Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta, tashi tayi tana fitowa daga dakin. Bata ganshi a falo ba, dakinsa ta nufa nan ma baya nan. Wajen gidan ta fito ta duba ko ina bata ganshi ba. "Ba dai ya fita ba? Ta fada a fili.

Cikin gidan ta dawo ta dauko wayarta tayi dialing number dinsa. Bugu biyu ya dauka yana fadin " Ina jinki"

"Kana ina? Ta fada a hankali"

"Na kusa karasawa gida zan gaidasu Inna ne"

"Shikenan" Ta fad'a a sanyaye. "Wani abu ne? Ya saka fada dan jin kamar bata so fitar tashi ba.

"A'a" Ta bashi amsa tana kashe wayar.

Kwanciya tayi a kujera tana lumshe idanunta, yana dawowa zata bashi hakuri daga aure jiya har ta fara b'ata masa rai? Da auren fari ne tasan zai mata uzuri ta rufe masa kofa sannan tana wani treating dinsa kamar stranger.

Tana cikin wanna tunanin wayarta ta fara ruri. Tana ganin sunan Zainab ta dauka da sauri tana fadin " Na dauka zaki ko da safe ai dan duk wasu kayan basan i da kikai musu matsugnni ba"

"Ba wannan ba Zarah, naga Yaya yazo ba wani fara'a ko washe bakin nan da sabon ango yake yi banga yana yi ba"

Shuru Zarah tayi na 'yan seconni kafin ta ce " Zarah dama ilimin karantar yanayin mutun kikayi ba harkar lafiya ba! Daga ganin sa sai ki fara wani banzan tunani"

"Hmm ke abunne yaban mammaki gasu Inna chan ma said tsiya suke masa wai baya dariya, toh nidai zan baki shawara a matsayinki na kanwata kardai ki bada damar da abu mara dadi zai fara faruwa tsakanunku kinji ko?

"Insha Allah, yaushe zaku zo?

"Zuwa gone sunce yau hutawa zasuyi ni da yau nake son tafiya na barwa kishiyata miji gwanda na koma"

Dariya Zarah tayi tana fadin " Dad'inta dai dashi kika ganta"

"Eh amma yanzu dai mijin mu ne! Ban ma fada masa ina ciki ba sai jiya na aka turo min da result na BT aka tabbatar min wata biyu"

"Masha Allah, ya kamata dai ya sani da wuri Allah ya saukeki lafiya"

Zarah ta fada cike da farinciki. "Amin, kuma karki fadawa kowa dan ko Aunty bata sani ba"

Murmushi Zarah tayi ta ce " Baki da matsala, yaushe din zaki tafi?

Daga d'ayan b'angaren Zainab ta ce " Gobe insha Allah, by 10 zamu zo gidan ki zuwa azahar sai na kirashi kinga kafin la'asar yazo sai mu tafi dan jibi Abuja zamu koma daga chan ma ya ce zasu wuce Lagos shida uwargida idan kwanata ya zagayo"

"OK Allah ya kara had'a kanku" Da Amin Zainab ta amsa sannan sukayi sallama.

White rice da stew tayi wanda yaji naman kaza taso yanka ganye a kai amma babu wanda zata aika.

Bata ci abincin ba ta zauna zaman jiranshi har yamma be dawo ba kuma ta kira wayarsa a kashe. Gaba daya bata jin dadin gidan.

Bayan tayi salkar magariba ta sake wanka ta saka doguwar riga me kyau amma mara nauyi.

Gamin yunwa na nema halakata yasa ta zuba abincin taci. Sai da akayi salkar ishai ya dawo.

Tana zaune a falo tana kallo taji sallmarsa. Kallonsa tayi sannna ta amsa tana fadin " Sannu da zuwa"

Murmushi yayi ma tabyana fadin " Ayi hakuri yau nayi laifi, Sule ne ya takura sai na zaga gari dashi shiyasa"

Ya karashe maganar yana zama kusa da ita. "Kinyi kyau" Ya fada yana kallonta.

K'asa tayi da kanta tana murmushi. "Sarkin kunya! Banci komai ba kawo min abinci"

Ya fada yana kallon TV.

Sai da ta kara warming din abincin sannan ta kawo masa.

"Amarya da heavy food haka? Ya fada yana fara cin abincin.

Bata ce komai ba sai murmushi kawai ds tayi.

"Kazar amarcin ki ma baki ci ba tana fridge" Ya fada yana nuna fridge din dake falo.

Bata ce dashi komai ba shima bai kara magana ba har ya gama cin abincin.

Sun dade a falo suna kallo har kusan 12am sannan ya kalleta ya ce " Bakya jin bacci?

Sai a lokacin ta samu courage din cewa " Kayi hakuri"

"Hakuri kuma Zarah? Me kikayi?

Shuru tayi dan itama bazata ce masa ga abinda tayi ba tasan dai bata kyauta ba.

"Amarya ai bata laifi ko ta kashe dan masu gida, tashi kije ki kwanta"

A sukwane ta tashi ta nufi dakinta, bayanta yabi da kallo yana murmushi.

Har bacci ya dauketa bata daina tunaninsa ba.

Washe_gari.

Karfe 11 saura su Inna suka zo har da Ummie da Zainab.

Tasha nasihohi sosai dan shima anyi masa nasa jiya. Sun kara zaga gidan sosai sai yamma sai Zainab ta tafi Ummie kuwa cewa tayi taga gidan zama babu inda zata tafi.

Sai bayan magariba Zayd ya mayar dasu Inna gida suna ta saka musu albarka.

Zarah na yi wa Ummie yankan farce Zayd ya shigo gidan yana kallonsu ya ce " Yanakan farce da daddaren nan salan ki yanke ta?

"Yayi tsaho dayawa dazu ta jimin ciwo" Zarah ta fada tana kallonsa.

Zama yay yana kallon Ummie ya ce " Kwakwis!

Turb'une fuska Ummie tayi tana kallon Zarah ta ce " Umma kinga shi ko?

"Shima ai kwakwis ne, baki ga kansa ba? Zarah ta fada tana murmushi.

"Amma nawa gashin yafi naki kyan gani ke kham kai kamar kwarya"

Zayd ya fada yana dariya.

Kuka Ummie ta saka tana kallonsa. "Ka gani ko? Kasan halinta yanzu bacci sai ya gagaremu"

"Ai dama yau ba bacci, hakurina ya kare" Ya fada yana daukar Ummie ya shiga daki yana rarrashinta.

Farcen data yanke ma ta ta zuba a dustbin sannan ta shiga dakinta.



*SABIR!* *SABIR!* Wai ni sa'ar ka ce ne? Bani biro na ina da abunyi fa"

Unbolo yayi ma ta yana fadin " Zoki ki kwata"

Dafa goshi Ummie tayi tana harararsa ta ce " Zan hadaka da Mama"

Kafin yayi magana yaji muryar mahaifinsa ya ce " Kai Sabir! Sa'ar kace? Ko an fada maka yayarka ce? She's like your mother"

"Kai! Daddy! Wannan yarinyar? Ya fada yana nuna Ummie.

Sake hade rai Yusuf yayi yana fadin " Ita fa! Daga yau kuma Aunty Ummie nake so naji kana cewa, ke kuma ki cigaba da sakar masa fuska"

Shuru Ummie tayi tana yin k'asa da kanta. Ficewa yayi ya barsu da sauri Sabir yazo inda take yana fadin " Daddy na ya aureki ne bayan tafiyar Mummy na?

Dariyata tuntsire da ita tana karbar bironta ta ce " A'a, Yaya Farooq ne ya aureni"

"Uncle Farooq? Ya fada yana zama kusa da ita. "Eh" Ta bashi amsa tana kallonsa. " Daddy ya ce min ya tafi wani aiki ba yanzu zai dawo ba meyasa baki bishi ba?

"Saboda makaranta" Tavfada tsna fara aikin Assignment dinta.

"OK, zan dinga ce miki Aunty amma nima zaki dinga ce min Handsome kin yarda?

Murmushi tayi ta ce " Waye yace maka kai Handsome ne?

"Mummy mana ta ce idan na kara girma na zama saurayi 'yanmata zasu dinga fad'a a kaina, kuma kinsan me? Ni balarabiya zan auro idan na girma nayi kudi"

"Toh Allah ya tabbatar" Ummie ta fada tana dariya.

"Amin, birthday naya kusa ki tanadi gift"

"Shekara nawa? Ta fada tana kallonsa. " 13yrs mana"

"Kai Sabir! Haji muryarta mamansa a kansa. Da sauri ya kalleta ranta a had'e ta ce " Uban me kake yi a nan?

