Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba. Dan bansan da wani kalma zan faɗa musu abinds ys faru bana cikin hayacina.

Hmm wato yadda na fara tafiyan har nabar cikin gida bayi ban samu matsala ba, sai da na nufi hanyar da zai kaini gidan Sultan, nan ne wani mugun tsoro ya kamani, domin lokacin dare yayi sosai. Ina tafiya sai naji kamar ana bina, da na ɗauka takuna ne. Sai da na saka ido sai naga abu kaman inuwa nabin bayana, an nan ne na shiga karanta ayatul kursiyu, ga wani masifaffen tsoro da ya turkeni ina karanta addu'ar ina sauri ina waige - waige.
Cikin ikon Allah na isa get ɗin farko, tun daga nan ban kuma cin karo da kome ba har na isa cikin gidan. Da sallama na shige falon farko ba kowa haka nayita ratsa falon har na isa falonshi.
Kamar kullum ba kowa a falon, sai karan da naji na ruwa a kitchen. A tunanina Samin ne da sauri na shiga, turus nayi ganin Sultan a gaban gas yana gani na ya tsuke fuska fiyye da kullum. Turus nayi ina zare idanu, ba kome yaja haka ba sai dan kwarjinin da yake dashi, kasancewarshi sarki. Komawa nayi da baya, har ya gama abinda zaiyi ya fita,
Mamaki nake yau da banga Masu tsaronshi ba, vibrate naji a jakata na saka hannu na cikin na ciro wayar da aka ajiye min tun kwanaki, sako na gani.
*Har kin razana ne da abinda ya faru, bamu miki kome ba kawai mun miki gargaɗine kawai matuƙar kika ce zaki bijire mana har cikin gidan Sultan zamu biyo ki*

Goge sakon nayi dan babu amfanin ajiyewa, zama nayi cike da damuwa bayan na shiga kitchen. Tallafe fuskana nayi na rasa meke min daɗi ban ɗaki na shiga nayi alola. Sallar na gabatar sannan nakwanta.
Zuciyata cike da sake sake, can da yunwa ta buwaye ni na tashi na fara niman abinda zanci kaman ance na buɗe friji nayi arba da kunafe, cirowa nayi, na kuna micro nasaka ina jin ya tirara na ciro na fara ci hannu baka hannu kwarya, ina ci ina kwalla ina sha'awar abincinmu na gida, irin biski, indalayi wani kunun kanuri ne, ɗan wake da tuwo miyar kuka, miyar ganye asalin taushe musaman miyar hajja kakata, dan har da kaɓewa take yanyankawa tasaka tantakwashi, idan za a ci da biski a zuba manshanu. Bansan lokacin da kuka ya kwace min ba, da gatana ina kwanciya a kasar tiles ga sanyin da yake shigana haka wata ran nake tashi na zauna akan kujera anan zan karasa kwana a zaune sabida bani da Yanci...........

#MJ#Mai_Dambu#Vote....


*Dalilin da yasa nace zan ajiye typing ni a gaskiya ban iya Editing ba kuma na faɗa muku ban iya gaskiya na, babu amfanin baɗi ba rai gwara na ajiye rubutun kawai dan wallahi ban iya ba, ai nayi kokari ma, ni Yar arewa ce amma a kudu aka haifeni kuma na taso acan, dawowarmu Bauchi shekara goma cif, ina ga idan ba ajinjina min ba toh kar a kushe min dan ko haifaffun arewa bazasu kalubalance ni ba, wannan shine iya gaskiya... Idan nayiwa wani laifi ya yafe min.....👏👏*
Oum Muwaddah....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: *_HAZAƘA WRITER'S ASSO_*

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

Page.٨
        ....... Kakan Angela yazo har gun Ashraf, amma fir aka hanashi ganin Ashraf, ni kuma nazo zan fita naga ana koran tsohon. Sai roko yake kar a kashe masa jikarsa. Komowa ciki nayi na duba inda aka ajiye takardun, na ɗauka na juya zan bar falon, mukayi kiciɓis dashi, kallona yayi yadda jikina ke rawa takardan sai da ya nemi faɗuwa, bai ce min kome ba ya raɓa gefena ya shiga duba sauran takardun, nima juyawa nayi na mai da mishi takardansa, cikin sassanyar murya nace.
    "Ranka shidaɗe! Ana mulki a cikin masarautarka ba bisa ka'ida ba, sannan kuna nuna fiffikon kabila akan sauran kabilun, Sultan katuna Allah ya baka mulki da izza dan gwada imani. Ka duba abinda kake aikatawa baya cikin tsarin addinin musulunci kwata kwata, abinda kake yi tankar na larabawan zamanin jahiliyya"
      Don Allah meye laifin wannan kalman.
       D'ago idanu yayi ya kalleni a sace, sannan ya maida kanshi cike takardun da yake yi, haushine ya kamani dake jikina ya saba da wahala, nace.
"Tun da nake ban taɓa ganin lusarin sarki irinka ba! Me kunyar nunawa duniya ko shi waye, an mai daƙai wawa suna shargalensu kai kuma sun mai da kai banza ana goga maka kashin kaza a idanun talakawanka, sam baka dace da zama sarkin alumma ba sai dai sarkin lusarai."
      Mikewa yayi, ya zagayo gabana, cikin matsanancin ɓacin rai ya shake wuyana, ina kakari tare da niman kwatar kaina, nace.
"Kaga Yarantar ba! Ka tsaya ka fuskanci gabanka ba faɗa da mace ba."
        Cillar dani yayi cikin ɓacin rai ya take min kafa, kara nasaka. Ina riƙe da wuyana cikin karfin hali koda tsaga jikina zakayi bazan daina gaya maka gaskiya ba, dan banga dalilin zuba maka ido kana aikata abinda ka gadama ba."
                 Zuwa yayi ya kamo karamin hijab din dake kaina tare da gashina ya shiga jana, har cikin dakinshi ya cillani saman gado,   ɓalle aninin rigarshi ya fara, da sauri na dira daga gadon zan gudu ya cafkoni tare da maidani da karfin tsiya ya fara niman rabani da kayan jikina, rike hannunshi nayi. Cikin tashin hankali nace.
"Don Allah karka min haka, ban taɓa zina ba, kayi tunani idan y'ar uwanka ko y'arka , ƙo kuma mahaifiyarka...."
     Cak ya tsaya da abinda yayi niyya,  cikin ɓacin rai ya sauka a gadon ya fita daga ɗakin,
                  A hankali na sauko nima, jikina a sanyayye na fito, babu abinda yayi min. Amma tsananin tsanarshi da kunya sun dame ni, a raina kuwa nace.
    *Insha Allah sai na kai ka gun Mahaifiyarka kuma yanzun na fara maka katsalandan*
                  Ban ganshi a gidan ba, ga baki ɗaya har tsawon kwana biyu.
                Ashe a wannan shashin ya daina zama yana nan a gidan, na gaji da zaman shiru na shirya zan tafi gunsu Hindu. Ina zuwa falon tsakiya najiyo muryansu Amir Ukshe yana lallaɓashi, a raina nace.
   *D'an banza dole kayita yadda kaso wato a nan lallaɓaka suke ni kuma ina maka hawan kawara.*
         Duk yadda suƙa so yayi musu abinda suke so yaki,  komawa nayi da baya, dan ko magana yaki musu, mutum sai kace bebey. Haka suka bar gidan cike da damuwa,
          ***
    "Barka da Zuwa! Shugaban Kabilar Husseinniyya! Adnan Bini Bilal  Alhusseinniyya! Kaine har ofishina."
      Cewa Amir Ukshe,
            Murmushi dattijon yayi ya mika masa hannu sukayi musabaha,  zama sukayi sannan Adnan bini Bilal, yace.
"Sai ka gannin kwatsam,"
 
   "Eh wallahi!" inji Amir,
     
"Nazowa Ashraf da kyautane mai daraja, idan bazaku damu ba na bashi auren Y'ata karama Rania, kwanan nan tagama karatunta na chemistry."
    Shiru Sultan yayi kafin yace.
" Toh amna ina ga me zai hana muje kaji ta bakinshi."
              Cikin jin daɗi mutumin yace.
"Nagode! Kayi hakuri ban maka ta'aziyar rashin da kayi ba, kuma naga har yanzun baku ɗauki mataki ba, haka zaku bar jinin yaron ya zuba a banza kenan, ya kamata kusan abinyi."
       Murmushi Amir yayi suka fito daga ofishin dake cikin fadar masarautar, Amir yayi musu jagora har cikin gidan Sultan, yana zaune ya saka wasu takardu a gaba. Zai saka hannu akan za a fidda wasu mahaukatan kuɗi, wanda ya fito ta Ofishin Amir Uzaifa, amma kamar wanda akawa dabaibayi.
         *Sun maida kai lusari!!! Wawa said yadda sukayi da kai*.
   Jin kalmomin yake kamar an watsa masa fire, abin haushi abinda yaso aikatawa da wancan kaskantacciyar baiwan, ya godewa Allah da bai kai ga aikata kome ba dan yasan da yayi d'an danasani a rayuwarsa,
         Da sallama suka shigo ya d'ago kanshi, ya kallesu, fuskarshi a sake. Bai ce musu k'ala ba, suka zauna tare da mika mishi hannu.
     Ajiye biron yayi suka gaisa, sannan ya maida hankalinshi kan takardan gabanshi, Amir ne ya gabatar mishi da Shugaban kabilar Husseiniyya, da kuma kudirinsa na bashi Y'arsa.
      D'ago kai yayi cikin kasaita ya kalle Amir Ukshe yace.
"Allah ya tabbatar"
    Shine abinda yafito bakinsa  cike da mamaki Amir ya kalle shi, haka kawai yaji ranshi yayi mugun b'aci tun yaushe yake binshi da maganar Sahelah, amma yaki tsayuwa ya saurareshi sai yanzun da aka bashi mace daga wata kabila ta maguzawa zai amsa, murmushi yake. Amir yayi sannan suka mike zasu fita.
       Ya d'ago kai yace.
"Amir! Ina niman Uzaif"
       Gyaɗa kai Amir yayi har suka fita zuciyarsa kamawa take da wuta, shugaban Kabilar Husseiniyya murna yake, abinsa amincewar da Sultan yayi babu ja balle bincike, dole suma a haifi sarki a cikinsu fatanshi d'aya Rania tana shigowa ta haifi ɗ'a namiji, dole daular Jordan ta dawo karkashin ikon Urdawa.

Bayan tafiyarsu ya tattara takardun ya dawo dasu gidan, ina jin motsinsa ban fito ba, da gayya ya sake glass cup ya fashe, masu tsaronshi da suka rakoshi zasu nufi kitchen ɗin ys ɗags musu hannu, fita sukayi a ranshi yace.
*Wancar bakar shaiɗaniyya ce idan akabi nata kullum sai an gutsire naman jikinta*
.....
Wuccewa ɗakinshi yayi ya samu kome a shirye, wanka ya faɗa, yayi sannan ya fito kayan shan iska yasaka wandon 3qrt rigar shirt me guntun hannu . Tare da fitowa, yana zama Samin yana kawo mishi tea, har ya ajiye zai tafi yace.
"D'auƙa kasha"
A razane samin ya juya cikin inda inda yace.
" Ranka shidaɗe ai akoshe nake"
Gyaran murya yayi sai ga Samudawarshi sun shigo.
"Ku bashi ya sha."
Ina daga kitchen, wato abinda na fahimta mulki yabi jikin Ashraf baya iya tsawaita magana, dakyar maganarsa suke haura kalmomi uku huɗu.

***
*NIGERIA*
Abuja.....
Zaune take ta zurfaffa tuninta, hankalinta kwana biyu a tashe yake, sabida yawan mafarkin Feener da take, balarabiya ce kana ganinta kasan hutu ya zauna mata, dan ya ɓoye shekarunta. Wayart ta ɗauka a sannu ta latsa number. Dake da sunan
Bint
Abinda wannan yar babyn kamfanin wayar tasaba ce mata kullum yau ma haka tace mata, bata taɓa jin haushin yar babyn ba kamar yau(😂 ai babu abin takaici da ya wucce sai kasakanƙance zakayi hira su maka babu kosisin da zakayi hira😂)

Badar ta nima cikin damuwa, ta kirashi ɗauƙar ƙiran yayi tace.
"Badar bazakayi wani abu akan tafiyar Bint na damu."
"Karki damu nasa a bincika mana inda take, harshi Anim ɗin ma yana kokartawa gun taimaka mana."
Kaman yana gabanta gyaɗa kanta, sannan tace.
"Allah ya sa lafiya ne shirun nata dan bata taɓa yin haka ba."
"Insha Allah, lafiya ne."
Da haka sukayi sallama, Nannah tasa damuwa sosai a ranta musaman mafarkinta najiya, yafi kowani mafarki muni.
***
*JORDAN*
Shigowar Uzaif falon da sallama yasa ya ɗago kanshi dan yana shigowa yaga ana fita da Samin, zama yayi cikin cushion ɗin falon ya mikawa Sultan hannu suƙayi musabaha. Shiru ne yabiyo baya kafin Uzaif yace.
"Sultan! Amir yace kana nimana"
Idanunshi nakan tashar aljazzira new na harshen larabci, kaman bai san da zaman Uzaif ba, haka ya share ya cigaba da kallonshi, gyaran murya yayi sai ga Ghaniyu ya shigo.
"Umarninka nake jira."
Maida bayanshi yayi ya jingina, sannan ya lashe lips ɗinshi cikin mugun miskilanci ya motsa da lips ɗin yayi magana kasa kasa.
"Ta kawo mishi ruwa."
Juyawa Ghaniyu yaƴi ya shigo kitchen ya samu inata mita, gyara murya yaƴi sai da na razana, murmushi yaƴo sannan yace.
"Da alamu zaki amshi aikin samin domin mun kamashi da laifin yunkurin kashe Sultan, ki kawowa Bako abin taɓawa, dan Kawunsa Uzaif ne yazo."

Kurawa Ghaniyu ido nayi sannan na taɓe baki nace.
"Hmm baya tunanin na shafa mishi baki."
Bai kulani ba ya fita abinsa, haka na shake tire da abin taɓawa sannan na kai na dire a gaban Uzaif.
Ina ajiye masa na bar gun, na dawo abuna na cigaba da sabgana, ina kewar gida sosai.
....... Taɓa abinda na ajiye Uzaif yaƴi sannan ya sake maida hankalinshi gun Sultan, zai magana Sultan ya wurga mishi tambaya kamar haka.
"Me zakayi da dalla billion 450?"
Zufa ne ya shiga karyo masa, nan ya shiga cewa.
"Sultan! Dama za'ayi kwaskwarima wa masarautar za mucire tsofin kayan ciki kasancewa watan ramadan ya k'aratu, sannan zamu sauya wasu abubuwan."

Mikewa Sultan yayi sannan ya nufi hanyar fita, cike da takaici Uzaif yace.
"Sultan tafiya zakaƴi?"
Girgiza kai yaƴi cikin ko in kula yace.
"Tsayuwa zanyi"
Ba yawa ba daɗi. Haka ya ficce yabarshi, bakin cikine ya turmushe zuciyar Uzaif, tunda yake bai tab'a gamo da mara mutunci irin Sultan ba...
*Yaushe Ya koma haka?*
Tambayar da yayiwa kanshi knn da hanzari ya bar falon....
***
Zaune yake gaban wani sirritaccen ɗakinsa, ya gama karanto wasu kalmomi, wani haske ne ya bayyana. Har sai da ya kare fuskarshi cikin kaskantar da kai yace.
"Ya shugabana! Yaron nan ya fara bijire min!"
Dube dube yayi, sannan ya ɗago kai, " Akwai matsala ƙuma daga gareka ne, kabar sauran yan uwanka su more shi,dan yanzun haka Raziyah tana hanya dawowarta daga turkiya itace ta lalata naka aikin,, snnan Alexandra shima, ga Abu Zarri wanda shi yasa ayi mishi dole katashi tsaye kuma ka bar kange musu arzikinsu tunda kama kana ci."
Buɗe baki Amir yayi zaiyi mgn Ra'ees yace.
"Yaki amsar tayi auren Sahela amma ya amshi tayi Adnan toh ai koda auren masa su akayi bazai zauna dasu ba dukkansu ba matansa bane, matarshi tana kusa da shi, kuma bata cikin ksbilarku. Itace zata zauna dashi babu dogon buri a tare da ita, amna shawara karku barshi ya shigo da ita dan tun kafin ya shigo da ita zata zabtare muku kimarku, sannan ka dakatar da Marhum yunkurin ganin bayan Ashraf tabbas nan gaba hukunci zata haura kanshi akwai zoɓen azurfa ka bashi ita a matsayin kyautar karin shekarar haihuwarsa ku haɗa mishi shagali ita zoɓe zatq kasance me jin umarninka ce ba tasa ba, karku sake ya shiga fadar domin idan ya taka ciki kome zai faru ciki har da abinda ya faru da iyayensa, kuma ya fahimci haka toh baki d'ayanku zaku zama baki a lahira hatta nima bazan tsira ba jiki magayi."

Yana gama faɗar haka ya ɓace daga jikin Madubin.
..........
*Hello ina son ku duba yanayin labarin da kyau gabaki ɗaya daga Jazziratul Arab ne, naso aro sunaye ganin navawa mutane wahala a cikin Abu Khadija yasa nayi amfani da sunayenmu na yau da kullum, zaku ji dai bakon sunayen ya zama dole asaka ne Musaman Rania, itace matar Sarkin Hussein Muh'd na kasar Jordan a yanzun, sai irinsu Alexandra Angela, Zoya Sahela, da sauransu arone kasancewa labarin larabawa da Yahudawa ga kuma Kabilun Urud...... Nasan kafin ni akwai marubutan da suka shiga yankuna na duniya dan labari amma Labarin masarautar jordan, dabane sabida har cikin littatafan. Tarihi irinsu Siratu nabiyyina Muh'd (S.A.W) Islam biography, Islam dictionary da sauransu nagode da fatan zaku fahimce ni.*

#MJ#HZƘ#VOTE......Ku taimaka da Vote na fara jin lalaci fa😂

Oum Muwadda....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

Page.٧
        *Banu Hashim*
   Watsawa Amir Ukshe wasu takardu, Amir Abu Zarri cikin mugun ɓacin rai da fusata, ya daki table ɗin gaban Amir Ukshe yace.
"Baka isa hanani rawan gaban hantsi ba, dukkanmu kabila d'aya ce kuma manufarmu d'aya ce, sannan burinmu d'aya. Taya zaka kange kome dan zalimci ka hana wasu? Raziya ta kawo takardunta kace bazaka saka baki ba, akan me? Ita kaɗai ta rage a Ashraf ya kira danginsa amma ka hanata samun kusanci da yaron meye nufinka? Ga takardun kuma dole a samata hannu itama dan dukiyar ba naka kai kaɗai bane."

        Mikewa Amir yayi ýa tawo inda Amir Abu yake, hannunshi yakai zai taɓa Amir Abu Zarri, cikin sauri yaja da baya, yana nuna shi da d'an yatsa yace.
"Macuci baka da bakin gaya min kome nasan kai waye, kuma dole ayi kashe muraba. Ka duba jaridar can da na kawo maka karka manta yarjejeniyarmu na bawa juna goyan baya maciyi amana."
Yana gama gaya mishi haka ya juya tare da barin ofishin.
Idan ran Amir Ukshe yayi dubu sai da suka ɓaci. Fuskarshi har ja tayi tsabar ɓacin rai, danna wani karfe yayi sai ga masu kula dashi sun shigo, nuna musu takardun yayi, suka tattara sannan suka zuba a kwandon shara suka fita.
***
Wani irin rikicine ya taso daga cikin kabilun Hashimiyya, wanda yaja hankalin, sauran kabilu guda biyu suka zuba ido suna kallon yadda wasan zai kayya, kuma abin takaici ba kome yaja wannan rikicin ba, sai dukiyar masarautar da suke watandarshi, karshe dai wasu daga cikin familyn Yasir sune suka, shiga alamarin inda aka dai daita ba tare da sanin Sultan Ashraf ba.
........ Takardun da zaisa hannun suka, na kalla suna kan wani table na daban, dake Allah ya ɗaura min karambani, zama nayi a kujeran table ɗin, na shiga ɗauƙar takardun ina dubawa, a hankali na shiga duba abubuwan da takardun ya kunsa, mamakine ya kamani sakamakon ganin zunzuruntun dallolin american da zasu cire daga baitul mali. Masarautar, jin motsin yasani mikewa nabar gun, kitchen na shige. Ina hango shi ya fara samusu hannu ko duba takardun bai yi ba. Mamaki ne ya kamani na fito daga kitchen ɗin tsoro da fargaba dake raina bai hanani fitowa ba nuryana na rawa jikina na ɓari nace .
"Sultan!!!" bai ɗago ba kuma bai fasa abinda yayi niyya ba, na cigaba da cewa.
"Allah ya baka mulki ne dan ya gwada imaninka bawai ka zama azzalumi ba, wannan sa hannun da kake yi ka duba meye ya kun..."
D'ago kanshi yayi idanunshi sunyi jajjur, takanta fuskarshi tayi ja. Ainun balle kuma ace meye a zuciyarshi, kura min ido yayi sannan ya danna ɗan kararawar. Sai da naji cikina ya murɗa, shigowa suƙayi idanuna cikin nashi, bai janye ba nima kuma haka, cikin kasa kasa da murya suka ce.
"Umarninka muke jira"
"Ku tafi da ita, taji a jikinta." yace, idanunshi cikin nawa,
Lumshe idanuna nayi cikin karfin hali nace.
"Me yasa bazaka fahimc..."
Juyar dani suka fitar dani, cigaba yayi da aikinshi.
Wato idan akwai mugayen mutane bayan larabawa ne, suna fita dani, suka wucce dani wani ɗakin ruwa. Suna shigar dani suka kifa kaina cikin ruwan sai da naƴi minti uku zuwa huɗu suka fidda, kuka nasaka ina jin numfashi dakyar naja numfashina, kafin na daidaita an sake tsumbulani cikin ruwan, har kusan minti biyar, bansan yadda zan muku bayani irin azabar da nake ji, amma bari na muku misali da kwarewa, idan wani kware da ruwa ya kuke ganin yake ji balle ni da ake tsuma kaina cikik ruwa bana jan iska, sai ruwa zalla nake ja.
Kusan minti ashirin suka ɗauƙa ana horani da ruwa, nayi laushi na masifar gajiya, suna ciro ni suka jefani gefe guda ina sauke numfashi ga kwallar wahala da nake fiddawa.
....... Bayan awa guda suka mai dani cikin gidan suka watsar a kasan kitchen ɗin da sauri Samin yazo inda nake ya ɗaga ni, kuka na saka mishi, coffee ya haɗa da sauri ya bani nasha, ina kuka, ganin yana juye ruwan coffee a cikin wani butar shan shayi, ya jera kofuna biyu. Zai fita dashi nayi maza na amsa, dan haka kawai naji ban yarda da coffee ɗin ba, dan a madadin ya bani na cikin tukunyar, a'a sai ya dafa min wani a cikin wani tukunyar ga kuma wanda ya dafa. Olready cikin siyasa na mike tare da cewa.
"Bani na kai mishi."

Ba musu ya bani, ina fita falon, da gayya nasake tiren ya faɗi a kasa, kome ya zube. Da gudu Samin ya fito bai yi wata wata ba ya tsinka min mari, dai dai fitowar Sultan ga kuma masu tsaronshi sun shigo, sakamakon jin karan fashewar abu. Cike da jin haushi ya kuma d'aga hannu zai mare ni, Ghaniyu ya dakatar dashi. Ƙasa ƙasa yayi da murya yace.
" Kina da dangantaka da bakakken aljanune, yanzun aka dawo dake daga ɗakin horo amma har kin kuma wani laifin, ke ko tsoron sul...."
Bai kai karshe ba na tsinkawa Samin Mari, duk suka zaro idanu. Hatta Sultan ɗin mamakine ya kamashi, dukda a tsorace nake. Nace,
"Bani da lokacinku idan kun damu da abinda nake wanda kuke kira da Sultan yayi magana."
Zasu yi magana ya d'aga musu hannu, takowa yayi har inda muke ya kalle su gabaki ɗaya suka fita daga falon takowa yayi gabana, d'ago kaina nayi naganni yar karama a gabanshi, tsaki yayi ya min sannan ya bar falon, komawa nayi kitchen. Ina shiga Samin na finciko ni, haɗani yayi da bango, tare da toshe min baki da hannunshi cikin zafin rai yace.
"Ina kyale kine sabida, baki cikin tsarina, wannan ɓarnan ƴa zams nakarshe da zaki min in ba haka ba zaki mutu. Dan ni an biyani kuɗin aikina ke da baki da rabo kita zama

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment