Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Muh'd Ashraf ya diro garin Oman tare da wasu daga cikin manyan masarautar, wani irin hidima ake sai ka rantse biki ake, duk sunsha ƙwalliya ban dani da iyata riga da zani ta atamfar Vlisco ce a jikina, idan baka lura ba zaka rantse doguwar riga ce. Me zip a gaba, kayan sun ɗauki jikina ya zauna dis. Ina zaune a falorn Nannah ya shigo, hankalina yana kan hira da Dr wanda yace min jibi yana hanya. Dan haka na maida hankalina muka buge da hira.
Kukan Aanih yasani d'ago kaina, ganinsu nayi tare yana rungume da ita, dake Aamih tana barci kusadani. Suna shiga sai ga Nannah tafito ranta a matuƙar ɓace tace.
"Safinah! Taya zaki bar yarinya ta tafi gurin kayan kallo badan Babanta ya shigo aƙan lokaci ba ai Allah kadai yasan abinda zai faru."

Shiru nayi kaina a sunkuye ina mamakinsa daga zuwa sai haɗa guri.
"Kiyi hakuri!"
Iya abinda na iya cewa kenan.
"Ki kiyayye gaba!"
Tana gama faɗar haka ta juya tabarni buɗe da bakina, ina jinjina irin kaunar da sukewa yaran, bayan kamar minti talatin sai gasu sun fito tare.
"Safinah! Hmm ko zaki samarwa Habibi abinda zai cine!"
Kan uban can lallai ma nice zan girka mishi abinda zai ci, kamar zan fasa ihu na mike sai wani cin magani yake, ajiyewa Nannah yarinyar yayi ya shige ɗakinshi dake kusada nata, yana shiga ya taradda falo madaidaici, sai ɗakuna biyu sannan ya shige ɗaya, zubewa yayi a gadon ya huta sannan ya mike tare da cire rigar jikinshi, singlet ɗinsa ya cire tare da zame dogon wandon jeans ɗinsa. Kasa sannan ya zauna a hankali yazare kafar, safe goshinsa yayi ya mike tare da buɗe sif ɗin kayanshi ya ciro farar jallabiya ya saka, sannan ya fito inda Nannah take zama yayi kamat bazai ce kome ba, ya ɗauki yarshi ya ɗaura a kirjinshi yana shafa bayanta.
"Hm ruwan wanka Ammih!"
Kura mishi ido tayi ciƙe da soyayyar gudan jininta, har ta buɗi baki zata kirani sai ga Natasha ta shigo.
"Yawwa Nata! Kije ɗaki..."

"Ba ita mamar yaran nan" daga haka ya lumshe idanunshi, cikin mamaki tace.
"Amma Habibi kai kace ta girka maka abinci ko? Tana girkin zata."

"Ammihna! Ita ɗin baiwata ce!" ya faɗa kasa kasa da murya dan kar Natasha taji ina har taji abinda yace.
"Binti!!"
Nannah ta kirani, da sauri na fito ina goge hannuna.
"Ki rage karfin gas ɗin ki shiga ɗakin Habibi ki haɗa mishi ruwan wanka."
Kallonshi nayi kamar zanyi magana sai na fasa a raina kuwa cewa naƙe.
*Na shiga uku! Mulkin ma a ko ina sai an nunawa duniya kenan? Ince da shi yake haɗa abinshi wato ganin gabar banza ga yar bello badin tazo za a fara juyata kamar waina*
"Toh Nannah!"
Nace sannan na wucce kitchen na rage karfin wutar na wucce ɗakin.
Ina shigewa da yan mintuna ya mike da yar ya nufo ɗ'akin, yana shigowa ya kwantar da ita, lokacin ina cikin ban ɗakin, ina zuba masa sinadarin kamshi da gyara fatarshi, hankalina yayi nisa gurin karanta jawabin jikin wani kwalbar turaren wanka, ashe har ya shigo yana tsaye kugunshi ɗaure da towel. Ina gamawa na ajiye kwalbar tare da juyawa, ban san lokacin da naƴi baya zan faɗa cikin ruwan ba. Gyara tsayuwarshi yayi sannan ya shiga takowa, cikin tsiwa nace.
"Wallahi karka kuskura ka taɓa ni dan zan wanka maka mari! Ni karka maidani yar iska. Na gaya maka ka tsaya a gurin fa zan maka rashin Mutunci."
Kunce towel ɗinsa yayi aikuwa na rufe idanuna da karfi tare da ɗauke numfashina. Bawai naga kome bane tsoron mugun gani ne yasani rufe idanu, shikam abinda yake gabanshi ya dame shi, ina jin ya shiga ruwan nayi maza na isa bakin kofa ina murɗa kofar, najita gam.
Karan key ɗin naji a bayana, juyawa nayi naga ya ajiyeta a gefe, ya nutsa a cikin ruwan ko fuskarshi baka iya hangowa.
A hankali na saɗaɗa naje gurin na kai hannuna da niyyar ɗaukowa, sai ji nayi an cafke hannuna.
"Ni kasake min hannuna! Wallahi zan maka rashin mutunci fa, ka sak."
Famjan!!!! Ruwan ya fantsamu a ko ina, fidda kanshi yayi tare kallon inda sabon soso da sabulu yake, ko kiftawa idanunshi bayayi gurin kawai yake son na kalla.

Sharce ruwan fuskana nayi, na dubd shi cikin mugun ɓacin rai nace.
"Allah Ya isa min fasiki kawai! Yaro karami da kai amma ka iya shaiɗanci."
Kokarin mikewa nake, amma mara mutunci ya rike ni, idanunshi a rufe, da karfi na ƙwace kaina tare da zabga mishi harara,
Dawo dani yayi da mugun karfi yace.
"Wanka zaki min! Idan kika ki kuwa! Hmm abinda zai biyo baya bazai miki daɗi ba."

Tsorone ya kamani tunda ya faɗi haka tabbas kome zai iya faru, kwalla ce ta fara zuba daga idanuna, na mike tare da ɗauko shapoo da sauran abubuwan wanke kai, na zuba a kanshi. Na fara wanke mishi kanshi idanunshi a lumshe, duk tsoro ya cikani dan gani nake kamar wani abu zai min, sai da na gama wanke mishi kanshi. Sannan na cuɗe masa baya da kirjinshi, a nan ne ya buɗe ido yana kallon yadda nake cuɗashi, dukda ina jin yadda yake kallona, ni kuwa naki na kalle shi. Ina gamawa nayi maza nafita dan naga idan nabi na rashin kunyarsa tabbas zan ce na wanƙe, Y'ay'an gwaibarsa da ayabar.(😉)
Duk najike jagab, babban towel na ɗauka na juya mishi baya, ina rike da towel ɗin.

"Bani towel"
Kamar na fasa ihu haka nake ji. K'in juyawa nayi, har sai da ya fito dan yasan bazan taɓa juyawa ba, takowa yayi ya iso bayana ina jin numfashinsa a bayana, tsorone ya cika min ciki, saka hannunshi yayi, ya janyo ni jikinshi. Rawa jikina ya ɗauka sabida ina jin yadda kayan aiki ke taɓani.(😹😎)

Bai karɓa towel ɗin ba ya dai sanya hannunshi ɗaya a tsakanin cikina, cire hannunshi nayi na mika mishi towel ɗin, sannan na wucce jikin kofa da sauri. Shi ko a jikinshi ya ɗauro towel ɗin, wani drower dake ban ɗakin ya buɗe ya ɗauko towel, sai da ya tawo tare da matse ni kaɗan a jikin kofar ya lalluɓe hannuna ya mika min towel ɗin, sannan yasaka hannunshi ta cikina ya sanya ket ɗin kofar ya buɗe, sannan ya janye ni da jikin kofar ya fita yabarni a gurin, yana fitowa yasami Natasha a tsaye, tsabar miskilanci, kamar baiganta ba, ya zauna a bakin gadon hannunshi rike da karamin towel, yana goge kanshi na fito ɗaure da towel ɗin iya cinya, duk sai naji a muzanta, kamar zan juya ban ɗakin, dukda babu abinda ya shiga tsakaninmu amma babu wanda zai gannin a cikin wannan yanaƴi bai zargemu ba, fuuu tajuya zata fita.
"Tasha!!!"
Cak ta tsaya bata fita ba, kuma bata juya ba.
"Tunda ban isa ba jeki"
Kamar shashasha, ta juyo idanunta na zubd ruwa. Nuna mata cinyarsa yayi , cikin shagwaɓa da sakalci ta isa gabanshi, ta zauna a sanyayye.

Mikamata towel ɗin yayi cikin rawan jiki ta fara goge mishi, sai ga ja'iri ya ruko k'ugunta tare da kifa kanshi akan cikinta, komawa ban ɗaki nayi na saka kayana na ajiye mishi towel ɗinsa na fito nasamu Nannah bata falon ɗakina na nufa na shiga nayi sabon wanka. Sannan na cire kayan na wanke na raɓa akan ɗan karfen da nake shanya pants ɗina da bra. Karo na farko a rayuwata danaji ina sha'awar manyan Nono, dan nima na burge Dr, musaman irin shigar da Natasha tayi ya mugun burgeni dan har kana hango tsakanin manyan nonuwarta, nima dai nawan ba laifi, amma dole na nime wasu maganin koda namu na hausa, zan nima na fara sha. Ko zasu kara auki.

Fitowa nayi na ciro doguwar riga. Lemon green me manyan stones yana haɗe da hularsa, nasaka ban saka bra ba sai bon short da nasaka taciki, sannan na ɗan gyara fuskana na murza kwali. Ina gamawa na fito falo na sameshi da Natasha suna cin abinci....

*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 17 pages Insha Allah*

Oum Muwaddah......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....

Page.٤٥-45
   "Sam karki damu ki gaya musu na shanye miki nono, dan ni banajin kome idan na kawo yarana ne dai aka k'i a basu nono toh ba makawa, zansha kuma bazai min kome ba. Idan kina son kanki da lafiyarki toh yarana a basu kulawar da ta dace, idan kuwa aka k'i Abie ɗinsu zai ɗauka musu fansa, idan haka ya gaggara Allah ya hore min lafiya ta yadda zan cinyeki ba kakkautawa."
              Juya mishi baya nayi dan na fahimci wannan da hajja kaka tafiyarsu d'aya ce, sam baya jin kunya ko girman maganar da zata fito bakinshi famcamata yake son ranshi. Ina jin fitarshi sai da na sauke ajiyar zuciya da naji ya fita, tare da nutsuwa.

            Ina jin wayata na tsiwa amma naki ɗ'agawa, haka har barci yayi gaba dani. Ina cikin barci naji ana tab'ani ina dubawa naga yaran ya kawosu. Tare da zuba minsu ya koma kan restchair yayi crossing leg yana kallona, Allah sarki yaran sai ture ni suke za susha, abinka da Uwa sai naji zuciyata tayi rauni. Tashi nayi na jingina da pillow, sannan na cirewa Aanih ta kuwa rike har tana zunguɗina, sannan na cirewa Aamih, tazo ta kama, duk sai suka bani tausayi. Haka suka sha ɗan abinda wancan lusarin Uban nasu yabari, sannan suka sake. Bawai dan ya ishesu ba, ina tunanin kawai sai ga Maid ɗinsu ta kawo feeder ɗinsu, sannan tafita, tashi yayi ya amshi d'aya ya mika min sannan ya ɗauki Aamih ni kuma na ɗauki Aanih.
    Daga bakin kofa Nannah take kallonmu, haka yayi mata daɗi a ranta kuwa har addu'a take Allah ya tabbatar mata da wannan mafarkin nata.

        Juyawa tayi tafita, ranta na mata daɗi. Wannan d'abi'a daga larabawa sai turawa, su kaɗai ne mutanen da suke hidima da yara, sabida girmama mace da kuma bata lokacinta na kanta, itama ta huta.
      Muna gama basu yazo ya kwashesu ya kaiwa Maids ɗinsu, ni kuma na cigaba da kwanciya, shigowar Nannah yasani tashi. Zama tayi abakin gadon tana kallon yadda nayi zuru zuru, tace..
"Meke faruwa? Dan Badaru ya kirani wai akwai wanda zai zo ɗaukarki, ku koma gida, gashi kowani shakuwa Habibi baiyi da yaranshi ba zaki ɗaukesu ku tafi."

   Shiru tayi tana kallon yadda nake goge kwallar dake sauka a idanuna, kaina sunkuye sannan ta cigaba da cewa.
"Tabbas zai biki! Dan bazai iya hakuri da yaran ba, ni kuma meye ribata. A yanzun nake bukatarshi, duƙda kece kika kawo min shi gashi zaki sake ɗauke minshi, shi yasa naso ki hakura da wancan ki amshi Uban yaranki dan bana son yayi min nisa, amma kika k'i safinah me kike so na baki dan ki xauna min da Farin cikina, Muh'd da yaransa sune farin cikina gashi zan rasa sabida ke. Zan baki nan da wani lokaci kiyi tunani akan haka dan bazan iya hakura a sake rabani dashi ba, shine kaɗai abinda ya rage min shida zuri'arsa."

     Tana gama faɗar haka ta mike zata fita cikin kuka nace.
"Nah!"
        Cak ta tsaya bata juyo ba, na mike zuwa gabanta kaina a sunkuye nace.
"Bazan taɓa yafewa kaina ba, idan na rabaki da farin cikinki, Nannah zan tafi nabarsu indai haka zai sanya ko farin ciki Nah zan barsu, don Allah ku barni nima nayi farin ciki ko sau ɗ'aya ne."

      Ganin Yadda nake kuka yasa jikinta mugun sanyi banga laifin Nannah ba ko sau ɗaya shekaru ashirin da shida tayi bata tare da d'anta yau ta same shi kwatsan zan tafi dashi dan wallahi tsaf Ashraf zai bini akan Yaranshi, kuma zai iya kome domin yaranshi.
Fita tayi ta barni a d'akin yana zaune a falon tawucce shi yana musu wasa, yaran sai walwala suke.
.......
Bayan fitarta na janyo jakata wanda muka zo dashi ko taɓawa banyi ba, na fitar sannan na ɗauƙo na yaran na ajiye, sai hand bag ɗina da na ɗauko na buɗe na shiga tattara kayana ina zubawa a ciki, wata abin charging na. Sai wasu kayan amfanina man shafawata da sauransu, na zuba. Dan nasan idan ya shigo da yamma maybe zuwa dare mu bar kasa.

Na gama shirya kayana tsaf, shigowar maids da shi kansa yasani d'ago kaina, kauda kaina nayi daga garesu na cigaba da shirya kome, kallonsu maids ɗin yayi suka ajiye abinda suka shigo dashi suka fita manyan jakukkuna ne har uku, ya zauna yana kallona yadda idanuna suke tsayayyar da hawaye.

"Wato na lura dake a duniya kina kaunar kuka"
Yadda yayi maganar yana nishi sai ka zata block inch tara ya ɗauka, ban bi takanshi ba na faɗa ban ɗaki na ciro Innerwear ɗina, duk na cusa a jakata.

Mikewa yayi bai kuma bin takaina ba, har yamma ina kwance da jikina sanye da arabia gown, naji karan wayata, ina dubawa naga Baby, mikewa nayi dakyar na zauna sannan na saka a kunnena nace.
"Baby! Ka iso ne?"
"Eh gani tare da Yarana har da Babansu."
Gabana ne ya faɗi badai wannan yaron ya same shi da wani shirme ba, a hankali na mike tare da gyara fuskana na fito, a sannu ina raba idanuna. Murmushi nayi lokacin da na hangoshi,, a sannu na isa gunshi mikewa yayi tare da riko hannuna ya zaunar dani. Sannan ya zauna akan kafet yana kallon fuskana yadda ya kumbura yace.
"Beauty! Kina lafiya? Kinga yadda idanuki suka kankance, meke damunki."
Ya kai hannushi zai taɓani hawaye suka zuɓo daga idanuna suka sauƙa akan hannunshi, riko hannuna yayi cikin raunin murya yace.
"Ina tare dake, duk wuya duk daɗi bazan taɓa barinki, ki zubda kwalla ba, share hawayenki bazan bar garin nan ba sai sake."

Duk sai yaji bai aminta da zamana a cikin gidan ba, cikin damuwa yace.
"Naso sai gobe zamu bar garin nan amma dole yau na nima mana ticket zuwa gida."

Kamar wacce aka hana cewa kome, haka na zauna ba hmm ba hmm, fitowar Nannah daga cikin ɗakinta ganin halin da nake ciki yayi mugun kashe mata jiki, haka kawai take ji a ranta taso kanta dayawa bata da adalci ta nuna son kai muraran a cikin alamarin toh ya zatayi bata da wani zaɓe da ya wucce haka, ita kaɗai tasan yadda take ji akan D'anta da jikokinta.
Zama tayi kusadani sannan tace.
"Dr ina ga ko zaku fitane, dan tunda bata taɓa fita ganin gari ba."

A dame ya kalleta yace.
"Akwai abinda aka mata. Wanda ya hanata magana, amma ina gani idan muka fita zata ɗan sake a ranta."

Ciro hank yayi ya mika min dakyar na amsa, ya mike nima na mike, tare muka fita hannuna cikin nashi, har gurin motar hotel ɗin da ya ɗauko. Muna shiga motar na kifa kaina a kancinyata na fashe da wani irin kuka me cin rai. Gayawa drvn yayi ya kaimu airport.

Can muka tafi ya shiga nima mana ticke, mun samu Oman toh Abu Dhabi. Jirginmu zai tashi uku na dare, dan haka ya dawo dani bayan ya rarrashe ni.
A sannu nake takawa bayan tafiyar Dr zamu haɗu airport, ina shiga ciki na samesu a zaune kallona Nannah tayi, cikin ɓacin rai tace.
"Wannan wani irin rashin hankaline da zaki tafi ki manta da yara, duba agogo karfe tara har da rabi."

Shiru nayi kaina a sunkuye, takowa yayi har inda nake yace.
"Meye matsayin Yarana a gurinki?"
Baya naƴi kaɗan dan naga haukar tashi zata motsa, cikin inda inda nace.
" Na yayesu ɗazun nan, idan kuma matsayi ne, toh su kaddaratace wnda na amshesu hannu bibiyu, haka yayi maka."

Juyawa yaƴi yabar barni a tsaye cikin karfin zuciya nace.
"Karfe uku jirginmu zai tashi, zuwa biyu zan tafi Nah idan na miki laifi kiyafe min."

Shiru tayi sannan ta bar min falon.
Nima wuccewa nayi jikina a sanyayye, haɗa kayana nayi tare da zama ina share kwalla, tashi nayi naje nayo alola sannan na gabatar da salla, Addu'a nake kawai Allah ya nuna min karfe uku na dare na tafi, na gaji da wannan rayuwar. Karan sako naji.
*Hey Beauty baki yi barci ba ko? Plss kwanta kisa Alerm 2:15*

Murmushi nayi sosai a raina ina cewa.
*Idan nasami Dr a rayuwata na more miji, dan kuwa zai jiyar dani daɗi da soyayyarsa, zai kaini wata duniya na daban, kuma zai girmana al'amarina*

Wani sakone ya shigo nayi maza na tura mishi,
*Baby kai me ya hanaka barcin?*
Murmushi yayi cikin zolaya Ya turo min da sakon da ya bani haushi.
*Ina hira da wata budurwan da muka haɗu da ita an Mumbai ce mai suna Arundhati*

*Toh ai sai kaje gurinta dan naga haɗin zai bada citta karka kuma nimata*

*Wayyo kiyi hakuri wasa nike miki waye ni da zan nime wata mace bayan kina nan*

Cikin jin haushi nace.
*Matsalarka kenan! Ni kan ai ko baka aureni ba zan iya hakuri na rungume kaddarata. Tun*

Cikin sauri ya turo min da.
.*Tun me?*
Share shi nayi naki magana, can ya kuma turo min da cewa.
*Plss tun me?*

Cikin jin haushi na tura mishi da cewa.
*Tunda bani da abinda zan fanshi dare mai daraja a gareka ba*
Kirana yaƴi cike da damuwa, ina gani naki dauka dan bana son bacin rai yanzun sai na sauƙe mishi rigimar da banshi yakar zomon ba, saƙo na tura mishi.
*Idan mun haɗu gobe zamuƴi magana akan haka.*
Kashe wayar nayi na gyara kwanciyata.

*02:00am.......*

Toh fa me zai faru kuma.....

*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 15 pages Insha Allah*

Oum Muwaddah......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....


Page.٤٦-46

02:00Am.....
Dake nasaka a raina zan bar garin har mafarki nayi wai tsakanin Ashraf da Dr sai faɗa suke akaina wannan na jana wannan jana, kowannensu so yake ya tafi dani. A na haka sai Allah yabawa Dr nasara fauce ni, a zubur na tashi. Zaune na tadda Nannah, da sauri na dira daga gadon na nufi Ban ɗaki naje nayi bukata ta nafito.
Cikin sauri na gyara fuskana, sannan na koma na zauna kusada ita.
"Yanzun Binti tafiya zakiyi ki bar yaranki? Ko tausayi basa baki?"
Ta watso min tambayar fuskarta cike da damuwa, sunkuyar da kaina nayi idanuna na cicciko da kwalla nace.
"Nah kiyi hakuri na tafi nice na bar miki su."

Gyaɗa kanta tayi sannan tace..
"Tashi ku tafi yana jiranki a waje."
Fita tayi daga ɗakin, sai ga maids sunzo zasu fitar min da kayana, ɗauka sukayi har da na yaran nidai bance kome ba, har gurin mota Nannah ta rakani, inda ta rike hannuna cikin sassanyar murya tace.
"Binti! Idan na rabaki da farin cikinki ban miki adalci ba, sabida cika min tawa muradin kika rasa taki, idan nace bazaki tafi da yaranki ba, toh na zama muguwa mara halacci, dan haka ki ɗauki kome da ya faru a matsayin kaddara ga yaran can mun bar miki har kiyayyesu, sai dai nasan dole zai zo amsarsu mungode kiyi hakuri da sanyaki kuka da mukayi kinzo cikin farin ciki yau gashi zaki koma ranki ba daɗi, ki gafarcemu. Sannan kyautarki da kika samu a masarautar anyi gaba dasu da fatan zaki yafe mana kura kuranmu."
Hawaye ne ya zubo min daga idanuna, nace.
"Nah karki damu ni ban taɓa rike kome a raina ba."
Buɗe min mota tayi na shiga.
"Nagode! Ki gaida mutanen gidan, suyi hakuri ban musu sallama ba."

Lumshe idanunta tayi tare da murmushi, ban sami nutsuwar zuciya ba sai da motar tashi. Ina ɗaga mata hannu tana ɗ'aga min.

Sai da muka bar cikin masarautar, na sauke katuwar ajiyar zuciya, sam banyi tsammanin ganin yaran ba, sai nagansu sunci kwallayi, har da abin wuyar wanda akayi ɗan kwaɗon da shap ɗin heart, na diamond. Kiran saudiya,
Wayata na ciro daga jaka, na haska fuskarsu, suna barci hankalinsu kwance, murmushi nayi.
"Kinji daɗi hakan?"
A zabure na leka, Wallahi Ashraf ke jan motar.

"Koma ki zauna"
Zama nayi zuciyata cike da tsoron kar ya min tsiya, koda muka isa shi da kanshi ya fidda min kayana, ya kaini har ciki sannan ya juya ya sumbaci yaranshi, ko Allah ya kiyayye bai ce min ba. Nima kuma ban damu ba, na zauna inata raba ido ta inda zanga Dr.
Biyu da rabi sai gashi nan yatawo fuskarshi ɗauke da murmushi, yazo ya zauna kusadani. D'aura kaina nayi a kafaɗarshi nace.
"Alhamdulillah! Ina cikin farin ciki."



2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment