Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taji ranta ya b'aci, a hankali ta zame daga gadon. Tayi ficcewar ta.

   Yana jin haka , ya sake murmushi, yana jin dadin yadda take kokarin kame kanta, da wata yarinyar ce tuni ta sake jiki dashi amma ita ta kasa sakin jiki dashi. A hankali ya cigaba da barci.
....itama a d'akinta kasa barci tayi sakamakon kamshin turaren shi da ya rike mata kaya, haka tayi ta juyi, har kusan karfe uku,kafin barci me nauyi ya dauke ta.

                     Da asubar farko, ta tashi ta gyara jikinta, sannan ta dauko kitchen ɗin ta haɗa abin karyawa tsaf, ta kai falon sama, ta jera mishi sannan ta koma d'akinta ta kwanta, bata kuma farkawa ba, sai karfe goma..tana jin kamar ana sa'in'sa, a hankali ta tashi zata fito. Taji Muryan Mahir yana faɗin.
"Ina ruwanka da rayuwata? Na tab'a bin rayuwar ka? Har kai ka isa ka nima min abokiyar rayuwa? Dat's my Opinions ba wani ne ya isa ya nima min mace da karfin cin tuwo ba. Ko ce aka akayi Ni Womeniser ne?"

"Mahir kana boye wani abu a cikin gidan nan naka?koma meye We shall see, aure kuma kasaka a ranka zaka yi shi domin kuwa Zoolfa itace mafarkin Hajiya."

    Wani wawan shak'a ya kai mishi tare da wullo shi waje, aikuwa take mara mutunci, ya cigaba da gaya mishi magana har da kiran shi dan luwadi, wannan kalmar ta dame shi ainun domin ko bayan tafiyar Nazzir, tsakanin shi da Allah yaji ciwon abun dan haka yaga Noorh sanye da wata doguwar rigar English wear, kawai yana tashi ya nufe ta.

      A hankali take ja da baya, yana kuma Binta har suka isa bangon falon, kafin ya zuba mata idanu, dauke kanta tayi daga kallon shi.
"Wai ni d'an luwadi ne?"
"Wallahi ban san kome ba a wannan rayuwar don Allah ka barni na tafi gurin dangina!"
"Idan na barki zaki dawo gare Ni?'
"Cab'ijam, me zanyi maka me zan karu da kai Ni dai ka barni na tafi gurin dangina."
"Ba zaki tafi ba, sai kin gaya min zaki dawo gare Ni!"
"Wallahi gwara na mutu da a dawo gare ka, akan me?"

   "Me nayi miki? Meye laifinta? Meye laifi" yana tambayar a haukace, wani irin aazabebben tsoron shi ya kamata,  dan haka a takure ta kalle shi.
"Don Allah ka rabu dani, meye nayi maka da ba zaka hakura ka yafe min ba."
Fisgota yayi tare da jefata kirjin shi yana me saka kanta a kafad'arshi, zaro idanu waje tayi. Kwalla na cika mata su, kokari take ta kwace daga jikin shi, ya matsa ta sosai.
         Kukan da take ne ƙasa ƙasa, yayi masifar tasiri a kan shi, kasa saketa yayi yana niman yaga fuskarta, d'ago kanta yayi tare da zuba mata ido,

                  "Baki jin kome a kaina Noorh?" Yayi mata tambayar cikin damuwa.
"Ni bana jin kome?"
"Da gaske?"
"Kana tamtama ne?"
"Me yasa baki jin kome a kaina?"
"Kawai bana son damuwa ne, kuma Ni zuciyata tana inda ya dace"

     "Ok!" Ya janye daga jikin ta, yana sauke ajiyar zuciya, ya wuce dakin shi baki daya.
Bai kula ta ba ma, itama bata damu ba, ta juya zata wuce taga shigowar Haroon, suka shiga kitchen, a tare suka yi abincin ranar, sam Mahir baya cikin nutsuwar shi, dakyar ya shirya tare da barin d'akin, yana fitowa falon yaji muryan Haroon da Noorh ana ta hira.

    Abin ya kona mishi, wato shine D'an iska ba zata mu'amalance shi da mutunci ba, sai wasu mutane na daban, kwafa yayi tare da barin gidan baki daya. Tunda ya isa gidan Ummi ya sameta tana shirin fita, zuba mishi ido tayi kafin tace mishi.
"Da na tura Nazzir ya kira ka shine ka ki zuwa, sannan ka buge da cin mutuncin shi."
        Shafa kanshi yayi tare da kallonta, sannan ya  dashi.
"Kiyi hakuri!"

Duk sai taji babu dad'i, ta kuma shi cikin kulawa tace mishi.
"Me yasa baka son ana zuba gidanka ko akwai abinda kake b'oyewa ne?"
A firgice ya kalle ta, can kuma ya wani boye razanar shi..
"Ni kuma? A'a kawai."
"Idan na kuma jin kana hana mutane shiga gidanka zan je naga abinda kake b'oyewa."
"Toh Ummi, babu kome ma a gidan."
Yadda yayi maganar sai da jikinta yayi sanyi, bata son fara zargin shi, domin kamar ta bashi kofar aikata abinda bai yi a baya ba.

   Shiga gurin Hajiya yayi itama ta kare mishi zagi, sannan ta kuma gaya mishi cewa an tsayar da maganar shi da Zoolfah, cikin b'acin rai yace mata..
"Wallahi kika Kuskura kika makala min ita, sai na saketa ana daura auren."

Kura mishi ido tayi, kuma tunda ya fadi haka. Babu shakka zai aikata, dan haka ta sauko cikin lallashi tace mishi.
"Toh ranka shi dad'e, wacece zab'inka." Share ta yayi tare da lumshe idanun shi, yana hango Noorh, yadda suke ta dariya da Nishadi tare da Haroon, take shaidanin zuciar shi ta shiga kawo mishi hari ba mamaki suna can suna aikata masha'a. Buɗe jajjayen Idanun shi yayi tare da mik'ewa zubur ya bar gidan.

            Da gudu ya figi motar shi,koda ya shigo gidan ya sami Haroon na wanke mishi wata motar shi, duk sai yaji babu dad'i amma kishin da yake cikin shi ya hana shi sukuni, shiga cikin gidan yayi ya same ta, tana saka turaren wuta.

          Buge hannun ta yayi tare da zuba mata ido.
"Meye kika dauke ni ne?"
"Kaga Mahir bana son damuwa! Don Allah ka bar ni magana, an ce kama kowa damanme ne irin ka da zai saka kan shi a irin matsalarka. Don Allah ka kyale ni."
Tana fadar hakan ta tsuguna tana kwashe turaren wutan.
"Waye meye nayi miki ne da zafi haka?"
Mikewa tayi, zata wuce ya kai hannun shi k'ugunta, d'agowa tayi cikin mamaki, tare da kallon cikin idanun shi, a hankali turaren stick din suka zube daga hannun ta, kawai wani Kaddararren al'amari da ta tuna kwanakin baya, ya dawo mata cikin idanunta, kallon juna suke cike da mamaki, shi kan shi yana tune da wannan yanayin da ya zauna a cikin brain din shi, hannun shi ya kai zai tab'a fuskarta tayi maza ta rike hannun. Bakinta na rawa take kallon shi a hankali.
"Don Allah ka kyale ni, ka bar ni na samu lafiya."
"Ba zan iya ba, i'm in luv."
"Da wa?" Ta tambaya kirjinta na bugawa..
"Da wata me kama dake shekaru goma sha biyu da suka gabata."
Ture shi tayi zata juya da gudu,  ya riko hannunta, tare da fisgota kirjin shi, yana me rike ta da dukka hannu bibbiyu..
"Noorh! Kaman."
"Kaga Don Allah ka rabu dani mana, duk ka nace sai ka lalata min rayuwa, meye nayi maka da zafi da ba zaka bar ni ba? Meye na tsare maka da ba zaka barni na rayu cikin salama ba? Don Allah karka takura min ka kyale ni."
Yadda tayi maganar cikin kuka da fada sai da ya kashe mishi jiki baki daya, a hankali ya sake ta, tare da juyawa ya bar gidan.
       Tunda ya fita take kuka, tare da takaicin ajiye ta da yayi a gidan babu wani kwakwaran dalili, haka ta zauna tayi kuka har ta gaji. Karshe a falon ta kwanta barci ya dauke ta..

       •••
Kwana biyu kafin Ramadan, rashin jituwar su tayi yawa, dan Noorh tana son barin gidan, bai kula ta ba, kuma bai kuma mata magana ba, asalima daina kula tayi baya tab'a dawowa, sai tayi barci karshe ma da yaga zuciyar shi tana yawan kawo mishi gulmar ta da Haroon, kawai ya san yadda ya raba zaman su, guri guda. Inda ya bawa Haroon aiki a Office din shi, kawai ya huta da zargin shi.
Suna zaune su uku, sun saka shi a tsakiyar su, duk sai ya basu tausayi, d'aya su Brst Usman Kamfut yace mishi.
"Amma Dr ya baka shawara nima ina bayan shi, idan ba haka ba, kuwa zaka jima kana ganinta babu yadda kayi da ita."

         Mikewa yayi zai tashi yace musu.
"Ina da Opinions akan yarinyar amma bana jin zan iya amfani da karfina dan na nime Yardan ta, kawai zan cigaba da binta har ta amince."

   "Allah ya wadaran naka ya lalace, jakin dawa ya ga na gida. Toh wallahi ka kyaleta tabar gidan ka, domin zaman ku a guri daya zaka iya durawa yar mutane ciki ka bar ta da tashin hankali."

      Zama yayi sannan ya kalle su, kafin yace musu.
"Yarinyar da ta gama, raba kanta ga wasu bata yi cikin ba, sai ni ne zanyi cikin, kawai ku tayani addu'a, amma wancan tsohuwar zata b'allo min August."
"Wallahi idan ka yarda yanzun mu tafi muyi maganar da ita, dan kasan dole."

    "Kai kyale ni, zanyi magana da ita amma bata wannan sigar ba."
"Kana nufin baka son ayi."
"Kai Dr bana son shirme, kawai ku manta da batun, amma zan shawo kanta."
"Yaushe kenan? Sai yaushe zaka shawo kanta, kasan iya adadin kusancin da kuke kara samun juna."
"Na sani mana, kawai bana son amfanin da karfin da nake dashi ne akanta."
"Toh me kake ganin ya dace kayi mata."
"Zan gaya muku?"
"Hmm! Baka da idea dan iska!"
"Toh alhudaduda."
"Bana son Iskanci, kai ba atab'a karewa da kai lafiya ba, dan banza wanda so ya cilla shi."

"Zan danna maka ashari'a."
"Sorry Bobo!" Da sauri ya d'ago kan shi, yana kallon Tamarah, wata mayyar yarinyar da take masifar son shi, amma baya sonta, duk fadin Lagos ita ke kiran shi Bobo.
     Mikewa tayi tare da, tana taku kirjinta yana wani girgiza, cikin wani daukar hankali. Dauke kai yayi tare da mik'ewa zai bar gurin tasha gaban shi tare da kaiwa Big Bom d'inshi wani irin cafka ya buge hannun ta, tare da murɗe dayan.
" Ina da wacce tafiki haduwa sama da kasa, idan son ganin su naka nasan yadda zan yi da ita nake da kika gama bawa wasu mazan damar yin amfani da ke ba." Ya ture ta tare da barin club ɗin, wato idan kaga club ɗin ba zaka tab'a cewa a Lagos yake ba, kudin shiga club ɗin kawai abin jinjinawa ne, balle ko ruwa zasu sha a zaune yake da gindin shi.

    Mahir yana shiga ne domin yasha soda, bayan nan baya kuma bin kome a gurin.kuma mafi akasari shida Aminan shi sun zab'i gurin ne domin tattaunawan sirri, shi yasa suke shiga gurin.
   •••
Lokacin da ya dawo gida, ya same ta a kitchen, dan yasan tunda ya hana Haroon shigowa gidan, shi yake zuwa musu da abinci, yana shiga ya samu ta gama jollop din rice wanda ya sha, kifi da kayan kamshi, har da kayan kamshi dangin cinnomi da mashroon powder, sai kanshi gidan yaƙe, cikin gadara da iko ya isa gaban abincin ta sauke ya saka wata yar bowl ya debi abincin sannan ya kwashe kome na kai duk abinda zata ci dashi ya juye, domin sai yanzun ta fahimci ashe bata cin abincin da yake kawo masu, dan haka ya juye har da salat din ya fita abinshi, ko kallo bai ishata, sauran ta kwashe da kanzon tafto.
   Tass ya cinye abincin, ya juya yana kallon yadda take cin nata,kamar ba zata ci ba, gyaran murya yayi tare da cewa.
"Yau zaki bar gidan nan!"

Da wani irin sauri ta d'ago kanta, cike da farin ciki.
"Amma kina da inda zaki zauna ne? Kinsan Lagos ba kamar Yola bane, akwai gang na yan iska, masu lalata yan mata."

  Cikin rashin wayo tace mishi.
"Toh ai kai ne zaka mai dani Yola sai ka basu hakuri."
"Ni kuma? Toh duniya zargina suke na kashe ki, har yanzun case din ake, sannan kuma dole ki bar gidan nan domin Aysar Haladu da Manager suna niman ki, zasu kashe ki, shin kin shirya haduwa dasu?"

  "Toh Don Allah kai ba zaka iya taimaka min bane?" Ta faɗi haka cikin rashin sanin abin yi.
"Tab! Bazan iya taimaka miki ba, domin gaskiya nima iyayena suna son na koma can cikin gidan na zauna dasu!"

"Don Allah,Mr Mahir ka taimaka min don Allah."
"Ke babu taimakon da zan miki,akwai kartin maza a wajen garin zasu iya ruined pride dinki su baki gurin kwana, amma Ni ba zan iya ba, maza ki gama ci,ki bar min gidana."
Kuka ne yazo mata tana rokon shi amma kememe, ya ki kulata karshe tace mishi.
"Don Allah ka rufa min asiri, na zauna na tsawon wata daya After Ramadan zan tafi ko ina ma"
"Ke baliga, Ni baligi anya baki hango abinda zai faru ba? Baki tunanin zan iya far miki."
"Ai nasan kai mutumin kirki ne, don Allah idan da hali ka ɗauke ni, aiki a kamfanin ka."
"Ta nan kika biyo?"
"Please wallahi zan na biyan kudin haya da albashin da zaka bani!"
"Wa zaki biya kudin hayan?"
Ya tambaye ta idnun shi a buɗe,
"Kai mana, kai zan biya wallahi bani da kowa kasani ai, kai ne garkuwa na, please kayi hakuri na zauna a cikin gidan nan, domin nan ne matsirana."

"Tab' bazan yarda ba, kin manta yadda kika yi ta kafta min rashin mutunci ne? Ko kin manta tijarar da kika min ne!"

A rud'e ta mike tare da zuwa gaban shi ta zuba gwiwar ta a kasa tace mishi.
"Don Allah kayi hakuri kome ma kace nayi zanyi kawai ka barni na tara kudin jirgin da zai kai ni gurin Family na, kaji."

Tausayi ta bashi, amma bai sanya ya hakura ba, duk da yana da burin shi, amma haka yayi ta bata wahala, tana kuka kafin yace mata.
"Ina da sharadi da kuma abinda zaki min sai na kyale ki! Su Ummi zasu tafi Umrah dukkansu, dan haka."
Ya mike tsaye, tare da giya hannun shi a bayan shi, yace.
"Zaki zauna na tsawon wata guda amma ba zaki zauna a yadda muke ba, dole zaki amince...
😉😜😂🤣
Eyyeeeee toh wallahi Kuyi Vote da Comments, kuma kuyi share din shi ko kuma Alqur'an naja bargona nayi ta jan ragona 🤩😍🤨 Lemme see wich can wuta bal-bal-bal zai tashi
#Team Mahir
#Team Noorh
[1/23, 11:09 AM] Addah Ramlat MANGA: https://my.w.tt/GmD0CxtiNcb

MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 2️⃣8️⃣
     MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Kallon shi tayi jikinta yana rawa, ta juyo gaban shi.
"Zan duk abinda kace don Allah karka kore ni!"
Wani kallon banza yayi mata, tare da dauke kan shi, ganin yadda take kuka sai Yaji haushin abinda yake mata, but halin Noorh da a zamanin  fir'una tazo tabbas. Itama sai Annabi Musa yasha fama.

                 Dauke kai yayi cikin mugun miskilanci ya cigaba da zarya a falon hannun shi goye a bayan shi, kamar bai san da ita ba, sannan ya d'ago kan shi yana faɗin.
"Zan baki zab'i daga nan zuwa gobe kawai"
Cikin rawan jiki ta karkace kanta tana me cewa.
"Duk abinda kasani zanyi."

Cikin wani irin jan aji, yake kallon smart watch din shi, tare da cewa.
"Na manta sharadin jeki idan na tuna zan gaya miki, amma ki kwana da shirin zaki bar gidan nan gobe."

     Kallon shi tayi bakin ta a sake tana share kwalla, cikin damuwa da tsoron karta mishi magana ya bayyana mata, cewa ya fasa yasata jan bakinta tai shiru, shi kuma haka bai mishi dad'i ba, yaso yaga ta ji haushi, amma sai bai ga haka akan face ɗinta ba, sai ma damuwa da tashin hankali.
           Haka ya bari yazo wucewa, ya kai hannun shi ya daki bom-bom ɗinta, cikin masifa ta juya, ta shiga zazzaga mishi tijara, dariya ne yaso kwace mishi ya kura mata ido, kafin yace mata.
"Ni kike gayawa magana? Daga an d'an make ki sai ki buɗe baki zaki min rashin mutunci, ke ni Ban da zuciyar musulunci, me zanyi da sauran gardawa,.da suka gama lalatawa.
          Toh zoki fita min a gida, yau zaki bar gidan nan ba gobe ba."
"Amma, dai kasan abinda kake haramun ne, idan ranka ya b'aci kayi hakuri ba zan kuma ba. Amma don Allah ko bani ba, ka taya matan da basa tare da ahalin su, yana min ciwo idan ka tab'a jikina sai naga dan iyayena basa raye ne."

      Duk sai yaji babu dad'i, domin yadda ya fahimce ta, duk abinda za ayi da ita, matukar ba za a tab'a kimarta ba, toh babu abinda zai dame ta, amma matukar aka tab'a kimarta duk sai ta rikice tayi ta fada.
Sab'anin wasu yan matan da kana tab'a su magana ya kare, sai dai ma su nuna maka sun fika zakewa.

               Mikewa yayi, ya bar gidan ma baki daya, haka ta wuni cikin damuwa da tararadin abinda tace mishi, kar ya kuma tambaye ta abinda ba zata iya bashi ba, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun,ta fadi haka yafi sau goma.

      •••
Tsare Mishi hanya Nazzir yayi, cikin isa da iko, bai ce kome ba, yaja motar da baya, da gudu sannan yazo a guje ya daki motar Nazzir sai da ya bugi wata bishiya da aka dasata domin kwalliyar fasalin gidan. Sannan ya wuce abinshi yana gargad'in shi da hannu ya shiga hankalin shi.
        Dan haka bayan Ya wuce, ya nufi gidan Ummi ya samu suna hada kaya.
"Ya Mah ba zaka umrah. toh ka shirya Aunty n..."
"Shii! Bana son magana, idan wani yaji fa?" Wuce ta yayi ya haura dakin shi ya kwanta, yana jin sam bai mata adalci ba, sam babu adalci a wannan al'amarin yaso kan shi da yawa, taya za ayi ya sako batu me girma haka?

   Anya Dr da Brst basu kai shi sun baro ba kuwa? Toh me zai ce mata? Shi baya son abinda zai kai ga cutarwa ne,.idan al'amarin ya fito, toh tabbas zai iya janyo mishi rikici a kamfanonin shi.
      
    Amma idan ya tuna da, yadda haka fitowar ta zai zama me musu bakandamiya sai yaji nutsuwa a ranshi, sabida yana da shiri na musamman akan Bayyanar da Noorh, shi yasa yake niman hadin kanta, toh ya fahimci. A yadda ya gama tsorata ta, zata iya bashi hadin kai a ruwan sanyi. Dan haka yana gidan har dare sannan zai fita zuwa masalaci, ya hadu da Baban Nazzir, nan ya gaishe shi sannan ya wuce, bayan sun fito sallah isha ne, suke tattaunawa.

Har yake kuma gaya mishi maganar hada shi da Zoolfah, kememe Mahir yace ba zai aure ta ba, abun ya bashi mamaki ya kuma gaya mishi cewa, ai wannan hadin tuntuni ake yi a familyn su, mahaifin shine kawai ya auri Mahaifiyar shi bare,
Mutumin ku yace bai san wannan batun ba, shi matar shi tana nan zuwa gare shi,.idan basu son Zoolfa ta zama karamar  bazawara. Toh su kyale ta, tayi rayuwarta da wani namijin ba shi ba.
         Wannan abun yabawa Kawun shi haushi, dama Nazzir yana yawan gaya mishi magana akan Mahir din sai gashi yau ya amince, har zai tafi yace mishi.
"Ko abinda ake gaya min gaskiya ce kana bin maza?"

"Eh duwawun su nake ci. Duk wanda ya Kuskura ya kawo min mace gidana ta duwawunta zan danna mata ciki kuma na mata wulakancin da sai ta gudu da kafarta, karewa ma na kawo maza su zo su taya ni farke duwawunta" Ya gaya mishi haka, sannan ya tafiyar shi, kai tsaye gidan shi ya nufa duk da akwai tafiya me nisa, amma dake ran shi ya b'aci, bai hana shi ganin tazarar tafiyar ba, yana cikin tafiyar kawai sai ganin wani yayi da mashin da mugun gudu yana zuwa dai-dai inda yake kawai yaji an soka mishi wuka za a ja yayi maza yaja da baya, tare da rike hannun mutumin ya dawo dashi baya, sai da ya fadi akan mashin din, yayi kan shi da gudu ya tashi tare da karawa da gudu, jinin da yake zuba a jikin shi ya sa shi bai bi mutumin ba.

         Cikin gidan shi ya shiga tare da rufe ko ina da security, sannan ya nufi ciki yana jin jiri.
A hankali ya isa har cikin falon, tana zaune taga shigowar shi da sauri ta mike, kamar wanda yasha wani abu haka yayi kanta sai da suka mannu da bango, bakin su ya hadu da juna, tare da  sumbatar juna, ita kanta b'ata tab'a kawo haka ba, sosai ya manne mata, yana sumbatar bakin ta, duk yadda taso ta raba shi daga jikinta yaki, da kan shi ya.janye bakin shi.
"Ki bar ture ni! Jiri nake ji an yanke ni."
  Kai hannunta tayi kan cikin shi taji damshi, da sauri ta d'ago hannun ta tayi tare da zaro idanu, bakin ta na rawa tace.
"It's blood!"
Sake shigewa jikin ta yayi tare da matseta.
"Suna son kashe ni ne!"
"Su waye?"
Ta tambaya a raunane, tare da kallon shi.
"Ban san su ba, amma tabbas zan mutu!"
"Don Allah ka rufa min Asiri, karka manta kace zaka kafa min sharadin, don Allah karka rufe idanunka. Kalle ni."

          Abin dariya, haka tayi ta mishi shirme, shi kuma dama haka yake so, ya sami abinda zai bashi damar shiga jikin ta, idan ta ga yana lumshe idanunshi zata fara girgiza shi har sai ya bude idanun shi.

      Bata waya yayi ta kira mishi Dr, can yazo ya duba shi tare da mishi dinki, basu guri tayi.
"Meye ma'anar haka?"
"Wallahi ban sani ba, kawai dai sun yanke Ni ne, kuma ba zan ce maka ga wanda yayi min haka ba."
         "Toh kuwa ya dace a saka security Camera a unguwar baki daya, yadda zai taimaka gurin gano masu aikata laifi."

"Toh zan duba."
"Gobe za a fara azumi baka cewa wancan Yarinyar kome ba."

    Lumshe idanun shi yayi tare da cewa.
"Zan mata domin har yanzun tana jiran sharadi na da zan gindaya mata. Nafi son idan su Ummi suka bar kasar ne, amma idan suna nan ba zanji dad'in isar da nufi na ba."

    Jinjina kai yayi sannan, ya hada kayan shi tare da musu sallama, yana fita Noorh ta shigo da fruit salat, tare da Farfesun kifi, wanda tayi ne dan kanta amma ta juye mishi bata sani ba ko zai ci, tunda ta kawo mishi yana kallon yadda fuskarta yayi jajjur, tana mika mishi kanta a sunkuye. Yana amsa yaji saukar kwalla me zafi akan hannun shi.

       Rike abincin yayi da hannu daya, sannan ya riko hannunta, ya ajiye abincin a saman gadon shi ita kuma yayi mata masauki a kan cinyar shi.
"Kuka na me?"
"Ba kai ne kake cewa zaka mutu ba? Kuma idan ka mutu bani da kowa, waye zai mai dani gida? Sai fatar mutuwa kakewa kanka."
"Do you love me?"
Kamar wanda ya watsa mata hot water, ta mike har da karkad'e jikinta, tana zabga mishi harara.
"Ubangiji ya yaye min, Allah yayi min tsari da soyayyarka, ai mafi girman kuskuren da zan tabka kenan a rayuwata,"

Kura mata ido yayi, tab'e baki yayi cikin nutsuwa ya fara shan ruwan farfesun kifin. Yana sha yana yatsina fuska,karshe dire mata abinta yayi cikin nutsuwa yace mata.
"Ki fara niman inda zaki, domin gobe zamu tafi Umrah da family na."
      Kura mishi ido tayi cikin jin haushi tace mishi.
"Babu inda zani, sai ka gaya min meye nufinka da Ni."

"Zaki bar gidan nan kuwa, tunda harshenki kamaninki"
"Wallahi ba zan bar gidan nan ba, gwara ma tun wuri kasan nayi dani."
"Fitar min a daki!"
"Babu inda zani!"
Yunkurin mik'ewa yayi, cikin sauri yace.
"Ya Ilahi, zan mutu!"
Lokaci guda ya shiga vibret, zaka rantse mutuwar zai yi,.har shure ² kafin kace kwabo Noorh ta birkice karshe yada kai yayi kamar wanda ya sheka lahira, da gaske.
Wani irin kuka ne ya kwace mata ta haura saman gadon, tana jijjiga shi mamalam yana jin kanshi a jikinta tuni ya wani lafe a kirjinta, shafa kanshi take tare da sheshrkar kuka. Tana cewa.
"Don Allah karka min haka, ka tashi kaji ni ban sha'awan soyayya ne, nafi son na ganni cikin familyna daga baya kome zai iya faruwa,.kuma ka fahimci abinda zance Wallahi iyayenka ba zasu amshe ni ba, don Allah kar mu b'ata lokacin mu a san zuciya mana."

  Wani irin murza kan shi yayi a boons ɗinta, cikin wani shauki yana kuma matse ta, a kirji shi kallon fuskar shi tayi ganin yadda yake squeezing din kirjinta da kanshi cikin wani irin yanayi me shegen dad'i, a karon farko da haka ya tab'a lafiyarta, narkewa ne

Please Login or Register in order to submit comment