Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakuri kome na duniya me wuccewa ne,Insha Allah wata rana sai labari."
Gyaɗa kaina nayi dan na kasa cewa kome har muka isa gidan.
..... Abinda ya faru kuwa, kwana biyu da suka wucce Anim yaje gun Abba dan ya fahimci da zaran aka sallame ni, Suleja zamu koma da Ummi shine munafuki ya sami Abba da cewa ya maida Ummi wannan ba darajarshi bane ace yar shi da uwargidanshi basa gidanshi kuma ai haka zai zamewa Safeenah abin gori, kuma a matsayinshi na babba me mutunci ya kamata ya kankaro darajarshi a idanun jama'a kar ya bari mutane su fahimci matsalar gidanshi.
Nan Abba ya amince, sannan yaje har Suleja, ya sami Yayan Ummi sukayi magana yace yaje ya same Babban yayansu dake Maiduguri, dan haka yana dawowa. Suka tafi da Anim inda aka maida Auren Ummi da Abba ba tare da izinta ba. Koda suka dawo Sheik Hayatudeen Kamfu ya kira Ummi yayi mata nasiha sannan ya gaya mata,abinda sukayi. Hankalin Ummi yayi mugun tashi data gayawa Abdul kwantar mata da hankali yayi sannan yace karta bari nasani dan ya fahimci ina ganin laifin kaina akan faruwan kome, parking da yayi ya dawo dani daga duniyar tunani. Na kurawa gidanmu ido, gashi nan na sake dawowa. A hankali Ummi ta fita, bangarena Ummi tazo ina fitowa ta miko min hannu na riketa sannan na fito a sannu, ganin Umma tafito ita da bakuwarta ya sani juyawa cikin mota da dan sauri, Ummi ta rike ni tare da girgiza min kai tace.
"Duk wanda yayi miki dariya ko habaici bai san kan rayuwa bane, idan kasan kan rayuwa baka dariyar motar gawa."
Riko ni sosai Ummi tayi, har muka iso gunsu Umma kaina a sunkuye.
"Hajiya Maryam! Ya me jikin dai? Kuyi hakuri ban zo muku jajje ba, sabida ina gudun kar nazo ace gulma ko wani abu na daban, dan kinsan duniya ba a iyar mata."
Murmushi Ummi tayi sannan tace.
"Hajiya Barakah ai duk wanda yazo gulma ko ganin wani abu toh zan iyacewa bai san me ake kira da kaddar bane, amma idan kasanta toh babu ruwanka da kalubalartan nawani."

"Hmm! Hajiya Maryam abar kasa a cikin gashinta, nima kamar yadda ya same ki nima ya taɓa samuna, domin kuwa Rashmar ta taɓa kinkimo min magana, wanda sanadinsa tunda muka rabu da Alhaji har yau bamu dai-daita ba, amma ni na zubda cikin gaskiya sabida damuwar zata min yawa ina zan kai damuwa dan a lokacin ji nayi ina ma bana raye."

Riko hannuna Dudu yaƴi muka shige, yana ce min.
"Kin tsaya bin nasu Ummi, da wancar maganarniyar matar sam magana baya damunta, da kuma suka zubda cikin ai gashi Rashmar ɗin haryau bata sake samun ciki ba, da sun bar mata cikinta maybe da tana da ɗanta na kanta."

"Nima da na rasa wannan babyn maybe har na koma ga Allah bazan rike ɗan kaina ba."
Matse min hannu yayi sannan yace.
"Karki damu Allah ya tsare."
Jingina kaina nayi a hankali nace..
"Dudu! Maganata ta dawo."
"Kuma munata binki ki gaya mana waye yasa a sace ki kinki faɗa sau nawa yan sanda na zuwa sai kice baki sanshi ba."

Bansan me yasa naki gayawa Mutane cewa Anim ne ya sace, kodan yadda ya nuna kulawarshi akan ciwona ne ban sani ba, amma wallahi na tsani Anim fiye da kome a duniya dan bana raba ɗayan biyu yana cikin sawun munafukai, sabida yadda yake pretending a gaban dangina da yadda yake cewa idan ya kama wanda ya sace ni sai yasa an minshi wulakanci da bakar izaya, sai na buɗe baki nayita kallon ikon Allah, mutum ya zama annamimi.

***
Jordan.....
Yau jumma'a bayan sallar Abu Zarri yazo zai shiga mota aka, kuskuran harbinsa. Bobyguard ɗinsa suka ture shi ya faɗi, daga nan aka shiga musayan harbi. Dakyar yan bindiga daɗin suka ware bayan an harbi mutum ɗaya a cikinsu. Koda suka koma gida jikinshi rawa yace.
"Ukshe!!!"
Ya kira da karfi, ɗauka rigarshi yayi. Ya fita da sauri sai gidan Ukshe yana zaune akan keken guragu, cikin zafin rai yakaiwa Ukshe tokari. Cikin izza irinta larabawa yace.
"Duk wanda yayi niyya ya fasa shege ne, idan na kyaleka Wallahi ba jinin Banu Hashim ke bin jikina ba. Wallahi tallahi Ukshe mu fara daga yau har ranar da duniya zata tashi."

"Abu Zarri! Na rantse da Ubangiji sai na hanaka farin ciki, Abu Zarri."
"Idan ka fasa kai shege ne. Banza mara mutunci. Banza kawai wallahi sai dai muga bayan juna."

.......
Banu Nazir..
"Alexandra!! Nazo maka Da tayu me gwaɓi, tsakanin Ukshe da Abu Zarri yayi tsamari, idan muka amshi mulkin kaga jordan ya dawo hannunmu, kuma zan ka goyan."
"Adnan! Kaje babu ruwana da haɗakar kowa, idan ina bukatar mulkin da kowa, iya ni zan kurmushe kowa."

"Zanyi murna idan ka nemi goyan bayanka ɗari bisa ɗari."

"Bana niman goyan bayan kowa Iyani kaɗai gayya. Zaka iya tafiya."
.....
Wato wani zazzafar bala'i ya ɓarke a jordan ga arziki ga mulkin babu sarki, sannan ga kaiwa juna harin bazata dan kowa yunkurin kashe junansu. Kuma duk wannan bala'in babu wata hukuma da tayi yunkurin shiga rigima, sabida an bar abin akan iyakar zuri'a guda suke wannan tashin hankali.
Ammar da Uzaif an barsuna matsayin sune masu, sulhu idan ka gansu sai sun baka tausayi sabida tsabar tashin hankali da ya addabi masarautar, kuma a wannaj yanayin Marhum ya dawo dama duk shirin Ukshe ne, idan yasa aka dawo dashi zai san yadda zai fito dashi, a cigaba da fafatawa.
***
Mikar da kafafuna nayi Anas yana matsa min, ni kuma ina rike da magarya, sai tsotsa nake ina gyaɗa kaina, dan ina sauraron kira'ar sheik Abdul Basi. Cikin suratu Maryam, shi kuma yaron ya dage dai matsamin kafar yake, a lissafina dai wata bakwai kenan, cikin yayi wani mugun girma, idan Abdul yazo zama yake yana min dariya, yace.
"My Mom Babys! Kinga hancinki kuwa kamar tukunyar miya musaman nan ɗin nan" buge hannunshi nayi tare da tura bakina, nace.
"Dudu! Kafita idanuna mana kasani a gaba da maganar hancina ya cika girma. Sai na gayawa Ummina."
"Toh kajina har kun fara raba halin ko? Maza karɓa wannan kisha, yana taimakawa gun haihuwa."
Wato wannan alamarin yana matuƙar kwantar min da hali, domin kuwa bana jin daɗin Abba da matarshi Amma Umma babu ruwanta, mamie uwar yaɓ zakale kan ba acewa kome.
"Eyye lallai kuwa, wato ga bawa nan, kinga banza. Bari kisa min d'a aikin akan cikin shegenki, toh wallahi a hir ɗinki dan na rantse da Allah kika kuma samin ɗa aiki sai na miki rashin mutunci, tashi muje shashashar banza kawai, karuwa tasi ba fasinja."

"Alhamdulillah ni cikin shege nayi wasu kuwa, abinda suke aikatawa na shirka yafi karfin kare yaci." na gaya mata tare da mikewa, aikuwa a zuciye tayo kaina zata dake ni, Ummi tace.
"Amma rashin hankalinki ya girmama Nuratu zaki daki Mace da ciki ko? Hmm lallai kuwa bar ganin kina abu bana magana, kika sake na fusata wallahi kika taɓa min Y'a da ciki sai kinyi danasani, dan ko Badaru ne ya taɓa min ita sai duniya tajimu dashi dan ni yanzun ina zaune da kowa sabida Safinatu ne idan babu ita wallahi bazan zauna da shi ba, kisa kai ki ficce min a falo mara mutunci."

Bata taɓa ganin ɓacin ran Ummi ba sai yau, dan haka tuni tasa kai ta fita tare da kwafa, zata rama. Kaina ne a sunkuye ina zubda kwalla, sam bana son fitina, shi yasa har na jure wahalar da Samudawar Ashraf gashi yau gidanmu ana rigima sabida ni, Allah kaɗai yasan ma'anar kwafar Mamie dan naga Babu Allah a cikin alamarinta.

Mika min hank akayi na ɗago kaina, ina kallon Anim, bansan lokacin da na galla mishi harara ba, tunda na fara magana yake sake son yaji me zance amma bai samu danar haka ba, dake Ummi tana gama gayawa Mamie magana ta shige ciki, shi yasa basu gami ba, jin hannunshi nayi a cikin zanina yana shafa cinyata, bansan lokacin da na tsinka mishi mari, dafe kuncinsa yayi. Yashafo marin yakai bakinsa ya sumbata, sannan ya kai kan bakina na buge hannun, leka kofar Ummi yayi, da sauri ya sumbaci goshina, na ture shi, nace.
"Bana cike da iskanci Mugu Azzalumi kawai kai ko tunani haɗuwarƙa da Allah bakaƴi sai iskanci da kasa a gaba wai kana kira da so."

........

Oum Muwadda......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
_Na sadaukarda wannan shafin ga Iyaye mata masu fafutukar kare Yaransu....A cikinsu Har da Mahaifiyata Allah ya jikanki da Rahama👏_

~_Ina muku fatan alkhairi Masoyan MJ daga Whatsp,Wattpad, Face book nagode_ ~

Page.٢٩-29

Daukar ɗaƴa yayi ya musu addu'ar da musulunci ta tanada domin ayiwa jarirai, yayiwa tafarkon wacce aka sayawa bam pink, sannan ya ɗauki wacce aka sanya mata purple bam, yayi mata kana ya maidasu cikin gadon.
"Dudu! Don Allah ɗaukesu a hoto sun min kyaune zan ɗaura a Status ɗina."

Tsuke fuska yaƴi tam sannan yace.
"Koda wasan wasa kar naga hotonsu akan social media, dan zan saɓawa kowa."

Tura baki tayi sannan tace.
"Plss zan ɗaura akan Dp ɗina,"
Hararar ta yaƴi sannan ya fito daga ciki ta biyo bayanshi, tana murmushi tace.
"Abban twins!"
Murmushi yayi ya tsaya, "Plss"
Mika mata wayarshi yayi ya barta ta koma, wani abinda ummi tayi ya kara haɗe kanmu ba kome bane sai cusa mana soyayyar junarmu, idan abu yasamu mutum ɗaya kama ya samu saurane, duk wani dabi'a irinta sako da sako duƙ bamu dashi, sam yadda take da sanyi hali haka muma muƙa ƙasance dan ita har wasu nace mata baci suna maryam ba, amma ko yayya ne mu dai muna son Uwarmu haka, dan tayi na mijin kokarin ganin mu tashi da tarbiya, akasin kaddara da ya faɗa min ne kawai zan iya ce wani abu.
D'akin ya dawo yasame Umma tana son komawa gida, Ummi da Sophia tare da Nanah suna nan, Abdul ya dawo da Umma ya kuma kwasosu Batul ya kawosu. Zuba min ido Khalil yayi sannan ya dubi Ummi yace.
"Allah yasa karshen matsalarta kenan"
"Amin" duk ɗakin suka amsa,
"Toh Ummi ina yaran suke?" Inji Khalilah, mika mata wayar Nanah.
"Duba gallary,"
Da sauri ta amsa, har suna rigayen karɓa, duba gallaryn tayi sai ga hotunan yaran,
"Masha Allah! Haka yaran suke da kyau,"
Aikuwa Khalil ya amshi wayar ya shiga bin hotunar yaran, sai murmushi yake sakewa.
"Ummina Didinmu ce ta haife su, masha Allah bari na ɗaura a Tweet.."
"Sai kasan amsar da zaka bawa Babansu dan Dudu ya hanani."
Inji Nanah,
"Ahtoh na hakura, tunda yace kar asaka."
Duk wannan yana cikin tsarin tarbiyan Umminmu domin idan babba yace kar ayi abu toh karami bai isa yayi ba, kuma koda laifi karami yayi bata taɓa kallonshi zata barshi da yayunsa su masa faɗa, sannan itama ta ɗaura da nasiharta, tunda Ummi ta haifeni har na girma Ummi bata taɓa dukana ba, sai tsawa shi yasa lokacin danaje jordan nasha wuyar jibgar sa suka min.

Basu bar Asibitin ba sai dare, aka bar Ummi, bayan tafiyarsu Dr HZ. Katagum ya shigo duba ni, sam Ummi bata san shine yayita hidima ba, cikin mutunta juna suka gaisa sannan. Ya kama abinda ya kawo shi yana gamawa yafita, ita kuma ta cigaba da laziminta.

***
Washi gari dakin ya kuma cika da yan uwana. Da mutanen arziki tun safe Abdul ya kira Nannah ya gaya mata haihuwar.
Tsabar murna kamar tafito ta wayar. Karfe biyar na yammacin ranar na farka, a sannu abubuwan da suka faru ya dawo min, lumshe idanuna nayi tare da fashewa da kuka. Kukan nawa ya sanar musu farkawata, Batul ce ta fita. Taje ta kira likita. Can sai gasu tare da Dr Katagum, yana shiga yace.
"Ku haɗa min tea! Sannan ku ɗan bamu guri, amma Mama karta fita ta tsaya dan taimaka min."
Duk suka fita, shi da Ummi aka bari. Ya ɗauko auduga tare da wani almakashin ɗaukar auduga, ya karɓi wani kofi. Da kanshi yakawo kwanon silve ya mikawa Ummi sannan ya umarce ni na buɗe bakina, ina ji ina gani ya wanke harshen tass, sannan ya kalle yadda nake kuka sosai,taɓe baki yaƴi cikin gatsali dan matsalarshi bai iya magana ba. Yace
"Yanzun ɗan wannan abin kikewa kuka, kika iya haihuwa sai wanke baki ne kike zubda hawayenki, toh ai sai ki ɗaura ɗammara dan yanzun zaki sha hot tea."
D'ago idanu nayi tare da kallonshi. Karɓan tea ɗin yaƴi sannan ya kurɓa, kana ya mika min.
"Ki godewa Allah da yabaki Jarumar Uwa! Inda nine da zafi zakisha, dan haka zuwa an jima zan dawo ki adana hawayenki"
Yana gamawa ya juya ga Ummi yace.
"Sannu Mama! Zaku iya amso mata yaran ta fara shayar dasu."

"Toh mun gode sosai," tace masa, har zai fita tace.
"Don Allah kaine Dr Katagum!"
Cike da jin kunya ya gyaɗa kanshi.
"Mungode sosai, da Hidima Allah yasaka da alkhairi."
"Amin, Mama!" yace sannan yabar ɗakin, da kallo nabishi sannan na kalle Ummi ina jiran karin bayani, karɓan tea ɗin tayi. Taje ban ɗaki ta haɗa min ruwan zafi sannan ta fito ta riko hannuna muka shiga ciki, Lallai na yarda Ummi Jarumar Uwa ce, ita da kanta tamin wanka tass bayan ta gasa min jikina yadda ya dace, sannan ta fito tace.
"Ki wanke jikinki kuma kisa ruwan zafi a gurin, banda shirme dan matuƙar baki gyara gurin ba kece a ruwa. Babu abinda ya dame ni."
Murmushi nayi a raina nace.
*Ummi kece kuwa me shiga damuwa*
Wanka sosai naƴi sannan na fito, riga da zani ta bani na saka, bakina yaƴi nauyi, dan haka bana magana sabida harshena.
Zama naƴi sai gasu da yaran, tea ɗin na karɓa ina sha tare da matse kwalla, ina gamawa ta mika min magani nasha, sannan ta shafa mun bonjula, akan harshena, ina gamawa tana samin yarinyar farko aƙan cinyata, d'ago kaina nayi na kalleta, murmushi tayi sannan tace.
"Idan da duniya zasu haɗu domin dakatar dake alokacin, tabbas rabonsu zan iya kashe mutumin da ya nemi dakatar dasu, Safinah rabon y'ace nada zafi tafi kowacce halitta zafin, Kuma ki duba da kyau yara biyu, ki godewa Allah da ina raye haka ta faru, da bana raye ko kuma Dudunki ba me kula bane, nayi imani da Allah mutuwa zakiyi, tunda kika ga sunzo toh ke baki isa dakatar dasu ba.Allah ya albarkaci rayuwarku dake dasuma."
Kuka nake sosai, ina kallon yaran, nama rasa me zance dan nayi kuskure a rayuwata, nice Babba kuma nice na fara zubda mutuncin gidanmu, ribar taurin kai har da shegu. Dafe goshina naƴi sakamakon sara min da yake Ummi tayi maza ta riko babyn.
Kallon Ummi nayi ina girgiza kaina nace.
"Ummina! Ni bazan shayardasu ba, kawai a shayar dasu Madar."
Make min bakina taƴi cikin wani irin ɓacin rai, wanda ban taɓa sanin tana dashi ba, ta kuma ɗaga hannu zata mare ni, haka ta kasa marin, saukewa taƴi ranta yana tafasa, ta dire min jaririyar ta ɗauki hijab ɗinta tace.
"Nagode."
Tasa kai zata fita, Khalil yace.
"Ummi! Ke da kika haifemu kikayi fushi da alamarinmu ina kuma wani na daban, Ummi idan kikayi fushi da ita bazata ga daidai ba, don Allah kiyi hakuri Didi bazata kuma ba."

Kallona yaƴi cikin jin haushi amma yayi kokarin haka yace.
"Didi baki kyauta ba ɗauketa ki bata abincinta ba a shayarwa ke aka shayardake,"

"Ibrahim sheg..."
"Ke kan wallahi baki da hankali." Inji Umma da tashigo ganin Ummi a tsaye yasa tsayawa a gun, gashi taji abinda Khalil ya faɗa min, uwa Uba katoɓarar da naƴi. Hmm bakin ciki yasa Ummi barin asibitin, ba ita ɗaƴa ba hatta yan uwana, dan Alakatafur naki bawa yaran nono, har Abdul sai da yaji haushina. Maida yaran akayi ni kuwa na cigaba da kuka na, Umma kaɗai aka bari. Muna zaune sai ga Dr Katagum ya shigo da yaran yana ɗauke da daya, nurse tana ɗauke da ɗaya..
Yana zuwa ya ja kujera ya zauna sannan yace min.
"Maza basu nono."
D'agowa nayi a tsiwa ce, muna haɗa ido naga ya cika min ido, dole na sunkuyar da kaina, na buɗe rigar na rasa ya zanyi da babyn, nurse yayiwa magana, sannan ya juya gun Umma da take min faɗa da harshen shuwa, tana gamawa, ta shiga masa godiya.
Nuna min yadda zan bawa babyn nono tayi, sannan ta ajiye min ɗayar, ta fita.
Babyn tana kama nono na lumshe idanu, sabida zafi.
Haka mukayita dambe da Babyn sannan ya amsheta ya sakata a kafaɗarsa, sannan yanuna min ɗayar.
Na ɗauka fita Umma tayi dan ana kiranta a wayarta bata ji.

Tana fita sai bumm muka ji kamar an wurgo shi ɗakin, ɗ'ago kaina nayi, bansan lokacin da yawu ya sarke min ba, tari na fara. Dr Katagum ya mike yazo ya amshi yarinyar ya kwantar da ita, sannan ya zuba min ruwa a kofi na zafi sannan ya ɗauki na goran faro ya zuba min, tare da mika min, da sauri na amsa.
Takowa Anim yayi yazo ya kalle yaran, cikin mugunta yace.
"Sannu uwar yan biyu, riba har da uwar kuɗi kenan."
Rike rigar Dr nayi ina girgiza kaina, kallon Anim yayi ciki mamaki yadda yake murmushi.
Gashi yana kokari taɓa yaran, cikin kuka nace.
"Karka barshi ya taɓa min su!"
Aikuwa ya rike hannunshi, tare da maidashi baya, dariya Anim yayi..
"Kice anan ma kin kuma samun aboƙin tayi, toh su yaran ubanansu nawane haka?"
Kuka ne ya ci karfina sosai.
"Wai Anim me yasa kake son cin mutuncina ne, laifin me na maka ne da zafi,me na tare maka a rayuwar duniya? Nayi danasanin saninka a rayuwata, kuma Ubangiji sai yayo min sakayya."

"Dalla rufa min baki, meye kika min, bayan kin lalata min nawa rayuwa, kika je kika kwaso wasu shegu a rayuwarmu."

"Yarana ba shegu bane, domin sa Ubansu sai dai kaine dai basu ba."
"Keee! Ni kika zaga?" cikin kwarin gwiwa nace.
"Eh ɗin na zageka."
Dukda ciwon dake harshena bai hanani kare mutuncina ba, kaina yayo zai dake ni, Dr Katagum ya dakatar dashi ta hanyar mai dashi baya.
"Dalla malam matsa min, dakai ba kaine aka yaudara ba, ka tmbayeta abinda ta min, da sadakina taje wank katon iska ya lalata min tanadina,"

Dafe goshina nayi hawaye na zuba wannan na ƙoran wanan. Dr yace.
"Shin wani irin tanadi aka lalata maka?"
"Bada mutuncinta na ace da tayi shine tanadina."

Murmushi Dr yayi sannan yace.
"Kenan dama ba ita kake so ba, Budurcinta ƙake hari, da zaka samu a waje bazaka taɓa damuwa da taje gidanka ba, ko kuma kana aurenta kaji yadda take ana kwana biyu zaka saketa ko?"
*Wacce amsa Anim zai bada???*

Oum Muwaddah......👏👏👏
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

 
*_Labarin daban yake da sauran._*


      
Page.٣٠-30

     Wuri-wuri Anim yayi da idanunshi zuciyarshi tana wani irin buga, kankance idanunshi yayi ranshi na kara ɓaci. A fusace yace.
"Kai waye? Da zaka sani a gaba da tambayoyi! Ita ɗin dadironkace, ko abar kaunarka ce? Gata nan da cikin jikinta na shayar da ita madaran jikina ko karya ce na miki? Da kanta tazo gurina muka tsallaka tsakiyar taku da ita har na wata gud.."

    "Azzalumin macuci Allah sai ya gwada maka iyakarka, wallahi babu abinda ya taɓa haɗani da shi, Wallahi ni ba fajira bace" na faɗa cikin kuka,
     "Toh cikin da kika haifa taya kika same su?"
  Dafe goshina nayi dan tsakanin da Allah Anim yake son lalata min farin cikina, a yanzun da nake kokarin tattara d'an kuzarin da na rasa shine bari ya lalata min su, ban tsammaci jin magana me kyau daga bakin Dr ba sai da ya doki dodon kunnena.
  "Malam! Idan na fahimta kana yin haka ne dan taki amincewa da kai ? Ni a tunani na idan kana son mace kuma ka ganta a gidan karuwai, babu abinda ya dameka ɗaukota zakayi ka aureta, sai gashi kaddara da rabo sunsa kana cutar da zuciyarta da ruhinta, kuma kana kiran haka da *SO* bayan babu wani masoyin gaskiyan da zai so cutar da abokiyar soyayyarsa, zan faɗa maka wani abu guda ba a haka zaka nuna soyayyarka ba, dan kana kusantata da ɓacin rai yana rage kima a idanunta."

       Tsaki yayi zai magana, sai gashi ya fita. A zafaffe Dr ya juya gareni tare da tsare ni da mayun idanunshi masu, matukar karfi da haiba.
   "Taya kika same su? Iya gaskiyar da kika faɗa shi zai bani damar dakatar dashi."

      D'ago kaina nayi na zuba masa ido, a sannu nayi kasa da kaina. Sannan na fara basu labari dan bashi kaɗai bane a ɗakin har da Umma da kuma Abbanmu wanda ya kira Abdul ya kawo shi.
               Da nazo inda kaddaran cikin yaran kasa faɗa musu kome nayi, kuka na sake me taɓa zuciya da ruhin me sauraranshi, sai da nayi ya ishe ni sannan na ɗago kaina na cigaba da cewa.
"Sam baya cikin hankalinshi, dan sun masa sihiri da ya samu taɓen hankali, nasan waye Ashraf dan na zauna dashi kafin faruwa alamarin bai taba kallona cikakke na sec, balle na mint. Mutum ne da ya kame kanshi daga masha'a

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment