Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basu kai ga barin cikin garin Amman. Suka cin masu. Basu musu kome ba yaron suka amsa bayan sun wurga mata jakar kuɗin dallar U.S, sannan suƙa mata gargaɗin da karsu kuma ganinta a kasar ko kuma su kasheka, domin kai ka rayu ita ta bar kasar baki ɗaya, domin kai tabar mahaifarta, dan tasan matuƙar ta koma kasarta zasu abin zai zama kamar yak...."

Mikewa yayi yana me zuba hannunshi cikin aljuhun wandonshi, ya kalle ni a sace sannan yace.
"Meye ya kawo ki.?"

"Tausayin Nannah da irin son da take min, yasani jin zan iya kome dan tayi farin ciki, dukda ta gargaɗe ni da zuwa nan ɗin." sunkuyar da kaina nayi tare da fashewa da kuka, nace.
"Nagama aikina. Amma na rasa tawa farin cikin, na rasa abinda zai cire zargi a zuciyar duk wanda zan au..."

Fita yayi daga ɗakin, na kuma rushewa da kuka, sabida son nagyarawa wasu zuciyarsu ni tawa zuciyar ta lalace. Taya zan fahimtsar da Anim, wallahi yasan halin da na jefa kaina ciki har abada bazai kuma haɗa hanya dani ba,

***
Ƴau kwana biyu kenan tunda ya tafi nake cikin damuwa, ga ciwon kullum yake, sam ban taɓa kawo wani abu a raina ba, kawai bar haka a matsayin typhord. Ranar da aka mai dani fada ina tsaye aka gabatar da laifina. Suƙa nemi nace wani abu amma naki magana, shima yace wani abu yaki magana, haka suka mai dani tare da masa caaaaa kuma dama sun sami labarin yaje gidan yarin dan haka Marhum ya faɗawa Amir Ukshe, sun tattauna akan Sultan.

***
Ina zaune ya shigo tare da mika min password ɗina, gyara tsayuwarshi yayi sannan yace.
"Nasamu a cikin kayanki, sannan nayi miki booking ɗin jirgi wanda zai tashi karfe sha ɗaya na rana zuwa jakarta na kasar Tunis, sannan ki rubuta min address ɗinki da Number wayar gidanku. Idan nagama abinda naƙe zanzo naga Ammina."

Jikina na rawan sanyi na rubuta mishi number Nannah sannan na mika mishi, garin karɓa ya shafi hannuna da sauri ya d'ago kanshi yana kallona yace.
"Baki da lafiya ne?"

"Fever ne, amma nasha magani, idan na isa gida zanje Abdul ya duba ni."
Tsare ni da ido yayi sosai, sannan ya taɓe baki yace.
"Waye Abdul? Ko shine zaki au."
Girgiza kaina nayi cikin gajiƴa nace.
"Kanina ne?"

Fita yayi daga ɗakin, kwanciya nayi a gadona wani irin farin ciki na cika min zuciya,
........ Washi gari aka mai dani, kamar da yadda aka saba naki magana, shima bai ce kome ba.
"Idan na fahimta Sultan Ashraf na kare mai laifi, bayan kuma shi ya saka doka...."
Bai kai aya ba Ashraf ya mike, daga kujeran ya cire duk wani abinda ya shafi na sarauta ya ajiye musu, sannan yace.
"Ni Muh'd Ashraf na ajiye muku mukamin ku, sannan zan tafi karku taɓa sakaƙancewa, dan dole wata rana ku nime ni."

Yana gama gaya musu maganar ya dawo inda nake ya riko hannuna muka fita, inda aka ajiye motarshi muka nufa Ghaniyu yaja motar, Zuwa Airport, naso muyi sallama dasu. Amma ban samu halin haka ba.

...... Tunda muka isa na zauna sukayita zirga zirga, sannan ya dawo da wata jaƙar takarda ya mika min sannan yace min.
"Kije ki sauya kayanki kowa kallonki yake."
Mikewa nayi jiri ya tafi dani. Da sauri ya tare ni, na zuɓe a kirjinshi ajiyar zuciya na sauke, ina rungume a jikinshi ya nufi gurin sauya kaya, shigar dani yayi sannan ya fito nasaka kayan na fito dakyar, dawowa yayi ya sanya hannuna a kafaɗarshi yana rike da k'uguna muka fito, dake ticker VIP. Ƴa saya min, muna fitowa ya kaini can. Zama yayi kusadani yana ce min sannu, zuba min ido yayi ganin yadda nake share kwalla. Ajiyar zuciya ƴa sauke sannan yace.
"Da zan tafi Madina ne karɓo takarduna, amma ganin halin da kike ciki yasani zan biki zuwa Nigeria, Naga ƴanayin j.."

Da sauri na katse shi ta hanyar gyara zamana nace.
"Lafiyata lau, kawai ciwon jikin dukar da nasha a hannun samudawarka ne."

Kauda kanshi yayi sannan ya mike yace.
"Insha Allah zan zo nan da wata biyu."

........ Gyaɗa mishi kaina nayi, tare da janyen idanuna akanshi,.yau ce rana tafarko da nake jin ba dad'i rabuwa da wani, shima ban san dalilinshi nakin tafiya ba, zuba min idanu yayi ya sauke a jiyar zuciya sannan ya fita, ina zaune can sai ga wata ma'aikaciyar jirgin tashigo rike da wani takarda mika min tayi, na amsa buɗewa nayi, zoɓe ya faɗo. Tare da wani ƙaramin rubutu aka ce.
*_Nasan bazan biyaki abinda kika rasa ba, bansan me yasa haka ya faru ba amma ina me baki hakuri da ki yafe min dan na zalince ki na rabaki da kimarki na Y'a mace ina kara baki hakuri , idan kin isa ki sumbaci goshin Ammina ina nan zuwa gareta_*
Lumshe idanuna nayi, zuciyata na min ciwo. Ainun ina jin sa,ada jirgin ya tashi,

....... Bayan tashinm ya kalle Ghaniyu cikin damuwa, yace.
"Yarinyar can bata da lafiya"

"Eh ranka shi daɗe, gaskiya Safinat bata da lafiya, tana da hakuri da juriya ne kawai, amma kana kallonta kasan bata da lafiya."

Haka sukayita tattaunawa har lokacin tashin jirgin Ashraf yayi.
Suka yi sallama da Ghaniyu, sun rabu cikin jimami.
***
*NIGERIA*
Abuja.....
Shakar iskar kasata yasani lumshe idanuna, a hankali naƙe saukowa daga matakalar jirgin. Har na iso arriver, ɗan jakata na ɗauka tare da fita daga cikin gun, ina fita nasame taxi, na gaji ga jirin dake damuna.

Sunan unguwarmu na faɗa mishi a gajiye, yace min.
"Madam 1.5₦" gyaɗa kaina nayi na shiga, tsoro da farga duk suƙa ciƙa min Zuciya.

......... Tafiyar awa ɗaya ya kaimu, ƴana tsayuwa a kofar gidanmu Khalilah tana fitowa zata taka kawayenta da suka zo jajjen ɓata na, yayinda Abdul ya zo zai shiga gidan. Na fito a hankali,

"Addah Feener!!!"
Wani irin kwalla ne ya zubo min, fitowa da gudu Abdul yayi lokacin na mike tsaye ya karaso guna, faɗawa jikinsa nayi tare da fashewa da kuk.......

_A ɗauri kashine ko a ɓata igiya😎_



MJ#HZƘ#VOTE....

OUM MUWADDA😇
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_*


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
    *_Maidambu ki zubda cikin nan na tsani cikin, Oum Muwadda don Allah a cire cikin Maman Walid don Allah karta samu matsala da family ta.....Chaiiiii ina kuke so na cusa kaina... Bari na ware muku wani abu da tunda ya shige Muku duhu Kaddara da Rabon dake tsakaninta da Sultan, haka kawai dan taga halin da mahaifiyarshi take ci taxo, sai kaddarar Ubangiji, aurenta aka saka amma aka fasa sabida karfin rabo, da anyi auren tabbas Anim Mutuwa zai yi ko kuma aje auren ba daɗi, Shi alamarin Ubangiji babu ruwanshi idan ya shirya ya shirya kenan har ranar da duniya zata tashi.... A ranar da abin zai faru taso komawa amma dake Allah ya nufa haka sai ya faru sai ya kasance tabbas wannan bangare na labarin ya tuna min kanwata Ya Allah ka bamu ikon cinye Jarabawarmu.....Shin A matsayinki na Uwa ya zaki amshi Feener Shawarar da zaku bada tayu Ummi ta fahimta ko kuma Abba Nagode👏_*

Page.١٧
     Numfashi nake sauƙa da sauri da sauri, rike rigarshi nayi kuka ya ƙwace min, ɗauƙa na zai na girgiza mishi kaina, raɓani yayi a jikinshi muka nufi cikin gidan, me taxi ɗine yace.
"Kuɗina fa!"

         Kawar Khalilah ce ta tambaye shi ya gaya mata ta ciro a cikin jakarta ta mika masa, sannan yaja motarsa yayi gaba.
          Kai tsaye Abdul ya shige dani falourn Ummi inda Yan uwanta daga maidugurin suka zo mata jajje, ga wasu danginsu Abbanmu. Kakarmu Hajja Kaka kanwar Baban Abbanmu, tana zaune kanta naɗe da laffaya, casbi ne a hannunta,

    Ganin  Abdul rike da mace yana shigowa yasa duk suƙa mike, kwantar dani yayi a kan kujeran falon, yace.
"Ummi! Alhamdulillah Allah ya dawo mana da ita, Khalilah jeki cikin motana zaki ga memo ɗin Asibitinmu ɗauƙo min maza."

  Da gudu tafi, Mutanen da suke falon suka haɗa baki suka ce.
"Allahu Akbar! Allah maji roƙon bawansa, Allah mun gode maka da kadawoma da ita gida lafiya."

   (Wai nace Hmm)
   
Nan suka shiga hidima akaina, karshe dai Hajja kaka ta matso cikin kulawa tace.
"Bawan Allah ko zaka wucce da ita asibitine?"

   Lokacin har Khalilah ta shigo da takardan rubutu yayi har dasu magunguna ya fita da sauri.
  
        Ummi kam tunda ta zuba min ido bata ɗaga ba, sam taki cewa kome kallona kawai take, Shigowar  Hajiya Amna da Hajiya Nuratu  wato Mame da Umma yasa duk suka ɗaga kansu, cikin alhini Umma tace.

"Barka da Arziki Safinatu, sannu Allah ya baki lafiya."
 
  "Amin Amnah," inji Hajja kaka,

  Zama Hajiya Nuratu tayi, tana kallona taɓe baki tayi sannan tace.
"Nikam ba makaranta kika tafi bane? Ko wani kika bine? Ya miki halin Yan dun..."

         Zama hajja kaka ta gyara, tare da rike tasbinta tace.
"Nuratu kenan! Ai ba awa motar gawa dariya, idan bai ɗaukeka ba ya ɗauki Uba nai ko uwatai! ehtoh a bakinki muka fara ji, tsalle ɗaya ake a faɗa rijiya, sai anƴi dubu ba a fito ba, harshenka kamaninka"

   "Ayya Hajja daga tambaya sai ya zama laifi"
       "Oho ke kika ji gun ai hannun hagu ba bakon wanƙe kashi bane.,"

     Shiru falour ya ɗauka, shigowar Nannah wacce Anas yaje ya gaya mata na dawo, kamar zata kifa cikin farin ciki da murna ta riko hannuna tace.
"Bint!!! Alhamdulillah, sannu bint"

      Ga baki ɗaya duk ta rud'e sai kiran sunana take, tana share kwalla. Shigowar Abdul yasata mikewa daga inda nake ta koma gefe, ruwa ya samin tare da allura,

          Har aka kira magrib ban tashi ba sai karfe uku na dare na farka, Ummi da Nannah na gansu  zaune akan abin sallah tashi nayi na zauna, ina kallonsu. Zare karin ruwar nayi na shiga wanka, dan zafi nake ji.

    Ina fitowa na buɗe wardrob ɗin Ummi na ɗauki.Hijab da doguwar riga na saka, sannan na tadda sallar dake kaina ina idarwa masalci suna sallah.
   
  Mikewa nayi na gabatar da sallah, sannan na fara addu'a. Ina idarwa barci yace gani nan nazo...
    Kallon Nannah nayi tare da sakar mata murmushi nace.
"Nannah kafa suna min ciwo musaman nan."

Na nuna mata gun  kaina na ɗaura a cinyar Ummi, nace.
"Ummi don Allah sosa min kaina."
    Zare hijab ɗin nayi ita kuma ta shiga sosa min kai Nannah na matsa min kafar, kafin kace minti biyar barci yayi gaba dani.

     ......... Suna ganin nayi barci Nannah ta ɗauko pillow tasa min, hira suka taɓa sama sama,, sannan suƙa kwanta.

...... Ina farkawa naga abokan aikina na gidan radio duk sun zuba min ido mikewa nayi ina murmushi yawu ya cika min bakina,  zubda yawun nayi tare da ɗaukar sabon brush a locker ban ɗakin, na wanke bakina sannan na fito nasamu sunyi min kunun tsamiya, da kosai. Murmushi nayi na fito  falour dan sun fita abincin aka bar min a ciki,, fitowa nayi nima da abincin na zauna a tsakiyar falourn,  ina zama Abbanmu na shigowa.
"Ina kwana Abba!"
   Zama yayi a kan kujera ya amsa da " lafiya ya jikin naki"

         "Da sauki" na bashi amsa a takaice,
   Nan sukayita hira da abokan aikina, ni dai bana iya dogon magana sabida amai.
          ..... Can suka mana sallama zasu tafi, tambayata sukayi yaushe Zan koma aiki nace musu wata sati.

             ...... Ga baki ɗaya wani irin kulawa nake samu daga iyayena har ƴan uwana, jikina kam da sauki babu duƙ abinda yake min yanzun wani mugun kwaɗayi ke ɗawainiya dani, musaman Nanah da Abdul.
         
       Kuma cikin ikon Allah babu wanda ya tambaye ni, ina naje har yan uwan Ummi suka koma, aka bar Hajja kaka kuma dama tana zuwa ta huta sai ta koma.
       Satina ɗ'aya na koma aikina, xuwan Anim gidanmu sau uku naki masa magana asalima bana fita sai na kwanta nayi barcin dole, yau muna gama aiki muka fito zuwa sallah, yaxo ya sha gabana.
   "Feener Kyari ki faɗa min me kike nufi dani? Laifin me nayi miki da zafi?"

        Gefenshi na raɓe zan wucce naji ya riko hannuna bansan lokacin da na ture shi ba, cikin ɓacin rai nace.
"Dole ne? Ka rabu dani tunda kaga naki kulaka."
    Daga haka nayi wuccewata kowa na mamakin yadda na mishi wulakanci.
     ....... Haka nake zuwa aikina duƙda na fara fuskantar matsaloli daga Anim bai dame ni ba, dan ba zamansa nake ba.

       ........
Muna zaune ni da Muwaddah da Sabirah, sai tsiya suƙe min wai na gaya musu wani magani nake sha ne nayi kiba haka, dariya nayi nace.
"Shaka fashe."
     Sabira ta fashe da dariya sannan tace.
    "Ni kuwa yanayinki kama da masu ciki yake min."
           Dariya nayi nace.
"Ba'.."
  Maganarce ta makale sakamakon faduwar da gabana yayi, ina yunkurin mikewa Anim yana zuwa, da sauri na ɗauki jakata na fita bina yayi da ido, shima ya biyo bayana da sauri kafin ya iso, har nayi ribas da mugun gudu sai yanzun abubuwan da suke faruwa ya dawo min kaina, dakyar na isa asibiti dake a rikice nake, har na shiga ban tsaya tunanin inda nazo ba, asibitin da Abdul yake aiki nazo fa. Tsabar ruɗewa.

  Ina kan sai share kwalla nake, har Wani abokin Abdul yazo wuccewa, yaga ina kuka shine ƴaje ya gaya mishi kaina a sunkuye, sai ji nayi an riko hannuna, dago kaina nayi naga wani sabon kuka ne ya kwace min, dago ni yayi  muka wucce ofishinsa, zaunar dani yayi a kujeranshi. Ya durkusa a gabana ganin yadda nake kuka wiwi, ya kura min ido sannan yace.
     "Safinah meke damunki?"
     Muryana na rawa nace.
"Nazo ayi min test ne!"
     "Test ɗin meye? Za a miki?"
    Rufe bakina nayi da hannuna, ina girgiza kai nace.
"Kusan wata ɗaya da wasu kwanaki bangan shi yazo ba"
  A ruɗe ya mike yace.
"Kwanta a wancan gadon."
   Jikinshi na rawa ya kunna computer scanner ɗin, sannan ya sani ɗage rigana ya zuba min luquid ɗin, ya ɗaura abin ya hasko mishi Abinda yake son tabbatarwa, dan tunda ya ɗaura nace "wash"

   A hankali ya shiga duba kwanakin cikin, sati shida cif.
   "Cikin Sati shida Why Safina?"

      Wani irin gigitacce kuka ne ya ƙwace min ina girgiza kaina.
     
  Wayarshi ya ciro ya shiga niman number Ummi, ya kirata.
"Don Allah kizo karki gayawa kowa."

         Juya bayana nayi, na kuma cigaba da kuka, tun daga ranar da abin ya faru nake kuka har iyau kuka nake, sallamar Ummi yasake kara kuka na, kujera ya ja mata ta zauna, zuɓewa yayi a kasa gwiwarshi duk a kasa, sannan ya ɗaura kanshi bisa cinyarta, a hankali tashiga shafawa kanshi, zuciyarta na rawa.
   
        "Abdullah! Meke faru?"
D'ago kanshi yayi kwalla na zuba daga idanunshi ya rike hannunta cikin kuka yace.
"Ummi! Shin bayan uwa akwai mutumin da zai iya jure zafin fitar ɗ'a daga jikinsa?"
     "Babu Abdullah uwace kawai take jure zafin fitar ɗanta a jikinta"

           "Ummi indai har haka ne tabbas babu uwar da zata gaza tsayawa d'anta, indai har zata iya tsaya masa tabbas ita kaɗai ce zata yarda da kaddararsa, indai har haka ne itace kawai zata iya amincewa da bukatarsa, indai har haka ne itace zata iya share masa kuka, Ummi duk duniya bamu wata bayan ke, Ummi indai har kika amshi kaddarar da tasamemu nayi.Imani da Allah bazaki taɓa ta gaiyara ba."
        Shafa kanshi tayi cikin karfin hali tace.
"Ina jinka!"
    "Ummi!!!!"
    "Na'am!!!"
   Nuna mata gadon yayi cikin kuka yace.
    "Tarbiyarki ce! Renonki ce! Shekara ɗai ɗai har talatin bata taɓa saɓa miki ba bata tab'ayin abin Allah wadarai ba, sai gashi a cikin shakara na talatin da d'aya tazo miki da kaddara shin zaki amsheta."

    Kallona tayi zuciyarta na wani irin bugawa,
. Sannan ya cigaba da cewa.
"Ummi baki ce kome ba"
      Murmushi kawai ta iya sakewa akan fuskarta.
    Goge kwalla yayi sannan cikin karamar murƴa yace.
"Cikin sati shida gareta."
     Rike hannunshi tayi da mugun karfi tana ambaton sunayen Allah sai ta tayi guda ɗari ba ɗayan nan cif kafin ta iya buɗe idanunta da ta runtsa, mikewa tayi ta gyara hijab ɗinta tace.
"Tasauko muje."

          Jikina ba kwari na sauka a gadon na ɗauki jakata, koda muka fita ban iya jan motana ba.

         motar da ya kawo Ummi nabi kwanciya nayi a baya, idanuna suƙa cigaba da kwalla, muna isowa ana fito da kayan Anim da ya kawo na aure, aka zuba a mota.

    Da sauri na shige cikin gida, ina saka kafana a falourn kunne na jiyo min........



  #MJ#HZƘ#VOTE.......

Oum Muwadda......

       
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*


Sadaukarwa ga Ummu Sayeed naji daɗin Yadda kika tafi bincike Yasin wasu rubutun kawai suke karantawa basa bincike balle su tabbatar da labarin gaskiya ne ko karya ne,😂
Page.١٨

"Alhaji Idan karya aka mata ai gata nan ka tambayeta ba da kanka zata faɗa maka,,

"Zo nan uwata!!"
Wani irin rawa jikina ya ɗauka tare da mugun tsoro da firgici, juyawa yayi ya haura sama.

Ban taɓa sanin haka yan matan da sukayi ciƙi a waje suke fuskarta tashin hankali ba, sai yau da ya faru a kaina. Rike Ummi nake cike da tashin hankali,

"Sai anyi magana ace lokacine bai yi ba, nan kuwa ana yaudaranmu ce da cewa miji bai zo ba, ashe anje gun wani katone ya zuba nasa basirar." Inji Mame Hjy Nuratu.

Lumshe idanu Ummi tayi da gudu Abbanmu ya sauko ganinshi ni kuwa na nime guduwa D'akin Ummi, cafko ni Mamie tayi tare da falla min mari. Akan fuskana. Sam idanun Abba ya rufe kawai ya rufe ni da mugun da wayar chajin laptop ɗin, zafi da azaba da suka gaurayani, kai ko dukar da samudawan Jordan bai taɓa tsoratani ba kamaemr dukan Abba kodan akwai tsoro ne a raina yasa duk na firgice.

"Ai gwara ka daketa yarinya ta zama annobar mace, mahaifinki na zaman lafiyansa kinje kinje ki ɗauko mishi ɗan gaba da fatiha, sai anyi magana ace ai mijine bai zo ba makira kuwa kinje sun gama dake shine zaki kwaso abin kunya ki zo masa da shi wannan da nice na haife ki yau zaki bar min cikin gidana dan ba zan iya rikon asara ba.."

A yadda na fahimci Abba babba burinshi bai wucce dukar cikina ba da kafarshi, ina gano nufinshi nayi maza na k'amk'ame ummi, jikina na rawa nace.
"Ummina ki cece ni bazan kuma ba. Wayyo Allah Ummina bazan kuma ba."

"Kaji ko Alhaji! Uwarta take niman ta kareta." inji Mamie.
Finciko ni yayi Ummi ta rike ni gam, cikin hargagi da kuma ingiza me kantu ruwa, yace.

"Maryam! Saketa ko kuma ranki ya ɓaci"

"Rayukarmu ne zasu ɓaci, ban hanaka hukunci ba, amma idan zakayi ka fara aiki da hankali yafi aiki da agogo, a cikin shekarun da tayi. Bata taɓa yin abinda zai ɓata maka ba, tun tasowarta take kare kanta, da sunanka. Shin d gangan haka ya sameta ko kuwa karfi aka gwada mata, yarinyar da ka ɗauketa zuwa ghana dan tayi karatu yau dan tazo maka da akasin kaddara sai ka juya mata baya, ka nunawa Ubangiji bai isa ya jarabeka ba, kanunawa Ubangiji baka da karfin Imani, kai Uba kenan ina kuma ni da nake Uwa."

"Wannan matsalarki ce! Alhaji idan baka ɗauki mataki ba hatta fita waje sai yafi karfinka, cikin shege taɓ ɗan gaba da fatiha fa. Da sakel an ba wa me kaza kai."

Gabaki ɗaya sake haukacewa. Abba yayi cikin tashin hankali da ɓacin rai yace.
"Nuratu! Ɗauko min wuka a kitchen idan ban kashe Safinah ba nayiwa kaina karya bani."

Abin nima ya samu, da gudu Mamie ta shige kitchen, sai da tayi rawa💃💃💃💃💃 "Shegiyar yarinya ta hanani rawan gaban hantsi yau dole ki bar gidan nan."
Da gudu ta ɗauki wukar tafita zuwa palour, karɓa yayi yayo kaina. Na fasa ihu tare da rike Ummina, kamar zata faɗi.

"Zaki faɗa min uban da ya miki ciki ko sai na miki yankan rago?"
Ya daka min tsawa, duk na kara rikicewa, jin ihuna yasa Umma da Hajja kaka suka fito da sauri, Nannah ta rufa musu baya. Finciko ni yayi yasa min wukar a wuya. Cikin kuka nace.
"Ummina karki tafi ki tsaya."

Cak ta tsaya ita batayi gaba ba, ita batayi baya ba. Taki kuma juyawa ta kalle mu, Nannah ce tasaka hannu ta amshi wukar, cikin ɓacin rai tace.
"Banda ina ganin girmanka, tabbas da na mareka wallahi."

Wurgar da wukar cikin zafin rai Hajja kaka tace.
"Yau naga jakar uba! Yo da kaɗauki zungureren wukar nan wata uwar zaka yi da ita"

"Hmm! Ai da zaku ji abin kunyar da yar gwal ɗinku tayi da bazaku ga laifinsa ba, domin d'an gaba da fatiha ne a kwance cikin mahaifarta." Inji Mamie ta faɗa tare da kumbura fuska tana hura hanci.

Tsaki Hajja Kaka tayi cikin ko in kula tace.
"Sai me dan tayi cikin shege! Ai gwara ita, wasu asalinsu idan kaji har duniya tatashi bazaka haɗa iri da suba, amma da kaddarar rabo ya haɗa aiki gashi ana zaune lafiya, wai kura na cewa kare mayye, yo wani dare ne jemage bai gani ba, ai sai daren mutuwarsa, abin kunya gaba ta bashi ba baya ba, kuma ba kanta farau ba, kuma ba akanta karau ba, wasu nasu kazantar ko kuda bazai so hawa kai ba. Balle yarinyar da tayi zaman a wata duniya na tsawon shekaru, dan yau ta dawo sai a nemi kashe min ita, don Allah yankata dan kwal ubanka, wato dan bani ce na haifeka ba, ka nuna min dan ban taɓa haihuwa ba shine zaka kashe yarka ko shawara dani bakayi ba ai da na gaya maka hanya mafi sauki da zaka kasheta. Ke Amnah ɗauko min igiya ya ratayeta ina ga irin wannan kisar ba a ciki tsananta bincike ba ko."

Wani katon harara ta masa sannan ta dawo kaina riko hannuna tayi, tare zaunar dani jikina bai fasa rawa ba, ta kalle ni cikin jin haushi tace.
"Yar banza da shege idanu kamar yayan kurna, taya kika bashi ya ɗirka miki ciki, yo yanzun da duniya ta cigaba, aiko wannan kororon roba yasaka, codan yako ko me." (Just for fun😂 Hajja kaka wooo)

Sunkuyar da kaina nayi dan na lura yau barikancin hajja kaka ya motsa,
Taɓe baki tayi cikin ko in

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment