Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan gaisawa"

"Gaisawa? Wai me yake damunku ne kai da Kaninka?

Hannunta ya riƙe ya ce " Mama not now please sai mun dawo"

Daga haka ya saki hannunta ya fita ya barta cike da jin haushin Zarah ganin ta mallake ma ta zuciyar yara musanman ma dai Farooq da yake sonta kamar zeyi hauka, ta samu da kyar ya dawo dai² shine Yusuf yake kuma kokarin kulla wata alaƙa da ita?

Kwafa tayi ta koma kujerar ta zauna ranta duk a ɓace.....

Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 6" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1171239230?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=4Y2gQG0j84rehZe0yQn4KxIg78D3ngmIhYq24zcNRKOKXwtocd5hCuRlkyL0kgQJAHwrhIILXMvByIdlDHcgw7DahgIvfa2Z%2F4SVGo%2BVI82gmUGNQSfrPkTmbF6q8pX8

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*

*Shafi na shida*

" Farooq wai me kake yi a ɗaki ne?
Karamin tsaki ya saki yana kallon Yusuf ya ce " Hutawa nake sonyi"

"Ok but abinci fa? Ko na kawo maka nan? Room slippers dinsa ya cire yana kwanciya a kan gado tare da jan duvet ya rufe jikinsa.

A kusa dashi Yusuf ya zauna yana taɓa kansa ya ce " Me yake damunka?

Lumshe idanunsa yayi yana furzar da iska kadan ya ce " Bakomai"

"Nothing? Kana tunanin zan karbi nothing a matsayin amsa?

Yusuf ya faɗa yana kalllonsa. Tashi zaune yayi yana riƙo hannun Yusuf ya ce " Dawowata Nigeria yasa komai ya dawo min sabo! Bana tunanin zan iya cigaba da zama Yusuf! Banaso ya kasance ina tunanin abinda bai dace ba"


Dafa kafadarsa yayi cikin son kwantar masa da hankali ya ce " Dama shi haka so yake, yana shiga faradɗaya amma yana daukar shekaru kafin ya fita gaba ɗaya wani lokacin ma baya fita gaba dayan sai dai ya ragu, inaso ka cire komai a ranka ka manta da dasuwar soyayyarta a zuciyarka lokuta da dama muna son abinda bazai zama alkhary a gare mu ba, ka cigaba da addu'a perfect match Dinka tana nan zuwa insha Allah"

Ture hannun Yusuf yayi daga kafadarsa yana faɗin " Bazan iya ba!

Daga haka ya tashi ya saka slippers dinsa ya bar ɗakin.


Ƙasa ya sakko ransa duk babu dad'i. Mama data fito daga kitchen yanzu hannunta riƙe da tray din abinci.

Karasowa tayi inda yake yake tana ajiye empty tray din a gefensa ta ce " Me ya faru naga kamar ranka a ɓace?
"Bakomai" Ya faɗa kamar anyi masa dole.

"Saboda Zarah ne, bansan menene matsalarsa ba matar nan tana da aure 8yrs da aurenta amma ya kasa cireta a ransa"

Yusuf ya faɗa yana karasa sakkowa daga stairs ɗin.

"Ai kuwa ko da ace yau mijinta mutuwa yayi bazan taba bari ya auri widow ba gwanda ma ka cire rai da ita! Nan da wata biyu ma zamuyi maka aure!

"What? Ya faɗa cike da mamaki.
"Sosai ma kuwa Farooq! Kuma *_UMMIE_* zaka aura ƴar Aunty ƙarama"

Da sauri ya tashi tsaye yana kallon Mama ya ce " _*UMMIE?*_ "Tabbas, da so nake ka huta sai muyi magana amma tunda ka zabi na faɗa ma ka yanzu gashi na faɗa ma ka kuma ka shirya gobe kaje wajenta"

"Mama UMMIE fa kika ce? That 18yrs old child?
"She's not longer a child Farooq! Kuma ko 10yrs gareta ba 18yrs ba wallahi sai ka aureta kaji m na rantse tunda baka da kirki"

Mama ta fada ranta a ɓace. " Calm down Mama, abun bai kai haka ba ai basai kin bata ranki ba"

Tashi tsaye Farooq yayi ya nufi sama da sauri. Zaunar da Mama Yusuf yayi yana fadin " Mama da kin bishi a hankali kinsan yaro ne"

"Yaro? Yaro fa ka ce 32yrs din ne yaro? Da ace yayi aure lokacin daya dace da yanzu dansa yayi wayo ba?

"Mamaa, shifa aure lokaci ne, idan lokacin yinsa yazo dole ayi shi"

"Bani ruwa Nasha" Mama ta fada tana kalllonsa.

A dining ya dauko ruwa mara sanyi tare da cup. Shi ya zuba ma ta ruwan ya bata tasha a tajiye a hannun kujera. Dauke cup din yayi yana faɗin " Ruwan ya isa?

Kai ta daga alamar eh sai kuma ta kalleshi ta ce " Yaushe yarinyar nan zata dawo ne?

Shuru yayi yana shafa kanshi dan Mama bata san cewa Yaji Ramlah tayi ba saboda yace bazai rabata da uwarsa ba ita kuma wai yanzu ta gaji da zama da surukarta duk kawayenta gidansu daban dana sirikarsu.

"Kayi Shuru" Mama ta fada tana kalllonsa.

"B..bansani ba"
Ya faɗa yana nufar dining.

"Bangane baka sani ba? Kai kwana nawa ka bata? Yau kwananta uku fa"

"Zan kirata na tambayeta" Daga haka Mama bata kara cewa komai ba.

★★★★

Cikin nutsuwa ta ke wanke kayan, a zahiri dai gata a zaune tana wanki amma kana kallonta kasan hankalinta baya tare da ita.

'Ta yaya zata zubar da cikin dake jikinta? Ta yaya zata bar rayuwar yarinyarta ta lalace ba arabi ba boko? Anya Shehu yasan me yake yi kuwa? Yasan me yake damunsa? Shi haka aka barshi ba arabi ba boko?


Saukar ruwan da taji a fuskarta shi yasa ta dawowa daga duniyar tunanin da ta shiga. Cike da mamaki take kallon Zainab kafin ta saki murmushi tana kokarin tashi tsaye. "Zauna abunki, ai ke wannan sai a shigo a sace ki baki sani ba"

Zainab ta faɗa cikin raha.
"Uhm, mu shiga daga ciki"
Zarah ta faɗa tana goge hannunta jikin zaninta.

"Kinga ni dai ki barni na shiga na ajiye kayannan sai na fito muyi wankin tare"

Zainab bata jira cewar ta ta shiga cikin falo ta barta a compound din gidan.

Bata dade ba ta fito tana fadin " Kawo nayi saɓi ke sai ki dauraya ki shanya"

Murmushi Zarah ta yi ta ce " Toh"

Basu dade ba suka gama wanki wanda duk yawanci kayan Shehu ne dan mugunta ya daina kai wanki ita take wankewa ta goge ta jera a closet.

Sai da suka gama sannan suka shigo falon.

"Ina UMMIE ta?

"Bata jin dadi tana ɗaki"

Zara ta faɗa a sanyaye.
"Me ya sameta? Cewar Zainab tana tashi tsaye.

"Zazzaɓi ne kuma tana complaining kanta na ciwo"

"Ok muje na ganta"
Zainab ta faɗa tana nufar dakin Zarah.
A kwance ta ga UMMIE sai hawaye takeyi.

Da sauri suka karasa. Zarah ta tallafo kanta tana fadin " Menene Mamana?

"Ummana kaina ciwo yake min kuma jikina yayi zafi dayawa, Ummana bana so na mutu"

Murmushi Zainab tayi tana fadin " Ba'a mutuwa sai kwana ya kare, kuma cuta ai ba mutuwa ba ce, zaki samu sauki insha Allah, Yawwa Zarah wani magani kika ba ta?

"Paracetamol" Zarah ta ba ta amsa. "Ok da kika je chemist ba'a rubuta allura ba?

"Bamuje ba Zainab! Be bani kudin ba"

Zarah ta faɗa tana goge hawaye da suka zubo ma ta. Cikin masifa Zainab ta ce " Wai ke wace iriyar macece ne Zarah? A kanki aka fara mutuwar aure? Wallahi da wannan auren gwanda babu! Ke kinfi damo ma hakuri! Wallahi gwanda ya sakeki ki huta ga masu san aurenki"

"Su waye Zainab? Bani da inda yafi min gidan mijina"

"Zarah ni bawai na ce ki nemi saki ba ne kawai dai ki dawo gida nasan da kanshi zai sakeki! Mutumin nan baya kaunar ki! Ace jikin yarinyar nan yayi zafi har haka amma ko kuɗin kaita chemist be baki ba? Me yake damunki ne? Ba komai ake yi wa hakuri ba wallahi, dubi jikinki duk shatin duka! Dubu goshin UMMIE a kumbure kuma nasan shine ya bigeta, wani irin so kike wa mutumin nan?

Share hawayenta tayi ta ce " Nima yanzu bana sonsa Zainab amma shi ɗin uban yara na ne! Bani da kamarsa, kinsan kuwa yadda duniya take kallon zawarawan mata? Zainab gwanda na zauna gidan mijina duk rashin dadinsa yafi min zaman zawarci"

"OMG! Zarah wallahi bawai yabon kai ba amma na tabbatar kiki kina fita daga iddah dan uwana zai nemi aurenki"

Cike da mamaki Zarah ta ce "Dan uwanki?
"Yes! Zarah Zayd ya dade yana sonki tun kafin ki hadu da wannan mugun mutumin kawai Allah beyi bane ya kasa furta miki kinsan halinsa kinsan yadda yake amma nayi mamakin yadda kika kasa fahimtarsa"

"Na fahimceki Zainab, kawai kice na kashe aurena na auri yayanki"

Zarah ta faɗa ranta ba dad'i.

"Zarah me kike tunani ne? Meyasa zan ce miki haka?

Banza Zarah tayi ma ta tashiga toilet.

Lokacin data fito bata tarar da Zainab ba, ajiyar zuciya tayi ta ajiye robar hannunta ta kalli UMMIE da bacci ya kwashe ta. Towel ta fara dora ma ta akanta. Aikuwa a firgice ta tashi tana sakin kuka. Da rarrashi zarah ta goge ma ta jikinta har zafin ya ragu. Tana shirin komawa banɗaki sai ka Zainab ta shigo.

Kallon zarah ta yi ta ce " Taci abinci?

"Bata ci komai ba"
Zarah ta bata amsa.
"Ok, ki bata ko koko ne sai na ma ta allurar"

"Kallonta tayi ta ce " a ina kika samu kuɗi kika siyo ma ta allura?

"Wanda ya damu da ita ne ya bayar! Ta bata amsa a kufule tana miƙa ma ta ledar magungunan kafin ta kara da fadin " Komai an rubuta yadda za'a ba ta, kullum zan dinga zuwa ina ma ta allura"

"Ina Zayd ɗin? Zarah ta faɗa tana kallonta.

"Zai tsaya ne? Kina so ya tsaya mijinki ya ce yazo kwartanci?

"Zainab Please! Zarah ta faɗa tana daga ma ta hannu.

Cikin takaici Zainab ta ce " Ke kika sani! Kiyi ta zama yana baki kashi, ki tashi ki hada ma ta koko nayi ma ta allura kuma ka kaya chan Zayd da Aunty sunce a kawo miki, kuma bikina ansa wata uku"

"Allah ya kaimu ya sanya alkhairy, jinkirin ya zame miki alkhary Zainab, Allah yasa kinyi dacen miji"

"Amin" Zainab ta faɗa ba tare da ta kalli Zarah ba.

"Bani da gasara kuma ya hanani fita ko zaki bawa gateman ya karbo miki?

"Kawo kuɗin" Zainab ta faɗa tana kallonta.

"Bani dasu Zainab amma nasan yaya ai zata taimaki ƙanwarta ko? Kuma bazata bar ƴarta cikin ciwo ba"

Cike da takaicin halin Zarah da hakuri irin nata ta fice ba tare da tace komai ba.

Bata daɗe ba ta dawo tana ajiye gasarar a cinyar Zarah. Murmushi Zarah tayi ta dauka ta nufi kitchen.

Zainab na latsa waya Zarah ta shigo da cup a hannunta.

Sai da ya huce sannan ta tashi UMMIE ta bata, da kyar tasha rabin kofin Zainab tayi ma ta allura ta baya magungunan sannan ta koma ta kwanta wani baccin ya kuma dauketa Zarah na shafa dogon gashinta wanda ya kasance golden sosai.

"Kinsan me Zarah?
Zainab ta faɗa tana kallonta.

"Ina jinki"

"Kyau da kyau ne ya hadu ya bada kyakkyawa, gaskiya UMMIE kamar ba yar bahaushiya ba, ke kyanki har zuciyarki amma mijinki iya fuska ne"

"Hmm" kawai Zarah ta ce.

"Amma Zarah meyasa baxaki fadawa kanwar mahaifiyarsa abinda yake miki ba naga kamar tana sonki"

"Zainab kenan! Matar data canza? Ƙanwarsa ce fa kawai take sona yanzu, kuma sun koma Qatar, daga ni sai shi"

"Shikenan Allah ya gyara"

"Amin"

Wayar Zainab ce ta fara ruri. Ganin sunan Zayd ya saka ta dauka tana fadin " Har ka taso ne?

"A'a, kira nayi na fada miki ki tafi gida dan sai dare zan dawo"

"Ok bakomai ai babu abinda zanyi a gida idan ka dawo ka biyo mu tafi"

"Ok toh ya Zarah?
Sai a lokacin Zarah ta kalleta.

"Tana nan dai yadda ka santa" Zainab ta fada idanunta cikin na Zarah.

"Ok, sai addu'a kawai Allah ya kawo karshen wannan lamarin, ya jikin UMMIE?

"Jiki da sauri ta samu bacci gashi sai gumi take zazzaɓin ya sauka ma"

"Masha Allah, toh ki gaishe da Zarah idan kuma tana kusa ki bata wayar"

Zainab bata ce komai ba ta miƙawa Zarah wayar. Hannunta na rawa kaɗan ta karbi wayar tana tuno kalaman Zainab "Yes zarah Zayd ya daɗe yana sonki tun kafin ki haɗu da wannan mugun mutumin....

"Hello Zee" Taji ya faɗa daga ɓangarensa.

"Ni ce"
Murmushi Zainab tayi dan tasan ba mamaki kalaman da ta faɗa ma ta Zayd ya daɗe yana sonta ke yi ma ta yawo a kai.

"Zarah ya jikin UMMIE?
"D..da sauki"
Ta bashi amsa tana kallon UMMIE.

"Ok toh Allah ya kara sauki, ki kula sosai kinji"

"Insha Allah"
Bai kara cewa komai ba ya katse wayar.

"Zarah wai haka kike zama ba waya?

"Kedai bari Zainab ni ba wannan ne ma dameni ba, ya ce wai UMMIE ta daina zuwa makaranta saboda ina samun damar fita sai na fa ke da zuwa dauko ta"

"Lallai ma wannan mutumin! Aikuwa bazai yu ba, ai ya ce ba yarsa ba ce ko? Toh zanyi wa Zayd magana idan kuma zaki bamu ita sai ta zauna tare da Aunty"

Da sauri Zarah ta girgiza kai ta ce " A'a, tana ɗebe min kewa sosai"

"Shikenan toh amma ina ganin hakan shine dai² saboda na farko zata samu ilimi mai kyau sannan kuma Kinga ko ba komai tarbiyyar ta zata gyaru duk da wasu abubuwan basu taba gogewa a kwakwalwarta ba, kuma bawai ina nufin baki ba ta tarbiyya bane a'a, kinsan halin mijinki! Be kamata ma ace tasan wasu abubuwan ba amma yanzu ta sani at 7yrs kawai"

"Hakane, shikenan zan faɗa masa"
Taɓa baki Zainab tayi tana fadin " Ni fa yunwa nake ji"

Itama Zarah tashi tayi tana fadin " Zainab inaso muyi magana a kan Zayd"

"Ok menene?

"Saboda ni yaƙi yin aure? Idan banyi kuskure ba zai kai 35yrs ko?

"Karki wani damu! Lokacin aurensa ne beyi ba, nima gashi ina cikin 30yrs zanyi auren fari!

"Hakane"

Zarah ta faɗa a sanyaye kafin ta ɗora da faɗin " Allah ya bashi mace ta gari"

"Amin, bakiyi girki bane? Zainab ta karashe maganar tana ɗan lauyewa.

"Banyi ba, muje dai yanzu mu dora"

"Kice dai baki da matsalar abinci?

"Hmm wallahi sai hakuri Zainab, kullum cikin shinkafa nake basir duk ya kamani wallahi kullum ba canji kuma ko dan fruit baya siyo min idan Kinga naci fruits toh ya gaji da jina a bushe ne"

Dariya Zainab tayi kafin ta ce " Kin ban dariya wallahi"

"Kedai bari muje kawai"

Zarah ta faɗa cike da damuwa.
Cikin tausayinta ta bita da kallo kafin ta ce " Allah ya saka miki ya kawo miki karshen wannan lamarin"

Bin bayanta tayi zuwa kitchen.

Babu komai sai shikafa ko miya babu. Kallonta tayi ta ce " Wai kullum ita kike ci? Tun safe har dare?

"Eh, amma wani lokacin yana siyo taliya da makaroni toh kwanaki ma ya siyo Nama kuma ya ɗan daɗe"

Jinjina kai Zainab tayi ta ce " Kwanaki kamar yaushe?

"Kedai mu bar maganar"

Zarah ta faɗa tana ɗora tukunya me ruwa akan gas.

"Kuma yana ci?

Zainab ta kara tambaya.
"A'a idan Kinga yaci abinci a gida toh yayi cefene"

"Ashe dai yasan baya adalci, bari kiga akwai 3k a hannu na yanzu bari naje nayi cefene sai muyi miya ki boye kya dan ji dad'i kwana biyu"

"A'a Zainab ki adana kudinki" Zarah ta faɗa tana riƙe hannunta. Kwace hannunta tayi ta fice daga kitchen ɗin.

Murmushi zarah tayi cike da jin dadin yadda Zainab take sonta.

Zainab ta daɗe bata dawo ba dan har Zarah ta sauke shinkafa ta zuba a kula.

Tana zaune tana tunani Zainab ta shigo da kaya niƙi² tana kallon Zahra ta ce " Zayd na kira ya aiko driver ɗin office dinku ya kaini kasuwa har da kudin ya bayar"

Tashi Zarah tayi baƙi bude ta kalleta ta ce " duk wannan kayan haka?

Ta karashe maganar tana karbar wasu ledojin daga hannun Zainab.

"Ai kece bakya faɗa nasan Zayd bazai taba barin ki cikin kunci ba da ace kina fada masa matsalarki da abun be yi miki worst haka ba kuma na faɗa masa maganar dawo da UMMIE wajen Aunty,Sannan ya ce .....

"Me wannan!? Suka jiyo muryar Shehu ya faɗa.....

Autar mama ce
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 8" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1172554033?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=pUrHe7li8HA5lqn8%2BBLqHvcYXZukfkQftmmBoOTh3ktzoU3nW2hrRK%2FY9LGH1LqJSeSF2Wu2IEBnrGaZ0ZGPYSa%2Ba4g13Z52Ry3%2F8YMktqqi%2FAaUeu%2F%2BA1jWAhmHfiX9

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*

*Shafi na takwas*

Idanu kawai ya zuba ma ta zuciyarsa na zafi sosai, a hankali yaga ta motsa idanuwanta. Da sauri ya taso yana fadin " Zarah"

Buɗe idanuwanta ta farayi a hankali tun tana ganin dishi² har ta fara ganinsa sosai, kanta taji yayi ma ta nauyi ga jikinta jishi duk a daddaure.

Kallon dakin tayi kafin abinda ya faru ya dawo kanta. "Ina UMMIE?

Shine abinda ta fara fada tana kokarin tashi zaune.

Aunty ce ta taimaka ma ta tashi zaune tana ɗan cije baki alamar tana jin ciwo.

"Sannu Zarah" Aunty ta fada cike da tausayinta.
"Ina UMMIE? Ta sake tambaya tana kallon dakin.

"Ummie tana wajen Zainab kuma tana lafiya, Zayd jeka kira likita kace ta farka"

Be ce komai ba ya fita daga daƙin.

Aunty na gyara ma ta pillow suka ji Knocking.

"Shigo" Aunty ta fada tana zama dan ta gama gyara pillon. Bakinsu dauke da sallama suka shigo, Yusuf ne a gaba sannan Farooq a baya ko wanne riƙe da lede.

Ƙasa tayi da kanta tana jin nauyi. "Bismillah ku shigo" Aunty ta faɗa tana tashi ta dauko tabarma wadda already a dakin take kasancewar private asibiti ne.

Shimfida musu tayi tana fadin. " ku zauna"

Sai da suka zauna ko wanne yayi zaman cin tuwo idanunsa a kan Zahra da kanta ke ƙasa har yanzu.

"Sannu da zuwa" Aunty ta fada tana kallonsu. Sai a lokacin suka kalleta suka ce " ina yini"

Amasawa tayi fuska a sake. Kafin Farooq yakara da fadin " Ya me jiki?

"Jiki da sauki Alhmdll Gashinan har ta tashi"

Be iya amsa ma ta sakamakon hankalinsa daya bar kanta ya koma wajen Zahra. Sosai ta canza ma sa yafi shekara biyu be ganta ba.

"Zarah sannu, ya jikin"
Cewar Yusuf yana kallonta.

Ba tare da ɗago ba ta ce " Da sauki"

Lumshe idanunsa yayi jin sautin muryarta. Dan taɓa shi Yusuf yayi dan yaga kamar baya hayyacinsa.

Numfashi ya sauke zeyi magana ZAYD da nurse suka shigo.

Kallonsu yayi ya ɗan haɗe ransa kafin ya ce " Har kun iso ashe"

Yusuf ne kawai ya iya amsa masa amma Farooq har yanzu ya kasa ɗauke idanuwasa akanta. Zayd na ganin hakan ransa ya kuma kuluwa shi baisan da wannan nataccen za'a zo ba da bai tura address din ba.

"Zayd! Yaji Aunty ta fada alamar ta daɗe tana kiransa.

"Na'am ya amsa yana kallonta. Girgiza kai tayi ta ce " Dauko magungunan da allurar da ka siyo"

Da toh ya amsa sannan ya nufi drawer yadauko su yana miƙawa nurse ɗin.

Allurar ta gyara sannan ta zuƙo tana kallon Zahra ta ce " Juya"

Sai a lokacin ta dan saci kallonsu Farooq taga duk idanunsu a kanta ya ke.

Kasa juyawa tayi duk da cewar bangaren da zata juya ba'a nan suke ba. Sauke idanuwansa yayi kasa yana ɗan sakin murmushi kaɗan abinda yakan dadewa beyi ba.

Shima Yusuf sauke nashi idanun yayi daga kanta. A hankali ta juya akayi ma ta allurar, magungunan ta bata ta sha sannan ta ce " ya kike jin jikinki?

"Da sauki dama ciwan bazai tafi lokaci daya ba"

Zarah ta faɗa a hankali.

" Hakane, ki kiyaye magunguna kinji? Insha Allah zaki samu sauki da wuri" Nurse din ta fada tana Murmushi.

Sallama tayi musu sannan ta fita.

Zayd ne ya gyara mata pillon ta yana fadin " me zaki ci?

"Bakomai" Ta fada tana lumshe idanunta.

Wayarsa ce ta fara ƙara, daukowa yayi yana duba me kiran. Vd call ne Zainab ta kirashi.

Dauka yayi yana faɗin " Ya dai?

"Hmm nufar dawo da UMMIE zanyi, yarinyar sai kuka take yi da kyar na lallabata taci abinci ita sai na kaita wajen Ummanta bansan ta yadda za'ayi ma ta zauna damu ba"

"Ok bata wayar" Ya faɗa yan kallon screen din.

A gaban Zainab Ummie ta zauna tana shan majina ta ce " Uncle Zayd Ni dai kazo ka kaini wajen Ummana Aunty Zainab tsoro take bani"

"Kut! Me kike nufi da tsoro nake baki? Zainab ta faɗa tana kallonta.

"Baki da kyau" Ummie ta fada tana taɓa ma ta fuska. "Lallai ma yarinyar nan waya kaiki ma muni? Ke kinsan irin munin da kike dashi?

Ummie ta tsani a ce mata mummuna hakan yasa ta fara kuka sosai.

Murmushi Zarah tayi tace " Bani wayar"

Miƙa ma ta wayar yayi, "Mamana" Ta fada tana sakin murmushi.

Da sauri Ummie ta daina kuka tana kallonta ta ce " Ummana meyasame ki haka? Meyasa aka sa miki audiga a fuska? Kuma meyasa fuskarki ta kumbura?

Shuru Zarah tayi dan bata da amsar da zata bawa UMMIE.

"Ummana Abba ya dakeki ne? UMMIE ta faɗa kamar zatayi kuka.

Kasa riƙe hawayenta tayi hakan yasa ta kifar da wayar tana fashewa da kuka ko zatayi zuciyarta tayi sanyi. Tana jin UMMIE

Please Login or Register in order to submit comment