Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tsayawa yaƴi sannan ya dawo da motar baya, duba jakar tayi taga babu karamar chanji. Sai dubu ɗaya cirowa tayi ta mika musu sadakar, Dukkansu makafine, sai da ta buɗe kofar ta saka musu a kwanon.

"Allah ya bada lada, ya kare miki gabanki da bayanki, ya kuma maidawa masharratan sharrinsu."

"Amin!" tace Zakari yaja motar, dan shi yaji sauki baya tare da wata damuwa. Nima sabida Aanih muke asibitin.

Suna barin gurin makafin nan babban cikinsu ya kallesu yace.
"Zuciyar Maryama da yaranta me kyau ne, yanzun zamu biya bashin da mukaci."

"Kawu ina Tanimu Dari!"
"Yana saudiya "
Shiru sukayi can suka ɓace.
***
Ina zaune duk tsoro ya gama cinye ni, murɗa kofar ɗakin akayi. Ummi ce da Zakari suka shigo kallon tsoro nake masu.

"Lafiya Safinah?"
A hankali na isa gabanta, kura mata ido nayi cikin kuka nace.
"Ummina!!"
Kallona tayi zatayi magana, damshi naji akan hancina, na share a hankali, jini ne yake ɗigowa daga hancina, zan buɗi baki nayi magana naji abu ya cika min wuyana zuwa bakina, kasa nayi da kaina sai ga gudar jini ya faɗo. Mikewa nayi.

Lokaci guda duƙ wani kafar jikina zubda jini yake, mikewa nayi jiri ya kwashe, na zube a jikinta.
...... Suna meeting wata Nurse ta shiga, dama hankalinshi yana kaina.
'Dr Zk! akwai matsala fa, matar nan fa tana zubda jini."
Mikewa sukayi shida Dudu, suka fito har suna bangaje junarsu.
A tare suka shigo ɗakin, kafin Dudu ya ɗauke ni, har ya ɗauke ni yayi waje dani, har lokacin zubda jini nake. Dakin gobe da nisa suka shiga dani, aka fara kokarin tsayar da jinin amna abu yaci tura.

Sunfi awa biyu akaina babu wani labari, dafe goshi Dr yayi. Sannan suka fito,
Kafin wani lokaci yan uwana duk sun shiga damuwa,
Zuba min ido yayi zuciyarshi ba daɗi, zama yayi ya sarkafe hannunmu, ya kai gefe fuskanshi. D'aya hannunshi yana shafa kaina,
"Safinatu! Na miki alkawarin zama dake a kowani hali. Kuma zan tabbatar miki."
A hankali ya mai da min hannuna, sannan ya fita.
........
Cikin fararen kaya suka bayyana a cikin ɗakin.
"Kawu wannan wani irin sihirine?"

"Eh toh Iqibal! Wannan mugun sihirine da mugaye a cikin bil Adam suke aikatawa,"

Shiru wanda aka kira Iqibal yayi sannan yace.
"Kawu taya za a lalata sihirin?"
"Allah zai kawo yadda za a warware."
***
Duba agogon Hannunshi yayi ya ga lokacin na kure mishi da sauri ya fita, ya kalle Dudu.
"Kyari bari naje Villa na dawo, daga nan zan wucce gidan gun Ammahna ko zata taimaka tazo taga halin da Safinatu take ciki."

Gƴaɗa musu kai yayi.
........
Tafiya yake da mugun gudu, taka birki yayi a tsorace ya fito sakamakon mahaukaciyar da ta shige gabanshi.
Tana dariya sosai tace.
"Ka koma bazaka ga Shugaban kasa ba, kaje mayanka acan aka tsuma yar tsanar."

Kaucewa yaƴi ya barta tana ta , haukarta. San baya tunanin maganarta gaskiya ne,
Kiranshi shugaban kasa yayi ya gaya mishi, zai shiga meeting.
Bai damu ba ya koma gidanu, yana shiga, katon Mansion ɗinsu ma aikata suka shiga gaida shi, bai bi takansu bai yi ba.
Ya shiga gidan a gigice yana kwala mata kira..
"Ammahna!!!"

Wata farar dattijuwa ce ta fito hannunta rikeda farin casbi. D'aya hannunta rike da sanda, murmushi tayi ciki dattako tace.
"Son! Lafiya!"
"Ammahna! Tana cikin wani hali."
Murmushi takara a karo na biyu tace.
"Safinatu ko?"
Gyada kanshi yayi, addu'o'i ta bashi sannan tace.
"Kaje ɗakin akwai Shafin shaiɗanu ka ɗauko a shafa mata shima yana taimakawa."
Ta kuma gaya mishi yadda zasu kula dani,
***
Cikin kwana biyu rak na koma abar tausayi, dukda ana addu'a. Da maganin gida, karshe dai aka dawo dani gida. Inda na cigaba jinya.
Ganin yadda nake wari ya ɗagawa kowa hankali, musaman Dr.
......... Ya gama duba wata mara lafiya ya dawo ɗakin ya kwantar da kanshi akan kujera, wani barci me mugun karfi yaƴi gaba dashi.
"Tun ranar da ciwon ya faru muka ce maka kaje mayanka, ka duba inda jini ke zuba zaka samu anan suka lankaya yar tsanan amma kayi biris sabida mahaukaciya ce, toh maza ka ɗauki ɗan uwanta kuje can Insha Allah rabb zaku ga waraka."

Firgit yayi tare da mikewa, ya fita daga ɗakin, ofishinsu Dudu ya nufa, yana zuwa yace.
"Kyari zo muje."

....... Da sauri suka fita, a mota ɗaya, suna barin garin abuja motarsu na lalacewa, dole suka ajiye motar suka sake niman shatar taxi.
Nan ma dai sai da suka fara tafiya, sannan motar itama ta lalace. Dakyar da ikon Allah suka isa mayankar, nan ma sun sha wuya kafin suƙa, sami yar babyn, suka fidda shi, ba tare da wata wata ba. Suka xuba mata fetir tare da wurga mata ashana dan akwai wasu mahauta a gurin.

Suna gamawa suka jiyo abinsu.

***
Buɗe idanuna nayi a gajiye. Na kalle Ummi da take rike da casbi.
A hankali nace.
"Ummina! Ina yarana?"
"Alhamdulillah! Safinatu, sannu bari na kawo miki su."

Dauko min yaran tayi ta sakaminsu kusadani, sannan tafita can sai gata ta dawo ɗauke da magani.

Tallafe ni tayi taban nasha, kiran Abdul tayi ta gaya mishi, sai gasu tare da Dr.
Wanka Ummi tayi min sannan na fito nasa kayana, zama nayi, a ɗakin sabida bani da karfi.
***
"Hmm! Bansan yadda akaƴi suka sami makarin ba, amma tabbas ta sami lafiya sosai. Dan yanzun na dubata sai cin abinci take"

Tsawa ya buga mata, tare da cewa.
"Bashi na tambayeki ba, taya kome yake lalacewa? Sannan waye yake kareta?"
A gigice Mamie tace.
"Yallaɓai!Allah mana. Don Allah ka kyaleni karka sakani a damuwa."
Kashe kiran yayi tabi wayar da kallo kamar doluwa.

***
*SAUDI*
Zama yaƴi ya ɗaura ɗaya akan ɗaya, hannunshi duk biyu ya jinginasu akan kujeran, ɗame bakinshi yayi baƴan lauyan ya gama masa bayani.
Lumshe idanunshi yayi, sannan yace.
"Ya yarana suke?"

"Ai yallaɓai! Duk lafiyansu lau dama Asma'uHusna ce Uwar ta kwanta akanta, Amma jikinta da sauki"

Buɗe idanunshi yayi, sannan yace.
"Da fatan babu matsala!"
"Eh toh babu kenan amma Fahad ya tabbatar min Uwar yaran ba lafiya."

Gyaɗa kanshi yayi sannan yace.
"Meke faruwa A jordan?"

"Gaskiya Yallaɓai iyakata Nigeria ka bani damar na tura wasu, Wallahi bani da masaniya da abinda ke faru."

"Yayi kyau."
Yana gama faɗar haka ya mike, tare da barin ɗakin ziyaran ƴa koma cikin gidan.
***
*Jordan*
Alamura sun tsananta sosai, dan har takai ana nunawa juna yatsa tsakanin Ukshe da Abu. Dakyar Ammar da Uzaif suka shawo kansu.
Shi Abu Zarri yace bazai bi shugabanci Ukshe ba dan babu Allah a cikin mulkinsa. Shima kuna Ukshe yace bazai bi Abu Zarri ba, kafin lokaci kalilan sun hautsinawa juna lissafi dan kamar zasu kashe junan,

Ana haka Marhum ya shigo naaarautar domin farautar duk wanda yaje cewa shi zai zama sarki, da duƙ me hannu a kamashi sai da ya kashe manyan cikin masarautar har mutane biyar.
A sannu zubda jini yazama abin ado a cikin Birnin Amman, domin an samu rabuwar kai wasu nacewa A baiwa Ukshe wasu na cewa Abu Zarri.
Ga kuma Marhum da yake kokarin ganin bayan kowa ya amshe mulkin.

***
Zaune muke ya sani a gaba, sai kunnani yake da tsokana naki kula shi.
"Insha Allah! Idan na kama mutum sai na cinye bakin tsiwar nan, wanda yake kin magana."
Dago idanuna nayi cikin nutsuwa nace.
"Amma baka da lafiya".

"Haka kowa ke faɗa! Wai tunda na haɗu dake na hau bishiyar kacen sonki."

"Kasan me kace kuwa.?"
Na tambayeshi,
"Eh nasani mana! Gaskiya na fada ina sonki! Amma kinki ki bani amsa sai guduna kike Why Safinah ko na miki tsofa ne. Ni ba kamar Anim sa Babansu Aanih ba. Ni na girma ko ba haka ba? "

Kauda kaina nayi na cigaba da kallon gefe nace.
"Babu ruwan so da tsufa ko na kasa, kawai abinda nasani........



Oum Muwaddah....... Kuyi hakuri na isa Page.40 zan saka muku yadda zakuyi payment ɗin.....Nagode
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....

*Alhamdulillah Barka da zuwa bakuwar duniya Ku tayamu Murna Malamata ta sauka An sani baby girl Um Nass marubciyar Yarda Da kai Allah ya raya babƴ ya kuma baki lafiyar shayarwa*



       Rubutuna dai dai nake jera number idan baki ga wani number ba ki tambayar......
Page.٣٥-35
"Sannan da kake maganar kodan ka manyanta ne, ni banga haka ba. Dan ni a mutum nagari nake kallonka, rashin amsa maka kuwa ba kome bane sai ina tsoron kar na faɗa sonka daga karshe ka bani wahala ne, na haɗaƙa da Allah idan kazo da niyyar cutar dani kaje nagode, karka gasa min ruhina da zuciyata."
       
  Tasowa yayi yazo gaba ya zauna kusadani har ina iya jiyo kamshin turaranshi, lumshe idanuna nayi. Sannan na sake ajiyar zuciya,
      "Ina son haka! Kin amshe ni kenan"
     Ware idanuna nayi tare da satar kallonshi, shima ni yake ƙallo.
    "Idan kika kuma satar kallona, sai na kai karanki gun Ummi ko Ammahna."
Har da murguɗa min baki,(😏)
       Buɗe bakina nayi ina kallonshi hura min iskar bakinshi yayi, kamshi Cool fresh
Doki hancina, sunkyar da kaina nayi ina wasa da hannuna.
    "Baki ce kome ba Safinah?"
   Na kasa d'aga ido na kalle shi, sabida kwarjininsa, tare da girmanshi da suka cika min ido,
    Sai wasa nake da yatsina, kallon yadda nake yatsun ya ɗago tare da kallon fuskana da yake sunkuye yace.
"Baki ce min kome ba, ga lokaci na tafiya."
              
     Dakyar na haɗiye yawun bakina nace.
"Na amince."
Ina faɗar haka na tashi da sauri zan bar falon cikin d'aga murya yadda zanji yace.
"Tafiyar tafi kome jan hankali, musaman yadda zubin halittar yake"
   Da sauri na shige cikin ina dariya, shi kuma ya mike yana darawa.
       ***
A hankali na warware, dan haka Abba da kanshi ya nima min visa zuwa Oman. Amma naki sabida nasan nisa da Dr, har Ammahnshi ya kawo min ita. Naji daɗin da tazo dan haka nayita hidima da ita, kin kawo mata Yan biyu nayi muna cikin hira sai ga Mamie matar da sai nayi sama da sati uku ban kalleta ba itace yau har cikin falonmu, dake ta ɗauko dakon min tijara sai gata tazo.
      "Feener ina shegun yaranki masu shegen kukan tsiyar nan?"
       Ji nayi kamar kasa ta tsaga. Na shige ciki na huta da bakin ciki,
    "Subhanallah"
    Ammah tace tare da kallon yadda na sunkuyar da kaina ƙasa, janye idanunta tayi a ƙaina ta maida kan Mamie tace.
"Baiwar Allah! Yanzun ke zaki ji daɗi a kalle idanunki a kira d'iyoyinki da shegu."

      "Hajiya ai yaran gaba da fatiha ne, dan haka ba wani abin kunya bane dan nakirasu da shegu tunda bamu san Ubanso ba, garin kwadayi akwaso yan  daka kuka. Batun a kira yarana da shegu bata taso ba, dan ban taba barin iyayena na tafi yawon karuwanci ba, kuma Ubanau kaɗai nasani ba wasu karti ba, idan zaki cewa Dr ya hakura toh idan kuma bazaki ce masa ba cutar zamani tayi ajalinsa."

     Tana gama faɗar haka tafita tabarmu a falon, jikina yayi sanyi hawaye ke jika min hijab ɗin dake jikina, jikina na rawa har mun zata tafi sai gata ta dawo tace.
"Hajiya! Kice ta kawo miki su kiga jinin masu fararan kunne sai ki tabbatar da abinda na gaya miki, hmm."

   "Nuratu!!!" Ummi ta bugata tsawa, cikin tsananin ɓacin rai tace.
"Fitar min a gida kafin na mugun baki mamaki."

  Da sauri ta fita tana cewa.
"Maryam uwar karuwa kakar shegu."
  Tashi na shige ɗakina da gudu na rufe kofar tare da sake kuka me mugun karfi, ina buga kaina da karfi a jikin bango.

      "Safinah buɗe mana kofar karki kashe kanki," Inji Ummi, itama Zuciyarta tayi rauni. Ammah itama tazo tayita magana amma fir naki bari, ga yaran suma sun tashi sai kuka suke.
           Naki kulasu. Kafin wani lokaci har gidanmu ya cika, da yan uwana har da Abba, ga Dr da Ammah takirashi.
   Dudu yayi na buɗe kofar naki ina kuka, tare da cewa.
"Ku kyale ni na mutum da bakin ciki."
          "Toh ai matsalar bakiwa AbdulHameed alkawarin zaki kashe kanki ba, hanya mafi sauki ki buɗe kofar nazo miki da allura sai ki cika kiwa kanki." 
   Kuka ne ya kwace min me tsuma rai, na buɗe kofar a hankali.
       Na tsaya a gabanshi. Shigowa yayi ya ɗauki Aanih ya mikawa Dudu, sannan ya dauki Aamih ya mikawa Ummi sannan ta tura kofar, ya jingina da jikin kofar harɗe hannunshi yaƴi a kirjinsa, yace.
"Zo nan Beauty!!"
      Dakyar na d'aga kafana na isa gareshi ina shashekar kuka, hannunsa yasa ya d'ago haɓɓana yace.
"Wani ya taɓa ce miki kina da kyau kuwa! Ban taɓa ganin wacce kuka ke mata kyau kamat ke ba."
            Janye hannunshi yayi daga haɓɓana ya cusa cikin aljuhun wandonshi, yace.
"Dukda na shaku da Ammahna, ban taɓa tuɓ kararta da maganar ina son mace ba, sabida girma da kunyarta, kuma sai akayi dace niɗin bantaɓa samun mace ba, dan ko Balkisu hadamu akayi, amma haɗuwana dake"
   Kara kusantoni yayi yadda nake iya jin saukar numfashinsa, "d'ago ki kalleni"
            D'ago fuskana nayi ina zubda kwalla.
     "Ina haɗuwa dake naji bana tsoron kome, da naji kome akanki naji zan iya baki dukkan nutsuwata, ko kwana biyu na gaza yi da kamuwa DA soyayyarki na faɗawa Ammanha, kinsan me yasa, sabida a haɗuwa dake nasan me ake kira da jajjircewa, da tsayawa akan kaifi ɗaya, koda na faɗawa Ammahna kaddararki murmushi tayi tace min.
"Idan tayi maka kana sonta ni yar rakiya ce tare da Addu'a, bazan taɓa hanaka farin cikinka ba, batun Yara musulunci ita yabawa, amma idan Ubansu yana ganin zai rukesu ba damuwa da nan dacan duk ɗaya ne."
  Kinji abinda tace min tare da bani goyan baya Safinah! Nifa ba kome nake so a tare dake ba, kece muradina, kuma mafarkina ce ke! Don Allah a duk lokacin da wani ya kuntatta miki ki tuna da mutanen da zasuyi kuka da kukanki, ki tunada mutanen da zasuyi dariya da dariyarki, a wannan zamanin Y'an mata dubu nawa suke sayarda kimansu dan abu kalilan amma ke rabo da kuma sadaukarwa, tare da kariyar Ubangiji ya rushe aurenki da wancan kawalin, kuma yarinya da yanzun ya cuceki ya haɗaki da damuwa, dan wallahi bayi da lafiya."
    Zaro idanu nayi ina kallonshi  alamun mamaki da tsoro, dariya yasaka har da dafe cikinsa yace.
"Matsoraciya! Daga jin batun ciwo ta kama zare kananun eyes ɗinta."

             "Na gaya miki gaskiya, muje ki kisamu su Ammah zata koma gida."
      Haka ya shiga gaba ina binshi a baya, har falon.
  "Ya Dr me ka gayawa Didi! Ita da take sha'awar zama shekakkiya sai gashi ka dawo mana da ita, me ka gaya mata."
     
   "Baby kace ta bari." na faɗa a shagwaɓe.
          "Batul Amor bata son ki rabu da ita, ko ana dole ne ta fasa sheke kanta sai ya zama abin tuhuma. Kinga kowa ya haɗiye tambayar da take bakinshi in ba haka ba zan cika iska a cikin allura nawa mutum kai tsaye yake tafiya ga zuciya. Lokaci guda sai dai aga  mutum ya yanki jiki ya faɗi. Sai mutuwa."
     Dariya suka kowa ya saka, Abba ya kalle shi cikin mutuntawa yace.
"Toh Dr! Nagode."
     Kallona yayi yasa hannunshi a fuskarshi kaman zai rike haɓɓanshi yana murmurshi nima, nayi maida mishi tare da gyaɗa mishi kaina.

          Da ido yayi min Alama da na same shi a waje zai fita, d'aga kafaɗana nayi,
         Motsa bakinshi yayi alamun plss.
Girgiza kaina nayi tare da kwaɓa fuskana alamun..
"No"
         Mikewa yayi yace.
"Batul! Jiya na ganki da wata yarinya ko zamu je ki bani address ɗinta."

     Kura musu ido nayi na kuma saka kunnena ina jiran amsar da zata bashi. Dake itama bakar munafukace, sai gashi ta mike tare da bin bayanshi.
      Raina ne ya ɓaci duk suka bani haushi. Ummi da take mika min yarinyar na amsheta tare da dangwarata  akan cinyata ina zumbura bakina, karshe na mike tare da barin falon, ina shiga na hango waya tana kawo wuta, da sauri na isa gareta na ɗauka. Sakonshi ne ya shigo min,
   *Heartbeat zan tafi tunda kinki zuwa zanje gurin kawar Batul I holp babu matsala."

    Tsuka naja masifa na cina na tura mishi.
*Allah ya raka taki gona! Thank God bani ce na kawoka ba kai zo da kafarka.*
 
   Dariya yaƴi sannan ya kalle Ammah yace..
"Ammahna Yarki fushi take dani."

   "Gwara tayi,in nice ma fasa son katon gauro irinka zanyi."
  Shafa sajenshi yayi fuskarshi ɗauke da wata sirritacciyar murmushi, haka ya cigaba da jan motar har ya isa gida, tana sauka ya wucce Asibiti. A hanyarshi na tafiya asibiti yaga kamar ana binshi, yazo wani kwana. Sai ga wata Hilux sa mugun gudum tana zuwa ta daki motar da take binshi, tuni motar ta hantsila gefen hanya, me hilux ɗin yayi cilla a guje.
                  Dawowa yayi da baya kasancewa mutane sun taru ana kokarin ciro mutanen da suke cikin motar. Ya kutsa kanshi. Matasane duk jini ya ɓata musu fuska,
    Karan wayarshi yaji  ya fita a cikin mutanen ya koma cikin motarshi ya dauka.
"Kayi Babban Sa'a a rayuwa da jana'izarka za ayi anjima"

      "Dakiki! Daba irinka ce maka akaƴi ni jahili ne? Ai duk wanda ya yarda da Allah baya taɓa tsoron mutuwa, amma dake kai gidahumi ne wai kana min barazana da mutuwa bayan rigata ce."

         "Matukar ina raye bazan taɓa barinƙa ka samu nutsuwa da Feener ba, sai naga bayanka."

         "Toh sai kaƴi gadin duniyar."
           
YA ALLAH MUNGODE KABAMU IKON CINYE JARABAWAR😭😭😭👏Ina cikin tashin hankali nida Family na ina baran Addu'arku Allah ya kawo mana ɗauki👏😭


Oum Muwaddah...
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*

_Jordan Historical_

*©2020*
BOOK ONE....



Alhamdulillah nagode sosai👏👏

Page.٣٦-36
      Tsaki Dr yayi sannan ya kashe wayarshi ya bar gurin, yana mamakin halin Anim.

       ***
Anim Kamil Matawalle, D'a ne ga tsohon Daraktar gidan Radion na kasa, Alhaji kamil mutumin kirki ne bashi da abokin faɗa, haka ma Hajiya Balaraba. Mahaifiyar
Yaransu Uku, Anim ne Babb sai , Saifideen, sannan Ummulkhairi, Tun farko haɗuwasu da Feener ba yazo yana sonta bane an sashi ya sace ne ya ɓata mata suna, sabida tana jagorantar wani shiri na yaki da tafautaci da Yara da Mata.
       Ganin tana tawayarwa mutane kai da kuma nuna musu illar bayarda yaransu, kuma mw gidanshi shiine ke jagoranta fitar da mata da yara  a cikin kasar nan. Dan haka tabi kauyika tana wayarmu musu da kansu, har mutane suƙa fara hankalta. Dan haƙa suka daina bada yaransu.
    
   Haka ya janyo karyewan arzikin Ubangidanshi, dan haka lokaci guda ya bawa Anim Hotonta da adress ɗin, ya kuma nima mishi aiki a gidan radion da Feener ke aiki, a hankali suka fara aiki  A tare har kuma shirin suƙe gabatarwa tare.

  ...... Ahankali mutane suka fara zargin suna son juna, dukda dai Feener bata ɗauki abun ba sai daga baya ta mika wuya suka fara soyayya sama sama, har dai yakai gaban iyaye.

      Anim yana da mata da yara Biyu mata, kuma bayi da lafiƴa yana fama da ciwon Hanta(😁😂😹 Yo na lura kun ra ja'a a wancan nikuwa labarin a kintse take) kuma cutar hanta tana cikin cututtuka masu hatsari.  Sun taɓa haɗuwa da Dr saubiyu loƙacin shi an gayyace shi domin yayi musu lectures akan yadda zasu kare kansu da kuma gudun jefa wani a cikin matsala, har an gama kome na maganar aurensu kwatsam sai Feener ta fito da maganar zuwanta Jordan, kuma dama A nufinsa idan zasuyin Hoton prewedding toh anan zasu, cima burinsu, kuma abinda zai baku mamaki an bawa Anim kuɗi dan yayi aikin bayan shi ɗin kawaline, fasa auren da tafiyarta ba karamin asara yaja mishi ba, har maigidanshi ya kwace rabin kuɗin.
         Abinda yafi ɗaga mishi hankali dawowarta da ciƙin dukda baya jin sonta,  Dawowarta yaji yana masifar kaunarta dan da farko tafiyarta ji yayi kamar ya bita, sabida tsabar sonta da yake, karshe ya maida musu da kuɗinsu, baƴan tace bata sonshi.
         Tsakani da Allah Anim yahakura, sai dai an sami matsala ranar da yaje dubata a asibiti, ya fito kenan ranshi a ɓace. Ya shiga motar garin tukin gangancin da yake, karshe yaje wata mota tabi takanshi....

           Dakyar aka ciro shi suna zuwa Asibiti aka fara bashi taimakon gaggawa.
  
   Duba wayarshi akaƴi suka sami lambar Mamie, kiranta akaƴi tazo taganshi. Shine takira wata kawarta ta gaya mata,ita kuma tazo da wani mutum suka fita dashi daga Asibitin......

Wannan shine asalin Abinda ya faru ina Mamie suka kaishi Oho.....
      ***
Ƙallon mara lafiyan yayi cikin sakin fuska yace.
"Yanzun ina ke miki ciwo?"
    Girgiza mishi kai tayi cikin murmushi,
"Ok gashi Allah ya sawwaƙa"
          Tura mata takardan yayi. A madadin ta ɗauƙa sai ta ɗaura hannunta akan nashi, janyewa yayi cikin ɗaurewan fuska yace.
"Hidayya! Bana son haka, duk zamanki a cikin asibitin kina cewa baki da lafiya nasani amma na shareki, pls

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment