Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga kuma Ummie group one and two suma ba'a basu a baya ba. Ummie kuwa zazzabi ne ma rufeta tsna dakin Kanwar Maman Aunty ta kwanta duk yawancin hotunan babu ita.

Sai da akayi sallar Azahar sannan akayi wakima hade da kdan kwarya. Robobi, Jaka da kuma memo wanda ke dauke da sunayen amarya da ango aka dinga rarrabawa.

Sai kusan la'asar sannan aka fara shirin tafiya wajen mota shida akayi saboda masu son zuwa ganin gidan amarya.

Zainab kuwa har tayi wa Ummie allura dan tun da ta shiga daki taga bata da lafiya ta saka aka siyo ma ta alkuara da sirinji. Kafin su iso kano har zazzabin ya sauka.

Bayan magariba suka iso dan baby wani nisa kasancewar a kauyukan dake cikin birnin kano chan karsheยฒ suke.

Gidan amarya aka wuce direct, Zainab da knata ta saka wasu ya mata da ita kanta bazata ce ga alakarsu ba lol...

Suka fara gyara gidan dan ya danyi kura. Kafin wani lokaci gidan yayi fes, Zainab ta kara gyara ko ina ta saka turare.

A tsakiyar gado aka zaunar da Zarah korar yan matan waje Zainab tayi tana kallon Zarah ta ce " Kin wani kakkame jiki me haka?

Bude lullubinta tayi ta ce " Bazaki gane ba amma kunyar Zayd nake ji wallahi"

Tsaki Zainab tayi tana fadin " Wallahi zaki ma daina ne, kinga nasan suna ta jiran fitiwarmu bari muje"

"Ina Ummie ne?
"Tan wajen Aunty kinsan suna gida said gobe su Inna zasuzo ganin gida sai su tafi ko zuwa jibi ne"

"OK" Zarah ta fada yana murmushi.

Fita Zainab tayi tana kada kan yan matan duk su ka fita.

Zayd na zaune cikin mota shi da wani dan Baffa na kauye yana ta masa hirar yadda rayuwar kauye take ta banbanta data birni sosai.

Wayarsa ce ta fara ruri. Daukar yayi yana karawa akunne tare da fadin " Hello Sir"

"Ango kasha khamshi! Ko da yake ni ma ai ango ne dan Mata ta tadawo yau, sorry bansamu zuwa ba saboda wani uzuri.

Murmushi Zayd yayi ya ce " Aikuwa ban karbi uzurin ba gobe zanzo na fadawa Mama zagayawar da kake wajen matarka bayan tayi maka hani"

Dariya Yusuf ya saki yana fadin " Karka fasa mana, Allah ya sanya alkhairy good nite"

Daga haka ya katse wayar. Zainab ce tayi knocking glass din. Saukewa yayi yana kallonta ya ce " Har kun tafi?

"Eh, ai nasan baku bukatar nasiha ko? Ta karashe maganar cikin zolaya. Fitowa yayi daga motar yana fadin " Kije da motar gida"

Karbar makullin tayi tana tsokar Sule dake yi wa ango tsiya. Sallama tayi masa sannan ta bar kofar gidan nasa.

Gyara hularsa yayi yana shiga cikin gidan tare da tarin addu'o'i.

Falon shuru ba kowa said sanyi ac da khamshi kawai. Dakinta ya nufa tana jin karar bude kofa tayi sauri rufe fuskarta tana gyara zama.

Tsayawa kallonta kawai yayi yana sakin murmushi tare da yin godiya ga Allah.

"Kinganni nan zumud'i ya mantar dani siyan kaza" Ya fada yana dafa kansa.

Fita yayi da sauri dan shaf ya manta.

Kusan karo sukayi da Zainba. "Ungo nan yanzu Sule yake fada min baka siyi kaza ba duk da dai ba gashin yan gau bace ta guri Bashir me gashi ce ga madara Aunty ta ce tana sa muku albarka"

Karb'a yayi yana ma ta godiya sannan ya rufo gidan.


Ganin ya dawo da wuri yasa ta tunanin me ya dawo dashi?

Zama yayi kusa da ita yana fadin " Kanwata ta siyo min, kije kiyi alwala"

Ya karashe maganar yana kallonta.

A sanyaye ta tashi ta nufi toilet yabi bayanta da kallo yana murmushi. Kafin ta fito har yaje yayo nashi alwalar. Tana fitowa ya jasu sallah kamar yadda sunna ta tanadar.

Bayan sun idar yayi addua me tsaho haka itama a na ta b'angaren. Yadda ake wankan tsarki kawai ya tambayeta, aikuwa ta bashi bayani. Murmushi yayi yana tashi ya fita daga dakin. Ajiyar zuciya ta sauke tana tashi da sauri ta dauki kedar kazar ta saka a kofar dakin ta waje ta kulle dakun da makullin she don't know why but she's feeling nervous.

Yana dawowa yaga ledar kazar a waje murmushi yayi yana kallon key din dake jikin kofarsa dan duk kofofin iri daya ne amma bazai bude ba tunda ta nuna bata so. Daukar ledar yayi ya nufi fridge din dake falo.

Fito da naman yayi a cikin foilpaper ya saka a plate sannan ya saka a fridge tare da madarar.

A Dustbin din kitchen ya saka ledar ya dauraye hannunsa sannan ya nufi daki.

Say biyu ya kirata amma bata dauka ba har yayi giveup said kuma ya kasa ya kuma dialing har ta kusa tsinkewa sai ta daga tana yin shuru.

"Good nite" Ya fad'a cikin kasalalliyar murya. Shiru tayi zuciyarta na bugawa tana tunanin anya ta kyauta? Ni kuwa na ce ji iya shege๐Ÿ˜’

"I love you so much Wifey" Ya fad'a yana sauraron numfashinta.

Katse wayar tayi da sauri. Murmushi yayi yana gyara kwanciyarsa kwanyarsa cike da tunaninta.....

*i received some reward yesterday duk da baki bayyana min kanki ba zanyi amfani da wannan damar na gode miki nagode Allah ya kara budi layin da kikayi min text me haha shiga nasan bakya so nasanki amma nagode please idan kinga sakon nan kimin magana ta number na nagode*

*sorry for the typing errors, and please a cigaba da hakuri dani saboda rashin update a kan kari*

Autar Mama ce.
โœจโœจ *UMMIE* โœจโœจ

_Labari daya danganci soyayya da kuma ฦ™alubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 19" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1183832592?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=ePKIBPqEnneIOT4mVcsRGjtgmw4P%2BOLgkyKbogqeXKvCAHSTISK2LgUd4Et37B9DonE0OE9TJ6ljR0RH8XNvLYxkCM9UXBEn3iX%2FTxVBSm%2BzWquXSOqlbf09railBLSV

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta ฦ˜awaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

Aslm ma abota biyan littafin Momin Haneef ce tana sanar daku littafin ta na ak'idar masarautar.

littafin nakud'ine idan kina buk'ata zaki iya fara biya tunkafin free page yak'are gamai son littafin ak'idar masarautar zai turo da kud'insa ta wannan account๐Ÿ‘‡

Nusaiba Rabi'u Union Bank 0087778987

Idan kuma katine zaku turo katin MTN ta wannan number๐Ÿ‘‡
07026368879

Bamuson vtu bazamu kar b'aba

Idan kinturo kud'in zaki turo mana da shaidan kin biya ta wannan number07026368879

Normal group 300 only
Zakuna samun page d'aya (1 )arana

Special group 400๐Ÿ‘‡
Zakuna samun page biyu (2) arana duk Wanda kikaga yamiki sai kishi ga.

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: ๐™ˆ๐˜ผ๐™ˆ๐˜ผ๐™‰ ๐™‰๐™๐™Ž๐˜ผ๐™„๐˜ฝ๐˜ผ,,๐™„๐™†๐™„๐™‡๐™„๐™ˆ๐˜ผ ๐˜ผ๐˜ฟ๐˜ผ๐™ˆ(๐™ ๐™ฎ๐™–๐™ช๐™ฉ๐™– ๐™™๐™–๐™œ๐™– ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*๐™ˆ๐˜ผ๐™ˆ๐˜ผ๐™‰ ๐™‰๐™๐™Ž๐˜ผ๐™„๐˜ฝ๐˜ผ* tazo muku da littafin (๐™†'๐˜ผ๐˜ฟ๐˜ฟ๐˜ผ๐™๐˜ผ ๐˜พ๐™€)

๐™„๐™†๐™„๐™‡๐™„๐™ˆ๐˜ผ ๐˜ผ๐˜ฟ๐˜ผ๐™ˆ( ๐™†๐™ฎ๐™–๐™ช๐™ฉ๐™– ๐™™๐™–๐™œ๐™– ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™) tazo muku da littafin (๐™†'๐˜ผ๐™‰๐™’๐˜ผ๐™๐˜ผ)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.

*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...


*K'ANWATA*

*Dandano!Dandano!!*


Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..


Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573


Nomal. guda d'aya N 300 ne

guda biyu N 500 ne


Special guda d'aya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne


Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

โœŒ๐ŸผFitattu biyu masu ban mamaki๐Ÿซ€Hakika babban goro sai magogin ฦ™arfe ๐Ÿ˜, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka๐Ÿซ, Fitattu biyu๐Ÿ‘ฏ๐Ÿฝโ€โ™€sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku ๐Ÿค“ sun shirya tsaf domin fadakar daku๐Ÿง  sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so๐Ÿ’‹๐Ÿ’ž, wohoho tabbas ๏ธsahun giwa๐Ÿ‘ฃ mai ษ“adda na raฦ™umi ๐Ÿช,Fitattu biyu๐Ÿ˜โœŒ๐Ÿผ masu tafiyar k'asaita, sheฦ™i, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka๐Ÿ˜˜๐Ÿƒ๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ Fitattun ฦ˜arshen shekara๐Ÿ˜ salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta๐Ÿ˜ maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari๐Ÿƒ๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*โœ๐Ÿฝ Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* โœ๐Ÿฝ Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ
Vip 700๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Shafi na sha tara*

Sabir ne ya fara sakkowa kafin ita, ran Mama a b'ace ta ce " Ramlah abun naki har ya kai na baki umarni kik'i ji? Kinsan yarinyar nan makaranta zata tafi ko? Ga Assignment bata gama ba saboda ba'a isa dake ba?

Shuru Ramlah ta yi ranta a had'e kamar zata daki Maman. "Yayi kyau, jeki kwanta"

Mama ta fad'a tana karbar ludayin dake hannun Ummie ta shiga kitchen. Bin bayanta Ummie tayi tana fadin " Yanzu zan karasa kiyi hak'uri"

"Ki je kiyi shirin makaranta" Mama ta fada ba tare da ta kalleta ba.

Ummie bata ce komai ba ta fita zuciyarta ba dadi.

Bata tarar da Aunty Ramlah a falo ba sai Sabir dake danneยฒ a wayarta.

'Lallai Aunty Ramlah bata da kirki' Ta fada a ranta tana zama kusa da Sabir ta ce " Bani wayata aiki nakeyi da ita"

"Aunty Mummy ta ce min wai Uncle Farooq baya sonki auren dole akayi masa"

Shuru Ummie tayi tana jin zuciyarta ba dad'i amma ta daure tayi murmushi ta ce " Ni da Uncle Farooq muna matuk'ar k'aunar junan mu, yanzu dai bani wayata"

Ta karashe maganar tana karbar wayarta a hannunsa. Yana zaune har ta kammala aikinta, tattara komai tayi ta ajiye a gefen kujera lokacin har Mama ta kammala girkin.

"Yawwa Ummie idan driver zai kaiki makaranta ki kai wa Yusuf wannan" Ta fada tana ajiye basket din da ta jerawa Yusuf abinci.

Da toh ta amsa sannan ta wuce sama. Ba ta dad'e ba ta sakko cikin hijabi har kasa da jakar makarantarta.

Sabir har ya fara cin abinsa yana yi wa Mama hira. Sallama tayi musu sannan ta tafi.

โ˜…

"Wai Shehu me yake damunka ne? Aikin ma ka dena fita! Duk ka zama wani iri.

Wani banzan kallo yayi ma ta kafin yaja tsaki ya ce " Dallah fice min daga d'aki"

"Wai me yake damunka ne? Kullum cikin tsawa da masifa! Cewar Sa'adah tana harararsa.

Ta shi yayi ya fice daga dakin yana buga kofa da k'arfi. Dogon tsaki taja tana fadin " A haka zaka kare ai, kuma aje a karbo Ummie ai an gama bikin"

Shehu yana fitowa ya zauna a falo yana dafa kanshi, gaba d'aya ya rasa me yake masa dad'i tun lokacin dasu Zarah suka zo.

Sale ne ya shigo yana busa sigari. Yana ganin shehu ya kashe sigarin yana fadin " Ashe bakayi bacci ba"

Dogon tsaki Shehu yaja ya tashi ya bar falon yana ji kamar zai rufe Sule da dukan tsiya.

โ˜…

Ummie ce a tsakiyar su tana bacci hankali kwance hannun Zarah a cikinta tana shafawa a hankali.

Ajiye wayarsa yayi yana tallafar Kansa da hannunsa sannan ya d'ora d'ayen hannun a kan na Zarah wanda ke cikin Ummie.

Kallonsa tayi tana d'an sakin murmushi ba tare da face komai ba.

"Zamu gyara wani d'akin musanman saboda Ummie"

D'auke hannunta tayi tsna tashi ta zauna ta jingina da jikin gado ta ce " A'a, gobe nake so ka mayar da ita dan bana so Shehu yazo yayi mana hauka"

" Hmm shikenan but ki daina fad'ar haka kinji?

"Me? Ta fad'a tana kallonsa. "Kince Shehu zaizo yayi hauka"

"Kaima gashi ka fad'a ai" Zarah ta fad'a tana dariya.

Tsayawa yayi yana kallonta kafin ya lumshe idanunsa zuciyarsa cike da haske da farinciki.

Dena dariyar tayi tana fadin " Bacci nake ji sai da safe"

Gyarawa tayi ta kwanta tana lulluba da bargo. Shima kwanciyar yayi yana kallon bayanta.

*ABUJA*

A hankali yake shan Coffee din yana d'an danna wayarsa. Ya kai kusan 30mins a zaune a wajen kafin ya kammala.

Wajen biyan kud'i ya nufa ya biya sannan ya fito daga coffee shop din. Yana isa bakin titi dan ya hau taxi yaji an tab'ashi daga baya. Juyowa yayi ya kalki mutumin.

Wani hoto ya nuna masa yana fad'in " Kaga wannan yaron ya wuce?

Wani kallo Farooq yayi masa daga k'asa har sama, bai ce dashi komai ba fara tafiya dan yasan wannan bazai wuce plan ba dan yau two days da fara sharia kuma da alamu nasara na tare dasu so anything can happen.

Sauri ya k'ara ganin mutumin sai binsa yake. Beyi aune ba yaji an buga masa abu a kansa. Wani irin haza-hazo ya fara gani, sake buga masa akayi daga nan be k'ara sanin inda kansa yake ba.

*KANO*

Tun daren jiya ta zama so restless, gashi yau ta tashi jikinta duk ba dad'i ko down stairs ta masa sakkowa.

Yusuf ne ya shigo d'akin yana kallonta ya ce " Mama lafiya? Tunda na shigo da asuba naga kamar baki da lafiya, gashi haryanzu baki dawo normal ba ko dai muje asibity?

Ta shi zaune Mama tayi tana kallin Yusuf ta ce " Duk inda Farooq yake baya cikin kwanciyar hankali, Yusuf naji a jikina"

Mama ta fad'a cikin sanyin murya.
Kafin Yusuf yayi magana wayarsa ta hau ruri.

Sunan Zayd da ya gani ya sashi mamaki, sai da ta kusa tsinkewa sannan ya dauka yana fad'in " Ango kasha turare"

"Uhm, brother dinka yana Abuja and he was kidnapped by some goons kuma ana zargi a kan Shariar da ake gunadarwa ce yanzu Zarah take nuna min news din ga hotan Farooq he was missing tun daren jiya, a coffee shop aka ganshi last"

"T..thanks" Yusuf ya fada yana jin jikinsa ya d'au zafi.

"Me ya faru?" Mama ta fada tana kallonsa ganin yanayinsa ya sauya.

"A'a bakomai akan aiki ne bari naje" Daga haka ya tashi ya fice da sauri.

Kiran Zayd ya kuma yi bugu uku ya d'auka yana fad'in " Hello sir!"

"Yawwa Zayd basu bada wani address a jikin news d'in ba?

Daga d'ayan b'angaren Zayd ya ce " A'a sir sunan coffee shop d'in kawai aka fad'a, but zaka iya dubawa a google a wani location yake a Abuja"

"OK Zayd nagode"
"Sir ka jirani ko a office ne bari nazo muje"

"Toh Zayd nagode" Yusuf ya fad'a yana kashe wayar zuciyarsa a tsinke.

Ummie dake tsaye a bayansa tun fara wayarsa jikinta duk a sanyaye duk da cewa bata san akan me yake maganar ba.

Yana juyowa suka had'a ido. Murmushi tayi kad'an ta ce " Ina kwana?

"Lafiya lau" Daga haka ya nufi hanyar bari falon. Da kallo ta bishi tana mamakin yadda ko d'an wasan daya sabayi ma ta idsn ta gaisheshi yau bahu gashi he's so tense ko me yake damunsa? Ta fada tana kallon k'ofar daya bi.

Bata da amsa hakan yasa ta nufi kitchen dan yin breakfast.

Zayd kuwa wanka yayi yana fitowa Zarah ta tayashi shiryawa, har yazo fita ta ce " Tsaya"

Murmushi yayi yana tsayawa ya ce " Menene"

Jikinsa ta shige tana sauke ajiyar zuciya tana jin wani sanyi. Rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta ya ce " First hug ko?

"Nidai bana so ka tafi" Ta fada tana kara matsewa a jikinsa. "So kike na kara yin wani wankan ko? Ya fada cikin zolaya.
D'agowa tayi daga jikinsa tana kallon fuskarsa ta ce " Mu tafi tare"

Hancinta ya ja yana fadin " A'a ki dai jirani zuwa dare insha Allah mun dawo ki kula da kanki kinji?

Sake rungumeshi tayi tana jin wani yanayi na daban wanda bata taba jin hakan a kan zayd ba sai yau.

"Yusuf yana jirana sai na dawo"

Sakinsa tayi yayi ma ta kiss a kumatu har mota suka rakoshi ita da Ummie data gama cin abinci a falo, sai data ga fitarsa sannan ta dawo cikin gidan tana murmushi.

Yusuf yana fita office ya nufa yadda ya saba tsayawa su gaisa da ma'aikatan sa yau beyi ba kowa yasha mamaki. Yana zama a office dinsa kira ya shigo wayarsa da Unknown number.

Da sauri ya d'auka yana fad'in " Hello"

"Yusuf! Yaji an kirashi da karfi. "Waye? Ya fada hankalinsa a tashe.

Dariya aka fashe da ita sannan aka katse wayar. Kafin yayi wani abu Zayd ya turo kofar yana kallonsa. Tashi tsaye Yusuf yayi yana fad'in " Mu tafi flight zamu hau ban damu ko nawa zasu ce tunda urgent flight ne"

"OK sir" Zayd ya fad'a yana fitowa, shima fitowa sukayi sannan suka bar kanfanin.

Kasancewar sa sannane the owner of Two brothers yasa basu wani sha wahala ba akayi ready din komai. Within one hour suka bar Kano.

Bayan sun sauka ya rasa ina zai dosa, gaba daya hankalinsa baya jikinsa.

Zaunar dashi Zayd yayi yana ciro wayarsa dan su duba inda location na coffee shop din yake.

Wani kiran ne ya sake shigowa wayar Yusuf, again unknown number ce. D'auka yayi yana karawa akunne ba tare da yayi magana ba.

"Zama samu gawar d'an uwanka a Coffee shop din da muka d'aukeshi"
Wani dum zuciyar Yusuf ta buga da sauri yabtashi ya ce " Ku fad'a min nawa kuke so Dan Allah karku kasheshi"

Dariya yaji an fashe da ita kafin kuma yaji ance " D'an uwanka taurin kai ne dashi mun ja masa kunne ya k'i ji! Bama buk'atar kudi ransa kawai muke bukata"

Sai kuma yaji shuru, kusan second biyar kafin yaji sound na muryar Farooq yana sonyi magana. "Zaku iya zuwa yanzu saboda ya samu wanka da sallar gawa kafin ruwa ya tafi dashi"

Kafin Yusuf ya ce wani abu yaji karar harbi. Wayar hannunsa ce ta fadi yayi suman tsaye idanuwansa suka firfito zuciyarsa tayi wani irin bugawa.

Rik'eshi Zayd yayi yana zaunar dashi sannan ya d'auko wayar da ta fad'i.

Kusan minti biyu sannan hankalinsa ya dawo jikinsa da sauri ya tashi jikinsa na rawa ya ce " Coffee shop Zayd muje"

Kafin Zayd ya ce wani abu wayar Yusuf ta fara ruri. Da sauri ya dauka.

Muryar Farooq yaji yana fadin " Brother karkazo, kar kazo is a trap please kat Mama ta rasa Two sons din... Be karashe maganar ba Yusuf yaji kamar an bugawa Farooq abu. Runtsa idanunsa yayi ya bude su zuciyarsa na tafasa.

"Karfe 1 na dare"

Daga haka yaji an jatse wayar. Kallon Zayd yayi ya ce " Sunce 1 na dare kafin nan zamu iya saka police cikin lamarin saboda a kamasu"

"Hakane, muje police station by now ma nasan suna investigation a kan case din"

Cewar Zayd yana kallonsa.

Police station beyi musu wahalar nemowa ba, already case din yana hannunsu kuma sun kara samun wani clue a kan lamarin bayan zuwansu Zayd.

SS a ka kira saboda badda kama tun karfe biyu na rana aka tura jami'ai guda biyar wadannan suka badda kama, wani yana siyar da abu wani yana zaune kamar pagal wani kuma yana gefen titi da kayan sana'ar gyaran takalmi wani kuma yana siyar da rake.

Ko wanne yana da distance da d'an uwansa kuma ko wanne yana gabatar da aikinsa yadda ya kamata.

Gaba d'aya Yusuf ya rasa nutsuwa.

Sun a zaune a police station kiran Mama ya shigo wayarsa.

Katsewa yayi ya kirata, cikin muryar kuka ta ce " Farooq!

Runtsa idanunsa yayi yasan by now tasan komai maybe Ramlah ce zata fada ma ta dan babu inda bata kurdawa a Internet zata iya ganin news din, Mama ba news take kalla ba, Mama... Sai kuma yayi shuru ya kasa cigaba da magana.

Zayd ne ya karbi wayar yana fadin " Insha Allah Farooq zai dawo gida cikin koshin lafiya Hajiya ki kwantar da hankalinki"

In charge a man case dinne ya karbi wayar yana fad'in " Mahaifiyarsa ce?

Kai kawai Zayd ya daga alamar eh.

Kafin d'an sandan yayi magana Mama ta katse wayat sakamakon faduwa da tayi a hannunta.

*KANO*

Bayan sallar la'asar Zarah ta maida Ummie gida bata shiga ba a kofar gidan ta tsaya sai data ga shigar Ummie sannan tasa me napep ya dawo da ita gida tana jin duk ba dadi jikinta.

Bayan ta isa gida ta danna kiran number Zayd.

Bugu d'aya ya dauka, "Ya ake ciki?

"Sai zuwa anjima, gobe insha Allah zamu dawo"

"Shikenan Allah ya kubutar dashi"

"Amin" ya amsa yana sauke ajiye zuciya.
Sallama sukayi . ta ajiye wayar tana lumshe idanunta.

Mama kuwa Asibiti suka nufa da ita banda juka babu abinda Ummie da Sabir sukeyi, tun Ramlah na tausayinsu har ta fara yi musu masifa.

Tashin hankali ne ya sakacta faduwa har ta suma, dakin hutu aka kaita ta huta kafin ta farka a sallamesu.

โ˜…

Kamar yadda suka fada 1am dai-dai suka cillo Farooq jamar tsumma ta cikin mota aikuwa ya gangaro ya dawo gefen titi kafin su rufe kofa aka sakar musu wuta amma ina babu wanda ya raunata a cikinsu sakamakon sun rufe motar da wuri kuma bullet proof ce.

Wani irin dukan kasa ACP yayi yana jin wani takaici, jiniyar yan sanda aka saka yana juyawa yaga jamiam fararen jaya sun saka motar a tsakiya sun firfito hannunsu d'auke sa bindigu.

Yusuf da Zayd me sika fito cikin d'aya daga cikin motocin da gudu suja nufi inda suka ga an saka gawar Farooq jini duk jikin farar t shirt din dake jikinsa ko kotsi bayayi.

"Go down! Go down! A in da Acp din ya fada da karfi kasantuwar daya daga cikin 'yan ta'adar ya fito da wata mahaujaciyar bindiga wadda ko ma'aikatan tsaro basu da irinta.

Harbi ya saki fatatata ta ko ina.

Sam beji zafin shigar bullent din ba sai abu me d'umi daya ji yana shiga jikinsa har cikin pant din dake jikinsa. A hankali ya sunkuyo yana kallon gefen cikinsa.

"Zayd! Yusuf ya kira sunansa da karfi ganin halin da yake ciki....

Musayar wuta aka dinga yi tsakanin police da yan ta'addar amma ina bindigun yan ta'addan yafi na yan sandan, tuni suka wuce mutun daya ne kawai ya raunata. Police wajen uku aka harba.

Cikin tashin hankali Yusuf ya tallafo Zayd ganin yana shirin fad'uwa, idanunsa sunyi ja.

Wani irin azaba ne ya ziyarci kwanyar Zayd lokaci daya .

Motar asibiti ce ta zo aka saka Farroq, Zayd sa kuma sauran mutun uku da suka samu harbi"

A motor ACP Yusuf ya bisu yana ji kamar ya fashe da kuka.....

*Sorry for the typing errors*

Autar Mama ce.
โœจโœจ *UMMIE* โœจโœจ

_Labari daya danganci soyayya da kuma ฦ™alubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 16" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1181220702?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=PLkLDk%2B4yH5fThRZchqXmVWogU%2BhnmNeYT5kf0941uz7byIYbcT1yMYZ6T%2FT%2FLHBcGtPGWjEAJECDsEN5%2F1delU41KIk5u6716t3MrHfXdwik3o6xd%2FX%2FWzsdDWZTMWE

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta ฦ˜awaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar

Please Login or Register in order to submit comment