Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana kallonsa.

"Yes! Amma be zama lallai ki tuna ba dan kina karama lokacin! Ya gida? Ya Zarah?

" Tana nan lafiya! Ta fada tana kallonsa.

"Good! Ina kika je haka?

"Munje gyaran gashi ne kuma dare yayi min"

"Ok muje na saukeki ko?

Girgiza kai tayi tana fadin " Bakomai i will manage"

"She sounds just like her mother, yarinyar is much pretty than Zarah! Lumshe idanunsa yayi yana tuna lokacin baya! Tabbas idan so cutane toh hakuri ma maganine! Yafi 16yrs da soyayyar Zarah a zuciyarsa hkan kaddararsa ce! Da ace yayi aure da wuri by now yana da yarinya kamar Ummie idan Allah ya bashi haihuwa, bagashi ba yanzu abokinsa zai aurar da yarinya, but haka Allah ya tsara! Murmushi yayi hade da sauke nunfashi ya ce " Muje! Bana son musu"

"Nifa ba inda zanje haka kawai kayi kidnapping dina? Kawai ka tsarar min napep ka biya kudin sai na tafi"

Ummie tafada zuciyarta daya.

"Kings malama wuce muje sai taurin kan tsiya da sace ki zamuyi da tuni ba munyi ba!

Cewar saurayin yana kallonta.

Idanunta ta mayar kansa sai kuma ta kankance ido tana nuna shi! Tabbas tasan fuskar nan!

"Ba sanina kikayi ba malama! Ya fada yana kallonta. Sauke hannunta tayi tana kallonsu ta ce " Na sanku! Amma na manta inda na sanku!

Yayyafi aka fara yi, kallonta *FAROOQ* Yayi ya ce "Mu je"

Tsintar kanta tayi da binsu, back seat ta shigaa tana addua.

"Idan ma saceki zamuyi shikenan ko! Toh ki daina saurin yarda da mutane! Saurayin ya fada yana kallonta ta mirror.

Shuru Ummie tayi tana kallonsa cikinta ya duri ruwa.

Sun dade suna tafi kafin su iso quarters dinsu, tayi mamakin ta yadda suka sani! Har kofar gidansu ya tsaya yana kallonta ya ce " Hankalinki ya kwanta?

Bata ce komai ta sakko daga motar. "Kice wa Zarah, Farooq na gaida ita"

Da toh ta amsa sannan ta nufi gida. Sai da sukaga shigarta sannan suka bar wajen


A zaune ta tarar da Zayd, Zarah,Khaleel suna kallo.

Karasawa tayi tana rakube².

"Sannu da zuwa ur highness! Cewar Zayd yana kallonta. "U...u..uncle Zayd wallahi abun hawa na rasa sai wanine ya kawo n... Bata karasa ba ta tuna ta kuna ballowa kanta ruwa. "Wani? Zarah da Zayd suka fada a tare.......

*Autar Mama ce*
[3/16, 4:47 PM] Brother❤: ✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma k'alubalen rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
Autar Mama

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow mr on wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 37" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1200948255?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=JdPhmeSq5WLUoINnEQ%2BuYaUHvoYDGYw1XLLpkSpH8dHHwBFwEe9Zh9tf0vVx4Imnx68%2B5JcGFToffKtycnpGL2a4NdHynHiOG1mOoSZVQ5%2BPdTSg0hrwE5YX2TK4SrTJ

*Whatsapp number, free to contact me 08142904255*

*BAK'AR SAKAYYA*

*Bak'ar sakayya, labarine a kan tsantsar soyyar gaskiya wadda ta fara tun daga yarinta, ya sota tamkar ransa! Yayi fada da kowa a kanta! Yayi kokarin sadaukar da rayuwarsa saboda soyayyarta! A nata b'angaren itama ta soshi soyayya me zafi hade kuma da yarinta... Shin kunsan me yake faruwa?.... Ko yaya Yidi da Bardo zasu kasance? Ya labarin soyyarsu zai kasance? Me kuke tunani a kansu?... Hmm a wajena kawai zaku samu wannan amsoshin akan nera 300 ga masu turuwa ta banki, masu turo kati kuma 400 ne masu idan kuma Vip group ne zaki biya 500 posting sau biyu a rana*

*Hmm, ga Yazeed fa! Yaro dan gata! Amma kash! Ya kasance dolo! Sanadiyyar hakan ya,rasa me zama dashi! Baya iya yin komai da kansa! Ya tashi ba tare da uwa ba! Yayansa kadai ne sanyin idaniyansa! Hmm Yidi ta shigo rayuwar Yazeed but how? Hmm wanna amsar zaku sameta ne a,wajena kuma duk cikin littafina me taken _BAK'AR SAKAYYA_*

*Soyayya ta wahalar da Bardo! Yasha gubar so! Yasha azabar so! Yasha masifar so! Soyayyar Yidi taso hallaka rayuwarsa!*

*Kukan jaririn da ya cika wajen ne ya tsorata ta! Ajiye tulunta tayi ta karasa gefen rafin gabanta na faduwa..... Hmmm Tsintuwa! Tsintuwar yaro! A gefen rafi... Hmm zaku samu cikakken labari a wajena ni Autar Mama akan farashi me sauki kamar yadda na fada normal group 300ne posting sau daya a rana! Idan kuma katin waya zaki turo zaki bada 400, sai vip group 500 posting sau biyu a rana*

*Shafi na talatin da bakwai*

Cize lebanta tayi na k'asa tana runtsa ido alamar kash!


"Khaleel aje a kwanta ko? Cewar Zarah tana kallonsa.

"Toh Umma" Ya fad'a yana tashi ya nufi dakinsa. Tasowa Zarah tayi tana kama kunnen Ummie ta ce " Waye wani?

"Auchhh Ummana da safi fa!

"Eh ai zafin nake so kiji! Waye ya saukeki a mota?

"Uncle Zayd Dan Allah kace ta sakar min kunne!

Ummie ta fada idanunta na kawo ruwa.

"Waye ya saukeki? Ya fada yana kallonta.

"Farooq! Ta fad'a da karfi dan Zarah kara murda kunnen take. Sakin kunnen Zarah tayi cike da mamaki ta ce " waye Farooq? Bayan Taj dama kina da wani abokin ne?

"Nifa bansanshi ba kawai ya ganni a hanya ya ce min Ummie wai ina kike shine na fada masa kina lafiya toh shine fa ya kawoni gida shine ya ce ince yana gaidake"

"Shine,shine, shine! Daga gamin mutun ki shiga motarsa? Zayd ya fada yana kallonta.

Shuru Ummie tayi tana shafa kunnenta. "Shikenan gobe da kaina zan kaiki gidansu Rahama idan yaso bayan biki sai naje na daukoki da kaina kuma ban yarda kuje wani wajen a motar wani ba idan ba ta Taj ko ta driver ba!

Tsalle Zarah tayi tana dariya kafin ta dawo kusa da Zayd ta riko hannunsa ta ce " Dama nasan kafi sona ita Ummana kullum cikin fada take min"

"Ai gyara take yi so kike ta barki haka ba kwaba?

"Ummana zamuyi magana da Uncle Zayd"

Wani kallo Zarah tayi ma ta kafin tace " Me kike nufi?

"Ki bamu waje! Cewar Zayd yana dariya. Zarah bata ce komai ba tashi zuciyarta cike da farinciki, tun zuwan ummie gidan 6yrs kenan Zayd be taba nuna ma ta wani abu wanda zataji ba dadi bahasali ma yafi nuna sonta akan Khaleel da Haydar.

"Yawwa Uncle please kudi nake so! Kaga zanyi make up at least casual makeup 15k kuma gobe mother's eve zanyi, jibi fulani day zanyi sai ranar daurin aure da safe zanyi da yamma lokacin dinner ma zanyi, ko da bazaka bani duka ba ka bani abinda zaka bayar said na hakura"

"Toh Ummie kwalliyar ce har 15k? Kice so kike ki fi Rahama kyau!

Dariya tayi ta ce " Ai ita bridal makeup ne nata sai yafi cika.

"Shikenan toh zan miki transfer din 60k"
"Uncle ba alakoro? Ta fada tana kallonsa.
Sai da yayi dariya sannan ya ce " Idan an koroki kizo akwai wajen kwana dayawa a gidan nan"

Dariya tayi ta ce " Nagode uncle, gobe da wuri zan tafi"

Daga haka ta tashi ta nufi daki, bata dade da zama ba taga credit alert 65k. Murmushi tayi tana latsa kiran layin Zayd.

"Nagode sosai uncle Allah y kara lafiya da arziki"

Da amin ya amsa sannan ta katse wayar tana danna kiran Rahama.

Bugu uku ta dauka tana fad'in " Network ya hana wayar shiga tun dazu naked kira, ya kika je gida?

"Lafiya lau! Basai kin kira Ummana ba Uncle sa kansa ya ce zai kawo ni sai bayan biki zai dawo ya daukeni"

"Haba! Cewar Rahama da karfi. "Eh! Ya Taj? Be kirani ba kwata².

"Hmm nima yau ban ganshi ba! Yanzu dai zan kwanta bacci nake ji nasan anjima zai kiraki"

Da toh Ummie ta amsa sannan sukayi sallama. Wayarta ta saka a charji tana nufar toilet, bata dade a ciki ba ta fito, cikin night gown me kyau ta shirya tana saka hular bacci bayan ta nade gashinta.

Kwanciya tayi ta cire wayarta a charji ta yi dialing number mahaifinta. Bugu daya ya dauka. Murmushi tayi kadan ta ce " Abba ashe bakayi bacci ba"

Daga daya b'angaren Shehu ya ce " Yes! Ya kuke?

"Lafiya lau Abba! Ya su Aunty Sa'adah?

"Duk suna nan kalau, ina fatan komai lafiya ko?

Murmushi ta saki ta ce " Eh Abba na" "Yawwa Allah yayi miki albarka! Turo min da account number dinki kwana biyu ban turo miki kudi ba"

Cikin farin ciki ta fara karanto account details dinta, dariya Shehu yayi ya ce " Turo min ta SMS"

Da toh ta amsa tana,kashe wayar dan nanan ta tura masa,ko minti 5 ba'ayi ba credit alert na 50k ya shi go. Zaro ido tayi cike da farinciki.

Kiransa ne ya shigo wayar, da sauri ta dauka tana fad'in "Na gani nagode sosai Abba, Allah ya kara budi da lafiya, daxu ma Uncle ya ban 65k kudin make up!

"65k din duk na make up ne? Cewar Shehu cike da mamaki. "Eh mana" Ummie ta amsa tana wanshare baki.

"Ki daina damun Zayd dayawa kinji ko? Duk abinda kike so ki min magana, rikeki ma da yake kadai ya isa, ni kuma zan dauki komai naki har da bashi zan biya wanda banyi a baya ba"

Dariya Ummir tayi ta ce " Toh Abba!
"Yawwa ayi bacci! Kuma ina fatan ana karatu?

Sai data juya idanunta sanna ta ce " Sosai ma! Kwana biyu banje mkaranta ba saboda bikin Rahama"

"Toh Allah ya sanya alkhairy ya kawo na Ummie na yar black arab din yarinyata"

"Aminnn Abba" daga haka sukayi sallama ta ajiye wayar tana murmushi.

"Kwalliyar 7k zatayi sauran kudin zata ajiye su a lalitar ta! Ta fada a fili tana murmushi.

Har kusan 12na dare tana jiran kiran Taj amma shuru, kashe wayarta tayi tasaka a charji sannan ta kwanta bacci.

Washe gari karfe 8 da rabi suka tafi gidansu Rahama shi kuma Zayf ya wuce aiki.

A compound din gidan ta gano Taj yana zaune a kan table litattafai a gabansa yana dubawa. Murmushi tayi ta karasa inda yake ta ja kujera ta zauna tana fad'in " Ya naga kana ta karatu?

Dago idanunsa yayi yana kallonta kafin ya sauke su akan littafinsa ya ce " On Monday za'ayi Inorganic chem. Test"

"Tabdijan! Ni bazan ma je ba! Kayi min Dan Allah" Ta fada tana kallonsa.

"Ya za'ayi nayi submitting paper biyu? "Pls Taj" Ta fada tana narke fuskarta.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce " Ok!

"Yawwa my one and o ly friend abu na gaba shine Dan Allah kayi hakuri ka rage kibar nan taka kaji ko?

Kallon jikinsa yayi kafin ya kalli Ummie ya ce "Bazaki iya auren me kiba ba?

Dariya tayi tana fadin " A' a nafison siriri gaskiya"

Shuru yayi yana kallonta, ganin ya kafeta da idanuwansa yasa ta kawar da na ta ta ce " Na fada maka bana son wannan kallon"

Dauke idanunsa yayi daga kan fuskarta ya cigaba da karatunsa.

Ta shi tayi ta nufi cikin gida aka fara shirin mother's eve.

Mahaifiyar Rahama ce ta biya kudin Make up dinsu gaba daya! Sosai Ummie tayi kyau komai yayi dai dai da kalarta har taso fin amaryar kyau lol...

Karfe 4 aka fara taron a compound din gidan da aka kawara da decorations masu kyau da daukar hankali.

Ba'a tashi ba said magariba ansha hotuna sosai Ummie an samu abinyi da ita din gwanar son ado ce da kwalliya hotuna da vds kham baa magana.

Tun safiyar ranar bata kara ganin Taj ba.

Bayan sallar ishai ta fito neman sa dan su fita restaurant cin abinci cox babu abincin da zata iya ci a gidan duk gani take yara sun jagwalgwala.

Har tayi wanka ta sauya kaya zuwa baya ta yane kanta da mayafinta kwantaccen gashin dake goshinta ya kara fito da kyawunta.

A zaune kusa da Gate man ta hangoshi suna cin abinci.

Karasawa tayi tana fad'in " Tun dazu said nemanka nake yi! Kana nan kana ta ci ko? Shiyasa ai bazaka taba rahe kiba ba"

Ajiye cokalin hannunsa yayi yana kallonta ya ce "Menene?

Turo baki tayi kadan ta ce " Yunwa nake ji fa tunsafe rabona da abinci"

"OK! Me kike so ayi? Ya fada yana kallonta.

"Ka kaini restaurant ko kuma ka siyo ka kawo min"

"Bari na dauko mukullin mota sai muje! Tana murmushi ta amsa shi kuma ya tashi ya nufi cikin gidan.

"Tana son Taj saboda yana da kirki shi abokine na gari! Be wani girme ma ta sosai ba he's jus 22yrs and childhood friend dinta ne tun a Secondary ita ta saka masa Taj dan a cewarta *TAJUDDEEN* yayi tsayi, da farko fada ne yake hadasu saboda suna competition akan me daukar na daya. Tun da suka shiga SS1 aka hadasu banchi daya shikenan suka fara mutunci sanadiyyarsa ta san Rahama, kuma shi da rahama step brother ne da kuma step sister, mahaifiyar Rahama itace babba, Allah be bata haihuwa ba har sai da babansu Rahama ya auro mahaifiyar Taj ta haihu bayan shekaru sannan mahaifiyar Rahama ta haifeta dagana nan babu wadda ta kara haihuwa a cikinsu, yaran 'ya'yan gata ne saboda mahaifinsu akwai yaran banki ba laifi, kawancenta da Rahama ya zama kamar yanuwantaka dan babu wanda be santa ba a gidan su haka itama Rahama (Kamar dai ni da yar masu kudi lol)...Kullum cikin yi masa tsiya take sabida kibarsa ko sau daya be taba jin haushinta ba!

"Mu tafi! Taji ya fada, kallonsa tayi da sauri taga ita yake kallo washe baki tayi ta ce " Ina motar?

"Gata chan nafito da ita! Ya fada yana nuna Corolla S din daya fito da ita. Gaba ta wuce sannan ya biyota a baya. Shi ya bude ma ta ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima.

Sai da suka hau kan titi kafin ta ce "Inaso zansha ice cream. "Ba yunwa kike ji ba"

Ya fada hankalinsa a kan titi. "Ina kufin bayan naci abincin" Gyada kai kawai yayi. Restaurant din dake kusa dasu ya kaita, taci abincin sannan suka nufi wajen shan ice cream. Bata jira ma ya fito ba shiga wajen tana shakar khamshin wajen.

Kallon mutanen wajen tayi taga kowa harkar gabansa yake yi. Karasawa tayi inda masu ice cream din suke ta ce "Bani ice cream vanilla sai me banana packaging zakayi min!

Da OK ya amsa, kallon Taj tayi dake gefanta wanda be dade da isowa ba.

" zaka sha? Kai ya girgiza alamar a'a. Me packaging din ne ya miko ma ta leda, Taj ya biya amount din da aka fara musu sannan suka fito.

Mutumin da ta gani jiya ta hango yana nufowa wajen tare da wata yarinya me kama dashi!

"Wannan ga dukkan alamu yar sa ce! Ta fada tana kare wa yarinyar kallo wadda baxa ta fi 6yrs.

"Sir! Taji Taj ya fad'a yana daga hannu kuma yana kallon direction din da wancan yake....

*Autar Mama ce*
[3/16, 4:47 PM] Brother❤: ✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma k'alubalen rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
Autar Mama

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow mr on wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 38" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1201331384?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=sT%2Bywo5Mlb840hSeqD02s0OM9kx9PtDo2mc8FCcBNJpgH%2B7zcKXTX%2BeT1%2F19B5sOqo76SIHeSW9FZhdzioTB483NW%2FJuizXrWNK0TRAfIHm9UfOdltTN%2FtjknVgFK%2BAL

*Whatsapp number, free to contact me 08142904255*

*BAK'AR SAKAYYA*

*Bak'ar sakayya, labarine a kan tsantsar soyyar gaskiya wadda ta fara tun daga yarinta, ya sota tamkar ransa! Yayi fada da kowa a kanta! Yayi kokarin sadaukar da rayuwarsa saboda soyayyarta! A nata b'angaren itama ta soshi soyayya me zafi hade kuma da yarinta... Shin kunsan me yake faruwa?.... Ko yaya Yidi da Bardo zasu kasance? Ya labarin soyyarsu zai kasance? Me kuke tunani a kansu?... Hmm a wajena kawai zaku samu wannan amsoshin akan nera 300 ga masu turuwa ta banki, masu turo kati kuma 400 ne masu idan kuma Vip group ne zaki biya 500 posting sau biyu a rana*

*Hmm, ga Yazeed fa! Yaro dan gata! Amma kash! Ya kasance dolo! Sanadiyyar hakan ya,rasa me zama dashi! Baya iya yin komai da kansa! Ya tashi ba tare da uwa ba! Yayansa kadai ne sanyin idaniyansa! Hmm Yidi ta shigo rayuwar Yazeed but how? Hmm wanna amsar zaku sameta ne a,wajena kuma duk cikin littafina me taken _BAK'AR SAKAYYA_*

*Soyayya ta wahalar da Bardo! Yasha gubar so! Yasha azabar so! Yasha masifar so! Soyayyar Yidi taso hallaka rayuwarsa!*

*Kukan jaririn da ya cika wajen ne ya tsorata ta! Ajiye tulunta tayi ta karasa gefen rafin gabanta na faduwa..... Hmmm Tsintuwa! Tsintuwar yaro! A gefen rafi... Hmm zaku samu cikakken labari a wajena ni Autar Mama akan farashi me sauki kamar yadda na fada normal group 300ne posting sau daya a rana! Idan kuma katin waya zaki turo zaki bada 400, sai vip group 500 posting sau biyu a rana*

*Shafi na talatin da takwas*

Inda suke ya k'araso yana murmushi ya dan daki kafadar Taj ya ce " Babban yaro!

"Sir how far na! Cewar Take yana murmushi.

'Lafiya Tajuddeen, kazo shan sanyi ko? Dariya Taj yayi yana durkusawa ya dauki Nawal ya ce " A'a! Na kawo Ummie ne! Ya fada yana nuna direction din da Ummie take tsaye idanuwanta a kansu.

" Oh ka santa ne? Cewar Farooq yana kallonta.

Dauke idanunta tayi da sauri daga kansa dan ita bata son yawan kallo musanman ma na k'urillah.

"Yes since childhood fa! Kawar Rahama ma sosai itace best friend a bikin ma"

"Oh i see! Shine kuka fito by this hour ko?

Farooq ya fada still idanunsa akan Ummie.

"Ummie ain't rigima ce ita tace yunwa take ji, yanzu ma haka daga restaurant muke shine ta dage sai tazo tasha ice cream"

Gyada kai Farooq yayi yana dauke idanunsa daga kanta ya ce " Ok ku gaida gida nima Nawal ce ta fito dani! Bata so ubanta ba saini marainin wayonta"

Dariya Taj yayi yana sauke Nawal a k'asa ya ce " Ai tafi sabawa da kai shiyasa... Juyawa yayi ya kalleta ya ce " Ummie ki zo ku gaisa da abokin Daddy sai mu tafi"

Karasowa tayi a hankali ta ce "Abokin Daddy ina yini?

Murmushi Farooq yayi ya ce "Lafiya lau 'yar Zarah!

D'agowa tayi ta kalleshi sai kuma ta kalli Taj ta ce " Mu tafi kar ice cream din ya narke"

"Toh" Cewar Taj yana kallonta.

Sallama yayi masa sannan suka tafi yabi bayansu da kallo yana murmushi.


Sai da suka dauki hanyar komawa gida sannan ta kalli Taj ta ce " ai na dauka yar sa ce"

Girgiza kai Taj yayi ya ce " Ai sir Farooq be taba yin aure ba!

Zaro ido Ummie tayi ta ce " Haba? Ai ya kusa sa'an Uncle Zayd ko ma ya girmeshi"

"Bansan shekarun uncle Zayd ba but shi 38yrs yake, tun be kai haka ba yake son wata sanadiyyar soyayyarta wata mace yasashi haka! A shekarun baya ma kusan tabin hankaline ya sameshi amma abun beyi tsanani ba Allah ya bashi lafiya! sanadiyyar da suka hadu da Daddy na kenan saboda shi likitan kwakwalwane"

"Ikon Allah! Wannan soyayya haka? Amma matar balarabiya ce?

Cewar Ummie cike da mamakin lamarin"

"Bansani ba, amma tabbas yana sonta kuma soyayyarta ne ya hanashi aure har yanzu! A baya ma fa ya taba aure amma ranar daurin auren ya gudu ya bar amaryar"

Dariya Ummie ta saki tana fad'in " Ya gudu ya barta? Tabdijan toh ya akayi?

"Sakinta yayi bayan wajen shekara da auren"

"Ikon Allah, toh Allah ya kyauta! Ya bashi macen data dace dashi kuma ta gari"

Da amin Taj ya amsa yana kara maida hankali kan tukinsa.

Washe_ gari.

Biki ya tafi yadda ya kamata sosai abun ya k'ayatar ranar Ummie ko kwalliyar ma batayi ba saboda lokaci ya kire me make up din bata zo da wuri ba.

Sai bayan isha'i suka dawo gida, ita da Raham ne kawai a dakinsu sauran yan uwa kowanne yana dakin da aka saukesu.

Wanka Ummie ta shiga bata dade ba ta fito tana goge kanta da towel. Rahama dake kwance a kan gado ta ce " Ummie kinsan me?

"Inaji" Cewar Ummie tana zama bakin mudubi.

Ta shi zaune Rahama tayi tana kallonta ta cikin mudubi kafin ta ce " Ke wai baki lura da komai a yanayin Taj ba?

Juyowa Ummie tayi tana kallonta kafin ta ce " Me ya faru dashi?

Karamin tsaki Rahama tayi ta ce " Wallahi Ummie bakya kwashewa! Duk wannan abubuwan da Taj yake miki kin dauka abotace kawai? Abubuwan sunyi yawa! Nifa nasan sonki yake kuma nasan kema kina sonsa!

Wata dariya Ummie ta saki harda tafa hannuwa. "Tab wallahi ki sake tunani bari ma yanzu idan nayi sallah zanje wajensa nasan yana chan yana karatu kuma zan fada miki yadda mukayi bana sosna baya sona kawai abotace ba irin taki ba"

Shuru Rahama tayi tana kwabe baki maybe ko tayi misunderstanding dinsu ne.

Ummie na idar da sallah kamar yadda ta fada haka ta wuce ta nufi wajen Taj.

Bata ganshi inda tayi tunani ba. Dawowa cikin gidan tayi ta nufi dakinsa. Sau biyu tayi knocking taji ya ce " Waye?

"Taj ni ce ka fito muyi magana"

Bata dade a tsaye ba ya fito yana sanye da single da short nikka, kallonsa tayi ta ce " Me haka?

"Kwanciya zanyi shiyasa, amma ina jinki"

"OK ka saka ko jallabiya ce ka fito! Da toh ya amsa sannan ya koma daki, be wani dade ba ya fito sanye da jallabiya.

Compound din gidan ta nufa tana fad'in " Inaso nayi clearing wani doubt ne"

"OK menene? Ya fada idanusa a kanta.

Shuru tayi itama tana kallonsa azahiri shi take kallo but a bad'ini tunani take yi akan maganar Rahama tasan dai Rahama akwai sa ido da bin kwakkwafi amma ita bata ga wani abu na nuna soyayya a tattare da Taj ba! Beside ma ita a matsayin Yaya aboki ta daukeshi! Infact ma bata son auren yaro tafi son auren babba kamar 30-35yrs haka wanda zai iya yin hakuri da ita dan tasan shes so annoying, duk tasan Taj ma yana da hakuri da kawaici amma ita sam bata ma wannan tunanin a kansa, "Toh ita tana da zabi ne ma? Tana da right din zabarwa kanta miji? Ya kamata ta daina daukar kanta da wani mahimmaci! Yes tasan tana da kyau but menene amfanin kyan nata? Bayan ita din ma yanzu ba cikakkiyar budurwa bace!

Runtsa idanunta tayi tana tuno lokacin da abun ya faru! Hawaye ne suka fara bin kuncinta. "Ummie! Taji Taj ya kira sunanta.

Bud'e idanunta tayi tana saurin goge hawayenta ta ce " Shikenan kawai kaje ka kwanta!

Kallonta yayi ya ce " Ummie wani abu ne?

Kai ta girgiza alamar a'a.

Shigowar motar Daddynsa ce yasa ya kalleta ya ce " Ki tafi ciki sai d safe"

Kallon motar tayi a sanyaye sannan ta wuce ta koma ciki"

Bayan ya gama parking ya fito yana karasowa inda Taj yake yana kallonsa ya ce " Taj! Inyi irinta Ummie.

Murmushi Taj yayi yana kallosa ya ce " Sannu da zuwa Daddy"

"Yawwa! Ya gama fuskarsa wani iri? "Bakomai Daddy!

"OK me kuke cewa da Ummie? Sosa kansa yayi kafin ya ce " Maganar karatune"

Shuru Daddyn yayi yana kallonsa kusan na minti daya kafin ya ce " Ina fatan dai bayan friendship babu wata alaka ko? Kasan dai ba aure zan maka yanzu ba!

Shuru Taj yayi dan baisan me zai ce ba!

"Yawwa muje ciki ko? Da toh Taj ya amsa yana bin bayansa suka shiga gidan.

Ummie kuwa bandaki ta shiga tasha kukanta dan tasan rayuwarta ta lalace! Saleh ya cuceta wallahi!

Har sai da Rahama tayi bacci sannan ta fito.

Washe-gari.

Tun karfe 8am aka fara makeup saboda 11:30 ne daurin auren.

Cikin lace fari kal Rahama ta shirya wanda akayi wa dinkin riga da skirt dan yayi kamar dai gowm amma riga da skirt ne sai farin net me kyau da tsada wanda a kayi pinning dinshi da jikin dan kwalinta ya zauna yayi dam tayi kyau abun ba'a cewa komai.

Sai kusan 11 aka fara yi wa Ummie duk fuskarta baby annuri saboda har yanzu bata bar ahiyar zuciyar kukan da tayi ba.

Cikin atamfa ta shirya dinkin doguwar riga wanda yayi mugun yi ma ta kyau kuma kalar atamfar ta dau fatarta. Suna zaune da kawayen amarya yan bokonsu wayar Rahama ta fara kara.

Gamin sunan mijinta yasa kawayen shewa ana kiyi sauri ki dauka. Daukar wayar tayi ta saka a handsfree ta ce " Hello!

"Sweet mie an daura!

Ihu suka kasa ana fadin

Please Login or Register in order to submit comment