Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..


Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573


Nomal. guda d'aya N 300 ne

guda biyu N 500 ne


Special guda d'aya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne


Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

โœŒ๐ŸผFitattu biyu masu ban mamaki๐Ÿซ€Hakika babban goro sai magogin ฦ™arfe ๐Ÿ˜, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka๐Ÿซ, Fitattu biyu๐Ÿ‘ฏ๐Ÿฝโ€โ™€sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku ๐Ÿค“ sun shirya tsaf domin fadakar daku๐Ÿง  sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so๐Ÿ’‹๐Ÿ’ž, wohoho tabbas ๏ธsahun giwa๐Ÿ‘ฃ mai ษ“adda na raฦ™umi ๐Ÿช,Fitattu biyu๐Ÿ˜โœŒ๐Ÿผ masu tafiyar k'asaita, sheฦ™i, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka๐Ÿ˜˜๐Ÿƒ๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ Fitattun ฦ˜arshen shekara๐Ÿ˜ salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta๐Ÿ˜ maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari๐Ÿƒ๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*โœ๐Ÿฝ Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* โœ๐Ÿฝ Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ
Vip 700๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Shafi na ashirin da takwas*

A hankali ya fara bud'e idanuwansa da sukayi masa wani bala'in nauyi, dishi- dishi ya fara ganin d'akin kafin kuma ya ga komai ya dawo masa dai-dai. Robar dake hancinsa ya zare yana runtsa idanu, ji yayi jikinsa yayi nasa nauyi sosai, kokarin takawa yake yi amma yaji ya kasa motsa kafafunsa.

Sabir ne ya shigo d'akin tare da Ummie da me yi masa magana. Idanuwanta ne suka sauka a Kansas, yana zaune ya dafe kansa hannunsa na jini dan ya cire har cannula da aka saka masa. Sunan Mama da Yusuf ta kira da k'arfi tana k'arasawa inda yake, kokati rike hannunsa me jini takeyi amma ya kwace yana zuba ma ta wani mugun kallo. Jinin jikinta tasha, a sanyaye ta mik'e Idanuwanta na cikowa da hawaye.

Yar rigeยฒ sukayi shi da Mama, ganin Farooq a zaune ba karamin dad'i suka ji ba, da sauri Mama ta nufeshi bayan tayi wa Allah godiya.

Zama tayi kusa dashi tana rik'e hannunsa dake zubar da jini ta ce " Yusuf kira likita"

Hannun Yusuf na rawa ya zaro wayarsa a aljihu yana latsa kira.

Mama sai shafa Farooq takeyi da ya runtsa idanunsa, abubuwan da suka faru har harbinsa da akayi, da sauri ya bude idanunsa yana shafa kirjinsa, aikuwa da dinki nan a kirjinsa har ya warke.

Kallon Mama yayi ya ce " Jiya?

Mama na kara danne inda jini ke zuba saboda ya tsaya ta ce " Ba jiya bane Farooq! Wata d'aya ne kawai babu a shekara" Ta k'arashe maganar hawaye na biyowa kuncinta.

Yusuf ne y dawo gefensa yana zama tare da fad'in "Sannu"

Kallonsa yayi yana dan yi masa murmushi. Likitan ce ta shigo tanayin sallama. Murmushi ne ya ziyarceta lokacin da ta ga Farooq a zaune.

Kara sawa tayi tana fad'in "Godiya ta tabbata ga Allah, Sannu Farooq ya jikin? Yanzu kana jin wani abu ne?

"Bana iya taka kafata" Cewarshi yana kallonta.

"Hakan na faruwa sakamakon rashin tafiya da bakayi ba har na tsahon shekara , amma hakan ba abun damuwa bane akwai magungunan da zaka sha sannan zaka dinga amfani da crouches na 'yan wasu lokutan nan da week daya komai zai dawo daiยฒ insha Allah"

Godiya Mama tayi ma ta sannan ta tafi bayan ta rubuta prescription na maganin.

A sanyaye Ummie ta nufi bakin kofa zata fita, Mama ce ta kira sunanta tana k'arawa da fad'in " Ina zakije?

Kasa rik'e hawayenta tayi aikuwa ta fashe da kuka me karfi tana ficewa da sauri. Kallon-kallo Mama da Yusuf sukayi kowannen su cike da mamaki.

" Uncle Farooq me tazo zata rik'e hannunsa shine fa ya kwace ya harareta" Cewar Sabir yana komawa bayan babansa dan yasan kad'an daga aikin Farooq ya dakeshi.

"Farooq kenan! Bari kaji a wannan zamanin dai wallahi samun mace irin Ummie abune mai wahalar gaske kaji ko? Kuma dole kayi accepting dinta if not zaka ga fushina sosai"

Ta shi tayi ta fuce daga d'akin. "Taso kayi brush yanzu zan kawo maka abinci kaci sai kayi wanka" Cewar Yusuf yana rikeshi.

Shi ya rakashi bandakin sannan ya fito, sai da yayi wanka Yusuf ya bashi kaya marasa nauyi ya saka sannan ya fito.

Yusuf na bashi abinci a baki ya ce " Anjima ko daddadare ne sai muje a aske sumar kanka tayi yawa"

"Hakane, but meyasa na gemu be taru ba?

"Ummie ce take aske ma ka shi na kan kuma Likita tace kar a taba a rabu da kai"

Farooq be kara cewa komai ba dan har da hammata da dayan wajen ba gashi sosai he hope cewa ba waccan yarinyar ce tayi masa ba.


Bayan ya gama cin abincin kiran Zayd ya shigo wayar. Dauka yayi suka gaisa daga daya b'angaren Zayd ya ce " Gobe by 9am akwai meeting da wasu client dinmu na America kuma suna bukatar kaje"

"Ohk" Yusuf ya amsa masa. "Yawwa ya jikin Farooq any improvement?

Sai da ya kalli Farooq dake kallonsa dan yana jin abinda ake fada.

"Farooq ya farka" Cikin murna Zayd ya ce " Masha Allah ny greetings please kafin nazo"

"OK zaiji, ya Zarah? Sunan Zarah da Yusuf ya ambata yasa Farooq kara maida hankali kan wayar da sukeyi.

"She's fine, ai munyi fushi bazaka zo kaga Khaleel ba"

"Sorry Zayd kasan yadda nake fama da ayyuka amma soon zanzo "

"Ok toh bye" Daga haka ya katse wayar.

"Zarah ta kara haihuwa ne? Ko kuma dan Zayd ne? Cewar Farooq

"Eh d'an Zayd ne tare da Zarah"

Zaro ido Farooq yayi ya ce " Zayd da Zarah kuma?
"Eh, ai sun rabu da tsohon mijinta Zayd ya aureta, duk da cewa Zayd ya rasa kafafunsa amma bata gujeshi ba kuma just 4 days da aurensu hakan ta faru"

"Aure?! Farooq ya maimaita kalmar. "Eh aure fa Farooq idan ma zaka rike matarka ka riketa sosai dan Zarah tayi maka nisan da bazaka taba kamota ba! Kuma kasani Mama bata sonta and yarinyar deserves to be happy saboda tasha wahalar a rayuwarta aurenku kuma bana tunanin zai saka ta cikin farinciki ina so ka koyawa kanka son Ummie ko dan tarbiyyarta, hankali da nitsuwarta nasan insha Allah bazakayi nadama ba"

Kasa cewa komai Farooq yayi zuciyarsa gaba daya babu dad'i.

*NIGHT*

Bayan sallar magariba Zayd ya dawo, a zaune yaga Zarah ta zuba uban tagumi. Bai ce da ita komai ba dan yayi tunanin abinda ya faru jiya ne yake damunta.

D'akinsa ya wuce, Aunty ce ta fito daga dakin tana fad'in " Yawwa gwanda daka dawo gata nan tun safe taki sanar dani me yake damunta taki cin abinci yaron ma da kyar take bashi nashi abincin.

Kallon Zarah yayi ya ce " Lafiya kuwa me yake damunki"

"Ina Ummie? Zarah ta fada tana kallonsu. "Tana d'aki wai karatu take nasan dai game takeyi"

Aunty ta bata amsa. "Ummie! Ummie! Zarah ta kira sunanta da k'arfi. Amsawa Ummie tayi kafin ta fito da sauri tana fad'in "Gani"

"Zonan" Zarah ta fada tana kallonta. K'arasawa tayi inda Zarah take.

"Fad'a mine abinda kika fad'a jiya"

Shuru Ummie tayi cikina na kugi indai ta bari kowa ya sani Abba kasheta zeyi kamar yadda ya fad'a! Duk abinda ta fad'a Abbane ya shirya ma ta duk da Saleh yana tab'a ta amma ba kamar yadda ta fadawa Mamanta ba Abba ne ya kara gishiri da maggi a kai.

"Nidai bazan fad'a ba" Ummie ta fada cike da tsoro.

Tashi Zarah tayi ta nufi kitchen da wuka ta dawo tana kama hannayen Ummie ta ce " Zaki maimaita ko sai yanka ki munsha romo?

Sosai yanayin Zarah ya bawa Ummie tsoro bakinta na rawa ta ce " Karya nakeyi wallahi Abba ne yace na fad'a miki haka, zaki dawo zama tare da my Dan Allah Ummana ko dawo" Ummie ta karasa fad'a hawaye na biyowa kuncinta.

"Wai me ya faru ne? Zayd ya fad'a yana kallonsu. Duk abinda Ummie ta fad'a ma ta haka ta zayyane musu tas sannan ta kara da fad'in " Shehu bashi da hankali wallahi da zuwa yayi ya nemi in koma ko da yarinta zan iya komawa amma sai ya fadawa yarinta tsassauran kalamai! Ya koya ma ta karya saboda biyan bukatar sa?

"Ummie tafi d'aki" Aunty ta fad'a tana kallonta, aikuwa da sauri ta koma daki tana ajiyar zuciya.

"Sai hakuri ai" Cewar Aunty tana zama a kujera.

Ajiyar zuciya Zayd ya sauke kafin ya ce " Ki shirya zamuje gidan Sir Farooq ya farka"

"Toh" Ta amsa ba tare da kalleshi ba.

Daki ya wuce kusan 5mins sannan Aunty tabi bayansa.

Bayan sallar isha'i suka shirya har Ummie da Khaleel Aunty kadai aka bari a gidan.

"Dagaske zaki iya komawa gidan Shehu?
"Eh! Saboda Ummie ba" Ta fada tana kallon titi.

"Shi kuma khaleel fa? "Shi ai bani da matsala akan tarbiyyarsa"

Ta kuma bashi amsa ba tare da ta kalleshi ba. "Hmm amma Zarah inaso kiyi hakuri a maida aurenmu"

Da sauri ta juyo tana hararsa, har zuciyarta tana son komawa dan tana son Zayd amma ba yanzu ba sai ta gasa masa aya a hannu.

"Zaki ko ma? Ya fad'a yana kallonta. Parking d'in da driver yayi ya saka ta kallon window. Har sunzo gidan.

Fitowa sukayi suka shiga. Ummie sai surutu takeyi wai nan ita da kaninta take magana.

Kiran Yusuf yayi in seconds ya fito bakinsa a washe.

Isowa yayi inda suke kafin ya ce " Sannunku da zuwa"

"Ina yini? Ummie ta fad'a tana durkusawa kadan (Gaisuwa me spring lol..)

Amsawa yayi yana shafa kanta ya ce " Hi beautiful lady"

Washe baki Ummie tayi dan tana so a ce ma ta beautiful.

Kallonsa Zarah tayi ta ce " Ina yini?

"Lafiya lau Fatima Zarah! Yusuf ya amsa yana sakar ma ta murmushi. "Toh a bani babyn! Ya fada yana mik'a ma ta hannu. Khaleel ta dora masa a hannun yaron sai dariya yake wadda hausawa suke cewa dariyar k'uda.

"Masha Allah, yaro yayo kyan Mamansa"

"Me kake nufi? Nidin mummuna ne?

Zayd ya fada yana kallon Yusuf. "Toh second Sabir,ka manta lokacin da aka haifi Sabir me ka ce?

Shuru Zayd yayi daga bisani ya yi murmushi ya ce " Baka da dama wallahi! Wato ramawa kayi?

"Sosai ma" Yusuf ya fad'a yana dariya.

"Mu shiga daga ciki ko" Ya sake fada yana yi musu iso zuwa falon.

*Manage yau banda lafiya*

*Free to contact me here is my number 08142904255*


Autar Mama ce
โœจโœจ *UMMIE* โœจโœจ

_Labari daya danganci soyayya da kuma ฦ™alubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 29" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1193678142?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=8kmIwzqyoEc1w4To2mDwx%2FO9etsrgqeVbsA1%2FLfHKNxMhyngsYhTxPYI9kRp4RJupwv3l4IgaLVjKI8CQkjJK3Tq1GGfbQPndNauIJOaPa%2FhXwq9wcgTZA%2FrKHxZCu53

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta ฦ˜awaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only๐Ÿ‘Œ*

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: ๐™ˆ๐˜ผ๐™ˆ๐˜ผ๐™‰ ๐™‰๐™๐™Ž๐˜ผ๐™„๐˜ฝ๐˜ผ,,๐™„๐™†๐™„๐™‡๐™„๐™ˆ๐˜ผ ๐˜ผ๐˜ฟ๐˜ผ๐™ˆ(๐™ ๐™ฎ๐™–๐™ช๐™ฉ๐™– ๐™™๐™–๐™œ๐™– ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*๐™ˆ๐˜ผ๐™ˆ๐˜ผ๐™‰ ๐™‰๐™๐™Ž๐˜ผ๐™„๐˜ฝ๐˜ผ* tazo muku da littafin (๐™†'๐˜ผ๐˜ฟ๐˜ฟ๐˜ผ๐™๐˜ผ ๐˜พ๐™€)

๐™„๐™†๐™„๐™‡๐™„๐™ˆ๐˜ผ ๐˜ผ๐˜ฟ๐˜ผ๐™ˆ( ๐™†๐™ฎ๐™–๐™ช๐™ฉ๐™– ๐™™๐™–๐™œ๐™– ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™) tazo muku da littafin (๐™†'๐˜ผ๐™‰๐™’๐˜ผ๐™๐˜ผ)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.

*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...


*K'ANWATA*

*Dandano!Dandano!!*


Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..


Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573


Nomal. guda d'aya N 300 ne

guda biyu N 500 ne


Special guda d'aya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne


Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

โœŒ๐ŸผFitattu biyu masu ban mamaki๐Ÿซ€Hakika babban goro sai magogin ฦ™arfe ๐Ÿ˜, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka๐Ÿซ, Fitattu biyu๐Ÿ‘ฏ๐Ÿฝโ€โ™€sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku ๐Ÿค“ sun shirya tsaf domin fadakar daku๐Ÿง  sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so๐Ÿ’‹๐Ÿ’ž, wohoho tabbas ๏ธsahun giwa๐Ÿ‘ฃ mai ษ“adda na raฦ™umi ๐Ÿช,Fitattu biyu๐Ÿ˜โœŒ๐Ÿผ masu tafiyar k'asaita, sheฦ™i, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka๐Ÿ˜˜๐Ÿƒ๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ Fitattun ฦ˜arshen shekara๐Ÿ˜ salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta๐Ÿ˜ maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari๐Ÿƒ๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*โœ๐Ÿฝ Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* โœ๐Ÿฝ Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ
Vip 700๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Shafi na ashirin da tara*

Sabir kad'ai suka tarar a falo yana aikin makaranta. Bakinsu d'auke da sallama suka shigo falon. Juyowa Sabir yayi yana kallonsu kafin ya amsa sallamar da sukayi.

Wajen zama Yusuf ya nuna musu yana fad'in "Bismillah ku zauna bari na kawo muku abin tab'awa"

Murmushi kawai Zayd yayi yana matso wa kusa da Zarah da Ummie dake zaune kan kujera.

"Ina yinin ku? Cewar Sabir yana kallonsu. "Lafiya lau handsome boy, ya makaranta"

"Alhmdll" Sabir ya amsa yana wanshare baki.

Da tray Yusuf ya dawo yana janyo table ya ajiye sannan ya ce " Bismillah, bari na kirashi"

Daga haka ya nufi upstairs. Ruwa kawai Zarah ta sha Zayd be sha komai ba. Ummie ce ta kalli Zarah ta ce " Ummana zanci" Ta karashe maganar ta na nuna cookies din dake kan plate akan tray.

" Ci mana, after all u are our guest! Sabir ya fad'a yana kallonta. Banza ta masa tana jira amincewar ummanta. Murmushi Zarah tayi ta ce " ki ci" Dariya Ummie tayi sannan ta dauka ta fara ci.

"U idiot! Sabir ya fad'a yana harararta dan ya tsani yayi magana ayi masa kunnen uwar shegu.

" Allah ya isa" Ummie ta fada tana zuba masa harara da manyan idanunta. "Ya isa haka sarkin masifa! Zarah ta fad'a tana zarewa Ummie ido.

Kwasar litattafan sa yayi ya nufi upstairs da sauri.

Yusuf na rike da Farooq suka sakko, Mama kuma a bayansu. Tun isowarsu Falon ya kasa d'auke idanuwansa a kan Zarah! Shi kham Allah y dora masa wani masifaffiyar soyayyarta baya jin bayan Mama da Yusuf akwai wanda ya kai Zarah a zuciyarsa, tas Zayd na lura dashi! Yasan dai basu san cewa sun rabu ba dan ko Sir Yusuf bai fadawa ba! Kuma baya jin zai fada masa dan tsaf Farooq zai iya zuwa neman aurenta kuma in har Farooq ya auri Zarah ko giya yasha bazai saketa ba dan yana hango tarin soyayyar da yake yi ma ta, tabbas yasan yayi kuskure amma zai gyara kuskurensa dan yana matukar kaunar Zarah yayi dakon soyayyarta na kusan 11yrs"

"Zayd! Tunanin me kake yi haka? Yaji muryar Yusuf. Da sauri ya kalleshi sai kuma ya sosa keya ya ce " Bakomai kawai ina tunanin yadda project da presentation akan deal din mu da client d'in Ametica zai kasance"

"Zayd kenan sarkin aiki" Yusuf ya fada yana murmushi.

"Hajiya Ina yini? Murmushi d'auke kan fuskar Mama ta amsa tana karawa da fad'in " Ko sau daya Yusuf be sanar dani abinda ya faru da kai ba! Ya jikin naka? "Da sauki sosai Hajiya, dan yanzu ina samun improvement sosai"

"Toh Masha Allah please don't bother your self da kudin siyan magunguna idan ya kusa karewa ka kira Yusuf, tabbas bamu da abinda zamu biyaka sanadiyar Farooq ka shiga wannan halin kayi hakuri"

"Dan Allah Hajiya ki daina sani jin kunya haka dama Allah ya tsara" Zayd ya fad'a yana murmushi.

Kan Zarah a k'asa ta gaida Mama. Amsawa tayi fuska a sake. Ummie ce ta sakko sanye da hijabi har kasa, idanunta ne ya sauka a kan mijinta yana kallon matar wani! Irin kallon da yake yi wa Zarah ne ya saka taji wani abu ya tokare wuyanta. Da kyar ta iya karasowa suka gaisa a sanyaye ta koma.

A gab an Farooq Yusuf ya tsaya yadda zai kareshi daga kallon Zarah dan yaga kamar hankalinsa ya gushe.

Itama Mama basu waje tayi.

"Farooq ya jikin? Zarah ta fad'a tana kallon saitin da yake. "Yusuf matsa daga gabana" Farooq ya fada ransa a bace. Ya san halin Farooq zai iya bashi kunya ya fito da abinda yake ransa hakan yasa ya matsa.

"Ya jikin? Ummie ta fad'a tana kallonsa. Idanunsa ya mayar kanta, murmushi yayi kadan ya ce " Da sauki cute baby like mother like daughter"

Da kyar Zayd yake hadiyewa.
"Allah ya kara sauri" Zayd ya fada yana kallon Zarah ya d'ora da fad'in " Mu tafi ko? Dare na karayi"

Bata ce dashi komai ba ta tashi tana gyara khaleel dake hannunta. " har bakin gate ya rakasu kuma ya sanar dasu cikin week dinnan zaizo saboda Khaleel.

Yana komawa Falo ya tarar da Farooq ya hade rai. Shima hade nashi fuskan yayi ya ce " Ka kyauta kenan? Kana abu kamar karamin yaro! Kasan fa matar aurece! Idan kaine wani yake kallon Ummie yadda ka dinga kallon Xarah zakaji dadi?

"Ummie? Wallahi ban damu ba! A kalleta mana! Bana sonta kuma bazan taba sonta ba! A da chan ina ma ta son 'yan uwantaka amma yanzu babu wannan! Wallahi duk wanda ya kara min maganar Ummie sai na saketa! Ina da wadda nake so a zuciyata idan kuma bansameta ba bazanyi aure ba!

'Ok wanna auren da kake da shi fa? Yusuf ya fad'a yana yi masa wani kallo. "Kai ka d'aukeshi a matsayin aure! Ni bani da aure dan wallahi idan akamatsa min zan bar kasar kuma na saketa dama ba sonta nake ba, ni babu macen dana tsana a duniya kamar Ummie!

A bun da Mama ta bata ta kawowa Ummie ne ya fado daga hannunta ya fashe, kararar fashewar kwalba ce yasa dukannin su suka juya. Ummie ce tsaye hawaye na bin kuncinta.

Dafe goshi Yusuf yayi dan yanayinta ya nuna cewa taji abinda suke cewa"

Farooq kuwa ko a jikinsa. "Kaga abinda ka janyo ko? Cewar Yusuf yana kallonsa.

"Sai me? Idan taji haushi taje ta sami Mama ta ce a raba auren, idan tasan ita din macece yar gata kamar yadda ta taba fada min"

Ummie bata ce komai ba ta juya ta nufi daki zuciyarta a dagule.

"Farooq inaso ka gane wani abu guda d'aya! Itafa Zaran da kake so matar aurece! Zayd da kake gani ko haukacewa yayi bana jin zai saki Zarah saboda yana sonta tun kafin tayi auren fari, kuma itama alamu sun nuna tana sonsa! Baka cikin tsarin rayuwarta! Farooq ba son Zarah kake ba! Da ace sonta kake bazaka so ka aureta ba tunda har tana cikin farinciki da aurenta kuma ka sani sarai Mama bata sonta a matsayin daughter in law, she deserves happiness yarinyar tasha wahala meyasa kake so ka kuma sakata cikin wahala bayan kasan ga inda zata samu farinciki?

"Ni ne zan bata wannan farin cikin! Baka ganin damuwa a tattare da ita? "Farooq meyasa ka fiya taurin kai ne! Wani irin mutunne kai? Mace da aurenta? Ka haukace ne?

"Eh na haukace! Na haukace Yusuf! Soyayyar Zarah ta haukata ni! Nace na haukace indai a kan Zarah ne! Ya fad'i maganar da iya karfinsa. Hakan yasa sauran members na gidan suka fito har Sabir da uwarsa kowa da kowa.

Sakkowa k'asa sukayi suna kallonsu. Kowanne ransa a b'ace. Cikin fushi Yusuf ya ce " Kaje kayi duk abinda zakayi tunda baka da hankaki kuma kasan abinda kakeyi ba daiยฒ bane ko a addini! Kaje ka aureta tana da aure tunda ka fara shayeยฒ"

"I will! Zan aureta! Kuma zaka gani! Daga haka ya tashi yana daukar chroches dinsa ya fara tafiya. Cikin takaici Yusuf ya daki kujera da kafarsa ransa ya b'aci sosai! A baya shima ai yaso Zarah said dai be bari soyayyar ta cinye masa zuciya ba saboda yasan kaninsa yana so! Meyasa shi bazai rarrashi zuciyarsa ba? Meyasa? Bayan yasan ita din matar wani ce? He pray kar Farooq yayi abinda zai sa kanshi a uku'

"Wallahi Mama ba mamaki asiri tayi masa dan taga dan masu kudi" Cewar Ramlah tana son kara kunna wutar. Banza Mama tayi ma ta dan ta fara tausayawa dan na ta a kan wahallalliyar soyayyar da yake fama da ita.

Bayansa tabi,cikin takaici Ramlah ta kama hannun Sabir suka wuce sama.

"Yaya wacece ita? Ummie ta fad'a tana goge hawayen idanunta. " Bashi da amfani idan kin sani! Ki dai bishi a hankali dan naga bashi da hankali zai iya sakinki"

"Ko jai sakeni ba ni bazan iya cigaba da zama dashi ba, gida zan koma bana sonshi idan kuma aka takura min wallahi said na shiga duniya"

Da sauri ya kalleta, sai kuma ya saki fuskarsa yana kallonta ya ce "kema rashin hankalin zaki gwada min? Ki shiga duniya? Ke! Kinsan me shiga duniya kuwa? Bar ganin kina da aure zaneki zanyi idan na kara jin kinyi wannan maganar",

Kallonsa tayi hawaye masu zafi na zubo ma ta. Matsowa yayi kusa da ita yana kallon yadda hawaye ke zarya a idanunta. "Ummie please... Kafin ya karasa ta rungumeshi da karfi tana fashewa da wani kuka me d'acin gaske. "She wish ace Yaya Yusuf aka aura ma ta ba Yaya Farooq ba! Wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana kokarin rabata da jikinta amma taki barin hakan ta faru sai kara rikeshi takeyi.

"Me haka Ummie? Nifa yayan mijinki ne! Is unfair sakeni please! Shuru tayi tana shesshekar kuka. "Kuka ya isa haka, but please kaki kara hugging dina haka kinji ko? Please"

A hankali ta sakeshi tana goge hawayen fuskarta bata ce dashi komai ba ta wuce sama da sauri shi kuma yabi bayanta da kallo zuciyarsa ba dad'i.

Babu irin rarrashin da Mama ba tayi wa Farooq ba amma yaki sauraronta dan yau ganin Zarah ya kara fama masa ciwon dake zuciyarsa ya dawo danye.

Gajiya Mama tayi amma ta kuduri niyyar zata je ta samu Zayd. Ni kuwa nace ki sameshi kiyi masa uwar me๐Ÿ˜.

*Manage please*
*Har yanzu banda lafiya*

*Masu nema na ga number na 08142904255, i promise zan dinga sakawa a karshen ko wani page ngd d kauna da kulawa*

*Naji dadin ydd kuke son book din gdy dubu dubu*

Autar Mama ce
โœจโœจ *UMMIE* โœจโœจ

_Labari daya danganci soyayya da kuma ฦ™alubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa

Please Login or Register in order to submit comment