gantalalliya bace da zan zauna ka kashe ni a iska,mugu kawai."
Ta juya da sauri tana jan kafarta, zuwa bakin kofar.
Yana zuwa bai damu da yadda take bin bango ba, ya sharbeta ta zube.
"Zan so ki kira ni da Boss."
"Wallahi da na kiraka da boss gwara na rasa harshe na."
"Yau daya kin sani nayi magana da yawa."
Ya faɗa tare da lashe bushashen lips d'inshi, sannan ya taka kafarta, sai da ta sake ƙara,.tare da rike kafar tana yarfe hannun, haka ya fice tare da rufe ta a cikin office din, yayi tafiyar shi.

          Domin shi bai san bata fito ba, dan ya san zata mike, kuma kofar tana iya tsayuwar minti biyar idan babu wanda ya gifta sai ta  rufe kanta, tashi tayi zata fita kofar taki budewa. Cire nikkab din da hijab ɗinta ta sake kuka. Sai da tayi ya ishe ta, sannan ta mike tare da shiga niman wayarta, ta samu, tayi kokarin kiran Tasleem, amma bata dauka ba, tayi iyaka kokarinta amma bata dauka ba, karshe ma wayar a kashe. Kamar yarinya karama haka tayi ta kuka tana ja mishi Allah ya isa.

        Shiga dakin tayi ta duba taga har da bowl tub, da sauri ta cire kayanta tare da cika  ruwan zafi ta shiga cikin ruwan, dogon gashin kanta, wanda ya kasance baƙi na asalin larabawa da fulanin asali ta sauka a jikin tub din, bata cika son jika gashin ta ba,idan bai zama dole ba,  wanka tayi tare da fasa kafarta, sannan ta fito daure da towel, a hankali ta fito, dake ta kwaso kayanta a Office din.

      Tana jin ana magana sama sama.
"Kasan ba zai tab'a saka hannu ba, me yasa kace nazo Office din shi?" Shiru aka yi dan ba zata ce tasan mutane ba, sake lek'awa tayi bata ga fuskar su ba, domin akwai abu a rufe a fuskar su,
Haka suka gama abunda ya kawo su, suka fita.
Da sauri ta saka kayanta, sannan tayi maza ta fito, saura  minti ɗaya kofar ta rufe kanta ta sami damar fita. Kusan rabin kamfanin wutar a kashe yake, dan haka nake tafiya a hankali, hango wasu manyan police dog nayi ban san lokacin da na dawo da gudu ba, na bakin kofar na danna makulin,.yana budewa na koma cikin office din da gudu zuciyata tana rawa. Ubangiji ya daura min tsoron kare wallahi. Dan haka na koma gwada kiran Tasleem wayar a kashe, sannan banyi saving Number nazzir ba, Badar kuma na kira yana busy.

            A hankali na shiga duba dube, a cikin office din shi, anan na kuma hango wata kofa, ta inda kujerar shi yake, tab'a inda nake tunanin shine Mabudin nayi na ga kofar ya buɗe, a hankali na fito, gurin shakatawa ne ko  hade da yar karaman hot tub, sai bar da yake gurin, a hankali na isa inda nake jin hayaniyar mutane, taka abu nayi na saka yar karamar camerar da Badar ya bani na shiga daukar su,  ina gamawa.

Na dawo dakin na kuma zama nazarci ɗaukar. Sannan na cigaba da Niman hanyar da zata kai Ni cikin part din, leka katangar nayi naga a shirye yake da Kwalba, tsaki nayi na sauka kasa, cikin yawon da nake na hango wani katon rariya, da zai kai ka har cikin wancan side din, a hankali na rarrafa har cikin gurin, na shiga bin ko ina ina daukar hoto, da video har zuwa cikin, inda shima na shiga ne ta kofar baya, ina gama abinda Zanyi na koma fitowa ta wannan rariyar, na koma Office din shi, shiru nayi ina nazarin kamar na ga wani katon lambatu. Da sauri na kuma hada kayana, na fito na shiga bin hanyar, ta karka shin kasa kwatar dakatar na fito babban hanyar kamfanin, anan na samu damar kiran Badar tare da gaya mishi inda nake, lokacin sha daya na dare, da kanshi yazo ya dauke ni.
"Noorh! Sannu. Kinyi aikin da na gaza yi, gashi kin dauko wani shashi na Abinda yake faruwa. Gaskiya nagode sosai."

"Ni yanzun ka barni na gaji, gida zaka ajiye ni, Amma wallahi sai na gwadawa Mahir ni yar halak ce."

   "Kinga don Allah ki ajiye wannan rigimar, mu  fuskanci abinda yake gaban mu.".
       Lumshe idanun yayi tare da jin zunzurutun k'iyayyar Mahir, yana kuma samun mafakar siyasa a zuciyata, sai na gwada mishi iyakar shi."

      "Noorh ki rabu da mahir!"
"Wallahi ba zan rabu dashi ba, sai na wulakanta shi a garin nan, wannan kamfanin sai na tsayar da kome na shi." Ta faɗa dai dai isar su kofar gidan su.

Fita tayi abunta, tare da buga kofar gidan, me gadi ya bude min na shiga, ina isa bakin kofar na sami Tasleem a zaune, shareta nayi na wuce abuna, dan na fahimci da gayya ta rufe wayarta.

      Ina isa bakin kofar mu, Dad yace.
" Ba zaki janyo min abun kunya ba idan kin gama service ɗinkin koma Bisra, ban ce mishi kome ba nayi wucewa d'akin mu, Sallah isha nayi sannan na Kwanta, sai lokacin Tasleem ta shigo itama ta Kwanta, ya zata kowa gantalalle ne irin ta, ta shiga min magana a hankali tare da tambayana.
"Ba dai kema kinyi losing virginity dinki ba?" Ta faɗa tare da kallona.
"Au wannan shine tunanin ku  a kaina? Hmm. Ni ba ballagaza bace na san inda nake dariya, sannan ba a haifi namijin da zai karb'an daraja ba, domin Ni nasan ciwon shi, kuma nasan darajar shi.

         Balle kuma da na fito a kabilu guda biyu, da suka san kimar shi ba zan tab'a watsi da al'adar mu da addinin mu ba."
.daga haka tayi juyawarta kamar ta da bayan ta suke mata ciwo.

           ---
Washi gari tana idar da sallah asuba. Ta koma abinta, har karfe bakwai Tasleem ta shirya bata ko d'aga kai ba, domin zazzaɓi yake damunta.

        Karshe da taga Noorh bata mata magana ba, shine ta tab'a tare da cewa.
"Ba zaki bane?"
"A'a Babu inda zani!"

        ....
A can kamfanin kuwa, hankalin shi kwance, ya shiga cikin office din shi, yana bin ko ina da kallo. Murmushi yayi tare da isa dakin shi , gadon da yake yatsine ya kalla, yana nazarin can kuma ya tuna ai ya kwanta. Amma me yasa ba a gyara dakin ba,.dan haka ya fita tare da danna bell din da zai kira masu aikin part din su.

         Dukkan su, suka shigo Cigaba yayi da aikin shi, tunda suka ga haka, jikin su yayi sanyi. Zai yi wuya idan ba koran su zai yi ba.

       "Yallabai!"
"Malam Abba! Kaje na baka hutun sati biyu"ya faɗa.

       "Don Allah kayi hakuri, wallahi ina da yara ƙanana." D'ago kan shi yayi, yagan su duk manyan ne, ba yara ba, sunkuyar da kai yayi sannan yace.
"Kuje! Amma kusami Nazzir, zai baku sako, wannan lokaci kamata yayi ku koma gefe kuna tare da kasuwanci wannan aikin ƙarfi ne, kuma shekaru yaja."

Ya fadi haka yana isowa gaban su, ya arde hannun shi a kirji, "karku damu, zan bawa Nazzir damar ya sallame ku da kyau."

    Daga haka ya wuce dakin, da kanshi ya gyara d'akin, tsaf ya goge. A ban dakin ne ya hango ribom din mace.
Cikin wani irin mamaki yake kallon ribom ɗin.

     Dauka yayi ya fito daga ban dakin, sannan ya koma Office din shi.  Ajiye kome yayi yana jiran jakar shi tazo.

      Bata zo ba shima kuma bai saka kanshi damuwa ba, ana tashi ya tattara yayi gaba abinshi.

   ---
Karfe biyu na rana, ta shirya zuwa kasuwa, anan ta samo yar karamar wayarta, me kyau, amma androind. Kuma ta hannu ce, tana isa gida ta daura layin da ta saya, a hannun irin masu sayar da kati suna tafiya.

   Dake mtn ne, take tayi transf din data, ta tura face book, da tweeter, tare da IG.
Sunanta da take amfani da shi a wancan wayar ta sauya, tare da bude har da Gmail.

Tana gyara face book ɗinta, tare da tweeter ta fara rubuce-rubuce akan kamfanin Hamoud Boualem da CEO din su, sosai tayi magana akan wulakanta mutane da yake, tare da yunkurin fyade ga yar bautar ƙasa.
         Sannan tayi alkawari sai ta bayyana musu, sharrin da Kamfanin yake dauke dashi wanda mutane basu sani! Sannan ya kamata mahukunta tare da gwamnatin! Jahar Adamawa! Gwamnatin tarayya! Hukumar lafiya ta jahar Adamawa, da ta kasa baki daya su shiga alamarin kamfanin Hamoud Boualem Company, sannan Tana kira da Malaman musulinci da na Kirista su fito suyi wani abu akan kamfanin Hamoud Boualem, sabida rashin amana da suke yi ga kamfanin.! Idan kuma ana kalubantar ta, toh ita taji zata bada shaida ga abinda idanun ta suka gani! Amma na farko hukumar yan bautar ƙasa, suyi da gaske domin daya daga cikin mutanen su, rayuwarta yana cikin hatsari sakamakon yadda CEO yake niman kashe, karku ce kashe kai ne idan haka ya faru, aka kisan kai ne! Domin bai dauki rayuwar kowa da daraja ba. Sai tashi.

          Sannan a musulunce dai an san giya haramun ne? Toh ya kamata hukumar hani da fataucin miyagun kwayoyi na kasar da jahar Adamawa, su fito su kalubalanci Hamoud Boualem, idan since karya ne, ita tana da shaida.

         Sannan zunzurutun rashin adalci, koran ma'aikata ba bisa ka'ida ba, ana cin zarafin su. A kamfanin Hamoud Boualem, ya ta'azzara. Abubuwan na cin mutuncin sai da Noorh ta rubuta, akan kamfanin Hamoud Boualem, sannan ta kuma jaddada bayanin akan wahalar da Mahir ya bata, ta hanyar kare sunanta. Sannan ta sake sakon tare da sake murmushin jin dadi.

         Bakuwa ce a tweeter, kafin kace me. An shiga watsawa a kafaffen sadarwan zamani. Tare da ririta alamarin ya girmama..

       (Matsala ta da fada da dan jarida! Mawaki! marubuci! Dan wasan kwaikwayo! Alqur'an suna tashi maka gwanjo sai ka ƙasa b'oya a duniya!)
Yarinya kiyi fatar kar Mahir Hamoud Boualem yasan kece kika mishi wannan daurin goron, dan shi talala zai miki!

_Zaku ji ni shiru na wasu kwanaki Insha Allah! Haka zai faru ne sabida uzurin da ya taso min! Don Allah karku zarge ni da wulakancin_
https://my.w.tt/xtVVXjuXhcb
MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 1️⃣5️⃣
     MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Zee Sardaunan
Sumayya Ahmad Aliyu, fateema Mustapha
Ga gaisuwar ku nan🤩😘 masu jiran Mah-Noor.....

_🤣Gaye You enter Noorh hand, zaka fadi gaskiyar ka, indai Noorh ce jininka sai ya kare, Yan leken asiri, naga sakonku! Wattpad fans kuma haka, My Hajiya Maryam Jikar kulu 🤣 Mommy Sultan kece kike bayan Noorh kowa ya fara jin haushinta_

#My Nikkab
Yana cikin gym room, yana d'aga karfe. Sako suka fara shigo mishi. Cikin gajiya da karar wayar shi, ya d'auka yana kallon Ummina, kiranta na katsewa hadiya tana kiran shi, dauka yayi tare da cewa.
"Beb!"
"Ka duba tweeter please!"
Cikin sanyin jiki ya bude idanun shi, sanan ya bi wayar da ta kashe da idanu, kafin ya tashi zaune yana jin faduwar gaba, a hankali ya bude data. Sannan ya shiga tweeter. Sako ne suka shiga sauko mishi, cikin faduwar gaba yaga sakon Noorh. Ji yayi zuciyar shi kamar zata diro kasa, ya kurawa yar ido.

           Lokacin guda yaga Aysar Haladu, wani matashin me kudi anan

Please Login or Register in order to submit comment