Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rike wuyarshi sakamaƙon shake mishi wuya da Irfan yayi, suna cikin wannan kokuwar sai ga Ammar babban ɗan Amir Abu Zarri yashigo ganin, yadda ake shirin kashe masa mahaifi, bai san lokacin da ya ɗauki wani kwalba ya jefi keyar Irfan, sake Amir Abu yayi ya faɗi kasa sumamme,

      Shi kuma Ammar yaje kan Babanshi ya ɗauke shi suƙa fito daga cikin ɗakin, ya kuma bawa masu tsaron kofar izin karsu bar Irfan ya fita, shi kuma ya wucce da mahaifinsa Asibitin.

         ***
   Daga falour bakin Amir Ukshe Raziyah tafito fusƙarta cike da farin ciki, shima bayanta ya biyo ƴace.
"Ki kula sosai, dama Abu Zarri ne ya tsare mana gaba, indai Ashraf ne bani da matsala dashi. Dan wannan halin da yake ciki ma ya ishe shi, haka zai zauna har karshen rayuwarsa kowa ya manta."

      "Ni haka ma bawai yayi min bane amma bazanki shawaranka ba ai da kasheshi mukayi haka zai fi alkhairi."

   "Me kike ci na baka sauka, ki jira nan da wani loƙaci mulki zai dawo hannunmu,"

    "Dukda haka naso da kashe shi baki ɗaya dan ina gudun kar wani abu yazo ya lalata mana shirinmu"

          "Idan muka kashe shi zaiyi wuya muma mukai labari, haka ma wadatar dashi."

  Haka suka tashirya yadda zasu kawar da duk wanda zai kawo musu shunku.
            ***
*NIGERIA*
Abuja.... 4pm

A firgice Ummi tafarka daga barcin la'asar ɗin da tayi akan abin sallarta, salatinta yasa Khalil da Fatima wacce muke kira da Batul. Da sauri suƙa nufin kanta, mika mata ruwa Khalil yayi wanda tasha kafin tayi sallar la'asar.
      "Sannu Ummi! Lafiya..?"
       Inji Khalil, janshi baya Batul tayi tare da dakatar da shi.
 
     Sallama yayi tare da shigowa falon ganinsu cirko cirko akanta yashi tambayar "Lafiya?"

Inji Abdullahi, " Ya Abdul Ummi ce mukaji tayi salati, shine muka bata ruwa ko Adda Batul" Inji Khalil,

Zama yayi kusada Ummi ya ɗaurs kanshi akan kafaɗar, yace.
"Ummi! Don Allah ki rage sanya damuwa a ranki, Insha Allah duk inda Safinah take zata dawo lafiy..."

"A'a Abdullahi! Safina tana cikin hatsari, naji haka a jikina tana gab da faɗawa cikin hatsari na ganta cikin mugun yanayi tabbas tana cikin mawuyacin hali." a raunane ta kai, kafin waninsu yayi magana tasake wani irin kuka mara sauti tasake a hankali me mugun taɓa zuciyar me sauraro tace.
"Ƴa Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkakku masu daraja ya Allah ka jarabce ni da abinda zuciyata zata iya ɗauka Ubangiji baiwarka tana cikin wani hali ya RahamanRahim Ya Allah badan na iya ba Ya Allah dan karfin mulkinka ka kare Safinatu a duk inda take."

Addu'ar da tayi kenan, duk falourn sai da suƙa zubda kwalla, shigowar Nannah baisa su fasa kuka ba, Abdul ne yayi ta maza ya faɗawa Nannah abinda ke faru, itama dai ƴau tun safe take yawan jin faɗuwar gaba tare da tunanin Safinah da ya addabi zuciyarta, gefe guda kuwa na zuciyarta yana son tabbatar mata da zarginta amma bata amince da hakan ba.
"Maman Bint ki daina kukan nan haka, Insha Allah Bint tana nan dawowa, Insha Allah ki daina takura zuciyarki da tunanin wani abu zai same ta da izini Ubangiji alkhairi ne zai faru da ita."

Da kyawawan kalamai Nannah tashawo kan Ummi tayi shiru, ita ba ƙome ke ɗaga mata hankali ba ƙome bane sai idan ta tuna cewa Safinah mace ce, me rauni ce bazata iya kare kanta ba idan wani abun kare kai yazo mata babu shakikinta a tare da ita, waye zai kare mata wani abun waye zai ceceta idan wani ya farmaketa cikin kuka tace.
"Mamin Bint!! Mace fa bata da karfi, idan wani ya farmaketa fa? A wannan duniyar da imani yayi karanci idan wasu suƙa cutar da ita fa, kasancewarta Ƴa mace me rauni taya zata tsira, wallahi nasan babu makawa Safin..."

Kwarewa tayi wanda ya haifar mata da tari me karfi, sai da aka bata ruwa tasha, ajiyar zuciya ta sauke tace.
"Allah kai kafini sanin halin da taƙe ciki"

Daga haka bata kuma magana ba, sai dai kwalla yaki barin idanunta......

Nannah bata bar gidan ba sai karfe biyar da rabi, lokacin Alhaji Badar ya dawo.
***
*JORDAN*
9:pm
Ganin dare na kara duhu, ga wani tsoro tare da faɗuwar gaba, yasani juyawa zan bar gidan, ban taɓa tsamanin zan ganshi ba sai ganinshi nayi a gabana, wani irin yanayi naji tare da tsoron da ya cika min zuciya baya nayi a razane na juya da mugun gudu cikin gidan, aikuwa ya rufa min.
Sakamaƙon duhun falon, bansan meye a gabana ba nayi tuntuɓe dashi take na zuɓe a gurin, zan mike naji kafar tayi min nauyi. Dole na mike da sauri kafin nace zan gudu ya bangajeni da kirjinshi na faɗi can gefe akan hannuna, sai da naji karan kashin hannuna. Kuka ne ya kwace min dukda falon akwai duhu sosai nasha mamakin yadda yake gane inda nake, matsawa nayi da sauri na shige ɗakinsa, nasamu na tura ƙofar zan rufe ya kaiwa kofar doka, kuka ne ya ƙwace min miƙewa nayi na shiga bin bango da bayana,, hmm ashe makunin wutar ɗakin na ta inda nake ja a jikin bango aikuwa wutar dakin ta kunnu, ashe jiya a duhu na ganshi, ƴau kam a haske nayi ido biyun dashi.

Bansan lokacin da ihu ya kwace min ba na rufe idanuna da mugun karfi, fincikoni yayi ya cillani saman gadonshi kaina ya bugu da allon gadon, bibiyu na fara ganinshi, yunkura nayi zan mike yayi maza ya diro kaina, kuka ne ya kwace min nace.
"Karka min haka Ashraf, don Allah karka rabani da kome na, gwara ka kashe ni kawai."

Kifeni da mari yayi wanda ya ɗauke min jina da ganina, kafin na dawo daga hutun rabin lokaci Ashraf ya keta min rigana har cikina, duka na kai mishi tare da yakushe fuskarshi, amma ina yaci karfina, kuka nake kalaman Nan yana dawo min.
_Taya zaki kare kanki? Karki tsomma kanko cikin wancan masarautar kyaleshi inda rai da rabo zamu gana, a matsayinki na ya mace taya zaki fuskancesu har ki samu damar ɗauko shi? Don Allah karki aiƙata abinda zanji na tsani kaina, dan matuƙar suƙa ganoki kasheki zasuyi idan ƙuma basu kashe ki ba zasu cut..."

Wani irin azaba ce tA dawo dani daga gajeriyar tunanin dana faɗa, tureshi nayi da mugun karfi na kwaci kaina, amma, kasancewa karfinmi ba daya ba, sake kamoni yayi ya shake min wuya. Ina ji ina gani na rasa kimata, darajata, budurcina, tun daga shekaran da na balaga nake tattalinsa, Ummi da Nannah suka tayani tattalinsa ta hanyar faɗa min sharuɗar da zan kiyayye, wanda bazan rasa shi ba, nima nabi. Yau gashi garin taimakon da tausayi nazo inda aƙa bautar dani, aka wulakantani, uwa uba aka rabani da Alfarmata. Ni Safinatu na rasa Darajata na yaudari iyayena, har da mijin da zan aura na tsallakesu na tawo ciƙawa Nannah Muradinta, gashi hakkin Iyayena da Anim ya kamani.
Ganin yadda yake kara tsaga jikina nayi wani yunƙuri nacire hannunshi ɗaya a wuyana, garin ya maida hannun zoɓen azurfan hannunsh......


*_A koda yaushe labari takan sabunta kanta, musaman wanda kake muradin isar da sako....Zan baku dama faɗi ra'ayoyinku....
Meye ya jefa safinah cikin wannan matsalar... Idan na gama page 13 naga Writerup ɗinku da sakon da wannan shafin ya kunsan zan sake muku musaman Whatspp grps ɗina ƙune zaƙu fara karanta Page 13 hmmm Wattpad kan na baƙu 12 ku more gobe nayi muku posting tunda rowar vote kuke._*

#MJ#HZƘ#VOTE&Share...

Oum Muwaddah....💅
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: *_HAZAƘA WRITER'S ASSO_*


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

Page.١٣


    Kwalla ne ke bin fuskana da ace ban hannun agogo zai dawo da na maida abinda ya faru matsayin mafarki, ajiyar zuciya ya sake tare da atishawa me karfi akai akai, har sau bakwai. Ji yayi gabaki ɗaya karfinshi sun kare, lokaci guda kuma fitinannen sha'awar da take rura zuciyarshi ta kara zaburar dashi, dan haka ya cigaba da abinda yake. Kwalla na sauƙa ta gefe idanuna na girgiza shi cikin kuka nace.
  "Ash"
   Rufe min baki yayi da hannunshi d'aya ya cigaba da abinda yayi. Sa'a kanina ne yau yake yadda yaso dani, Sa'an Abdul.
......Kwallar dake bin fuskana nake jin ɗigarshi har gefen kunnena,  idan nace ban wahala ba nayi karya, na bar iyayena nazo na rasa kome na,

... Sai da yayi kusan mintuna hamsin da biyar, loƙacin bana cikin hayacina sannan ya janye daga jikina ya koma gefe tare da jan bargon ya lulube kanshi ya kama wani irin barci.

      ***
Faruwan alamarinmu yayi dai dai da fashewar madubin tsafin Amir Ukshe, acan kashmir kuwa gidan guru ne ya kama da wuta, har dashi gurun bai tsira ba..
        Duk yadda mutane suka so taimaƙonshi abin yaci tura, haka suna ji suna gani ya ƙone ƙurmusu. Gidan da yake ciki kuwa ta rubta cikin kar kashin kasa, kamar ba a taɓa wanzar dashi ba a gun.
        *Karshen taɓaɓɓe kenan*

     ***
     Amir Ukshe kuwa wani mugun mafarki yayi, ana binshi da gudu garin ceton ranshi ya faɗa cikin Rami.
Da Ihu ya farka sai me bakinshi a karkace, gefenshi na dama tashanye har da bakinsa, duk yadda yaso magana ya kasa karshe dai tashin hankali da baƙin ciki yasanya yayi sumar dole.

    ...... Alhamdulillah Abu Zarri jikinshi kam da sauki, dan kuwa har yayi magana bayan amfito dashi daga gobe da nisa.
.......
             Bayan kwana uku.....
     A hankali nake buɗe idanuna har suka buɗe tar Hindu, Salmah, Mujahidah, Azrah sune nagansu a zagaye dani a ɗaƙin Azrah. Mikewa naso yi, Azrah ta mai dani tana cewa.
"Kiyi a hankali jikinki da ciwo fa,"
  
   Mai da kaina nayi tare da lumshe idanuna, kwalla na zuban min.  Juya musu baya nayi, kuka nake sonyi taki zuwa. Ji nayi kamar na jika jikina na  saka hannu zan duba naji an rike min hannuna. Juyawa nayi naji tsigar jikina ya tashi da wani irin tsoro ya cika min zuciya ba kowa bane ya rike min Hannu sai Abil ɗan gidan Amirsh Raziya.

              Ja nayi da baya, ina girgiza kaina, tare da sauke wasu kwalla masu zafi. Cewa yayi.
"Ku fita dasu, naji da wannan kazar wajen."
           Kuka ne ya kwace min haɗa hannuna nayi cikin tashin hankali sabida har yanzun ban daina tuno muguntar da Ashraf yayi min ba. Yau ga wani zai kara min, haurowa gadon yayi tare da niman taɓani, na sake kara me karfi na faɗi kan matashin ts baya, murmushi yayi sannan yace.
"Taimaƙonki zanyi naji ance wani ya kwashi daɗi a jikinki shine nima nazo jin ya tak..."

      "Yana da kyau ka tsaya a kan abinda ya zame naka bashiga hurumin da bana kaba, ku kaishi gidan horo."

     Inji Sultan Ashraf wanda Ghaniyu ya turoshi a keken guragu, sakamakon yadda baya juran dogon tafiya.
       Fita akayi ds Abil, kura min ido yayi yana kokarin tabbar da kanshi da gaske abinda yaƙe jin kamar mafarkine ya faru. Dagaske ne daman,

*A'a mafarkine? Anya ƙuwa Wacecen ita? Daga ina take? Meye ya kawota?*

Tambayar da bai da amsarsu shine yake tayiwa kanshi. Danna wani abu yayi a jikin keken ta turashi gaban gadon, hango goran ruwa yayi, ya ɗauka tare da buɗe bakin. Ya tashi daga keken ya koma bakin gadon, ya haura sosai. Ruwan ya kurɓa ya furza min a fuska.
"Wayyo Allah Ummina! Don Allah karka min."

    A firgice na tashi, tare da ƙamƙame jikina, na fashe da kuka kai. Kai hannunshi yayi zai taɓa ni, na kuma sake masa kara tare da zuɓewa a sume, kallona yayi cikin tashin hankali sak irin wannan muryan yaji a mafarkinsa, gyara min gashina yayi sakamaƙon hautsinewar da suƙayi.

Shafa gashin yayi yana jin yadda suke da laushi da tsantsi loƙaci ɗaya, karewa fuskana kallo yayi. Wato mutumin da bai da tsoro ranar da ya tashi tsorata yafi kowa tsorata.

Sauka yayi daga gadon, har zai juya idanunshi ya sauka akan jinin da ya ɓata inda nake ƙwance.

D'agani yayi yaga baki ɗaya kayana sun jiƙe, ta baya.
"Ghaniyu!!"

"Umarninƙa nake jira!"

"Dr Fu'ad."
Sauka yayi daga gadon ya koma gefe yana kallona, cike da tashin hankali. Bayan kamar minti goma sha biyar sai gasu nan fita Dr Fu'ad yace suyi. Ya cigaba da dubani, sosai ya fahimci matsalata sannan ya shawo kanta, fitowa yayi ya miƙa musu takrdan magani, yace.
"Ranka ya daɗe, karku takura mata har yanzun bata fita daga firgici bane dan da alamu wanda yayi mata fyaɗen ya gwada mata rashin Imani dan yaji mata mugun ciwo wanda yayi sanadin da sai da nayi mata ɗaki a ciki, ciwon da tajine ya haifar mata da zubda jini amma Insha Allah nan da sati zata warke."

Kanshi a sunkuye ya jinjina maganar da Dr yayi mashi,
Bayan fitar likitan , ranshine ke ɓaci danna abinda zaisa keken tafiya yayi ranshi na kara ɓaci kamar zata kama da wuta, duk yadda Ghaniyu yaso taimaƙa mishi abin yaci tura.

Cikin fada ya wucce, ba zato batsamani, ya wucce buɗe masa kofa aka fara yi,.har ya isa cikin fadar kujearan da yake mallakinsa ya tunkara tashi yayi ya zauna.

Duƙ wani wanda yake da ruwa da tsaki a masarautar sai da ya shigo faɗar, kanshi a sunkuye yace.
"Ina Amir Ukshe? Ina Amir Abu Zarri? Meke faru? Na bada awa goma a tattaro min duƙ wani abinda ya faru daga ranar da nacika shakaru Ashirin da tara, zuwa yau, ko kuma nasoƙe mukamanƙu. Daga yau na dawo kan kujerata babu wanda zai umarcrni sai dai ni na umarta duk wanda na kama da laifi wallahi billahil azim zansaka Shafiq ya gutsire masa kai"


Yana gama faɗar haka ya sauka ya koma kan kekenshi sannan Ghaniyu ya turashi suƙa bar cikin fadar. Ranshi kara ɓaci yake idan ya tono abubuwan da suka faru suna shiga cikin ya juya tare da kallon Ghaniyu yace.
" Ka gaya min meke faru? Shin nine na lalata mata rayuwarta? Ka gaya min meye ya faru da ita."

... Kan ghaniyu a kasa ya shiga bashi labarin abinda ya faru.
"Lokacin da muka zo nida Sheik Habibullah, munxo mun sameku cikin wani mugun yanayi, ita tayi dogon suma. Kai kuma kana barci, nan dai muka kira Azrah taxo ta fidda ita tare da kawayenta, kai Sheik da almajiranshi suka maka ruki'a anan aljanin yake cewa daga cikin masarauta aka turoshi amma wanda yayi aikin ya mutu, karfin zamanshi a jikinka zoɓen nan ne, abinda ya faru daku, shi ya karya kashi sittin na karfinsu koda aka kaita can gun bayi.Azrahce take kula da ita ga kuma Amir Ukshe da Amir Abu dasuma ba lafiya.. Har samun labarin da naji Abil zai kai mata farmaki har zuwanmu..."

" Da gaske ba mafarki nake ba? Na cutar da ita?" shiru Ghaniyu yayi fashewa da kuka yayi sosai sai da yayi ya ishe shi sannan yace.
"Ghaniyu ban taɓa zina ba a rayuwata. Me yasa sai ita? Ga mata birjin me yasa sai wacce takame kanta ghaniyu na cuceta Innalillah.."

Rike kanshi yayi wanda yake masa wani irin sara kamar zata fashe. D'akinshi ya koma ya zubawa gadon ido bakin ciki na ƙara ciƙa mishi zuciya ji yake kamar ya haɗiyi zuciyarshi,tsanar mulkin ya kara cika mishi zuciya. Wani mugun ɓacin rai yake ji tabbas a wannan yanayin duk wanda ya kuskura tunkareshi da wani abu zai iya bada umarni a sauke mishi kansa yadda yake ji ba sauki sai na Rabbi.

.........
A can shashinmu ban kuma farkawa ba sai bayan sallar magrib, a hankali na sauke kafafuna daga gadon sannan na mike akan kafaffun sai ji nayi jiri ya kwashe ni zan xube. Azrah ta tare ni.
"sannu ki barƴin kome da karfi."
Tace min, gyaɗa mata kai nayi. Cikin nutsuwa na wucce ban ɗaki tsarki nayi sannan nayi alola nafito. Abin sallah sallah nasamu tashinfiɗa min, a sannu na fara gabatar da sallar dake kaina, inda yake bani wahla, ruku'u sabida cinyoyina da suke ciwo.

Ina gab da idarwa dan har nayi tahiyya, kawai sai ji nayi kaman Ashraf ya rungume ni, bansan lokacin da na fasa ihu ba na shiga kame jikina,
Wasa wasa sai ga sanadin haka yana shirin taɓa min kwakwalwata, dan sai da Azrah takira Ghaniyu shi kuma yaje ya gayawa, Ashraf tunda na ganshi na rufe idanuna gam tare da rike jikina, ina sauke a jiyar zuciyar daga karshe na kama barcin dole.

Ficcewa yayi daga ɗakin. Kafin gari ya waye Ashraf yayi kusan sawu goma yana xuwa dubani, zuwanshi na karshe ne ƴazo yasamu ina sallah, dukda tausayin da yake ji bai hanashi cewa Ghaniyu idan na warke na dawo bakin aikina, dan ina bukatar na.....



#MJ#HZƘ#Vote........


Oum Muwaddah...💄
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: *_HAZAƘA WRITER'S ASSO_*

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

*_Gaskiya naji daɗin yadda wasu suƙe tambaya game da Nasabar dake tsakanin Safeenat da Sultan, wasu kuma suna tambaya akan meye dangatar Kabilu guda uku nan... Idan me karatu bai manta ba  ya ƙoma shafin farko na labarin inda na faɗi kabilun da suƙa kafa masarautar... Duk da na warware muku kabilun amma har yanzun kuna rayuwarƙu tana cikin ƙwale ƙwale😁😂 May god bless oll ɗinku_*



Page.١٥
   Da sauri Ghaniyu ya ciro wayarsa ya kira Dr Fu'ad, ya gaya mishi halin da Sultan yake ciki,  cikin mimtuna ashirin da biyar ya iso gidan, yasame Ashraf kwance ya rike marar shi baya ko numfashi buɗe akwatinsa yayi ya dauƙo drip ya saka mishi sannan ya gyara mishi kwanciya ya kalle ghaniyu yace.
"Yaushe ya fara wannan ciwon?"
     Shiru ghaniyu yayi dan baya son tona sirrin uban gidanshi, kawai ya fahimci tun ranar da ya samemu cikin mugun yanayi ya jefa Ubangidanshi cikin mugun yanayi, har zuwa yanzun da ya faɗi.

           Cigaba da aikinsa Dr Fu'ad yayi yana gamawa ya miƙawa Ghaniyu takarda yace.
"A nima masa maganin nan zai taimaka masa gun rage ƙarfin abinda yake ji."
       Tattara kayanshi yayi yace.
"Allah yasawwaka idan ruwan ya ƙare ga yadda zaka zare mishi."

     ...... Bayan fitar shi Ghaniyu sai da ya zauna har drip ɗin ya kare, sannan ya zare daga jikin sannan ya cigaba da gadinsa har ya farka....

     Dakyar ya miƙe yana dafe goshinsa, kauda kanshi yayi cike da kunya, ciji lips ɗinshi yayi yana shafe gashin kansa tsuke fuska yayi sosai yana wani cin magani yace.
" Fu'ad yace wani abu?"
  
    (Wai nace ɗan renin hammata cin maganin naye😏)
       Sunkuyar da kai Ghaniyu yayi sannan yace.
"A'a ya shugabana, ga takardan maganin da ya bani"

   Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
"Toh wancan yarinyar fa?"
     
    Cike da mamaki da ban dariya, yace.
"Wacce yarinya kenan?"
    
  Takar wanda ghaniyu ya shika mishi ashar ya kuma tamke fuska cikin jin haushi kamar ya rufe ghaniyu da duka ya kauda kanshi bai kuma magana.

"Tuba nake ranka shida. Safina kaƙe nufi tana c..."
   Fitowata yashi yin shiru kasa kasa yace.
"Ranka shi daɗe gata nan tafito."
   Mikewa yayi ya wucce cikin ɗakinshi, ni kuma na wucce kitchen na shiga kokarin ɗaura abincin rana.

       ***
   Wani irin rayuwa muke a cikin gidan, tsakani da Allah Ashraf ya hanani sakat, idan yana gida bana iya sakewa dan yadinga bina da ido ƙenan. Yadda bazan fahimci ni yake kallo ba.
       Lokaci guda kuma magoya bayan Amir Ukshe sun shiga zanga zanga, akan soke shi da akayi, dukda manyan cikin fadan sun haɗe kansu dan su nuna mishi suna sama dashi, kuma sun fishi a shekaru. Shi kuwa ya shiga dakatar dashi, dan sun rantse ba zai kai labari ba, dake kainuwa ne Allah ya cigaba da kare shi duk yadda sukayi babu abinda yake raguwa sai ma karuwar da yake, samu na karfin iko.
         Kuɗin da Amir Ukshe ya kwasa shi ya dinga cusa musu suna mishi bori, shi kuwa ya musu tsiya inda ya datse asusun su baki ɗaya, ya kuma saka aka katse musu wutarsu tare da iskar gas ɗinsu. Yaransu da suƙe makarantu a kasashen waje ya saka aka dakatar dasu, duk wani logonsu sai da Ashraf ya karya kafin yasami nutsuwa, suma suka shiga hankalinsu dan yanzun sun fara shakkarsa har suna cewa ya fara mulƙin kama karya.
         Dama ya-ya mutanen da suƙe ji da izza da jin kai ina kuma ya haɗu da mulki, lokaci guda salon mulkin matashin sarki ya taɓa zuciyar mugaye suka cigaba da mishi kallon angulu da kan zabo.

       ***
Yanzun kusan sati uku kenan, da farun tsautsayina da wancan shashashan.. Sunan da zuciyata ta amince min nakirashi da ita kenan. Ina jera abinci ya fito dashi sai dogon wando da bakin singlet, kau da kaina nayi, da sauri na bar gun ko kallon abincin bayi ba ya zauna a kujeran falon yana kallo,

    Zuwa nayi na dauki filet ɗin na fara kokarin zuba mishi abinci.yace
"Ina azumi."

      Kutt nace a raina, wato ga yar iska na gama wahala yace min yana azumi, kallon agogon nayi naga karfe tara haushi naji na fara cin abincin juyawa yayi yaga na zauna ina ci.

      Shafa sajenshi yayi sannan ya kara karan, tv yadda ya kure volume ɗin, haka kawai naji zuciyana ya fara tashi, cigaba da tura abincin nayi dan kuma tun ina girkawa karnin namar kasar take hawa min kai, yunkurin amai nayi na tashi da sauri na faɗa ɗakina naje nayita kwarawa, sai da nayi ya ishe ni. Sannan na zauna na wucce gajiya, kafin na gyara ɗakin tass.

          Na fito daga ciki nazo na tattara na waje, ina cikin gyara gun da aman ya taɓa sai ga Dr Fu'ad, tawowa Ghaniyu yayi yace.
"Yar uwa! Kizo ga liƙita zai duba ki, ashe baki ji daɗi ba."

          "Ni kuma za a duba kai ni lafiyata lau, kace yaje abinsa. Ni bani da matsalar kome."

       Duk yadda suka so dubani fir naki, nace lafiyata lau.

...dan hka likitan yayi tafiyarshi.

  ...... Abin mamaki baya karewa ina gab da karasa abinda ya kawoni, na fara wani irin zazzaɓi da dare zan kwana banyi barci ba sai asuba, kullum sai na makara, ga wani shegen yawun da bana iya haɗiye shi, idan nayi yunkurin haɗiye shi toh amai zantayi kamar hanjin cikina kamar zasuyo waje.
   Sam ban taba duba wani abu yana damuna ba, kawai na ɗauki haka a matsayin zazzaɓine.

          Yau na tashi da wuri dan idar da kudirina, dan haka ina gama abin karyawa na buɗe kwalbar guban na zuba a cikin ruwan coffee ɗin da nasan da ita yake fara sha. Dukda nasan cikin biyu za ayi ɗaya, ko na mutu ko

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment