Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi na kalle shi. Bansan lokacin da kwalla ya shiga saukowa daga idanuna ba, sake min hannuna yayi sannan yace.
"Kiyi hakuri, wallahi bansan dariyar zai sakaki kuka ba, kiyi hakuri bazan kuma ba."
      Buɗe motarsa yayi ya ɗako tissue ya mika min, goge kwallar nayi, kaina a sunkuye. Dan kunyar kaina nake ji na kukan da nayi akan abinda bai taka kara yakarya ba.

     "Kinsan me yasa na miki dariya! Sabida kin kawo abinda hankali bazai ɗauka ba, tabbas Babansu Twins yarone kamar yadda kika ce, amma ya kamata ki ɗaga shi daga cikin jinsin yara ki kaishi cikin na manyan sabida,  Yan biyu, da kuma nan gaba zan kara fahimtar dake abinda nake son ki gane."

   "Meye haɗinka da kawar Batul?"  na tamvaye shi tare da tsare shi da idona,
  D'age min gira yayi cikin tsokana, ya shafa kanshi sannan yace.
"Idan kin amince, rana d'aya za a kawo min ku."

     Kallonshi nayi bakina har rawa yake nace.
"Kana nufinm"
  "Eh ku biyu zaku zauna,"
           Kauda kaina nayi cike da zafin rai nace.
"Ok, kaje ka zauna da ita dan ni ba zan zauna da sa'ar Batul muna gogayya da ita ba."

     Mamaki na bashi yadda na ɓata rai, akan yace mu biyu zamu zauna, murmusa min yayi sannan yace.
"Kin cika kishi! Bana fatan rike mata biyu, amma ki sani kishi ke haifar da kishiya, ki sassauta kishinki ni mijin mace ɗaya ce
tal."

        "Wacece a ciki ni ko Ita."
       Na tambayeshi, gyara tsayuwarshi yayi tare da kura min ido, yace.
"Banda sai anyi aure zaki halatta min wallahi da idan ɗauke ki yanzun na kaiki cikin gidana, babu wanda zai kuma kallon tafin hannunki."
  
  Kallonshi nayi cikin wani bakon yanayi, haka kawai naji ina tausayawa ƙaina, lokaci guda idanuna ya fara da ruwa. Sunkuyar da kaina nayi sabida saukarsu. Suna d'isa  a kasa. 

"bansan me yasa ba, bansan me nake ji ba, kawai ina tausayawa rayuwata ce idan na rasaka, Dr ka tafi kawai dan ina jin tsoron kar na fara sonka kuma nazo na rasaka."

   Takowa yayi gabana tare da soka hannunshi a cikin aljuhunsa d'aya yace.
"Ki d'ago kanki ki kallr cikin idanuna, ce min kina sona."
       Girgiza kai nayi wani irin kuka ya kwace min, dafa jikin motar nayi, nace.
"Ko baka ce ba, ina sonka mahaukacin son. Wanda zai iya tarwatsa zuciyata idan na cigaba da ɓoyewa, Hameed kaje kawai idan kacigaba da zama dani bazaka karu da kome ba, sai tsantsar damuwa"

       "D'ago kice min na tafi ni kuma zan iya juyawa." ya faɗa min yana kusantar inda nake.
       "Bana son Adil da Ammah su."

   "Ke! Lafiyarki kuwa kinzo kinsa garjeje a gaba , kina kuka shi kuma da yafiki shirme yabi ya rikice kai jama'a duniya tayu lalacewar zabi."

          Da gudu na shige cikin gida ina kuka, koda na isa falon ban tsaya ba na shigesu Ummi da suke zaune.
        
Bin bayana yayi da ido, bai masan me hajja ke cewa ba, shi damuwarsa nice, haka ta gama surutunsa.
             Haka ya shiga motarsa ya bar gidan zuciyarshi ba daɗi, na rasa gane meke faru dani matukar zan haɗu da Dr tausayinshi nakeji haka mukayi kusan kwana goma, dakyar ya dakatar da shirmen da nake mishi. Tsakanina da Hajja kuwa toh ko Tom nd Jerry sun sallama mana, domin kuwa taƙanzo tamin maganar banza ni kuma na shareta idan ta buwaye ni ce mata nake Hajja ko zamu nimo tsohon irinkine a ɗaura muku aure, bata kuma bin takaina.

    ........ Tsakanina da Dr soyayya ɗoɗarr domin kuwa na gabatar dashi har anyi magana, karewa ma Sadakinsa na hannun Iyayena, an bari sai na yaye yarana wanda suke da wata huɗu zuwa biyar.

      ***
Watansu Aanih bakwai aka shirya mana tafiya zuwa Oman, tsakani da Allah nasaka Ummi agaba ina kuka bazani ba, dan nasan idan naje sai su nemi rike min yarana wanda nake ji yanzun kamar rayuwata ce su ɗin ko ciwon hakori suƙe tare muke dasu, dan har tsokanata Dr keyi wai amka uwar son yara, bana jin kome, gefe guda har da tunanin dr yake hanani tafiya, dake Ummi ta harbo jirgina sai tashiga rarrashina da cewa.
"Ayya Uwata kwana nawa ne kamar yau ne fa, har kun dawo."

  Da ire iren magana masu daɗi da laushi, tasamu na amince amma sati biyu zanyi, murmushi tayi a ranta tace.
*Ta yaro kyau take bata karko*
              Kin gayawa Dr nayi, ranar da yaji. Ya kirani amadadin nai mishi magana sai na saka mishi kuka, na rasame zance mishi.
           "Ya isa Beauty! Dalilin da yasa kika ɓoye min kenn bazaki iyafaɗa min ba sabida kuka zaki min? Karki damu duk inda kike kisa ranki muna tare, insha Allah zan biyoki soon, an jima zanzo."

   Daga haka ya kashe kiran, ranar nayi kuka me cin rai sosai dan gani nake kamar basu min adalci ba,.

           Da dare da yazo kasa sake jiki nayi inata ɗari ɗari, dake yanzun a falon Abba muke hiran haka ya gama shirunsa sannan ya ajiye min rafan kuɗin Oman har guda uku, sannan yasa kai zai fita. Cikin sauri nabi bayanshi na rungume shi tare da sake kuka ina cewa.
"Kayi hakuri bazan kuma ba"
          Wani irin yanayi yaji ya sauko mishi tare da kasala me mugun kashe jiki, janye hannuna yayi wanda nasa na kamkame shi, ya janyo ni gaba cikin damuwa yake kallona.
   Lumshe idanunshi yayi cikin damuwa yace.
"Toh ya zan miki! Nazo amadadin ki tarɓe ni da kalamai masu daɗi sai kuma kika sani a gaba da kuka, kinsan yadda nake ji. Banda kar na shiga hakkin yaran nan ba, wallahi bazan bar gari yawaye ba tare da kin zama mallakina ba."

  Lumshe idanuna nayi tare da saka hannuna a wuyarshi na kara tsayina tare da d'aga kafana,  haɗa fuskarmu nayi kafin yayi yunkurin dakatar dani, na haɗe bakinmu guri guda. Kallon fuskana yake musaman yadda kwalla ke sauka wannan na koran wannan a guje, a sannu ya buɗe min bakinshi na rasa yazanyi, kawai sai na nemi janye bakina daga gare shi, rike bayana yayi da hannunshi duk biyu ya zura harshenshi cikin tare da lalluɓo nawa, buɗe idanuna nayi da sauri. Lumshe nashi yayi sannan ya buɗe. Yana kallon cikin kwayar idona yake, lumshe nawa nayi, a sannu na kwace bakina ina sauke ajiyar zuciya, kuma sai na fashe da kuka tare da kifa kaina a kirjinshi ina kuka, sunkuyar da kanshi dai dai kunne na yace.
"Thanks for thi hot kiss"

🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃
Yau nayi batsa😎😏 naji cass...
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*




Oum Muwaddah......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....


Page.٣٩-39
Sun fito zasu inda motarsu take kawai aka buɗe musu wuta, cikin sa'a suka sami Dr a kirjinshi gefen, take ya zube a gurin.
Dudu dasu Ummi da Abba kuwa basu same su ba, ana cikin haka wasu maharan suka zo aka fara musayan wuta, abinda ya kuma ɗaga kowa hankali dan ba karamin d'agawa mutane hankali yayi ba dan har cikin inda mutane suke harbin ke shiga.
Haka sukaƴita harbim juna har masu harbin baya suka samu kashe mutanen da sukayi harbi Dr, wani abin mamaki wadancan sunfi su iya sarafa makami, kuma sun iya harbi a nutse kamar suna, shi yasa suka same damar kashesu, suna gaba kashe su. Suka dawo kansu Abba.

"Kutashi ga mota can zai kaiku gida, sannan shi Dr zamu wucce da shi Asibiti."
Dake a kwai tsoro a ransu haka suka mike, tare da bin umarninsu har cikin motar, suna shiga ana tadda motar zuwa gida.
Komawa kan dr sukayi tare da kamashi suka sakashi a motarsu zuwa Asibitinshi. Cikin gaggawa aka amshe shi, ana kokarin ceto rayuwarshi.

Cikin kwarewa su Dr Shahban tare da wasu drs suka rufa akanshi, hankalinsu yayi mugun tashi. Kafin wani lokaci labarin harbinshi ya karaɗe ko in, har takai shugaban kasa da kanshi yazo asibitin domin duba lafiyarshi,

Tsawon awa takwas akayi ana faman ceto ranshi, amma ena abun ya faskara dole shugaban kasa yasa hannu aka fiddashi da jirgin fadar shugaban kasa zuwa. India, sabida bullet ɗin ya kuskuri zuciyarsa, abu mafi hatsari a tare da ciwon shine da zaran akace za a cire bullet ɗin da karfi toh tabbas mutuwa zayi. Shi yasa duk suka birkice akanshi suka rasa ya zasuyi dashi.
Dole aka tattarashi sai Mumbai.
***
Wani irin mafarki nayi me cike da firgice, akan dr zubur na mike tare da janyo jakata na ciro wayata, na fara kokarin niman gida. Abin haushi ashe number kasata ce bazatayi a kasar ba, tilas ni wurgi da wayar ina tsaki, tun bayan sallar asuba na koma barci, duba gun yaran nayi naga suma barci suke, saukowa nayi a gadon, na nufi ban ɗaki.

Wanka nayi sosai sannan na fito, na same Nannah tana zaune tasa jikokinta a gaba, tana kallonsu. Dake akwai rigar wanka a jikina, har kusan kwanjina na nemi guri na zauna nace mata.
"Barka da safiya Nanna"

Fuskanta ɗauke da murmushi ta kalleni cikin sakin fuska tace.
"Binti! Kin tashi lafiya, ya kwanan kawayena? Naga sai barcinsu suke"

"Hm! Ai haka suke ko a gida basu cika rikici ba, sai dai ko idan suna jin yunwa."

Kallona tayi taga hankalina nakan jakata ina kokarin ciro mai na da nake shafawa. Girgiza kanta tayi, dan tun kafin n iso tasame labarin abinda ya faru, dan haka tayi kokarin ɓoyewa dan kar naji na ɗ'aga hankalina tsaf tasan halina zan iya juyawa gida.

Ina gama shafa man, na zuge akwatina tace.
" Binti ga kayanki a nan!"
Ta nuna min wall dress drower, a sanyayye na juya gurin drower. Zan buɗe sai ga wasu yan mata su uku sun shigo cikin unifoam brown, suna gani na a tsaye suka zo ɗaya ta rike ni tamaidani bakin madubi, ta zauna dani akan stool. Sannan ta buɗe wani drower set na kayan makeup ne, ta cirosu ta fara bazasu saman dress mirro ɗin, d'aya kuma ta buɗe gurin kayan sawa ta fara cirowa tana ajiyewa. Dogayen riguna ne masu masifar kyau da tsada.

Wani irin kwallayi suka min me matukar ɗaukar hankali, Nannah tana kallonmu sai murmushi take, karku manta larabawa a harkan kwalliya da k'awa daga su sai India. Dama dama turawan Uk, suma suna cin Uwar dukiya ga.

A hankali suka gama min kwalliyar sannan, suka shiga nuna min kayan. Musaman Nannah ta nuna musu ɗaya gefen aka buɗe, royal gown ne masu mugun ɗaukar hankali,
A hankali ake fiddasu ɗaya bayan ɗaya, aka suka fiddasu sosai wata maroon na hango wanda akayi combinet da Golden, na nuna musu.. A sannu suka ciro rigar aka ajiye min kallon Nannah nayi, ta sakar min murmushi, mikewa nayi na shiga inda zan sanya inner wear, ina gamawa na ɗauki rigar nasaka, ban zuge zip ɗin, fitowa nayi suka gyara min zip ɗin.
A hankali suka gyara min zaman rigar , sannan na zauna suka gyara gashina suka saka min wani siririn veil da karamin crown. Safar hannu suka samin, sannan suka buɗe inda takalma suke na nuna musu wata golden tare da pouse ɗinshi, abin haushi ana fidda takalmin naganshi heel ce, kamar zanyi kuka nace.
"Babu flat ne? Nifa ban iya amfani da heel ba."
"Ma! Ai duk shigar da zakiyi dole takalmar kenan."
Juyawa nayi na kalli Nannah da take jinmu hannunta rike da wayarta.
"Binti size ɗinki kamar yadda nasani ne ko?"
Gyaɗa mata kai nayi cike da sakalci, murmushi tayi sannan tace.
"Mantawa nayi na gaya musu baki saka takalmi masu tudu. Amma yanzun zasu kawo, bano bace na shirya miki kayan ba, Aunties ɗinki ne. Amirah Zahra da Amirah Khadija, sune suka shirƴa miki,"
Muna cikin haka sai ga manyan bags an shigo dasu takalmar ce kaman na farko aka shiga shirya min su. Sannan suka ciro min takalmin nasaka. Suna dabda gama shirya ni sai ga masu kula dasu Aamih, kallonsu Nannah tayi. Naga sun dukar da kansu kasa, suna niman afuwarta na makarar da sukayi, cikin sauri suka isa bakin gadon, ɗaya ta wucce ban ɗaki ta haɗa musu ruwan wanka, ɗaya kuma ta zauna tana shafa kan Aanih, cikin nutsuwa tanayi tana hura mata iskar bakinta a kunne, mika yarinyar tayi, a hankali tasa hannu ta ɗauketa tare da mikar da ita yarinyar tayi mika sosai sannan ta maida ita kafaɗarta. Ta shiga zare mata kayan jikinta. Sannan ta ɗauki wani farin showel ta lulluɓata dashi, suka nufi ban ɗaki bakina a sake nake kallonsu, duk wannan shirin da ake min babu wani motsin arziki sai aikinsu kawai, haka ya ankarar dani inda nake, masarautar me daraja na takwas a daular jaziratul Arab, wato yankin gof. Dan haka dole kome zasuyi susa nutsuwa da hankali, dole su maida tunaninsu kan abinda ake, zan iya cewa a sanina Nannah mace ce mai faranfaran da jama'a. Amma zuwana jiya. Na fahimci kaskantar da kanta tayi,sabida rashin ɗanta, da kuma rashin gida. Yau gani ga ita sai murmushi wanda ada itace kejana da hira yanzun jinin sarauta haɗi da Izza suna yawo a jininta, gata dai amma ba magana ba kome sai murmushi.
Suna gama shirya ni, suka shiga fesa min wasu turaruka masu karfi, wanda yasani atishawa. A kiɗime ta ɗago ta kallesu cikin rawan jiki suka shiga min sannu.
"A'a babu kome, jikina ne baya son turaren amma ina lafiya."
Na faɗa musu a sanyayye, nuna min kusada ita tayi na zauna, ina jin kewar gida.
"Bari su shirya Kawayena sai mutafi ki karya ki kuma bi yan uwa da iyaye su ganki."

Gyaɗa mata kai naƴi, ina son sabon sim amma narasa yadda zanƴi kaina kasa nace.
"Nah ina son kiran yan gida."
Mika min wayar hannunta tayi, na ɗ'ago kaina zan mata magana lumshe idanunta tayi. Karɓa naƴi na mike zan ɗauko jakata, D'aya daga cikin yan mata tace.
"Amirah! Me kike bukata."
Murmushi na mata, sannan nace.
"Jak"
Ban rufe bakina ba ta ɗauko cikin girmamawa ta mika min, sannan tace.
"Kina da daraja me girma a cikin masarautar nan, duk abinda kike bukata basai kin wahalar da harshenki ba, nunawa zaki yi. Mukuma zamu idar miki, dan ke kamar y'ace a cikin gidan, Sabida Sultan Ash."
D'aga mata hannu Nannah tayi ta haɗiye maganar cikin girmamawa, duk sai naji ni banbarakwai. Wayata na ciro na fara niman Ummi wayar akashe, sai na nimo Abba shima haka, a dame na kalli Nannah nace.
"Nah wayarsu bata shiga."
"Ki duba Dudu."
Shima da nasaka ban same shi ba, sai da na gwada sau uku kafin nasame shi a sakalce nace mishi.
"Dudu!!! Me yasa wayarku yaki shiga ne? Tun ɗazun nike nimanku."

Muryanshi a sanyayye yace.
"Kiyi hakuri kinsan jiya, wayar Ummi ta faɗa uwa. Na Abba ina ga yasa a chargi."

"Toh yayi kyau! Kana asibitine ina son kiran Dr, ko ya shiga tiyata ne?"

"Ohh! Sorry dr ya bani sako na gaya miki kan cewa sun kai shugaban kasa India ba lafiya sosai zasu ɗauki dogon lokaci yayita nimanki yau bai same ki ba, amma yace na gaya miki bazaki jinsh ba, sai Shugaban kasa ya sami sauki Insha Allah."

Jikina ne yayi matuƙar sanƴi nace.
"Shine bazai kirani ba! Ok Allah ya dawo dasu lafiya kace ina gaida Ummina da sauran Yan gidan."

"Toh zasu ji, kishafa min kan My lovely kids."

"Hmm" na iya ce mishi dan jikina ya bani suna ɓoye min wani abu amma bani da hujja akan haka, sai dai taya Dr zaiyi tafiƴa bai gaya min ba anya hankali zai ɗauka.

Haka na watsar da zance na mikawa Nannah wayarta,Girgiza kanta tayi tace.
"Ki rike a gurinki"

"Thank You Nah."
Karamin murmushi tayi sannan ta mike nima nabi bayanta, masu kula da yaran suka rufa mana baya, Shashin Sultan AbdulMuttalib bini Abu Safyanu, shashine mai girma me tattare da kayan k'awa da ado tare da kwalliya irinta Sarakunar larabawa, faɗar yanayin shashin tankar lalata lokaci ne, sabida iya tsari da kƴau shashin sarki AbdulMuttalib yayi, mun same shi tare da ahalin gidan bani ɗaya suna zaune.

Muna shiga wata babba baiwa tare da wasu bayin suka fara gud'a irintasu, harshensu suƙe kaɗawa, tare da ɗan bubuga baki.
Kallona Nannah tayi cikin nutsuwa tace.
"Me zaki bawa masu miki maraba da zuwa, masarauta na takwas a cikin Nahiyar larabawa,"
Duk sai na diriri ce. Ma rasa me zan basu, kawai sai na shiga cire awarwaron zinarin da kuma wani irin zobe me haɗe da sarka tare da abin wuyar, yan kunnaye, sarka kafa da zubunarsu na cire na mika masu shi da hannu biyu.

Gud'a sosai aka saka tare da, sake sauti irinta kidansu na larabawa, suka shiga cewa.
"Tarihi ya maimaita kanshi. Yau Mun amshi Sarauniya ta uku na daular Hashmiyya Sarauniya Safinatu Binti Badar Bni Ibrahim Kyari, kin shiga kundin tarihin masarautar Oman. Dan kece ta uku da tabada kyautar kayan adonta ta fanshi kimarta a hannun Bayin da suka tarɓeta, Sarauniya Jasmin Matar Sarki Yasir da tazo ganin Sarauniya Nana Asma'u irin kyautar da tabawa bayi kenan, sai Sarauniya Nana Asma'u itama tabada wannan kyautar ga Baiwarta Azrah a masarautar Jordan wannan abin yazame me muku tarihi dan duk wacce zata zama sarauniyar gobe toh sai tayi wannan makamancin kyautar mungode kuma a kema za a baki kyauta masu daraja a duniya"

Tsabar tsoro da firgici kamar zuciyata zata dirko daga kirjina zuwa waje, sabida kaɗuwar da nayi. *Sarauniyar Gobe? Tarihi ya mai maita kanshi? Na shiga uku Hameed ɗina*

A ɗimauce na ɗago kaina sai arba nayi da wasu manyan tire har guda biyu ɗ'aya shake yake da Lu'ulu'u wato diamond wadda akayi wani abin wuya da tsayinshi daga wuyata har kirjina haɗe da yan kunnaye da zubunarshi, da babban abin hannunsa. Daga Amirah Zahra....

😬😡 *Koda wasa kubar tunanin Tarihi zai maimaita kanshin dan Feener Rabon Dr ce heee😎😏😒*

   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*

Oum Muwaddah....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....

Page.٠٤-40 Masha Allah..

*Na shiga uku na lalace! Ni Safinatu ba dai wancan yaron suke nufi ba*

*(Kuji min Safinah da bidi'a a wasan kwarzo da kuka buga antashi 1-0 shine zaki kirashi da yaeo😎😏😒 Salon Mom Sayeed tasami abik fada bana son reni)*
  Kululu naji cikina ya bada sauti, ga kirjina da yayi min nauyi, tsinkewar gaba. A lokaci guda narasa kuzarina da ɗan karsashina.
       
"Sarauniya Safinatu! Ga kyautar jauhari da Lu'ulu'u daga Gimbiya Khadijah, sai katafaren gida a can wajen gari daga Yarima Ubadullah, sai kyauta me girma daga Sarki AbdulMuttalib ya bada kyautar manyan shagunarshi na zamani dake cikin garin."

     Haka sukayita faɗa min abubuwar da muka samu na kyauta ni da yarana, amma bana fahimtar kome. Sakamakon jin abinda ya nemi kundume min tunanina.
            Ana gama bayyanin muka wucce gurin cin abinci, shima cin abin kamar baza aci ba. Sabida izza kallonsu nake kawai. Yadda suke cikin abinci a nutsu kuma baka jin kome sai karan cokula.
       
         Ban iya cin wani  abin kirki ba sabida damuwa da tashin hankali. Dakyar na iya ɓoye halin da nake ciki dan kar Nannah ta shiga samuwa, yar autar sarki Safyanu itace ta mike cikin yatsuna fuska tace.
"Alhamdulillah, muje Amatullah"
      Mikewa yarinyar tayi dukkansu yan mata ne basu wucce Batul ba, amma idanunsu a tsakar ka yake, dan ina lura da ita yarinyar farkon wacce suke kira da Natasha, tunda aka gabatar dani take cika tana batsewa.

             Ina ganin Nannah ta ajiye cokali nima na ajiye nawa, sun ɗan tab'a hira sannan duk suka mike har dani, ɗakin Nannah muka waccey shima idan nace zaɓ faɗi haɗuwarshi ɓata lokacine.
     Muna shiga na zauna a falo har lokacin zuciyata ba daɗi sabida kiɗimar da nake ciki. Gaskiya zuciyata tana cikin ruɗani. Bansan ya akayi ba na iya haɗiye tashin hankalin da nake ciki.
   Can sai gata tafito, ita da Yan matan nan. Suna gani na suka fara harara ta, basa gaba damuwar dake cin zuciyata ya isheni.
        Kaina a sunkuye  suka zauna a can gefe dani, suna zagina cikin larabci sai da suka ji muna magana da Nannah, suka tsorata.
           Cikin kulawa Nannah ke tambayana kwana nawa zan musu.
       Wasa na fara da farcena  sannan nace mata,
"Sati biyu!"
     Murmushi tayi sannan tace.
"Safinah gashi na tambayi Abbanki zaki min wata biyar, har Abbansu kawayena ya fito tunda saura wata huɗu ya fito"

     Kamar zanyi kuka nace.
"Toh Nah Allah ya nufa."

     Kallona tayi cikin nutsuwa tacigaba da magana.
"Idan kinga zamu takuraki, kiyi kwanakinki ki koma in yaso daga baya zamu zo"

   Cikin jin kunya na girgiza kaina nace.
"A'a Nah ba kome zan iya zama"
    
      Shiru tayi ta share kamar babu magana abakinta, kallonsu Natasha tayi cikin ta nuna musu hanyar waje.
   Da sauri suka fita tare da jin ba daɗi. Kallona tayi cikin nutsuwa tace.
"Abbanki yace kin tsayar da miji ko?"
    Da sauri na ɗago da kaina loƙaci guda zuciyata tana wani irin bugawa. Gyaɗa mata kai nayi idanuna na ciko da kwalla.

"Safinah! Ni a tunani na da ki auri wanda zai miki gori. Ina ga ki auri Mahaifin yaranki mana dagake har shi Ashraf ɗin zuciyarku zai fi samun nutsuwa."

Girgiza kaina nayi lokaci guda hawaye na zuba daga idanuna nace.
"Don Allah kiyi hakuri na rigada na bawa Hameed zuciyata, karkuyi kokarin rabani da abinda zuciyata kedo, yin hak Zai sani jin ba daɗi."

            Kura min ido tayi tana jin haushi, murmushi tayi tare da ɓoye abinda yake ranta tace.
"Bar kuka! Bazan miki dole ba shawara ce kawai na baki, tunda kina da wanda kike so Allah ya nuna mana lokacin."
  Goge kwalla nayi tare da ce mata.
"Kiyi hakuri Nah"
   Girgiza kai tayi cikin nuna ba

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment