Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ake bukata ba, domin Aunty Mariya sun tattauna da Ummi akan lafiyar ƙwaƙwalwar ta, kuma itama tayi na'am da abinda tace.
"Insha Allah zai barta ta samu sauki ba zai zauna a kasar ba ma balle ya kawo muku matsala."

         Gaskiya Ummi Uwa ce, domin tsayawa tayi ka'in da na'in,  ta tabbatar da Mahir ya bar kasar, sannan ta kwantar da hankalin domin ciwon Noorh din ana son mata jinyar shi na gaske yadda zai taimaka lafiyarta ta dawo, dan haka suka yi nazarin abinda ya dace da lafiyarta aka fara saka lokacin da za a cire Babyn cikinta,

      .... Bayan watanni uku da kwanaki, aka mata aiki inda suka ciro yara uku kyakyawa masu kama da Baban su, musamman matan biyu namiji ɗaya, shine ya dauko Noorh, hoton su Ummi ta tura Mishi, kamar zai yi hauka daya gansu.

          Haka kuma ta hana shi zuwa, zama yayi a gaban abokan shi yayi ta zabga murmushin jin dadi, yana gaya musu matar shi ta haihu yara uku.

         ----
After few days.

Aka fara daura Noorh akan magani, dama sabida drugs ne yasa suka mata aiki aka cire babyns ɗinta, a hankali lafiyar ya fara shigarta, har ta fara fahimtar ta haihu, amma nutsuwar da take samu ya hanata magana, sai da tayi sati Uku sannan aka kawo mata yaranta, idan kaganta sai ka zubda kwalla sani anyi mata aski an kwashe gashin kanta tass, sai yar robon bututun hancin.

          Lokacin da Dadah ta ganta tayi kuka ta tausaya mata, balle Kuma Nanah cewa take.
"Mariyah Maisarah Don Allah kar na rasa A'isha kamar yadda na rasa Salha."

     Matukar kana da imani inda ka ga yadda suke kuka sai ka zubda kwalla, haka tayi ta murmushi tana kallon su, musamman yaranta.

         A cikin kwanakin ne Allah ya tunkud'o Mahir, lokacin da ya ganta kuka yake, tare da rungume ta. Juyawa yayi ya kalli Dr Naaz.
"Meke damun Noorh!"
"Ba wani abu bane ciwon dake brain ɗinta ne, yake son shiga matakin Cancer, shine aka mata aiki aka cire Yaran kagan su ko suna ba asamu su ba."

   Rungume shi tayi tare da kifa kanta a kirjin.
"Mahir"
"Shiii!"
Shafa kwal-kwal din kanta yayi, hawaye na sauka a idanun shi.
"Baby I love you!"
Kuka ne ya kwace mata,
"Honey me too!"
"Iyayen su da suke kallon su ta window glass sai da suka zubda kwalla."
Haka yana ji yana gani aka fitar da ita zuwa dakin da za ayi mata aikin ƙarshe.

       Ko kallon yaran ya kasa, zaman dirshan yayi a bakin kofar aikin, yana kuka da duk zuciyar shi.

  Lokacin da Faruq yaga yadda Mahir ya koma,.sai da yayi kuka domin bai tab'a tsammanin.son da sukewa juna ya kai haka ba.

             Bayan awa goma sha biyar, aka fito da ita, da sauri Mahir ya mike,tare da rike hannun ta, har dakin da aka hana kowa amma shi ba a hana shi, shiga ba,
Shi ya zauna da ita tsawon kwanaki har ta farka, yana tare da ita, shi yake mata duk wani abinda take bukata ya hana kowa zama da ita, Nanah da Dadah suka tsaya mishi.

         Watan ta biyu, dauketa da yaran shi suka gudu, Japan acan  ya shiga aikin shi da ya kai shi. Ita kuma tana samun kulawa daga Dr din da ya dauko mata,

        Sai da suka shekara daya cif sannan suka dawo shima sabida anan nime su ne.

        Da safe suka sauka, yana rike da Hamid wanda suke kiran shi da Nahid, ita kuma tana rike da Nahla da Nahidah, Sunan Maryam Nahla sai Nahidah sunan Salha, sunan Ummi da sunan Ammyn Noorh.

Har zuwa lokacin babu abinda ya shiga tsakanin su na aure, sabida rashin lafiyar da take fama dashi, amma ya kudirin aniyar matukar suka haɗu, toh ba sauki sai na Allah.

     Karb'an Nahidah Nanny tayi, tana murmushi dake tun anan Algeria aka hadata da Nanny, karb'an Nahid Faruq yayi tare da mikawa Mahir hannu, suna dariya.
"Daga tafiya aiki sai ka rike min kanwata!"
"Gata nan na dawo maka da kanwarka! Nima kuma na fasa baka kanwata."

    Dariya suka saka, sannan suka nufi motar Faruq ana hira, ita dai tana jin mijinta, a ranta idan kaga Noorh ba zaka tab'a cewa tayi ciwo ba.

      .....bayan wani lokaci, sun nutsu kowa sai haba haba yake da Noorh, musamman da ya kasance itace ta fara haihuwar yan uku. Shi yasa suke bata wani irin daraja, tana kwance a dakin Dadah. Tana jin yadda Dadah take bala'in.
" Bazata zo ba Hisham, nace jikata ba zata shiga maganar Husaini da yar shi ba, ku..."

            "Dadah! Bar hana Aeesha aikata alkhairi," inji Mahir,

            "Toh shikenan!" Ta faɗa dake tana jin maganar Mahir sosai, dan haka da kanshi ya shiga dakinta ya dauko Noorh suka sauka har inda  Iyayen Tasleem suke. Ya zaunar da ita,
"Gata nan!"
Kallonta Tasleem tayi, a ranta tana jin ina ma da itace zata samu wannan matsayin, ina ma da itace zata tsaya a position din Noorh, wani irin kallon tsana takewa Noorh, daga sama har kasa. Wani kallon iyayenta tayi sannan tace.
"Ku tashi muje babu me niman Alfarmar mahaukaciya. Nufinki ya cika kin zama abinda kike bukata, kin samu yadda kike so."

        Mamaki ne ya rufe iyayenta, takasa boye bakin cikinta, ta kasa boye b'acin ranta, ta kasa boye kyashi da Hassada da yake damunta.
      
     "Tasleem kenan! Ke akanki kin rasa me yake damunki! Ke akanki kin rasa me kike so! Toh Alhamdulillahi, hakurin da nayi da tawakkalin da nayi, dauke kan da nayi! Shi yasa na sami kome na rayuwa, large family, Hero Huby, shi ya kuma kara bani halattattun yara uku, Allah ya bani kome ne dan ya jarabci imani na, dan haka Tasleem kiji tsoron Allah ki cire kyashin da hassada a ranki. Baba ka basu rabin dukiya na suje su karata da shi."

          Jikin iyayen ta ne yayi sanyi, suka zube har kasa suna godiya, ko ta kansu ban bi ba, na barsu a gurin, zuciyarta fess na sauke  tunda na gaya mata abinda yake damunta ta gaza ganewa.

    Bayan tafiyar su da watanin aka yi bikin Faruq da Naaz, sai Adeemah da Usman Kamfut, haka muka sha biki babu kama hannun yaro, tunda muka biyo an kawo amarya Lagos, Yallabai ya hanani komawa.

        *Bayan shekara biyar*
"Mommy, Kinga Nahid ko? Wai yana ce min yar lukuta" kallon Nahla nayi, sannan na kalle shi yana zaune ya zubawa tv ido, cikin jin haushi wanda ya hadu da tsohon cikin da nake dawainiyya dashi.
"Nahid! Ka fita idanu na, na rufe wallahi ka bari na kama.."
"Babu me kama min Yarona a cikin gidan nan, ki gayawa yan matanki su fita idanun Ya'yan su."
"Honey!"
"Baby Love, ki daina mishi fada a gaban su, mata ne su kuma shine Ubansu nan gaba, don Allah kar a cinye min Ubana dan anga bana nan"
Mik'ewa nayi zan bar falon,
"Toh kiyi hakuri Mommy!" Kallon yaron nayi, sannan na shafa kanshi, nace mishi.
"Bana son ganin kana kiran yan uwanka da sunayen banza, ko baka son su kiraka da yaya ne?"
"Ina so Mommy, wai dan na cire wani tasha ana abun kika ce mana babu kyau shine tace min yayan banza. Kuma ga Nahidah ban dake ta ba, kashe tv nayi nace muyi home work, shine ta kuma murguda min baƙi, nace mata yar lukuta."

    Shiru nayi ina kallon ta, sai kokarin komawa bayan Abban su take..
"Abba kacewa Mommy Am sorry, ba zan kuma ba."
Ta faɗa tare da rungume shi tana kuka.
"Toh Mommy kiyi hakuri ba zamu kuma ba."
Shafa kan Nahid nayi sannan nace mishi.
"Karka manta kai babba ne, a duk inda Baba yake sarki ne, kuma shugaba ne, kayi hakuri da Kanenka kaji."

Gyada kai yayi sannan ya kwashe kayan shi, zuwa dakin shi.
Wato Hamid yana da hakuri, amma Maryam bata da hakuri ga niman tsokana, ga fadar banzan magana, sahla kan babu ruwanta, duk abinda za ayi sai ta gadama tace ta gani, haka na haife su kowa da halin shi, kuma kowa da abinda yake so.

       Ko abinci ne Nahid baya cin duk wani abun taliya ko Indomic, amma zai ci tuwo musamman na masara, har gurin matar me gadin mu yake zuwa ta zuba mishi abinci, ita kuma Salha a duniya bata da abinda take so kamar kayan zaki da tea, idan zata sha tea magana ya kare.

     Maryam kuma, toh ita ba damuwarta kullum ayi dankalin turawa da Whiter rice da stew, dan haka kullum me girkin mu haka yake mana abincin dan ma idan naji haushi ina hana su nace kowa yaci abincin duk gida.

        ..... A bangaren Ummi ta same min good Mother In-law, tana masifar kaunar mu da jikokinta, Adeemah ta haihu ta sami danta namiji, Samiha itama bana Allah ya bata haihuwar ya mace,  Dadah kuwa kamar zata lashe Ni, idan tazo ganin mu ko naje can da yarana..

          Duk bayan wata shida ina zuwa duba lafiyar kaina, Alhamdulillah na samu sauki.
.....
A safiyar Laraba,muka samu labarin mutuwar Baban Nazzir, sakamakon cutar ciwon zuciya da ya kashe shi, sai dai muka mishi Addu'a.

        Sannan naje gurin Ummi nayi mata ta'aziya, Shibha da ta zama yan mata, ta kalle ni.
"Wallahi kina daurawa kanki dumi, gwara da ya mutu mun rage mugun iri."
"Shibha baki da kirki zan ci mutuncin ki!" Inji Ummi,

                "Allah Ummi, baki ga."
"Zanci kaniyarki da Shibha!"
Dan dole tayi shiru, bata kuma magana ba, Nazzir ana can kiri-kiri, ana can gwabza. Tare da haduwa da tsagerun yan iska wanda suka dama shi suka shanye, kuma suna cin Ubanshi dai dai gwargwadon. Manager shima ya hadu da tashi matsalar ciwon sugar, Aysar Haladu ne dai yafi su gamuwa da mugun matsala, domin haka kawai aka ga jikin shi yana zabgewa.

             ----
A cikin satin nan muka je Ghana duba matar Badar, ashe Mahir yana faɗi tashi akan su, basu da matsalar kome, domin duk wata hidima nasu ya dauka.

                       Matar nan ta Yola muje mun nime ta, Mahiry ya bata kamfanina, tare da duk yarda sannan ya cigaba da niman wani taimako jama'a,. Tuni kamfani ya kuma dawowa kamar da.

          A can Annaba kuwa, Tasleem tayi hauka tayi kuka tayi bakin ciki take gayawa iyayen ta ai asiri Noorh tayi mata ta dauko duk wani matakin rayuwar da take ciki ta cillata cikin bakin ciki da talauci, dan haka bata yi deserved iyaye irin su ba, da familyn Noorh ta dace, ganin kamar ta zare yasa suka mikata asibitin mahaukata, domin sun san cewa tsinuwar Allah da hakkin marainiya yake tafiyar da rayuwar su. Ga taslim a raye amma kullum tana jin ciwon ina ma ace itace Noorh, sai ta kafta mata rashin mutunci (😜🤨 asalin Yar macukule kenan)

Naaz da Faruq, suna zaune lafiya da yar su takwarar Ammyna Salha.
        ***
Tun daran jiya nake jin ciwo, amma naki gaya mishi, domin nasan yanzun zai iya birkitawa kowa lissafi.

   Bayan tafiyar shi, ciwon ya cigaba, kiran Ummi nayi dake yaran suna makaranta, tana zuwa muka tafi asibitin. Tun safe nake Abu daya har ƙarfe biyar na yammacin ranar na sauke kyakyawan Baby boy dina sak kama yake dani,  a lokacin aka gayawa Mahir ina asibitin.

   Barin abinda yake yayi, ya tawo asibitin, ba tare da ya saurari abinda suke cewa ba, ya shigo d'akin. Mika mishi hannu nayi, ina murmushin jin dadi nayi mishi, ya samu ana shirya babyn,  gashina yayi buzu buzu. Matse hannuna yayi tare da cewa.
"Kome da lokacin sa, amma ban tab'a sanin cewa cikakken kalmar Mahnoor sirrin mu ne ba, sai ranar da kika kasance min Bakuwar Fuska a gare ni.

    Thank You Noorh"
"Thank You mijina da ka zame min gata, ka kuma yi hakuri da halina da dab'iata nagode sosai da zab'ena a matsayin matar ka,kuma abokiyar rayuwarka. Ni ba zan tab'a maka kallon Bakuwar Fuska ba" rungume juna suna murmushi.....

   Happy end...

Alhamdulillah sauran  abubuwan da suka rage me karatu ya rasa da tashi baiwar....🤨😂🙏🏼 Nagode sosai Allah ya kuma hada mu daku a *Bakuwar Fuska ... Bayan sallah Insha Allah Nagode bye Friends zanyi missing dinku sosai idan kuka ji shiru toh Ko mutuwa ko halin rayuwa! Ina muku fatan Alkhairi 🙏🏼😢*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment