Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taken _BAK'AR SAKAYYA_*

*Soyayya ta wahalar da Bardo! Yasha gubar so! Yasha azabar so! Yasha masifar so! Soyayyar Yidi taso hallaka rayuwarsa!*

*Kukan jaririn da ya cika wajen ne ya tsorata ta! Ajiye tulunta tayi ta karasa gefen rafin gabanta na faduwa..... Hmmm Tsintuwa! Tsintuwar yaro! A gefen rafi... Hmm zaku samu cikakken labari a wajena ni Autar Mama akan farashi me sauki kamar yadda na fada normal group 300ne posting sau daya a rana! Idan kuma katin waya zaki turo zaki bada 400, sai vip group 500 posting sau biyu a rana*

*Shafi na talatin da biyar*

Ummie na kwance a babbar kujera a falon Aunty Zarah tayi ma ta firfita dan an dauke wutar nepa, Zayd ne ya fito daga d'aki yana kallonsu ya ce " Aunty ta ce ki kaita dakinta"

Goge hawayenta tayi tana ajiye maficin sannan ta kalli Ummie ta ce " Mamana zaki iya tashi?

Daga kai Ummie tayi alamar eh kafin ta fara kokarin mikewa, taimaka ma ta Zarah tayi sannan ta riketa tana ta gwale kafa har suka isa dakin Aunty ta kwantar da ita a kan gado, fitowa tayi ta barsu ita da Aunty, A kusa da Zayd ta zauna tan fashewa da kuka me zafi da k'una.

Kwanto da ita yayi jikinsa yana shafa ta alamar rarrashi, sai da tayi me isarta sannan tayi shuru ta fara sauke ajiyar zuciya a hankali.

Zayd ne yayi breaking silence din da cewa " Zan shigar da case insha Allah za'a nemowa Ummie hakkinta"

Girgiza kai Zarah tayi tana tashi daga kafadarsa ta ce " Bana so! Bana so duniya tasan halin da nake ciki! Kasan dai idan Yusuf ya ji wanna maganar dole zai ce dan uwansa ne zai zama me kare ta ni kuma duk abinda zaa saka 2brothers family bana sonsa saboda press zasu iya shigowa ko nan gaba Ummie ta girma za'a dinga kallonta da abunne maybe ma mijin aure ya gagareta ni dai na hakura duk wanda ya bata ma ta rayuwa zai gani insha Allah bzan taba yafe masa ba amma inaso wannan lamarin ya tsaya iya mu saboda future din 'yata bawai dan bana so a karbar ma ta hakkinta ba a'a bana so in lalata future dinta"

Ajiyar zuciya Zayd yayi yana kallonta ya ce " Hakane! Maganarki abar dubawa ce amma rashin daukar mataki shi zaisa ayi ta aikata barna!

"Hakane Zayd! amma na barshi da Allah, Allah ne zai saka min koma waye! Ummie dai bazan kara barinta ta koma wajen Shehu ba har abada, ina fatan zaka rikemin ita kamar kai ka haifeta"

Murmushi Zaud yayi kadan yana riko hannunta ya ce " Zarah! Dago jajayen idanuwanta tayi tana kallonsa. "Zarah! Ni Zayd na miki alkhawarin rike Ummie kamar 'yar dana haifa kuma ta bangarena babu wata matsala insha Allah"

Zame hannunta tayi daga cikin nashi tana kwantowa a kafadarsa zuciyarta cike da baki da radadin abinda ya samu yarta.

*5months later*

"Ummie! Ummie! Ummie! Da karfi Zarah ke kiran sunan Ummie amma bata amsa ba. Kallon Zayd tayi dake breakfast a dining ta ce " Kar dai ace yarinyar nan bata tashi ba? Yanzu fa 8 saura kuma ta ce exam din Maths ne dasu first period"

"Ki je ki duba mana" Bata ce dashi komai ba ta tashi tana nufar dakin Ummie. A kudundune ta ganta cikin bargo tana sharar bacci.

Yaye bargon tayi tana kallonta ta ce " Bana son sakarci ko wanka bakiyi ba?

Bude kyawawan idanunta tayi ta zubasu a kan mahaifiyarta cikin magagin bacci ta ce " Ni bana son zuwa makaranta fa"

"Bana son sakarci tashi! Wata nawa kikayi ba makarantar? Saboda kinji dadin zaman gida ko? Ga Uncle Zayd zai tafi aiki ki bari ya tafi baki shirya ba said dai ki tafi a kafa"

Da sauri Ummie ta tashi tana saukowa daga kan gadon. Zarah na tsaye har ta shiga toilet. Murmushi tayi kadan tana kallon kofar toilet din 2weeks kenan data fara ganin walwala a idanun Ummie itama hakan ba karamin dadi yaui ma ta ba.

Ko minti 5 Ummie batayi ba ta fito tana fad'in "Ummana kayana"

"Wannan dai ba wanka bane" Cewar Zarah tana nufar closet dinta ta zuge ta dauko ma ta uniform dinta tare da inner wears.

"Kin daiji abinda na fada miki ko? Ko da wasa ban yarda wani yasan me ya faru da ke ba idan kika kuskura kika bari ko cikin kawayenki wa ta ta sani sai na mai dake gidan babanki"

Da sauri Ummie ta girgiza kai tana fad'in " Uncle Zayd ya ce ciki ba dan abinciki kadai akayi shi ba! Bazan fadawa kowa ba insha Allah"

"Yawwa! Koma waye yayi miki hakan Allah zai saka miki" Zarah ta fada tana mika ma ta kayan.

Shuru Ummie tayi tana kallon Mamanta, tasan idan ta fada ma ta Saleh ne wata kila ciwan zuciya ne zai kama mamanta shiysa bazata fada ba Allah ya isanta tsakaninta da Saleh"

Sai kusan 8:15 sannan ta kammala shirin, tana fitowa ta kalli Zayd dake latsa waya ta ce " Uncle Zayd kai zaka rakani ka ce asibiti ka kaini check up shiysa na makara idan ba haka ba Uncle din maths bazai bari nayi exam ba"

"Karya? A ina na kaiki asibitin? A mafarki? Zayd ya fada yana kallonta. Kwabe fuska tayi tana tabe karamin bakinta ta ce " Wallahi fail zai samin idan baka fada haka ba kuma *TAJUDDEEN* Zai zo na daya"

"Shikenan naji amma bazanyi karya ba" Ya fada yana kallonta. "Wannan Tajuddeen din shine kishiyarki ko?

Zarah ta fada tana mika ma ta lunch box din ta. "Eh mana! Cewar Ummie tana kallon Ummanta.

"Toh muje kar ki kara makara"

Fita Ummie tayi tana fad'in " Tohm.

Daukar jakar aikin Zayd tayi tana kallonsa fuskarta dauke da mirmushi ta ce " Anjima zamuje allurar rigakafi"

"Toh Allah ya tsare hanya, shima yau bacci yake sha yayi gadon yayarsa"

Zayd ya fada yana dariya. "Muje toh" Cewar Zarah tana kallonsa.

Karbar jakar aikinsa yayi yana matsowa kusa da ita yayi ma ta light kiss a lips dinta ya ce " Huta a daina bawa unborn wahala! Dariya tayi tana kallonsa ta ce " Tabdijan na fada maka cike dani? Kai dai jeka kar Ummie ta kara makara"

"OK bye i love you" Ya fada yana nufar hanya fita. Addua sosai Zarah tayi masa yana amsawa har ya fita.

A kujera ta zauna ta sauke ajiyar zuciya.



A kwance yake a kan sofa yana kallon silin wayarsa akan kirjinsa.

Turo kofar dakin akayi amma be sani ba! Kusa dashi Mama ta zauna fama fad'in " Yanzu Farooq rayuwar kulle kai a daki ta zabarwa kanka? Lokaci fa ba jiranka yake ba! Sa'anninka har yara ne dasu! Tayaya zaka kwallafa rai akan abu daya? Kana ji ai tana da aure ko? Kuma tana son mijinta, haka ma mijinta yana sonta! Meyasa bazaka dauki kaddara ba? Shi fa bawa ba komai yake nema kuma ya samu ba! Kayi hakuri ka samu mace kayi aurenka! Tumda kaki zabina na baka ka yar! Gashinan dan uwanka ya aura dama shine mijinta kuma har Allah ya basu rabo daga yin auren kana nan a zaune wai anya kuwa da zuciya a kirjinka kai baka tausayin kanka?

Duk wannan suruntun da takeyi baiji ba ganin bai kulata ba ya saka ta daki kafarsa, da sauri ya kalleta yana tashi zaune ya ce " Mama!

"Eh nice! Na gaba babatu a iska ko? Toh ka fito da macen aure ni na gaji da ganinka haka! Ko aiki baka zuwa! Ka zama kamar wata mace kullum a daki"

Numfashi ya sauke yana kallonta ya ce " Just pray for me Mama" Daga haka ya ta shi ya shiga toilet.


**
Yau Yusuf zai dawo dakinta, gaba daya ta rasa me yake ma ta dadi musanman da da Mama ta ce ma ta ai Ummie ciki ne da ita! Gani takeyi yafi ma son Ummie a kanta taso daukar shawara kanwarta ta fitar da Ummie daga gidan amma bata son ta sabawa ubangiji akan abinda shi yace ayi idan zaa iya adalci kuma idan ta zauna tayi tunani tabbas itace mara kirki itace bata kula dashi har ya samu damar cewa zaiyi aure amma idan zatayi wa kanta adalci tasan irin son da mijinta yake ma ta amma tayo watsi da damarta gashi nan yaje ya auro yarinya karama kuma ta fita kula dashi dan har kiba taga Yusuf din yayi! Ajiyar zuciya ta sauke tana kufira niyya me kyau a ranta insha Allah zata samu Mama ta bata hakuri akan bad manners dinta shima haka har Ummie dan idan batayi wasa ba zata iya rasa aurenta akan mugun halinta!



Cikin damuwa Shehu ke kallon Sa'adah dake jera kayanta a kwati ya ce " Haba Sa'adah! banyi tunanin haka daga gareki ba sam! Shi arziki da talauci ai duk na Allah ne kuma ina san ran karbo hakkina daga wajen yan damfaran saboda ba kdai suka danfara ba, kiyi hakuri mu zauna nayi alkhawari baxan sake yi miki ba dai² ba!

"Ni wallahi dama aurenka ya isheni! Shekaran jiya dana je gidan Zarah kamar na hadiyeta saboda yadda take jin dadin gidan mijinta ta kara kyau da kiba! Kuma bawai kudi mijinta yafika ba ko yanzu da kayi asarara kudade masu yawa mijinta bai kaika kudi ba amma yafika sau dubu wallahi!

"Na sani kuma na miki alkhawari wallahi zan gyara zan zama the most ideal husband idan kika barni wa zan aura?

Dariya Sa'adah ta sheke da ita tana fad'in " Kaje ka auri balarabiya yar uwarka maka kai da kake da larabawa?

Bata rai yayi kadan ya ce " But ke nake so ai!

Juya ido tayi tana saka hijabi ta ce " Kaga tafiyata wallahi nayi dana sanin yaudarar kawata!

"OK ki cire cikin dake jikinki da kuma Ihsan duk ki ajiye tunda bada su kika zo ba!

Cewar Shehu dan duk ya hanata tafiya.

Tsaki tayi ta nufi hanyar fita. Ihsan na goye a bayanta tana bacci.

Da sauri ya karaso gabanta ya durkusa ya ce " Dan Allah Sa'adah kiyi hakuri"

Shuru Sa'adah tayi tana kallonsa, hade hannayensa yayi alamar roko.

"Toh nidai inaso zanje gida na kwana biyu"

Ta shi yayi yana fad'in "Toh muje ki rage kayan! Daga nan zamu biya wajen Zarah sai mu bata hakuri ita da mijinta"

Murmushi tayi kadan sannan ta ce " Toh......

*TSOKACI!*

*Toh da farko dai zaman! gidan Shehu da Zarah tayi, tabbas biyayya a aure abu ne mai kyau amma Zarah tayi zaman da zata iya ma rasa ranta da sunan biyayya wanda hakan be dace ba!* *Tabbas Zawarci ba abune mai dadi ba amma kasancewar mace bazawara ba shi zaisa ta ding kyamatar kanta ba! Zaman gidan miji dama ba tabbas ne dashi ba!* *Kuma shi aure rai ne dashi! Duk ranta ya mutu kuwa dole sai hakuri!*
*Tabbas mini me duka ba wanda za' a zauna dashi bane! Fatanmu Allah ya bamu mazaje na gari ku da kuke da auren Allah ya kara dankon kauna ya baku zaman lafiya me dorewa*

*Sai maganar Alhaji Zayd! Bincike fa abune me kyau a ko wani lamari! Karkiga/karkaga Zaud yaci bulus komai yazo masa d sauki be zama lallai a wajenka/ki ya zamana hakan ba! Sai mu kula!*

*Dan karshen Shehu da Sa'adah ya kasance haka bashine zai baka daman kayi abinda yayi ba maybe naka zaka kare a wulakance ne! Dan abinda yakeyi ko kare bazai ci ba! Allah yasa mu dace maza masu dukan matayensu Allah yasa su gyara! Kawaye masu cin amana Allah ya shiryeku! Bawai be hallata ba amma ai ba dadi cin amana! Allah yasa mu dace*

*Rashin biyayya ga iyaye illa ce babba! Kuma rayuwa ba komai kake nema ka samu ba misali Alaji Farooq,Allah ya bamu ikon cinye jabawarmu Amin*

*Ramlah ta gane gaskiya kafin lokaci ya kure ma ta wash kuwa basa yin damada sai lokaci ya kure! Kukan kurciya jawabi ne..... Allah yasa mu dace*

*Karshedai Ummie da Yusuf sun samu future me kyau, is better duk da farko Ummie auren sa tayi dan biyayya but yanzu ansamu syy a ciki*

*Sai kuma Ummien Zarah! Kaddara ta riga fata! Tabbas Zarah ta danyi sakaci amma ba yadda bawa ya iya idan hakan rubutattciyar kaddararsa ce*

*Dang Adam ajizi ne inda aka ga nayi ba dai dai ba zaku iya gyra min nagode*

*Kar kuga inata jawabi bafa gamawa nayi ba saura dai kiri an dai gama da labarinsu Zarah saura tauraruwarmu*

*6years later* *Don't confuse ur self Ummie is now 18yrs old... Lol....*

Autar Mama ce.
[3/16, 4:47 PM] Brother❤: ✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma k'alubalen rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
Autar Mama

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow mr on wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 36" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1200575398?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=f51FFVd%2FMDRLSvNuwhXRZGhQDF1OTE0YlhvS3nVmPKIp%2BhyBAjzvxufrLmHq8uwJ1jA4lTwY2zVUWHjJFCiJQz9UvzyufNWPpARmvqXCGQV4oP3XrMWvxlPIWYTZpKEF

*Whatsapp number, free to contact me 08142904255*

*BAK'AR SAKAYYA*

*Bak'ar sakayya, labarine a kan tsantsar soyyar gaskiya wadda ta fara tun daga yarinta, ya sota tamkar ransa! Yayi fada da kowa a kanta! Yayi kokarin sadaukar da rayuwarsa saboda soyayyarta! A nata b'angaren itama ta soshi soyayya me zafi hade kuma da yarinta... Shin kunsan me yake faruwa?.... Ko yaya Yidi da Bardo zasu kasance? Ya labarin soyyarsu zai kasance? Me kuke tunani a kansu?... Hmm a wajena kawai zaku samu wannan amsoshin akan nera 300 ga masu turuwa ta banki, masu turo kati kuma 400 ne masu idan kuma Vip group ne zaki biya 500 posting sau biyu a rana*

*Hmm, ga Yazeed fa! Yaro dan gata! Amma kash! Ya kasance dolo! Sanadiyyar hakan ya,rasa me zama dashi! Baya iya yin komai da kansa! Ya tashi ba tare da uwa ba! Yayansa kadai ne sanyin idaniyansa! Hmm Yidi ta shigo rayuwar Yazeed but how? Hmm wanna amsar zaku sameta ne a,wajena kuma duk cikin littafina me taken _BAK'AR SAKAYYA_*

*Soyayya ta wahalar da Bardo! Yasha gubar so! Yasha azabar so! Yasha masifar so! Soyayyar Yidi taso hallaka rayuwarsa!*

*Kukan jaririn da ya cika wajen ne ya tsorata ta! Ajiye tulunta tayi ta karasa gefen rafin gabanta na faduwa..... Hmmm Tsintuwa! Tsintuwar yaro! A gefen rafi... Hmm zaku samu cikakken labari a wajena ni Autar Mama akan farashi me sauki kamar yadda na fada normal group 300ne posting sau daya a rana! Idan kuma katin waya zaki turo zaki bada 400, sai vip group 500 posting sau biyu a rana*

*Shafi na talatin da shida*

12pm.

Tana sanye da atamfa wadda akayi wa dinkin doguwar riga me kyau ya yafa mayafinta medium ta rataye jakarta a hannu tana latsa wayarta.

Sakkowar Ummanta ne daga stairs ya saka ta kalli direction din da manya idanunta masu brown eyeballs.

"Har kin shirya?

"Eh Ummana! Ta ce zan rakata saloon shiyasa"

"OK! Ki dawo da wuri kinsan yanayin garin na damuna, ga wannan kema a wanke kiki kan na gaji da ganinsa a haka"

Karbar kudin da Ummanta ta mik'o ma ta yi tana dariya a zuciyarta kuwa ba wani wankin kai da zatayi zata saka a lalitarta ne idan yaso ta dawo gida ko da daddare ne ta wanke tayi stretching din abunta.

"Wannan murmushin fa?

Da sauri ta daina tana fad'in " Bakomai amma Ummana dubu uku fa!

"Eh dubu ukun in ce wankewa kawai za'ayi?

Turo baki kadan tayi tana kallonta ta ce " Kudin mota fa?

"Abbanku ya baki tun safe ko kin dauka bangani ba? Wai *UMMIE* ina zaki kai san kudi ne?

"Na tafi nidai" Ta fada tana yin gaba. "Toh Allah ya tsare" Cewar *ZARAH* tana murmushi.

Da amin Ummie ta amsa tana ficewa daga gidan.

Sai da ta fita daga quarters dinsu sannan ta samu napep.

Tafi ce me dan tsayi tsakanin gidansu da inda zata je. A wani gida me kyau suka tsaya, fitowa tayi tana kallon me napep din ta ce " Nawa zan baka?

"350 new Hajiya" Ya fada yana kallon cute face dinta. "200 ce dani gaskiya! Daga nan zuwa nan shine zan baka 350? Haba Malam?

Murmushi yayi yana kallonta ya ce " Haka yake kudin 400 ne ma na rage mini kinsan yadda ake fama da komai na kasar nan yayi tsada"

"Eh nasani amma 200 zan baka"
Girgiza kai yayi yana fadin " Hajiya kawai ki sallameni 350"

Dari biyar ta zaro a jakarta tan kallonsa ta ce "Ban dari uku! "Hajiya dari 350 ne fa kudinki" Me napep din ya fada yana fitowa.

"Toh dauki 250 idan baza dauka ba gaskiya sai dai ka barmin kudin motar!

"Toh kawo! Ya fada yana kallonta. "A'a fara bani 250din sai na baka dari biyar din"

Cewar Ummie tana tsareshi da manyan idanunta.

Girgiza kai yayi ya dauko 250 ya bata sannan ta bashi 500 din hannunta ta juya ta shiga gidan.

Compound ne babba me dauke da abubuwan ban sha'awa, karasawa tayi zuwa wani kofa tana danna door bell.

Ko minti daya batayi ba aka zo aka bude, tsalle tayi ta chafeta tana fad'in " Na dauka baxaki zo ba ke da mukayi karfe 10 na safe"

"Gani nan dai nazo! Kinshirya dai ko? Ummie ta fada tana kallon budurwar wadda itama bazata wuce sa'ar Ummie ba.

" Eh! Mu shiga ki gaida su Hajiya sai mu tafi tun dazu driver ya dawo daga kai Taj makaranta yana ta jiranmu"

"OK" Shigowa cikin falon sukayi, ba kowa sai TV dake aiki.

"Ina zuwa! Daga haka budurwar ta wuce up stairs.

Ummie na zaune ta sakko ta ce " Taso muje!

Da toh Ummie ta amsa tana fad'in " Nan da jwana uku yarinya!

Dariya tayi ta ce " Kema ai kinsa wasa!

"Ke Rahama? Ni din? Toh waye yace miki ina da manema? Kefa bari kiji duk yawancin sanarin nan saboda kyauna kawai suke tare da ni! Dana gane haka shiyasa duk nayi waje road dasu!

"Uhm but akwai wanda ke sonki tsakani da Allah!

"Ke dallah kyalesu! Nidai fatana Allah ya bani na gari"

Da Amin Rahama ta amsa sannan suka nufi wani daki.

Manyan mata ne su biyu a zaune suna hira! Har kasa Ummie ta durkusa ta gaidasu, cikin fara'a dukanninsu suka amsa.

"Aunty ki bani kudin" Cewar Rahama tana kallon dayar matar.

"Toh, Hajiya kawo ajiyar dana baki" Wadda aka kira da Aunty ta kalli dayar matar dake kama da rahama da alamu itace mahaifiyarta.

"A'a nifa bansan da zancen kudi ba! Dariya Rahama tayi tana daukar purse dinta ta ciro ATM ta ce " Aunty me kike so!

Cewar Rahama tana dariya. "Dubu 7na yarda ki cira 3k kuma ladan ajiya"

"Hajiya kudin kunshin fa kinsan fa ni da Ummie ne!

"Toh kar dai ayi min barna! Ku tafi karku kai yamma sabida yanayin damuna"

Da toh suka amsa sannan suka fito iyayen nayi musu addu'a.

Hijabi da nikaf Rahama ta saka tana fad'in "Yau yan uwan Aunty da Hajiya zasu fara zuwa, why not kicewa Umna zaki dawo nan zuwa bayan biki sai ki tafi nasan bazata hanaki ba yafi kullum ki dinga zirga².

" Uncle Zayd nefa matsalar! Bazai yarda ba!

"Awwwwn! Nifa son uncle Zayd dinnan nake! Dama zeyi wuf dani" Rahama ta fada tana dariya.

"Lallai kina so Ummana tati kuli-kulin kubrah dake!

Dariya Rahama tayi ta ce " Aikuwa, fatana Allah ya bamu mijin da zai somu kamar haka! Kina ganin fa yadda yake wa Umma wallahi abun birgeni yake yi!

"Kedai bari a bun nima yana birgeni wani lokacin har kunya Uncle dina yake ban yasin"

Dariya Rahama tayi suna shiga back seat a tare.

"Allah ya kara musu zaman lafiya da kaunar junansu"

Da Amin Ummie ta amsa dan tana jin dadi idan Rahama tayi wa iyayenta wannan add'ar.

Rage murya Rahama tayi tana fad'in " Ke kinsan me?

Girgiza kai Ummie tayi tana kallonta ta ce " Inaji"

"Ance a daren farkon mace ana ganin jini shine yake da tabbacin macen bata taba saduwa da namiji ba! Ni wallahi duk tsoro ya kamani duk da nasan ban taba saduwa da wani ba amma ina tsoro idan jinin bai fito ba fa? Shuru Ummie tayi zuciyarta na wani irin bugawa da karfin gaske,sosai kanta ya dau charji! Abinda ya faru da ita 6yrs back ya dawo kanta! "Ta yaya zata iya yafewa Saleh? Ya lalata ma ta rayuwa? Yanzu me makomarta? Duk namijin daya aureta sai ya gane ita din ba budurwa bace!

"Ummieeee! Rahama ta kira sunanta "Kukan me kike? Cewar Rahama tana kallon hawayen da suke kuncin Ummie.

Da sauri ta goge hawayen tana fad'in "Bakomai!

Daga haka ta kife kanta ta fara rera kuka.

Cike da mamaki Rahama ta ce " Ummie wai lafiya?

Shuru Ummie tayi har suka isa inda zasu je Ummie bata kara yin magana ba"

Tabbas Saleh yaji mata ciwan da bazai taba warkewa ba! Ya goga ma ta tabon da bazai taba goguwa ba! Bayan haka ya darsa ma ta mugun tsoro a zuciyarta tun bayan faruwar abun abu kadan ne yake gigitata!

"Ummie Dan Allah ko fad'a min menene?

"Karki yarda ko da wasa wata wai da sunan kawa tasan tarihinki! Ki bata iya abinda zaki iya amma banda fyaden da akayi miki! Wannan sirrinki ne Ummie! Idan kika yarda wata ko wani ya sani Allah ya isa"

Ta tuno maganganun Ummanta.

"Bakomai Rahama" Daga haka ta shiga saloon din. Badan Rahama ta yarda ba ta bi bayanta.

Anyi musu gyara gashi sunyi kyau musanman ma Ummie da gashinta yake me kyau chan dama hadin arab da fulani.

Jan lalle akayi musu sai Rahama da a akayi wa baki banda Ummie dan bata so cewarta wait baking kunshi na fararene.

Sai bayan magarib aka gama.

Suna fitowa Ummie ta kalli Rahama ta ce " Sis ku tafi gida ni zan hau napep daga nan"

"A'a kizo mu kaiki!
"No Ku tafi yanzu zan tsari mota"

"Toh Ummie nagode zan kira Umma na fad'a ma ta gobe idan zaki zo ki taho da kayanki na fitar bikin"

"OK toh" Daga haka Ummie ta nufi bakin titi ita kuma Rahama suka wuce. Ta tsayar dame napep uku amma duka bazasuje ba.


Tafiya ta fara you tana yi tana tsayar da napep amma bazasu je inda zata je. Iska aka fara yi me dadi! Dama tun suna Saloon hadari ya fara hadowa ganin ya baje kafin su fito yasa hankalinta ya kwanta amma yanzu kham da alama hadewa yake karayi.

Wani napep ta kuma tsara tana fadin " AGK quarters? "Nawa zaki biya ya fada yana kallonta.

"300" Cewar Ummie tana kallonsa, kai ya girgiza be jira ta kara Magana ba yaja mashinsa dinsa ya tafi.

"Dan kut****** dubu nawa da kake so na baka? Aikin banza!


Fitar motar data dallarota ne ya sakata kare fuskarta tana fad'in " Wannan ai rashin adalci ne! Saboda kana da mota ka ganni a kasa?

Gani tayi an rage hasken fitilar, tsaki tayi tana sauke hannunta ta kalli motor me kyau da ita. "Aikin banza! Ta fada tana fara tafiya. Fitowa yayi daga motar, yana kallonta! Saurayine wanda bazai wuce 21yrs ba.

"Hiey! Ya fada da dan karfi. Juyowa tayi ta nuna kanta alamar ni?

"Yes! Ya fada yana kallonta.

Kallon ko ina tayi taga ba kowa,da sauri ta juya ta cigaba da tafiya kamar zata fenna a guje.

" Follow her! Sautin murya ya fito daga cikin motar. Shiga motar saurayin yayi yana takawa yabi bayan Ummie da zuwa yanzu ta fara gudu"

Wani wawan reverse yayi yana fakawa a gabanta.

Ihu ta kwalla me kara, cike sa mamaki saurayin ya kalli dayan mutumin dake gefensa ya ce " Yarinyar nan bata da hankali!


Murmushi yayi ya bude motar ya fito yana kallonta. Gaba daya ta rude, karasawa yayi kusa da ita ya ce " Ummie!

A hankali ta dago tana kallonsa. Tsira masa idanu tayi dan his face look so familiar!

Daga sama har kasa ya kalleta sosai kafin yayi murmushi a zuciyarsa ya xe " So Zarah ta ajiye yarinya kamar wannan? And shi yana nan 38yrs ko aure be taba yi ba all because of her!

"Hiey kamar na sanka! Ta fada

Please Login or Register in order to submit comment