Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zargin Mamie da Badar, akan ɓatar Binti. Kuma ta tafi  kome zai faru(😎😏 Mamie mek sho yu run)
  
      Sai da ya gama Addu'a sannan ya kalle Ummi cikin tausayawa yace.
"Mariamah kukan zuci kike? Karki zubda kwallarki dayawa a duk inda Safinah take Insha Allah yau zuwa gobe zata dawo gareku, da Allah muka dogara ba da wani ba, Allah da kanshi yace alkur'ani waraka ce."
   Tunda Safinah ta ɓata har yau Ummi bata zubda kwallarta ba, sai dai kawai zata zauna tayi ta sauke a jiyar zuciya, kimanin sati uku zuwa huɗu kenan.
             Alkur'ani aka raba irin bugun sokoton nan. Dan a cikin jakarsa yake, ya bawa kowa falle uku-uku, sannan ya fara da fatiha.....

          ***
   Tunda Mamie ta isa garin Abuja tasa Abba ya kira kowa, cikin ruwan sanyi ta gabatar da abinda zatayi sannan ta fidda takarda tace.
"Aranar uku ga watan biyar, Nuratu kinyi waya da wannan number sau uku, ana saura sati Safina zata ɓata.  Bayan kwana biyu acc ɗinki na bankin Access sun amshi naira dubu ɗari shida, daga wata acc ɗin, bayan sace Safina. Ranar goma ga watan shida kunyi waya da wannan number bar aka kuma turo miki da naira dubu ɗari bakwai, sannan an kiraki ne daga can tsakiyar ruwa atlanta ocean, ranar  ashirin da ɗaya ga watan shida an kuma kiranki, tabbas kinyi kuskure. Waye shi?"

     Zuba ke karyowa Mamie sosai duk yadda taso rike fitsarinta kasawa taƴi, dan ta jika inda take zaune jagwab
     ***
       Yana shigowa ya ganni na kifa kaina da jikin gadon yana ɗago fuskana yaga na bishi sharaf na zube a jikinsa, ga bakina ya koma gefe. Yawu na fita me yauki haɗe da jini.
   "Safeenah" ya shiga girgizani. Ganin bana motsi yasashi ɗaukata dukda nauyin da na kara. Haka bai dame shi ba ya fita dani da sauri.  Kamar zai tashi sama, filin da aka tanada dan saukar privet jet ya nufa dani tare da kiran masu tuka jirgin. Suka taimaka mishi aka sani a ciki sannan ya kallesu yace.
"Ku tabbatar da kun kaita Abuja akan lokaci, idan wani abu ya sameta kuyi kuka da kanku."

    "Yes sir!" suka ce mishi, tare da fara tada jirgin, sumbrta Goshena yayi,  sannan yace.
"Kece sila! Ina sonki da zuciya ɗaya kika maida min so cuta. Allah ya baki lafiya zanzo na aureki."
      Rufe kofar yayi, tare da juya musu baya, har suka tadda jirgin har suka tashi sama.
    D'aga kanshi yayi yana tare da bin jirgin da ido har suka ɓaccewa ganinsa. Tafiyar awa biyu ya fitar damu yankin tekun.
       A cikin awa uku da rabi suka sadani ga wata karamar asibitia cikin abujar gudun kar a kamasu yasa suka rufe min fuskana, sai da suka gama kome sannan suka bar asibitin. Dr Muhsin shine yazo kaina domin dubani. Dake yaga sun rufe min fuska, kamar bazai buɗe ba, sai wani tunani yazo masa ya ɗaga mayafin.
"Safeena!!!"
Ya ambata da karfi, gumine ya shiga karyo masa,  wayarsa ya lalluba ya shiga niman Abdul cikin tashin hankali ya same Abdul yace.
"Duk inda kake ka tawo asibitin Alheri."
   Bai barshi yayi magana ba ya datse kiran, Abdul kuwa yana can, Nannah tana yanta Abba da Mamie.
           ..... Bayan minti ashirin ya iso, tsananin faɗuwar gaban da yake ciki, ya hanashi fitowa. A sannu ya tattaro yar jarumtarsa ya fito daga motar tare da rufewa ya nufi cikin asibitin, kiran layin Dr Muhsin yayi yana ɗauka yafito daga ɗakin da aka sakani, a sannu ya isa ɗakin. Tare da kura min ido, zuwa yayi bakin gadon ya ɗaga lulluɓen fuskana. Ji yayi kamar zai faɗi Dr Muhsin ya tallafeshi, kamar yaro karami yace.
"Da gaske Safinatu ce!"
"Be a Man! My frnd karka sa nace ka rako maza mana, ka tsaya mu taimaketa, yanzun nake son ɗiban jininta aje a gwada ko akwai sugar sai musan abinyi dan kaga yadda ta kumbura za a iya rasa Uwar ko Babyn."

   Fita Dr yayi shi kuma yaja kujeran ya zauna,  yana kallon kumburarren fuskana, har dr muhsin ya shifo tare da nurse da kuma, da bututun shakar iska, wato oxygen aka samin sannan ya bada dama aka ɗibe jinina, suka fita zuwa lab, can bayan wani lokaci suka dawo aka samin, mika mishi report ɗin yayi cikin lallashe yace.
"Bata da matsalar kome sai kumburin da tayi, zuwa an jima zamu kaita ɗakin gwajin zuciya. Sannan yana da kyau kakira mutane gida ka gaya musu."

   Wayarsa ya ɗauka ya kira Ummi da suke tsaka da addu'a. Ya sanar mata,
    Sannan ya kuma kiran Nannah ya gaya mata, tuni ta kyalesu Mamie wacce aka musu ɗaurin wulaƙanci aka watsa a bayan kanta.
                ........
   Lokacin da Nannah ta gama zayyanowa Mamie abinda tasamu akanta, cikin rawan jiki ta amsa. Ba tare da jin kume ba Nannah tasa aka tafida ita har bayan gidan aƙa fara tsoma kanta cikin ruwan swimming pool. Da taga zata mutu shine ta buɗi baki zatayi magana Abdul ya kira Nannah.
       Kota kanta bata bi ba, tafito inda tasa drvn gidan ya kawota asibitin.

     Kafin awa ɗaya yan uwana da dangina sun cika asibitin, kowa yana min fatan samin lafiya, sun samu cikin ya fara kuzari nice ma dai ban farka ba. Sai da na share awa uku biyar cur sannan na farka, tunda na farka nake kare musu kallo dan gani nake kamar mafarki nake, ina son magana harshena yaƴi min nauyi, dan haka na sake lumshe idanuna barci yayi gaba dani.
     Ban kuma farkawa ba, sai washi gari da misalin sha ɗaya. Buɗe idanuna nayi naga Ummi da Nannah, hannuna ɗaya na kai kan cikina  naji yana kicking yadda ya dace. Murmushi na sake tare da cewa.
"Babynsu Nannah"
         Kura min ido Ummi tayi taga nasake magana, tasowa tayi sannan tace.
"Kina son wani abu ne bama jin abinda kike cewa."
      "Ummi baku fahimtar me nake cewa kenan."
      Nan ma Nannah tazo tace basu fahimci nake cewa ba. Saka hannuna nayi na shafa fuskana naji bakina ya koma gefe. Kuka nake son yi amma na kasa, da karfi na rufe idanu na, na shiga sauke ajiyar zuciya. Ina jin Ummi tana kiran Abdul tare da gaya mishi halin da nake ciki.
        Barcin dole ne yayi gaba dani, dan ban farka ba. Sai karfe biyu ina buɗe idanu na, sai akan Anim. Mugu ɗan masara ana goyaka, kana karya uwarka. Kukan da ban samu damar yi bane ya kwace min na shiga fisge-fisge saura kiris na faɗo daga gadon Abdul da Nannah suka tare ni, fita ABDUL yayi  sai gashi tare da Dr Muhsin. Alluran barci suka min Idanuna na kan Anim.
      Ajiyar zuciya Nannah ta sauke, tare da cewa.
"Abdul ko za a cire abin cikine wannan wahalar tayi yawa, kullum babu sassauci daga wannan sai wannan, gabaki ɗaƴa Safinah ta fita hayacinta."

     "Ai matsalar shine cikin bai cika bakwai ba, amma da zaran ya cika bakwai insha Allah zamu cire babyn, dan girman cikin ma yana rinjayarta." Inji Abdul,

    "Ni a ganina ku bar cikin ya shiga watansa in yaso sai a cire mata, dan nima na karaya da alamarin Safinah, na yau daban na gobe daban."

         "Kuma ana cire mata yaron zan bawa Alhaji Zubair yayan Nuratu it....

          👏👏👏
_A cikin duniyar nan kowa ya tara abin fada, amma kalilan suke iya ajiye nasu, ba sauki rungumar Alamari me wahala ga karamar irina, Hidimar miji da Hidimar yara.... Ba abu me sauki bane ɗaukar nauyin da bai zame maka tilas ba, idan kiɗa ya sauya dole rawa ya sauya....._


Uom Muwaddah...
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
_Na sadaukarda wannan shafin ga Iyaye mata masu fafutukar kare Yaransu....A cikinsu Har da Mahaifiyata Allah ya jikanki da Rahama👏_
Page.٢٨- 28

" Ban tab'a karo da mutum mara mutunci irinka ba, banza mugu fasiki, mujirimi kawai. Kafit."
Maganar da ban karasa ba kenan na haɗiyen dole, sakamakon jin bakin d'an iska da nayi cikin nawa, duka nayita masa. Tare da ture shi da karfin tsiya, na kuma tofa mishi yawunsa a fuska, kazamin banza shafo yawun yaƴi, tare da lashewa har yana lumshe idanunshi, girgiza kai yayi da takaici ya kamani. Bansan lokacin da na ɗauki kwallo goriba na kwalle goshinsa, kam uban bala'a alkur'an sai akan idanun Abba. Tsabar na tsorata garin na yunkura zan mike sai da naji bayana ya amsa, tare da zuban abu a jikina.
"Safinah! Rashin mutuncinku har ya kai ya taɓa mutumin da yake jeka ka dawo akanki, yau zaki gaya musu."
Dakyar na mike dan naga yana gun Anim wanda goshinsa ya fashe, zasu fita ni kuma na shige gurin Ummi, ga baki ɗaya na birkice domin dakyar nake ɗaga kafana, ga cikin da yawo kasa baki daya.
"Ummi!"
Na kwala mata kira da karfi sannan na durkushe a gun, sabida jikina wani irin rawa yake, har cikin kashin jikina rawa suke. Ga zufan da yake karyo min haɗe da wani mugun sanyi me shiga jikin mutum.

"Safinah! Haihuwar ce."
Gyaɗa mata kai nayi cike da azabar da yake addabar gangan jikina tare da yin dagadaga da ruhina, duk sai ta ruɗe kamar bata taɓa haihuwa ba, komawa ban ɗaki tayi ta ɗauko kujera ɗan tsuguno, ta nuna min yadda zan ɗaura hannuna a kai tafita da sauri, sai side ɗin Umma.
"Amnah zoki taimake ni Safinah ina ga haihuwa c.."
Ai Ummi bata gama maganarta ba Umma ta fita da sauri, suka nufo side ɗin Ummi, umma tace.
"Har cikin yakai haihu ne?"
"Eh toh ina dai tunanin bakwai kenan."
Suna shigowa kukan ɗan karamin jariri na musu maraba da zuwa, da sauri Ummi ta ɗauko hijab ɗinta ta mikawa Umma ta saka jariri a kai, ta shiga niman inda kwalin rezanta yake. Tana samu ina sake wani nishi tare da cewa.
"Ummina ki yafe min"
"Iƙon Allah har biyu? Sannu da aiki Safina."
Inji Umma yanke cibiyar ɗayan akayi dan basu samu hankalinsu da su fahimci gender yaran, yanke ɗaya cibin sukayi, kara na saka sannan na zuɓe a gun ina tauna harshena, ranar Ummi tashiga mugun tashin hankali, Umma ce tayi maza ɗauki wani. Karamin roba ta cusa min a bakina, tare da nima min doguwar riga suka saka min, hawaye ke zuba a idanun Ummi, kota kan yaran basu bi ba.
"Maryam! Babu lokaci kira mana Dudu."
Jikinta na rawa ta fara niman wayarta, wadda yake kan dress mirror, amma sam hankalinta bai je gun ba. Asalima birkicewa tayi sabida ganin jinin dake zuba. Umma ce ta gani bata cewa Ummi kome ba, ta ja hannunta ta zaunarda ita a kusada jariran, sannan ta kira Abdul.
"Maza kazo Safinah ta haihu, kuma tayi sarkewar hakori muna cikin tashin hankali."
"Gani nan a cikin gidan."

Kashe wayar tayi, sannan ta kalle Ummi tace.
"Karki manta Allah yana tare dake karki bari Safina taga karayarki akan idanunki, yin haka shi zai ta shiga sabo.."
"Ummi zaman me kuke yi baku san rayuwarta na cikin hatsari ba, Ummi ki jida yaran ki yanke musu cibiyar tunda sun tawo tare, sannan ki naɗesu kufito Zakari ya kawo ku dan ɗakin yan bakwaini za a kai su."
. Sa hannunshi yayi ya cinciɓeni tare da fitowa waje dani, Umma na bin bayanshi, ganin ya ɗaukoni yasa Zakari ya buɗe masa motar yasakani, shiga Bayan Umma tayi, shi kuma ya zagaya zai shiga mazaunin drve. Abba ya shake mishi wuya, tare da kifa mishi mari.
"Abba don Allah ka bari na kaita asibiti, rayuwarta na cikin hatsari."
"Idan ta mutu uwarka ce? Ni zaku renawa hankali ku haifa min shege a gidana, dan."

"Abba!!!"
Ya kirashi da karfe, cikin ɓacin rai ya kwace rigar yace..
"Wallahi idan ban takeka da mota ba Allah ya tsine min Albarka."
Ganin da gaske yake Ummi ta daka mishi tsawa.
"Kul!! Bawan Allah, muje ka rabu dashi Allah ya kyauta."
Gabar motar ta shiga, dole Abba ya matsa, Abdul ya fita sai huci yake, tare da dukar kan motar, Har suka isa asibitin. Dauka na yayi, tare da shiga ciki dani, su Ummi suka rufa mishi baya.
Yana shiga nurse da likitoti suka, tare shi aka shige dani ciki. Sannan ya faɗawa wata nurse ta amshi yaran, ta wucce dasu ɗakin kula dasu, ni kuwa suka rufa min dan cito rayuwata.
Idan ka rayu babu jarabta a rayuwa ka binciki imaninka, Aslhamdulillah nagodewa Allah da yake jarabta rayuwata, kuma bana bakin ciki da haka sai godiyar Ubangiji. Da nake ba dare ba rana.
........
"Hmm kagani ko! Ai na gaya maka Maryam ta rabaka da yaranka musaman wancar karuwar, tunda ai ba yau ta fara cikin ba. Sau nawa tana zubda cikin a ɓoye daga ita sai wancar munafukar balarabiy..."
Wani mugun kallo ya bita dashi wanda yasata haɗiye maganarta, cikin fushi da ɓacin rai yace.
"Balarabiyar mutum ce! Daga cikin mutanen kirki ita tankar waliyiyya ce, domin zuciyarta takai kololuwar kyautatawa, duk abinda nake bata min magana sabida dalilai guda biyu ne. Dalili na farko tabani dukiyarta ina kuma cin gajiyarta, ko sau ɗaya bata taɓa saka idanunta akai ba, Dalili na biyu sabida, sadaukar da rayuwata da nayi sabida ita, wannan dalilin Yasa Gimbiya Asma'u bata da kataɓus akaina, dan tana gudun kar tamin magana nace dan taga ta tallafi rayuwata shi yasa tayi min magana, ban taɓa jin kunya a rayuwata irin na yau ba, da Abdullahi yace zai take ni da mota, sabida yar uwansa, idan na cigaba da tsawallawa. Wata rana zuciya bata da kashi zasu tanka min, dan ma Allah ya basu jarumar Uwa, wacce duk abinda nayi mata bata duba a bisa laifi sai dai ajizancin ɗan Adam."

"Kenan.."
"Don Allah fita ki bani guri bana son damuwa gabaki ɗaya kin chaxa min kai da wanne zanji da naki ko da na yarana, zaki iƴa fita."
Ya nuna mata hanya, fuuuuu tayi waje.
***
Sun kai awa biyu kafin likitotin suka fito, babban cikinsu wanda zai kai kimanin shekaru arba'in ya fara fitowa cikin ɓacin rai yace.
"Dr Kyari! Sam baku kyauta ba, wani irin abune haka, ban da Allah ya takaita wallahi mutuwa zatayi, kun bar mace a cikin mugun yanayi, ina ma mijinta yake?."
Shiru duk sukayi, "Oh sorry bansan ya mutu ba, kunga kodan tunanin mijinta zaisata cikin damuwa, don Allah a kiyayye gaba."
Gyaɗa kai sukayi kaman wasu dolaye, suna tsaye aka turo ni zuwa ɗakin hutu, shafa kaina Ummi tayi cikin juriya tace.
"Allah ya baki lafiya ya shirya zuri'arki."
"Amin" Umma da Abdul suka ce, tafiya Abdul yayi gun biyan kuɗi, aka ce masa Dr Hameed Zaki Katagum ya biya, kome har na yaran sannan zuwa an jima za a maidata ɗakin VIP. Mamaki ne ya kamashi, dan yasan Dr Hameed Zaki Katagum, mutum ne da babu abinda yasa a gaba sai aikinshi baya shiga rayuwar kowa, sannan baƴa kyautatawa kowa, ga tsananin masifa, kowa shayinsa yake sabida mutum neda yatsaya akan gaskiyarsa, baya karya duk abinda ya faɗa iya gaskiyar ce. Basi jima da rabuwa da matarsa, Zuwariyya ba, sabida ta zubda masa cikinsa dan tana shayarwa a cikin asibitin yayi mata tijara, Murmushi Abdul yayi sannan yace.
"Mungode."
Ya bar gurin, dawowa gun Ummi ya faɗa musu abinda ke faru, godiya sukayi tare da sanya mashi albarka.
"Ummi bari naje gida na dawo."
"Allah ya tsare a dawo lafiya." suka ce mishi, da sauri ya tafi.
........
Sophia ta gama abincin rana tana saka kayanta ya shigo gidan, kallon jikinsa tayi a tsorace tace.
"Baby lafiya ? Waye yaƴo a tsari."
"Kwantar da hankalinki Honey, Feener muka kai asibiti ta haihu, amma ba lafiya, babys ɗin suna ɗakin kula da jarirai."
A ruɗe ta kalle shi, "Nikam bari nasa kaya ka kaini."
Ganin yadda duk ta ruɗe yasashi riko hannunta yace.
"Honey! Tana lafiƴa fa muje ki yi min wanka, sannan wai yaushe zaki fara sallah ne na gaji wallahi bayana da marana daurewa nake kawai amma..."
Rufe mishi baki tayi da nata, sannan ta zare towel ɗin ya faɗi kasa, shigewa jikinshi taƴi tare da ɓalle botirin rigarsa, daga nan suka zube gado,
( toh ina zan iya wannan kallon🏃🏃🏃)
........ Bayan wani lokaci suna rungume da juna, sai mita take masa shi kuma yana, shafa bayanta.
"Baby jikina ciwo! Yake min."
"Meye yasa kikayi tsarin iyali? Kuma da zakiyi baki gaya min ba ko baki san zan fiki sanin wani tsari zaki yi ba, gashi ina zaman lafiƴa kin janyo min duƙ wata sai kinyi jini sau uku, plss duk abinda zakiyi ki faɗa min, sabida ni likitane, kuma ina da hanyoyin da zan kiyayye dan ɗauƙar ciki, nima kuma ina son ki huta."
"Kayi hakuri bazan bazan kuma ba."ta faɗa mishi a raunane, tasa mijinta yana da yanayi da mabukatar maza kuma tasan hakuri yake mata, in wani namijine tuni ya tsunduma bin matan layi, tare sukayi wanka sannan suka fito.
Ta ɗauki babban flask ɗinta ta cika da ruwan zafi, kana ta haɗa da manyan kofina guda biyu, sai abincin da tayi tasan bazai ci wani abu a halin yanzun ba. Ta haɗa kome sannan suka fita, can gida yaje ya ɗauki kayanmu a cikin wata karamar akwati ya fito daga gidan.

A bakin get ya haɗu dasu Batul da Khalila, da kuma Khalil ya gaya musu haihuwa,, Batul na shiga cikin gida ta kira Nanah Asma'u ta gaya mata na haihu.
........
Suna isa ana canza min ɗaki, sannan, suka nufi ɗakin. Har dasu Ummi, ajiye kayan yayi zai fita sai ga Masijan ofishin Dr H.Z Katagum, ya kawo kaya niƙi niki, ya shiga dashi, sannan yafita ya sake shigowa da wasu kayan. Bakinsu Ummi a buɗe suke kallon wannan abin mamaki, yana gama shigo da kayan yace.
"Inji Dr Zaki Katagum."
"Mun gode."
Yana fita, Umma ta shiga buɗe kayan. Ledar farko kayan tea ne danginsu Madara ovalti, milo bournvita, cornflas, goldenmo, sugar me iyali, garin coffe, leda na biyun, kuma madaran jarirai ce, da pampas, wipes sai set na kayan sanyi, da kuma kayan jarirai irinsu Overolly, pink nd purple, da kuma wasu yan kananun safarsu. Leda na uku gashashiyar nama ce, wacce taji yankankun kabeje da albasa da tumatir gashi yasha yaji.(😎😏 saura naga cutar kwadayinku ya tashi ni dakune )

....... Mamaki ne ya kamasu Dole Abdul ya fita, zuwa ofishinsa. Koda yaje yasamu baya nan, dole ya dawo. Yana shiga yasami Nanah Asma'u tazo.
"Abban Affan muje ka nuna min jariran."
Karban kayan yayi suka tafi, suna shiga Nurse ɗin da take kula dasu. Tace,
"Dr Zaki yazo ya duba yaran sannan yace za a kawo kayansu,"
Mika mata kayan yayi, ta amsa, sannan ta mika musu safar hannu, ta kaisu har inda yaran suke, kura musu ido yayi an mannasu da juna, suna jin ɗumin junansu. Abin gwanin sha''awa, karewa yaran kallo Asma'u tayi, sannan tace.
"Dukda bansan Babansu ba Dudu yaran nan kamar an raba gardama ne. Domin babu abinda suka ɗauƙa na Didi, hatta farcensu irin ɗaya ne da na Nannah, duba sajensu mana."

Juyawa yaƴi ya kalle nurse ɗin yace .
"Maza ne ko mata?"
Murmushi taƴi sannan tace.
"Dukkansu Matane, Dr ban taɓa karɓan yara kyawawa irinsu ba, kyansu kamar yaran laraba"

Me karatu kayi nazarin kyau irin na Ashraf, asalin balarabe ne dan haka kyan yaran ya zarce ayi bayaninshi a rubuci kalleshi da mahangarka, yaran sun haɗu wai dama bakwaini ne........


Oum Muwadda.....👏👏👏
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

Page.٢٧

   "Kayi hakuri Baby bazan kuma ba insha Allah zan bata hakuri Baby ka maidani ɗakina. Bazan kara ba ka maidani ɗakina kaji baby." ta karshe maganar cikin kuka, jawota yayi gabanshi yana kallon fuskarta a sannu jikinshi na kara sanyi wani irin kewarta yake ji,  d'ago haɓɓarta yayi suna kallon cikin idanun juya yace.
"Ina jin tsoron kar na mai dake ki hanani aikata alkhai."
   Rufe masa bakinshi tayi da hannuta  tare da girgiza kanta.
"Wallahi tallahi bilahi Azim, bazan cuce koda kiyashi ka kawo cikin gidan da sunan naka, bazan taɓa cutar dashi ba dan Allah ka yarda dani."

    "Toh irin wannan dadumar kin manta a gidan surukaina nake, don Allah sake ni kafin ki kayardani kin min fyaɗe."
       Murmushi tayi tare da kifa kanta  a kirjinta, tace.
"Baby I miss u"
"Ke dai faɗi gaskiya, daga ganin ɗ'an Ummi kanin Didi Feener kin gigice" duka ta kai mishi irinta masoya tace.
"Sai na gayawa Didi kana gulmanta,"
               Raɗa mata abu yayi a kunne, ta ɗago kanta da sauri tana kallon fuskarshi, gyaɗa kanta tayi tare da ɗaura kanta a tafukan hannunshi. Janye hannunsa yayi ya riko hannunta suka fita, har sun isa gun motarsa.
"Affan fa?"
         "Kyaleshi Baby muje kaji."
     Murmushi me sauti yayi sannan yace.
"Ban gane ba sai wani rawan jiki kike, ina tsoron karki cinye ni ɗanye."
              Dariya tayi sannan tace.
"Ai in danye ne da sauki, if i catch."
           "Yarinya ki bi a hankali sau nawa ina win ɗin ki yau ma muje a sake gwada."

"Wayyo Allah ni banja muyi haka da kai ba."
Haka suka isa gidansu sosai suka shirya tsakanin miji da mata ya tabbata.
***
*SAUDI*

"Abisa hujjojin da kotu ta haɗa, mun sallame Sultan Ashraf akan zargin da muke masa, tare da bashi hakuri sai kuma muna gargaɗinsa da kar yakuma yin shiru akan gaskiyarsa, dan haka kotu ta ɗaure shi har na tsawon wata goma babu tara dan ya zama gargaɗi da izina ga mutane irinshi, sannan a gefe guda Mun mika Marhum ga Hukumar kasarshi kamar yadda jami'in jakadar Kasar Jordan ya bukata, alkali na gama bayanin ya mike, nan mutanen cikin kotun suka ce kotuuuuu.
***
Nigeria.
Yau aka sallame ni a asibiti bansan ya akayi ba, sai ganin Dudu naƴi ya wucce damu gidan Abba, kallon Ummi nayi itama ranta a ɓace yake, kana ganinta kasan ranta yakai kololuwar ɓaci, lumshe idanunta tayi taki magana. Kwantar da kaina nayi a kafadarta a hankali kwalla ya shiga sauko min, daga idanuna riko hannuna tayi cikin rarrashi tace.
"Kiyi

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment