Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma nayin kukan tana fadin " Ita bata son Abba tunda Abba mugune yayi ta dukar ma ta Ummanta yana sata kuka"

"Duka!? Itace kalmar da Farooq yayi ta maimaita wa a zuciyarsa.

"Zarah ya isa haka! Aunty ta fada tana tasowa ta nufota.

Kallon Zayd Yusuf yayi ya ce " Muje waje"

"Ok sir" Ya faɗa yana yin gaba su kuma suka biyo bayansa.

"Waye yayi ma ta wannan abun? Waye ya daketa haka? Cewar Farooq yana kallon Zayd.

"Mijinta ne! Ko akwai abinda zakayi? Zayd ya faɗa a ɗan kufule.

"Yes! Idan ta yarda ni mai iya kaishi court ne kuma na tsaya ma ta a yanke masa hukunci dai² da abinda ya aikata"

Murmushin gefen baki Zayd yayi yana rungume hannayensa ya ce " Ita zaran ce zata baka hadin kai? Bari kaji, yadda take son wannan mijinta ko kai baka san kanka haka"

Ya karashe maganar yana kauda kansa daga kallon Farooq. Tsaki Farooq yayi yana shafa kansa cike da takaici.

Murmushi Yusuf yayi yana kallon Zayd ya ce " Relax bro tana da aure fa! Kishin bai da wani amfani, and meyasa ka dawo da kudin dana turo maka?

Dan kasa yayi da kansa kafin ya ce " Bakomai kawai dai.. sai kuma yayi shuru

"Kawai dai baka son taimakona ne ko?

Yusuf ya karashe maganar yana murmushi.

"Ba haka bane sir, naga ina da kuɗi meyasa zan karbar maka naka?

Amma ai ni nayi niyya na baka ko? Yanzu ka biya komai na asibitin?

Cewar Yusuf yana kalllonsa.

"Eh" Ya bashi amsa a takaice.

"Ok shikenan, zuwa gobe zan dawo na kara ganin jikin nata, Allah ya bata lafiya kagaida Ummanku kace mun tafi"

"Insha Allah" Zayd ya amsa ba tare da ya kalleshi ba. Farooq bai ce komai ya wuce. Bayansa Yusuf ya bi yana kiran sunansa.

Dogon tsaki Zayd yaja kamar wata mace sannan ya koma cikin ɗakin. Ayaba ya tarar da ita tana ci da alama ta daina kukan. Ledojin da suka kawo ya ƙalla kafin ya ce " zarah ya jikin?

"Da sauki fa" ta fada tana ɗan yi masa murmushi.

Shima murmusawa yayi kadan yana zama a kujera tare da janyo kujerar zuwa gaban gadon da take.

Idanu ya zuba ma ta cike da tausayin halin da ta ke ciki.

"Zayd ya kamata ka tafi gida dare na kara yi"

Aunty ta fada tana kalllonsa.

Numfashi ya ja sannan ya sauke da ɗan ƙarfi ya ce " Hakane, nasan zuwa gobe ma zasu iya sallamar mu"

"Allah yasa" Aunty ta fada tana kallon Zarah.

"Amin, na tafi Allah ya kara sauki Zarah"

Da Amin ta amsa shi kuma ya fice.

Aunty ce ta dawo kusa da ita tana fadin " Ga kaji nan su Farooq sun kawo in zubo miki zaki ci?

"Na koshi Aunty bari nayi sallah sai na kwanta"

"Toh muje na rakaki.

Aunty ta taimaka ma ta ta kama ruwa sannan tayi alwala tazo tayi sallah kafin ta kwanta.

Washe _gari

8am a asibitin tayi wa Zayd shi da UMMIE, Zainab kuma ta wuce wajen aikinta.

Ummie na ganin Zarah ta nufeta da gudu ta fadin " Dorani a kan gadon"

Zayd ne ya karaso ya dorata kusa da Zarah yana cewa " Ina kwana?

Murmushi Zarah tayi ta ce " Ina kwana?

"Lafiya lau, ya jikin?

"Naji sauki fa, dazu ma da nurse tazo yin round ta ce idan kazo kaje maybe sallama ce dan na ce ma ta bana jin wani abu sai iya ciwon da ya ji min kuma dama shi sai a hankali zai warke"

"Hakane bari naje toh" Ya faɗa yana ficewa daga ɗakin.

Kaya Aunty ta fara haɗawa, sai yanzu ta kula har da kuɗi a cikin kayan da su Farooq suka kawo.

Miƙawa Zahra kudin tayi ta ce " Ungo nan"

Cike da mamaki Zahra ta ce " Wannan fa?

"Masu dubiya ne suka kawo miki, riƙe kudinki karki bari yaronan ya gani kinsan ya iya fitina yanzu zai ce Bazaki amsa ba kuma bashi da dalili"

Murmushi Zahra tayi ta ce " Toh"

A cikin jakar Aunty ta jefa kudin tana murmushi.
Kamar yadda sukayi tsammani sallama ce, ya biya komai nasu, kayan ya ɗauka ya kai mota sannan suka fito tare dadi Zarah.

Gida ya nufa, Zarah ta manta rabon da ta zo gida, gaba ɗaya unguwar ta sauya ma ta. A kofar wani gida me kyau kuma ma dai²ci yayi parking yana kallon UMMIE dake zaune a front seat ya ce " Shikenan na dawo miki da Ummanki ko?

Murmushi tayi tana daga kai alamar eh.

"Yawwa toh sauka muje"

Buɗe motar sukayi suka firfito, shi ya shigar musu da kayan cikin gida sannan ya nufi wajen aiki.

★★★★★

"Farooq! Farooq! Ganin hankalinsa baya kanta yasa ta dan dakeshi a kafa tana fadin " Kai kullum baka da aiki sai tunani? Ungo wannan zaka kaiwa UMMIE idan kaje kuma kar ka kuskura ka ce ni na baka ka bata nasan halinka sannan ka tashi ka shirya dare na yi"

Ɓata rai yayi yana saukowa daga kan gado ya ce " Kaina ciwo yake Mama ki bari gobe na je"

"Ai baka isa ba kuma! Na faɗa musu ga kanan zuwa, kafin na ɓata ma ka rai kayi abinda na ce, kuma Allah idan kaje ka bata wa ƴar mutane rai kaima sai na bata naka ran"

"Ok" Ya faɗa yana shiga toilet. Itama fita tayi daga ɗakin.

Tana sakkowa ta tarar da Yusuf ya dawo daga office yanzu.

Ko zama beyi ba ta ce " Fada min! Yaji Ramlah tayi ko kuma me? Ni ban taba ganin ta tafi hutu ta zauna haka ba gashi jika na ko ziyarta na bayayi, ka fada min gaskiya ko kuma ni naje har gidansu na jiyo me yake faruwa"

Ajiye files ɗin hannunsa yayi tare da rigar suit dinsa ta sama yana kallon Mama ya ce " Ko ruwa fa bansha ba"

"Na sani ai! Ina jinka meyasa ta tafi?

Numfashi ya sauke kafin ya ce " Kyaleta Mama, she's not serious abinda take so bazai taɓa faruwa ba! Sai dai idan bazata iya ba na saketa! For God sake muna zaune lafiya for more than 10yrs shine yanzu zata budi baki ta ce wai lallai sai na raba muku gida, ƙawaye ne suke zugata kuma zasu kaita su baro ta! Ina zan kaita? Duk wannan girman gidan ke kadai take so ki zauna? Ai ko Farooq ne yayi aure a nan zai zauna ballantani ni, bazamu bar mahaifiyarmu da zaman kadaici ba"

Ya karashe maganar ransa duk a ɓace.
Shuru Mama tayi tana jajanta lamarin ita a iya zamanta da Ramlah bazata ce ga abinda take ma ta dan ta musguna ma ta ba, ba yabon kai ba tasan ita ɗin mother in law ce ta gari a wajen Ramlah amma kuma zugar ƙawaye da koma waye zai kaita ya barota.

Ajiyar zuciya tayi ta ce " Shikenan, zata gaji tadawa ne kai kuma idan kaje bikonta Allah ya isa, sannan ka karbo Babana daga wajenta"

Daga haka ta barshi a tsaye a wajen.

Shafa kansa yayi yana furzar da iska me ɗumi ta bakinsa sannan ya dauki kayansa ya nufi dakinsu.

Da kyar Farooq ya iya shiryawa cikin shadda me gajeren hannu ɗinki zamani wanda suke rigar iya cinya.

Yayi kyau sosai, amma ransa duk ba dadi. Wayarsa da mukullin mota ya dauka tare da sakon Mama sannan ya fito. Be tarar da kowa a falon ba, ficewar yayi ba tare da ya nemi kowa ba.

A hankali ya dinga tuki, tafiya daya kamata yayi a minti 20 yafi 40mins a hanya, kiran mama babu wanda be shigo wayarsa ba amma be dauka ba dan baya jin zai iya yin magana da ita a yanzun.

Sai daya isa kofar gidan kanwar Mama sannan kira Maman.

Cikin fada ta fara fadin " Wai baka isa bane? Kuma meyasa baka daga kirana ba?

" Mamaaaa! Ya faɗa yana wani shagwabewa. Katse wayar tayi shi kuma ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kashe motar ya dauko abinda mama ta bashi ya fito.

Knocking din gate ɗin gidan yayi sau biyu.

"Waye? Yaji an fada cikin siririyar murya. "Dallah bude min kofa" Ya fadi kamar zai make me maganar. Tana jin muryarsa tasan Farooq ne. Da sauri ta buɗe kofar tana fadin " Uban dan masifa"

Harara ya watsa ma ta yana fadin " Me kika zo ji?

"Ziyara mana ko za'a hanani? Ta fada tana dariya. "Uhm yayi" Ya faɗa yana yin gaba. Karasa dauraye wando yarnta tayi ta biyo bayansa da sauri.

Gida ba wani babba bane amma fa yana da kyau sosai. Bakinsa dauke da sallama ya shigo falon.

Fuskar Aunty ƙarama dauke da murmushi ta amsa tana fadin " Ai na dauka ka fasa zuwa"

Shafa kansa yayi ya tsugunna ya gaida ita. Amsawa tayi tana ɗorawa da faɗin " Ya su Addan?

"Kowa lafiya" ya fada yana komawa kan kujera ya zauna.

"Farooq an kara girma"
Cewar macen data buɗe masa kofa dazu.

Banza yayi ma ta yana kallon wani waje daban"

"Ke dai bazaki bar tsokanar sa ba ko? Kamar wani sa'anki" cewar Aunty ƙarama tana Murmushi.

"Wata biyu fa kawai ya bani"

"Amma dai na girmeki? Ya faɗa yana harararta.

"UHM sannu gyambo"
"Hadiza kawo masa ruwa mana"

"Barshi dai wadda yazo wajenta ta bashi, bari na kirata"

Ta fada tana nufar wani Balcony.

Tashi Aunty ƙarama tayi tana fadin " Kar dai a nunawa Auta tah izza da girman kai"

Murmushi kawai yayi gaba ɗaya basu sanshi bane amma kham bashi da ko daya a cikin abinda ta faɗa,shi har ga Allah yarinyar bata yi masa ba kuma baya sonta.

Shi kadai aka bari a falon. Yana cikin latsa wayarsa ta shigo. Khamshin da take yi shi ya ziyarci hancinsa hakan ya saka shi ɗagowa ya kalleta.

Atamfa ce a jikinta ruwan hoda da baƙi tayi daurin modern ture kaga tsiya tayi kyau kham dan kyau kana ganinta kaga usulin Fulani.

Cikin karamar muryarta irin na yayarta ta ce " Assalamu alaikum......

Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 9" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1173459205?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=7%2FTrllilk4yOV0VOahBpYAG%2FAaOjxTOLkHXzkyr9I8Tc3S9zedz4zHs6zFNtifWikSFtCqvi3icH66wkPfLT%2FLTLevwKVNC%2FUTVfl2nI5YFhbn%2BqfBX2NKZjSxcgNPMC

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)

𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.

*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...


*K'ANWATA*

*Dandano!Dandano!!*


Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..


Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573


Nomal. guda d'aya N 300 ne

guda biyu N 500 ne


Special guda d'aya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne


Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Shafi na tara*

Chan ciki ya amsa yana ɗauke idanuwasa daga kanta.

Zama tayi a kusa dashi fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Yaya ina yini?

"Lafiya" Ya faɗa yana mayar da wayarsa aljihu.
Kusan minti ɗaya babu wanda yayi magana a cikinsu, shi yana nazarin me zai ce ma ta ita kuma tana jiran yayi magana"

Numfashi ta sauke a hankali sannan ta miƙe tsaye tana fadin " Bari na kawo maka abin tabawa"

Bai ce da ita komai ba, tasan dama da wuya yau maganar hakan yasa ta nufi kitchen.

Abin tabawa da ruwa da kuma leman hadi ta jero a tray babba sannan ta fito. A gabansa ta ajiye tana cewa " Nan dai gidan ba bakon ka bane, ka sakko kaci"

Wani kallan tara saura kwata yayi ma ta kafin ya ce " Kinsan abinda ya kawo ni ko?

Ƙasa tayi da kanta tana Murmushi kafin ta ce " Eh"

"Ok! Ni bazan iya yin musu da mahaifiyata ba ko bijire ma ta, kuma bawai ina so kema ki saɓawa naki iyayen ba, amma inaso ki samu sauki ne a rayuwarki UMMIE! bana so ya zamana garin karfafa zumunci an tarwatsa shi, ina sonki bawai bana sonki ba amma so ba irin na aure nake miki ba UMMIE so na yan uwantaka nake miki, inaso ki sanar da su ban miki bakya sona"

Ya karashe maganar yana kafeta da idanu.

Idanuwanta duk sun ciko da ƙwalla. Hankici ya miƙa ma ta ya ce " Ba kuka zakiyi ba UMMIE,Ni haka nake, duk abinda naga bazan iya dauka ba bana ɗorawa kaina"

Tashi tsaye yayi yana miƙa ma ta sakon Mama ya ce " Gashi inji Mama"

Daga haka ya gyara rigar jikinsa ya bar falon.

A wajen ta daskare ta kasa motsi ko kadan dan batayi tunanin zai iya faɗa ma ta maganganu makamantan wannan ba ballantana wannan"

Lumshe idanunta tayi wasu hawaye masu zafi suka siyo kuncinta.

"UMMIE lafiya" Taji Aunty Hadiza ta fada tana dafata.

Fashewa tayi da kuka tana riƙe hannun Hadiza. Zagayowar gabanta Hadiza tayi saboda daga bayanta ta tsaya jikin kujera.

Zama tayi a gefen ta yana riƙo hannunta ta ce " Meya faru?

Aunty ƙarama ce ta fito daga ɗaki tana kallonsu dan taji sautin kukan UMMIE.

"Nidai bana sonsa Allah bazan iya auransa ba"

Ta fada tana goge hawayen dake zubo ma ta.

"Bangane bakya sonsa ba! Cewar Aunty ƙarama tana kallonta cike da rashin fahimta.

"Shi ne mana, da kinsan baya sona kika ce shi zan aura?

UMMIE ta kuma faɗa tana kuka.

"Shi Farooq dinne ya ce baya sonki?

Cewar Hadiza tana kallonta.

"Eh mana" Ummie ta bata amsa.

Shuru sukayi gaba ɗaya kusan na minti biyu kafin Aunty ƙarama ta dauki wayarta dake kan kujera. Da sauri Hadiza ta riƙe hannunta tana fadin " Me zakiyi?

"Zan kira Adda ne naji ko itane ta ce yazo ya faɗa ma ta haka?

"Umma dan Allah ki kyale Aunty babba haka, ke kanki kinsan bazata turo Farooq yayi abinda yayi ba, kuma ni a nawa ganin tunda har ya fito ya ce baya sonta banga amfanin wannan hadin ba dan UMMIE ce a wahala dan ta kasancewa yar uwarsa wallahi hakan bazai hana shi wulakanta ta ba shifa namiji ne! Ai ba kwantai tayi ba kawai a bar maganar hadin nan matar Cushe ba ta daraja tunda baya so shike....

"Ke dallah rufe min baki, me kika sani? Yaushe aka haifeki da zaki zauna kina lecturing dina haka?

Cewar Aunty ƙarama tana kallon Hadiza.
"Shikenan zan kira Baffa wallahi na fada masa inyaso ya dawo"

Daga haka Hadiza ta bar wajen ranta duk ba dad'i.

Zama Aunty ƙarama tayi kusa da UMMIE tana shafa kanta ta ce " Karki damu Farooq mijinki ne kinji?

Ummie bata de komai ba sai ajiyar zuciya kawai takeyi...

★★★★★

Hadarin daya hado a garin shi ya saka ta fito ta fara kwashe wankin da Zainab tayi kafin ta tafi aiki.

Tas ta kwashe su tana komawa daki, saboda iska da ake yi alamar hadarin ya taso ruwa daf yake da sauka.

Kallon UMMIE tayi dake cin tuwo ta ce " Kyakkyawar Umma an samu abinda ake so ko?

"Eh, Aunty Zauna ta iya tuwo"

"Yau kuma kece da yabon Zainab? Cewar Aunty da ta fito daga uwar ɗaka.

Dariya UMMIE tayi ta cigaba da shan miyar kuka dake cikin ruwan.

"Sannu Zarah, ina ta sauri na fito na kwashe kayan ashe har kin kwashe"

"Eh Aunty, sun ma bushe bari na ninke ma ta"

Cewar Zarah tana fara ninke kayan.

Tayata Aunty ta farayi. Suna cikin ninkin Aunty ta kalleta ta ce " Zarah!

"Na'am Aunty" Zarah ta amsa tana kallonta.

"Maganar aurenki da Shehu! Ni bana so ki koma gidansa cutarwar tayi yawa"

Murmushi kaɗan zarah tayi ta ce " Ya zanyi Aunty?

"Kina nufin zaki koma?

Taji Muryar Zayd ta ziyarci kunnent. Da sauri ta kalli bakin kofar dakin, shine tsaye ruwa ya dan jikashi.

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi ba tare da ta ce komai ba.

Karasa shigowa yayi yana kallonta ya ce " Komawa zakiyi Zarah?

" Meyasa zaka titsiyeta haka? Aunty ta fada tana kalllonsa.

"Ku barta ta amsa! Ki fada min zaki koma?! Ya faɗa ransa duk a ɓace.

Shuru tayi ta kasa amsawa, bata tunanin zasu fahimci abinda ta fahimta, babu yadda zatayi shi din mijinta ne kuma uban yaranta.

"Bakya ji na ne? Y fada kamar zai daketa. Matsawa baya tayi dan taji tsoro.

"Uncle Zayd meyasa kake wa Ummana tsawa?

Cewar Ummie tana lashe hannu. Saita temper dinsa ya fara yi idanunsa har sunyi ja.

"Zo muje UMMIE" Aunty ta fada tana kama hannunta.

Daukar kwanon tuwan Aunty tayi suka bar wajen da bata so anayin wasu abubuwan a gaban UMMIE.

Matsowa yayi kusa da Zarah yana kallon kanta dake kasa ya ce " Zarah fada min, kina son komawa?

Sai a lokacin ta ɗago ta kalleshi amma ta kasa furta ko da kalma daya.

"Zarah Please! Enough! Enough Dan Allah bazan iya jurewa ganin ki cikin wahala ba, zuciyarta tana zafi"

"Why? Ta fada tana kafeshi da idanu.

"Kinason kisan dalili? Ya faɗa yana kallonta ransa duk ya kara ɓaci idanunsa sunyi ja.

"Uhm" Ta fada tana dan matsawa baya.

Runtsa idanunsa yayi kadan tana juya ma ta baya tare da yin addu'a a ransa.

Da sauri ya bar wajen kamar wanda ake bi.

Dogon ajiyar zuciya ta sauke tana zama a kan kujera, dagaske idan ta rabu da Shehu Zayd zai aureta? Duk da bata so shi amma tana jin zata iya zama dashi dan bai da wata makusa a tare dashi, kuma tana da tabbacin zai riƙe ma ta yaranta kamar nashi! So zata nemi saki ne a wajen Shehu? Tabbas! Zata kaishi kotu dan a raba auren! Tana wannan tunanin Zainab ta shigo hannunta riƙe da lema, bata wani jike ba saboda Husband to be dinta ne yake ya daukota kuma ya bata lema ta shigo gida saboda kar ruwa ya jikkata kafin ta karaso cikin gida.

"Zarah! Tunanin me kike yi haka? Ta fada tana ɗan yarfa ma ta ruwan dake jikin lemar.

Dogon numfashi ta sauke tana fadin " Har kin dawo?

"Eh, me aikin yamma tazo min da wuri shiyasa, amma tunanin me kike yi haka?

"Kinga bana son dogon surutu ki canza kaya kizo ga abinci muci"

"Shikenan" Zainab ta faɗa tana nufar dakin da Aunty ta shiga dazu tare da UMMIE.

Bata daɗe a ciki ba ta fito tana kallon Zarah da ta kuma lulawa duniyar tunani. Abincin ta zubo har ta kawo gaban Zarah ammma bata sani ba.

"Sakko daga kujera muci abinci"

Sai a lokacin ta kalli Zainab ta ce " Toh" a hankali ta sakko ta saka pillon kujera sannan ta zauna suka fara cin abincin duk hankalinta baya jikinta.

Sai da suka kammala cin abincin sannan Zainab ta kalleta ta ce " Kunyi Maganar komawa gidanki da Aunty ne? Naga duk yau dinnan sai a hankali"

"Hakane munyi maganar amma bana tunanin zan kuma komawa idan bazai sakeni ba zan kaishi kotu ne kawai"

Murmushin jin dad'i Zainab tayi kafin ta ce " Amma naji dad'i, ai ba kowani zama akeyi wa hakuri ba ke kham kinyi hakuri iya hakuri Allah dai ya tabbatar mana da alkhairy"

"Amin" Zarah ta amsa tana sauke ajiyar zuciya.

★★★★★

Baya jin zai iya zuwa gida a yanzun dan yasan by now Aunty ƙarama ta kira Mama ta sanar da ita abinda yace da UMMIE dan yasan ba boyewa Ummin zatayi.


Shi kanshi be san inda zai nufa ba tuki kawai yake yi dan bai da wani wajen zuwa gaba ɗaya baya jin dadin yanayin yadda yake ciki, da ace Mama zata kyaleshi yaji da abinda yake damunsa a zuciyarsa da yafi sauki amma yanzu bai san ma da me zaiji ba.

Gefen titi ya gangara yayi parking yana kallon tsirarrun motocin da suke wucewa.

Lumshe idanunsa yayi yana jinginar da jikinsa jikin kujera tare da dafa goshinsa da hannunsa na dama.

Wayarsa ce ta fara ruri, dubawa yayi yaga Yusuf ne ke kiransa. Ɗauka yayi yana karawa a kunne ba tare da yayi magana ba.

"Farooq! Yaji Muryar Mama kamar zata fasa wayar. Runtsa idanunsa yayi yana ɗan cizar lebansa, tasan da ita kirashi bazama lallai ya dauka ba shiyasa ta kira da wayar Yusuf.

"Baka ji ne wai?
Ya sakeji ta fada ranta alamar a ɓace yake.

"Ina kan hanya ne shiyasa" Ya fadi yana whining down Dan taji karar motoci sosai.

"Ok kayi sauri ka dawo ina jiranka"

Daga haka ta katse wayar. Ajiye wayar yayi yana kunna motarsa ya bar wajen ya dauki hanyar komawa gida.

A tsaye ya tarar da ita ranta duk a ɓace, hannayensa ya zuba cikin aljihun wandonsa yana kallonta ya ce " jirana kike shine kika zo nan kika tsaya? "Bansani ba! Wai Farooq me yake damunka ne? Bazaka girma kasan inda yake maka ciwo ba? Ita yarinyar da ka kasa yin gaba a rayuwarka domin ta gata chan har da yarinya ɗaya! Ko yau ta mutu tana da mai yi ma ta addu'a, amma kai fa? Wai wani irin aljanune da kai ka kasa cire mata wani a ranka?

Murmushi yayi kaɗan yana dafa kafadarta ya ce " Relax mana! Shikenan kiyi hakuri bana so kina bata ranki akan petty things irin wannan"

Kwace kafadarta tayi daga hannunsa tana nufar cikin falon ta ce " Ni dai na fada maka kuma ka saka rana ka koma ka bawa UMMIE hakuri dan aurenka da ita babu fashi insha Allah"

Bai ce komai ba ya nufi hanyar matattakala. "Baka ji bane? Mama ta dake faɗa tana kallon bayansa. "Insha Allah" Ya faɗa ba tare da ya jiyo ba.

★★★★★



Please Login or Register in order to submit comment