"Bakomai" Ya fad'a yana tshi tsaye. Wani banzan kallo tayi wa Ummie tana fadin " Mama ta ce ki fora abincin rana"

Da toh Ummie ta amsa tana ajiye Aikin makarantar ta nufi kitchen ita kuma taja hannun Sabir suka bar falon. Tana cikin girkin tajiyo muryar Mama tana kiran Aunty Ramlah.

Fitowa tayi daga kitchen din tana fadin 'Tana sama"

"Water yake girki toh?
Mama ta fada tana k'arasowa kitchen din.

Ganin ba kowa sai Ummie yasata fadin " Ke Ramlat ta bari da aiki? Ba Assignment kika ce zakiyi ba? Karfe nawa yanzu? 12 saura fa? Kuma kina da class karfe 1 na rana!

Bata jira cewar Ummie ba ta koma falo tana kwallawa Ramlah kira ranta a matukar b'ace......

*sorry for the typing errors*

Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 20" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1184208159?utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&utm_source=android

*Please subscribe, and like my YouTube channel*

https://youtu.be/9m2j2vaiKjw

Aslm ma abota biyan littafin Momin Haneef ce tana sanar daku littafin ta na ak'idar masarautar.

littafin nakud'ine idan kina buk'ata zaki iya fara biya tunkafin free page yak'are gamai son littafin ak'idar masarautar zai turo da kud'insa ta wannan account👇

Nusaiba Rabi'u Union Bank 0087778987

Idan kuma katine zaku turo katin MTN ta wannan number👇
07026368879

Bamuson vtu bazamu kar b'aba

Idan kinturo kud'in zaki turo mana da shaidan kin biya ta wannan number07026368879

Normal group 300 only
Zakuna samun page d'aya (1 )arana

Special group 400👇
Zakuna samun page biyu (2) arana duk Wanda kikaga yamiki sai kishi ga.

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)

𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.

*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...


*K'ANWATA*

*Dandano!Dandano!!*


Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..


Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573


Nomal. guda d'aya N 300 ne

guda biyu N 500 ne


Special guda d'aya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne


Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Shafi na Ashirin*

Ya kasa zama kwata² hankalinsa yayi matukar tashi gaba d'aya hankalinsa baya jikinsa.

Wani doctor ne ya fito daga d'akin tiyata yana wuce Yusuf. Da sauri Yusuf ya bi bayansa yana fad'in " Ya ake ciki?

"For now bazamu iya cewa komai ba musanman shi d'ayan da suka harba a k'irji saitin zuciya"

Daga haka ya bar Yusuf da kullewar ciki sam be lura cewa a saitin zuciya aka harbi k'aninsa ba.

ACP ne ya dafa shi cikin son kwantar masa da hankali ya ce " Insha Allah komai zaizo da sauk'i"

Shuru Yusuf yayi yana zama a kujera gumi na keto masa.

Yana zaune doctors biyu suka kuma shiga wajen tiyatar.

Anfi 4 hours har bayan sallar asuba wajen 6 sannan likitoci da nurses suka fara firfitowa.

Da sauri ya nufi wajen wani likita yana fad'in "Ya ake ciki?

"They are out of danger ins ha Allah sai daj bazamu ce komai ba gamr da lafiyarsu sai munga sun tashi it can be possible Sufi slipping into a coma and me harbi daga baya zuwa ciki gaskiya ya d'an tab'a masa laka, shi kuma me harbi kusa da chest d'insa nan da three days zamu kuma masa hoto, ma'aikatan tsaro kuma is not that serious Allah said ya basu lafiya"

Daga haka ya bar Yusuf idanunsa sunyi ja, yanzu me zaice Zarah? Me zai cewa Mahaifiyar Zayd?

Da kyar ya iya zama a kujera yana dafa kansa gaba d'aya duniyar tayi masa zafi.

Yana zaune aka fito dasu, da ido kawai ya bisu dan baya ji ma zai iya tashi. ICU aka nufa da Zayd da kuma Farooq.

Da kyat ACP yayi convincing Yusuf suka tafi gidansa.

Anan Yusuf yayi wanka ya canza kaya amma ko ruwa be kai cikinsa ba duk da kokarin ACP.

By 10am suka dawo asibitin. ICU suka tafi riga aka basu suka saka da hula sannan suka canza takalmi suka shiga.

Ko wanne a kwance kamar gawa amma na'ura na nuna cewa suna da rayuwa.

Kwallah ne ya cika idon Yusuf, shi yanzu bashi da courage d'in da zai kira Zarah ya sanar da ita halin da ake ciki, ji yake dama shi harbin ya samu ba Zayd ba.

Basu wani dad'e a ciki ba suka fito.

"Yusuf ya kama ta ace iyalan Shi abokin naka sun sani dan bamu san ranar farkawarsa ba"

Iska ya furzar me d'umi kafin ya ce " Bansan me zan fad'awa matarsa ba, bansan ya zata d'auki maganar ba, just 4-5days fa da aurensa"

Dafa kad'arsa ACP yayi sannan ya ce " Dole hakannan zaka fad'a musu, ko kuma ka koma Kano sai ku taho tare"

"Shikenan"
Cewar Yusuf yana tashi tsaye.

"Yanzu zan tafi dan bana so na kwana a Kano"

"Shikenan muje nayi excorting d'inka zuwa filin jirgi"

Baba daya Yusuf be san me zai cewa Zarah ba hankalinsa ya tadhi matuka.

Tun saukarsa a Kano ya hau napep zuwa Gidan Zayd yafi minti goma sha biyar a kofar gidan kafin ya d'aga hannu ya fara knocking.

Zarah dake shirin fitowa dan zuwa gidan Aunty, ta bude kofar. Kallon² suka tsaya yi sosai gabanta yayi wani mummunan fad'uwa. Muryarta na d'an rawa ta ce " I...ina Zayd?


Shuru Yusuf yayi ya kasa uttering ko da word d'aya ne.

"Muje saga ciki Zayd yana lafiya" Yusuf ya fada yana shigowa compound d'in gidan.

Biyosa tayi ta ce " Ina mijina?

"Zarah relax please mijinki yana lafiya"

"Ka fad'a min gaskiya" Ta fada hawaye na biyo kuncinta.

"Actually nun hadu da accident ne kuma Zayd ya karye a kafa amma yana nan lafiya shi ya ce ma na dawo na d'aukeki saboda ki kula dashi"

Tsayawa tayi tana kallonsa zuciyarta tak'i gamsuwa da abinda yake fad'a ma ta, tana ji a jikinta kamar wani abu munnuna ya faru da Zayd.

"Muje karmu b'ata lokaci kinji? "Mahaifiyarsa fa?

Zarah ta fad'a tana kallonsa. "Muje gidan na ta mu tafi tare da ita sai yafi jin dadi ma"

"Yusuf! Ta kira sunansa.

Be yarda ya kalleta ba ya ce " Muje Zarah dan akwai flight din da za I tashi by 3 inaso mu sameshi"

Gabansa ta dawo tana kallonsa ta ce " Zayd ya rasu ko?

"Wace iriyar magana ce wannan? Ya fada amma be kalleta ba.

"Idan ba haka ba meyasa zaka dawo cikin wannsn yanayin? Ka fad'a min gaskiya! Ta fada tana fashewa da wani irin kuka.

"Zayd yana raye kawai karaya ce ya samu"

"Naji a jikina wani abu mara kyau ya samu mijina, Dan Allah ka fad'a min"

Shuru yati zuciyarsa n karaya dan Zarah ta bashi tausayi, destiny is testing her yarinyar tana shan wahalar rayuwa, aurenta na farko bata ji dadinsa ta jure wahala na tsahon 8 years, lokacin da zata samu farinciki kuma ga wani tashin hankalin abinda yafi damunsa shine harbin ya taba wa Zayd laka wanda da wuya ya cigaba da tafiya dan daga abinda yayi cikinsa zuwa kafafuwa basu sake aiki ba sai dai wani ikon Allah.

Kasa daurewa yayi ya tsugunna yana jin hawaye sun cika masa idanunsa.

"Na sani dama! Tunda Zayd zai tafi naji bana son tafiyar, kun kashe min mijina kun huta ta fada tana sa hannu ta ture Yusuf ya fad'i a kasa.

Itama fad'uwar tayi tana fashe da wani kuka zuciyarta na yi ma ta wani irin radad'i.

Tashi tsaye yayi ya ce " Zarah Zayd be mutu ba na rantse miki, please ki tashi mu tafi"

Wani banzan kallo tayi masa tana tashi tsaye ta nufi hanyar fita daga gidan da gudu.

Bin bayanta yayi bayan ya rufo gidan, rikota yayi ganin kamar ta zare.

"Me haka Zarah?

Kokarin kwace hannunta take yi amma ta kasa.
Shi ya tsarar musu napep zuwa gidan Aunty.

Aunty na wanke² ta gansu sun shigo Zarah na tafiya kamar ba mutun ba idanunta kyar waje d'aya. Da sauri ta tashi tana kallonsu ta ce " Yallab'ai me ya faru haka?

"Mama, ko d'auko hijabi zamu tafi Abuja"

"Zayd ya rasu ko? Aunty ta fad'a tana kallonsa.

Girgiza kai yayi sannan ya ce " Be rasu ba"

Bata k'ara cewa komai ba ta shiga d'aki sai data kashe komai na gidan sannan ta fito tasan cewa Zayd ya rasu dan tun ba yau ba take jin jikinta ba dadi ga yawan bari da faduwar gaba da takeyi ashe Zayd ne zai rasu.

Har suka isa Abuja babu wanda yayi magana. ACP ne ya d'auko su a airport suka wuce asibiti.

Ko takalmi Zarah bata cire ba ta shiga ICU da gudu, inda Zayd yake kwance ta nufa tana masa wata iriyar runguma dan duk zatonta gawar sace a kwance dan bata lura da komai.

Nurses ne suka zo kanta ana kokarin b'anb'areta daga jikinsa.

"Zarah d'agashi bashi da lafiya"

Yusuf ya fad'a yana yi wa nurses din Alana dasu matsa. Matsawa sukayi shi da kanshi ya cire Zarah daga jikin Zayd ya gyara masa abinda aka lullubeshi.

"Ka ce min karyewa yayi? Meyasa zaka yi min karya? Meyasa! Ta fad'a tana chakumar wuyan Yusuf idanunta sunyi jajawur.

"Please take her out"
Wata nurse ta fad'a tana kallon Yusuf.

Aunty kuwa ACP ya sanar da ita ba mutuwa yayi ba addua tayi masa ta fito.

"Muje? Yusuf ya fad'a yana nuna ma ta hanyar fita. Wani matsiyacin kallo tayi masa kafin ta koma kusa da Zayd ta riko hannunta cikin muryar kuka ta ce " Dan Allah karkayi min haka"

"Please Sir take her out bama son hayaniya",

Nurse din ta sake fad'a.

Sai a lokacin da Zarah ta tashi zata fito ta hango Farooq. "Toh me ya faru haka? Ko dashi akayi hatsarin? Ko dai mutanen da suka kamashi ne suka harbi shi shida Zayd?

A hankali ta k'arasa inda yake jikin abinda aka rufeshi duk jini ya b'ata, Hannu tasa ta cire sheet din, tsaga ta gani a jikinsa sosai kusa da gefen zuciyarsa.

Da sauri ta rufe tana d'agowa ta kalli Yusuf. K'arasowa yayi inda take ya riko ta suka fito ganin tana shirin fad'uwa. Zaunar sa ita yayi kusa da Aunty, sannan ya sanar dasu duk abinda ya faru, sosai Zarah ta ke kuka.

"Yanzu kana nufin bazai sake takawaba? Aunty ta fada cikin tashin hankali.

"A'a insha Allah idan ya farfad'o zamu kaishi waje domin chan sunfi nan kayan aiki insha Allah komai zai wuce"

"Allah yasa, shi kuma Farookun fa?

"Insha Allah babu wata matsala kawai dai za'a d'orashi a kan maganine da zarar ya farfad'o dan bullet din be tab'a masa heart ba"

"Allah ya basu lafiya" Aunty ta fad'a cike da damuwa.

Da Amin suka amsa banda Zarah da magana ta gagareta.

"Zamuyi booking hotel saboda ku samu wajen kwana"

Yusuf ya fad'a yana tashi tsaye.

"Is not safe their Yusuf, akwai empty room a gidan zansa ta gyara musu inyaso ni da kai sai mu kwana d'aki daya"

Girgiza kai Yusuf yayi sannan ya ce " A'a ACP abun kuma sai yayi yawa"

Dafa kafad'arsa ACP yayi yana d'an murmushi ya ce " Karka damu"


*KANO*

Tunda suka dawo daga asbiti Mama ke kiran number Zayd amma not reachable, sai wajejen 8pm sannan ta samu ta shiga.

Har tagama ringing be d'auka ba. Ummie ce ta karbi wayar daga hannunta tana fad'in "Dan Allah Mama ki kwantar da hankalinki bari na cigaba da Kira"

Mama dai bata ce komai ba, sau uku Ummie tana kira be d'auka sai a na hud'un.

Yana dauka ta mik'awa Mama.

"Yusuf ina Farooq?
"Mama yana nan lafiya zuwa next week zamu dawo insha Allah ya samu karaya ne a kafarsa"

Wani irin ajiyar zuciya Mama ta sauke kafin ta ce " Toh Allah ya dawo daku lafiya bashi wayar"

"Ai asibitin dana kaishi ba'a barin a zauna, ki kwantar da hankalinki yana nan lafiya"

"Ton Yusuf ka kula dashi kaji? Da toh ya amsa sannan sukayi sallama.

"Ya Yaya Farooq din? Ummie ta fad'a tana kallonta.

" Ya samu karaya a kafa amma Yusuf ya ce da sauki"

"Allah ya kara sauki" Ummie ta fada tana kwanciya kusa da Mama dan itama sai yanzun ta samu kwanciyar hankali...



Banda ihu da kururwa babu abinda take ji jikinta sai radad'i yake da ciki da uban dukan da Shehu yake yi ma ta.

Yarda belt d'in yayi ransa a matukar b'ace ya ce " Waye ubanki da zaki zagi nata uban?

"Allah ya isana wallahi shegu dan kutmar uba wanda be gaji mutunci ba dan akuya"

Cewar Sa'adah tana hararasa. "Ke! Ni kike yi wa Wanna zagin? Ya fad'a cikin tsananin b'acin rai.

Banza tayi dashi. Batayi aune taji ya fara yin kutufo da ita yana zuba mata maruka ta ko ina. Ihu ta saka me karfi dan wani irin ciwo da mararta yayi. Fita yayi ya barta a d'akin, Ummie na kitchen tana wanke² taga fitarsa. Tab'a baki tayi ta ce " Yau Aunty sa'adah ta dandana yadda Ummana take ji"

Saleh ne ya shigo kitchen din yana binta da wani shegen kallon. Tsaki tayi a fili tana d'auraye hannunta ta ce " Bani hanya"

"Kwakwis" Ya fad'a yana zame ma ta hular kanta duk da cewa gashi ya tofo ya kwanta"

"Kaima ai kwakwis ne" Ta fad'a tana kokarin fita daga kitchen din.

Rik'o hannunta yayi da sauri ta kwace ta ce" Karka k'ara tabani, Ummana ta ce ba kyau"

Dariya ya feshe da ita yana fadin " Lallai! Shekararki nawa wai? 9yrs fa? Mtsww dallah wuce in taba ki inji me? Ke ba nono ba ke ba d'uwawu ba"

"Wanda nake dashi said ka kwace"

Daga haka ta fice ta barshi a kitchen.

"Lallai ma wannan yarinyar wato ya lura tun bayan dawowarta daga bikin uwarta ta koyi yab'a masa magana" Kwafa yayi sannan shima ya fito daga kitchen d'in.

*Some days later*


*sorry for the typing errors*

Autar Mama ce.

✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 22" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1185191016?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=i7vjLl4Pap4KVxPR1R%2FXMiDiN7bEkc4p0j%2FGRgYRt09jMW%2F8HSdaREb9P6QC%2BRO2fBWgsAo4KlEgvrub%2FKYUkFaYgMU%2Bom8w1cy6QsJ5wBqV5uu4GZY0wW7A%2Bi9So6qh

*Please subscribe, and like my YouTube channel*

https://youtu.be/9m2j2vaiKjw

Aslm ma abota biyan littafin Momin Haneef ce tana sanar daku littafin ta na ak'idar masarautar.

littafin nakud'ine idan kina buk'ata zaki iya fara biya tunkafin free page yak'are gamai son littafin ak'idar masarautar zai turo da kud'insa ta wannan account👇

Nusaiba Rabi'u Union Bank 0087778987

Idan kuma katine zaku turo katin MTN ta wannan number👇
07026368879

Bamuson vtu bazamu kar b'aba

Idan kinturo kud'in zaki turo mana da shaidan kin biya ta wannan number07026368879

Normal group 300 only
Zakuna samun page d'aya (1 )arana

Special group 400👇
Zakuna samun page biyu (2) arana duk Wanda kikaga yamiki sai kishi ga.

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku

Please Login or Register in order to submit comment