Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

  Yau kwana biyar kenan, kullum sai anzo an ɗauki yan matan ɗakinmu ba, ba'a dawo dasu sai dare. Ashe da ina cikin kariya ce zamana a shashin Sultan ƴanzun kuwa, ina cikin hatsari domin kuwa sau biyu ana farmaka na,

                   Karshe komawa d'akin Azrah nayi, naje na zauna. Ita kam ana ɗan shakkarta.
                Maidani kitchen akayi na cigaba da aikina, sam hankalina yaki ƙwanciya da tafiyar da akace Sultan yayi.
    Azrah nasamu da cewa.
"Mama! Hmm nifa ina jin akwai matsala zanje na duba gidan Sultan."

       Shiru tayi tana kallona can tace.
"Ki bari mana idan ya dawo sai muje dake ko?"

            Gyaɗa mata kai nayi badan nason ba, dole na hakura dan kwanakin da zanyi ya fara karatowa, dan yanzun saura wata ɗaya da sati biyu.

       ***
Sati biyu da suka wucce.
A ɓangaren Sultan kuwa, tunda ya shiga gun shagalin aka cigaba da hidima, har loƙacin sallah ya wucce, bayi ba, sai dare wajen sha biyu ya koma gida, dake sun sunja hankalinsa sosai har yasha wani ruwan inabi, tun daga sa'ilin yaƙe jin shi a buge, koda ya dawo gidan dakyar yayi sallah ko addu'a bai yi ba, ya kwanta.

         Tunda ya kwanta yake jin wani irin sanyi, a hankali yaji wani iska me karfi ya shige shi, bargo yaja ya rufe kanshi.
                      Daga nan kuma bai same ke faruwa ba.
     Washi gari da asuba Amirah Raziyah tazo taga halin da yake ciki tafita bayan ta kwashi kusan awa guda a cikin gidan. Da karfe goma Amir Ukshe yazo. Yaga halin da yake ciki jan kofar shiga gidan yayi ya rufe.

              A sannu gidan ya koma kamar irin  mugayen gidan nan matattaran shaidanu.  Gidan yayi wani irin datti, yanar gizo gizo. Sannan daga nesa kaga gidan zaka rantse yakai kimanin shekara ɗari ba kowa, sannan Masu tsaron gidan ma Yanzun ba kowa, suma sun koma cikin fada.

                ****
   A cikin wata guda kome ya nemi lalacewa, daga ciki har da samun gawar Angela, wacce Sultan ya saƙeta.
     Wanda ya haifar da wani irin rigima, gashi yaki ci yaki cinƴewa dan kullum sai anyi kamar za'aƴi bata kashi.  Karfi da yaji Amir Ukshe yake gudanar da Zalimci. Da Abu Zarri yaga haka shine yaje har gidansa nan ya samu Raziyah itama tana ruwan bala'i.
          Cikin son zaman lafiya Abu Zarri yace.
      "Meke faru? Sannan ina Sultan? Me kuke ɓoyewa."
          " Me kuwa zan ɓoye muku bayan kunsan baya gari kunemi shi mana."

      "Wannan shine karya! Kai kasan me ka masa."
  Inji Raziyah.
          Duk yadda suƙa so Ukshe yayi magana yaki sai suka shiga, koƙarin sanin gaskiya.
       ........ Nima nayita bin Azrah amma taki bani goyan baya, abinda na fahimta akwai abinda taƙe ɓoye mim dan har anzo an min barazana za'a kashe ni matuƙar na shiga maganar sultan.
           Nayi Imani da Allah akwai me ƙoƙarin kai gulmata, dan haka na shirya ranar bayan sallahr asuba, dake kitchen zan nufa sai na fita daga gidan na wucce gidan shi, dakyar na shiga, sabida yanar gidan. Ina tafiya sai naji abu ya wucce da bala'in gudu ta bayana ina juyawa zanga ba ke.
     A haka har na tura kofar ɗakinshi bakina ɗauƙe da ayatul ƙursiyu.

          Ihu akayi wanda ya tada tsigar jikina, har sai da na toshe kunnena.
         "Meye ya kawo ki duniyata. Nasame gangan jiki zaki zo ki rabani dashi."
   Dif naji an faɗo a bayana ina juyawa na ga Ashraf a cikin mugun yanayi ihu na saƙa, aikuwa yayi wurgi dani sai da na bugu da bango. Gabaki ɗaƴa jina da ganina suƙa ɗauƙe na wuccin gadi.
     Tsalle yayi ya diro gaba, kafin na yunkura yasake kwallo dani, sai da na bugu da gadon sosai.. In samu arzikin ihu ma gatane, ƙoƙarin shiga.kasar gadon na fara yazo ƴa finciƙe ni ya cillani da jinki mirorr, tsabar wahala har sai da nayi aman jini.
              Ya karan buɗe kofa naji idanuna dishi dishi, banga waye ba. Sabida bana gani sosai.
            Gurnanin shi naji ashe wai nima yake, dan gun mirror ɗin aƙwai shirgin da ya tara, mikewa nayi tare da kama jiƙin mirror sai gashi dif kamar an jiwo shi daga sama, ja da baya na fara, ina son yi addu'a amma bakina yayi nauyi.
                 Cafke wuyata yayi dan wani irin zafin yake da kafin kayi wani yunkuri ya cin maka.
         
              Ina ambaton Allah ihu yayi tare da  cillar dani , na mike zan fita mukayi karo da Ghaniyu, da sauri ya cilla ledar da yakawo mishi, sannan ya jani muƙa fita.
              Ya kulle ƙofar, sai da muka bar cikin gidan ya hankaɗani cikin tuhuma yace.
"Ba yau na fara zarginki ba, dan sam baki kama da baiwa ba ƙo wacce ta tashi cikin wahala wacece ke?"
 
    Goge jinin dake baƙina nayi sannan na sunkuyar da kaina.
   
  "Bazaki min magana sai na kaiki gun Amir Ukshe?"

      Idanuna ne suka ciko da kwalla nace masa.
   " Safinatu Badr Ibrahim"

    Kura min ido yayi cike da mamaki yace.
"Ke! Wani hauka ne ya kawo ki nan, haba shi yasa kika nace da yawa ashe ke Jinin Badar ce toh zan baki shawara ki haɗa kayanƙi ki bar garin nan ko kuma ki su wulakantaki."

     Girgiza kaina nayi cikin gaji nace.
"Babu inda zanje, dan nayi alkawarim sai na maidawa Nannah D'anta."

     "Kin hauƙace?"
     "Eh da alama amma bacan can ba, yawwa kaga halin da yake ciki ƙo zaka taimaka min ka nima mana malamin da zai taimaka mana ayi jinyarsa dan naga abin nashi kamar jinn n"

      "Lallai baki da hankali nima zuwan da kika ga inayi, abinda zai ci nake kawo mishi idan aka san cewa muna zuwa nan dagani har ke sunanmu matattu. Kinga muje kafi."

   Kwace arm ɗina nayi da ya riƙe, cikin ɓacin rai nace.
   "Me kake kawo mishi?"

   Katsaye yace min.
"D'anyen nama."
   Ban san loƙacin da amai ya tazo min ba, sai da nayi tukun nace.
"Wani irin rashin imani ne haka? Taya zaka bawa mutum me rai ɗanyen nama?"

      Cikin damuwa ya kalleni sannan ya ce.
"Amir Ukshe ne yasani dan har da jin.."
   "Jini??? Kamar mayye sabida Allah zaku maida ɗan adam kamar Daba aiko kuraye da karanunka basa shan jini, ni dai ka nimo min, gidan wani malami mu kaishi idan bazai yuwwu ba mu kaishi ba, sai ina aka taɓa yin haka." na faɗa cikin faɗa.

   Kallona ya tsaya yi ganin yadda na kafe kamar kaska, ajiyar zuciya yayi sannan yace.
"Zan nima miki amma babu ruwana."
   "Ai idan zaka cire  babu ruwanka ka cire , domin ana kama ni kai zance kasani ka gane."

     Kallona yayi ciƙe da takaici yace.
"Amma baki hankali ke mahaukaciyar ina ce? Da zaki min sharri"

       Gaba nayi abuna dan nasan dole yayi min abinda nace Har na kusan fita yace.
"Karki a ƙowa yasani amma ki faɗawa  Azrah" nan ne na cibirki na juya na gaya mishi yadda muƙayi da ita.

   "Eh ai nasani dan mun yanƙe hukuncin karmu gaya miki sabida yadda kika damu akanshi."

   zaro ido cike da takaici nace.
"Ta ina na damu? Kawai naga bai dawo da wuri bane shine nake tambayarta."

(😾 Malama stop firintandi😰)

    "Koma dai menene kibi a sannu gudun karki wurga kanki cikin matsala."

_Sorry ban muku alƙawari ba, amma idan nasami kaina zaku ganni Kamar kullum muna fama da rashin wuta_

#MJ#Vote#Sulfee

Oum-Muwadda🍢
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: *_HAZAƘA WRITER'S ASSO_*

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

Page.١٠



     Mik'ewa  nayi  Cikin Sanyi  jiki. Ina  kallonshi kauda kai yayi sannan  yayi  gyaran murya,  ghaniyu me shigo cikin  girmamawa  yace.
"Umarninka make jira."
     
    Kamar  bazai  magana ba. Ya d'an  motsa  labb'ansa  YA tauneta sannan  ya  d'an  lasheta, kasa-kasa yayi  da  murya yace.
   " ka canza  min wani"

          Kallon  mamaki  nake  musu, Ina  tsaye aka sake  sabon  kujera, zuwa  yayi  ya  zauna tare  da juya  kan kujeran, bansan  ya akayi  tsaki  ya  kwace  daga  bakina ba,  bai  d'ago ba  Dan yasan  nice zanyi  haka,
                 Mamakine  ya  ya  rufe ghaniyu, tunda  yake ba'a  tab'awa  sultan  abu bai sa ayi hukunci  ba  sai  yau,  a madadin  ya  sallamemu  sai  ya kyalemu a tsaye  ya cigaba da aikinshi.
       Wasu  takardu ya kwaso zai fara cike musu, dukda  ban  duba  tarkadun ba,  amma na fahimci na cuwa cuwa ce.
    
  "Wallahi Allah sai ya tambayeka , abisa dukiyar alumma  Da ake b'arnatarwa, anya kana tsoron Allah."

           Fuskarshi kawai zaka kalla ƙasan maganar ta buge shi sakamaƙon yadda jijjiyar goshinsa suke fito ɗara ɗara.
   "Kai min ita ɗaki."
  
       Ji nayi cikina ƴa hautsine, ciƙe da damuwa Ghaniyu ya kai hannunshi zai kamo ni nace.
"Basai ka kaini ba! Ni zan kai kaina ka gane ai ba yau ka fara ba. Amma nasan daga yau bazaka kuma ba, idan nice kai basai san kaini ɗaki ba ko a iya nan zak...."
 
      Ɗagowa yaƴi idanunshi har suna wani oil tsabar ɓacin rai gashi sunƴi jajjur.
            Ya kalle kofar fita juyawa Ghaniyu yayi ranshi ba dad'i, har yakai bakin kofa ƴa juyo. Cikin ƙanƙar da kai yace.
"Ya shug...."
    Yadda ya kalleshi yasa shi fitar dole, ji yake kamar kanwarshi za'a tozarta,
       
      Takowa yayi gabana, ganin yadda nake haɗiye yawun tsoro, dukda shi ba ma'abocin dariƴa bane sai da ya sake fuskarshi, lashe pink lips ɗinshi yayi sannan yashafe kwantacciyar sajenshi, juƴawa yayi yabarni a gun.

            Ajiƴar zuciya na sauke, sannan na koma kitchen fitar da bamuyi ba kenan, bamu kuma haɗuwa ba sai da karfe biyu, lokacin abincin rana. Yau a tantirance ya fito min dan daga shi sai gajeran wando iƴa gwiwa, da singlet fari ƙal. Sau ɗaya na kalle shi ban kuma ba, dan tsabar tsoro jikina rawa ya kama, kusan dalili sabida ban saba ganinshi a haƙa ba, ban saba ganin kanena suna wannan shirgar ba.
       Gashin kansa ke ɗigar da ruwa, yana sauƙa akan karamin towel ɗin dake kafaɗarshi.  Zare towel ɗin yayi ya cilla min a fuskana,
         "Ƙambu" nace a fusace, *"Me wannan ɗan renin hankalin yaƙe nufi nice zan goge mas."*
               Buɗe mishi kular abincin nayi zubawa Mansaf ido yayi. Na fahimci ita yake so, zuba mishi nayi sannan na saka mishi falefale, a gefe sai dafeffen ƴ'aƴ'an zaitun da karas, wanda na ɗiga man zaitun da khaltufa.

             Sai fruit juice wanda na jefa mishi ƙanƙara.
     Kin cin abinci yayi, kanshi na duke.
        Ɗaukar towel ɗin nayi naje bayanshi, jikina narawa na fara goge masa jekakken gashinsa. Wanda nake shakar kamshin sinadarin da aka wanƙe gashin da shi.
   "Hand drie"
       Sake goge kan naƴi na nufi ɗakinsa, ina zuwa nasamu akan gadon har na ɗauka zan fito sai na koma jikin mirorr ɗin na kai hannuna zan ɗauki mai sai na fasa wani ɗan karamin kwalbar turare na gani.

    Tsautsayi yasani ɗauƙa, kaman wanda aka maƙe hannuna ya faɗi aikuwa ya fashe. 

(🙊😏 Zaki sani bake wauta ba)

           Zaro ido nayi, na shiga tattara kwalban. Na zuba a cikin mazubin shara, daƙe cikin ɗaƙin. Banda rashin kai irin nawa sai na goge turaren da ya taɓa hannuna, a jikina sannan nafito. Ina zuwa ya shaki kamshin turaren, cigaba yayi da kwasan gyara bai bi takaina ba. Tsauwar jiranshi nayi har ya ƙare cin abincinsa.

          Sannan na jona wayar na fara busar mishi da gashin.
       "Kinsan kuɗin turarene?"
       Shiru nayi ban iya cewa kome ba dan nasan nayi masa ɓarna ko ma dai nawa ne,
       Ina gamawa yayi gƴaran murya sai ga Ghaniƴu, komawa cikin falourn ƴayi, sannan yace.
     "Ku kaita ɗakin horo."

    Zaro idanu waje nayi, kamar zan fasa kuka nace.
   "Yarintar ta motsa ko?"
      
          Banga fuskarshi ba amma ina da yakinin yaji ciwon abinda nace masa,
.........
           Fita dani ghani ƴayi, sai da ƴa masifance ni, sannan yace.
"Don Allah ki bar lakatanshi, sam bai san meye kawazuci ba."
     Dariƴa nayi sosai nace.
"Toh ai gashi a bayanka."
             
    Hmmm Sultan Ashraf mugune na bugawa a jarida, dan daga ni har Ghaniyu jikinmu sai da yayi laushi kuma ya sauyawa Ghaniyu gun zama zuwa bakin get, aka kawo wani me kiran mutanen farko Irifan.

          Gaskiya zan iya daga jiya zuwa yau na zama kamar jaka, matsalar da na fara fuskata shine Irfan ɗan iskane, dan koda ɗakin horo zai kaini toh ƙoƙarinsa yakai hannunshi kirjina.
                   ***
Ƴau saura kwana uƙu bikin murnan zagayowar ranar haihuwar Sultan wanda aka shirya a babban falon shashinsa.
                  Sun kawo takardun list ɗin abinda suƙe bukata na gyara falon da Cake ɗin da za'a kawo mishi na ranar, zunzuruntun sun kware a sata, wasu mahauƙatar kuɗin suƙa yanka mishi.
   
      Kai tsaye ya soƙe musu yasa abinda yake ganin shi zasu buƙata.
...... Sunji Haushi dan wanda ya kawo takardun Abil ɗan Raziƴa. Da fushi ya nemi barin gidan amma ya dakatar dashi.
   
   Kawo mishi ruwa nayi zan wucce naji ya kai min duka a baya, juyawa nayi na tsinka mishi mari.  Fuska Sultan yayi ya cigaba da kallonshi, kamar baya gun, yasa fuska. Mikewa Abil yayi cike da mamaki yadda na zabga mishi mari, amms Sultan bai ce kome ba.

                   Finciko ni yayi tare da murɗa min hannuna sai da kashin yayi kara. Ihu na saka ciƙe da jin azabar  a hannuna,  bai fasa ba murɗa min hannu ba har sai da yaga ina kuka sosai sannan ya hanƙaɗe ni na faɗi, sake take min kafa yayi, ihun da naƴi ne sabida ji min ciwo da yayi a yatsun kafana,

       Bai ƙƴale ni ba sai da yaji min ciwo a duk kafa, sannan ya suri takardan yace.
"Na kƴaleki amma kika ɓari na kamaki, sai na jiyar dake azabar da baki taɓa gani ba, dama ance ku kajin african sunfi na ƙo ina zaki dan.,"

  Gyara murya Sultan yayi sai ga Irfan ya shigo, ciƙin girmamawa yace.
    "Gidan ladabtarwa zaka kaishi"

          Aikuwa suka kaɗa keyarshi zuwa gidan ladabtarwa. Mikewa yayi ya bar falour, dakƴar na iya jan ƙafana zuwa kitchen. Nayi kuka sosai dan sai da na gasa kafar. Dukda ciwon bai sa Sultan hakura da abincin dare ba sai da na abinci mara nauyi....

       Ƙin ci yayi ya sunkuƴar da kanshi yana latsa wayarsa. Ga azabar ciwo ga wulakanci, na koma cikin sauri na fara ƙoƙarin ɗaura wani sai jin murƴan mutane suna dariƴa irinta abota. Kaman ance na leko Sultan ne da wani matashi me sanye da kayan gidan abinci. Murmushi kawai yake doƙawa, mutumin sai dariya yake,

     Suna hira zuwa yayi gun dinne table ya ɗauki filet yaje ya juƴe abinda ya kawo masa, yasa a gaban sultan ɗin.
    
      Maqbul ce sai kamshin citta da garlic yake, ji nayi raina yayi mugun ɓaci ina can ina fama ciwona ashe ɗan renin hammatan yana can yayi odar abinci.

           Sauke abinda na ɗaura nayi na zauna akan kujera, ji nayi duk na kuntatta baki ɗaya,
             ...... Ina jin hirar su har suƙa watse, amma baƙon yafi surutu, dan ɗan akida baya faɗar kalmar da ta haura uku,
                   ***
Washi gari da safiya, sai ga Amirah Raziyah tazo, bansan shigowarta ba sai ji nayi an rufe ni da duƙa, ta ko ina.
             Duka sosai yana ɗakin motsa jiki yaji hayaniya, shine ya fito har zuwa kitchen ganin kanwar Mahaifinshi tana ɗaukar doka a hannu kamar yadda ɗanta ya ɗauki yayi rashin hankali.

                "Ina jiranki idan kin gama."
        Yau kam naji har ya kara da na kullum, juyawa tayi a fusace tace.
"Ashraf! Akan me zaka sa a wulakanta min D'ana."
      Ba kulata ba yayi wuccewarsa ciki biyoshi bayanshi tayi, kamar zata tashi sama.
           D'akinshi yashige bai fito ba, sai da ya share awa biyu cur, sannan ya fito ƴa zauna gun cin abinci, buɗe abinci nayi.
        Kallon roasted nut yayi da kuma, soyayyar kwai, sai golden macarroni, wanda na dafa da namar gwangwani, na zuba masa, mai da dubansa yayi kan butar Coffee, garin zuba masa kwalla da suƙe zuba a idanuna ya zuba cikin tea ɗin, duk abincin haka kwallana ya sauka a cikin.

            Mika min towel yayi nazo bayanshi ina goge masa gashin kansa, Amirah Raziyah ce tazo ta zauna, daƙe bai bani damar nasa mata ba, ita da kanta ta zuba kome. Tana shirin fara ci sai ga Amir Ukshe. Zama yayi shima, Amirah ta zuba mishi abinci.
    "Hand..."
  Bai kai karshe ba na bar, ina gab da shiga ɗakin yace.
"Don't touch anything."
              Shigewa nayi, kallonshi sukayi sannan suka maida kallonsu ga junarsu.
     Kowannensu yana fatan samun nasara akan abokin gwabzawansa.

           Ina shiga naga wata arniyan suit ɗin da zai saka, silver ce tayi kƴau iya kyau,    kallon laptop ɗinshi nayi wacce take kunne, haka kawai naji ina son duba. Email ɗina tunawa da nayi yace kar na taɓa kome, ya sani juyawa, aikuwa mukayi karo dashi. Inda kaina ya bugi kirjinshi bai damu ba ya raba gefena, ya kalle ni da wutsiyar ido, a ranshi yana cewa.
   *Bata jin magana*
   Fita nayi ya ɗauki files ɗinshi, ƴa fito ƴazo ya same ni a tsaye zama yayi naje bayanshi na fara aikina, ina gamawa na bar gun dan na lura da magana a bakunansu.

       Ina barin gun kuwa Amirah Raziyana ta ajiye coƙalinta tace.
"Ashraf!!!"

            "Sultan zaki ce" kanshi a duke yayi maganar kamar bashi ba, cikin kuluwa tace.
"Naji Sultan a wani hujja zaka rufe ɗan uwanka? Me yasa baka abu da tunani ne, ka rufe min yaro"

       Miƙewa yayi ba tare da ya kallesu ba yace.
    "Ina son zama daku?"

      Mikewa Amir Ukshe yayi cikin ƙanƙar da kai yace.
"Sultan! Gobe zagayowar ranar haihuwarka, wanda yayi dai dai da ciƙa shekaru ashirin da shida a matsayin sarkin Jordan na huɗu."

    Gyaɗa kai  yayi  sannan ya juya, yayi taku biyu cike da kasaita yace.
"Gobe!!! Ranar zagayowar Mutuwar Iyayena!!! Gobe zan buɗe fadar sarkin Jordan A Gobe Inshs Allah zanƴi abubuwan da na gaza yinshi na tsawon shekaru da dama"
      Juƴawa yayi abinsa yabarsu tsaye,
   " Tabbas ƙome zai lalace gobe"
     Inji Raziyah,
      Taku kaɗan Amir yayi cikin ƙaɗuwa yace.
"Zan dakatar da kudirinka gobe."

            Fita suƙayi cike da tashin hankali fitowa nayi cikin murmushi nace.
    "Insha Allah nan da wata biyu zan rabaku dashi."

        Kowa idanunshi ya rufe, musaman Amir da Ra'ees ya gargaɗeshi akan kar su bari Sultan ya shiga fada, yau gashi ya ambaci mutuwar iyayenshi da maganar mulkinsa kenan dole ƴau ya nemi ra'ees.
            Itama Raziyah tana komawa gida takira bokanta na Turkiya.....


             Ɓangaren Sultan kuwa tunda ya shiga binciƙe a laptop ɗinss.....


     _Alƙawari ya ciƙa ƙo.....Burinsu d'aya muradinsu ɗaya.... Nashine ya banbamta da nasu....Itama nata burin nan....Nawaye zai ciƙa_

         '''Allah nagaji......Kuƴi manege idan nasamu hali toh amma banyi alƙawari ba.....dan bana ɗaukar alƙawari.....✌'''

*#MJ#HAZAƘA#VOTE*

Oum Muwaddah
         
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: *_HAZAƘA WRITER'S ASSO_*

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

 
*_Labarin daban yake da sauran..._*

Page.١٢

  "Iƴakaci suka kamani nace kaine kasani yin kome kuma kaga dole a yanke mana hukunci tare mu mutu tare." na gaya mishi haka,

  "Kee mahaukaciyar ina ce da zaki ce nine na saki wallahi karki jefa ni cikin matsala." yace min kamar zai fashe da kuka,
      Kauda kaina nayi tare da fashewa da dariya nace.
"Ka shiga hannuna, kuma dole ka amshi hukuncina."

    Ɓata rai nayi sannan nace.
"A kunnen Amir."

     "Shikenan na amince." murmushi nayi sannan nace.
  "Yawwa yaron kirki."

         Da sauri na bar gidan, ina addu'ar Allah yasa karsu nime ni, Allah cikin ikonsa, kuwa na shiga kitchen ina cikin taya wata, aikin sai ga Sahela. Tashigo duba girkin da muke tayi sannan ta kalleni cikin harshen turanci tace.
"Daga wata ƙasar kike?"
  
     Kauda kaina nayi sannan nace mata.
    "Senegal!"
         Shiru tayi tana kallona, sannan tace.
    "Ina son a girka min abinci me kƴau dan ina da bako daga masarautar marocco inda hali ayi mashi irin girkinsu, sannan a tsaftacce kome gudun faruwan matsala. Idan yaci lafiya ya koma gidanshi lafiya kuntsira idan aka samu matsala kuyi kuka da kanku."

    Tana gama zabga kashedinta ta cikawa bujenta iska. Ranar a kitchen muka wuni. Dan sai Biyar muka gama abincin. Shashinmu na nufa naje nayi wanka tare da gyara jikina, ina gamawa Ghaniyu na aikowa yana nima na.

      ... Da sauri na fita. Ina zuwa na same shi bakin kofar fita daga masarautar, a gaggauce yace min.

"Anjima zan zon da Sheik Habibullahi, dan ya duba Sultan."
 
        Gyaɗa mishi kai nayi san.nace
"Ince ba dai malamin tsubu bane?"
         
   "Eh gaskiya wannan baya cikin malam da kike tunani. Dan yasan abinda ya dace." yace min,

  
  Shiru mukayi dukkanmu muna sakawa da kuncewa a ranmu, katse shiru nayi da cewa.

"Dai ka tafi, anjima zan xo."
  Nace mishi tare da komawa cikin gidan.
       ***
*BANU NAZIR*
      
         "Ya shugaba! Sun kashe yarinyar ta hanyar bata guba ne da karfin tsiya, bayan Sultan Ashraf ya saketa, sannan ba iya kisarce matsala ba su shida suka mata fyaɗe, sam basu kyauta ba, sanadin haka kakanta ya kashe kansa."

         "Ba kashe kai bane! Kisan kaine kuma sun lakato tsuliyar dodo dan sai na girgiza masarautar baki ɗayanta, idan banyi haka ba, bancika ɗan halak ba."

       Inji Alexandra,
        
    Shiru manyan fadar Alexandra sauƙayi, kafin wani dattijo wanda ya fisu shekaru yace.
"Idan zaku yanke hukunci, ku dinga dubawa meke faru? A yanzun haka nasami labarin Sultan Ashraf ba lafiya."

    Yuuuu sukayi da idanunsu akanshi, suna jiran kanun labaran daga bakinshi. Gyara zama yayi ya faɗa musu abinda yake faru.
 
    Nan suma suƙa kulla tasu ta yadda zasu rusa jagorancin Amir Ukshe.
      
       ***
Da dare na fita tare da nufar gidanshi. Ina zuwa nasamu babu kowa, basu iso ba. Tsayawa nayi daga waje gudun farun irin wancan dukar dan har yanzun jikina ciwo yake.
   ......
A can cikin garin kuwa bayan lokacin da Ghaniyu yaje, yasamu an kawowa Malam Habibullah wata mara lafiya, yana fama da ita. Dan haka ya tsaya jiranshi.
      ***
"Ukshe! Yayi nasaran raba Ashraf da mulki tabbas dole na dakatar dashi dan bazan cigaba da ganin yana aikat..."
      Bai karshe ba ya

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment