Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki rabu dani ina da matar da zan aura."

       Rausayar da kai tayi cikin yanga da yauki, irinta goggagun Yan mata sannan tayi fari da idanuta tace.
"Dr! Nifa na jima ina sonka Nashiga a tabiyu"

      Murmushi yayi tare da jingina a jikin kujeran da yake Yace.
"Ke tun lokacin balki kike bina, karki manta kefa kawarta ce, zaki dame ni"

         Naɗe hannunta tayi a kirji tare da kallonshi tace.
"Wannan matsalar balki ce! Ni takaina nake."
    
      "Hmmm! Yayi kyau"
       Sako ya turo min tare da cewa.
   *Hey Beauty har yau fushin ne? Ina kewarki sosai har da yarana*

    Yana ta jiran reply amma fir naki tura mishi.
      
  "Dr Magana nake da kai! Fa kuma kayi min shiru."
  D'ago idanunshi yayi ya ɗaura akanta, sannan ya maida kan wayar ya kuma turo wani sakon
*Beauty kina gasa ni don Allah kiyi hakuri! Wallahi bani da wata bayan kenan*

    "Ina magana ka share ni."

Tattara abubuwanshi yayi da sauri ya mike zai bar officer ɗin, tayi maza tasha gabanshi cikin marairecewa tace.
"Don Allah kace min wani abu mana"
Duba wayarshi yayi da sauri ya fita ta gefenta.
Takaicine ya turmusheta ranta na kara ɓaci cike da jin haushi tace.
"Allah dan ni akayi ka, itama balkisun nice na rabaku."

Ta kuma bi kofar da harara, kamar shi yaƴi mata wulakanci.
***
Farcena nake kankarewa zan kuntsa lalle a hannuna da kafana, naji Sallamar Hajja Kaka, watsar da rezan nayi na tafi da gudu na rungumeta ina cewa.
"Wayyo Amaryan Dudu tazo ku fito mu fara Celebrat."
Tureni tayi cikin sababi tace.
"Dalla can, me kika samu wan salebirita. Zagi a fakaice, ina d'iyoyin albarka"
Shareta nayi nacigaba da gyara farce, dama can mun saba duk lokacin da muka had'u na nuna farin cikina sai ta disgani. Kuma tayi burinta ya cika, karan sako naji na jawo wayar naga sakon Dr..
*Gani a waje ina jiranki don Allah"
Banza nayi dashi.
"Ke hafiran banza akaina miskilancinki zai motsa,"
Shigowar Zakari da kayanta, ya sani kallonshi nace.
"Malam Zakari don Allah kacew.."
Ban karasa ba sai gashi ya shigo,
"Ke miskilar banza ba magana nake dake ba?"

Share su nayi nace.
"Malam zakari zaka iya tafiya."
Sannan na mike zan bar falon, rike baki tayi cikin salati da salami tace.
"Amma wannan yarinya anyi yar banza."

"Beauty!!"
Cak na tsaya ni banyi gaba ba ni banyi baya ba, karasowa yayi yana kallona yadda nayi kicin kicin da fuska, murmusa min yayi sannan yace.
"Don Allah bani minti ɗaya mana,"

"Ah barka da zuwa, Hajja! Dr kaima kazo kenan."

Cike da kunya ya sosa kanshi yace.
"Hmm! Eh."
Cikin mutuwar jiki ya bini da kallo ganin na tafi na barshi, dawowa yayi ya zauna a kujeran dake kusada hajja kanshi sunkuye yana jin ba daɗi yace.
"Ummi! Ko zaki mata magana wallahi zolayarta nake, bawai da gaske ba, zaki iya tambayar batu. Amma duk Safinah ta ɗauki zafi dani sosai bana jin daɗin haka."


Taɓe baki Hajja tayi cikin kunar rai tace.
"Yo naga sokanci, toh kuka zakawa Maryam ɗin dan wancan me zubin lomar tuwon taki kulaka,, sai me ita da tayu kwantai yo ina abin moruwa a jikin kasusuwa, yarinyar da nonor arziki babu duk ya tsofai, itace zaka hana kanka sukuni, toh sai kacigaba in yan mata ne, yanzun ake haihuwar wasu, kazo kana ihu dan wancan me kugun kamar na zanzaro tana fushi da kai ka damu, dube ka jibgege irinka kazo kana damun kanka akan wancar me kiran bulogarin."

Bai da niyyar dariya haka yayita dariya, fitowa nayi na shiga kitchen naji irin tanadin da Hajja take min, tsuka nayi ƙasa ƙasa a raina nace.
"Zamu gauraya da juna idan muka haɗu."

Tunda na shiga kitchen ɗin baɓ fito ba. Sai dai naji Ummina tana bashi hakuri, da gayya naki fitowa yaran ma naki kawo mishi su.
Bansan me Ummina tace mishi ba, sai da nafito naga bayanan taɓe bakina nayi a raina nace.
*Kaji dashi gulmame kawai*
Haka muka share kwana uku bama niman juna, ni dai a cikin kwana uku na watsar da kome amma Dr sai da mukayi sati biyu yana horani, ba kira ba txt duk sai naji ba daɗi na rasa wanda zan tunkara da maganar ana haka sai ga Dudu da matarshi ya kawota wuni zuwan Hajja. Dake a gurguje ya kawota, ko shigowa bayyi ba ya tafi.

Sai da dare da ya shigo ɗaukarta, nake mishi ba'a nace.
"Dudu kaida Uban gidanka kuna fushi dasu Twins toh sunyi fushi daku."

Zaro ido yayi dan bai fahimci kome ba, yace.
"Ai dama baku haɗuwa ne? Ai kullum yana zuwa gidan nan ko Batul?"

Kallon tuhuma nayi mata lokaci guda ta shiga yin tsili tsili da idanunta, cikin ɓacin rai na daka mata tsawa.
"Meye matsalarki da Dr? Wallahi Ummi ki ja mata kunne zan karyata akanshi."

"Toh ba a gidana zaki fara kishin banza ba, kishin wofi toh ba a gidana ba, idan kin matsu kidaina share shi mana ki ga ko zai kula min Y'a sakarya kawai."

Tashi nayi na bar falon cikin ɓacin rai na kuma banke kofar ɗakina,

Ina shiga ja wayata naga sakonshi sama da 15 tun sati biyu da suka wucce, rubuta mishi sakon nayi da cewa.

*Dama ka shigo rayuwata ce ka azabtar da zuciyata da ruhina? Me yasa ka koya min sonka bayan ba sona kake ba Why Hameed!*

Yana meeting yaga sakon, da sauri ya mai da min da cewa.
*Wallahi bashine manufata akanki ba! Manufata So da Kauna, Alhamdulillah tunda kin turo min sakon biko*
Zare idona nayi cike da mamaki dama bikonshi nayi taɓ ɗijam, *Aji Down*
Nace a raina, sannan na maida mishi da cewa.
*Allah ya kiyayye min nayi bikonka*

Dariya yayi kasa dan ma yana cikin manyan likitoti, shi yasa bai sami matsala ba, kuma taɓa irin Dr akwai matsala dan ko albashin da ake biyanshi na kula da lafiyan shugaban kasa, karshe ne balle kuma asibitocci uku yake aiki dasu a garin Abuja banda Alheri dan nashine nakanshi.
Ƙamar ya mike dan farin ciki sabida sun shirya da Beauty.
Ana gama meeting ɗin Dr Shahban na mishi magana suna da shiga tiyata bai kula ba yayi gaba abinshi zuciyarshi na gurin Yar Ummi.

... Bayan shiga ɗakina Hajja ta bankawa min harara, ciki sababi tace.
"Banda masifa! Wancan jibgegen katon take ihu akan banda so bai mata adalci ba ina ɗan kugunta zai iya ɗaukar shi, tana nan kamar lomar mayyu, kananun mata da jaraba yanzun ita a tunaninta zata ɗauk..."
Sulalewa Ummi tayi, yayinda Dudu da Batul tare da Khalil suke dariya kamar cikinsu zai ciwo. Haka Umma da Ƙhalila da suka shigo take gaya musu abinda yake faruwa tace.
"Amnah tunda Uwata ta haifeni ban taba ganin jarababbiyar mace irin Yakolo ba, ko ina zata kai wancan katon da take barbaranshi, Ina gaya muku duk ranar da ya rotseta sai kun kai mata a gaji dan yadda na ganshi karkarfa za ayi, shi yasa zan bawa Badaru shawara yasat, tafidda wani dan wallahi wannan ya haye ruwan cikin yar banzan can toh ta kare mata, dan sai kunyi dogon biki, ai manyan maza bana irin Yakolo bane kyanta ta sami dai dai irinta ɗan cas ko likita bokan turai"

Dariyar Dudu yaki tsayuwa, har da rike ciki haka ma Sophia itama dariyar ce, kowa a falon dariya yake. Bansan meye matsalar Hajja akan Dr ba wai ita dole na rabu dashi, na nemi wani tsabar barikanci matar nan ranar ido da ido tace min.

"Wallahi kika sake, wancan katon ya hayeki toh billahilazi, karshe da yoyon fitsari zaki wayi gari na dai gaya miki."

Da ta bani haushi nace.
"Toh ko D'an uwanki Alhaji Ibrahim Kyari zaki aura min,"

"A'a bai kai can ba, nia tawa tunanin ki hakura idan Uban yaran nan yazo sai ku taru kurufawa juna asiri,"

"Wa? Ni jikar Ibrahim walƙahi ko cikin Yan biyu tsautsayi yasa shi min fyaɗa m, ina ni ina Yaro wanda bai gama mallakar hankalinshi ba,ai idan nasake wani abu ya kuma shiga tsakanimu renani zai yi dan haka bar batunshi yaron da ba a gamawa tsarki ba shine zan barshi ya mallaki jikina, Yo Hajja banda yana cikin hauƙa yaushe zai nemi wani abu daga gareni ainni matar Manya ce irinsu Dr ba sa'an Dudu ba."

Rike baki tayi cike da alajabi tace.
"Amna ai ya cika miƙi mahaifa da mara da ruwan jikinshi, yar banza kafira. Idan ba namijin duniya ba babu namijin da zai iya ɗauraki saiti yar wofi wancan jibgegen, kwakuleki zai yi ya barki da azaba."

Ai tunda na lura aljanun batsarta suna kusa na sharta ban kuma yarda mun sake maganar ba dan bana ciki da iskanci😂


*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*


Oum Muwaddah......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....
Sorry da spelling error
Page.٣٨-38

"Idan kina kuka ni kuma nayi ihu kenan? Meye amfanin kukanki d'aga min hankali zai yake, idan kinga da matsala."

"Bani ce da tafiyar ba Abbanmu ya shirya, wai kar Nannah taga kamar mun rike mata jikoki da gaya."
Shafa fuskana yayi sannan ya sumbaci goshina, sannan yace.
"Toh haka ma yayi Allah ya dawo daku lafiya, idan nagaji da jiranki zan biyo ki."

Shiru mukayi dukkanmu zuciyarmu ba daɗi,janye jikinshi yayi ya lakaci fusƙana yace.
"Bari naje asibiti ina da marasa lafiya."

Tunda yasa kai ya fita nake tsaye a gurin kamar wacce aka dasani, kuka nake kamar wacce aka min mutuwa. Dakyar na tattara na koma ciki,
***
Kwanakin da suka biyo baya da sauki, sai dai Dr yaki mu haɗu. Sai txt amma fir yaki muyi magana ta waya, ana jibi zamu tafi na sayi Data ta banki, playstore na shiga na sauke whatsp. Nayi sitting da layina, buɗe data nayi. Sannan na shiga sakwanine suka shiga saukowa, suna gama sauka na shiga duba Dr.
*Zuciyata tana kewarka*
Ina cikin sakon ban fita ba, can yayi min reply da cewa.
*Nima haka haske rayuwata! Na zata kin tafine*

Harara na tura mishi me cike da jin haushi nace.
*Haka ma zaka ce min!😏"
A dame ya turo min saƙon ban hakuri.
*Kiyi hakuri aiki yayi min yawa*
Cike da jin haushi nace na shiga voice not.
"Nagode ka cigaba da azabtar da zuciyata dan baka kaunarmu, nagode."

Yana gama sauraron voice ɗin wanda nake magana har da kuka, sai ga video call.
D'auka naƴi na ajiye agabana ina kallonshi. Kurawa juna ido mukayi wallahi har ya faɗa.

"Kiyi hakuri."
Cikin rawan murya nace.
"Ko dai kana guduna ne sabida Abinda ya faru har nayi hmm wallahi ni ba yar iska bace, kawai na rasa yadda zanyi ne amma bazan kara ba"

Murmushi yayi tare da gyara zamanshi, ya zuba min ido sannan yace.
"Toh keda ma kiss ɗin baki iya ba, shine kika dami kanki da cewa dan kin sumbace ni na gujeki! Ki duba abu ɗaya nifa ba wani abu nake muradi a gunki ba sonki nake da zuciyata baki ɗaya, dan haka idan kiƙa ce min nazo zaki kara min wani sumbar tare da rike wuyata kamar za a tsinke min ita."

Rufe fuskana nayi ina dariya, cikin jin kunya nace.
"Don Allah kabar faɗan haka. Kana sani jin kunyarka sannan ina baka hakuri da abin wallahi bansan zaka."

"Ba damuwa indai ana kula da tsoho irina ta hanyar zazzafar sumba haka ai ko waje alkur'an bazan fita ba, na dinga adanaki kenan"
Jan karamin pillow nayi tare da rufe fuskana nace.
"Pls Baby ka bari mana"
Dariya yaƴi sannan yace min.
"Ina da aiki, zan leko anjima."
"Ok Allah ya kaimu."
Nace mishi, da dare kuwa sai gashi munyi hira sosai. Har ya gama ya tafi.

***
Yau zamu bar Abuja zuwa Oman, amma ji nake kamar zan mutu tsabar bakin ciki. Da maraici jirginmu zai tashi kamar, zanyi hauka haka nake ji dan Dr yaki zuwa. Tun ina raba idanu har lokacin tashinmu yayi ba dr ba labarinshi, sai da aka fara kiranmu. A sanyayye na saɓi Aamih a kafaɗata hawaye na zuba daga idanuna.
Ji nayi an zare Aamih, ajiyar zuciya na sauke sakamakon kamshin turaren Adidas.
Cak na tsaya, a sannu yazo yaja hannuna muka shiga tafiya sai da ya kaini har cikin jirgin. Ya kaini gurin da zan zauna, ajiye min ƴarinyar yayi, a bazata naji lallausar lips ɗinshi ya sauka akan goshina yace.
"Zanyi kewarku Allah ya dawo daku lafiya. Idan kin sauka pls kk kirani."
Gyaɗa kaina nayi yasakai ya ficce daga cikin jirgin, naji ba daɗi wai ma dan ban zama matarshi ba kenan.

***
*SAUDIA*
Shigowa yayi ya zauna, idan ka ganshi za ɗauka yafi shekarunsa sabida ya wani tara kasumba da da gemu sai fuskarshi tafito ɗan das, zama yayi. Sannan ya kalle lawyer cikin son karin bayani.

"Yallaɓai! Gimbiya Safinah tare da Gimbiyoyin suna hanya gobe Idan Allah ya kaimu, nima yau zan koma"

Murmushin da yajima bakyi ba itace ta kwace a fuskarshi yace.
"Idan sun huta akawosu"

Gyaɗa kanshi yayi sannan yace.
"Yallaɓai dukkansu har da Mahaifiyarsu."

Cikin ko in kula yace.
"Idan zata zo ba, idan kuma taki koda karfin a kawo min yarana su naƙe buƙata."

Tsakani da Allah Ashraf ya nuna shi ya ranshi yake so, dan haka yake cewa lawyer idan yaga ba suda matsala a karɓa a hannuna dan yana gudun kar na lalata mishi yara da rashin kjnya.

Da haka suka gama tattauna, sannan lawyer ya tashi dan komawa masaukinshi.
***
Mun isa Oman da karfe biyu na dare, Nannah da wasu mutanen tare da Yan uwanta suka zo tarɓana, na gaji zaman guri ɗaya, ina sauka a jirgin na hangota cikin bakar abaya. Sakar beharen, tayi kyau da tanaɗe kanta da bakin mayafi.

Fuskana cike da kunya da nadamar ɓata mata rai danaƴi ta bar kasan, kallona tayi cikin farin ciki tasa hannu ta amshi, Aamih. Tana shafa kanta tace.
"Barka da zuwa Oman Y'ata takaina"

" Barka dai Nannah. Mun sameku lafiya ya bayan rabuwa."
"Alhamdulillah Safinah yasu takwara da fatan basu wahalsheki."
Murmushi nayi, muka isa gurin motar da aka jera, ɗaya daga ciki. Kiran Rover range. Aka buɗe mana muka shifa tare, sai hira take min ina binta da eh aa.
Har muka isa wata haɗaɗɗiyar masarauta, iya haɗuwa ya haɗu, shima tafiya muke a hankali har muka isa inda zamu sauka.
Kallon yadda kowa ke sha aninsa babu wani tunanin. Dare yayi, duk inda muka wucce sai an zube ana gaishemu.

Har muka isa cikin gidan, anan naga tarba na musaman. Dan kamar Ashraf ɗinsu suƙe ganina.
Har dakin Nannah takaini anan naga wani irin duniya da aka narkan, a cikin ɗakin jikina ne yaƴi sanyi ganin yadda matar ta zauna a gidanmu kamar mara galihu, sai jikina yayi mugun sanyi.
A bakin gado ta zaunar dani sannan tashiga hidima da ni, masu aiki sunayi da jikonkinta, abinda ta fara bani madara da tumaric, nasha sai jikokinta kuwa wanda ama tasaka aka haɗa musu, ruwan wanka har da wasu irin turaruka, wanda yake cikin wani fure.

Gaskiya mun same tarɓa me kyau, ina fitowa doguwar riga nasama na gabatar da sallar dake kaina kafin na juya na kwanta, lokaci guda barci yaƴi gaba dani, ban san lokacin da aka dawo min da yaran ba dan barci yaci karfina.

Koda ta leko tasamu ina barci ga yaran da suƙe gefena suma suna tabarci, ɗakinta ta wucce. Inda tasame yan uwanta ana hira..
Abisa aladar Larabawa basu cika barci da dare ba, sunfi gane suyita yawo ko a zauna ana hira ana kurɓan shayi, Da safe kuma idan manyane su rama barcinsu idan yarana ne. Idan sun dawo makaranta zasu yi ina nasan ban wucce Oman ba tsabar barci yayi daɗi, banji kukar Aanih sai da ita Nannah taji tazo dauketa, taba ta ruwa tasha sannan ta.
Tashe ni na bata nono. Ina bata ina gyangyaɗ, dakyar na bata tasha ina ganin ta koshi na tintsira sai barci nima muka nayiwa kaina masauki, haka Nannah tafita tare da min addu'a.

Ta rage mana karfin Ac ɗin, sannan ta lulleɓe mu da babban bargo sannan tafita a dakin, jin d'umi yasani gyara kwanciya ashe bani ɗaya bace har da yaran

***
*Baya bata kad'an*

Jirginmu na tashi yan uwana da Dr suka fito, kawai aka fara.....
*Aka fara Me......"


Kuyi hakuri da pagen ba tsayi...😎
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*

Oum Muwaddah......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....

    MOM SAYEED, RAHAMA AHMAD, MAMAN KHALIL da MY ZAHRA sauran Yan Team ɗin Hajja Ƙaka, toh tana miko GWS......

   Wannan Naki ne sis FAUZIYAH kiji daɗinki...
Page.٣٧-37

" Nadai gaya miki ki rabo da wancan me zubin Inyamuran, ina dalili! Me zakiyi da mutum dinkinkina."
  Ta shigo min ɗakina tana mita, zuba mata ido nayi cike da takaici kamar zanyi magana sai kuma na kyaleta, sabida karan wayata ɗauka nayi na manna a kunne  Cike da jan aji tare da miskilanci.
"Hmm!"
       Murmushi ya sauke wanda ya doki dodon kunnena, lokaci guda ya saukar min da wata kasala, har sai da na lumshe idanuna.
    "Beauty! Ina jiranki pls"
     Ajiyar zuciya na sauke tare da sake wani munafikin murmushi nace.
"Ok!"
          "Thank You!"
       "Are Welcome My Beauty" ya faɗa, bai kashe kiran ba. Nima kuma haka muna manne da wayar a kunnenmu, sai murmushi muke sakewa junanmu.
      
   Sake baki Hajja tayi tana kallon Ikon Allah, musaman da taga sai murmushi naƙe sakewa kuma ban kashe kiran ba, zama tayi a bakin gadon. Tace,
"Da alamu sai Badaru ya ɗauko masu maganin Aljanu dan bana tunanin lafiyarki lau, kin manna abu a kunne ke ɗaya sai dariya kike ai wani taga haka yace ba lafiya dalla aji."

        Katse kiran nayi a kufule nace.
"Meye matsalarki Hajja."

   Na mike ban ɗaki nashige dan  bazan iya da hajja ba, sam bata da kunya kome zata faɗa a tsirarar shi take faɗa kuma bata damuwa da abinda zai fito bakinta kome tafamjama famjam.
       Nasan na ɓata lokaci gurin wanka, ina fitowa daure da towel tana zaune abinta, zama nayi na fara gyara fuskana da jikina sai da na kyalkyale ko ina, sannan na ɗauko bra ɗina zan saka amma dake matar nan yar duniya ce, karkata kanta tayi.

"Hmm. Me zaki sanyawa rigar nono, ba dai wannan abun ba? Abu sai kace me kirgan dangi, wai ma na tambayeki taya kike shayarda yaran nan  ne dan naga sun musu miri-miri."

   Juyawa nayi na kalli bakin kofa na tabbar  ba kowa juyar sa kaina nayi, cike da bakin ciki nace.
"Zoƙi ficce min a ɗaki! Dan ke ɗin nan sai kija ayiwa mutane girgizan kasa ana zaman lafiya da maganarki nan da kike yi mara daɗin ji balle gani."
 
       Haushi na bata aikuwa tatura min baki, tana taune asuwakin bakinta, gown ɗin Atamfa nasaƙa, wanda aka fidda min shap ɗina sosai ganin yar sa'idon bata fita ba na ɗauki pant ɗina da under na shige ban ɗaki sororo tayi tana kallona, cike da alajabi har na fito. Taɓe baki tayi irin ko ajikina, na zata har zucine sai da nazo ina fesa turare tace.
"Yanzun Yakolo saka kayan ma, sai a ban ɗaki wata uwar zan gani, kika iya saka kwanseti a gabana sai wandone zaki gudu ban ɗaki, ko ce miki akayi zan kalleki ne."

   Naɗe gyale na nayi cikin sauri nace.
"Ke kika damu"
  Na fita da sauri, rakani tayi da harara tana dafe gwiwarta zata mike daga bakin gadon, na sake shigowa da sauri na kalli fuskana sannan nafita da mugun sauri.
"Ba dole kita sauri ba, sam yarinyar bata da auki, sai kace bulaliya."

     Ita kaɗai tayita mita tsabar masifa nacinta.
  .....
    Tunda na fito ya kura min ido. Ko kiftawa bayayi, zuciyarshi cike da farin ciki, yayinda fuskarshi taki ɓoyewa sam. Har na iso jikin motar na tsaya hannuwana harɗe a kirjina , nace.
"Assalamun Alaikumun"
  
   "Amin Waalaikumun Salam, Beauty! Barka da zuwa."
      Buɗe kofar yayi tare da zaro kafafunshi waje, a hankali ya yunkuro yafito, sai yanzun na lura da girman da Hajja take cewa yayi min, tsayi yake dashi sai faɗi. Kuma yana da murɗaɗɗiyar jiki, kana ganin tarin tsokoki, lumshe idanuna nayi sakamakon kamanceceniyar da suke da Ashu, sabida shima yana da k'iran irinta zaratan mazaje.
  Hura min iskan bakinshi yayi. Fuskarshi ɗauke da murmushi yace.
  "Kina tunanin Babansu Twins ko?"
   Ya ɗaga min gira, tsuke fuskana nayi tare da tura bakina gaba nace.
"Baby!!"
    Ware idanunshi yayi, cikin jin haushi nace.
"Ba halin nayi tunani sai kace na wncan yaron nake yi"
    
  Dariya sosai na bashi, dan yakasa rikewa yasai yi yake kamar yaga taɓaɓɓiya, haushi ya bani na juya zan koma cikin gida yayi wuf tare da riko hannuna, a tsiwace na buɗe baki zanyi magana, muka haɗa ido dole na haɗiye sannan na kalle hannuna da ya riƙe.

      "Kiyi hakuri mana" yace cikin wani irin murya, d'ago idona

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment