Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rikice dan bata so Shehu ya ƙara laƙa ma ta sata dan ba yau ya fara ba.

"Kinga ki daina wahalar da kanki! Nasan ke kika dauka kika siyar fada min uban me kikayi da kuɗin?

Ya karashe maganar yana kama gashin kanta. Runtse ido tayi tana faɗin " Dan Allah ka sakar min gashi wallahi ban daukar maka zobenka ba"

Ƙara matse gashin yayi da ƙarfi yana fadin " Karya kike, ai nasan ba yaune karo na farko da kika fara yi min sa ta ba fada min me kika siya da kuɗin?

Kasa magana tayi sai hawaye dake zubo ma ta ga kanta daya fara ciwo.

Tureta yayi da ƙarfi, cikin hansazari ta dafa gado hakan yasa ba ta fadi ba. "Rubbish, zaman hakuri kawai nake da Zarah! Amma soon zan karo aure zaki gane baki da wayo! By 7pm akwai party da zamuje na client dina da kuma wannan shegen me gidan naki muna aiki da shi akan wani project idan naga kunyi magana dashi sai na ci uwarki"

Bata ce komai basai hawaye kawai da ta keyi zuciyarta na yi ma ta zafi da radadi. Toilet ya shiga ita kuma ta tashi ta fito daga dakin ta nufi na ta ta fara kukan bakin ciki dabara shin uwa, dan yanzu bata da wanda take fadawa damuwarta, abu kadan take iya fadawa Zainab"

Ƙarfe sha biyun rana ta shirya cikin dogon hijabi ta dauki jaka dan zuwa dauko Ummi daga makaranta dan 12:30pm suke tashi.

Tayi fayau da ita, kana kallon fuskarta zaka san tana cikin damuwa. Bata da kudin mota hakan nan ta fita dauko ta, tafiyar ba ta da tsaho sosai amma da ɗan nisa.

Gate man ne ya tsayar da ita yana fadin " Hajiya Alhaji ya ce kar na barki ki fita"

Wani banza kallo tayi masa tana faɗin " Matsa min na wuce"

Kin matsawa yayi, da tayi kokarin bi ta gefensa ya riƙo ma ta hijabi. Cikin bacin rai ta daukeshi da mari tana fadin " Baka da hankali ne?

"Wa kike tunanin zai baki daraja bayan wanda ya ajiye ki a gidan ma baya darajaki?

Kalaman da taji daga bakin me gadin kenan. Hawaye masu zafi taji sun zubo ma ta. Da sauri ta sharesu tana fita daga gidan zuciyarta na zafi.

Kasa tsayar da hawayenta tayi dan kukan da take yi tana dan jin sanyi a zuciyarta.

Bata san inda take jefa kafarta ba, horn din da taji a tsakiyar kanta ne yasa ta matsawa da sauri tana kallon motar dake yi ma ta horn din wasu kuma suna wucewa.

Matsawa ta yi daga titi ta koma chan gefe tana cigaba da tafiya.

"Zarah! Zarah! Taji ana kiran sunanta. Juyowa tayi da sauri jin kamar Muryar Zayd.

Aikuwa shine, yana sanye da long sleeve baka da wando me laushi shima baki haka canvas din ƙafarsa haka ya yatsuke sosai yayi kyau abinda samartakar sa ta fito sosai.

Murmushi ta saki tana fadin " Zayd?!

Shafa kansa yayi ya ce " Zarah! Ya kike?

"Lafiya lau, ya kwana dayawa? Yasu Zainab da Aunty? Ya kake?

"Kowa lafiya Zarah, amma kinyi rashin lafiya ne?

Da sauri ta girgiza kai sai kuma ta ce " A..ah ina nufi eh nayi"

Idanu ya tsira ma ta yana tunani kafin ya ce " Ok Allah ya sawwake ina zaki je haka?

"UMMIE zan dauko daga makaranta"

"Ok muje na kaiki" Murmushi tayi ta ce Toh ta nufi motarsa kirar accord shi ya buɗe ma ta ta tshiga sannan ya zagaya ya shiga nashi bangaren.

Tayar da motar yayi suka bar wajen.

A hankali yake tuki yana kuma kallonta lokaci zuwa lokaci. Kasa jurewa yayi ya ce " Zarah kina cikin matsala ne?

Kasa riƙe hawayenta tayi ta fashe da kuka me ƙarfi. Da sauri ya ce " Zarah me ya faru?

Kasa magana tayi shima kuma cewa komai ba ya har suka isa makarantar su UMMIE. Tana tsaye a bakin titi tana ta kalle².

Tana hango Zayd da Ummanta ta nufo su da sauri tana rungume kafafun Zayd ta ce " Uncle"

Dagata yayi sama yana fadin " Kyakkyawata kuma amaryata ya makaranta?

Dariya tayi kafin ta kalli Ummanta ta ce " Uncle Zayd meyasa ka dakar min Ummana take kuka?

"Duka kuma? Ai ba'a dukan ma ta ban daki Ummanki ba"

"Ba'a dukan mata kuma? Toh meyasa idan Ummana tayi wa Abba laifi sai ya fara dukanta rannan ma ina jin tana ihu ya kulleta a daki shekaran jiya ma har cizar ma ta baki yayi kuma yana matse ma ta non... "UMMI! Zarah ta faɗa da ƙarfi cikin tsawa. Da sauri ta yi shuru tana kallon Zayd da ya cikada mamaki sosai.....


*Yawan comments dinku shine yawan typing, ina jin dadin ydd kuka karbi littafin daga farawa*

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!

Autar Mama ce
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 4" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1169654318?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=8C2Fd9czCvwD51O8dPwQMdH%2B%2F%2Fk9fQCol1RJcVGrVSUqvyvvkThZDzU3oa9W%2BTZeHJzVmnWExV1HTa0NqW2iqI6pAxteS%2F9Y0Py310kduFY06Wo%2BovOQrx9qh255jalg

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

*Shafi na huɗu*

"Zayd zamu tafi saboda kar ta makara a islamiyya"

Zarah ta faɗa tana ƙoƙarin karɓar UMMIE daga hannunsa. Sauke UMMIE yayi yana faɗin " UMMIE tafi mota ina zuwa"

Ba musu ta tafi dan taga ran Ummanta a ɓace yake idan ta tsaya yin wani maganar Umma zata iya dukanta.

Sai daya ga shigarta motar ta rufe sannan ya danna makulkin motar ta rufe kafin ya kalli Zarah dake kokarin barin wajen ya ce " Meyasa ki ke kokarin kauce wa ne? Zarah! Ni fa ɗan uwanki ne, ko ban chanchan sanin danuwarki ba ne?

"Bakomai Zayd, Kasan yaro da surutu muje ko? Ta fada tana danyi gaba dashi. "Zarah! Ya kira sunanta yana haɗe ransa.

Tsayawa tayi tana goge hawaye ta kafin ta juyo ta kalleshi, shi ma kallonta ya ke kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce " Meyasa baki taba zuwa gida ba akan matsalar da kike fuskanta? Meyasa zaki bari yana dukanki? Meyasa zaki bari ki zama baiwa a wajensa?

Shuru tayi ta kasa cewa komai zuciyarta na zafi.

"Zarah talk to me" Ya faɗa yana matsowa daf da ita.

"Zayd is not the right time please! Mu tafi gida" Daga haka ta barshi a wajen tana fighting da hawayena dake zubowa bisa kuncinta.

Girgiza kai yayi yana bude motar kafin ya karaso ta shiga.

Har ƙofar gida ya kaita, bata ce dashi komai ba ta sakko tana buɗe back seat ta fito da UMMIE.

Fitowa yayi daga motar yana kallonta ya ce " Not Even a good bye? Aren't you missing me?

Ya faɗa dan yaga murmushinta, amma ko kadan bata dara ba.
A hankali ta ce " Nagode ka gaida Aunty da Zainab"

"Shikenan zasu ji, ranar asabar me zuwa za'a zo tambayar auren Zainab kar kice ban fada miki ba ki"

"Allah ya kaimu ya sanya alkhairy" Ta fada tana rufe masa murfin motar.

Har ta shiga cikin gida bai daina kallon gate ɗin gidan ba, tabbas yana son sanin abinda ke faruwa da ita ko ba komai ita ɗin yar uwarsa ce kuma zumunci me dad'i sukeyi dan tun mutuwar mahaifinsu mahaifinta shi ya dauki dawainiyarsu har ya kawo karfi kafin shima ya rasu, bata da uwa ba ta da uba, tana bukatar kulawa da rarrashi da kuma kwanciyar hankali amma ga dukkan alamu bata samun ko daya daga ciki.

Dogon numfashi yaja sannan ya shiga mota ya bar wajen.

Wanka Zarah tayi wa UMMIE sannan ta sakata yin sallah ta kuma bata abinci kafin ta kwanta zuwa 3pm su tafi islamiyya.

A kusa da UMMIE ta zauna tana shafa goshinta a hankali har UMMIE ta yi bacci. Duniyar tunaninta ta faɗa wanda ya zame ma ta abokin hira a lokaci irin wannan...

*********

"Ma'am this card is for you" Wani colleague ɗin ta ya miƙo ma ta. Karba tayi tana juya card din me kyau kafin ta ce " Waya baka wannan Kabir?

Murmushi yayi yana kallon Card din ya ce " Sir Farooq"

"Ok zaka iya tafiya" Ta fada tana kalllonsa. Fita yayi daga cabin dinta, ita kuma ta miƙe tsaye tana buɗe card ɗin.

*Farooq*
Shine sunan da ta fara gani a saman card din bayan ta bude an rubuta shi da italic bold sosai.

*Zamu iya fita dinner?Stay blessed dear*

Shikenan abinda ke jikin katin. Ta karanta yafi sau goma kafin ta turo baki kadan ta ce " But how? Ta yaya zan bashi amsa? Toh meyasa yake so mu fita? No way! Bana son zuwa ko ina da kowa, wannan be dace ba sam! Idan rayuwar kasar waje yayi ni ba ita nayi ba ahtoh"

Juyowar da zatayi ta ganshi a tsaye yasha bakin glass yayi kyau sosai.

Matsawa baya tayi da sauri tana fadin " K...kk..kai?

Cire glass din yayi ya ce " Eh, Ni ne"

"Uhmm... Ah.. S..sss..sir din yana ciki" Ta fada tana kokarin wucewa.

Hannunta ya riƙo yana dawo da ita gabansa ya kalleta ya ce " Zarah eye contact please"

Yusuf dake cabin dinsa yana hangosu sai dai ba sosai yake jin abinda suke faɗa ba.

Kasa kalllonsa tayi hannunta sai rawa yake. Sakinta yayi yana sake fadin " Zarah ki kalleni"

Ya faɗa yana matsowa daf da ita. Matsawa baya tayi tana fadin " S..sir yana kirana"

"Zarah Please! Ya sake faɗa a ɗan ƙufule. Fitowar Yusuf yasa ta nufo wajensa da sauri tana faɗin " Sir kaina yana ciwo zan iya tafiya gida?

Kai ya daga ma ta alamar eh. Bata yi ko minti ɗaya ba ta bar wajen.

******

"Duk da be furta ma ta kalmar so ba amma ta daɗe da fahimtar cewa Farooq sonta yake yi! Ta dade da gane hakan kuma yayansa ke dakatar dashi saboda yasan ta kusa aure, da tasan haka auren Shehu zai zame ma ta da batayi ba"

"Ummana ki daina kuka kinji? Kallon UMMIE tayi da sauri, duk hawayenta ta digo a fuskar UMMIE hakan ne ya tasheta kenan.

Goge hawayen tayi ta ce " Toh Mamana"

Murmushi UMMIE tayi tana lumshe idanunta.

7pm.

Ta shirya tsaf cikin lace me kyau wanda sawa ta biyu kenan tayi masa sawa ta farko da zasuje wani taro da Shehu kuma saboda wannan taron ya siyo ma ta, shi kadai ne kayan da zata iya sakawa ta fita.

Ta shirya UMMIE ma cikin riga da wando masu kyau amma sun ɗan koɗe. Tana gyarawa UMMIE dogon gashinta da tayi ma ta style me kyau dashi ya shigo hannunsa dauke da babbar leda fuskarsa babu yabo babu fallasa.

Wani matsiyacin kallo ya wurga ma ta yana fadin " Dalla Malama cire kayan nan ga wannan ki saka sannan akwai na wannan aljanar ƴartaki a ciki na baki 5mins ki shirya sannan mayafi zaki saka bazaki bi ni da hijabi kamar matar liman ba"

Bata ce dashi komai ba ta ɗauki ledar daya cillo. Fito da kayan ciki tayi, abaya ce me kyau sosai milk ƴar yayi sai flat shoe da hand bag me kyau. Sannan jeans da shirt me kyau na UMMIE.

Ajiyar zuciya tayi tana cirewa UMMIE kayanta ta canza ma ta sannan ta kara gyara ma ta gashinta tayi wani bala'in kyau.

Hula yar ƙarama me kyau ta dauko ta saka ma ta, kafin ta ce " Jeki falo ina zuwa"

Da toh ta amsa tana ficewa daga ɗakin.

Da sauri ta shirya cikin kayan daya kawo ma ta ta fesa turare kadan ta fito.

Shima a lokacin ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya yayi kyau sosai dan dama shi ɗin me kyau ne.

Ɗauke idanunta tayi daga kansa tana riƙo hannun UMMIE ta ce "Mun gama"

Wani gauron ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " Idan mukaje kika dinga ƙasa da kai kamar tsohuwar akuya zaki gane baki da wayo sannan bana so ko da kalma daya ya shiga tsakaninki da ex-boss ɗinki kin dai ji ko?

Ƙoƙarin mayar da hawayenta tayi kafin ta ce " Toh"

Bai ce komai ba ya fice, da sauri ta riƙo hannun UMMIE suka biyo bayansa.

In 15mins suka iso inda zasuje.

Fitowa yayi daga motar yana riƙo hannunta ita kuma ta riƙo na UMMIE. Tana jin yadda yake ma ta mugunta yana matse ma ta yatsu amma ba ta ce komai ba.

Wajen ya hadu sosai, ana dan jiyo hayaniya kaɗan kaɗan.

Matsowa yayi daf da ita yana yana rada ma ta " Zarah kar kiyi abinda zaisa raina ya ɓaci, kuma kija bakin wannan baƙar yar taki nasan ta da shegen surutin tsiya"

"T..toh" Ta amsa masa.

"Ashe dai zakuzo" Taji muryar Zayd ya faɗa. Da sauri ta ɗago tana kalllonsa. Yasha kyau cikin riga da wanda na kanti kamar a sace shi.

Murmushi tayi kadan zatayi magana Shehu ya matse ma ta hannu da ƙarfi. Hakan yasa tayi Murmushi kaɗan. Zayd yaga lokacin da Shehu yayi ma ta muguntar amma sai ya basar yana fadin "Barka dai Shehu ya kake?

"Ai ka ganni ina lafiya ko? Shehu ya faɗa yana jan hannun Zarah su bar wajen, UMMIE sai waigen Zayd daya bisu da kallo ta ke.

Komai a tsare yake kuma kowa an rubuta sunansa a inda zai zauna tare da iyalansa.

Zama sukayi Zarah na yan kalle². Tashi yayi ya barsu a wajen. UMMIE ce ta kalli Zarah ta ce " Ummana me muka zo yi nan wajen?

"Taro za'ayi na wajen aikinsu Abba"

"Ummana yunwa nake ji" UMMIE ta kara fada tana kallon Zarah.

"Yunwa kuma? Baki ci abincin dana baki ba?

Kai UMMIE ta daga alamar eh.

"Toh kiyi hakuri anjima kadan zamu koma gida kinji?

Da toh UMMIE ta amsa tana kwanciya s jikin Zarah.

Ita kuwa Zarah Shuru tayi tana kallon mutane tana tuna lokacin da suka zo makamancin wannan taron da Sir Yusuf.

"Masha Allah, wannan babyn wacece? Ta juyo wata murya daga dan gabanta sosai. Da sauri takalli jikin ta taga ba UMMIE. Kallon matan dake gabanta tayi ta hango UMMIE a kan chair sai murmushi take zubawa ɗan dama tana kaunar ace ma ta me kyau.


Da sauri ta tashi ta nufi inda suke tana fadin " She's my child"

Wata beautiful lady daga cikinsu wanda tasha ubansu lace da gold ko ina sai kyalli ta ke ta yi sauri kallon ta ta ce " Zarah!

Zarah kham kallonta take yi dan bata santa ba.

"Ummana zan ci abinci" UMMIE ta sake faɗa tana kallon Zarah.

Sai a lokacin Zarah ta daina kallon matar ta sauke UMMIE daga kujerar har sunyi gaba ta jiyo Muryar matar tana fadin " Sakatariyar Yusuf ce fa a da! Babu irin binsa da batayi ba daga baya kuma ta dawo kan brother in-law Dina Farooq gashi yanzu 8yrs da aurenta ko 7 ne Brother in law Farooq ya kasa yin aure kullum bai da zance sai na Zarah, da kyar Mother in law dina ta sa ta koma karatu shine fa har yanzu be dawo ba, and naji Yusuf yana faɗin ta bar aiki ne saboda mijinta yana zarginta to ba mamaki ma wannan yarinyar ba ƴar mijin bace dan kyanta ba irin na hausawa bane"

Sosai Zarah taso hadiye bakin cikin dake cinta.

Hannunta taji an kamo, da sauri ta kalleshi fuska ba yabo babu fallasa ya ce " Wajen uban wa kika je?

Kwace hannunta tayi da sauri tana jan hannun UMMIE suka fito daga wajen. Yaso biyo bayanta amma baya so hankalin mutane ya dawo kansu hakan yasa ya Kyaleta amma yau kham zata ci ubanta.

Kuka ta fashe dashi bayan sun fito, maganganun matar na dawo ma ta, UMMIE ma kukan ta fara tana riƙe Zarah. Bazata iya daina kuka ba dan hakan yana sa taji ɗan sanyi a ranta, rungume UMMIE tayi ta kara fashewa da kuka sosai.

Ta kai kusan minti biyar a waje tana kuka kafin ta miƙe tsaye tana goge idanunta, ta gogewa UMMIE na ta idanunta. Juyowar da zatayi ta ga ZAYD a kanta.

Da sauri ta juya masa baya tana kara goge idanunta.

"Uncle Zayd Ummana sai kuka take yi nima shiyasa nayi kuka, Dan Allah ka bawa Ummana hakuri ni bana so inganta tana kuka"

Rage tsaho yayi ya dawo yana riƙo UMMIE ya ce " Nima haka UMMIE, kukan Ummanki yana sa ni naji zafi a zuciyaata yana sani na kasance cikin damuwa, amma insha Allah watarana sai labari"

Tashi tsaye yayi ya kalli Zarah ya ce " Muje na kaiki gida"

Bata ce komai ba, shi yafara yin gaba hannunsa riƙe dana UMMIE har suka iso inda motarsa ta ke.

Wayarsa ce ta fara ruri. Dubawa yayi yaga Yusuf ne. Karamin tsaki yayi kafin ya daga yana faɗin " Hello"

Tana ji Yusuf ya ce " Zayd ka dauko files a mota kazo ina jiranka"

Kallon Zarah yayi kafin ya ce " S..sir zan kai Zarah gida ne bata jin dadi"

"Ayyah kace ina gaisheta ya UMMIE? "Ok sir"

"Yawwa, kafin ka tafi ka kawo min files ɗin"

Be jira cewarsa ba ya katse wayar. "Ina zuwa" Zayd ya fada barin wajen.

Jingina tayi jikin motar tana riƙe da hannun UMMIE.

"Hawaye basuyi deserving zuba a fuskarki ba Zarah"

Da sauri ta kalleshi. Sosai ya kara manyanta rabon data ganshi 2yrs kenan.

"Sir" Ta fada tana kalllonsa.

Hankici ya bata yana fadin " Wipe those tears Zarah. Hannunta na rawa ta karba tana goge fuskarta.

"Ummana mu tafi yunwa nake ji"

Buɗe motar Zayd yayi yana fadin " UMMIE shiga"

Ba musu ta shiga seat din gaba.

"Insha Allah komai zaizo karshe kinji? Dama shi gidan aure gidan hakuri ne, ki dage da addu'a" "INSHA ALLAH, kayi hakuri da abinda ya faru banyi tunanin Shehu zeyi wannan banzan tunanin ba"

"Bakomai Zarah, Allah ya kara sauki"

Daga haka ko minti ɗaya be kara baya bar wajen.

Gidan gaba ta shiga sannan Zayd ya tada motar suka bar wajen.

Maimakon taga ya dauki hanyar gidanta sai ya dauki hanyar zuwa gidansu..

*Hmm Zayd sannu da kokari😒*

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!

Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 5" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1170077868?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=3R%2FLSi5vzgol6do%2B6oYxpiyTKptpWkP75lsBTMcmvRmXkZmbklBlk2PLM%2F5k%2FEclnLMVHKOu%2B87X8T%2B%2F7F%2FFKuQMLMOJ0HmZecuCWx%2BstZICbCVSKE%2FGMNIYkAfeSNhE

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*

*Shafi na biyar*

"Zayd ina zamuje? Ta fada tana kalllonsa cike da mamaki.

Ko kulata beyi ba ya kara speed. "Ka tsayar da motar nan Zayd, ina kake tunanin kai ni?

Nan ma banza yayi ma ta yana tukinsa. "Idan baka tsaya ba zan fita duk da kaa gudu"

Sai a lokacin ya rage gudun ya ɗan kalleta ya ce " Zarah gida zan kaiki"

"Na ce maka ina bukata ne? Dan Allah ka mayar dani gidan mijina yafi min"

"Miji? Har wannan ya kai matsayin ki kirashi da mijinki Zarah?

Kau da kai tayi daga kalllonsa ta ce " Eh, ko ba komai shine uban ƴata kuma bazan taba canza hakan ba"

"Good yayi kyau, amma duk abinda zaki faɗa ki fada amma gida zaki dawo"

"Wai Zayd meyasa baka fahimta ne Dan Allah ka kaini gida idan bazakaje ba ka saukeni"
Birki yaja ganin yadda take magana a zafafe.

Kallonsa tayi da sauri dan ta ji tsoron birkin daya taka. Horn aka farayi masa ba kakkautawa, gefen titi ya gangara yana dai² ta parking ɗinsa yayi yana faɗin "Fita"

Da mamaki ta ce " In fita kuma?

Banza yayi ma ta dan baya so ya yi ma ta magana cikin tsawa.

Shuru motar tayi dan UMMIE tuni tayi bacci.

Fitowa yayi daga motar ganin bata da niyyar fita zagayo ya bude bangaren da take ciki ya ce " Fito"

Kalllonsa ta tsayayi cike da mamaki dan batayi tunanin dagaske yake ba amma yanayin fuskarsa ya tabbatar ma ta dagaske yake.

A sanyaye ta fito daga motar tana rike da UMMIE.

Rufe murfin motarsa yayi ya zagaya ya shiga ya bata wuta ya bar wajen.

A baya ta goya UMMIE tana kallon titi, ita bata da ko sisi gashi yayi nisa da ita ballantana ta ce zata tafi a kafa.

Ta dade a tsaye a bakin titin kafin ta fara tafiya UMMIE goya a bayanta.

Sam Zayd be yi ma ta adalci bada zai sauketa a titi a daren nan.

Kusan minti talatin ta dauka tana tafiya amma ko rabin hanyar gida batayi ba.

Tasan yau kashinta ya bushe a wajen Shehu. Tana cikin wannan tunanin taji horn a bayanta.

Da sauri ta juya tana kallon motar. Zayd ne, bata san lokacin da ta saki murmushi ba.

Fitowa yayi ya kalleta ya ce " Am

Please Login or Register in order to submit comment