Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ta amsa ba. Murmushi yayi a fili ya ce " Komai ya kusa zuwa karshe Ramlah!
"Karshenta kace aure zaka kara ko? Toh kayi mu gani"

"Shikenan ko fara shirin zama da kishiya dan nan da wata biyu zuwa uku zanyi aure insha Allah"

Da sauri ta kalleshi, sai kuma ta fashe da dariya ta ce " Yusuf kenan! Ni dinnan! Ni kadai ce matarka wallahi! Baka isa ba! Idan kaga kayi aure toh sai dai mutuwa nayi"

Daga haka ta fice ta barshi a dakin yana murmushi.

A unguwarsu Ummie yayi sallar magariba. Yana idarwa ya nufi gidansu. A kofar gidan ya tsaya ya fara knocking.

"Waye? Yaji muryar Ummie. "Yusuf! Ya fada atakaice. Kusan 10s sannan ta bude tana kallonsa. Shigowa yayi yana fad'in " Aunty fa?

"Ta je gidan barka dazu har yanzu dai bata dawo ba amma anjima kadan zaka ganta nasan ta tsaya a yi magariba ne sannan ta taho"

"OK" Ya fada yana yin gaba. A kujera ya zauna sannan Ummie ta shigo tana fad'in "Bari nayi sallah"

Daki ta shiga ta dan jima sannan ta fito ta nufi kitchen ta kawo masa ruwa da lemo ta na zama dan nesa dashi ta ce " Ina yini?

"Lafiya lau Ummie ya makaranta?

"Alhmdll munyi ma hutun 2nd semester"

"OK Allah ya bada sa'a" Da amin ta masa tana dauke ka ta daga kallonsa.

"Yanzu an girma an dena jin tsoro a tafi an barki ke kadai" Ya sake fada hankalinsa a kan wayarsa.

Murmushi kawai Ummie tayi tana kallon TV.

"Zaki iya auren me mata da d'a?

Taji ya jefo ma ta tambayar bazata. Zuciyarta tace ta buga kadan bakinta na dan rawa ta ce " N..n..nidai kawai ina addua Allah ya bani na gari wanda zai soni tsakani da Allah kuma ya kula da ni"

"Masha Allah hakan abune me kyau! Ummie! Ya karashe maganar yana kiran sunanta. Kallonsa tayi ba tare da amsa ba. Ajiye wayarsa yayi yana maida hankalinsa gareta ya ce " Zaki iya aurena?

"Kai kuma? Ta fada cike da mamaki. "Eh Ummie! Ni, ko na miki tsufa?

Kai ta girgiza alamar a'a kafin ta dora da cewa " Nasan zaka aureni ne dan ka gyara kuskuren da Yaya Farooq yayi zaka aureni ni dan ka gyara duk abinda ya bata! Ni kuma bana son irin wannan auren! Nafiso na auri wanda yake sona"

" Ni nace miki bana sonki ne?

Ya fad'a yana kallonta.

"A'a amma nasan dalilin da yasa kake son aurena kuma ni bazan iya kishi da Aunty Ramlah ba!

Kafin ya kara wata maganar Aunty karama ta shigo bakinta dauke da sallama.

"Wai Allah ne ya taimakeni hadari ya hado lokaci daya nasha wuya kafin na samu napep! Ummie bani ruwa"

Ta karashe maganar tama cire hijabin jikinta.

Sai a lokacin ta kira da Yusuf sake zaune. "Au! Ashe kana nan! Toh Adda ta turo ka ne ko yaya?

Murmushi yayi yana fadin " Sannu da zuwa, ina yini?

Zama tayi tana amsawa, ruwan da aka kawo masa ta dauka ta tsiyaya ta sha tana fad'in " Ya addah?

"Tana nan cikin damuwa wallahi" "Ai shikenan ni ai na dena fushin da ita amma banda Farooq tunda bai da mutunci!

"Hakane kiyi hakuri Aunty karama insha Allah zai gane kuskuransa" "Ai dole ma wallahi! Ummie ko ba kanwarsa bace ai be kamata yayi ma ta haka ba ballanata sun hada jini! Ni har kunyar mutane nake wallahi! Bana so asan sako min ya yayi wallahi!

Aunty ta karashe maganar cikin takaici. Murmushi Yusuf yayi yana dan kallon Ummie kafin ya ce " Bamu waje" Tashi tayi ta koma daki jikinta duk a sanyaye.



"Wai yau babu aiki ne Zaydu? Aunty ta fada tana kallonsa. Gyara wuyan rigarsa yayi yana kallon TV ya ce " Akwai bazan je ba ne Aunty Yusf yace na huta na kwana biyu"

"Toh, sai ka raka Zarah ta ce zata ce gyaran gashi kuma zata biya gidan Zainab"

"A'a! Ni na gama shiryawa tafiya zanyi" Ceqar Zarah tana fitowa daga daki hannunta rike da mayafi.

Ajiye jakarta tayi sannan ta yafa mayafin tana dora jakar a kafadarta bayan ta kara gyara goyanta.

"Wai mayafi zaki saka? Zayd ya fada yana kallonta. "Gashi ka gani" Ta fada tana dauke kanta faga gareshi. "Ai mayafin babbane!

Cewar Aunty tana kallon Zarah. "Ni ba ina damuwa bane da ita ta fita babu mayafin ma amma ta ajiye min yarona kar rana ta dafar dashi"

Zaro ido Zarah tayi tana kallonsa cike da mamaki. "Eh ki fita ba mayafi amma Indai da khaleel zaki fita sai kin saka hijabi.

Kwafa Zarah tayi tana cire mayafin da jakar ta kwanto khaleel dake bacci ta ajiyeshi a cinyar Zayd ya gyara rigarta sannan ya yafa mayafin ta rataye jakar ta ce " Aunty na tafi"

Daga haka ta nufi hanyar fita.

"Zarah! Zarah! Zarah! Ya kira sunata da karfi amma ko juyowa batayi ba. Murmushi Aunty tayi dan tasan ba tafiya zatayi ba tunda har zataje gidan Zainab to ba yanzu zata dawo ba kuma bazata bar Khaleel a gida ba"

Mik'awa Aunty Khaleel yayi yana tashi tsaye, sosai kafafunsa suka fara rawar kerawa, baki bude Aunty take kallonsa kafin ta kira Zarah da karfi. Jin yadda Aunty ta kirata ya saka ta dawo da sauri.

Zayd ta gani a tsaye amma kafafun na rawa sosai. Kasa motsi tayi ta kame tana kallonsa tana ji kamar mafarkin data saba yi ne.

Da kyar ya koma ya zauna kafafunsa na yi masa wani iri. Hawayene suka fara biyo kuncin Zarah hawayen da ake kira da tears of joy. Karasowa tayi tana kallonsa.

"Yaushe ka fara tashi? Ta fada tana rike damtsen hannunsa. Idanu ya tsira ma ta yana kallon cikin idanuwanta wad'anda ke cike da farinciki.

"Kusan sati biyu kenan da idan na tashi faduwa nake but yanzu akwai improvement sosai, doctor yace tu da kafafun basu sirance ba zan dawo dai dai insha Allah"

Zayd ya fada yana kallonsu. Rungumeshi Zarah tayi tana fashewa da kuka dan tana yawan mafarkin wannan ranar.

Lumshe idanunsa yayi yana dan shafa bayanta a hankali. Kusan 1min tana rungume dashi kafin hankalinta ya dawo jikinta. Da sauri ta matsa tana goge hawayen idanunta.

"Ni rashin kunyar nan ta isheni! Kafin ku janyo min abin magana gwanda amaida auren nan, zan kira kan in mahaifan ku jibi lahadi azo a mayar da auren nan gaba bansan me zan gani ba"

Aunty ta fada tana tashi ta saka khaleel a kafada ta nufi daki.

Riko hannun Zarah yayi ganin tana son tashi. "Kin yarda? Kai ta gyada alamar eh. Murmushi yayi ya ce " Allah ya tabbatar mana da alkhairy!

Amin ta fada tana kwace hannunta ta gyara mayafinta ta jakarta ta nufi daki.

Bata dade ba ta fito sanye da hijabi da bayanta goye da khaleel.

"Sai dai ki tuka kanki dan nace driver yaje gida hutun 2days"

"Ba marsala zan hau napep kawai"

"OK toh sai kin dawo ki kula" "Insha Allah ta fada tana fita.

Bata dade a saloon ba saboda ba layi, karfe 3 saura ta je gidan Zainba. Sosai suka sha hira nan take shida ma ta ramar lahadi zaa mayar da auren, dan dole Zainab ta tilasta ma ta suka je gidan kunshi iya ja akayi ma ta me kyau. Dan abun gyara Zainab ta ba ta sannan ta bata wasu kaya data di ka musu ita da Ummie ta ce ta ajiye idan Ummie tazo ta bata.

Sosai kayan sukayi kyau tunda yanzu magariba tayi kuma basu da wani nisa sosai zata biya ta kaiwa Ummie kawai idan Shehu ya yarda ma zata taho da ita dan ta dade bata ganta ba.

Sai da tayi sallar magariba sannan ta bar gidan Zainab. Said data biya super market ta siyowa Ummie da Ihsan abubuwan kwadayi sannan ta nufi gidan Shehu.

Tasan Ummie zata ji dadi idan taga kayan dan yarinyar tana son ado sosai.....

Knockin din gate din gidan tayi, me gadi ne ya leko yana fadin " Waye? Ganin Zarah ya sashi fadada murmushinsa. Hade fuska tayi dan ba wani zaman dadi sukayi da me gadin ba, gaida ita yayi ta amsa tana wucewa cikin gidan....

*magane pls kiyi hkr dani two days dinnan insha Allah kafin ramadan zan gama insha Allah*

Autar Mama ce
[3/16, 4:47 PM] Brother❤: ✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma k'alubalen rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
Autar Mama

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow mr on wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 34" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1199411815?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=BNv4QvqeVlFq%2BXa1cLZ3%2FgtWAXlIf5yUSz05bDANUxAj%2FkcpCkmhKbmxGp92O4dBr1Bh%2FIqzS2qj9vwzmub9cxFTSH9vR2RVjjFYmBWl446Rkj5Mju7jfE2SzWxOp6vv

*Whatsapp number, free to contact me 08142904255*

*BAK'AR SAKAYYA*

*Bak'ar sakayya, labarine a kan tsantsar soyyar gaskiya wadda ta fara tun daga yarinta, ya sota tamkar ransa! Yayi fada da kowa a kanta! Yayi kokarin sadaukar da rayuwarsa saboda soyayyarta! A nata b'angaren itama ta soshi soyayya me zafi hade kuma da yarinta... Shin kunsan me yake faruwa?.... Ko yaya Yidi da Bardo zasu kasance? Ya labarin soyyarsu zai kasance? Me kuke tunani a kansu?... Hmm a wajena kawai zaku samu wannan amsoshin akan nera 300 ga masu turuwa ta banki, masu turo kati kuma 400 ne masu idan kuma Vip group ne zaki biya 500 posting sau biyu a rana*

*Hmm, ga Yazeed fa! Yaro dan gata! Amma kash! Ya kasance dolo! Sanadiyyar hakan ya,rasa me zama dashi! Baya iya yin komai da kansa! Ya tashi ba tare da uwa ba! Yayansa kadai ne sanyin idaniyansa! Hmm Yidi ta shigo rayuwar Yazeed but how? Hmm wanna amsar zaku sameta ne a,wajena kuma duk cikin littafina me taken _BAK'AR SAKAYYA_*

*Soyayya ta wahalar da Bardo! Yasha gubar so! Yasha azabar so! Yasha masifar so! Soyayyar Yidi taso hallaka rayuwarsa!*

*Kukan jaririn da ya cika wajen ne ya tsorata ta! Ajiye tulunta tayi ta karasa gefen rafin gabanta na faduwa..... Hmmm Tsintuwa! Tsintuwar yaro! A gefen rafi... Hmm zaku samu cikakken labari a wajena ni Autar Mama akan farashi me sauki kamar yadda na fada normal group 300ne posting sau daya a rana! Idan kuma katin waya zaki turo zaki bada 400, sai vip group 500 posting sau biyu a rana*

*Shafi na talatin da hudu*

A kofar falon ta tsaya tana gyara Khaleel dake mutsu² zai fara rigima.

Tana shirin kwankwasa kofar Shehu ya bude yana shafa fuskarsa dake cike da damiwa.

Mutuwar tsaye yayi yana kallonta, sosai kirjinsa yayi wani mummunan bugu. Bake-bake yayi a jikin kofar yana fad'in " K..Ke ce da daddaren nan?

Kallonsa take yi ganin sa duk a birkice. "Zan wuce nazo ganin Ummie" Ta fada tana kallonsa.

"Ummie tayi bacci zaki iya tafiya"

Sosai take ganin wani bakon lamari a tattare da Shehu ya wani susuce duk ya birkice kamar mara gaskiya.

"OK ga wannan ka bata" Ta fada tana mika masa kayan hannunta. Karba yayi ita kuma ta juya ta tafi zuciyarta cike da tunani kala².

Tana fitowa bakin gate din ta fara tafiya zuciyarta na darsa ma ta wani abu! Tun da take da Shehu be taba hanata shiga gidansa ba ko bayan rabuwarsu amma yanzu ta karanci wani yanayi daban a gareshi ko dai Ummie bata da lafiya? Ta fada a fili. Tsayawa tayi da tafiyar tana tunani.

Ko minti daya bata kara ba ta juya ta koma gidan,ko knocking fin kofar falon batayi ba ta shiga, da sauri Shehu ya mike tsaye yana kallonta.

"Ina Ummie? Sa'adah ce ta fito daga daki hannunta rike da bowl tana fadin " Taki cin abincin bansan yadda zanyi b.. Bata karasa zancen ba sakamakon ganin Zarah da tayi.

"Ina Ummie? Zarah ta sake fada tana kallonsu.

" Yaya Ummiy bacha da yafiya" Cewar Ihsan dake kallon Zarah.

Sosai hankalin Sa'adah dana Shehu ya tashi,kafin suyi uttering wani word sin Zarah ta nufi dakin da Sa'adah ta fito da sauri.

A kwance taga Ummie duk ta rame sai uban hanci da idanuwa da baki kallon drip din da aka da mata tayi da sauri ta karasa hawaye na zubo ma ta.

A hankali Ummie ta juyo jin shigowar mutun, ganin fuskar Ummanta ya saka ta saka kuka tana fad'in " Ummana kicewa ciwan nan ya tafi Ummana bana so na mutu! Ummana inaso na girma na rama miki dukan da Abba yake miki, Ummana inaso na girma na zama likita Ummana inaso na temaki mutane marasa abinci da wajen kwana Ummana kicewa ciwan nan ya tafi" Ta karashe maganat hawaye masu zafi na biyowa kuncinta kana ganin yadda take magana kasan tana cikin tsananin ciwo.

Karasawa jikin gadon tayi tana zama gefen gadon ta rike hannunta wanda ba'a sa ruwan ba, "Ummie tun yaushe kike rashin lafiya amma baki ce Abba ya kawoki wajena ba? Me yake damunki?

"Zazzabi ne kawai da typhoid" cewar Sa'adah tana kallonsu. "Sannan nan dina yana ciwo" Ummie ta fada tana nuna kasanta, "Kuma Yaya Saleh n... Kafin ta karasa Sa'adah tayi caraf ta ce " Kuma Saleh ne yake kaita allura"

Shuru Ummie tayi ganin yadda Shehu ke yi ma ta wani kallo, ita dai tasan karya Aunty Sa'adah tayi kuma suna fita zata fadawa Ummanta gaskiyar abinda ya faru ai taji Sa'adah ta ce fyade Saleh yayi ma ta kuma bazata taba yafe masa ba.

Rungumeta Zarah tayi zuciyarta na zafi. "Dare nayi yanzu kar a nemi a gida" Cewar Shehu yana kallonta.

"Babu me nema na,bazan tafi na bar Ummie ba zan kwana a nan if not zan dauki yarinyata mu tafi idan taji sauki sai na dawo da ita"

"What? Baki da hankali ne? Toh ba'a gidana ba wallahi da wani masifa kike so naji? Dana ummie ko kuma da zamanki da zai dinga raunata min zuciya ko kuma da asarorin da naked fama dasu na dukiyata? Baki isa ba wallahi! Tafiya zakiyi! Shehu ya fada ransa a bace.

Ta shi tayi tana kallonsa ranta a bace ta ce "Nima bason zama nake a inda kake ba Shehu! Sabida yarinta kawai zan zauna ai nima inada gida ba'a bola nake ba"

Ze kara wata maganar Sa'adah taja hannunsa tana fad'in "Muje"

Ransa abace yabi bayanta. Muryarta chan kasa ta ce " Wai meyasa baka da saiti ne? Kai da zaka lallabata ta tafi shine kake ihu?

Dogon tsaki yaja yana barinta a wajen ya wuce dakinsa. Da sauri ta koma wajensu tana fad'in " Ai Ummie kamar 'ya take a wajena Zarah! Da kin tafi ni ai ne kula da itane"

Ajiyar zuciya Zarah ta sauke tana tashi tsaye ta ce " Gobe zan dawo gwanda a komar da ita asibiti"

Cikin tsananin farinciki Sa'adah ta ce " Shikenan muje na taka miki" ......




Tun ranar da Yusuf ya bar gidan ta kasa gane kan Aunty ko me ya fad'a mata oho! Wannan wani irin abu ne! Ta auri kani ba soyayya kuma ta sake auren yaya ba soyayya? Duk da Yusuf da Farooq halinsu ya banbanta amma ita kham zuciyarta batayi na'am da auren ba kuma ita tsoran matarsa take ji duk da Aunty ta ce gidanta daban.

"Ke Ummie! Tunanin kuma fa? Ga maganin sanyi chan na ajiye miki tun safe har yanzu baki sha ba ko? Toh karki mayar da hankali ki shanye ga wani ma Hadiza ta aiko dashi tafiyayye daga chadi ba dadi ne dashi ba haka kuma zaki shanye shi kafin ki fara shan tsumin mu na fulani! Danni yanzu nake jin zakiyi aure! Tun farko bansa inda kaina yayi ba da banyi tunanin hada ki da Yusuf ba yaro kamar ba dan uwan Farooq ba!

"Aunty nifa bana sonsa! Cewar Ummie tana kumbura fuska. "Eh ni kuma ina sonsa ubanki ma yana sonsa kuma dole ki aureshi ki dauki auren nan a matsayin auren biyayya kinji ko?

Hawayene suka fara biyo kuncinta zuciyarta ba dadi. A dan fusace ta tashi ta shiga daki. Bata dade da zama ba kiransa ya shigo wayarta ranta a bace ta dauka ta na fad'in " Kazo ka fadawa Aunty ka fasa danni bana sonka bazan iya kishi da wannan matar taka ba gaskiya!

"Auuuccchhhh ya fad'a yana karawa da shhhhh, kinji yadda maganar ta soki zuciyata kuwa UMMIE? Kinsan 2weeks ma yayi min tsaho? Ji nake kamar nazo na cewa Baffah a mayar dashi gobe... Cikin takaici ta kashe wayar zuciyarta ba dadi a nan dakin taci kukanta har ta gaji bacci ya dauketa.



Kayan da Mama ta siyowa Ummie wanda zata saka ranar daurin aure ta zubesu a falo tana kara kalla, kala uku ne sai gold necklace guda daya dayan kuma silver sai takalma da purse.

Farooq ne yake sakkowa daga stairs yana latsa wayarsa, kallon² sukayi da Mama kafin ta dauke kanta daga gareshi, kallon kayan yayi ya ce " Mama business kika fara ne?

"A'A kayan Ex wife dinka ne ko kuma ince sister in law to be dinka"

Cike da rashin fahimta ya ce " Sister in law to be? Ramlah ma dake kitchen kunnenta na kansu.

"Eh mana! Karka ce min Yusuf be fada maka ba? Toh idan be fada maka ba ni bari na fada maka! Yusuf dai yayanka! Zai auri Ummie! Ummie dai matarka daka saka, ka watsa min kasa a ido shi ya goge min"

"What!? Ummie? Haha Mama! Ummie fa? Ya zaayi na aureta na saketa kuma ya aureta? Farooq ya fada yana kallon Mama.

" Eh! Nace Eh! Ko haram ne? Ai kai kaga baka so shi kuma tayi masa! Kaje ka nemo zabinka sai na aura maka tunda ni ban iya zabe ba".

Farooq be kara cewa komai ba ya fice, Ramlah dake kitchen kuwa ta ciji baki tare da kudurin abinda zatayi da shegia Ummie! Tunda ta zabi aurar mata miji dama a kanta Yusuf yake ta wannan rawar kafar?.....



Tun karfe 12 na rana Zarah ta fits Aunty ce kawai ta san Ummie ba lafiya dan jiya basu yi magana da Zayd ba kuma yau da wuri ya fita.

Tafi minti goma tana knocking gate din gidan Shehu kafin gate man ya bude kofar kadan yana kallonta ya ce " Ba kowaa gidan"

Cike da mamaki ta ce " Kamarya ba kowa? "Eh sun fita tun dazu"

Shuru Zarah tayi kafin ta dauko wayarta a jaka tayi dialing idn number Shehu, bata shiga kwata², cike da takaici ta juya tana tunanin me yasa zai ma ta haka bayan ta fadawa Sa'adah zata zo?

Jikinta duk a sanyaye ta nufi gida, dan cutar Ummie ta firgitata yadda ta rame sosai.

A kasalance Aunty ta ganta ta shigo, "Lafiya dai? Ya jikin Ummie?

Ajiye jakarta tayi tama cire hijabin jikinta ta sakko da Khaleel dake goye a bayanta, gwiwa a sanyaye ta ce " Wai basa nan! Na kira wayarsa ma bata shiga"

"Ba mamaki sun tafi asbiti anjima idan Zaydun ya dawo sai ya kaiku zuwa lokacin sun dawo"

Da toh kawai Zarah ta amsa dan a jikinta tana jin something is really fishy.

Karfe 8 saufa Zayd ya dawo gida a gajiye,Zarah ce kawai a falo ta zuba uban tagumi. Gyaran murya yayi har sau biyu amma bata ji ba. Kusa da ita ya karaso yana fad'in " Zarah! Da sauri ta kalleshi ta ce " Na'am! Tana sauke ajiyar zuciyar.

" Lafiya dai? Tunanin me kike yi haka? "Ummie ce ba lafiya kuma tun safe nake kiran number Shehu bata shiga,jiya naje gidan da daddare yau ma na koma amma basa nan kuma layinsa baya shiga"

"Toh, bari nayi wanka inzo muje, sannan gobe karfe 2n rana za'a daura auren mu zuwa jibi sai mu koma gidanmu tare da Ummie idan ta kara jin sauki sai ta koma gida"

"Toh Allah ya kaimu ya bamu zaman lafiya" Da Amin ya amsa yana murmushi.

Sai kusan 9:30 suka nufi gidan Shehu, tun daga nesa suka hango motar Shehu ta shiga gidan, daga dan nesa sukayi parking sannan suka fito Zarah na dan rike dashi saboda har yanzu kafafunsa basuyi kwari sosai ba.

Ita tayi knocking din kofar sau biyu, karamar kofa gate man ya bude yana kallonsu kafin ya ce " Basu dawo ba fa!

Daga haka ya fara kokarin rufe kofar. Karfin da Zarah bata san tana da shi ba ta saka ta tura kofar da karfi ranta a matukar bace ta shiga gidan tana fad'in " Ubanwa zaka raina wa hankali? Zayd ne ya biyota yana yi wa mai gadin kallon banza. Ko knocking batayi ba ta afka falon.

Ganin Sa'adah tayi tare da Ummie dake tafiya kafa a wangale kamar wadda akayi wa kaciya.

"Me ya sameta? Zarah ta fada tana karasowa cikin falon.

Kallonsa sukayi su duka, Shehu ido ya raina fata.

Kula Ummie ta saka tana fad'in " Ummana ni bana son tafiya wajen ciwo yake min Aunty Sa'adah tace sai nayi"

A gaban Ummie Zarah ta durkushe tana fad'in " Ne ya sameki a wajen?

"Ance miki typhoid ne"
Shehu ya fada yana tada jijiyar wuya.

Banza tayi dashi tana rike hannun Ummie ta ce " Mamana me ya sameki?

"Dan Allah Ummana ko tafi dani bana son na kara zama a man wajen!

Juyowa Zarah tayi ta kalli Zayd da suma kallonsu yake yana mamamkin me ya samu Ummie haka tayi wannan ramar.

Kokarin fincike Ummie daga jikin Zarah Shehu yayi yana fad'in " Baki da inda ya wuce gidan Ubanki!

Sake rungumeta Zarah tayi zuciyarta na karaya.

"Ummana Dan Allah ko tafi dani! Ummie ta sake fada tana kara kankame Zarah.

"Me ya faru da 'yata? Cewar Zarah tana yi wa Shehu wani kallo.

"Ya kike so nayi! Ya kike so nayi da rayuwata! Dame kike so naji? Kinsan asarar miliyoyin kudin da nake yi? Ke wace iriyar mahaukaciya ce! Ko ance miki nima bana sonta ne? 'Yata ce fa? Ni na haifeta! Kuma ina sonta! Ance miki a son raina wani ya bata mata rayuwa?

Wani dum zuciyar Zarah ta bada wani sauti.......

"B'ata ma ta rayuwa? Zarah ta maimaita tana tashi a sukwane idanunta akan Shehu, "Zarah Dan Allah calm down zan miki bayanin komai! Cewar Sa'adah tana kallonta.

"Ka fada min abi da ke faruwa!

Cikin fushi ya kalleta ya ce " Na gaji da boye miki! Ke ba kowa bace da zanji tsoranki! Fyade akayi wa Ummie!"

Ya fada da karfi yana kallonta. A hankali Zarah ta karasa inda yake yana kokarin chakumoshi amma jikinta yayi week sosai dishi² kawai take gani dan tayi matukar girgiza, da sauri Zayd ya karaso yana fad'in " Zarah calm down please!

Ture Zayd tayi aikuwa ya fadi amma be ji faduwar ba ya fara kokarin mikewa, daddageea tayi da tsinke Shehu da mari amma zafin da zuciyarta ke yi ma ta ko madam be ragu ba, chakumeshi tayi ta fara duka ta ko ina, har karfinta ya kare,awajen ta sulale tana fashewa da wani kuka me dacin gaske wanda baby wanda zai fahimci halinta da take ciki sai me da.......

*Kuyi hakuri kwana biyu ina samun matsalar charji wayana bata da rikon charji but insha Allah zanyi kokarin ganin mun kammala kafin Azumi*

Autar Mama ce.
[3/16, 4:47 PM] Brother❤: ✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma k'alubalen rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
Autar Mama

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow mr on wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 35" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1200202021?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=aNtaFNbP7NptSLcL98SFJmhatlQWgEOjsgY4wzr8ULE7kSl%2BwfVrvMVAS6TQ3er%2Ff113kDIVEjEDT6MHvztUxuDJwM5932iyCLhgsdsJwNF1I8cuVnDkSXr6V9FzCn1Z

*Whatsapp number, free to contact me 08142904255*

*BAK'AR SAKAYYA*

*Bak'ar sakayya, labarine a kan tsantsar soyyar gaskiya wadda ta fara tun daga yarinta, ya sota tamkar ransa! Yayi fada da kowa a kanta! Yayi kokarin sadaukar da rayuwarsa saboda soyayyarta! A nata b'angaren itama ta soshi soyayya me zafi hade kuma da yarinta... Shin kunsan me yake faruwa?.... Ko yaya Yidi da Bardo zasu kasance? Ya labarin soyyarsu zai kasance? Me kuke tunani a kansu?... Hmm a wajena kawai zaku samu wannan amsoshin akan nera 300 ga masu turuwa ta banki, masu turo kati kuma 400 ne masu idan kuma Vip group ne zaki biya 500 posting sau biyu a rana*

*Hmm, ga Yazeed fa! Yaro dan gata! Amma kash! Ya kasance dolo! Sanadiyyar hakan ya,rasa me zama dashi! Baya iya yin komai da kansa! Ya tashi ba tare da uwa ba! Yayansa kadai ne sanyin idaniyansa! Hmm Yidi ta shigo rayuwar Yazeed but how? Hmm wanna amsar zaku sameta ne a,wajena kuma duk cikin littafina me

Please Login or Register in order to submit comment