Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kome tace.
"Ba kome, ki kwantar da hankali."
        
    A haka muka tab'a hira sama sama.
        Har lokacin sallah yayi muka mike. Tunda na dawo na zauna nake nazarta halin da nake ciki.
     ****
    *Mumbai*
Tunda suka iso garin aka fara kokarin ceto rayuwar sa cikin Yarda da kai suka sadaukar da lokacinsu anyi aikin cikin natsara da takatsantsar. Cikin ikon Allah sai gashi sun sami damar ciro bullet ɗin. Sannan suka fito dashi, dukda sunyi booking ganin liƙitan ta Onlind shi yasa basu tsame matsala ba.
   Sai dai muce Dr Allah ya baka lafiya.
             ***
       "Wallahi Ummi duƙ sai na ruɗe na rasa me zance mata sabida ta rutsani sosai."

   "Allah ya kyauta"
Iƴa abinda Ummi tace.
Tana mamakin irin son da nakewa dr.
    ***
Saudia...
    Yau ya fito fuskarshi nan a cunkushe ya zauna a kujeransa.

    "Sultan! Maman Yan biyu tana can masarautar da yaran"

       "Asaka ido akanta da yarana"
   Gyaɗa mishi kai yayi cikin nutsuwa har ya bar gurin, zuciyarshi na cike da farin ciki da jin daɗi yaranshi suna kusadashi.
   *Alhamdulillah*
Sosai yayita murna kamar wanda aka bawa aljannah.
   ***
Wato wani irin rayuwa na fara fuskanta. A cikin masarautar wani mugun  tashin hankalin wanda yasani kuka a ɓoye, dan lokaci guda Nannah ta hanani yarana, kuka nake zama naƴi tunda Nannah taga ina damuwa, sai ta shiga kawo min yaran, sau biyu ina basu nono ni kuwa, so. Yarana da kaunarsu ya cika min zuciya. Lokaci d'aya na fara jin za araba Uwa da yaranta.
              
        Shigowa tayi ta same ni ina share kwalla zama tayi sannan tace.
"Gwara ni, ina da sauki sosai
Domin kuwa Idan mahaifinsu yazo zai rabaki dasu ne shiyasa na miƙi tayi aurensa."

    D'afo kaina nayi a raunane sai ga kwalla sharrr. Duk yadda naso hana kaina kuka sai da nayi me isata, kuma bata hanani ba.

"Toh Nah ni narigada na tsayar da Dr bana jin kowa a raina sai shi, don Allah sau ɗaya kubarni na bi muradin zuciyata mana, Hameed shine mafarkina, ya tanadar min soyayya da farin ciki, Nah!"

"Ya isa Safinah bazan miki dole ba tunda kina da wanda kike so, amma kisani ko zaki koma keda d'aya zaki koma, domin kuwa haka muke al'adarmu zamu amshesu a nimo larabawan kauye a koya musu larabci."

Cikin shashakar kuka nace.
"Nah! Karku rabani da abinda zuciyata ke so!"

Girgiza kai tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace.
"Safinah! Yaran Shegune!"
A razane na ɗago kaina cikin raina nace.
*Shi kenan Sun rabani dasu*
Wato shi yasa Malam bahaushe yace magana d'an aikene duk yadda kayi shi wata rana sai ya dawo maka, yau gashi ya dawo min.
"Nannah dan girman Allah karki rabani dasu, wallahi zuciyata bazata iya d'auka ba ina mahaukacin sonsu dan jikina suka tsaga, qaddara ce tasa na samesu ta baibai... Amna ba gama garin shegu bane don Allah ki rufa min asiri ki barni yau na koma."



Sam bata jin dadi kukana amma bata zaɓi da yafi haka, mikewa tayi ban kuma ganinta ba sai a gurin Cin Abinci na gansu har da yaran, suna rikici.

Tabbas larabawa mugayen mutane ne akan yaransu, yaran suna gani na suka fara mika min hannu, dan yau tunda ta shigo aka kawo min su, na basu suka sha, har yanzun da kusan karfe biyu na rana.

Tunda nasa abincin a gaba sai juyawa nake yi, kukansu jinshi nake a cikin brain ɗina, duk yadda naso dakewa na kasa, juya abincin nake zuciyata na wani irin bugawa. Ajiye cokalin nayi a raina nace.
*Badani da goyan mayyu ba*
Mikewa nayi naje na amshi yaran na raɓa ɗaya a kafaɗa, ɗaya kuma na riketa a kweɓina na fita daga falon cin abincin.

Murmushi Nannah tayi ta cigaba da cin abincinta ranta kwal, suna gamawa Yayanta yace.
"Nana Asma'u! Karki sa yarinyar can ta tsane ki! Dan uwa ce zata iya jure duk wani tashin hankali akan yaranta, haka da kike mata zai sanyata taji bazata iya ganinki da kima ba."

Jinjina alamarin tayi cikin yarda da shawaranshi, bata ce uffan ba har ya tashi ya fita. Maman Natasha ta kalleta sannan ta kalle Natasha da tayi raurau da idanu tace.
"Amirah kina ganin haka da kikayi zai."

Juyawa Nannah tayi cikin murmushi tace.
"Safinah! Nake so,, sai da taja numfashi sannan ta cigaba da cewa.
"Natasha bazata iya da halayar jama'ar jordan ba, amma Safinah tasan halayar wasu ciki har da Ashraf ɗin tasanshi fiyye dani saninda na masa, a halin yanzun Ashraf baya bukatar jinin Sarauta a cikin rayuwarshi, domin bazata bashi gudummawar da nake bukata ba, shiya kuka ga ina nisantata da yaranta, nisan tazara dake tsakaniksu shi zai sanyata amincewa amma bazan taɓa mata dole akan D'ana ba dan tasha wuya a hannunshi."

Tana kaiwa aya ta mike abinta, tafita daga d'anki cin abinci.
***
Ina kwance nasaka yaran a gabana bayan na gama basu nono, har sun same barci, ni kuwa kuka nake sosai sabida tashin hankali da tararadi. Dafani tayi na mata banza sai da tajuyo gabana tace.
"Kiyi hakuri! Ki amshi tayina."

"Nah! Haramun ne nima a cikin nima, Sadakinshi na hannun Abbana! Kuma bana jin zan yafewa kaina cin amanarshi don Allah kiyi hakuri ki nima mishi auren Batul ko Khalilah"

"Kece Masarautar take bukata! Kece zaki iya abinda muka gaza yinsa! Kece kaɗai zakin iya tankwarashi."

"A'a Nannah! Ni bazan iya ba don Allah kubarni haka Ni zuciyata Hameed kad'ai nabawa Muwahalin gina fadarshi, sannan Shi Ash"

Kasa faɗar sunanshi nayi sakamakon nauyin da yayi min, kallon yaran nayi kamar zan saka kuka nace.
"Nah! Ki maidani gida."

"Zan maidaki, amma sai yadawo yaga yaranshi,"
Tana gama faɗar haka tasakai tafita.
Zama nayi cikin damuwa, wayar da tabani na ɗauka tare da kiran Ummina, ina kuka nace.
"Ummina! Don Allah ki gayawa Nannah na amshi Sadakin Hameed tasani a gaba da amsar tayi D'anta."

Cikin sanyin jiki tace.
"Safinah! Baki ganin zatace kin kawo karata ce? Kiyi hakuri tunda Hameed kike so baza a miki dole ba, amma ki cire son yaran nan a ranki zaki fahimci dalilin haka."

"Ummina bazan iya basu Yarana ba! Domin musulunci ya bani su don Allah Ummina karki sare min kwarin gwiwata, Ummi rabani sa yarana zasu yi, wallahi za a kawo miki gawata."

Kashe kiran nayi ina kuka sosai. Kara wayar tayi na duba My Dudu na gani, cikin sauri na ɗauka tare da mannawa a kunnena nace.
"Dudu! Zasu kwace minsu."
"Ya isa ki kuma nutsu ki saurareni"
Haɗiye kukan nayi ina gyaɗa kaina, kamar ina gabanshi yace.
"Koda su Abba sun amince zasu tilasaki auren wanda baki so I promise you bazan taba barin haka ya faru ba kinji Yayata, sannan shawara ɗaya. Kicire idanunki akan yaran idan tasa aka kwashesu kema ki fita harkansu da yaran, sai abu nagaba karki kara barin idanunki su zubda hawayenki, kinsan me yasa suka biyo miki ta jikin yaran sabida sunsan yaran sune Rauninki weakpoint ɗinki, idan kika sake zuciyarki tayi rauni zaki dawo kasar nan ba tareda yaranki ba, abinda zan gaya miki shine kifita batun yaran suna sonsu kina sunsu, sai kubuga wasan yadda dole ɗayanku ya hakura, ke sunsan bazaki iya hakura ba akan yaran kema sai ki duba ta yadda zaki rama sai a tashi wasan 1-1 amma sai kin koyawa zuciyarki jarumta, in ba haka ba toh ba makawa ranki zai ɓaci kiyi tunani dakyau, na barki lafiya Yayata"

"Nagode Duduna ai na bar maka girman dan nice yayar a baki amma a zahiri kaine yayan nice kanwar nagode Dudu."

Murmushi yayi sannan ya kashe wayar duƙ abin duniƴa ya dame damamiya irita, na kuma shiga tunanin taya zan kwaci kaina kamar yadd Dudu yace.

Dan Wallahi bani bada yarana ina zan iya wannan ɗ'anyen aikin na gama shan wahala da ciki a kore ni da cikin yau dan sun fito sun zama mutane ace za a rabani dasu Wallahi karya kenan....



Kuyi hakuri jiya na gama Typing hmm ya goge😭😭 ban sani ba ko wannan pagen zai yi ma'ana shi yasa sai na koƙa gado naja bargona na kwanta Bazan iya bakin ciƙi biyu ba😭
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*

Oum Muwaddah......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....

_Allah ya kyauta hmm 😹😹😂 Wuya makarantar Kare: Godiya ga MJ 2 paid grp inayin kowani member na cikin grp ɗin da sadaukarwa da kuka min😍😘_


Page.٤١-41
Shiru nayi ina tunanin toh taya zan fara, shin ta ina zan fara nan da nan na takura kaina da tunani, kafin wani lokaci ciwon kai ya sakoni a gaba, ajiye kome nayi nace daga baya na duba alamarin.

***
Jikin Dr da sauki sosai don har ya farka, a hankali yake magana sabida harbin ya taɓa zuciyarshi dole ya kiyayye duk abinda zai yi dole yayi cikin nutsuwa da takatsantsar.

Sati biyu kenan da aikin kenan, kuma za ace anyi nasara tunda ga alamu sun tabbata, India suna cikin jerin kasashen da likitotinsu suka iya aikin zuciya da koda, shi yasa mutane suka fiya damuwa da zuwa can. A yanzun dai yana kwance ne. Za aiya cewa Alhamdulillah tunda kome nashi lafiya.
***
Jordan.
........
Shiru Fadar tayi sakamakon mahawaran da ake tsakanin Magoya bayan Abu Zarri da Ukshe.
Can wani daga cikin tsofin masarautar ya mike ya fara magana da cewa.
"Dole D'ayanku ya hakura d'aya yayi mulki na tsawon shekara d'aya in yaso wata shekara wani ya karɓa yayi shekara d'aya. Wannan shine kad'ai shawaran da zan baku matuƙar kuka amince toh ba makawa za asami zaman lafiya da fahimtar juna idan kuka k'i za a fuskanshi zubda jini a tsakaninku, mu kuma bama fatan nulkin yafita daga cikin Banu Hashim dan yin haka tankar kwarawa Makiyan Allah karfine, don Allah ku dubi maganata da fuskar tausassawa bata fuskar kausassawa ba. Idan kuma kunga bazaku iya hakuri ba toh sai dai mu dawo da me guri gurinsa.

"Kai!!! Tsohon kwano Wallahi babu wanda ya isa ɗare wancan kujeran sai ni ko Ubana ne yace zai zaune kujeran sai na aikashi garin da ba a dawowa Wallahi kuma na kara maka da tallahi ni Marhum sai na zama sarki na biyar a cikin jordan. Kamar yadda aka kashe min d'ana ya tabbata haka zamana a wancan kujeran ya tabbata."
Cewar Marhum wanda shigowarshi kenan cikin Fadar, ya kuma jiyo abinda Tsohon yake fad'a.
Zai wucce inda kujeran yake, D'an Uwanshi kaninshi wato Amir Uzaif wanda aka bawa Matsayin Mahaifinsu Ukshe, waziri yayi maza yasha gabanshi tare da girgiza mishi kai yace.
"Wannan kujeran ɗauke take da jinin Adilai, babu fajiri ko fasikin da ya isa hawarta ya zauna lafiya in ma daga sarkine ko zuri'arsa ba zasu taɓa zama lafiya ba, shekaru dubu d'aya da hamsin bayan wafatin manzon Allah larabawa da kabilu daban daban sunzo kuma sun kafa daula amma dake babu adalci basu kai labari ba, har zuwa lokacin da Kabilar Banu Hussein suka amshi mulki aka kifar dasu, dukda musulmai ne bai hana su jagoranci mulkin zalinci ba. A sanadin zalincinsu Yahudawa suka amshi kasar da karfin tsiya."
Kallon cikin idanunshi yayi cikin nutsuwa yace.
"Shekara ashirin d'aya Musulman jordan sukayi suna fuskartan Azaba da iziya daga Yahudawa Isra'ila."

Takawa yayi gabanshi cikin jin zafi da kuma kishin kabilarshi da Hashim, karkace kanshi yayi cikin ɓacin rai yace.
"Idan kaga na barka ka jagoranci jordan Numfashina ya katse daga doran kasa, amma matukar ina numfasawa Jordan ta Muh'ad Ashraf ce dashi da duk abinda zai haifa wannan itace alkawarina da na ɗauka na kare wancan kujeran, karku manta su Masoya da Makiya haihuwarsu ake akan turba mabanbanta, haka Nasara da Faɗuwa samar dasu ake daga jinsin D'auk'ak'a.
Yau ya faɗi yaja da baya..."

"Uzaifa!!!" Ukshe ya daka mishi tsawa har sai da fadar ta amsa.

"A'A baba! Karka fara kun kirkiri kiyayya kuya kuya, haka zalika kune kuka kafa tarihi, dole yasa aka haifi me shafeta, ita fansa kishiyarta ramuwa ce, na rantse da Allah bazan taɓa barin koda kiyashine ya kusanci wancan kujeran kuma da zaran an sake Ashraf zan dawo.."'"

"Sai kasheka!!" inji Narhum,
"Ya isa!!!" Ukshe ya daka musu tsawa cikin ɓacin rai yace.
"Ku same ni a gida"

"Kuma nasami labarin an sake Irfan na zarta da duk wanda yaga Irfan ya kashe shi." inji Uzaif.

"Wai kai waye ya tsaya maka da zaka bada umarni mubi! Ko shi wanda kake karewa ne ya baka kuɗi ka kare shi? Nawa ya baka? Nawa ƴa saye kA? Wallahi naji bakin cikin haihuwarmu a ciki ɗaya, nayi alwadar zamanka d'an uwana kuma da kai da Ashraf nine ajalinku."

"Kace nawa aka saƴe ni! Nawa ya bani, toh bari na tuna maka wani abinda baka sani ba ko nace ka manta, Shi d'aya aka haife shi, kuma kabilarshi suka masa lakani da Al Amin, sabida gaskiyansa. Kishinsa K'uraishawa suke, dukda ya bijiro da wata addini bai hanasu yarda dashi ba, toh irin yardan da suka bashi alokacin da suke kiranshi Al Amin kasan meye sunanshi? Itace ake kira da Kishin kabila. Wallahi idan bakayi da gaske ba zaka mutu."

"Ni kakr gayawa Magana son ranka! Eyye sai na kasheka."
Dakyar aka shiga tsakaninsu, kowa ya jinjina wannan kasadar na Uzaif sabida kishin kabilarsa da kuma yarda da Ashraf da ita kanta daular ƴa bada rayuwarsa kuma ashirye yake ya bada rayuwarsa dan cigaban masarautar.

Janshi Ammar yayi cikin rarrashi yace.
"Haba Uzaif me yasa ka zama mara hakuri ne. Mulkin jordan ko Ashraf yana nan ko baya nan Allah zai cigaba da kare masarautar, bai dace kayi wasa da rayuwarka ba, idan yau aka kasheka ya kake so Meenar tayi da yaranka."

Idanunshine suka cika da kwalla wanda suka sami damar saukowa, yace.
"Kasan kama Ashraf da akayi da Hannun Mahaifina da D'an uwana, taya zuciyata zata yafe min abinda suka aikata, tunda kaga Sabida mace Ashraf ya bar masarautar nan ga abinda suƙa masa, toh tabbas bazai kuma dawowa ba, idan ba wani ikon Allah Ashraf yayi fushi damu kenan"

"A'a zai dawo Insha Allah, muyi koƙarin ganin mu daidaita wasu abubuwan in yaso ana sake shi sai muje mu dawo dashi."

Juyawa yayi yabar Ammar a gurin. Ya mafita daga cikin Fadar gidansu Ghaniyu yaje, yaga gidan na kone babu kome a ciki, kwallar tausayi da bakin cikin kasancewarshi D'an Ukshe ne ya zubo mishi dan yaƴi Imani da Allah da sa hannun Mahaifinsa."

"Hmm! Mulkin zalinci da ake gudanarwa a kasar nan Allah ya kawo mana ɗauki dan mun rasa gane waye sarki waye yan baran danshi, tunda muke bamu taɓa ganin fuskar sarkinmu ba, mudau muna bin azalimai kawai Allah ka kawo mana agaji."

Shiru Uzaif yayi jikinshi na kara mutuwa, juyawa yayi ya kalli tsohon. Wanda yake cike da wahala, dole yaja kafarshi zai bar gurin tsohon yace.
"Ku kula da kyau dan akwai masu shirin ganin masarautar Banu Hashim ta wargaje sabida rashin adalcinku."

Tafiya tsohon yayi yaki bawa Uzaif damar ya masa magana.
Haka ya gama ɓata lokacinsa ya bar gurin.

***
Oman....
Ina jin yaran na tsalla ihu nayi banza dasu, dan ko jiya Sai da Natasha tazo ta ɗaukesu bata dawo dasu ba sai da jikin Aanih yayi zafi ta dawo min dasu. Ban da ikon hanawa da zasu ce min nice bare kuma bakar fata ban isa rabasu da jininsu ba.

Shi yasa yanzun ma da suka dawo min da Aamih tana kuka naki kulasu, sai ma gyara kwanciyana da nayi, bawai dan bana jin kukan ba sai dai dole na koyawa kaina share kukansu, sabida nasan nan gaba dasu za ayi amfnin cutar dani, tunda gashi an fara za a ɗauke su karfi da yaji a tafi dasu. Suna kuka amna na fahimci basa kai yaran gurin da Nannah take dan bata kaunar jin kukansu itama, cike da jik haushi na mike na zauna ina karewa Aamih kallo. Dan takaici take bani, inda aka sasu kuka daban ni da suka zo suna min daban. Jawota nayi ta fasa wani irin kara tana shiɗewa. Da sauri nayi kanta tare da cire mata. Zaro idanuna nayi ganin yadda kafadarta ya kumbura.
Kuka ne ya kwace min, cikin tausayawa nake kallonta. Duba Aanih nayi itama hannunta dai dai gwiwar hannunta a kumbure, tana kuka ɗaukarsu naƴi na fita dasu zuwa ɗakin Nannah wacce take zaune ana tirara mata gashinta, tana ganina ta mike da sauri ta amshi Aanih tace.
"Safinatu meye yasami Maryam da Asma'u."

Bakina ya gaza furta kome girgiza kaina nake cikin kuka. Bata iya cewa kome ba, ta kalle me tirara mata gashi, ɗaukar wayarta tayi ta mika mata, a hankali tashiga lalubar number can ta manna a kunne tace.
"Yanzun nake son ganinka."
Kashe kiran tayi sannan ta zuba min ido cikin ɓacin rai tace.
"Me ya faru dasu?"
Har na buɗe bakina zan gaya mata gaskiya sai kuma wani tunani yazo min da zaran na faɗa ba yarda zatayi ba, tunda iyakata kawo minsu suke bazance ga abinda ake musu ba. Sai nace mata,
"Faɗowa sukayi daga gado!"
Sunkuyar da kaina nayi, kallona tayi cikin rashin yarda tace.
"Toh daga yau idan kun kwana acan kuzo nan ku zauna sai lokacin kwanciya yayi kukoma."

Sam banji daɗin haka ba, amma babu yadda na iya tunda tafini Iko da yaran dan haka na gyaɗa mata kai alamun amincewa. Muna haka likitan yazo ya dubasu nan ya gano gocewa ce, ya musu gyaran amma sunsha kuka, ana gama musu na shigar dasu cikin d'akinta na basu nono sai da suka koshi har sun fara barci sai ga Natasha tashigo, da uban gadaranta tazo zata ɗauki yaran na dakatar da ita, ta hanyar cewa.
"Kinzo ki karasa min sune wanda kukayi bai isheku ba sai kin kara da wani, karki kure hakurina."

Cike da rashin kunya ta kalli tsakar idanuna tace.
"Kinsamu ma ana ɗaukar shegun yaranki marasa daraja a cikin msarautarmu, idan kika kuskura masarautar jordan tasan da ke yanke miki wancan siririn wuyartaki zasu yi, banza karƴa mara daraja."

Kura mata ido nayi bansan me zan faɗa mata ba. Amma ina kallon yadda ran Nannah ya ɓaci dan tashigo lokacin da Natasha take zagin gudan jininta, har da dalilin haka naki magana.

"Natah!!! A razane suka juya ita da Kawarta Amah, jikinsu na rawa matsa musu tayi suka wucce. Itama tabi bayansu, har cikin gidan sai da tayi musu tass sannan ta gargaɗesu akaina sannan tace.
"Yara bazan rabaku dasu ba. Amma Uwarsu basa'arku bace, nice na hana maganarki da Ashraf ba Binti ba, kar na kuma ganinki a gurinta......


😇😇😇😇
*Inayinki Mommy Sayeed keda sauran.....Mom Abul ƙema na gaisheki*

   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 19 pages Insha Allah*

Oum Muwaddah....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....

Page.٤٢-42
   "Idan kuwa kika bari na kuma kamaki da laifi makamancin haka toh raina zai ɓaci kuma zan hasala, ita ɗin bakuwarmu ce kar na kuma ji kar na kuma gani."
Tana gama faɗar haka ta juya abinta dama faɗar ce ta kawota kuma ta gama, nima bata kyale ni ba da tashigo.
     "Me yasa baki rama ba? Eyee bata kai  Batul ba sa'ar Khalil ce dan haka daga yau duk wanda ya taɓa ki karki kyaleshi idan kuma na samu an taɓaki kinyi shiru zan baki mamaki."

Tana gama faɗar haka ta fito tabarni ina fama da yaran, karshe da taji kukansu yayi yawa ne tashigo ganin duk na rasa yadda zanyi dasu yasata taimaka min da ɗaukar Maryam, muna rarrashinsu har suka samu barci.

           ***
Wani irin d'akine me cike da tarkace kaman na bokanci, Juya musu baya yayi cikin ɓacin rai yace.
"Kowani wayewan gari ina kara jin nisar dake tsakanina da ita, itace burin zuciyata amma mutuwa tayiwa gangan jikina iya ka da ita, me yasa kuka dawo dani bayan can yafe dacewa dani? Bazan iya hakura da ita ba dole mutafi tare dole tabini mu cigaba da rayuwarmu a can."

      "Ranka ya daɗe ai"
"Karka min kome Nuratu! Kece kika dawo dani idan narasa Safinah."
   Daga haka ya koma jikin Wani abu ya kwanta.
     Fitowa sukayi Hajiya Nuratu ta kalle Kawarta Salmah a dame tace.
"Salmah! Nayi danasanin tadda wannan alamarin gashi yana niman zame min alkakai"

   "Karki damu Nuratu zamu san abinyi babu abinda zai faru sannan kiyi ƙoƙarin ganin Yarinyar ta dawo."

Gyaɗa kanta tayi dan ta gamsu da shawarar da Kawarta ta bata, har gida suka ta sauke Salmah, sannan ta wucce gida. Jikinta a mace sabida bata san ta yadda zatawa Abba Magana ba, dan tana gudun kar ya d'agota. Dan haka ta ajiye a ranta zuwa ranar girkinta ta masa magana.
***
Duk yadda naso kauda kaina akan wancan fitsarariyar yarinyar na kasa, domin iskanci take min a bayan idanun mutane, ranarda ta kaini bango munxo cin Abinci Nannah tafi nima mana visa, zamu tafi Umra daga nan ita zata duba yaronta.

Ni da yarana muka fito gurin shan iska, ashe ita da kawayenta suna can gefen lambun da muka zo, ina rike da wayar da Nannah ta bar min, yau ma gwada sa'ata nake ko zan sami Numbersa. Amma shiru takaici ya ishe ni.
Aamih ce naga tana kokarin mikewa tsaye bakina a sake, dan naga basuyi wani rarrafe ba, dan yanzun ne ma Aanih take ja, ita kuma Aamih take rarrafen zaki. Abin alajabi sai gashi ta mike tsaye, aikuwa ta fashe da dariya, shiru nayi ina lissafin wataninta, sai naga basu wucce wata bakwai ba, dan yanzun kusan watanmu biyi kenan À Oman. Ai ganin haka itama Aanih ta shiga kokarin mikewa dariya na musu tare da rungumesu, ina cewa.
"Aanih kiyi hakuri kawai Aamih ta fara, tunda itace Babba."



2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment