Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Shafi na sha biyu*

Ƙarar slippers dinsa dake sauka bisa tiles din dake jere a stairs ya sanar ma ta da isowarsa.

Ransa a ɓace yake sosai, ƙarasowa yayi kusa da su yana karewa kayan lefen kallo zuciyarsa na tafasa sosai.

" Yawwa Umarun Mama zo kaga kayan 500k kawai zaka ciko saboda za'a karasa siyayya sannan za'a bawa amarya kudin gyaran jiki da sauran abubuwa"

Mama ta faɗa tana kalllonsa fuskarta cike da annuri.

"Ok" Kawai ya faɗa yana neman waje ya zauna.

"Bro! Wannan hade ranfa?

Cewar Yusuf yana kallonsa. Dama jira yake, kallon Yusuf yayi ya ce " Nifa bana son yarinyar nan wallahi!

"Farooq kenan! Aikuwa tunda kaƙi bi ta lallams zaka bi ta dole! Umarni kuma nake baka ka aureta!

Daga haka ta tashi ta basu waje. Kusa dashi Yusuf ya dawo yana taɓa kafadarsa ya ɗan duka alamar rarrashi sannan ya ce " Hakuri zakayi, tun farko laifin ka ne da ace ka fito da mace kayi aurenka da yanzu ba wannan zancen akeyi b...

"Enough please! Farooq ya faɗa da ƙarfi yana tashi tsaye. Da kallo kawai Yusuf ya bishi, tsabar takaici tsaki Farooq yaja yana barin falon!



Da kyar aka iya ceto rayuwar Zarah! Ba karamin jini ta zubar ba wanda shima da kyar ya tsaya kuma dole ayi ma ta karin jini.

Leda biyu na jini ya siyo aka ajiye dan ya huce kafin a saka ma ta, nurse ɗin dake kula da ita ne ta kalleshi kafin ta maida dubanta kan drip din dake shiga jikin Zarah ta ce " cikin jiki ta ya zube! Kuma akwai ragowar pieces zakuyi flushing dinsu idan magungunan da muka rubuta beyi flushing dinsu ba, and tana bukatar kulawa sosai"

"Insha Allah" Ya faɗa yana jinjina kai kamar na kirki.

Duk abinda aka bukata a asibitin ya siyo ya ajiye.

**

Ɓangaren Sa'adah kuwa su na tafiya ta koma daki tayi kwanciyarta. Tana ta jiran dawowarsu amma har dare shuru.

Wayarta ta dauka ta kira shi har sau biyu amma bai dauka ba. Gaba daya haushi ya isheta, ƙaramin tsaki tayi tana kwanciya tare da lumshe idanunta.


A asibitin Shehu ya kwana har wayewar gari Zarah ba ta tashi ba.

Sai da Nurse tazo ta duba ta sannan ya taho gida dan yayi wanka ya tafi aiki Sa'adah kuma ta zauna da ita kafin ya dawo.

Jinin zarah ya fara cin karo dashi duk ya bushe, cike da mamaki yake kallon duk inda jinin ya zuba, direct dakin Sa'adah ya nufa, a kwance ya ganta tana latsa wayarta. Tana ganinsa ta mike da sauri tana fadin "Baby ya jikin Zarah? Da kyar jiya na iya yin bacci, ga wayarka a gida shiyasa ban kiraka ba ya take yanzu?

Ajiyar zuciya ya sauke yana ɗan shafa kansa ya ce " Cikin dake jikinta ya zube"

Wani murmushi Sa'adah tayi kafin ta tsuke fuska kadan ta ce " Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, ya zube?

"Hakane, amma meyasa baki gyara wajen dana ce ba?

"Wani waje kuma? Ta faɗa cike da bariki.

"Da zamu fita jiya ban faɗa miki ki gyara wajen ba?

Bata amsa masa ba ta wani riƙe cikinta tana yin ƙara. Da sauri ya riketa yana fadin " Lafiya?

"Tun jiya cikina ke ciwo kaɗan²" Ta fada tana wani shuumun murmushi.

"Sannu, kwanta bari na kawo miki magani"

"Uhm" Ta fada tana zama. Fita yayi ya shiga dakinsa be daɗe ba ya dawo riƙe da maganin ya ballo ma ta sannan ya bata ruwa tasha tana bata rai tare da jero masa Allah ya isa ranta dan shi ya sa ta shan magana ba tare da ciwo ba.


Kwanciya tayi tana wani bata fuska, rufeta yayi yana faɗin " Ki kwanta bari na gyara wajen nazo nayi Shirin aiki"

"Ok" ta fada tana bin bayansa da harara.

Shi ya gyara wajen da jini ya bata har dakin Zarah da toilet komai ya gyara.

Sai wajen 12 yayi shirin aiki, bacci ya tarar da Sa'adah tana yi, hakan yasa ya barta ya fita.

Yana shiga mota yayi dialing number Zayd, har ta gama ringing be dauka ba, text message ya tura masa sannan ya dauki hanyar zuwa asibiti.

Yana office yana duba yadda building dinsu na Canada yake tafiya yaga wayarsa tayi haske. Dubawa yayi yaga missed call daga Shehu sannan kuma ga message daya shigo just now.

Ganin sunan Zarah a message din yasa shi saurin budewa ya fara karantawa a fili.

*Zarah tana asibiti, tayi bari ka tura Zainab ta kula da ita dan babu kowa a wajenta ga address ɗin.....*

Shuru yayi bayan ya gama karantawa kusan na minti ɗaya sannan yayi wa Zainab forwarding din message din, ko minti uku ba'ayi ba tayi masa reply da

*Ina wajen aiki*

Ajiyar zuciyar yayi sannan ya kira lambar Aunty, bugu uku ta ɗauka.

Bayani yayi ma ta sannan ya kara da fadin " Zan turo Kabir ya daukeki sai ya kaini zan bashi address ɗin"

"Toh Allah ya bata lafiya"

Da Amin ya amsa sannan ya kashe wayar ya fito daga office ɗin.

Cabin ɗin dake kusa da nashi ya shiga, ya sanar da Kabir abinda zeyi masa sannan ya bashi mukullin motarsa, shi kuma ya koma office.

Kasancewar su UMMIE sun kusa tasowa daga makaranta yasa Aunty ta ce su biya makarantar su daukota.

Sai da suka fara biyawa sannan suka nufi asibitin.

A bakin gate ɗin asibitin ya sauke su sannan ya koma.

A reception Aunty da Ummie su ka tsaya dan yi tambaya.

Kiran sunan Ummana da UMMIE ta fara yi yasa Aunty kallon direction din da Ummie take kalla.

Zarah ce sanye da riga irin wadda ake sawa patients a wasu asibitocin hannunta na hagu sanye da cannula an liƙe da plaster kanta kuma hula ce me laushi itama duk ta asibitin, kafarta ko takalmi babu, rigarta duk yayi stain da jini.

Gaba dayanta ta zama wata iri,da sauri Aunty ta Ummie suka nufeta. Jikin Aunty ta faɗa tana sakin wani kuka me ciwo. Da kyar Aunty ta iya ɗago da ita ta ce " Meyasa kika fito daga ɗaki?

Cikin tsananin kuka Zarah ta ce " Aunty Dan Allah ki kaini gida! Bazan iya cigaba da zama da wannan azzalumin ba! Ya barar min da cikina Allah ya isa tsakanina da Shehu Allah ya wulakanta shi yadda ya wulakanta ni Allah ya bi min hakkina Allah ya hana shi jin dadin rayuwarsa Allah ya isaaa"

Ta karashe maganar tana ɗora kanta a kafadar Aunty tana sakin wani sabon kukan.

" Ummana Allah ya saka miki, duk wanda yasa Ummana kuka shima sai yayi kuka insha Allah" UMMIE ta faɗa hawaye na biyo cute shiny black chick dinta. Janyonta aunty tayi ta runguemsu su duka hawaye na zubo ma ta.

"Malama! Malama! Suka juyo Muryar wata tana fadi a kusa da su. Dagowa Zarah da Aunty sukayi suna kallonta.

Nurse ce, kallon Zarah tayi ta ce " Kinsa hankali ya tashi, be kamata ki fito a wannan yanayin ba muje in baki abinci kisha magani"

Da sauri ta girgiza kai ta ce " a'a sallamata zakiyi"

"Sallama kuma? Nurse din ta fada cike da mamaki.

"Eh" Aunty ta bata amsa.
"Ok but no refund gaskiya kuma mijinta ya biya kudi sosai saboda a kula da ita gwanda ta ,auna taji sauki sosai dan bazamu dawo da kudin ba"

"Bakomai" Aunty ta fada tana kallon nurse ɗin.

"Ok toh ku jira anan na kawo mata druge da allurorinta"

Da toh kawai Aunty ta amsa ma ta ita kuma ta bar wajen.

Number Zayd tayi dialiy bugu uku ya ɗauka yana fadin " Ya jikin Zarah?

"Ka zo dai asibitin"

Daga haka Aunty ta kashe wayar. Basu daɗe a wajen ba Nurse din ta dawo riƙe da jaka wanda ke dauke da tambarin asibitin. Aunty ce ta karba tana yi ma ta godiya ita kuma tayi wa Zarah addu'a tare da wasu yan shawarwari sannan ta tafi.

15mins ya dauki Zayd kafin ya iso a asibitin. A zaune a reception ya hangosu da sauri ya karaso yana fadin " Me kuke yi anan?

"Muje gida tukunna" Aunty ta fada tana riƙe Zarah.

"Meyasa wai kuka fito Aunty? Gashi Zarah tayi staining basu tsayar da jinin bane?

Ya faɗa kamar zai yana kallon Zarah.

"Riƙeta muje" Aunty ta faɗa ba tare da ta bashi amsa ba.

Top din suit din jikinsa ya ciro ya sakawa Zarah sannan ya riketa yana fadin " Muje"

Da kyar Zarah take iya takawa saboda jiri dake dibar ta kadan²

A seat din baya ta kwanta Aunty da UMMIE suka shiga gidan gaba sannan ya shiga shima suka dauki hanyar gida.

Bayan sun isa gida Aunty ce ta taimakawa Zarah ta gyara jikinta sannan ta bata kayan Zainab ta saka, kunu ta dama ma ta tasha sosai sannan ta sha maganunan ta ta kwanta idan Zainab ta dawo tayi ma ta allurar.

A kusa da ita UMMIE ta zauna taga taba ma ta fuska.

A hankali Ummie ta ce " Ummana sannu"

"Yawwa Mamana" Zarah ta amsa tama ɗan yi ma ta murmushi.

Kallon UMMIE Aunty tayi ta ce " Zo muje ki cire uniform kici abinci"

Jikin UMMIE a sanyaye ta taso ta biyo bayan Aunty.

Basu dade da fita ba Zayd ya shigo yana kallonta fuska ba yabo babu fallasa.

"Ya jikin?

"Da sauki"

Ƙarasa shigowa yayi yana zama a gefanta ya ce " Shi ya kara dukanki har kikayi ɓari?

Goge hawayenta tayi ta ce " Shine mana! Kuma inason kai ƙara kotu indai har bazai sakeni ba"

"Saki kike nema? ZAYD ya kara tambayarta.

"Eh"
Shuru dakin yayi na kusan minti biyu. Wayar Zayd ce ta fara ruri. Zarota yayi a aljihun wandonsa yana duba me kiran.

Ganin sunan SIR YUSUF yasa ya ɗauka yana fadin " Hello Sir"

"Yawwa! Ya jikin Zaran?

Sai daya kalleta sannan ya ce " Da sauki"

"Ok kayi min kwatancen asibitin"

Cewar Yusuf daga ɗaya bangaren.

"Mun dawo gida ai, an sallamota yanzu ma bacci take yi"

"Ok toh ka gaisheta"

Zayd be ce komai ba ya katse wayar.

Lumshe idanunta tayi tana sauke numfashi a hankali. Idanu kawai ya tsira ma ta yana jin zuciyarsa nayin sanyi.

A jikinta taji kallonta yake yi. Buɗe idanuwanta tayi, aikuwa suka haɗa ido, da sauri ta sake rufewa tana fadin " Bacci zanyi"

Tashi tsaye yayi yana gyara zaman tie dinsa ya ce " Ok"

Daga haka ya fice.

Shehu na dawowa daga office ya nufi asbiti amma aka shaida masa relatives dinta sun zo sun tafi da ita.

Number Zayd ya kira wajen 10 na dare. Bugu daya Zayd ya ɗauka yana fadin " By now kaji labarin Zarah bata asibiti ko? Karka wani damu kanka Zarah bazata sake dawowa inda kake ba ballantana ka samu damar wulakanta ta"

"Kaga Malam bana son shashanci ka gane ko? Ka dawo min da matata ko kuma kaji sammaci"

"Karka fasa!" Daga Haka Zayd ya kashe wayar cike da jin haushin Shehu.


Kwanan Zarah huɗu taji sauki ba lafi dan tana samun kulawar da ta dace sosai har yanzu Shehu be sake kira ba ka be zo ba, Zayd kuma br fadawa kowa yadda sukayi ba 3 days back dan yana so Shehu ya kai ƙara kuma ya zama shi za'a kama da laifi.




*Monday*

First day kenan da zai fara zaman office a Nigeria! Baya son minor² cases su dameshi! A Nigeria kuwa bashi ma wanda be taka kara ya karya ba sai ace an tafi kotu. Ni kuwa ce ko bera biyat te tai na nemi hakkina😜.

Cikin Stuart Hughes diamond edition suit ya shirya, ya sanya stemar shoe me dan karan kyau a ƙafarsa, RLX watch ya saka a hannunsa, gyara tie dinsa yayi ya fesa turare kadan sannan dauki wayarsa da mukullin mota ya sakko.

Kallon Mama yayi dake jera underwears a cikin akwati. Taɓa baki kadan yayi ya ce " na tafi aiki"

"Allah ya kiyaye"

Ta fada ba tare da ta kalleshi ba.

Tsayawa yayi yana kallonta kafin ya ce " Mu first day at work babu wani special prayer?

"Ai aikin ba sabo bane a wajenka ko? Kuma Ni kullum cikin yi maka addu'a nake"

"Ka tafi kawai kaina da neman magana"
Yusuf dake dining yana breakfast ya fada yana kalllonsa.

" Wai yarinyar nan basu dawo daga Dubai din bane? Na gaji da wanke² da girki kullum"

Cewar mama tana zuge akwatin lefen UMMIE.

"Bata dawo ba, kuma kota dawo ai bazanje biko ba! Aure zan kara"

"Eh nima ba cewa nayi kaje bikonta ba jikana nake so ya dawo"

"Shi zai miki wanke² da girki? Cewar Farooq yana kallonta.

Dariya Yusuf ya tuntsire da ita dan dama abinda yake ransa kenan.

"Kai bana son shirme" Mama ta fada tana hararasa.

"Shi da ya kusa kawo miki wata daughter in law din? Kinga kin kusa daina wanke² Kuma ke kika ƙi yarda akwai maid"

"Eh bana so inada sirika mezanyi da maid? Kuma jima din ai ba zama nake ba ina tayata da wasu ayyukan"

"Ni dai na tafi"

Farooq ya faɗa yana ficewa.

Kusa da Mama Yusuf ya dawo yana riƙo hannunta ya ce " Mama dan Allah ki kyale yaron nan da maganar auren UMMIE idan ma kina ganin bazaki iya ce musu a fada ba ni zan aureta for the sake of my brother happiness, wallahi baya sonta jita mun dade muna magana dashi ya fado min baya sonta kiyi hakuri ki bashi dama ya fito da wadda yake so auren yayi wuri nan da one month fa Mama, wallahi ina gujewa yarinyar shiga matsala ne tunda har ya fito ya ce baya sonta"

"Ka gama? Mama ta fada tana kalllonsa. A hankali ya ce " Eh"

"Toh naji! Maganar aure Kum ba fashi Allah! Zai dora ahankali ne, kawo min akwatunan nan daki an gama haɗa komai zuwa jibi za'a kai insha Allah"

Bai ce komai ba ya dauki akwati daya yabi Bayan mama dashi zuwa dakinta ransa duk ba dad'i....

*Kuskure! Hmm*

*A cigaba da hakuri dani pls*

Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 11" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1176077869?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=DbaEwy%2FfUJagV6G6DjuEm3qm3rp1m5%2FpfrV0k%2BT8LNUPFS0DxHtFveoh%2FS5S%2BPiigU5mpSrfofw%2BfekauLm%2B7Gz59pWG03K%2F4CYxrroJttcUkVJzSxPdxF8Ml8xnqkH5

*Please tun a farko nayi bayani idan zaki fara bi ki fara bi kafin nayi nisa dan bazan iya turawa ta Private ba, fatan zaku fahimta*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)

𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.

*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...


*K'ANWATA*

*Dandano!Dandano!!*


Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..


Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573


Nomal. guda d'aya N 300 ne

guda biyu N 500 ne


Special guda d'aya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne


Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Shafi na goma sha ɗaya*

Washe_gari

Kafin Zarah ta tashi daga bacci har Juwairah tayi karin kumallo. Wajen 9am sannan Zarah ta tashi, wanka ta farayi kafin ta shirya as usual cikin kodaddiyar atamfa amma kuma a wanke a goge take.

Juwairah ce ta shigo hannunta riƙe da tray ta jero bowl me dauke da sc of egg gefe kuma cup din shayi ne duk ta haɗa komai sannan bread.

A kan gado ta ajiye kusa da Zarah tana faɗin " Kici abinci bari na kaiwa amarya nata Hajiya"

"Sannu da aiki" Zarah ta faɗa tana Murmushi.

"Yawwa, anjima ki tambayi Yaya sai muje gidanku naga UMMIE"

"Toh" Zarah ta amsa tana murmushi. Fita Juwairah tayi baya dade ba ta dawo tana faɗin " Har karfe goma wai basu tashi ba ya wani balbaleni da masifa kamar wata ƴarsa"

Ta karashe maganar tana zama a kan gado kusa da Zarah.

"Fushin menene haka Juwairah? Kinsan ai yadda maza suke behaving idan sunyi sabon aure ko? Toh dan haka ki daina wani bata ranki"

Turo baki kaɗan Juwairah tayi tana gyara zamanta a kan gado ta ce " Indai namiji ne zata gani ai"

"Aikuwa" Cewar Zarah tana kurbar shayinta.

"Kinci abinci kuwa?
Zarah ta tambayeta.

"Uhm" Itace amsar da Juwairah ta bawa Zarah dan haryanzu haushi take ji.

Murmushi kawai Zarah tayi ta cigaba da cin abincinta.

Ni kuwa nace kici da kyau akwai lokacin da zaizo ruwa ma da kyar zai wuce miki😜

Sai wajen 12 sannan su Zarah suka fito daga ɗakin, Hajiya da Aunty Rabi duk suna falo sunayin kallo.

Kara Hausawa sukayi da Zarah amma banda Aunty Rabi da ko iskar da ta kwaso ta bata kallah ba.

Ita da Juwairah ne suka hau gyara gidan kafin azahar sun kammala har abincin rana. Har lokacin Amarya da ango basu fito daga daki ba.

Abinci Sarah ta zubowa su Hajiya tana faɗin " Bismillah"

Hajiya ce kawai tayi ma ta sannu sannan ta dauki abincin ta fara ci, Aunty Rabi kuwa daukar abincin tayi ta fara ci ba tare da ta kalli Zarah ba.

A kwano daya Juwairah ta sako musu abincin suna zaune a falo suna ci, Sa'adah da Shehu S²😜 suka fito daga daki sai dariya suke.

Kallo ɗaya Zarah tayi musu ta dauke ka ta daga garesu.

Juwairah kham ko kallonsu batayi ba.

A kujera ya zaunar da ita yana fadin " Hajiya Aunty Rabi ina kwananku, ko ince ina yini?

"Lafiya" Hajiya ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba.

Aunty Rabi kuwa wanshare baki tayi ta ce " Ango kenan! Sai yanzu nasan kayi aure fara'a fal fuska"

Murmushi yayi yana kallon Sa'adah.

Itama Murmushi tayi ta kalli su Hajiya ta ce " An yini lafiya?

"Lafiya kalau yar nan" Aunty Rabi ta fada tana dariya.

Hajiya kuwa da lafiya kawai ta amsa dan wannan ba tarbiyya Sa'adah ta nuna ba.

"Ke baki iya gaisuwa bane? Shehu ya faɗa yana kallon Juwairah.

"Ina gini? Juwairah ta fada chan ƙasan ranta ita kadai tasan me tace.

"Lafiya lau" Sa'adah ta amsa tana murmushi.

Zarah kuwa abinci kawai take ci ko kallonsu batayi ba.

"Aunty Zarah ina yini?
Cewar Sa'adah cikin ƙissa.

Murmushi kaɗan Zarah tayi tana ajiye cokalin hannunta ta ce " Amarya antashi lafiya?

"Alhmdll ina fatan kinyi bacci me dad'i?

Murmushi Zarah tayi tana faɗin " Sosai ma irin wanda ban taba yi ba"

Jinjina kai Sa'adah tayi kafin ta ce " Toh fatan dai wannan baccin zai dore, dan kamar jiya naji wata Black cat ta shigo gidan nan kuma da alama she's very dangerous"

Dariya Zarah tayi me sauti dan ita da Sa'adah kar tasan kar ce.

Ruwa ta kora ƙadan sannan ta ce " Aikuwa idan wannan magen ta ce zata hanani sakewa zan koreta ne zan saka ta cikin buhu na kaita bayan gari"

"Ok hakan yayi"

Sa'adah ta fada tana wani juya ido.

"Yaya zamuje gidansu Zarah"

Juwairah ta fada tana kalllonsa.

"Ok" ya amsa yana zama kusa da Sa'adah. "Ku bani hankulanku nan"

Cewar Hajiya tana kallonsu.

Hankalinsu ne ya komo kanta.

Cikin nutsuwa tayi musu nasiha da faɗa sosai kafin ta ɗora da cewa " zuwa jibi insha Allah zamu koma dan mu fara shirye-shiryen bikin Juwairah"

"Allah ya kaimu ya kuma sanya alkhairy" Sa'adah ta fada tana kallonta. Da Amin suka amsa.

Juwairah ce ta zubo musu abinci sannan suka shirya ita da Zarah suka tafi.

Aunty kawai suka tarar a gidan, Zayd da Zainab suna wajen aiki UMMIE Kuma tana islamiyya.

Sai yamma lis sannan UMMIE ta shigo gidan tana shan alawar jani in jaka jakar makarantar ta a wuya wanda ke dauke da littafi daya Almurshid.

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo tana fadin "Aunty yau Yasayyadi ya zaneni saboda banyi rubutu ba"

Sam bata kula da su Zarah ba.
"Toh sai a dinga yin rubutu ko? Juwairah ta fada tana kallonta. Sai alokacin ta juyo ta kallesu. Da ƙarfi ta ce " Ummana!"

Sai kuma ta nufota da sauri tana fadawa kan cinyarta.

Rungumeta tayi tana jin wani dad'i a ranta. "Ummana shine kika bari a nan ko?

Shafa kanta Zarah tayi tana ƙoƙarin mayar da hawayenta ta ce " A'a Mamana, ban barki ba dan san raina ba amma ai nasan kinfi jin dadin zaman nan ko?

Da sauri ta daga kai ta ce " Eh kullum sai Uncle Zayd ya kawo min nama da lemo idan zai dawo daga aiki kuma ya ce min yana sonki yana kaunarki wai zai aureki"

Shuru falon yayi, a hankali hawayen da take rikewa suka zubo bisa kuncinta. Da sauri ta sharesu tana daga UMMIE daga jikinta ta ce " A cire uniform ko?

Da toh UMMIE ta amsa tana nufar inda Aunty ta ke ta ce " Na dawo fa"

Murmushi Aunty tayi tana kallonta ta ce " Na ganki fa ai ni ba makauniya bace kamar Mamanki"

Turo baki tayi tana nufar hanyar ɗaki ba tare da tace komai ba.

"Aunty zamu tafi dare yayi" Zarah ta faɗa tana tashi tsaye.

"Baxaki jira ayi sallar Magariba ba lokacin ma Zayd ya dawo sai ya kaiku"

"Aikuwa dai Aunty Zarah mu

Please Login or Register in order to submit comment