Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lalace ba sai yanzun da kaddara ta faɗo mata, wallahi badan yana kunyar Ummi ba da ya maka abba a kotu."
Zaro ido Fatima tayi tace.
"Abban Affan da fatan cikin bai zub..."

"Na nawa kuma ai ta zibda cikin naso ta haifi yaron da Abba yaganshi, cikin safina ba gama garin ciki bane, dan cikine da yake da gata gaba da baya, akan cikin nan kuwa nasan sai Safinah ta zama abin alfahari a cikin danginmu amna dake lusara ce dan farin cikin Abba ta zubda shi."
Rike baki Fatima tayi tana zare idanunta, kafin tace.
"Amma wallahi akwai kura! Dan kuwa Anyi rigima akan cikin..."
Nan ta gaya musu aikuwa Nana Asma'u me zatayi banda dariya, tace.
"Lallai akwai wuta a gaba."

"Ai ni zan faɗa mata gaskiya Safina ce ta zubda cikin, kinsan da zata tafi me tabani, wallahi wani akwati ta bani zallar sarkoki da yan kunaye ne a ciki a na sayar na dinga saya mata abinda take so, kinga wannan alert ɗin yau da safe aka turo shi da dallar amurka zunzuruntu kaunar da takewa wancan sakarya, da abin cikinta, ɗazun sai da takirani ya take ya cikin wallahi yau sa safina kasa dani take tana tashi sai na mata dukar kawo wuka."

Shiru sukayi kowa da abinda yake yawo a ranshi, har Baban Sabir yazo tare da Annur.
Sai karfe tara da rabi suka tafi, aka barmu daga ni Fatima. Abdul ya koma gida.

........
Washi gari da safe Nana ta kawo mana abin karyawa, karfe goma sai ga Ummi tazo. Har lokacin ban farka ba.
Sai karfe uku da rabi na farka dishi dishi na fara buɗe idanuna, a hankali idanuna suka buɗe. Ummi da Abdul na gani a zaune Fatima ta tafi makaranta, Nana kuma ta koma gida yin abincin rana.

Gyara zama Ummi tayi cikin ɓacin rai tace.
"Zubda cikin kikayi? Duk wahalar da naƴi da rasa aurena da nayi ya zama a banza, na koma gida a matsayin bazawara Kin min adalci Safinah, laifin meye Muka miki da zaki zaɓi zub da cikin, Wallahi idan Hajiya Asma'u taji abinda kika aikata har abada bazata taɓa kallonki da kima ba, nagode da abinda kika aikata min, banda Hjy Asma'u daga ce mata cikin jikinki na D'antane har da rawan jikinta ta amshiki, toh wallahi zan gaya mata cewa cikin ba na Ashraf bane har kin zubar da shi."
Lumshe idanuna nayi, tare da komawa na kwanta. Kwalla nabin gefen fuskana, ji nake kamar na fasa ihu. Fita tayi Abdul yayi yana share kwalla, domin ina jin sautin kukan Ummi, kokarin tashi nake amma bani da karfi komawa nayi na kwanta na cigaba da kuka.

......... Sai da Nana ta kawo abinci Ummi ta koma dan tace matuƙar ta cigaba da ganina bakin cikina ne zai kasheta, Ummi da Abdul fushi suke dani, ina samun sassauci ta ɓangaren Fatima da Nana, Khalil da Khalila, Abba Lawan sau ɗaya yazo ya koma, dan Umma ta gaya mishi. Ganin halin da nake ciki ya ɗaga mishi hankali, dan sai da ya same Abba da maganata. Karshe yayi masa bibiɗi, suka rabu dutse a hannun riga.

Kwana na biyu aka sallame ni, koda na dawo gidan Abdul bai nunawa Matarsa muna rigima ba, sai dai ya ɗauke min wutane sosai. Duk sai na shiga damuwa, amma ina kokarin jan saura kimata da ta rage. Dukda naso kin biyewa Matarshi da take min iskanci, idan ina jin yunwa Atm ɗina nake ɗauka da keyn motana, tafiya gidan Abinci nake naje nasayo abincin da raina ke so.

***
Kwanaki sun haura satitika, satitika sun haura watanin, a yanzun kusan wata Huɗu babu Ashraf ba labarinsa, nayi kuka sosai gashi babu wanda ya faɗawa Nannah cikina ya zuɓe.

........ Duk iskancin da Sophia take min ban tankata ba, haka zata zo idan ina falo tayita habaici har sai na bar falourn zata hakura.
Wani abin da yake damuna, yawanci kamar jaka. Idan nasaka abinci a gabana sai naga bayan kwanu, ga kuma kwaɗayi. Idan naji kamshin girkin Sophia kamar xanyi hauka, amma dan rashin mutunci bata bani. Yau ina jin kamshin abincin da ya cika gidan na mike a hankali dan kwana biyu jikina nauyi yake min, ga ciwon jikn da bansan dalilinsa ba. Na nufi kitchen ɗinta tana fama da aiki na shiga da sallama nace.
"Don Allah Sophi abincinki zaki samin ko kaɗane"
Wani kallon banza tayi min sannan tace.
"Toh kwartonki bai kawo miki bane? Ko kuɗin da ake min burga ya kare ne."

Girgiza kai nayi cikin tsananin bukatar abinci nace.
"Dan girman Allah ki bani koda kaɗane kika ce na biya zan biyaki."

Dariya ta fasa tare da tafa hannunta tace.
"Wow kice kwartonki yana sake miki kuɗi, ok ga Acc numberna naji 50k"
Jikina na rawa na koma ɗaki ma ɗauko wayata na tura mata, tsabar wulakanci kuɗin na shiga tace.
"Zan baki amma sai kin min wanke wanke, ki wanke min kayana sai nima nasaka miki."

Sunkuyar da kaina nayi tabbas duk macen da ta zubda kimarta sai an wani gari sa'an kaninka shi zai sakaka aiki, murmushi nayi tare da cewa.
"Bani wankin, na fara dash.."

"Bazaki wanke ba! Ni Sophia kika ciwa mutunci yayata kikewa haka? Ba damuwa Didi jeki ɗaki zan kawo miki abincin da kuɗinki."

Kamar zanyi magana sai na fasa, shiga kitchen ɗin yayi itama ta ɓata rai tace.
"Ai nayi kokari tunda Uban da ya haifeta ya kor..."

Abincin ya ɗiba har yazo bakin kofa yace.
"Ki ajiye mata kuɗinta, sannan kuma ki haɗa kayanki idan zan koma zanyi ajiyeki a gidanku, aai kuma ina miki albashir da next week zanyi aure idan na kaiki ki musu bayani azo a kwashe kayanki.........

**** Ban kar zo man ba ...🏃
......
*(Ina kira gareku ban manta Ashraf ba, ina sane dashi babu yadda saudia zata yanke mishi hukunci har sai ta sami shaidu da kwarara akanshi ku biyo ni cikin labarin me cike da ban haushi da ban tausayi sadaukarwa soyayya, makirci hassada kiyayya rashin fahimta kyashi mugunta,munafuci zalunci, yaudara cin Amana)*

#MJ#HZƘ#Vote....


Oum Muwaddah....... 😎
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_*

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*



Page.٢٠
  "Waye shi? Waye zai min iyaka da muradina? Na rantse sai na kashe su."

      Tura kekensa Amir yayi tare da barin ɗakin, da gudu ya riko keken Amir Yace.
"Waye shi?"
 
"Ko waye ne baya bukatar gabatarwa, idan lokaci yayi zaka ga kowaye."

       Yana gama faɗar haka ya tura keken yayi gaba abinsa.
   Wato wani irin rikici ya ɓarke a kasar jordan, dangane da mulki wanda yakai duk wanda yayi tari akayi akan mulkin sunanka matacce. Tsabar mulkin zalimci kuma kujerar gata nan amma ta haramci mutane dayawa.
       Dan haka sai aka fara samun yan hatsaniya da yamutsi. Wanda ya kuma sabunta rigima a tsakanin mgadarar masarautar suna tankawa junarsu. A gefe guda kuwa Banu Nazir da Banu Hussein suna nan suna nasu shirin..
       .....
Sati biyu kenan da Ghaniyu ke niman Ashraf bashi ba labarin,, ya damu sosai da rashin samunshi a waya.
          ***
*Nigeria*
Abuja.....
      Kwana na goma kenan laulayi ya sani a gaba, bana iya cin kome sai ruwa aketa ɗaura min, magana me tsawo ma bana iya yinshi sosai. Ga zubda yawu amai kam ba a magana. Bani da karfi a jikina sai yadda akayi dani.
  Ina matukar jin wahala, har na tsani cikin da me cikin dan wallahi da zanga Ashraf a gabana zan iya mishi abinda ban tsammani ba.  Dan ya gama lalata min rayuwata da kuma farin cikina.
   ....... Dafani Nannah tayi , ajiyar zuciya na sauke sannan na k'akaro murmushi tare da sunkuyar da kaina. Dan yanzun ina matuƙar jin nauyinta,
      Ledar hannunta na kalla naji yawun bakina yatsinke, agwalimace a cike da yar karamar bakar ledan nan, gyara zama nayi ina jin wani mugun daɗi ya cika ni.

        Juyewa tayi a wani bowl ɗin da Ummi ta kawo min salat, ta wanko min A banɗaki ta kawo min,
      Dake ɗakin da muke VIP Ward ne, mu kaɗaine a cikin ɗakin. Tunda na amshi agwalimar nake mata wani irin kallo, sannu na fara sha kamar nasami tuwo. Har wani lumshe idanuna nake, shigowar  Abdul yasani buɗe idanuna tare da sakar masa murmushi. Dan ya zame min jiki bana magana sai murmushi, shida wata mace yaki ya matsa min naga wacece.
    Sai lekata nake ina son ganin wacece, karshe matsawa yayi.
   "Ummina ce"
Wancakalar da bowl ɗin nayi tare da dira da karfi naje na rungumeta, kuka ne ya kwace min. Rungume ni tayi tana buga bayana,  cikin mita Abdul yace.
"Yanzun dan girman Ubangiji meye haka, baki san akwai abu a tare dake bane, wallahi wannan tsalle kamar a zuciyata kika yishi. Kuma ina kishi, kuma ina taya babyna jin b...."

     Wani irin kallo na masa, dan duk abinda ake bana kaunar maganar cikin, kauda kaina nayi cikin kuka nace.
"Wallahi idan bai zo ba zubda cikin zanyi dan cikin y."

      "Wallahi kika taɓa lafiyar cikin nan sai kin kare rayuwarki cikin bakin ciki da nadama,, kuma na rantse wani abu ya faru da cikin ni dake ne, nonsense."
Haushi yasashi ficcewa,
  Kukane ya kwace min, Nannah ta maidani bakin gadon, cikin damuwa zatayi magana na dakatar da ita.
    "Nannah! Meye laifina dan nace zan zubda cikin nan, Ummina nifa taimako naje. Na gaji da ganin Nannah tana zubda hawayenta, Ummi nasan keda Nannah zaku fahimceni. Wallahi ba yadda kuke tsamani bane na same shi tunda yazo a haka me zai hana na zubda shi."

  "Waye me cikin?" Inji Ummina.
Kaina a sunkuye, na ɗago shi cikin rawan murya nace.
"Ba zakiyi fushi dani ba? Idan na gaya miki."
    "Akan me zanyi fushi dake? Ai da zanyi da ban saurareki ba kamar Yadda Abbanku yayi miki haka zan miki."

           Kallon Nannah nayi cikin kuka nace.
"Am sorry Nannah!"
Girgiza kai tayi tare da nuna min tana ji na.
        Shigowa Abdul yayi yace.
"Ummi naga kiranki."
        Bata bi tankashi ba, kallonshi nayi tare da mika mishi  hannuna, zuwa yayi tare da rikewa, ya zauna a kusadani. Daura kaina nayi a bisa kafaɗarshi kwalla nabim fuskana lumshe idanuna yayi tare da fashewa da kuka sabida hango ranar nake a idanuna, da yadda nayita rokon Ashraf yakyaleni amma abin yaci tura, haɗiye kukan nayi amma naki buɗe idanuna nace.
"Cikin..."
   Shiru nayi tare da mugun fargaba ya cika min zuciya, matse min hannuna Abdul yayi cikin kwarara min gwiwa yace.
"Faɗa Safina, kina inda baza'a kalubalance ki ba. Karki ji tsoro mun yarda da kaddara me kyau ko mara kyau muna tare dake,"

    "Na Sultan Muhammad Ashraf bin Abdullah Alhashmiyya."
   
Mikewa Nannah tayi jikinta na rawa, ta riko hannuna cikin wani yanayi, tana kallona kawai sai tasa sake hannuna tabar ɗakin baki ɗaya, tasowa Ummi tayi tazo inda nake ta kifa min mari, Abdul zai tare ta daga mishi hannu, ta kuma ki faɗa min mari,
   "Ummi"
    "Hmm" tace mishi.
Sake kifa min marin tayi na sake wata gigitacciyar kuka nace.
"Na tuba nabi Allah da manzonsa na biki."
        Iska taja sannan ta kare min kallo, tace.
"Ko yanzun na rage nauyin da yake dankare cikin zuciyata, da kika san jordan zaki me yasa baki gaya min ba, shine marin farko da na miki na kigane rashin gaya mana zaki tafi. Mari na biyu, da kika tafi da kin kira kin shaida mana halin da kike ciki da bazamuyi kasa a gwiwa ba, zamu cigaba da miki addu'a har Allah ya dawo dake ya kuma kareki dagq duk wani mugun abu. Mari na uku, shirun da kikayi bayan Abdul ya gano kina da ciki da tun lokacin kik gaya mana cikin waye, ba maƙawa Abbanku bazai fusata ba gaki kin girma amna har yanzun tunaninki irina Anas ne, shashashar banza shashashar wofi, kawai kin jefa zukatarmu cikin fargaba, kinsan yadda nake kwana kuwa, idan na tuna cikin jikinki. Ji nake kamar ana cenawa zuciyata wuta, ina son nayi barci cikin salama abu yaci tura da zaran na kwanta kukanki ne yake hanani rintsawa gani nake kina fama da ciwo a rayuwarki, sabida ke yau har sake ni Badaru yayi dan na nuna mishi ke nake so sama da kome, kin barni ina tuninan baki san waye Uban cikinki ba, tunda ance mana kin shiga yanki Syria, ashe Safinah bakinki cike yake da magana kike kallon kowa ganga ba rufe, wallahi kin ɓata min fiyye da kima, kin sani cikin zulumi. Kinsani naji na tsani kome  raina, Ya Ubangiji karka ka mata da laifin wahalar da zuciyata ya Allah ka kawo mata karshen wahalarta Allah ya shirya mana Zuri'a alummar musulmi baki ɗaya. Sakarya kawai."
     Tana gama gaya min haka taficce Abdul yabi bayanta, komawa nayi na kwanta, hawaye nabin gefen fuskana, sosai nayi kuka tare da ɗan da nasanin abinda na aikata.
           Na jima kwance ina kuka, jin kaman wani na kusadani, yasai buɗe idanuna, Anim nagani zaune idanunshi sun kaɗa jajjur.
  Tashi nayi na zauna tare da takure kaina guri guda, domin yanzun idan ba Abdul ba bana kaunar na keɓe da wani namiji.
   Tashi yaƴi yaje ya rugo kofar, ya shiga tawowa yana ɓalle botton ɗin rigarshi, ja da baya nake. Cike da tashin hankali na fara girgiza masa kai cikin kuka nace.
   "Karka min haka Anim! Wall.."

       Zame wandonshi yaƴi ya kuma tun karoni, juyawa ɗakin ya fara min kafin wani lokaci duhu ya rufe min ganina baki ɗaya, gyara wandonshi yaƴi tare da rigarshi ya share kwallarsa. Zuwa yayi ya zauna yana kallon yadda na kara kyau, kwalla ne ya zubo mishi daga idanunshi. Shafan fuskana yayi cikin raunanniyar murya.
  "Wani irin kaddara ce ta rabani dake? Me yasa cikin bai zo a kaddararmu ba yazo a kaddararki ke ɗaya, yau kwana goma barci ya kaurace min, bana jin daɗin kome sai tunaninki, matata da ta dame ni korarta nayi, Why Kyari? Ban kai irin namijin da kike buƙata bane da zaki samu. Nasan nafi wanda yayi miki wannan illar kome, dan nayi imani ina da makamin da zata cika miki kugunki ba sai kinyi tunanin wani namiji ba, sannan na miki Alkawarin zama dake har da yaron cikinki dan Ina sonsu Allah ya nufa a can zasu fito dan haka y'ay'ana ne daga wannan na cikinki har wanda zai zasu zo bayan aurenmu. Zaki haifa mim yara dozin dozin..."

     Haka yayita sambatu, karshe da ya gaji yasa kai ya ficce yana share kwalla.
          Zuwan wata nurse taga halin da nake cikine yasata fita takira Abdul. Yazo ya duba ni. Da yaga na farfaɗo ya saka ya fita.
      .........
Bansan me kuma yan gidanmu suke bukata ba dan yanzun sun tsananta fushi dani, kowa ya kaurace min. Baki ɗaya tun daga ranar da Nannah tafita bata kuma zuwa ba. Ummi ma haka, Umma ce da Nana Asma'u  suke zuwa sai dare su koma.

      Na kuma shiga damuwa fiyye da kima, abinda ban taɓa tunani ba shi yake zuwa min. Zan iyayi ba kawai dai na kosa da nagan ni a gida.
   Satina biyu aka sallame ni zuwa gidan Abdul.
           Abinda ban sani ba kuwa, tunda na faɗawa su Ummi me cikin. Nannah taje tasame Abbanmu da maganar, dan su fahimci juna. Da fari jikinsa yayi sanyi amma lokacin da shaiɗaniyar matarsa ta saka baki a maganar sai gashi an juya maganar da cewa Ummi da Nannah suka turani Jordan, karshe dai Mamie tayiwa Nannah tijara, kuma Abba bai hanata ba, karshe dai Nannah ta basu hakuri, da kuma rokon idan na haihu zata nimawa Ashraf aurena, Mamie tace.
"Bazamu bashi aurenta ba, dan aƙwai yayana da yake da mata uku shine ya nemi aurenta kuma Alhaji ya bashi ita dan ya karɓi sadakinsa. Kije idan kun gadama ku zubda cikin."

          Kan Nannah a sunkuye yake a sannu ta d'ago kanta idanunta sunyi wani irin ja. Hatta fuskarta sunyi ja murmushi tayi, sannan ta mike tace.
"Safina ta haramtawa kowani ɗa namiji sai Ashraf, ki rubuta ki kuma ajiye babu namijin da ya isa tsayawa a gaban Sarki na huɗu, Nuratu mijinki yasan gidan da nafito. Dan haka ki kiyayye harshenki, idan wani abu yasami cikin jikinta."

Dariya tasa sannan ta ficce, sai da ta isa bakin kofa. Ta juyo cikin izza tace.
"Idan wani abu yasamu jikana dake jikin Binti! Toh wallahi sai na ɗaure kaf ahalinku sai an bawa manyan kifaye namarsu ke hatta Badaru da yake Uban Binti hukuncina bazai tsallake kanshi ba, kuma koda wasa wani yayi wa Binti kallon Banza ko ya ambaci cikinta da wani kazamin suna, wallahi na rantse da Allah idan jinin sarauta ke yawo a jikina sai nasa an yanke masa harshensa ko an cire idanunsa. Idan wasa kuke ganin a gwada, zan baku nan da sati biyu kuyi yadda yayi muku, kuyi abinda ya kamaceku, zan tafi Oman kuma zan dawo dan cikin Binti."

   Fita tayi bata kuma bin takansu ba taje ta ɗauki passport ɗinta, ta bar gidan tare da kiran Abdul, ya kai yata Airport. Shi da Ummi,
  Dama Ummi ta koma gidan yayanta dake Suleja, Alhaji Ahmad Kamfut.
      Ba sosai take zuwa ba dan ma suna fushi dani, fitowa nayi daga ban ɗaki ina ɗaure da towel. Naji an bankaɗo labulen ɗakin, Siphia ce hijab ɗina na shiga ja zan saka tayi tsaki, tare da cewa.
"Aikin banza karuwar banza kawai, ba a gidana xaki haifa min shege ba wacce ta zamewa Iyayenta bakar kaddarar "

             Saka kayana nayi ban kulata ba, na cigaba da saka kayana. Ina son zan fitane ina gama shiryawa na ficce a gidan sanye da bakaken kaya, na nufi wani shagon saida magani. Dukda ina tsorace amma haka na mika musu kuɗin suka bani, juyo tare da dawowa gida, kitchen na shiga zan ɗauki ruwa, ta hanani ta hanyar ce min.
   "Nan gidan tsaftattatun mutane ne, ba masu kazamta ba. Masu zuwa aikata zina yanzun ma an dawo daga gu..."
  Tsinka mata mari nayi cikin ɓacin rai nace.
"Kin isheni, gwarani tsautsayine ke kan bansan me zai faru dake ba nan gaba bana miki fata."

Na tureta sannan na ɗauki goran ruwa na fito cikin d'aga murya tace.
"Karuwa kawai."

    Tsabar ɓacin rai ina shiga ɗakin maganin guda uku na ɓalla tare da haɗiyesu lokaci guda. Sannan na ɗauki abin maganin nasaka a cikin bahaya na sake mashi ruwa ya tafi.
   Dawowa nayi na kwanta, dukda ina kokarin ɓoye tsorona amma a haka nake bawa kaina kwarin gwiwa.
  
Barci me karfine yayi gaba dani, har na minti talatin kafin maganin ya fara aiki, wani mugun murɗane ya taso min, na buɗe idanuna dakyar, tashi nayi naga yadda jini ke malala a bakin gadon, wani masifaffen tsorone tare da mugun ciwon ciki. Wanda yana murdamin jini yana ketowa da mugun karfi, har wani fuuuu yake.

             Maida kaina nayi jikin gadon,  nasake yunkura zan tashi  wani jiri ya dawo dani tare da tsinkewar Jini tsuuuu. Sharaf na koma idanuna suna masu kafewa...............

    *Toh burinku ya cika ciki dai ya zuɓe kowa ya huta kar naji any korafi😎😏*

Wallahi ku bar tambayata daga farko😭

#MJ
#HZƘ
#Vote

Oum Muwadda......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*




GA KYAUTAR SHAFI NAN NOVELLA Ku kaɗanku...

Page.٢٣
Bansan iya adadin lokacin da na ɗauka ina barci ba, ni dai yunwar cikina da kuma wutsilniyar yaron cikina yasani na tashi, mika nayi tare da addu'ar tashi daga barci. A sannu na kebin ɗakin da kallo hannuna dafe da cikina, a karon farko da naji tausayin yaron cikin ya cika min zuciya, sunkuyar da kaina nayi ina shafa cikin a raina nake cewa.
*Kai ma kashiga cikin kundin kaddarata ko? Gashi tun baka zo duniya ba na fara wahalar da rayuwarka daga wannan sai wannan*

D'ago kaina nayi cikin nutsuwa ina karewa ɗakin kallo, kome na cikin ɗakin farine. Hatta kayan jikina fari ne, *Waye ya sauya min kayana?"*
Tambayar da ban same amsarta kenan, murɗa hannun kofar akayi. Da sauri na ɗago kaina ina jiran shigowar wanda yayi nasaran kwamusheni.
Turo kofar yayi ɗan karamin bakinshi ɗauke da sallama. Mikewa nayi jikina na rawa, haka ma bakina ya kasa furta kome, sai nuna shi nake da yatsa kamar mareniya nace.
"Anim Kamil Matawalle! Meye nayi maka ne da zafi? Wa...."

"Anna shigo min da abincin."
Take wata baturiya ta turo abincin a keke. Raina a ɓace tsiwa nacina nace.
"Uwar me na maka da zaka satoni? Nd ina nan?"
Bangaje shi nayi na fita banga hanya ba, dan naga kamar hotel ne. Zan iya cewa na manta da ciki a jikina na zura a guje, nayita ratsa kofifi da manyan faloka har na sauko kasa, ganin kofar karshe yasani karawa da gudu, ina tura kofar na zaro idanuna. Fisgoni yayi baya.na kwace kaina na fasa ihu nayi tare da zubewa lokaci guda na fashe da kuka me tsanani. Ina hango inda nake wani bakin cikine ya kamani. Na tun kari kofar yayi maza yasha gabana cikin tausassiyar murya yace.
"Pls ki saurareni!"
D'ago jajjayen idanuna nayi, a sannun na lumshesu. Nace,
"Anim! Why me? Nayi chanchanci haka daga gareku ko? Me yasa duk wata damuwa sai nice zaku ɗaurawa, a bisa tsautsayi na tafi can kaddara rubta dani, yau gashi dan son kanka karabani da iyayena, kai ma jikin nawa kake bukata ko? Ince jikine yake ruɗarku kuke ganin wani abin arzikine, ya ɗauki nashi kason kaina muje na baka, tunda haka Allah yayi ni kowani namiji ya ɗibo dattinsa ya zuba a kaina, muje na baka."
Tunkara shi nayi raina a ɓace, sai masifa nake.
"Kyari!!! Ni..."
"Me zaka gaya? Ehhe meye zaka gaya min?
"Amma ya dace ki saurareni" ya faɗa da sigar lallashi.
"Wallahi Allah sai yasaka min mugu azzalumi, macuci."
"I heard that daga bakin Rabi'atu."
Tsaki nayi na juya zan koma ɗakin, yana biye dani sau biyu ina ɓata kafin na amince yayi min jagora zuwa ɗakin, ina shiga na fara niman wayata nasameta a kasar pillow, ɗauƙa nayi naganta a kashe, ina kunna wayar naga babu service, fita nayi na koma har hanyar ɗazun babu service babu alamarshi.

"Ai bazaki taɓa samun service ba sai ini ne naso ki samu, ki bani."

"In baka wata uwar? Lallai Anim baka da kunya da mutunci nice zan baka kain..."

"Ke ni bana son hauka! Ki bani lokacinki muyi magana na gaskiya, Step Mother ɗinki ce taje gidanmu ta faɗawa Innata, kome ina shirin na tambayeki gaskiya na kuma jin irin haka a bakik abokan aikinmu, nifa ban taɓa kallonki da sigar sha'awa ba sabida nima Ubane ina da nawa yaran bazan so.."

"Don Allah get out" na

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment