Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya har cikin gidan ya kai ni,sannan ya tsaya tare da mika min tissue, na bude tare da cewa."thanks!"
Na ficce abuna, tunda daga bakin kofar shi gidan cikina ya murɗa, dan na hango ta tana kuka a jikin window..
Ina shiga ta juya gurin Mommy, cikin kuka tace..
"Mommy shine ya kawo ta, Mr Nazzir Abu Aswad, Mommy na shiga uku mutuwa zanyi don Allah Mommy ku kore A'isha daga gidan nan!"

#Vote
#Comments
#Share😍😘🌹
https://my.w.tt/fpBMaONrHbb

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 0️⃣5️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

~#HB Family~

Wani dan iskan rawa jikina yake tare da zaro idanu waje, cikin karaji tace.
Fitar min a gidan Ubana, bana son kuma ganinki, bana so? Bana kaunar ganinki, fita ko na saka a kashe min ke!"
   Ta shiga turani da karfin tsiya, hawaye ke tsiyaya a idanuna, a hankali momy ta tako tare da zuwa gaban mu, ta kifa min mari.  Kafin ta kuma d'ago kaina.
       "Ke! Kike niman hanyar da zaki wargaza farin cikin Baby Queen?"
Bakina na rawa nace mata.
"A'a momy wallahi ba  yadda take tsammani bane, wallahi babu kome a tsakanin mu, kawai tana zargi ne don Allah kiyi hakuri wallahi ba zan kuma shige mishi ba."
          Kallona a hankali tana danne zuciyarta ga abinda yake tinxirata, gani take me zai hana ta lalata fuskar da mutane suke rawan kai akan shi. Idan ta tuna kuma yadda dangin Mahaifiyar Noor suke mahaukatar masu kuɗi ne, sai taji jikinta yayi sanyi. Dan tasan tana tab'a lafiyar Noor kamar ta kashe yarta da ranta ne.
     .Sake ajiyar zuciya tayi sannan tace mata.
"Karki kuma sakewa naga kin fita zuwa HB. Company idan kuma na fahimci haka toh zan lalata miki."
"Insha Allah ba zan kuma ba kiyi hakuri don Allah."
   "Wuce ki bani guri."
Da sauri na bar falon tare da hayewa sama, ina wucewa suka bini da kallo.
"Momy!"
"Bana son ci da zuci, idan muka mata wani abu kece zaki fara faduwa, idan muka barta kece zaki moreta. Dan haka ki zuba mata ido, zan barta ta koma amma kafin nan kin shigewa Mr Nazzir.

Yadda babu wanda ba zai san kuna soyayya ba, karki sake ki bada damar da wata zata gane cewa kina jin haushin Noorh, dan haka ki shige mishi. Insha Allah akwai wata mata mari, tana hada magani na musamman, sabida irin su Mr Nazzir.

        ---
A hankali na zube a bakin gadon,  na fashe da kuka. Tare da dafe goshina..ina kuka ina karawa, sai da nayi ya ishe ni sannan na mike na cire kayana na shiga ban daki nayi wanka tare da alola na fito.

           Na saka dogon riga, tare da hijab nayi sallah. Sannan na kwanta a kan abin sallah. Ina sauke wasu kwalla masu shegen zafi. A hankali har barci ya dauke ni.
      ---
Lagos.
A duniya Allah ya halicci mutane da halayyar su daban daban, wasu zaka samu suna masifar son sanyi wasu kuma suna son zafi, haka wasu kuma suna matukar son ruwa. A cikin wannan dabi'ar Mr Hamoud Boualem ya gina Iyalin shi. Mutum ne mai matukar kaunar ruwa. 

        Shi yasa da ya tashi gina gidan shi ya gina a bakin tekun Lagos, a banana island. Inda ya saka ka je har kasar Kuwait aka zano mishi hoton wani dankarerren gida, me mugun kyau, inda ya sanyawa gidan sunan.
Narrabeen beach housa. Yayinda mutane kewa gidan lakabi da honey house, kasancewar gidan guda hudu ne a cikin unguwar.

   Gida na daya gidan Shi da iyalin shine, kafin rasuwar shi. Four bed room ne, sai kitchen guda biyu da falo uku.

    Hajiya Maryam itace matar shi, daga ita bai kara aure ba, ita daya ce tal. Hajiya Maryam tana da yara biyar namiji ɗaya sai mata uku.
Mahir shine babba, me shekara talatin da uku, sai Hadiya. Wacce take da shekara shirin da takwas. Tana aure a lekki. Sai Suhaila wacce take da shekaru ashirin da hudu, tana karatunta na karshe a Calgary.
    Sai Adeemah wacce shekarunta Ashirin da daya, tana karatun a jami'ar Abti Yola, sai yar Uwarta su Alishbah. Itace take secondry school, ss2.
        Mansion din cike yake da ma'aikata, wanda suke karkashin kulawar mahaifiyar Mahir, kasancewarta babbar  Judge na garin lagos.
Mace mai addini da Sanin ya kamata, sannan bafulatana ce gaba da bayanta, dan ko Hausar ta har yanzun bata ware ba. Gidan.
       Sai Mansion na gaba, gidan Barraq Abu Aswad, Mahaifin Mr Nazzir Abu Aswad. Kanin ne ga Hamoud Boualem, wanda suka kasance Uwa daya.

     Dan kimanin shekaru saba'in idan ka ganshi ba zaka ce ya kai haka ba, tare da matar shi Sahiba, yaran su uku.

          Nazzir shine babba, sai Nurul Sahar, sai kuma  Zoolfa. Suna da mugun ji da kansu, basu cika son mutane suna zuwa gurin Hajiya Maryam ba, toh ya zata yi ita na mutane ce, Hamoud Boualem asalin su yan kasar algeria ne. Wasu damuwa irinta zumunci yasanya Hamoud Boualem ya bar kasar shi ta Haihuwa,

   Ya dawo Naija da zama, lokacin da  yazo ne ya nemi inda zai fara kasuwanci sai ya zabi zaman yola, a can ya hadu da Hajiya Maryam, har suka yi aure.  Ana suka haifi mahir, sannan ya kafa kamfanin shi na soft drink, Sabida yana da asalin babban branch din shi a Kasar shi ta Haihuwa. Wato Algeria.

.... Bayan haihuwa Mahir suka tafi Algeria anan suka samu family house din su ya kuma tarwatsewa, sakamakon matsalar  cikin gidan su, a cikin mutanen da suka bar gidan har da dan uwantar su. Shima ya bar garin biskira. Haka ya dame shi sosai,. Da zai koma ne ya tafi garin bechar inda mahaifiyar shi take aure, ya daukota da kanin shi Barraq Abu Aswad. Mahaifiyar su mai suna.

   Hadiya, tazo ta zauna dasu lokacin Hajiya Maryam tana karatun ta akan lawyer. Haka suka ci-gaba da zama a Yola har matar Barraq ta haihu lokacin Mahir na da shekara biyu har yanzun suna tare da Hajiya Maryam.

       .... A hankali kome na family yake tafiya cikin tsarin Ubangiji, sabida Mr Hamoud Boualem yana bawa kowa damar yayi abinda yake so. Har Mahir da Nazzir suka girma, aka kai su makaranta mafi tsada da kyau wato king Abdul azeez Saudiya. Acan suka fara karatun su har suka kai matakin digiri.

         Anan ne kuma suka raba jaha, domin shi Mahir yana son aikin tsaro, yayinda Nazzir ya zabi kasuwanci. Mahir ya tafi College of militry USA. Inda ya samu degree din shi a fannin binciken sirri, sannan ya kuma sake samun degree na biyu, akan yaki da ta'addanci. Dan haka ya dawowa gida Najeriya hukumar sojojin ƙasar suka dauke shi a shashin sirri.
        
     Amma daga baya ya ajiye aikin bayan wani irin tashin hankali da akayi a ƙasar naija, wanda aka samu fada tsakanin bangarori biyu na ƙasar, yanzun haka ya ajiye aikin baya damuwa da kowa, sai kasuwancin shi da kamfanonin mahaifin shi musamman wadanda suke dakon mai dasu.

      Mahir yana da matukar kirki amma bai da mutunci kasancewar yayi aikin soja, abu kadan yake fusata shi, bai cika hayaniya ba, har yau Mahir yana da mafarkin akan wata mace da suka haɗu. Amma ya manta inda suka haɗu.

      Mutum ne da ya kasance miskili,. Bai da magana amma yasan kan mugunta, domin idan yana gari. Yana da Office a cikin gidan shi, akwai wani a cikin gidan mahaifiyar shi.

       Idan aka mishi abinda bai masa ba, zai iya hana kowani mai aiki  barci a ranar, ya saki kuyi ta aikin da babu. Idan yana barci ba a hayaniya a cikin gidan su ko gidan shi. Atleast dai bai son kwaraniya, shi yasa ya ajiye aikin militry, yace aikin militry bana mutane irin shi bane.

           ......
Sauran Mansion din kuwa, sun hada nashi dana Nazzir. Duk cikin gidajen gidan Mahir yafi na kowa haduwa da haska Mansion din sabida gidan sama ne da fuskar gidan yake kallon taku, sannan Bayan anyi building gidan, amadadin katanga wasu irin Glass me mugun kauri aka saka a jikin gidan Amadadin bango.

           Anyi tsarin gidan farin paint ne, yadda haka falon gidan guda hudu ne, kamar yadda dakunan gidan suka kasance huda uku.
        Falon shi na farko wanda yake sama kayan cikin kujerun falon ba wasu dayawa bane amma gray colour ne, sai dan gurin shakatawa, wanda daga falon kana hangowa, kuma kana hango tekun Lagos. Sannan shima falon yan me dauke da dinning table kujeru guda ukku

      Sai na biyu, shima multicolour ne, amma a kasa yake, sannan akwai littafai, tare da frame na wall, da dinning table, sai yan wasu drower masu shegen kyau na jikin bango wanda aka yi shi daga wood. Akwai yan step da zai haura dakai falon sama. Zuwa bedroom din shi.

      Sai daga nan kana hango ruwa ta falon shima fantastic babu laifi.
     Sai falo na uku, wanda ya kasance kujeran anyi su da wani irin itaccen ne kamar yadda ake basket, sannan kome na cikin falon is Whiter.
 
    Sai wani dan trow da aka saka na ash colours, sannan tsakiyar falon akwai wani katon basket wanda aka daura Flower a kan shi. Shima kuma a kwai dinning table a cikin shi sannan yana dauke da kujeru guda hudu.

Wall din falon an manna frame masu shegen kyau, da tsada domin a Moscow ya sayo su.

     Sai kitchen a falon sama akwai kitchen wanda kome na kitchen ɗin gray colour ne, hatta iland din kitchen ɗin sannan akwai wasu chair, masu kyau a jikin iland din, wanda mutane hudu zasu ci abinci a gurin, asalima kitchen ɗin yana cikin falon ne.
    Kitchen na biyu, yana kusa ne shi kuma kome nashi brown da Golder ne, me mugun kyau, kome a tsare yaƙe.
        Dan wani home Office din shi wanda yake kusa da falon kitchen shima kusan kome iri daya ne da kayan kitchen ɗin kasancewar da wood aka yi kayan kishin cin ba da cafara ba, normal katako ne. Sai labrary da aka jera books, da wasu manyan kujeru masu shegen kyau. Tare da wani dan gurin da aka mai dashi na hura gawayi. Ko itacce yana ciki sabida sanyin Teku.

                 Sai tables din da aka daura laptop din shi da wasu abubuwan na aiki daga cikin office din kana hango waje ta window Office din.

    Sai kuma bedroom din shi yana farko yana zagaye da wani irin glass wanda ya kasance blue black, aka shiga cikin shi zai rufe kanshi sannan ya sake wasu irin labule masu kama da net. Sama gurin kuma yana bada haske light blue, tare da sanyin ac. Gadon yana tsakiyar zagayen ne.

     Sai wasu takarkace nashi tare da wani dizn na doki, a dakin cikin bathroom din kuwa, akwai soup bowl freestanding tub, a cikin ban ɗakin. Mai shegen kyau. Wanda idan ka gani sai kayi sanyin shiga cikin shi.

       Akwai wash tub, shima bowl ne masu mugun kyau. Da wani wardrob inka ajiye rugunar wanka da towel da inda ake ajiye kayan wanka, irin su sabulu, soson wanka, brush da maclean. Da inda ake ajiye kayan gyaran fuska.

        Sai kuma daya rum din wanda ya kasance bai cika Yarka ce ba, amma bed din cikin shi kome na ciki  pink da Golder ne akwai royal chair a cikin dakin sai tv da wanda yake saman wani  stand wardrob, tare kwalbar Flower. Kana hango bakin ruwa ta jikin gurin. An sake wasu labule net. Haka ma gadon ya sha shimfid'a.

  Sai daki na uku.  Yana kallon takun sosai shi kam royal bed ne, idan nace zan muku bayani bazaku fahimta ba, amma bari na nuna muku kome daki daki....
Mu hadu a next page.....🌹



  The honey house...

    



First falo..



   Second falo.



Third falo.



The master bedroom



Lady bedroom



     The royal bedroom..

  



Fisrt kitchen.





The Home office...

     So mu hadu a next page... Amma gaskiya zan tafi hutu, maybe sai sabon shekara, idan kuma kinyi Vote da comments insha Allah zan iya dawowa..
Please commenta, Vote, And share 🌹😍😘
      https://my.w.tt/8Q5hDfaJJbb
   MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 0️⃣6️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

~promotion~

A cikin dakuna biyun man akwai
Manyan bath tub na Alfarma, wanda mutane biyu zasu iya shiga su zauna,
   Second rum akwai.  Retangle corn tub, musamman daga Japan aka zo dashi, aka saka a cikin bathroom din,

Sai third rum, akwa  luxury alcover tub, shi kam wani zuwan Mahir Moscow ya zo dashi, dan ya burge shi.
A ta wajen gidan akwai wani katon costco hot tub, na wanka  aka ajiye shi. Shima mutane biyu zuwa sama da biyu zasu iya shiga cikin shi suyi wanka. Sai kuma Luxury Gym room inda aka zuma inda kayan kayan karfe ne da yake d'agawa, sabida murdewan jiki.

       Sai Games room, inda aka zuba kayan games na manyan maza har da karamin Bar, gidan a iya kawatuwa ya kawatu, zai yi wuya ka shiga gidan ka fito cikin dadin rai, sabida babu inda bai hadu na.

      Duk wannan haduwar gidan bai tab'a burge Mr Mahir ba, sabida yayi alqawarin duk wacce zata shigo gidan, toh ba karamar jaruma ba, shi yana da buri. Amma ya barshi da mahaliccin sa.

       ••
"Maryam! Shin ba zaki yiwa Mahir magana akan auren nan ba, anya kun min adalci? Haka zan koma ga Allah banga jikokina ba?"

      Cikin nutsuwa Ummi ta gyara zama sannan tace mata.
"Jaddih kiyi hakuri! Wallahi Baba kaman me cutar aljanu, wancan watan da suka wuce Ni dashi muka yi magana akwai Nabeeha yar abokiyar aikina tana Kano, mun yi aiki da ita aka meda ta Kano, yaron nan suka haɗu da ita yarinyar me sunan. Anjum, hmm Yarinayr ta dama haukacewa akan shi. Tana komawa gida ta nunawa mahaifiyarta da Murna Uwar ta kirani take gaya min ashe Mahir ya dawo. !na amsa mata da eh anan take labarta min yadda suka yi da yarta, hmm Hajiya na sami Mahir muka yi magana tare da niman Alfarmar kar ya kunyata ni."

Dariya Alishbah tayi tare da cewa.
"Ummi bari na bata labarin abinda ya ce da yarinyar. Lokaci da yaje ya dawo, dan ko awa uku bai yi ba. Jaddih yana zuwa bai yarda ya shigo ba sai da dare.

         Kamar wani wanda ya had'iye wuta haka ya shigo, ya zauna Ummi tace "Baba ya hanya da fatan ka ga yar gidan Hajiya Halimar?"
     
Kallon wani kujera na musamman tayi a falon, ta muna kwashewa da dariya sannan ta cigaba da cewa.
"Jaddih bawan Allah nan ya gyara zaman shi akan kujeran, kamar wanda Ummi tayi mishi fada, ya cigaba da latsa wayar shi. Sai da Ummi ta kuma magana ya bude baki kamar wanda yake ciwon hakuri yace.
"Ummi don Allah meye laifina da zaku hada ni da wata yarinya me siffa kamar tumatir, gaskiya bazan iya rayuwa da ita ba!"

  Haka ya mike tare da barin gidan, nan shiru Ummi tayi  ina ganin kawar Ummi tana kiranta amma taki dauka.

       Idan baki manta ba akwai Jadwa yar Kanwar Ummi, haka yarinyar nan ta haɗu da Ya Mahir, Cope town tayi ta mishi magana, ya Mahir ya shareta sai da suka zo hutu, ta mishi abinci ta kai mishi wancan dakin Ya Mahir ya juye abincin Karen shi Dolna. Wai bata iya girki ba. Ko shi ya shiga kitchen sai ya dafa abinda zai fi nata.
Karshe munafikin karen shi yayi ta barci shine ya dauko wani bindigar shi wai sai ta gaya mishi me tasakawa karen yake barci."

    Aikuwa kakan tayi shiru, tana sauraron jikarta, gyara zaman lullubinta tayi sannan ta kuma rike calbin hannun ta, ta sake murmushi. Sannan tayi gyaran murya tace.
"Ashe yana magana haka?"
"Hajiya yana yi, idan yaso idan bai soba sai ya manna abu a kunnen shi yayi shiru abin shi Allah kadai yasan yawan mutanen da Baba ya sani jin kunyar su, daga yace wancan ta cika kyau, tayi fari da yawa, sai yace ta cika surutu, bakinta babba ne, kai ina bakinta yayi karami wai kawai na tambaye shi Yarinyar tayi maka? Shine sai yayi ta zage su, akwai yarinyar da yace min wai Ummi wancan yarinyar tana da kirji da yawa, haihuwa daya zasu kwanta, wata kuwa ce min yayi idan ya fara tsufa tana da boom zata iya rasa gwiwarta, wata kuwa ce min yayi matsalar yarinyar ta haɗu sai dai guntuwa ce, daya kuma yace min tayi tsayi dayawa, Hajiya babu yarinyar da ba zai kusheta ba, daga tayi tsayi sai ta cika siranci. Na rasa gane mishi kuma idan zai fasa ba zaka ga yayi dariya ba fa a'a cikin kamewa yake maganar"

      "Shi yasa kwanaki nace yaje su daidaita kansu da Zoolfa, kallona yayi sannan yace min.
"Bata da kunya."
Da ya bani Haushi nace mishi.
Toh kai wacce irin mace kake bukata?
"Ban sani ba, amma ina jinta a rayuwata." Ina sake bude baki zan kuma mishi magana ya janyo  mashin kujeran ya rufe fuskar shi Alamar baya son maganar ma kenan.
     Yadda kuka san me aljanun haka yake, yanzun zai yi abun Arziki an jima zai shuka na tsiya..
    •
Yola.
Tun asuba dana farka, na shiga nayi alola nazo na gabatar da nafilla, ina idarwa na gyara gurin kwanciya na, na kuma kwanciya abuna.
             Ina cikin barci naji kamshin turarena, bude ido nayi cikin barci na kalli Tasleem sanye da unifoam dina, ban kulata ba na gyara kwanciya na gabaki daya kayana tayi amfani dashi, tana shiryawa tana tauna chewgum, tana gamawa ko sallama babu tayi tafiyarta...
      .... Karfe goma ta isa kamfanin, kanta na wani irin hayaki ta isa Office din Badar, ta gama abinda zata yi sannan ta cigaba da aikinta dake baya cikin office din. Shigowa yayi ya same ta.
"Ayya Slim lady! Ina Noorh?"
Wani irin yaken renin hankali tayi mishi tare da wani yarfe hannun tace mishi.
"Oh yar aikin gidan mu ce, kuma mun sallame ta koma inda tafito." Sannan ta cigaba da abinda take tana wani fisga kamar wacce ake zugata.
    Karfe sha daya Mr Nazzir ya leko tare da kallon su ganin yadda kowannen su ya juya yana abinda yake gaban shi yace musu.
"Ina A'isha Omar Jimeta?"
Shiru tayi. Kafin ta wani lalle shi a fisge tace mishi.
"Ayya ta koma garin su."
"Wat?"
Wani karamin murmushi tayi sannan tace mishi.
"No dama anyi maganar auren tane toh taje a tabbatar ne maybe zata dawo da auren ne, ta karasa service."

   Shiru yayi na wasu lokuta, kafin ya sake murmushi yace mata.
"Ok! Kizo mu fara aiki dake, ita kuma tunda tana da aure sai ta zauna a Office din Lion."
    Sam tattaunawar bai burge Badar ba, kallon Badar tayi cikin jin dadi tace mishi.
"A Cigaba da zaman nan, mu sami promotion, and am pity for you guys da kuke min hassada, ita kuma kafin tazo i get wat i want."
Ta wani mishi bye bye da finger. Murmushi yayi tare da cewa mata.
"Am wishing you all the best"

Ta fita tana wani rawan kai, tare da jijji da kai, har ta isa Office din shi.
        Yan mata dayawa da suke aiki a kamfanin sunji haushinta, tare da tsanar ta. Aikuwa tayi ta zuba Iskancin ta, son ranta uwa uba wani shegen shakuwa ce mara ma'ana ya shiga tsakanin su da Mr Nazzir. Shakuwr da kowa sai da ya fahimci a tsakanin su akwai yarda.
        A hankali ya bata wani irin power, wanda ya sanyata rena kowa a cikin kamfanin, kai yadda Tasleem tasamu dama a cikin sati Uku zaka dauka Ubanta ne ya gina kamfanin, nan kuwa yar banza, bata da lasisin kome a cikin kamfanin sai na bautar ƙasa.

    A yadda suka shaku da Mr Nazzir,  har fita yawo suke, bayan an tashi aiki, zai zo ya kawota gida, sannan ya kuma dauke ta zuwa yawo, Iyayen ta ba karamin dad'i suka ka ji ba, su maganin farin jini, tare da na makiya, irin su  Noorh. 
A tsakanin su da Mr Nazzir bata hana shi yayi Romance da ita, kome zai yi da ita zata barshi amma bata yarda ya tab'a virginity ɗinta ba, yana fara yunkurin zata fara rokon shi ya kyaleta, abinda ya lura da ita shine tana da kwaɗayi ita da iyayenta. Dan haka ya shiga zubawa Ubanta kudi tare da bashi cantrac, nan kan Ubanta yayi girma, sabida yarshi ta janyo mishi hanyar Arziki, gori da bakar magana tare da haibaci. Noorh tasha, sai dai bata cika damuwa ba.
         Basu barta ta koma kamfanin ba sai da ta cika wata uku da kwanaki, yadda sannan suka ce ta koma, lokacin da ta dawo kome ya sauya, bata cika zama cikin mutane ba. Mr Nazzir ma bai cika mata magana ba, kawai idan ya ganta ma kauda kai yake, a hirar da suka yi da Badar ta fahimci sharrin da aka mata na tayi aure.
   Dawowar ta kuma Tasleem ta ke gayawa Yan team ɗinta, ai ta kashe auren ne, haka suke mata kallon ayaba ita kuma tana musu kallon biri.

        ••
Lagos.
Yadda Ummi da Alishbah suke aiki zaka iya rantsewa. Baki zasu yi daga Algeria, zunzurutun yadda aka shirya table da abincin sama da bakwai.
            Gidan kuwa an saka turaren wuta dana tsinke babu inda bazaka ji dadin kamshin ba,

     Adeemah da aka bata gyaran dakin shi ta wanke toilet din yakai sau goma, idan tayi ta goge ta kunna wani karamin fan da yake saman dakin, shi an saka shine sabida idan an wanke ban dakin a kunna ya bushe.

      Ta gama saka turaren wuta, sannan ta fito ta gyara gadon, sosai. Tana yi tana cewa.
"Haka kawai sai ka gama mishi bauta, yana zuwa zai ce bai mishi ba, wallahi matukar bai mishi ba toh ba makawa sai dai na gudu Abuja gurin Yafendo, wallahi bazan zauna ya kashe mutane da aikin Bala'i ba
       Kana gama nan zai ce nan bai fita ba, kana gyara nan zai ce bai fita ba, shi gashi mr tass-tass! Allah bazan iya ba."

         "Idan kin gama zagin shi kya fito ko? Allah Adeemah ki fita idanuna, Hidaya da Suhaila saka su aiki yaƙe kuma basu tab'a mishi musu ba, wato gaki nan mara kunya Allah yasa yazo ya same ki ya fasa min bakin nan."
   "Ummi kiyi hakuri!"
Fita tayi ta barta a tsaye tana gyara mishi dakin shi, tare da kunkuni, kasa kasa tace.
"Uwar me zai  mana a gida bayan yana da nashi gidan ya koma can ya zauna mana."
   Dakyar ta gama sannan ta fito, ta samu anje dauko shi tare da Alishbah, hada kayanta tayi ta bar gidan, hatta Ummi bata sani ba, gidan su Zoolfa ta koma.  Dan itace sa'arta, dake Adeemah wacce Kawayen ta suke kiranta da Deem Queen. Suna da mugun rawan kai. Yara ne masu mugun ji da kansu. Ga rashin kunya dan ma ita ita Deem Queen, Mahir yana cin Ubanta.
       A ka'idar gidan, sai kana 300 level, aka gabatar da saurayi, toh tun tana shiga aji daya ta fara rawan kai, tuni Mahir ya je ya dawo da ita tare da zaneta, dan suna tare ne anan lagos da Zol Queen, take aka raba su, ita aka mai da ta Abti, ita kuma Zolqueen tana nan a jami'ar lagos.
        A can ma ya saka mata ido sosai, domin hatta motsin ta yana gaya mata, an sanar da duk abinda take yi.

        Bayan ta baje kayanta a dakin Zolqueen, kallon juna suka yi tare da cewa.
"Allah na huta, idan zai dame ni na gudu gurin Yafendo...
......
😘😍🌹Mr Mahir 🤣 kai ɗaya mata sun shiga uku da kai...
Please Share And Vote comments
https://my.w.tt/3Nb7WDqOPbb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 0️⃣7️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

Kuyi hakuri! Abubuwan ne suka min yawa, amma Insha Allah zaku Cigaba da ganin shi koda ba kullum ba! Insha Allah

Please Login or Register in order to submit comment