Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna mishi hanyar kofa..
Murmushi yayi sannan ya shiga ɓalle rigarshi, dafe cikina nayi a tsorace nace.
"Na haɗaka da Allah karka cutar da Yaron da bai san waye shi ba."

Murmushi yayi cike da kwarin gwiwa yace.
"Toh zaki saurareni?"
Gyaɗa kaina naƴi kwalla na zubo min,
"Ok zauna kici abinci!" yace min.

Ba musu na zauna tare da wurga mishi tambaya nace.
"Ina ka kawo ni?"
"Atlanta Ocean muna cikin jirgin ruwa ne" yace min a takaice, tausayin kaina ne ya kamani. Me yasa rayuwa take wasan kwallo dani.
Zama yayi ya shiga zuba min sannan ya fara ɗiba zai bani na kauda kaina yace min.
"Hmm"
Babu wasa a fuskarshi, amsar abincin nayi a sannu yayita bani, har naci kaɗan, sannan nakauda kaina nace.
"Yaushe zaka maidani gun Ummina da Duduna"
Taɓe bakinsa yaƴi sannan yace.
"Sai lokacin da naƴi niyya."
Kura mishi ido nayi jikina yayi mugun sanyi,
"Duk akan me?"
"So!!!"
"Cuta dai! Matawalle wannan ba so bane cutane."
Shafa fuskana fuskana yayi fuskarshi cike da damuwa yace.
"Cutie sabida so na ɗauko ki, naga mutane zasu min shamaki ne dake, Dudu, Innata, Rabi'atu. Zasu min katanga dake suna shirin min bakin ciki. Kinga yadda ciki yayi miki kyau, ina son ganinki a haka shi yasa na kawo ki nan, pls ki barni na taɓa ki."
Zaro ido nayi ina ja da baya tare da girgiza kaina, bakina na rawa nace.
"Karka min haka, Anim wallahi ni ba mazinaciya bace."

Ina matsawa yana matsoni, sai da muka kure gadon, rufe idanuna nayi. Kwalla ya shiga zuba min. Hannunshi naji a kan cikina yana shafawa a slow, tsigar jikina ya mike. Kwalla masu zafi suka shiga zuba da mugun gudu. D'ago kanshi yayi yaga yadda kwalla suke wasan tsare akan fuskana, abinda najine yasani buɗe idanuna,
*Allah sarki Sultan banda wannan abinda ya faru damu bai taɓa kuskuran taɓa ni ba*
"Anim!!" na kirashi a hankali,
"Hmm! Cutie."
Girgiza mishi kai nayi, hannunshi naji a bayana, kuka nake wiwi ina tureshi haka Anim ya cigaba da, bin jikina.

"Ashraf!!!"
Na ambaci sunanshi, d'ago kanshi yayi da jajjayen idanunshi Jijjiyar kanshi yayi raɗa raɗa, yace.
"Uban cikinki ko? Safina meye yasa?"
"Wayyo Allah na! Nace da karfi, ina rike hannunshi. Mugunta zalla ya min, danne cibiyata yaƴi.
"Idan kika kuma kiran sunanshi sai na illata wannan abun domin kuwa shi ya hanani ke shi ya rabani dake,"

Bansan wata irin rayuwa nake ba, daga wannan matsalar sai wannan. Ji nake ina ma banq cikin duniyar nan, sai da yayi da kanshi ya kyale ni, anan na kwanta na cigaba da kuka.
***
*Suleja*
Kallon agogen falon Ummi tayi. Karfe biyu saura na rana Safina babu dalilinta, mikewa tayi ta fito har part ɗin Mama ta zauna cikin damuwa tace.
"Maman Abideen har yanzun Yakolo bata dawo ba, kuma karfe goma take dawowa. Kinga har biyu fa."
"Maman Safinah kina da hankali kuwa, yarinya tun goma bata dawo ba, shine baki faɗa ba yau da ita ɗaya ne ai da sauki mace da ciki fa."

Kamar zata rufe Ummi da duka haka take ji, ta shiga kiran Abideen yana ɗauka ta gaya mishi sannan ta kashe.
Shima asibitin yaje akace bata zo ba, tashin hankali wanda ba asa masa rana. Ummi takira Abdul ta gaya mishi halin da ake ciki, shi kuma ya faɗawa su Nana da Abba.
Lokacin da Abba yaji labari, tsabar tsoro ɗaukar takai mishi yayi ya ɗaura akanshi, hularsa a hammatarshi. Yakira Abdul yace.
"Gimbiya Asma'u tasani ne?"
Abdul yace.
"A'a bata sani ba."
"Shi kenan takare min, dan mutuwa zanyi tace bata kyale kowa."
Hankalin kowa a tashe yake, Mamie kam gani take kamar wasa Nannah take, kuma tana da masaniyar sace Safinah dan yayita bin Abdul ya gaya mishi inda take amma fir yaki, da yaga tana bautawa kuɗi sama da kome shine yayi amfani sa kuɗin ya tambayeta tace bari ta tambayi khalil. Zuciyarshi ɗaƴa Khalil tana tambayarshi ya gaya mata, tana Suleja. Jim kadan takira Anim ya gaya mishi.
Shi kuma yayo hayar kwararru a kidnapping suƙa kwamushe. Baiwar Sultan mamar magajin gobe (😥😹😂)

***
*OMAN*
Kallon ruwan dake gudu a lambusu take jikinta na bata akwai wani abu, dake dab da faru. Kawai ta ɗauki wayarta ta kira Abduƙ bugu biyu ya ɗauka,kamar ya kifa yace.

"Nannah! Akwai matsala."
Tashi tayi kamar zata zuba da gudu tace.
"Ba dai wani abu yasami Binti ba."
"Nannah an saceta."
Mikewa tayi wayar ta subuce a hannunta, zama tayi jikinta kamar wacce bata da karfi.
Zubur ta mike ta nufi cikin gida........
A ranar ta baro kasat zuwa nigeria
***
Duk inda ake tsamani zanje an duba bana gun jikinsu yayi sanyi, da farko sun zata kamar yadda nayi wanca tafiya, sai da aka je har airport aka duba, gabaki ɗaya, hankali kowa sai da ya tashi kwana biyu tsakani sai ga Nannah. Abin ba a cewa kome dan kuwa Nannah tana isowa batabi takan kowa ba, aka shiga bincike da lokacin........


Kuyi hakuri, Waleed ba lafiya jiya kwana mukayi bamu runtsa ba yanzun ma ina rubutun kamar wacce aka sani dole in Barar Addu'arku........

#MJ
#Vote
#HZƘ.....

Oum Muwadda....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

Page.٢٢

  Tawowa yayi ya kawo min abincin, sannan ya ajiye min kallonshi nayi zai fita nayi maza na rike hannunshi, cikin rawar murya nace.
"Kayi hakuri Dudu."

      Murmushi yayi min kaɗan sannan yace.
"Kici, idan bai isheki ba a karo miki."
        Girgiza kai nayi, nasaka abincin a gaba na fara ci, har zai fita nace mishi.
"Abdul! Don Allah ka kaini suleja ina kewar Ummina."
  
   Gyara tsayuwarshi yayi, sannan ya shafe kwantaccen gashin kansa yace.
"Ok ki gama sai na kaiki in yaso jibi sai ki dawo."
      Gyaɗa mishi kai nayi, shi kuma ya fita.
    Sosai naci abincin sannan naje ban daki na wanke bakina bayan nayi wanka, na shirya cikin bakakken kaya, doguwar riga da bakin gyale, sannan na ɗibe kayana sosai. Sannan na fito na same Madam sophia a tsaye. Yana fitowa ya ɗauki jakana, muka fita, gaba ya buɗe min na zauna yasa jakar a baya  itama tashiga yajamu muka tafi.

     ........ Har gidan iyayenta ya kainta wanda yake kusada gidanmu, kallonshi nayi zanyi magana muryarta ƴa katsemu tace.
"Karuwa hankalinki ya kwanta, kin rabani da mijina. Muguwa azzaluma baiki aure ba harkin kashe auren kaninki, a haka zaki kare."
          Ji nayi kirjina yayi min nauyi, dakyar nake jan numfashina, tabbas an taɓani amma ba kome.  Bai damuwa yaja motar muka bar layin. Tunda muka ɗauki hanya bai ce min kome ba. Nima haka muna dab zamu shiga suleja naga masu fura da nono..
"Dudu! Zansha fura."
    Sauka yayi a gefen hanya sannan ya fita, yaje ya sayo min. Yana shigowa  ya mika min, naji jikin goran yayi matuƙar sanyi, buɗewa nayi na fara sha, wani sanyi daɗi tare da garɗi me shiga rai ya gauraya furan ina kurɓa tare da lumshe idanuna, komawa yayi da baya yasake sayo min gora biyu, dan tun bamu bar gurin ba na kusan shanye goran.
            Kafin mu isa gidan Uncle Ahmad na shanye goran farko na kuma buɗe na biyu shima sai da naga bayan rabinsa naji cikina ya cika, kwanar da zai kaini gidan. Muka hango mai sayarda gashen masara, tare da ayaba a gashe. Bani manta lokacin da na gama karatu aka turani Imo naci ayabar da gyaɗa.
  "Dudu! Ayaba da Masara,"
     Tsayawa yayi yasaya min sannan muka wucce gidan,  Yaran gidan suka taremu da murna gasu da tarbiya, karɓan kayan sukayi tare da kai mana ɗakin Ummi, Gaida Mama Saratu mukayi  tayi mana yar nasiha sannan muka wucce, ɗakin Ummu tana zaune akan abin sallah  ɗan karamin part ne har da kitchen a ciki, koda zata so wani abu ta dafa da kanta, ajiyar zuciya na sauke. Sannan na zuɓe a jikinta tare da sake ajiyar zuciya. Murmushi ta sake tare da ɗan tureni cikin tsokana tace.
"Abinda Dudu bazaiyi ba shi kika fi aukinyi, baki san kin girma bane."
Tura baki nanayi gaba sannan na kara, kwanciya jikinta ina sauke ajiyar zuciya tare da maida kwalla, kamar yadda nasaka kaina akan cinyar haka Abdul ya ɗaura aƙan kafaɗarta  muka shiga hiran. Cikin gajiya da mutuwar jiki nace.
"Ummina na gaji jikina ciwo yake min tare da mugun nauyi gashi bansan waye zai min tausa ba amma jikina na mugun damuna."
       Gyara zama Abdul yayi sannan yace.
"Tun yaushe haka ya fara damunki?"

      Juya idanuna nayi cikin jin daɗi yadda Ummi take matsa min kafafuna nace.
"Dudu kusan wata uku kenan, tunda abin nan ya fita."
   Na karshe maganar a raunane.
      "Tashi muje a dubaki."
   Abdul yace min.
Taɓe baki nayi nace.
"Allah bani zuwa ko ina, bana son fita yanzun ma baka ji yadda nake jin amai bane, da zaka ce min mu sake fita."

       "Kyaleta tukun ko zuwa gobe zansa Abideen ya kaita."
             "Yawwa Ummina, Mother like no Other. Ilove you so much." na gaya mata ina lumshe idanuna,
   Zaro ido Abdul yayi, sannan yace.
"Ina bolar mutanen da aka tsana Ummi kinganta ko akan idanunki kenan"
          "Dudu har yanzun baka daina kishin nan ba." nace mishi tare da gwalo.
      Gyara zama yayi sannan ya sunkuyar da kanshi, ya faɗawa Ummi abinda yayiwa Sophia.
  
  Dariya tayi tare da cewa..
"Toh su me yar uwa shine har da koran yar mutane gidansu, baka ci riba wallahi ai bazata damu ba kaje kadawo da ita kuma ka Safina bazata koma ba, in dama dan itace ta zauna a nan,  idan kayi hakuri zaka sha mamaki yanzun ka maida ita ɗakinta batun aure kuma ka jany.."

      Cike da jin haushi na mike nace.
"Ummi kince ya maidata ya maidata, amma Aure kan wallahi sai yayi nice ma zan haɗa maka kaya ko sisinka karka kashe."

Make bakina tayi, cikin fushi tace.
   "Me garinku! Ce miki akayi auren haka zai yi ba lissafi, dan ta miki laifi sai ku mata ramuqar gayya, kul kada naji ko na gani, aure bazan hanaka ba, amma ba yanzun ba kaje ku sasanta tukun."
            Fuuuu na mike a falon na shige inda nake tsamani kitchen ne naje na saka furar sannan na fito zuwa ɗakinta ina shiga na zube a bakin gadon, tare da kwanciya.
Ban san tafiyar Abdul ba dan ban tashi ba sai uku saura, a gurguje naƴi alola, tare da gabatar da sallah. Ina cikin addu'a Ummi ta leko.
"Yakolo me kike so zaki ci."
Kasancewar sunan da take kirana dashi kenan sabida sunan Kakata ce dani. D'ago fararen idanuna nayi masu cike da barci nace.
"Taliyar murji da miyar jajjage amma Ummi na manja, sai ko alale duk wanda nasamu zanci."

Shiru tayi can tace.
"Ina ga alalen zaki samu taliyar zance a kawo min daga kano aƙwai Asiya kanwar Matar kawunku zatazo wani sati."

Gyaɗa kaina nayi, ita kuma tafita, akan sallayar na gungura. Karfe huɗu da rabi na farka, tare da mika, sannan na nufi ban ɗaki nayi wanka. Anan na karewa kirjina kallo sunyi wani irin cika. Dan wani lokacin idan nasaka bra ciwo suke min, dake kuma bani da irin mugun halittar nan. Sai haka ya tafi da jikina, amma maganar gaskiya nayi mamaki cikar kirjina, domin sunyi girma ba laifi dan suna tsaye ne car..(😎 kar a fassara min maganata)

Marata na shafa naji yayi min ɗim, ɗan latsashi nayi naji yayi min tauri ga zafin da yake min dole na hakura na fito.
Dukda ina da matsala a duk lokacin da watana yaƴi amma nakan share wata biyu ana uku nayi hailata sai dai tunda nayi yunkurin zubda cikin. Ban kuma ganin hailata ba gashi har wata huɗu.

........ Ina idar da sallar la'asar na fito falon nasamu har Ummi ta gama min, zama nayi jikina har da rawa, ga yaji a gefena. Ci nake ina wani lumshe idanuna tsabar daɗi, ina cinyewa ta kuma kawo min karɓa nayi na cinye. Zaro ido tayi.
"Yakolo cikinki yayi yawa fa."
"Wallahi kuwa Ummina, bari na sha furar nan inaga zan koshi."

Ina shiga kitchen ɗin ta bini da ido, cike da tausayi. Bata san na fito ba sai da na shiga shan fura me sanyi, ina shanyewa na tuna da masara da ayaba. Ɗauka nayi na fara ci ta kwace.
"Haba ina zaki kai su?"

Tura baki nayi sannan nace.
"Ummi bana jin daɗin bakina babu tauna don Allah taimaki jaririyarki mana"
Yadda na mata sai da tayi dariya, sannan ta mika min ina karɓa na kwaɓa fuska nace.
"Ummina bari na ɗumama su."
Tashi nayi naje ɗumamawa, ni da naje abu daban sai gani na koma yin wainar fulawa, lekowa Ummi tayi taga abinda nake. Murmushi tayi tazo ta ja kujera ta zauna ina kwaɓa fulawar.
Har na fara soya tana murmushi, dan tun da nafara nake cin ɗaya ɗaya, kafin na gama na cinye kusan rabi.
"Anya Safinatu cikinki nan ba rowa yasaki ba."
Wanda zan kai bakina ne ya faɗu kasa, cokalin hannuna shim Ya faɗi.
"Kina mamaki bayan kinsha magani yafita ko? Ai tunda Allah ya tsara shi a kaddararki ba makawa sai kin haifeshi, shawara ɗaya ce ki nutsu har Allah ya rabaku lafiya, tunda na amince da kaddararki ina ga babu amfani ki sare, idan kikayi haka zan ɗauka dan mahaifinku kikayi idan kika haifa min cikin zanyi farin cikin ansar kaddararki hannu biyu. Kuma zanyi alfahari dake, shi yasa nace bazaki koma ba ki zauna a nan ki haihu."

Wani iri nasiha Ummina take min wanda yake bin jikina da duk wani gabba yana kashe min su.

Ga wani irin soyayyar da take gwada min akan cikina da kuma ni kaina, bansan wa tabawa aika ba sai ga kayan baby. Cikin katon jaka, kunya ya hanani ko kallon kayan, dan wallahi yadda na tsani Ashrf haka na tsani cikin jikina ya yaudareni da cewa zai zo kuma ya barni cikin hatsari.

........ Yau monday na fara zuwa asibiti, ina bin layi aka zo kaina. Sunana suka tambaya na gaya musu, sai da suka ce.
"Sunan Mijinki fa, kin bamu safina kawai."

Shiru nayi cikin tashin hankali na lalube wayata na turawa Abdul text lokacin yana tare da Anim, turo min yayi da "kisa Abdul"
Haka kawai sai naji zuciyata tayi min nauyi.
"Ashraf!!"
Nacewa matar kaina a sunkuye, "Amma baki jima da aure ba ko? Irin wannan kunyar har ina."

*Da kinsan matsayin cikin da kallon banza zaki min* nace haka a raina.
Nasha yawo a cikin asibitin dama privet ne, ina gamawa Abideen yazo ya ɗauke ni, sai wash wash nake. Shi kuwa yayita dariya wai nafi kowa ragonta.
***
*SAUDI*
Shiru lawyershi yayi yana kallon yadda ya koma, can lawyer ɗin yace.
"Yallaɓai!"
D'ago kanshi yayi cikin kokarin ɓoye damuwarshi yace.
"Ina jinka"

"Kayi magana man, wallahi mahaifiyarka tana cikin damuwa, sai."
Naɗe hannunshi yayi sannan ya koma jikin kujerar yace.
"Kace mata karta damu haka Allah ya nufa, ta roka min ita wacce tazo dominta da ta yafe min, sai me?."

"Baiwarka Safinah!"
Kuraqa lawyer idanu yayi kamar zai cinye shi da su. Sannan ya sauke su akanshi tare da kauda kanshi, haɗiye yawu lawyer yayi sannan yace.
"Tana ɗauke da cikinka?"
Dunkule hannunshi yayi kamar zai kai naushi, ya ɗago tare da bin lawyer da ido, sannan ya mike zai bar gun lawyer yace.
"Tana cikin halin rayuwa dan sanadin cikin zuri'arta sun tarwatse."
Bai saurari Lawyer ba. Ya koma ciki kwalla na zubo mishi. Tabbas har da hakkin Safinah ke ɗawainiya dashi, ya lalata mata gobenta ya kuma ɓata mata rayuwarta, gashi har da rabo a tsakaninsu.

Gwara ya amince da laifin dan bai san yadda zai fuskanci safinah ba, shi da yace nan da wata biyu...... Lumshe idanunshi yayi.

***
*Abuja*
Shan gabanshi tayi cikin bala'i da masifa tace.
"Nice zaka munafutarta bayan kaji abinda karuwarka tayi na ƙunya aka fasa maganar aurenku shine yanzun ka koma binta. Na rantse sai naga bayanku ada can ma sabida Innarka na amince a yanzun kuwa zaka gani dani kake zance."

Bai kulata ba yayi ficcewarsa. Ya rasa inda zai kai fitinar Rabi wallabi ta buwayi rayuwarshi, bai san inda tajiyo ya koma niman Safinah ba, shi abinda yasani yana tare da Abdul, kuma yana samun labarinta kuma Insha Allah sai ya aureta.

***
Shiri nake amma jikina a sake, dan bana son zuwa asibitin dukda yanzun cikina watanshi na biyar kenan, ina jin yadda yake juyawa. Gashi yayi wani mugun girma, har ma yana son fin wataninsa, a yanzun babu takalmin da yake min sai silifas, duk zuwan Abdul sai yayi min tsiya wai na tara tsokoki kumatai, tabbas haka ne dan a wata biyar na zama ruguzun ruguzun. Gashi na kara buɗuwa sosai, ina gama shiryawa na fito. Yau babu Abideen da zai kaini, sallama nayiwa Ummi nayi addu'ar fita a gida, sannan na nufi bakin titi. Ina jirar taxi sai ga wata Audi, me tintec. Sauke glass ɗin akayi na kauda kaina. Me motar yace.
"Malama Safinah! Shigo na kaiki mana." da mamaki na kalle shi sai na kauda kaina.
"Kishigo cikin ruwan sanyi dan duk nan da kike gani akwai mutanenmu, kuma zasu iya sakaki a cikin motarda karfin tsiya, kawai ki shigo."

Shafa cikina nayi a hankali naji yadda yake juyawa sakamakon bugun zuciyata, kwalla ce ta zubo min me zafi, nasaka hannu na buɗe motar, bakina ɗauke da addu'ar niman kariyar Allah. Ina jan kofar ana sako hannu tabaya aka shaka min ɗan farin kyale, bingirewa nayi da barci ....

#MJ#HZƘ#Vote......


Oum Muwadda......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_

     *_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

Allah yasaka da alkhairi nagode sa addu'arku jiki yayi sauki sosai
Page.٢٤

  Zare jikina nayi cikin na Anim,  a hankali naja bargon da ya lulluɓemu na sauka rigata da na hango a kasa, nayi maza na suturta jikina. Sannan na shiga ban ɗaki, fitsari nayi. Jin cikina ya takure guri guda yasani shiga cikin kwanon wankan na cika da ruwan ɗumi na fara wanka. Ina idarwa na lumshe idanuna, tausayin makomar rayuwata nake.
      Buɗe idanuna nayi cikin sauri bansan shigowarsa ba, sai hannunshi nayi a kirjin, buge hannun nayi.
"Wai meye ne haka? Ni bana son iskan...."
Buge min bakina yayi bansan lokacin da nace.
"Allah ya isa min"
Sake buge bakin yayi. Sannan ya cigaba da murza dukiyar fulani na,
Wani munafukin nishi na sauke, tare da tura kirjina gaba. Ina lumshe idanuna, loƙaci guda kwalla na zuba daga idanuna.
Shiga cikin ruwan yayi, tare da kwaɓe kaƴansa. Hannunshi naji yana shirin wuccewa kasata, nayi maza narike, idanuna akanshi muryana na rawa nace.
"Don Allah karka min haka! Karka manta kaima Ubane zaka ji zafi idan akawa Yaranka ha..."

"Ki bar gaya min Maganar banza domin ai baki min adalci ba da kika watsar da aurena, sannan kika dawo min wani abu daban, ina raye kika watsar min da virgin ɗinki abinda na tanadawa kaina, kika bawa wancan ƙaton bayan kinsan akwai mamallakinsa, sannan banyi magana ba nazo inayin abinda yadace zaki min Allah ya isa."

Bakinshi ya kai wuyata yana lasa tare da kai hannunshi kan cinyata yana shafawa a hankali, bani da abinda zanyi kuma bana jin zan iya yin kome, sai kuka zan iya cewa na tsani kaina da rayuwata badan kashe kai haramun bane da na rataƴe kaina na huta da masifar rayuwa.
Ganin yadda nake kuka wiwi yasa shi ɗaga hannunshi a jikina cikin takaici yace.
"Amma shi balaraben da ya same a ɓagas ince bashi kanki kikayi ba tare da gardama ba sai ni da muka ajiye maganar aure a tsakaninmu. Wai ni kam meye laifina son da nake miki shine laifi ko kuma soyayyata a gareki."
Mikewa nayi tare da ɗauraye jikina na fara kokarin fita yayi maza zai fincikoni na dafe cikin tare da kura mishi ido. Murmushi na sakar mishi tare da cewa.
"Ina ga baka san abinda ake kira da sarauta da mulki ba, sabida baka taso cikin gidan da suke da nasaba da mulki ba, kana k'etare iyakarka. Idan har jarumar Uwa zata iya sadaukar da rayuwarta dan soyayyar d'anta me kake tunani zatayi akan soyayyar jikanta, ba barazana nake maka ba kayi a hankali da shiga hurumin daular da babu irinsu a cikin yankin Jaziratul Arab."

"Tsoratani kike!?"
Ban kalle shi ba, nace.
"Shawari nake ba."
Fita yayi daga cikin ruwan cin matsanancin ɓacin rai yace.
"Ke kin isa?"
Wani banzan kallo na mishi sannan na fito, ba kaya yafito tare da niman nayi magana ya ɗirka min tijara, ni kuwa bani da lokacin haka. Falo na fito tare da kwanciya a dogon kujera, tun da nasan inda nake ban kuma fita ba, na mikawa Allah alamarina sannan ta ko ina sallah nake, dan bansan inda alkibilar take ba. Bana jin daɗin kaddarata amma yana iya tunda a juye tazo min, nayi imani da Allah rayuwata bata da amfani, dan daga wancar matsalar ta toshe still wani zai buɗe, a iyakar rayuwata ban taɓa jin bakin cikin d'a namiji ba sai yanzun.
Tunda naga na kwanta shima sai yazo ya kwanta a kujera me cin mutum biyu, ya zuba min ido ganin yadda nake barci. Haka ya matuƙar burge shi, dan haka ya ɗauko tap ɗinshi ya fara min hotuna.
.... A yanzun na daina mishi magana, kallonshi ma banaƴi abinci kuwa sai naga zai taɓa min lafiyar cikina, zanci amma ina cikin damuwa sosai, a cikin kwanaki uku zuwa huɗu har kafafuna sun kumbura. Gashi ko nan da ban ɗaki na shiga haki nake, duk sai naji na masifar gajiya. Sai mugun ciwon kan da ya sani a gaba musaman idan na kwana tunanin Ummina da yan uwana, toh nan ne fa, zan tashi fuskana a kumbure.

***
*Suleja*
Duk inda ake tsammanin ina nan babu ni babu labarina. Mamie tana sane da haka amma tayi banza da kowa ta cigaba da tsabgar gabanta.


2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment