Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mungode da ka sauraremu. Allah yasa mudace "
    
   "Nine da godiya."
  Mikewa sukayi sannan suka fita, a waje suka haɗu dashi, kowa ya ɗauke mishi wuta, shima ko a jikinshi ya shige.
       ......
Mikawa Ummi Sajida nayi na mike zan shiga ban ɗaki naji wayata na tsiwa. Ban ɗakin na shiga sannan na fito banbi takan wayar ba na ɗauki Husnah wacce take lashe bakinta, murmushi nayi cikin jin daɗi nace.
"Ummi! Aami ta cika niman rigima kalli yadda take lashe bakinta, kamar bata ci kome ba."
      Dariya tayi sannan tace.
"Aikinga ita Aani bata da rigimarta, ga hakuri."
        
   "Hmm! Allah yasa karsu ɗauki miskilanci wancan shashashan uba..."
D'im naji an kaiwa bakina duka, da sauri na ɗago kaina ina dafe bakina cikin rawan murya nace.
"Ummi bafa da Dr nake ba, wancan yaro."
   Sake buge min bakina tayi, na rike kaman zanyi kuka nace.
"Ummi sabida Ashraf."
   Wani dukan takawo min na kauce, cikin jin haushi tace.
"Uban yaranki kike kira da shashasha? Har da cewa yaron can ga shaidan yarontaka a hannunki, ima yarone sai ki girmama shi kodan yaranshi, balle."

       Shiru tayi kodan girman maganar da zai fito bakinta,
Ko yayya kika ga ɗ'a namiji ki girmama alamarinsa, da kike kiranshi yaro ai sa'an Abdul ne kuma kinga Abdul yana da mata me yasa baki taɓa kiran Abdul da Yaro ba sai Uban y'ay'anki! Bana son reni, ba mamaki Allah ya nuna miki iyakarki ne dan renashi da kike yi, ko ba haka ba?"
     Abunka da sokuwa(😹) sai na shiga bata labarin artabun da mukayi, har lokacin da abin ya faru da kuma dawowa na gida.

       Cikin tausayawa ta kalle ni sannan ta kalle yaran, tayi murmushi sannan tace.
"Lokacin da kika ki maganar auren, kowa yayi mamaki, amna da kika ce karatu zaki, sai naji sam ban amince da tafiyarki ba. Dukda haka na kasa dakatar dake, har Abbanku na gayawa bana son tafiyar dan jikina na bani babu alkhairi."
   Siraran kwalla suka sauko mata, gogesi tayi tare da sumbatar goshin takwaranta. Sannan tace.
"Da nayi yunkurin hanaki, ba mamaki rabonsu ya zama ajalina, tunda Allah ya nufa sai sun zo ɗin toh babu wanda ya isa dakatar da ikon Allah,  naji daɗi da taimako kikayi. Allah yasa hakan ya zame miki izina da duk masu taurinkai irin naki. Sannan kafin Nannah ta tafi taga ya min Baban yaran yana can a saudiya a rufe."

         A razane na dago kaina inakallonta, jikina sai rawa yake. Nace,.
"Ummi! Me ya faru da Sultan ɗin? Kinsan sabida ni yayi murabus. Innalillahi"

Kuka ne ya kwace min, ba kome yasani kuka ba sai makomar yarana, ubansu a rufe.
     Ta gaya min dalili rufe shi, bayan naci kuka na koshi nace.
"Zai rina! Dan mutum ne me tsananin ko in kula, ga wani miskilancin da yake ji dashi Ummi Wallahi maganar da kika ga Ashraf yayita sosai ki duba girman Alamarin, maganarshi bata wucce harrufa huɗu, itama ɗin dan ta zama dole ce. Ban taɓa ganin miskili irinshi ba, zan iya cewa idan da zaki matse shi bai sai meke faru a cikin masarautar ba, shi yasa suka kayi amfani da yardaddenshi ya zuba mishi makaman."

         "Allah ya kyauta! Wallahi na tausya mishi, yaro karami a cikin miyagu."
     "Hm! Ummi kenan wallahi na tausayawa matar da zata aureshi dan wallahi makiyanshi sunyi nisa kiyayyarsu akanshi babu sauki zasu iya zubda jinin kowa dan suga bayanshi, kuma abinda zan iya cewa nayi shine ankarar dashi kurakuranshi, da ace har yanzun yana sarkine da na tunatar dashi matan da suke a wulakance a cikin masarautarshi, Ummi kinsan abinda na fahimta ga mulki ga dukiya amma sun gaza samin nutsuwa dashi, gani suke kamar ya hanasu watayawa. Shi yasa sukayita kokarin sai sunga bayanshi, Allah yana kareshi. Akan shi naji na tsani mulki da sha aninta bana kaunar milki, Alhamdulillah ina cikin farin ciki da yaranshi matane kuma basu da gurbi a cikin masarautar da mulkin."

     "Toh Allah ya tsare! Amma abun da ɗaure kai."
     "Indai akan mulki da dukiya ce babu ɗaure kai dan kowa yasamu rana zai baza shanyarsa son ranshi."

           Munyi masa fatan ya cinye wa'adinsa, lafiya.
        ***
*SAUDI*
Mika mika mishi  iPad ɗin Lawyer yayi cikin girmamawa, amsa yayi, ya kalli yaran cikin wani masifafan soyayyarsu.
   "Har ta haihu??"
   
"Kamar yadda na gaya maka yarinyar ta fuskanci matsala a rayuwarta, sannan Fahad ya tabbatar min akwai mutane biyu da suke bibiyar rayuwarta, d'aya likitane. Babu sharri a tare dashi ɗaya kuma Fahad yayi bincike akanshi shi yasaceta, lokacin da cikin yaran. A halin yanzun bata fita sabida gudun kar ya kuma saceta."

           Dunkule hannunshi yayi idanunshi sunyi wani mugun ja ya kuma buɗesu, sannan yace.
"A tura  masu tsaro"

     "Yallaɓai! Ghaniy.."
  Yadda ya ɗago kanshi sai da yabawa lawyer tsoro dan har jini jini yake ganin ya kwanta akasan idanunshi,
         "Baiwata da Yarana! Kome ya faru kaine. Saura wata takwas na fito."
  Yana gama faɗar haka ya mike,
       Har ya isa bakin kofa,
   Cikin yaren Urdu yayi magana(Jama'a me Ashraf yake nufi da canza yare😎😒😏 Gulmar ma baza a barni nayo cikin salama ba)
Shi kuma Lawyer yace
             "Toh! Yallaɓai"
   
Lawyer na komawa masaukinshi ya ciro laptop ɗin Ashraf ya fara aiki
       ***
Yau yarana watansu Uku, wanda yayi daidai ɓarin da matar dudu. Tayi, dukda Ummi ta hanani zuwa ji nayi hankalina ya tashi, dole na shirya yaran na saka jakar goyon baby na Sajida Wacce nake kira da Aanih, sai Husnah wacce nake kira da Aamih. Aanih a gaba Aamih a baya, sannan na fito tare da bawa Zakari daman ya kaimu asibitin kamar zaiyi kokari sai ya fasa muka fita,
      Muna barin cikin gidanmu,  wata jibgegiyar mota tana rufa mana, kamar zasu bi takanmu Zakari ya matsa musu yana mita, munzo traffic, sai ga wata mota tazo da mugun gudu, zata shege damu. Abin mamaki sai gani mukayi wata babbar tanka tabi ta kanta.
Ai ganin haka yasani fasa ihu, tare da kamkame jikina, karan jiniyar yan sanda da fire service,
  Da sauri nasakai zan fita naga an shigo tare da ture Zakari gefe, akayi baya da motar, zanyi magana dani har zakari aka watsa mana hoda.
    "Eh kome ya kammala karkashin jagorancin D28 Code 29 grps"
   Iya abinda na iyaji kenan, sannan wani kafirin barci yayi awon gaba dani.

         ***
Fitowar Dr kenan daga Asibiti, zai shiga motarshi,,  sai ji yayi an Duke keyarshi da abu, durkushewa yayi tare da rike keyar, sai ganin mutumin da ya duke shi, ya faɗi a kasa, ko shurawa. Sakamakon harbin da aka mishi ta keya har sai da yafito goshinsa, lumshe idanunshi yayi sannnan ya yanki jiki ya faɗi a gurin.

        ***
Buɗe idanuna nayi a hankali na sauke akan Ummi wacce nake hango ɓacin rai a idanunta, mikewa nayi da hanzari kaina yayi mugun sarawa dole na koma, ina lumshesu nace.

"Ummina! Yarana fa?"
      Wani banzan kallo tayi min cikin matsanancin ɓacinrai tace.
"Dk cikin yarana, kece kika fita zakka. Ko yayya na saka doka sai kin rusa min ita, yanzun badan Allah ya kare ba, me kike tunanin zai faru. Wallahi Safinah ki fita a idanuna na rufe."

    "Don Allah Mariama ki rabu da ita haka, da muka samu duk suna raye barka zamu sannan mu godewa Allah, sai Dr shima ya farfaɗo Insha Allah, Ubangiji zai shiga tsakaninmu da duk me nufarmu da sharri, yanzun haka munyi magana da Hukumar yan sanda, kuma Allah zai bamu nasara."

      "Alhaji hankalina bai kwnta ba Ina ganin Safinah ta tattara tabi tafi Oman zatafi samun kariya a can."

    Shigowar Mataimakin IG, yasata yin shiru, gaisawa  sannan yace.
    "Alhaji Badar! Mun sami labarin kaida iyalinka tare da Dr Katagum ake hari, amma abin mamaki ba maharan bane suka turo mana sakon D28 Code 29Grp"

         🏃🏃🏃🏃🏃Yacn kaina har ciwo yake,

     _Domin cancare chakwalkwalin Chakwakiyar  zaku iya sheke   naira 150 a cikin asusun bankina kaitsaye domin dakon Book 2, idan kuma Katine zaku iya Kumdume katin Mtn na naira 200, Mu kafta saura pages 28 na karkare Book One ga wata Chakwakiyyar ta fashe kune min taku...Karku manta idan transifer ɗin kati Vtu 200 ne idan kuma kaitsaye ne zuwa asusuna na banki 150 ne sayan nagari mai da kuɗi gida Arashin araha ake barin tayi, koda kuɗinka sai da rabonka abin dace ne ɗan fari ya mutu idan kun shirya naji motsinku daga marubuciyarku wacce bata san raggonci ko lalace ba ƙullum suburbuɗeku take da labarai sinki sinki_


     

Oum Muwaddah......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

 
*_Labarin daban yake da sauran._*

_Kun gane Nufina kuwa? Book One free ne daga page 1 to 60, Book 2 zuwa inda zan tsaya na kuɗine wai ina gaya muku ne ku shirya tsaf_😹


Page.٣٣-33
Zaro idanu nayi waje, tare da kifkifitawa, nace.
"Ummi ina yarana?"
Buɗe min bakina tayi cike da jin haushi matar da tun da tahaifeni ban taɓa jin tayi zagi koda Qaniyarki bata taɓa faɗa a gabana, sai yau wai itace ke ce min.
"Suna gidan Qaniyarki"
Zaro idanu mukayi hatta Abba sai da ya kalleta anya ita kuwa.

"Ummi zagi kikayi fa!" inji Khalil, juyawa tayi a fusace tace.
"Qaniyarka zan fasa muku kai, haba jama'a ke ɗaya kin addabi rayuwar kowa, Haba don Allah Safinah anya kina son ganin dai-dai a rayuwarki kuwa, ke ko damuwa da rayuwar yaranki bakyayi, toh idan Sajidah ta mutu sai ki san yaren da zaki gaya Ubanta da Kakarta, ina ga baki san ina kika saka kanki ba."

Mikewa nayi tare da dirowa a gadon, jikina na rawa. Fita nayi da gudu, ni kaina bansan inda zani ba, dan su Abba sun biyo ni da sauri mukayi karo da Dudu, rike hannuna yayi na fashe da kuka, tare da faɗawa jikinshi nace.
"Dudu! Aanih! zasu kashe min Yarinya bansan me zancewa Abie ɗinsu ba."
Riko hannun yayi muka nufi ɗakin da aka kwantar dasu, tana kwance tare sa yar uwanta, ita tana barcin wahala. Wani mahaukacin soyayyarsu ce ta daki zuciyata na kura mata ido, sai yanzun na lura da bata kai Aamih haske ba, tana a haske amma me duh. Dan idan ka cika saka ido zaka ga fatarta har wani sheki yake, yayinda Aanih kuma tafita haske sosai dan itace Ashraf a fuska, amma a zahiri Aanih ta fita hakuri.
Sumbatar kumatunta nayi ruwan kwalla ya sauka a fuskarta motsi tayi, tare da sake yar kara irinta wahala. Kamar ance d'ago kai, harɗe hannunshi yayi a kirji. Kanshi yasha bandeji murmushi ya sake min. Na kauda kaina tare da mai dasu kan yaran, haka kawai nake jin wani abu na fisgana, wani irin yanayi nake ji akanshi.
A sannu nasake satar kallonshi, gira ya d'age min tare da kashe min ido, kunya ya bani na kauda kaina. Ina murmushi ƙasa ƙasa,

Har inda nake ya iso yana kallon yadda nake shafa kan Aanih, ina kuma jin idanunshi na yawo a jikina, lokaci guda ya saukar mun da mugun kunyarshi tare da ganin tulin girmanshi da ya cika min ido.
Hannunshi yakai zai ɗauki Aamih, hannunmu ya haɗu da juna. D'ago ƙai mukayi a tare muka kurawa juna ido, janye idanuna nayi daga gare, mai dashi nayi kan Aanih da take barci.
"Ina jin bakon yanayi a tsayuwarmu na yau idan kika bani dama."

Gyara kwanciyar yarinyar nayi na raɓe gefenshi zan bar d'akin, sai ji nayi ya riko hannuna. Tsigar jikina ne ya mike sabida ban taɓa shiga irin wannan yanayin ba sai yau. Duk abinda Anim yayi wasu abubuwa a tare dani ban tab'a jin kome a game dasu ba, kai ko Ashraf da shi na fara sani a duniyata ban ji kome ba, ina jin kewarshi na kata'i sabida halayarshi da suka min, ina son halayarshi fiye da kome.
Dawo dani yayi gabanshi, ya zuba min ido cikin sanyin murya yace.
"Zan iya hakuri har ki yayyesu, amma bazan jure shirunki ba. Am 45 now na rabu da Aieesha, pls ki taimaki gwauro irina ki bashi gurbin."

Dakyar na had'iye yawun bakina cikin inda inda nace.
"Abban Adil! Ina son fita."

"Zama da Sultan ya maida ki miskila irinsa ko? Ga sona a cikin idanunki but kina pretender kamar baki jin kome a kaina, ki bani dama na karshe rayuwata dake."
Ga baki ɗaya na gaza furta kome domin bansan wani irin yanaƴi nake ji ba, sake hannuna yayi sannan ya kwantar da jaririyar, addu'a yayi musu. Sannan yasani a gaba har bakin kofar da aka kwantar dani.

"Safinatu!!! Zan baki dama daga nan har ki yaye yaranki, don Allah karki cutar da zuciyata."
Jikina ne yayi mugun sanyi, sunkuyar da kaina nayi ina wasa da farcena wanda ban jima da musu lalle ba.
"Ina son mace me lalle! Haka yana kara mata martaba da kima."
Takowa yayi har gabana, dukda mutanen da suke kaiwa da komowa, bai hanashi sauke nauyin dake cikin zuciyarshi ba.

"Safinatu! Ki bani amanar kanki da rayuwarki, Insha Allah bazan baki kunya ba."

*Wayyo Allah na ashe haka mace take ji idan tasame me sonta ji nake nafi kowacce mace sa'a.*
Ɗ'agowa naƴi da niyyar ce wani abu ina haɗ'a ido dashi sai naji bazan iya ba, haka nayita motsa bakina. Karshe na juya da sauri na shige ɗakin, na rufe kofar tare da sauke wata ajiyar zuciya.
"Wannan mutumin zai kashe ni da salonshi, mutum sai kace majnun"

"Didi ke kuma Lailah, eyye Our didi falling in love"
Ware idanu nayi dan ban tsamaci yan butan uwa suna cikin ɗakin ba, take na bone fuska.
"Toh Didi! Idan babansu Aamih yazo ya zaki yi?" inji Batul,
Wani tsuke fuska nayi, cikin ɓacin rai nace.
"Kinga nayi miki kalar matar yaro? Ai Ashraf saike Batul ni nafi karfin Yaro karami."

Bakinsu a sake suke kallona, cike da mamaki, fahimtar abinda yake yawo a zuciyarsu ya sani fara kame kame, Ummi tana kallonmu bata ce cikanku ba, sai dai da alamu bata ji daɗin furucina ba.
Dukda na jefa musu kokwanto haka suka share batun amma tabbas suna nazartan Alamarin fiye da tunanina, karshe ina zaune bayan tafiyarsu Ummi tare da jagorancin yan sanda. Karshe gidanmu sai da aka saka mana yan sanda.

"Didi!" d'ago ido nayi na kalleta, dake ina chatt da Dr.
"Dama da naji kince Abie ɗinsu Aanih Yarone sai ni! Am sorry da tambayar da zan miki, kuma wallahi ba cin fuska bane, kince yaro taya."
Tsuru tsuru tayi tana kallona jikinta na ɓari.
Saukowa nayi daga gadon na mikar da ita, sannan na bata labarin abinda ya faru.
Kuka sosai tayu tare da bani hakuri, tace.
"Bai kyauta ba"

"Eh amna kaddararmu"
Na gaya mata kamar ance ɗago kaina Dr na gani, fuskarshi a haɗe. Shigowa yayi sai da yazo kusadani ya hura min iskar bakinshi, tare da sake murmushi.
"Kinga fuakarki kuwa! Haka kike da jin tsoro? Gwara ki zama jaruma."

Murguɗa bakina naƴi cikin jin haushi naki ma cewa kome, ina hararanshi.
Hirarsu suka yi shi da Batul, sun jima kafin ya fita, ko minti biyu bai yi ba sai ga sakonshi ya shigo min har da fuskar mage.
*Am so sorry Angel😿*

*Toh meye kuma?😒*

*Ina son wannan kallon da alamu an tura that cute lips ɗinan*
Rike bakina nayi cike da mamaki ina ware idona akan screen ɗin na tura mishi tambaya nayi.
*Taya kasan na tura bakina?😙"

*Tun daga ranar da Kyari ya kawo ki a sume bayan kin same matsalan nan, bayan mu miki allura. Naga alamun Yar Ummi sakaliya ce*

Cizon lips ɗina nayi na kashe data.
Sai ga kiranshi ya shigo min, kin ɗauka nayi karshe da ya dameni nasaka mishi busy.

Ban kuma bin takan wayar ba, sai da yamma zanje bawa yaran nono ina shiga, na same shi yana riƙe da Aamih ta dawp normal sai zare idanu take, nuna min gurin zama. Cikin nutsuwa na zauna sannan ya mika min Babyn kallon agogon da yake ɗaure a tsintsinyar hannunshi yaƴi sannan ya fita.
Can da ta koma barci sai gashi ya shigo amsarta yayi ya kwantar da ita sannan ya ɗaura min Aanil. Itama fita yayi ina maida nonon cikin rigata yana shigowa, kwantar da ita yayi sannan yaja kujera ya sani a gaba, yana kallona kamar wanda yasami majigi. Ni kuwa kunya yake bani naga babba kamanshi yasani a gaba yana min rawan kai.
"Toh kice wani abu mana!"
Lashe lips ɗina nayi a hankali sannan nad'ago a hankali na saci kallonshi, aikuwa muka haɗa ido da sauri na kauda kai, cikin zolaya yace.
"Allah duk ranar da na kama mutum sai na cire ƙunyar nan na barshi sintir"
Mikewa naƴi na fita da sauri, ya biyo bayana yana dariya, manyan da kananun likitoti sai mamakin Dr Zaki suke, su abin dariya yake basu, wai lokack guda ya zama madness in love.
Kuma karku manta nifa har yanzun na kasa cewa ga Ajin da nasaka Dr ba, amma ina jinshi a cikin raina da zuciyata ƙo motsi yayi ina jinshi in my Body, balle kuma yayi magana sai naji kamar nafi ko wacce mace Sa'a. Da farko dai Dr ba baki bane dan shi yafini ma haske, yanayinshi sak da irin mutane Madaras, idan yana abu zaka rantse kace Shivarao ne, Babban jarumin andraprudashe, na kasan India, dukda ya, yana da tsari da zubin halittan manyan maza, mutum ne mai yawan gargasa, dan ko hannunsh zaka ga haka, balle kanshi dan a yanda na fahimce irinshi ba mamaki after 2weeks yake askin gashin kanshi.

Idan zance a cikin zaratan maza waye gwanina zan iya rufe idanu nace Dr, dan takowani lungu ya iya saita soyayya meyin lugulugu da zuciyar D'aya mace. Balle ni kuma da nake uwarsu wance, A iyakan rayuwata wannan karone na fara son ɗa namiji bawai shirmen da nayi tayi aka Anim, Idan da Dr na samu a farko zaiyi wuya na, tsallaka na bar aurenshi, sabida irin mafarkin danake yau gashi na same shi, mijin da zai girmama Alamarina. Na sameshi, ya fahimce ni,kuma ya fahimci kaddarara, kuma tsaf yake ya zauna dani, gaskiya ina cikin farin ciki.
Haka mukayita shirrita dan kana ganinmu kasan sabin shigane a love, dan mun kasa ɓoyewa a gaban kowa.
***
Washi gari ina zaune akan abin sallah, inata jiran kiranshi dan ya sabar min da haka,
Tura mishi sako zanyi sai ga nashi sakon ya turo min.
*Ina da Meeting kuma zanje ganin shugaban kasa sabida nike duba lafiyanshi By Angel*

Sai naji ba daɗi, tura mishi sakon fatan alkhairi nayi nace.
*Ok Baby! Allah ya bada sa'a! Ubangiji ya kare min Honey."
Sai da sakon ya tafi naji kunya ta kamani.
*Alhamdulillah ni kika kira da Baby ina son sunan kibar honeynan Baby ma ya isa*


*_Bawai ku turo min kuɗin ku nake nufi ba, na gaya muku ne kafin na gama Book One Free ne, bana son sai na gama nace muku Two na kuɗine tsaf wasu zasu zageni akan haka, kuma Am Sure that akan na maida na kuɗi dayawanku zasu daina Comments da Voting sai dai nasan haka bazai sani kasa a gwiwa ba._*


Oum Muwaddah...
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....

UMMU ALMUSTAPHA kina girmama Chakwakiyya,
MAMAN SADEEQ ta zauren Sainah ina jin daɗin comments ɗunki.

Fatan Alkhairi gareki Aunty Umma🍀
  
Uwar miji uwar kankanba, BabarTankwali me katon kai😂😹 Daga ke sai Aunty Umma kuka nuna min Sonso nagode......

Masu tambaya Number da Acc kuyi hakuri na shiga page.40 zan saka muku, ku fara booking👏 Ina muku sonsoriya😹

Page.٣٤-34

Murmushi nayi cikin jin wani farin ciki ya lulluɓe ni, na tura mishi.
*Don Allah ka nutsu idan kaje gaban shugaban kasa karka kwafsa*

      Ina tura mishi na kashe wayar dan nasan yanzun zai addabi rayuwata da sako.
    Komawa bakin gado nayi na zauna, na gaji da asibit gaskiya.

      Cire hijab nayi na ninke, sannan, ina idarwa Ummi tana shigowa, kallonta nayi cikin zolaya nace.
"Ummina! Gaskiya munyi fushi ni su. Princess"
       Taɓe bakinta tayi cikin ko in kula tace.
"Ai zamanku nake dasu, sai ku sani a koma inda na fito."
         Kunshe dariyana nayi sannan nace.
"Haba! Hajiya Ummina ai bai kai haka ba, tunda gashi har da sammako kikayi, dan ganinsu. Shi yasa nake jin kishinsu."
 
     "Sabida sun kwace miki fadarki ko?"
  Naji muryan shi, kallonshi nayi tare da masa magana da ido, baka shiga meeting ɗin ba.
     Kallon Ummi yayi ita kan hankalinta nagun ajiye min abin karyawa,
      Gefen kirjinshi ya zana da yatsar hannunshi, sai ya kama tare da ɓata fuska, sannan ya watsa yatsunsa, ban san lokacin da nace.
"Ta fashe!!"
      A razane Ummi ta juyo tace.
"Wacece?"
     "Dr mana!"
       Ina juyawa babu shi babu alamarshi, itama kallon kofar tayi, taga bakowa.
      Dafe goshina naƴi nace.
"Baki ganshi ba anan har yace min su Aanih sun kwace min Fada"
            Kallon Mahaukaciya tayi min, share zance nayi na cigaba da kallon kofar.
   Kunna wayata nayi na ajiyeta a kasar pillow. Abin karyawa da Ummi ta kawo min na ɗauka zan ci sai na tuna banyi brush ba. Kawai na shiga ban ɗaki zan wanke bakina, da fari ina buɗe panpo ruwa ya zuba na fara wanke bakina, kamar ance kalli madubi. Sai naga yayi dishi dishi kamar an buɗe ruwan zafi gogewa, me zangani Anim ne bakinshi na ɗigar da jini. Ya ka turo hannunshi da mugun zafin nama zai shake wuyata.
     Addu'ar niman kariya daga miƴagu da shaiɗanu nayi da mugun karfi har sai da madubin ya tarwarse. Shi kuma na nemishi na rasa, burushin da banyi ba knn, na fito bakina duk kumfa.
      "Ummi!!!"
Na kirata babu ita babu dalilinta babu kuma abincin da takawo min, kara wayata tayi naje nasaka hannu zan ɗauka, sai naji kamar a cikin ruwa na tsoma hannuna, ina zarowa jini ne.
   A tsorace na cigaba da addu'a take jinin ya ɓace, Ummina nagani cikin rawan jiki nace.
"Ummina!!!"
        "Ina kika shiga ne! Gamu nan zuwa da abin karyawa."

       Wasu siraran hawaye ne ya zubo min nace.
"Ummina akwai matsala!!"
   
     "Name?"
    "Sai kunzo "
   ***
A hanyarsu ta zuwa suka haɗu da wasu mabarata har zasu wucce.
"Zakari ɗan tsaya na bada sadaka."



2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment