Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Da yammacin rana Zarah ta farko, taji dadin jikinta sosai, Auntu ce da Zainab a kusa da ita. Rufe idanunta tayi kadan, abubuwan da suka faru suka dawa ma ta.

Sake bude idanunta tayi ta kalli Zainab ta ce " Ruwa"

Da sauri Zainab ta kalleta tana fad'in " Zarah!

Aunty ce ta bata ruwan tana fad'in "Sannu Zarah!

Sai data gama shan ruwan sannan ta ce " Yawwa Aunty" Fita Zainab tayi suka dawo tare da doctor ta duba Zarah ta kuma tambayeta ko tana jin wani aje ba dadi? Amma Zarah ta ce a'a dan bata jin komai.

Karfe bakwai da wasu yan muntuna suka dawo gida, Zayd na zaune a falo yana latsa wayarsa suka shigo.

Ko kallon inda yake Zarah batayi ba, Zainab ma haka ta taimakawa Zarah ta nufi dakin Aunty.

"Ga danka sai ka kula dashi! Cewar Aunty tana ajiye babyn a cinyar Zayd.

"Haba Aunty in kula dashi ta yaya? Me zan bashi? "Nono! Ko baka dashi? Murmushi yayi kadan kafin ya marairaice fuska ya ce " Haba Aunty Zayd ne fa! Meyasa zakiyi min haka?

"Kaima meyasa zakayi wa marainiya haka? Me tayi maka? Da wannan zaka saka ma ta?

Shuru yayi ya kasa cewa komai dan kham sai yanzu yake kara dana sanin sakin ba tare da jin ta bakin Zarah ba. A wajen Aunty ta barshi da Babyn dake kuka kadan kadan kamar mage lol...

Ji yayi babyn yayi masa karami a hannu, sunan Zainab ya fara kira da kari, kamar anyi ma ta dole haka ta amsa tana fitowa.

"Ungo nan" Ya fada yana miko yaron.

"Tab, ni gida zan tafi" Daga haka ta wuce ta barshi a wajen. Yana gani har ta fita daga falon.

Kallon yaron yayi kafin ya dan taba kumatunsa da karamin yatsansa zuciyarsa cike da farinciki samun jininsa a duniya.

Sai kusan 9 sannan Aunty ta fito daga d'aki tana fadin " Zamu kulle gida ka tafi"

Da mamaki ya kalli Aunty ya ce " In tafi ina?

"Gidanka! Ta bashi amsa tana kallonsa. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta ya ce " Aunty Dan Allah kiyi hakuri shi dama aure rai ne dashi nima bawai a son raina na saki Zarah ba kinfi kowa sanin ina kaunarta tun kafin ma tasan menene so sai yanzu kuma dana sameta sannan zan wulakanta ta? Dan Allah Aunty ki bar wannan mutuwar auren a matsayin kaddara kawai"

Shuru Aunty tayi tana karantar yanayinsa gaba daya, tabbas akwai wani boyayyen sirrin fa yake boyewa! Toh me Zarah tayi masa haka? A yadda tasan Zayd dai tasan cewa bazai taba fadar dalilin sakin Zarah ba kuma bata jin itama Zarah tasan dalilin sakin"

Numfashi ta sauke tana karbar babyn hannunsa ta ce "Haka zaka zauna ba aure? Kazan yadda lalurarka take ko kana bukatar me kula da kai"

"Hakane Aunty, Amma bana bukatar aure dan babu macen da zata yarda ta aureni ko da akwai bazan ma iya wani aure ba, amma tunda ina da mahaifiya nasan baza taba bari nayi kuka ba"

Ya karashe maganar yana kallonta. "Ba ruwana fa! Dan bazan yi abinda zan sa Zarah taji ba dadi ba! Kaje chan ka nemi me kula da kai"

Da ga haka ta wuce ta bar shi yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi kadan.

Har ta rufo gidan ta dawo be bar wajen ba sai kunsan 11 na dare. Dakin Zarah ya nufa ko knocking beyi ba ya shiga, a zaune ya ganta tana sharar kwallah. Sosai jikinsa yayi sanyi kallonta yayi ya ce " Zarah sannu"

Goge hawayenta tayi tana fad'in " Yawwa sannu"

Karasowa yayi bakin gadon yana fad'in " Ya jikin? "Da sauki" Ta bashi amsa tana kokarin kwanciya.

"Zarah! Kiyi hakuri nasan bazaki ji dadi ba kuma duk rashin dadin da kikeji a zuciyarki nawa ya ninka naki!

"Kat kaji komai ba wani abu bane ai ya wuce kaji ko kaje kayi bacci"

Ta fada tana son boye damuwarta. Tsaywa yayi yana kallonta,dan dagowa tayi taga ita yake kallo murmushin dole tayi masa tana ce wa " Dare yayi kaje ka kwanta"

Daga haka ta ja bargo ta rufe har kanta wani kuka me daci ta fashe dashi amma bata bari aound din ya fito sosai ba. Sarai yaji ta dan hankalinsa na kanta kuma darene ko ina yayi shuru.


Rayuwarsu haka take tafiya sam Zarah bata yarda ta nunawa Zayd tsantsar damuwa, ya dawo gidan ya tare Aunty ce ke dan taimaka masa wani lokacin ma kyaleshi take duk da abinda baya ma ta dadi amma tana so ta kara nuna masa mahimmancin Zarah a wajensa.

Wattanni biyar kenan da yin sakin da kuma haihuwa, sosai Zarah tayi kokarin cire damuwa a ranta ita da babynta wanda yaci sunan Mahaifin Zayd wato Ibrahim ana ce masa khaleel duk suna cikin koshin lafiya dan ya girma ba kamar da ba duk da be zama wani kato sosai ba kuma time by time suna zuwa asibiti.

B'angaren su Yusuf kuwa ya kwana uku da dawowarsu Nigeria har yanzu Farooq be tashi ba tun Mama da Ummie na kuka har sun gaji sun daina.

Ummie na zaune kusa dashi har likita ta gama saka masa ruwa tare da gyara masa robar da yake karbar abinci ta hanci.

Kallon Ummie rayi tana fad'in karki wani damu kinji? Insha Allah daf yake da tashi da yarda Allah"

"Toh" Ummie ta amsa a sanyaye.

Fita likitar tayi ita kuma Ummie ta zuba masa idanu gashi har ana shirin rufe shekara amma bai tashi ba, shi ba'a raye ba sannan shi ba'a mace ba.

Ramalah ce ta shigo d'akin gana fad'in " Sashi da kike a gaba ba shi zaisa ya tashi ba Ummie! Kije ga wanke² chan a kitchen kuma kinsan kuna da makaranta ko?

Ummie bata ce komai ba haka zalika bata tashi ba ballanata ta kalki Ramlah.

"Ummie magana nake fa! Juyowa Ummie tayi tana ma ta wani kallo kafin ta ce " Dan Allah ki kyaleni da rashin lafiyar mijina zanji ko kuma da hayaniyar ki?

"Oh Miji? Dan Allah fa! Aunt har miji gareki? Toh uwar me mijin ya taba tsinana miki? Ina ce daga yin auren ya gudu ya barki?

"Ramlah! Taji muryar Yusuf ya fada da karfi. A dan tsirace ta kalleshi kafin kuma taja tsaki tana neman hanyar fita ya riko hannunta ransa a matukar bace ya ce " Wace iriyar babbar banza ce ke? Baki da kirki sam! Kiyi wa Mama sannan kiyi wa Ummie? Ke baki iya respecting din kanki bane?

Kwace hannunta tayi tana galla masa harara ta ce " Anyi din" Daga haka ta fita tabarsu. Girgiza kai yayi cike da takaici, amma yasan maganinta! Aure zai kara dan taga ita kadai ce yasa takeyin abinda tayi niyya!"

Kallon Ummie yayi ya ce " Ki tashi kiyi shirin makaranta zan saukeki kafin na tafi aiki"

Da toh ta amsa tana nufar closet dan already tayi wanka kaya kawai zata sauya. Fita yayi ita kuma ta shirya ta fito bayan tayi wa mijinta addua.

Da yamnacin ranar Zarah na zaune a dan madai daicin compound din gida ta shimfida tabarma dan ana dan zafi kuma an dauke nepa, latsa wayarta kawai take yi.


Kofar gidan da aka bude ya saka ta dgo tana kallon me shigowa. "Zayd ne tare da driver dinsa.

Kallo daya tayi masa sannan ta dauke kanta ta cigaba da abinda takeyi. Fita driver yayi yana rufo kofar.

Murmushi Zayd yayi yana kallonta ya ce " Shikenan dan nayi saki babu wani zuminci tsakanin mu? Komai ya kare kenan?

"A'a naga kamar kana tare da bako ne" Zarah ta bashi amsa tana sakin fuska. "Uhm" Kawai ya ce ya nufi falo. Tana zaune har ya fito yana fadin " Nima bari na sha iska, Aunty tace iska kike sha"

"Eh" Ta fad'a ba tare da ta kalleshi ba.

Kafin ya ce wani abu aka fara knocking din kofar. "Turo" Cewar Zarah tana kallon kofar.

Yasha wani hadadden yadi me haske da daukar ido gashin kansa yasha gyara ba hula a kansa hakan ya kara fito da dan manyantar da yayi asalin yarensa ya kara bayyana a jikinsa. Sosai yayi kyau kamar ba shi ba. Ummie ce ta shigo daga baya rike da hannun Ihsan dake tafiya sannan kuma Sa'adah.

Da kallo kawai Zarah da Zayd ke binsu, sosai wani abu yake tokare wuyan Zayd kirjinsa na zafi.....

*manage*

Autar Mama ce
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*


https://www.wattpad.com/1192513300?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=AipQ7zVj0uqK3Z0hFJpQqzbTgnEr3NYfZoi%2FtYwb80y0Qozvu%2B4oXjDx2pQdSL2tQ%2FsyKiAoa7UIcuwpdpVqs0qDAvPKdHor07%2FNfJ4%2FGvmRLvQgAA10vecikTHB4ibH

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)

𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.

*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...


*K'ANWATA*

*Dandano!Dandano!!*


Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..


Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573


Nomal. guda d'aya N 300 ne

guda biyu N 500 ne


Special guda d'aya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne


Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Shafi na Ashirin da bakwai*

Wani irin kallo Zayd yake bin Shehu dashi ransa amatukar b'ace ya ce " Malam me ya kawo ka?

"Ashhhh a bun da zafi haryanzu na sani sorry" Shehu ya fada yana wani cize baki tare da dafe saitin zuciyarsa.

Idanun Zayd sunyi ja sosai ransa ya gama b'aci, Zarah kuwa kallonsu kawai takeyi ganin yadda ran Zayd yayi matukar baci ganin Shehu wanda da chan ba hakan ne yake faruwa ba duk da baya sakar masa fuska amma baya hade rai kuma bacin rai baya bayyana har haka.

"Anyway ni ba fad'a nazo ba dama mun fita ne shine na kawo Ummie ta zauna zuwa jibi zanzo mu tafi"

Kallon Ummie yayi yana fad'in " Two days kawai kuma kin daiji abinda na fada miki ko? A hankali ta daga kanta alamar eh.

Kiran Ihsan yayi tazo ya rike hannunta sannan ya kalli Zarah ya ce " Baki da lafiya ne? Naga duk kin rame"

Girgiza kai tayi kafin ta ce " A'a lafiyata kalau"

"Ohk" Cewar shehu yana bin ta da wani mayan kallo.

"Bazaka tafi ba? Zayd ya fada yana ji kamar ya tashi ya tureshi amma bazai iya ba.

"Ok zan tag but soon zan dawo kaji ko? Dan kayi wasa da damarka!

Daga haka Shehu ya fice, kallon Zarah, Sa'adah tayi tana fad'in " Zarah ba magana?

Murmushi Zarah ta sakar ma ta kafin ta ce " Ya kike?

"Ina lafiya Zarah, Dan Allah Zarah kiyi hakuri da abinda na miki a baya kinji ko? Wallahi da ace ina da yadda zanyi da zance Shehu ya dawo dake mu zauna naji yace min Zayd ya sakeki"

"Get out! Zayd ya fada da karfi. A dan tsorace Sa'adah ta matsa baya.

"Karki damu Sa'adah indai komawata gidan shehu alkhairy ne zakiga na dawo, dan shi din miji ne na kwarai"

Zarah ta karashe maganar tana kallon Zayd ta gefen ido. Murmushi Sa'adah tayi ranta fal farinciki dan ta gaji da halin shehu ga bala'in jaraba gwanda Zarah ta dawo da yaje ya auro ma ta wata tasan zasu zauna lafiya tasan Zarah bata da matsala itace dama ne matsala yanzu jyma ta sauya ta gane shehu ba dan goye bane.

" Bani number dinki" Sa'adah ta fada tana mika mata wayarta. Horn din da Shehu yake dannawa yasa Zarah tayi saurin saka ma ta number sannan ta fita. Kokarin tashi take ta koma cikin daki dan magariba ta kawo kai amma ya janyo hannunta ta dawo kan tabarma ta zauna da karfi.

"Auuccchhh" Ta fada tana runtsa idanunta.

Kallon Ummie yayi da yaga ta zama so silent ko magana ma batayi masa ba. " Tashi ki shiga ciki" Bata ce komai ba ta wuce sim-sim.

Matse hannun Zarah yayi da karfi yana fadin " Zaki koma gidan shehu?

"Eh zan koma kuma haka isa ka hanani ba! Zarah ta fada tana kokarin kwace hannunta. Kara saka karfi yayi ya damke hannun ko motsi bata iyawa.

"Ka salad mine hannu" Ta fada tana kallonsa. Kin saki yayi aikuwa da karfi ta kira sunan Aunty. Da sauri ya sakar ma ta hannu yana fad'in " Me haka? Yarinta ko me? "Bansani ba! Ta fad'a tana tashi ta nufi cikin falo.

Daki ta wuce bata kara fitowa ba sai bayan isha'i.

Baya falon hakan yasa taji dadi, Ummie ta gani zaune a kasa tana cin tuwo sai Aunty da ke rike da khaleel.

"Mamana ko nema na bakyayi ko? Cewar Zarah tana saka pillo ta zauna kusa da ita.

"Ummana na fara fitsarin jini"
Sosai gaban Zarah ya fadi, haka ma Aunty tayi saurin kallonta. "Fitsarin jini kuma? Zayd da fitowarsa daga daki ya fada dan yaji abinda tace.

"Eh haka Aunty Sa'adah ta fada min, amma Yaya Saleh ya ce wai jinin al'adah na fara kuma Aunty sa'adah ta ce min wai jinin al'adah wani abincin turawa ne"

Shuru Zarah tayi da sam bata san me zata ce wa Ummie ba gaba daya jikinta yayi sanyi shekarun Ummie basu wuce 10 ba amma har ta fara al'adah?

Ta tambayi kanta. Ni kuwa nace ma za'a fasa.....

"Cinye tuwanki kizo nan" Cewar Aunty tana nuna ma ta kusa da ita. Da toh Ummie ta amsa ta cigaba da abinda takeyi.

Kusa da Zarah Zayd ya matso yana kallonta ya ce " Ya naga kamar kina da damuwa?

Ta shi tayi tana nufar daki da sauri. Bin bayanta yayi, a zaune ya ganta a bakin gado tana kallon waje daya.

"Zarah! Ya kira sunanta. Kallonsa tayi kafin ta mike tsaye ta ce " Kawai ka dinga shigo min daki haka kawai!

"OK Amma ni ai yayanki ne ko? "Bansan wannan ba! Idan zaka shigo ka dinga neman izini na gaskiya"

Ta fada kamar zata dakeshi. "Ok shikenan, Zarah inaso muyi magana"

Wani kallo tayi masa kafin ta ce " Magana? Indai akan komene bazan koma gidan ka ba! Tunda ba yadda banyi da kai karka sakeni b amma ka sakeni ko dan kaga na amince da aurenka da wuri shiyasa?

"Zarah please! Inaso ko nutsu muyi magana"

Zama tayi tana fad'in "ok"

"Inaso ko fada min ranar da Shehu yazo daukar Ummie me ya faru? Ina nufin kafin na sakeki

Shuru Zarah tayi ta fara tunani,tas ta tuna shigowar Shehu da shakawa Ummie abun bacci sannan itama ya shaka ma ta but daga nan bata sake tuna komai ba, hakan besa tayi wa Zayd magana ta cigaba da hashashenta...
Da sauri fa kalli Zayd ta ce " Shehu!

Cike da mamaki ya kalleta ya ce " Me shehun yayi?

Shuru tayi a ranta ta ce " So Shehu can stopped to any level dan ya cimma nasara a bukatar shi? Me ya aikata? Dagaske yayi zina da ita kamar yadda tunaninta ya bata ko kuma yayi framing dinta ne saboda mijinta ya saketa? Da chan yasan yana sonta yake ma ta wannan cin kashin lokacin da take gidansa? Meyasa zai ma ta haka?

"Zarah! Zayd ya kira sunanta ganin kamar ta b'ata.

Hawayene suka zuba idanunta tabbas wannan dalilin yasa Zayd ya shiga damuwa har dokin zuciya yasa ya kaishi ga sakinta! Ba laifinsa bane amma ai shima ya kamata yayi bincike! Anya kuwa ma hakane? Ta fada aranta.

"Zarah me kike tunani? Zayd ya fada yana kallonta.

Goge hawayenta tayi ta ce " Me Shehu yayi? Ka fada min gaskiya!

Hannunta yake konarin rikowa ta tashi da sauri tana matsawa baya ta ce " Me yayi? Shuru Zayd yayi dan besan me zai ce ma ta. Zarginta ua tabbata ganin yadda maganar take da nauyin furtawa a wajen Zayd.

A bakin gado ta zauna tana dafe kanta cike da takaici, bata jin shehu zaiyi zina da ita a yadda ta sanshi dai duk da tasan bashi da kirki amma tasan da kyar ya aikata abu irin haka!
"Zarah Dan Allah kiyi hakuri i realized my mistake wallahi! I act before i think shi ya janyo duk wannan"

"Ka fita zan kwata" Ta fada tana hawa kan gado.

Matsowa yayi inda take yana kallon fuskarta juya masa baya tayi ranta duk ba dadi 'Zayd me iya bada shedarta ne akan bazata aikata irin wannan abun ba amma gashinan har ya yarda bayan yasan waye Shehu.

Hannunsa taji a gefan cikinta da sauri ta tashi zaune tana kallonsa. Shima kallonta yakeyi. A hankali ya ce " Zarah! Nayi kewar lokutan da muka kasance tare! Dan Allah kiyi hakuri"

"Na hakura" Ta fada tana canza direction din kwanciya yadda bazai iya tabota ba.

Murmushi yayi kadan yana kallonta. Itama kallonsa take kafin ta juya masa baya. Matso da wheelchair machine dinsa yayi jikin gadon yana kokarin hawa amma ya kasa dan ya kasa daga kafarsa. Tashi tayi zaune tana kallonsa ta ce " Me haka ne Zayd?

"Please Zarah! Ya fada yana narke fuska. " Na hakura ai kasan dai yanzu mu ba ma'aurata bane ba kyau ka fita kuma kasan shedan"

"Babu abinda zan mini Zarah! Infact ma babu abinda zan iya, just relax"

"Zayd bansan me kake yi a dakin ba har yanzu" Aunty ta fada tana shigowa. Kallon Aunty sukayi a tare itama su take kallo kafin ta ce " Muje dare yayi" Ta karashe maganar tana kallon Zayd.

Shafa kansa yayi kadan yana kallon Auntu sannan ya amsa da toh.

Washe-gari Zarah na feeding din Khaleel Ummie ta shi go tana fad'in " Ummana Uncle Zayd ya ce wai wannan k'anina ne?

"Eh ko bakya so? "Ina so mana" Ummie ta fada tana hawa kan gadon kusa da Zarah. "Ummana in fada miki wani abu bazaki dakeni ba?

"Eh" Zarah ta fada tana kallonta. " Yaya Saleh ne yake taba min nono yana matse min kamar yadda Abba yake miki"

Wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarci Zarah zuciyarta ta buga da karfi. Da sauri ya daga rigar Ummie, aikuwa tavfara kirgyan dangi gasu nan sun fara tsowa kadan.

"Ummana kuma ina jin zafi sannan ya ce idan na fadawa kowa mutuwa zanyi bazan girma na zama likita ba, Ummana ni bana so na koma wajen Abba saboda Yaya saleh yana taba min jiki kuma malamin mu ya ce ba kyau namiji ua dinga tabawa mace jiki idan ba mata da miji ba sannan Abba ya ce ince miki ki koma gidansa idan ba haka ba wai almajiranci zai kaini in dinga bara, amma karki fada masa na fada miki ni dai bana son komawa gidan Abba ki tafi dani gidanku tare da Uncle Zayd"

Ummie ta karashe maganar hawaye na biyo kuncinta. "Kin tabbata Saleh be taba miki wani abu ba? Zarah ta fada muruarta na d'an rawa.

" Eh Amma yana samin hannu a cikin wandonsa kuma nidai bana so duk ranar dana ki sai samin hannu a cikin masai kuma ya hanani fadawa kowa a islamiyya ne malamar mu take fada mana bamu da abokin sirri irin uwa shiysa na fada miki kema karki fadawa kowa"

Shuru Zarah tayi dan ta kasa cewa komai idanunta duk sun ciko da kwallah, tana nan zaune Saleh zai lalata wa 'yarta rayuwa? ......

*manage*

Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 28" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1193278149?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=3CJWnNWa7wnIsC%2FoELb6IgNzvgNm4ynk%2BLwJtbdNs8bb0GcSFTxHvcePreyw53FXrPF6ebqueRgiR7wSr9XikCv9vo%2BIX9sAgqq8UfSGTb4CcX%2BXj7o0LfLh3E%2Bszo79

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)

𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.

*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...


*K'ANWATA*

*Dandano!Dandano!!*


Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen

Please Login or Register in order to submit comment