Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shafe awa ɗaya a gun kafin dattijon yafito rike da sandar dogarawarsa ta Azurfa kana ganinta sai wani irin shaiki take, zama yayk duk suka zuɓe tare da kai mishi gaisuwa. Jinjina kanshi yayi idanunshi kan Feener wacce kanta yake sunkuye bazato yace.
"Shekarunki nawa? Sunanki? Daga wani yankin duniya kike?"
D'ago kanta tayi taga yayi mata wani irin kwarjini da cika ido, sunkuyar da kanta tayi jikinta na karkarwa, bakinta na rawa har tana tauna harshenta tace.
"Safeenat Hadi! Daga senegal"
Bai kuma ce mata kome ba, ya maida hankalinshi kan agogon falon, sannan ya kalle Naja'atu yace.
"Ku kaita."
Mikewa sukayi tare da ita suka fita a falon.
Shiru yayi zuciyarshi nakin amincewa da baiwar Sarkinsu, amma bai da hujja hanata.
Can gun bayi aka maida ita, tare da nuna mata ɗaki. Zuwa anjima za'a zo akaita, tare da jera mata dokokin zama a cikin gun girkin.
~_~
Bayan awa gudu sai gasu Naja'atu, kiransu Hindu akayi suka tafi wani bangare na gidan, aka sasu sukayi wanka, sannan aka basu wani riga iyakarshi ya rufe kirji,amma cibiyarsu a buɗe, yana sa guntun hannu, amma tawajen cikin kuwa wasu silala aka saka masu wani irin kara, sai wani wando me tsagu har cinyar gefe da gefe, ga wani jigidar karfen, sai wani awarwaro da aka basu suka saka. A kafarsu wanda yake bada wani kara cuuu.
Sai wani hula shima me karafun, wanda kana juya kai zai bada sautin.
Sakasu akayi a gaba, aka kaisu wani falo na daban gun cike yake da manyan mutane. Suna shiga gun aka sauke sauti dake akwai makaɗa, take aka umarce dasu fara rawa. Irinta larabawan zamanin Jahiliyya. Dake dukkaansu larabawane. Kuma sunsan kan rawan, ita rawan dai anayinta da k'ugune sannan anayi ana juya kowani kusurwa najikin......

VoteMj#Follow Mai_Dambu....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: *_HAZAƘA WRITER'S ASSO_*

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_
*®2020*
*BOOK ONE*
 

Page-٣
       Wannan dabi'ar da ake a cikin masarautar iya emirater council ne suƙe wannan ɗabi'ar. Banda sarkin dan sam  bai ciƙa shiga sabgar ba, kodan kasancewarsa shi ɗin matashine ko da yake baza ace haka ba, dan idan akayi dubi da yanayinsa ba mazaune bane a masarautar, kaisu wani ɗaki akayi nan wata baiwa ta nuna musu yadda zasuyi rawan sannan suka fita zuwa wannan falon.
      Inda suka same su da manyan cikin fadar, nan aka sake musu sauti suka shiga rawan yayinda makaɗa suka shiga sake musu sauti, gefe guda manyan fadar suna watsa musu salala, tare da ruwan taccecen inabi...
   Duk wannan abinda ke faruwa Sultan Ashraf bai san da haka ba, shigowar Amir Ukshe ne ya tsayar da kiɗan da rawan. Zama yayi a cikin tattausar shinfiɗinsa, yana karewa kowa kallo kafin yakishingiɗa aka cigaba da shagali.
            ***
    Wani kitchen aka kaini mai girman gaske, kome na cikin kitchen ɗin royal colour ne, wato komi na na cikin kitchen ɗin ruwan golden ne hatta cokala da kofuna duk iri ɗaya ne. Bangaje ni da akayi ne ya dawo dani daga duniyar kauyanci, tsaki matar tayi cikin izgilanci tace.
"Matsalar akawo maka bayi daga africa kenan, gashi tazo ta buɗe baki tana kallo kamar wata doluwa, zaki wucce ko sai nasa guard sun zanemana ke"
     Gaba nayi ina raba idanuna, bansan me zanyi musu ba dan haka na tsaya a gun ina kallon yadda suke haɗa girki kai kace taro ake. Kafin na ankara sai ji nayi an zabga min bulala a  jikina,      a razane na ɗago wani murɗeɗɗen mutum ne sanye da farin riga da bakin wando anyi masa tambarin masarautar a gefen kirjinshi ta dama, dariya duk masu girkin suka saka, nuna min aikin wata dattijuwa yayi, an ajiye min, kasancewa an faɗa musu na iya girkin larabawa su gwadani sannan akaini ɓangaren da zan zauna.
             A sanyayye na karasa gun na tsaya buɗe panpo nayi na wanke hannuna, sannan na kalle abinda zanyi. Man zaitun da y'ay'anshi, zuma, da tafarnuwa sai kayan kamshi dangin curry masala, da kuma kaza katuwa, sai dankalin turawa da kayan miya tattasai ja da kore tumatir manya guda huɗu, sai wani maggi wanda yake da faɗi sai albasa, dafa kafaɗata tsuhuwar tayi sannan tace min.
"B'akuwa wannan shine irin abincin da Sultan Ashraf yafi so, da fata.."
       "Kee! Tsuhuwa koma bakin aikinki ko kuma jikinki ya nusardake inda kike." inji mutumin da ya zane ni, da sauri matar koma bakin aikinta.

         Shiru kitchen ɗin ya ɗauka baka jin kome sai karan ajiye filet ko wani abu ko kuma cokali.  Cikin sauri na fara aikina,  ana wanke kazar  ajiyeta a matsami ruwan ya gama ɗigewa, sai a koma kan irish ɗin shima a yanyankashi ba yankan chips ba. Yankar albasa akwance, za'ayishi sai a ajiye a cikin wani bowl akoma kan kayan miyar shima yanyankasu ke, a zuba akan dankalin, sai a zuba man zaitun da zuma a cikin kayan miyar tare da maggin da y'a'yan zaitun nan a cakuɗasu guri guda, sai a ɗauko kazar a zuba a cikinta, idan dama an raba kazar ta kirjine sai a saka zare da allura a ɗinketa, idan kuma ta kasa aka buɗeta sai a juye takasar, amma larabawa sunfi  buɗeta ta kasa.
          Sai a ɗinketa sannan a sake niman bowl azuba man zaitun, da maggi a haɗa ashafa a jikin kazar sai a saka an pan ɗin oven a saka a cikin.
                    Duk bayan mintuna goma zai ayita buɗewa ana zuka wuka a ciki, yadda za aji dahuwarsu.
     ........ Bayan mintuna talatin da biyar aka ciro, matar da take da alhaki kula damu, itace zata fara dubawa. Tana gama dubawa ta kalleni tura min tayi gabana, cikin tsukewar fuska tace.
"Kici."
     Cikin sanyin jiki na yanki namar na kai bakina naci,  suna ganin naci suma suƙa rufawa namar, tass suka cinye.
       ...... Daga nan suka sani dafa normal tea. Irin nasu na larabawa wasu ganyenma bansan su ba sai yau, ina gama suka sake bani aiki. Kai nasha azaba dan kafata har rawa yake. Dakƴar suƙa sallame ni daga kitchen ɗin.
        ***
    Ina shigowa ɗakinmu nasami Yan matan nan, suna kuka cikin sauri na karasa gunsu na zauna a tsakiyarsu. Daura kansu suƙayi a jikina tare da fashewa da kuka, suna cewa.
"Feener! An wulakantamu anci zarafinmu, bayan munyi musu rawa sai da suka nemi yin lalata damu. Feener har da Sarkin ma."
   Zaro idanu nayi waje, Zakiya tace.
"Feener Mujahida an mata fyaɗe tana bay.."
  Turesu nayi na shiga ban ɗakin na sameta tsugune rungume da jikinta tana wani irin kuka, durkusawa nayi na rungumeta. Cikin kuka tace.
"Feener! Narasa darajata, dama haka bayi suke fuskanta? Na rasa iyaƴena a yakin syria ban taɓa kuka irin nayau ba gashi akan idona sarkin wannan masarautar yake tamin haddi bayan sun wulakantamu. Feener zan gudu."
          Girgiza mata kai nayi cikin kuka nace.
"Kiyi hakuri"
    Narasa me zan gaya mata, dakyar nasata tayi wanka, sannan tafito a hankali abincinmu aka kawo mana, a wulakance aka ajiye mana, nice na cigaba da lallashinsu har suka taɓa abincin zan fara ci kenan aka buga kofar mikewa nayi na buɗe.
   "Kizo mu kaiki shashin Sultan Ashraf yau zaki fara aikinki."
                     Fitowa nayi na bi bayan mutumin.  Fita mukayi daga shashin bayi sannan muka nufi cikin wani shashi wanda yafi kowani shashi kyau da haɗuwa,
               
  Tazarar tafiyar da yake tsakanin get ɗin gidan da cikin tafiyace ta minti arba'in da biyar, amma cikin sauri muka isa gidan, bansan yadda zan kwatanta muku yanayin gidan, domin baka jin motsin kome a gidan sai takuna, kasancewa takalmina flat ne toh kuma yana bada sautin, tun da muka haura barandan. Masu tsaron gidan suke bina da kallo sabida sautin takalmina, falon farko da muka shiga,  aka dakatar damu, wani bulalar me kama da itace aka zabga min a kafana, sai da nasake kara.
    "Shiiiii!" shine abinda me tsaron kofar falon, ganin haka mutumin da ya kawo ni yasake murmushi can kasa makoshinsa ƴace.
     "Ghaniyu muna godiya da tarɓan da tasamu,"
     D'aga mishi hannu mutumin yayi, muka wucce, kwalla ne ya shiga saukowa a idanuna, tare da tarin dana sanin mara amfanin da nakeyi tun bamu isa cikin ba. Falon farko babba ne na fitar hankali, ga kaƴan alfarma a cikinsu. Sannan muka ratsa falon dan mun samu da mutane suna zaune babu wani hayaniya ko magana asalima zaman hutawa suke.
                Haka muka wucce su babu wanda ya dago ya kallemu, balle kasa ran zasu mana magana, wani dogon korido mai tsayi shima tafiyar minti goma zakayi ya kaika kofar falo na biyu.
                  Muna zuwa aka buɗe mana kofa, muka shiga ciki mun sami mutane biyu a zaune kowannensu da abinda yake yi, sannan muka wucce, inda mukayi tafiyar  minti ashirin da ɗaya, sannan muka nufi wani tafkeken falon me cike da abubuwan burgewa, irinta gidan sarauta. Babu kowa a falon sai tv da yake aiki. Tsayawa yayi a gun sannan ya kalle ni tare da mika min, takarda yace.
"Idan Allah ya nufa zamu sake saduwa toh sunana Sheik, zaki iya tsayuwan jira har lokacin da ya fito sai kisan yadda zaki bashi takardan domin yasan da cewa kece bakuwar da zaki fara girka mishi abinci sannan kiyi takan tsantsar da aikinki domin nan ba'a san kuskure ba kina yin abu kaɗan zaki ji a jikinki."

  Yana gama faɗar haka ya juya ya tafi, abinshi.
               Jingina nayi da bango ina kallon Inda Allah ya kawo ni. Bayan wasu mintoti, na gaji da tsayuwa na zame na zauna, na cigaba da tsammanin fitowar sultan, shiru kake ji.
    Awa ɗaya ya wucce wasu awowin suka wucce bai fito ba. Can da naga har lokacin sallah yayi bai fito ba, sai na juya na fita niman inda zanyi alola da sallah. Karshe dai sai da na dawo shashin bayi nayi sallah sannan na koma.
      Ashe ina fita shima yana fitowa, ganin takarda asaman kujeran falon yasashi sanin an shigo falon yana ciki bai bi takai ba yayi ficcewarsa, zuwa masalaci.  Koda ya dawo a falon farko ya tsaya sabida mutanen da suka zo masa dubayya, da kuma mishi Jajjen ya jiki. Suma dai matasane sa'aninshi kuma yan Kabilarsa na Banu Hashim, daga cikinsu kuwa har da Jikan Amir Ukshe.
           A hankali nake takowa sabida ba'a son karar takalmina ko sautin da zai dame mazauna gidan.
         Da sallama na tura kofar na shiga duk sunji sallamar amma babu wanda yayi yunkurin amsa min, asalima kamar basa gun kare musu kallo nayi anan na fahimci dukkansu yan bana bakwai ne.
          Abinda yasani cewa haka kuwa ba kome bane sai dan luran da nayi dan akala bazasu wucce 28-29 ba, domin babu wanda ya haura talatin. Taɓe bakina nayi na wucce,
         Har inda aka kaini, tsayuwa na cigaba dayi,  wasa wasa banga idanun sarki ba sai bayan sallar la'asar, na gaji da zama na mike zan koma can shashin bayi, ina rike handle kofar zan fita shima ya rike zai shigo. Bazata muka buɗe kofar tare, har sai da kaina yayi karo da kirjinshi.
     Da sauri nayi baya ina zare idanu, bai tsaya bin takaina ba yayi wuccewarshi,  bin bayanshi nayi da ido tare da dafe goshina nace.
"Wayo ni Safinatu! Toh waye sarkin ne?  Toh ko wannan ne? Amma ai lokacin zuwanmu baya falon mutane huɗu muka wuce a falon farko, na biyu kuma mutane biyu ne, ai ko shine Sultan Ashraf ɗin?"
         Ni kaɗai nayita lissafin can nace.
"Toh kenan sarkinsu yarone, taɓ dole yayi abinda ya gadama,"
     Tsaki nayi cike da takaici.
"Mugu azzalumi sai da ya ɓatawa Mujahida rayuwa dan sun ɗauki mulki sun bashi, Allah ya is...."
            Ganin fitarshi nayi da sauri nabi bayanshi ina cewa.
"Ji mana! Don Allah zoka min iso da Sultan Ashraf."
       Nayi haka ne dan na cire tantamar dake raina, ko kallo ban ishe isheshi ba, sai ma masu tsaron lafiyarshi da suka tare ni suka kaini wani dakin duhu. Me kula da bakin kofar ɗakin ya shiga yayita zane ni. Har sai da nayi laushi,  wanda yaja har na suma, sannan suka watsa min ruwan kankara, a firgice na farka  sabida azaba ko kuka ban samu damar yi ba,, cikin kakkausar  mutumin yace.
       "Daga yau ko tsuntsu kika ga zaiyi kuka wanda zaisaka Sultan cikin damuwa ke zaki kora mishi,, sannan ki tashi kije kiyi aikin da aka kawo ki yi, Sannan sultan baya son hayaniya koda kuwa ta fashewar abune toh zaki ji a jikinki"
          Jawo yayi ya watsa a waje tankar kayan wanki. Dakyar na mike zuciyata na min zafi, lura da nayi dare yayi sosai yasani  niman hanyar can shashinmu.
             Koda naje buɗe kofar falon na biyu najishi a rufe dole na dawo falon Sultan, abin bakin ciki koda na shima nasa a rufe karshe sulalewa nayi na zauna, na fashe da kuka.
         "Wani tsautsayine ya raboni da gatana nazo nan ana wasan kura dani." abinda nace knn ina kuka.
            ***
  "Yallaɓai Alexandra mun mun sami labarin an sami wata Yar african da."
    "Benjem kaje kasan meye ya kawo Yar african masarautar jordan."
   Daga haka yayi shigewarsa ciki dan yayi imani da abinda bokanshi ya gaya mishi.
      ***
     Fitowa yayi zai tafi masalaci ya ganni a zaune na cusa kaina cikin cinyoyina, kauda kanshi yayi ya bar gun. Saukar bulala naji yasani mikewa zubur ina sosawa ciki mutumin ya nuna min na shiga, yana bina har kitchen ya nuna min, sannan ya nuna min bango inda aka kafa wata yar allo da aka saka jerin sunayen abincin da za'a girka......

#HZƘ
#MJ
#MD.....Follow me: Mai_Dambu

Oum Muwadda...
    
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

Page.٥
     Wato ɗakin da aka kaini yafi kowanne axaba, dan yadda kasan gidan bread haka cikin ɗakin yake , ga hayakin tire gas, nasha mugun wuya kafin suka fiddani.
         A kitchen suka watsar dani zan iya cewa ban taɓa cin azaba irinta yau ba nasan mutane zasu so jin taya akayi na bar iyayena nazo nan ake wulaƙantani kaɗan daga cikin tarihina.
           Safinat Badr Kyari shine ciƙakken sunana. Mahaifina ya fito daga kabilar Kanuri ne daga kasar Nigeria.
     Mahaifiyata kuwa Shuwa arba ce dan ko hausa bana ji sosai sai turanci da shuwa sai larabci.
         Nice Babba a gidanmu ina da shekaru 32 sai, kanina Abdullahi wanda yake tsaƙanin 28/29 Yana da mata har da yara biyu sai Nanah Asma'u wacce take da shekaru 25 tana da aure da yaro ɗaya na batarta da tsohon ciki. Sai. Sai Fatima tana da shekaru 21. Kafin ɗan autanmu Khalil yana da shekaru 17 bana ya gama scndry.
     Mahaifinmu nada mata biyu har da Umminmu uku kenan Hajiya Amnah babarbariya ce daga Bama, tana da Yara huɗu.
     Maryam suna kiranta da k'iose Tana da shekaru 25 sa'a Nana Asma'u ce. Sai Kaltume tana da shekaru sha tara, sai Sa'ar Khalil dan rana ɗaya suka haihu da Ummi ana kiran yarinyar da Khalilah, Hajiya Amnah muna kiranta da Umma. Sai Hajiya Nuratu fitinanniyar gidanmu  kenan,
            Matar tasaka ni a gaba sosai musaman da taga Nannah ta janye ni ta kuma nuna musu tafi sona sama da kowani yaro a gidan, Hajiya Nuratu wacce muke kiranta da Ammin tana da yara maza babban ɗanta sa'an Fatima ne yana da kusan ashirin yana jami'a shi dasu fatima, sunanshi Abba lawan, sai Salamn shima sa'ansu Khalil ne, sai Ruwaidah tana da shekara goma sha uku, da ɗan karaminmu Anas.
   
   Mu goma sha biyu ne cif a gidanmu,  Abbanmu haifaffen garin Amman ne nakasar jordan, sabida Mahaifin Ibrahim  yayi aiki a karkashin  , Sultan Yasir tun kafin ya zama sarkin jordan kasancewarshi na likitar har zuwa lokacin aka kifar da mulkin sultan Yasir, ya tattaro ya dawo maiduguri. Daga baya masarautar ta nemi ya koma bakin aikinshi yaki. A lokacin Abbanmu yana aiki a babban asibitin maiduguri ya auri Umminmu. Da Kakanmu yaga ya dan manyanta sai ya tura Abbana Masarautar jordan.
                 Ya tawo da ummi ya cigaba da kula da sarki Abdullah har aka haifeni, a lokacin Sarki Abdullah ya auri Nana Asma'u daga Masarautar Oman.  Tazo tasamu ina da shekara biyu, zuwanta yasa abubuwa suka fara faruwa, ganin haka muka dawo gida ni da Ummi. Sai dai duk bayan wata shida Abba yana zuwa mana. Ina da kusan shekaru  bakwai Abbanmu ya dawo shi da Nannah inda tazo tayita jinyar zuciyarta sabida rabata da sukayi da d'anta. Wanda suke sa'anin da Abdullah dan shekarun Abdullah uku.
                  Taso jan Abdul yana ɗibe mata kewar D'anta wanda bata kiran sunanshi. Sai Abdul yaki. Karshe nice taja, ni kuwa a lokacin da mugun son jiki tunda ta fara jana a jiki na sake zama sakaltacciya. Abba ya ya hajiya Amnah, wacce tana zuwa taga Nannah aikuwa hankalinta ya tashi, dukda Abba yana aiki amma albashin baya kai mishi yadda ya dace, ga fitinar Hajiya Amnah akan sai Abba ya kori Nannah yaki shine tayi fushi har da daka yajinta. Lokacin kuwa Allah ya saukarwa Abba wani iftila'i domin kuwa an koreshi a gun aiki ganin abinda zamu ci zai fi karfinshi Nannah ta kirashi mika mishi jakar da aka bata a masarautar jordan tayi, tace.
"Badar! Bazan iya biyan abinda kai min ba, dan ka ɗauko ni daga kasar jordan har nan kasarku, ka kuma ɗauki nauyin cina da sha,  kana ɗawainiya dani, dukda kaki faɗa min an koreka a gun aiki ga ɗawainiyar Iyali gana yaranka ka ɗauki wannan dukiyar dan ni bansan me zanyi dashi ba, sun bani a matsayin sayan ɗ'ana sukayi, ina tsoron abinda ya faru a kan sarakunan baya ya komo kansh."
    Muryanta ne ya shiga rawa alamun kuka zatayi fitowa nayi daga ɗakin naje kusada ita na ɗaura, kaina akan kafaɗarta cikin larabcin da take koya min nace..
"Nannah kiyi hakuri, idan na girma zan kawo miki  d'anki nan kinji, kiyi addu'a na zama babba kinga sai kome yazo min da sauku."
   Tunda tabawa Abbanmu kuɗin Allah yasanya mishi albarka, sai ma wani irin bunkasa dukiyar yake, dan kasuwanci yake daga dubai, lokaci yaja sosai dan har na gama primary schl zan shiga scndry a lokacin Nannah ta fara bani labarin, masarautar jordan. Dan bani mantawa na taɓa ce mata.
   "Nannah taya zan shiga masarautar har na dauko miki shi?"
   Dariya tayi sannan tace.
   "Ke ba kamar sauran mutane bane kuma idan aka san zuwa kikayi zaki tafi dashi kashe ki zasuyi, ina son ganinki zama tankar sarauniya ki bar tunanin wancan duniyar."
     Tura baki nayi cikin kunkuni nace.
  "Nannah! Ni ki gaya min taya zan shig."
         "Safinat! Masarautar babu tausayi ko imani, dai dai da kwalba idan kika fasa, hukuncine, sai kin wucce get huɗu da masu tsaronsu kimanin mutane ɗari uku, sannan ki isa cikin gidan bayan kin wucce dogon baranda kafin ki isa falon farko, wanda yake ɗauke da karti majiya karfu mutane goma suna tsaron falon farko, ki shige tacikin falon kije falo na biyu inda zaki samu. Wasu masu tsaro har mutane ashirin. Sannan ki yi tafiyar minti arba'in da zai kaiki cikin inda Sultan Ashraf yake. Taya zaki shiga? Wani hatsari zaki fuskanta na matsayinki na Y'a mace? Shin zai yarda ya biyo ki? Idan mugayen da suke tare da shi zasu barki ki fito musu da shugabansu? Idan suka san kudirinki na sace musu shugabansu me kike tunanin zasuyi don Allah ki rufa min asiri karki saka haka a ranki kinji yarinyar kirki."
         "Amma Nannah ina ganin fit .."
     Rufe min bakina tayi cikin damuwa tace.
"Ina gudun faɗa miki kome mutanen suna da nuna kabilanci musaman ke da kike da duhun fata. Suna kyamar bakaken fata."
             Shiru nayi dan a lokacin banfi shekara goma sha biyu ba. Aukin tambayar tsiya.
             Bunkasar da Abba yayi ne ya tattaramu muka koma abuja da kasuwancinsa dan yafi karfi tacan da lagos.
                    Bayan na gama scndry naki karatu a jami'ar kasan nan, rimi rimi akayi min kome a medicine inda aka kaini Ghana, ina zuwa can na koma Mass com, inda na shiga karatun babu wanda yasani a gida sai da nayi shekara ɗaya nazo hutu.  Suka sani ranar nasha faɗa a gun Abba, ganin faɗan yaki karewa Nannah tafito tasa baki take Abba ya hakura, amma ya ji badaɗi.
                  Wannan dalilin yasa Hajiya Nuratu take kara jin tsanata. Musaman da yanzun kome Abba zai yi sai yaji tabakina.
              Har na koma. A sannu gidanmu ya fara cika, kafin na gama jami'a gidan an cika ba laifu. Shekaru biyar na dawo daga Ghana, naje bautar kasa a Imo. Ina gamawa nasamu aiki da gidan radio na kasa dake Kaduna,
       Amma Nannah taki dole aka dawo dani Abuja, dukda shakuwar da mukayi da Nannah baisa idan nayi laifi ta ɗaga min kafa ba, faɗa take min sosai.
     Lokaci ya tafi dan bayan na fara aiki na koma makaranta nayi degree na biyu, abin mamak shine na koma kamar me cutar junnu dan bana kaunar maganar aure, kuma lafiyata lau, ganin haka ya ɗaga hankalin Iyayena. Murmushi nannah take kawai idan taga sun sani a gaba suna min faɗa, bata hanasu dan nima da nawa shegantakan, cikin ruwan sanyi manema suke zuwa min karshe basa kwana biyu na koresu, fata fata kuwa. Ni a tunanina idan nace zanyi aure waye zai cikawa Nannah burinta shiyasa naki  auren kowa, tunda nasa a raina zan dawo mata da ɗanta na kuma ji na gani.
        Na taso da wannan burin a raina ko iyayena basu san da shi ba hatta itama Nannah bata sani ba dan tabar min maganar, ni kuwa tausayinta yasani kudirawa a raina sai na dawo mata da ɗanta.
     Bayan shekara biyu da rabi na gama degree na, na biyu. Wanda yayi dai dai da haɗuwana da Anim. Sabon shugaba gidan radionmu, da wasa muka fara sama sama, sai gashi mun kulla soyayya, wanda yaje har gaban iyayenmu.  Aka tsayar da magana maganar aure a tsakaninmu, tunda naga haka hankalina ya tashi. Karshe na nemi Aliee dan kasan jordan ne na zaunen syria ne, mun haɗu dashi a ghana ne yaje wani course. Nan nima n kirkiro tafiya course ɗin shekara guda. Dakyar aƙa d'aga bikinmu, dan ma Anim yana da mata har da yara biyar.
      Kuma dan bokone sosai irin mutanen nan masu akidar boko, dan haka ban sha wuyar shawo kanshi ba ya amince aka. Kwana uku tsakani na wucce jordan. Sau uku ina niman aiki a cikin masarautar suna hanani, karshe sai Aliee ne ya faɗa min basu bani aiki ba dole sai nazo a matsayin baiwa, banso haka ba. Amma babu yadda na iya idan na tuna yadda a gidanmu, dukda an aurar da ƙanena haka bai taɓa damuna ba Ammi tayi min gori har dasu habaici baisa na damu ba, a yanzun nayi na damar tsallake auren Anim da nayi gashi ba biyan bukata, tunda nazo a baiwa dole naga tasku. Da gatana nazo ana wulakantani dan ko Aliee ban faɗa mishi abinda ya kawo ni ba.
      ***
Ajiyar zuciyar na sauke, tare da goge kwallana. Dakyar na mike na shiga jan jikina zuwa ban ɗakin na watsa ruwan zafi me mugun zafi, sannan

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment